← Book details Sanadin Soyayyar Shan Minti Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 16

Sashe 11

Sanadin Soyayyar Shan Minti Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda su Yaya suka tafi Mama ta tashi tayi kalaci sannan tayi wanka ta zauna, duk da abun duniya ya isheta amman hakan bai hana Mama yi man addua ba,tana zaune Yaro yayi sallama yace. "Wai Aminu yace yana son magana da Khadija." shiru Mama tayi tana kallon Yaron da Aminu ya aiko sannan tace. "Maza kaje kace mashi ya shigo daga cikin gida." tafiya yaron yayi yana cewa. "To shikenan." bayan ya fita compound din gidanmu ya tadda Aminu jingina a jikin motarshi sannan yace mashi. "Mamanta tace ka shigo daga cikin gida." murmushi Aminu yayi sannan yace. "To shikenan nagode sosai kaji boy." tafiya yaron yayi yana murna, haka Aminu ya shigo har parlour sannan ya zauna ya gaida Mama, ansawa Mama tayi sannan tace. "Aminu ya ka baro gida da kuma mutanen gida."? Cikin jin kunya yace. "Duk suna lafiya Mama, kuma suna gaisheku." murmushi Mama tayi duk da tana cikin damuwa amman tayi kokarin boye ta tace. "Allah sarki ina ansawa, Aminu sai dai kayi hakuri dakai ni mu baki ɗaya, amman Am... "Mama dan Allah karkice ba zaki auran man Khadija ba dan wannan kaddarar ta hau kanta, wallahi ina sonta a haka mudun ba Khadija ba ba zan iya auren ko wace mace ba, na roƙeki karki yi man haka."ya ida maganar yana hawaye, itama Mama hawayen take dan tasan nayi rashin masoyin gaskiya, girgiza kai Mama tayi tana murmushi mai ciwo sanann tace. "Da ina hali da gobe zan sa a daura maka aure da Khadija da na yi imani da kana kaunarta sai dai bani da yanda zanyi dan Khadija ta haɗa kayanta ta gudu ta barmu dan kawai nace zan ɗaura mata Alhaji Salahu." tashi yayi tsaya yana cewa. "Inalillahi wa'inna'alaihijirun, Allahunma'ajirni fi'masifati wa'akirni khari manha(note:-Idan kunga mistake wajen rubuta Addu'a ba laifina bane bani da zaɓi ne dan ba komai na iya rubutawa da hausa ba, dan hausa tana da wahala sosai😢, sai kuyi man uzuri my dear's fan's 🥰) hawaye yake sosai sannan yace. "Mama tunda kin yarda da zaki aura man Khadija nayi maki alkwarin zan nemota duk inda ta shiga a faɗin duniyar nan, dan itace rayuwa ta, Allah ya jarabeni da ciwon sonta dan Allah Mama karkice banda kunya ina faɗin haka a gabanki bason ya zanyi control din son Khadija bane, ni zan tafi neman Khadija Mama." tashi Mama tayi da sauri ta rike hannun rigar Aminu tana hawaye tace. "Aa Aminu ban yarda kaje neman Khadija ba, dan ko kaje ba ganinta zakayi ba kuma Jamilu ya bada cigiyar ta, kaje ka zauna gida idan ta dawo zan gaya maka, idan kuma ba'a ganta ba sai kayi hakuri sannan kayi Addu'a Allah ya baka wanda tafi Khadija." kuka Aminu ya tashe dashi sannan yace. "Mama nine ya dace da nemo Khadija duk inda ta shiga a kasarnan ba Yaya Jamilu ba, tunda ni zan zama miji a gareta dan Allah Mama na roƙeki ki barni na nemota abunda nike bukata a wajenki shine ki saman albarka a matsayinki na mahaifiya ta Mama." ya ida maganar yana haɗa hannun wanshi waje ɗaya, cewa Mama tayi. "Allah yayi maka albarka Aminu amman ban yarda da kaje neman Khadija ba, sannan ban cika son musu ba." ɗaga kai yayi alamar to sanann yace. "To Mama ba zanje ba, amman Mama ba zan taɓa yin aure ba har sai Khadija ta dawo gareni zan mata addu'ar dawowa lafiya, zan tafi Mama na barki lafiya." haka ya tafi ya bar Mama tsaye ko motsi ta kasa, sai yanzun take yin nadamar abunda tayi sai yanzun ta gane abunda su Yaya Jamilu suke gudu kenan amman ta kasa fahimta cewa tayi. "Kaicona ni Hafsat, tir da mai hali irin nawa mai shegen zuciyar tsiya da zafin rai, na biye ma zuciya naƙi yarda da kaddarar da Alllah ya kawo man a gida, gashi nayi sillar gudumwar marainiyar Allah, wayyo Allah na." haka Mama ta kama cewa tana kuka mai tsuma rai.

*~~~~~~~~~~~~~~~*

Hirji

*waiwaye*

Share hawaye na nayi sannan nace. "Ni sunana Khadija Bello, amman ana kirana da Auta a gidanmu kenan, ƙawaye a kuwa suna kirana da black beauty, na taso cikin gata gaba da baya duk da cewa ina da wata biyar cikij ciki Allah yayi ma mahaifina rasuwa, amman bansan wani abu wai shi maraici ba, ban taɓa neman abu na rasa ba a duniya dan da bansan Baba ya rasu ba, dan nasa Yayana Jamilu shine Babana yanda yake nuna man gata ko ƴarshi babba wanda na ba shekara ɗaya a duniya baya nuna mata irin son da yake man, dan saboda ni yasa mata suna Khadija itama amman ana kiran ta da Dejja komai tare ake yi mana shi nida Dijje sai dai fita gata tunda ni na kasance Auta kowa so yake nace gidanshi zani hutu, dan ko har rigima yaiyena suke akan kowa yana son nace gidanshi zani sai Mama take raba gardama tace bani zuwa wajen kowa."

