← Book details Sanadin Soyayyar Shan Minti Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 16

Sashe 7

Sanadin Soyayyar Shan Minti Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin murmushi da jindadi Alhaji Salahu yace. "Haba Hajiya daman abunda kika zo kice man kenan harda kuka? Ai ba wani abu bane daman na jima da son Khadija a cikin zuciya ta gayawane kawai banyi ba amman ko maiyasa kike son aura man ita." cikin farinciki da sakin fuska yayi maganar dan shi gode ma Allah yake cikin zuciyar shi, cikin tsoro Mama ta fara maganar. "Alhaji ba zan boye maka komai ba tunda kaine wanda zata aura, Khadija dai ciki tayi amman a halin yanzun cikin ya zube tana asibiti so nike tana dawowa ta ida samun sauki sai ayi bikin naku ko lefe karda ka kawo sadaki kawai zaka kawo dubu 20."

Washe kazamin bakin shi yayi sannan yace. "Idan wanann ne ai ba damuwa, shikenan amman ina son a daura auren nan da sati biyu masu zuwa Hajiya." cikin jindadi Mama tace. "Insha Allah, Alhaji nagode sosai Allah ya ƙara girma da buɗe, yanda karufa mana asiri kaima Allah ya rufa maka." washe baki kawai yake haka ya rako Mama har kofar gida yana ce mata sai ya shigo ganina idan muka dawo daga asibiti dan shi baya son zuwa asibiti da can ma yaje ya fara duba lafiya ta, ita ko Mama sai dadi takeji gani take ta gama yi man gata ta samaman wanda zan aura ya rufa man asiri a cewarta.

Koda taga motar Yaya Jamilu da ta Yaya Fatima a kofar gida tasan suna cikin gida shiyasa ta chanza fuska ta dauki mataki tun a waje dan tace ba wanda ya isa ya hanata aura mani Alhaji Salahu koda dangin mahaifinane dan basu tsinata mata tsiyar komai ba lokacin da Babana ya rasu dan haka basu da iko a kanmu daman tasha cewa haka shiyasa ba wani zuminci muke da dangin Baba ba saboda rashin jituwa dake tsakaninsu da Mama.

Koda ta shigo samun waje tayi ta zauna ta kama kallonsu daya bayan daya sannan tace. "Jamilu ya jikin Auta fatan dai komai yana tafiya dai dai."? Kallonta yayi sannan yace"lafiya lau Mama, amman muna son muyi wata magana dake dan Allah Mama." duk da tasan maganar da zasuyi mata dan tasan Yaya Amina ta gaya masu yanda sukayi da ita, amman sai ta wayance tace masu. "Ina sauraranka Jamilu wani abu ke faruwa ne? Duk na ganku kamar ba lafiya kodai wani abu ke faruwa da Auta ne."? Girgiza mata kai Yaya Jamilu yayi yana hawaye, saukowa yayi ya durkusa kasa ya kama kafafunta yana hawaye yace. "Dan girman Allah Mama, ki duba maraicinmu bamu da kowa sai ke, ke daya ce muke gani muji dadi nida yan'uwana mahaifinmu ya rasu, dan Allah Mama munzo neman alfarma a wajenki dan Allah karda kice ba zaki yi mana wannan alfarma ba Mama."ya ida maganar yana kuka dan Mama tasha gaban shi sosai tunda itace mahaifiyarmu dole ya bita a sannu dan ya shawo kan matsalar a sannu da dai ace ba Mama bace wata ce daban to da karfin tsiya sai ya anso man hakina amman yanzun dole su bi a hankali su shawo kan Mama ta fasa auraman Alhaji Salahu .

Kallonshi Mama tayi tana shafa mashi kai alamun lailashi yana daina kuka, sannan tace. "Jamilu inajinka wata alfarma ce wannan zaku tambayeni harka kai kuka suma kuka, karku tadda man hankali mana gaya man ina sauraran ka idan baka iya gayaman sai ke Bintu ke gaya man." shiru Yaya Jamilu yayi sannan yace. "Mama dan Allah karda ki aura ma Auta wannan tsohon mutumin, Mama karkizo daga baya kina cizon yatsa kina da nasani, Mama dan Allah karki ɓata rayuwar Auta da kanki wannan auren da kike niyar yi mata wallahi shine babban kuskuren da zaki aika a rayuwarki sanna... Cikin fushi Mama ta katse Yaya Jamilu tana cewa. "Yi man shiru Jamilu wallahi ko yanzun nayi maka baki, har ka isa kace zan tabka babban kuskure dan zanyi ma Khadija Aura, Auren shine kuskure ko kuma cikin da tayi ta hanyar zina bai zama kuskure ba sai Aurar da ita zai zama kuskure? Dan ubanka gaya man wa zai iya aurenka bayan ta bayar da budurcinta bisa titi? Gatan da zan mata shi ne zai zama kuskure Jamilu? Anya Jamilu kana neman albarka ubangiji Allah kuwa? Ace ni Uwarka mahaifiya zaka sa gaba kana gaya mata magana son ranka kana gaya mata abunda duk yazo bakin ka sai kace kaine ubana."? Kuka Mama ta fashe dashi tana cewa."tabbas haka maganar take da akace baiwa zata haifi uwargiyarta yau ga abun yazo kaina, kunan duk kun haɗaman kai baku yarda na aura ma Khadija Salahu ba ko? To ku sani nan da sati biyu za'a daura masu aure akan sadaki naira dubu 20 kuma ko lefe bance ya kawo ba, sai dai ku mutu idan kun tashi. "

Cikin kuka Yaya Fatima tace. "Wallahi Mama karki ce muna maki rashin kunya amman dole mu gayamaki gaskiya a matsayinki na mahaifiyarmu wallahi Mama mudun kika ce zaki aura ma Khadija wannan tsohon banzan to kin ɓata mata future kuma daga baya sai kindawo kina da nasani marar amfani Mama, ya kamata ki duba wannan maganar tamu idan auran kike so yi mata a bari ta dawo sai ta fidda wanda take so cikin samarinta na tabbata cikin akwai nagari mai sonta tsakani ga Allah, wanda zai aureta koda ko ta haifi cikin da tayi balle ma yanzun da ba cikin a jikinta ya dace kiyi tunani Mama ki duba gaba Mama ba'a duba baya idan ta wuce mun roƙeki wannan alfarmar Mama."

