← Book details Sanadin Soyayyar Shan Minti Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 16

Sashe 2

Sanadin Soyayyar Shan Minti Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dan ubanki ke har kin isa ki gaya ma Aziza bakar magana? Ina ruwanki da dani Dejja? Sannan ina ruwanki da rayuwa ta? Idan ma da sherin datake bina ina ruwanki rayuwarki ce ko tawa? Ba tun yanzun ba na lura da kina saman ido a cikin makarantar nan kina man baƙin ciki dan kinga ina tare da babbar yarinya kamar Aziza wayaiya wanda ta waye ba kamar ke ba BAGIJAJIYA, ba wanda bata san komai ba kanta kamar... "Dakata haka Aunty Auta." Dejja ta yanke man maganar ranta ɓaca, kallona tayi sama da ƙasa sannnan tayi tsaki ta watsar ce man tayi "wallahi baki isa ba ki kama gaya man wannan maganganun da kawai kina ƙanwar ubana, iyakarki kenan fa ƙanwar uba ba fa uwata ba, to ki sani baki cikin wanda zasu kama gaya man irin wannan maganar nayi shiru na kyaleta ba, dan kinga ina hakuri dake kina man abunda kika gadama dan kawai kaddara tasa kinzo man a ƙanwar uba? Shikenan to komai kikazo dashi nima na iya, kuma ba Aziza ba? Kije nabarma Aziza ke daga yau idan har ni Khadija Jamilu Bello to wallahi ban sake yi maki magana akan rayuwarki idan kinyi da kyau matsalar ki ba tawa ba, haka idan ma kinyi marar kyau duk matsalar ki tunda rayuwarki ce ba tawa ba, kuma ba rayuwata za'a ɓata ba taki ce za'a ɓata dan haka ba ruwan Dejja wallahi." cikin fushi na cacimi Dejja da dambe aiko ta biyeman muka kama damba cewa dakyal ƙawarta Jamila ta rabamu tana mata faɗa akan mai zara biye man muyi faɗa bayan ni ƙanwar Babanta ce, ni kuwa raina ya ɓaci waya na kira Yaya na fashe mai da kuka na gaya mashi karya da gaskiya akan abunda Dejja tayi man, sannan nace bani ba Dejja, sosai Yaya Jamilu y tada hankalin shi, nan ya kira Dejja yayi mata wankin baban bargo yace idan har bata bani hakuri ba, to bashi ba ita, ni kuwa ina gama gaya mashi na koma room dinmu na gaya ma Aziza yanda mukayi itako murna tayi tace "kin kyauta Beauty da kikayi maganin yar'banza yanzun sai kice karanki babu banbaka ba mai sa maki ido, muna cikin maganar Dejja ta shigo tana kuka nan ta fara bani hakuri ina cewa banyi sai da Aziza tasa baki sannan nace nayi, nan cikin daren nan Dejja ta kwashe kayan sawarta tas ta barma room din ta koma room din Jamila ƙawarta da zama baki ɗaya, haka kuma ta gaya ma Yaya Fatima abunda ya haɗamu bata boye ma har tashin da tayi ba, Yaya Fatima ta kira ni tayi man faɗan wulakanci aiko na fashe da kuka na kira Mama na gaya mata karyar da Aziza ta shirya man akan Dejja ta zageni dan na gaya ma Yaya Jamilu yayi mata faɗa shine Dejja tayi zuciya ta sake room ta gaya ma Yaya Fatima karya ita kuma Yaya Fatima ta kirani tayi man zagin wulakanci, cikin daren Mama tayi ma Yaya Fatima faɗa sosai sannan tace daga yau bata yarda Dejja ta sake zama room dinmu ba, dan haka kowa yayi harkarshi tunda Dejja bata da kunya har ta iya zagina, sosai Mama ta goyi bayana a wannan faɗan haka su Yaya Jamilu da su Yaya Amina suka goyi bayana banda Yaya Fatima dan tasan Dejja bata yi man rashin kunya hakanan ba tare da dalili ba, ba yanda Yaya Fatima batayi ba akan ta nuna masu aibun raba mana room da akayi ba amman suka kasa gane manufarta daga karshe ma Mama tace bata son aka maganar tunda a raba room.

*ku cigaba da comment kamar yanda kukeyi ni kuma zan cigaba da surburbuɗo maku typing da kuma posting kullun insha Allah 🥱*

👇👇👇👇👇👇👇

*SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!*

💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃

*Matso kiji ƴar uwa* 👂👂

*Shahararriyar marubuciyar nan wadda tayi ƙaurin suna gurin kasheku da dadaɗaɗan litttatafanta wato Aisha Umar Ibrahim (Real eeshow ) yauma gata tazo muku da wani shahararen book ɗinta wanda ta daɗe tana tanada muku shi cikin farashi mafi sauki wato 200 kacal.*

*Ga sunan book ɗin kamar haka*
👇

🌻 *BAR RAINA ALLURA*
*( Itama ƙarfe ce)*

*Domin neman ƙarin bayani kan wannan book zaku iya tuntuɓar mu a kan lambobinmu kamar haka* 👇
*08108362334 or 08135361133*

*Ƴar uwa karki bari a baki labari domin wannan salon na dabanne kamar yadda marubuciyar take ta daban.*😍😍😍😍