Hawaye ta kuma sherewa sannann tace. "Mu biyar ne iyayen mu suka haifa a duniya, Jamilu ne babba sannan Fatima sai Amina daga Amina sai Aisha sannan ni ni kuma Khadija, ina primary one akayi ma Yaya Fatima aure, tana auren wani babban dan'siyasa a cikin birnin katsina dan har cikin lefenta sai da yasa key din mota sannan kuma bayan biki ya kai duka gidanmu hajji harda ni duk ban da wayau a lokacin, soyayya ina ganinta sosai har abun ya wuce a gayashi ban taɓa neman abu na rasa ba, sannan kuma ba'a taɓa yi man faɗi a gidanmu komai nayi dai-dai ne, gwara ma Yaya Fatima itace idan nayi laifi takan yi man haragaga ta dan tsorata, amman duk ranar da tayi man haka zata sha faɗa ne wajen Yaya Jamilu yace ya lura ta matsaman tana son hanani rawae gaban hatsin, shiyasa ban damu da na cika zuwa gidanta ba, dan ko Yaya Amina bata son ko ƙuda ya taɓani balle akai da faɗa shiyasa nike yawan zuwa gidanta kuma komai nike so komai tsadarshi tana yi man shi bata taɓa ceman babu ba kuma bata taɓa ko dungurina balle tasa hannu ta bugeni ita ina js one akayi aurenta tana auren babban dan'kasuwa a cikin jahar katsina dan kasashe kasashe yake zuwa business dinshi, idan ko ina gidan zasu wata kasa dani ake tafiya danko nasha zuwa america da london bansan adadi ba, yaran Yaya Amina uku duka maza ne, amman basu zaune wajenta suna wajen kakarsu ta wajen Uba a nijer take zaune wajen Yayanshi da zama ya maidashi nijer baki ɗaya, amman aunty Fatima bata taɓa haihuwa ba amman tayi ɓari sau uku, shiyasa ta dan huta daukar ciki tana zuwa india ana bata magani yanda mahaifarta zatayi kwari sosai har ta ringa riƙe ciki ya kai ranar haihuwa wannan kenan."

"Itako Yaya Aisha ina SS 3 akayi bikinta da wani lecturer din Umaru musa yar'adua university katsina, anan makarantar suka hadu har akayi aurensu itama tana da yara biyu mace da namiji, tunda na kai SS2 na fara yin samari kala kala sai dai bani kula ko ɗaya daga ciknsu dan ba wannan bane a gabana karatu ne a gabana, dan Yaya Jamilu yasha gaya man yana son na zama likita sai diyarshi Dejja ta lawyer haka yake yawan gaya mana shiuasa yasa mana son karatun a cikin zuciyar mu tun muna ƙananan mu, ya kuma tusa mana tsanar soyayya ba tare da mun gama karatu ba, da wannan tarbiyar na tashi bani kula ko wane namiji duk kyunshi kuma duk kudinshi nidai abunda nasan Yaya yace shine mu maida hankali wajen karatunmu yanda zamuyi achieving din future dinmu, amman yace idan muka sa soyayya a hidimar ba zamu maida hankali ba, balle har mu zama likita da kuma lawyer."

"A 2011 mukayi candyn secondary school dinmu, sannan kuma a shekarar muka samu admission a buk kano, kamar yanda Yaya ya tsara mana haka ta kasance ni na samu medicine and surgery ita kuma Dejja ta samu Islamic low, haka muka fara karatunmu girma girma da arziki,tunda naje jami'a na hadu da wata ƙawa Aziza ita ta saman suna BEAUTY, duk ni baƙa ce amman ina da kyau ba laifi dan ina da manya idanu kuma ina da hanci da ƙaramin baki, room dinmu ɗaya tare muke yin komai da Aziza sai dai halinmu ba ɗaya ba, dan ita tana yin soyayya ni kuma bani soyayya dan bamu fara riƙe waya ba sai da zamu shigo university sannan Yaya ya siya mana waya nida Dejja, tunda Dejja ta lura da Aziza tana da rawar kai ta fara nuna man mu rabu da ita dan bata ga hankali a wajen Aziza ba, amman ni sai na nuna mata idan muna tare da ita sai mu jata jiki ta zama irin halinmu, amman idan muka rabu da ita ai sai ta ida lalacewa ya kamata muyi jahadi wajen gyara ma Aziza tarbiyar ta, ba dan Dejja taso ba ta yarda da gurguwae shawarata ba, dan Yaya yasha gaya mata karta kuskura tayi gardama dani koda kuwa sau ɗaya ne a rayuwar ta mudun tayi gardama dani to kamar tayi gardama dashi ko kuma su Yaya Fatima tunda nona ɗaya nasha dasu, dan kuwa Aunty Auta take ceman, shiyasa Dejja bata gardama dani koda kuwa taga inayin ba daidai ba sai dai ta kira Yaya Fatima ta gaya mata dan ta lura cikinsu ita ɗaya ce kawai take man faɗa idan nayi abu ba daidai ba, idan ma ta kama sai ta zaneni da bulala ba ruwanta shiyasa bani zuwa gidanta idan ba ita ta matsaman akan sai nazo nayi mata hutu ba."
Chapter 11 · 0% Book details