Shiru Mama tayi tana kallon Yaya Fatima yanda ta gaya mata magana har haka, dan a lokacin Mama tayi nisa batajin kira ta dauki abun da zafi ta kasa daukar kaddarar da tazo mana, komai zasu gaya mata gani take rashin kunya suke mata a matsayinta na mahaifiya a garesu, kallonsu tayi su dukansu sannan tace. "Na lura dukanku bakinku daya harda ke Aisha da nike ganin zaki bani hadin kai wajen sama ma yar'uwarki rayuwa mai inganci, amman sai naga akashin haka sun hure maki kunne ko."? Girgiza kai Yaya Aisha tayi tana kuka tace. "Mama ba haka bane gaskiya ne su Yaya Fatima suka fimu, wallahi Mama ni tun yanzun na fara da nasanin abunda nayi ma Auta, Allah ya ganar dani kema Mama ya kamata kiyi imani da kaddara Mama kefa ke cema mu ringa kai zuciyar mu nisa idan zamuyi ma yaranmu hukunci, amman Mama maiyasa ke a wannan karan kika kasa kai zuciyarki nisa wajen yi man Auta hukunci? Hukuncin da kika yanke yayi mata tauri da yawa nasan ba zata iya daukarshi ba." tunda Yaya Aisha tayi wannan magana Mama ta sake fasala cikin fushi tace. "To ku sani wallahi duk garin katsina ba wanda ya isa ya hanani aura ma Khadija Salahu koda hukuma ce kuwa, kuma wallahi duk wanda ta sake zuwa da sunan yi man magana akan karda na aura ma Khadija Salahu to wallahi sai na tsine mata albarka ko waye a cikin ku, dan haka ku tashi ku bani waje marar zuciya wanda basu kishin uwarsu."

Haka suka fita ba wanda ya sake cewa komai, gidan Yaya Jamilu suka ce danyi magana dan basu son suyi magana a asibiti gudun karda naji abunda ke faruwa na tada hankalina har yakai da na samu wani ciwon na daban.

Zama sukayi a parlourn Yaya Jamilu sannan Yaya Amina tace. "Yaya mai zai hana muje mu gaya ma Baba Ali ba wata ƙila idan shi yayi mata magana zataji ta fasa wannan jagulalan auren."? Shiru Yaya yayi yana tunanin mafita cewa yayi. "Amina kinsan dai ko yaje ba wani ji zatayi ba, karshe ma suyi fada kinga ba dadi dan Mama na lura tayi nisa cikin wannan lamarin ta daukeshi da zafi bayan kaddarar Auta ne a haka bata isa ta tsalake kaddarar taba haka ta zano tata kaddarar kowa da yanda ya zano nashi kaddarar, amman Mama ta kasa gane hakan." cewa Yaya Fatima tayi. "Hakane Yaya amman maganar Amina abun dubawa ce idan bashi muka kaima kukan mu ba wa zamu kaimawa dan ba kotu zamu kai mahaifiyarmu ba, dole dai hakan zamuyi Yaya." shiru Yaya yayi sannan yace. "Haka maganarki take Fatima, amman ku tashi ku tafi gidajenku mangariba na matsawa ni kuma zani wuce asibiti na kara ganin lafiyar Auta na kai masu abincin dare komai kenan gobe sai mu tafi gidan Baba Ali din muji yanda za'ayi." ba dan sunso ba suka tafi gida shi kuma Yaya asibiti ya wuce ya kawo mana abinci da kanshi ya zuba abincin ya matso kusa dani ya zauna ya fara bani abincin da kanshi da naso na ƙici amman sai na daure naci yana gama bani ya bani magani nasha sannan yace. "Auta dan Allah kiyi hakuri kisama dangana a ranki ki yarda da kaddara haka taki kaddarar take Auta kuma mu yaiyanki mun yarda da kaddara kuma mun ansheta hannu biyu wallahi Auta muna tare dake nidai fatana ki fidda komai a ranki ki cigaba da rayuwarki yanda kikeyi a da, sai dai kiji tsoron Allah kinga izinar da hau kanki sai ki kiyaye kinji Auta."?

Cikin jindadi nace ma Yaya. "Insha Allah Yaya nagode sosai da kulawarka amman Yaya wai da gaske bani sake haihuwa."!? Na karasa maganar ina zubda hawaye, sha fa kaina Yaya yayi sannan yace. "Aa Auta ba'a fidda rai ga rahamar Allah, kuma shi Dikko baida tabbacin baki sake haihuwa saboda ba wanda yasan ikon Allah dan Allah Auta karkisa wannan a ranki kinji? Komai yayi farko yana da karshe." tunda yayi man maganar hankalina sai ya kwanta nan mukai ta labari dashi sai da kai isha'i sannan yace shi zai tafi gida sai gobe zai dawo haka ya tafi ya barni hankali kwance muma labari muka sha da Dija sannan muka kanta.

Share
Comment
And
Vote
[12/31/2020, 11:02 PM] Jamila writar: *A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
_na ɓata rayuwata😭_

Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*
Chapter 7 · 0% Book details