*karki bari kiyi missing ɗin wannan book ɗin hajiya.*

Share
Comment
And
Vote
[12/31/2020, 11:02 PM] Jamila writar: *A SANADIN SOYAYYAR MINTI*
_na ɓata rayuwata😭_

Na
*Jameey yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA WRITERS ASSOC📚🖊️*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
_________________

https://chat.whatsapp.com/KjAoWMWhoSICFg5gHjtn2t

*Wattpad JameelarhSadiq*

Page 19⏩20

"Tunda muka raba room da Dejja Aunty Asiya, ba sake wata sabuwar rayuwa dan bani karatu ban damu da nayi karatu ba, abu yayi nisa ko lecture ban cika zuwa sai randa nayi niya sannan zan tafi, koda naje bai zama dole agama dani ba."

"Inalillahi wa'inna'alaihijirun, Auntyna kiyi man uzuri nasan labarina yana ɓata maki rai ko? Hmmm! Dole tasa nima nike baki shi, dan bani son ina tuna da abunda ya faru dani a baya." na karashe maganar ina kuka, dan sai yanzun na yarda na tabka babban kuskure wanda bai gyaruwa a wajena sai dai nayi addu'a Allah ya yafeman, amman ko na bar dama Allah ya bani dama amman ni nayi watsi da damata, na biye ma son zuciyarta, nazo daga baya ina dana sani,kallon Aunty Asiya na sake yi ina kuka sannan nace "nasan kina cewa Aziza ce sillar lalacewar rayuwata ko? Ko ɗaya ba ita bace duk tana da wani ƙamasho a ciki, amman nice mai laifin tunda bani ɗaya ta fara yima tayin ba harda Dejja, amman da yake ita Dejja ba haka ta zano kaddararta sai ta tsalake, ni kuma da yake haka tawa kaddarar take sai na faɗa a tarkon nata sosai."

Kallona Aunty Asiya tayi sanann tace"tabbas Khady kin tabka babban kuskure, duk bansan ina labarin naki zai kware ba, amman ina jinki Khady." murmushi nayi sannan nace, bari nayi sallahr la'asar sannan mu cigaba da labarin namu." itama tashi tayi tana cewa. "Har wanka ma kiyi, nima bari nayi wanka na gyara jikina sai na yi mana girki muci abinci." tashi mukayi a tare kowa ya wuce yaje yayi abunda yayi niya, sai da na fara yin wanka sannan nayi sallah, na shafa mai sannan na fito lokacin da na fito har Aunty ta gama dafa mana taliya fara da manja da yaji, sai yan'keke da tayi mana, zama mukayi muka ci abinci sanan tace "bari na kai kwanonin kitchen na dawo ki cigaba da ban labarin ko."? Murmushi kawai nayi bance mata komai ba, haka taje ta wanke su sannan ta dawo ta zauna tace "ina jinki Khady ki cigaba da ban labarin nan, bansan ya kaimu gobe, tun safe muke labarin." dariya nayi sannan nace "Aunty kenan, ni banga abunso a labarina ba, labarina da babu abun burgewa a ciki sai dai kayan haushi da taƙaici." itama murmushi tayi sannan tace "na yarda da maganar Aziza da tace maki Yaro Yarone, inbanda abunki Khady, ai labarinki shine abunji musamman ma ga yan'matan zamanin nan, masu son abun duniya irinki da kuma masu biye ma son zuciyar, da wanda suka dauki soyayya da muhimmanci har ya kaisu da aiki da nasani irin naki, so nike ki gama bani naki labarin sannan nima na baki nawa." ɗukar da kaina ƙasa nayi ina share hawaye, dan kuwa duk abunda Aunty tace gaskiya ne sai dai ance DANASI ƘEYA CE, KUMA TANA BAYA tabbas haka maganar take, cigaba da cewa nayi.

“wata rana da ban taɓa mantawa ba,ranar da fita zani kasuwa dan yi mana cefene sakomakon kayan abincinmu sun ƙare bamu da komai sai dai muci kayan lakumashe kayan da samarin Aziza suka kawo mata idan sun gama *SOYAYYAR MINTIN SU* take kawo sai muci, gajiya nayi da zaman yunwa yasa na shirya dan zuwa kasuwa nayi mana provision, tunda na shiga kasuwar na hadu da gani gaye ya fito cikin wata elentra kallo ɗaya nayi mashi naji ya tafi da zuciyarta, dan wani irin mugun sonshi naji ya kamani daurewa nayi naƙi yi mashi magana saboda class da nike son ƙankaroma ƙaina, shago ɗaya muka shiga dashi shima ga dukan alamu yazo yasan wani abu ne, samun waje nayi na zauna ina jiran wanda na iske a shagon su gama abunda ya kawo su sannan nima nayi, shima kusa dani ya samu waje ya zaune ya ƙuraman ido yana kallona, da yaga zan ɗago idanuna sai yayi sauri ya maida hankalinshi a wayarshi, abunda bai sani ba shine duk abunda yake ina sane dashi dan hankalina yana kanshi saboda na kamu da sonshi, bayan wanda muke jira sun gama ya sun tafi sanna na tashi na fara kwasar kayan da nazo siya, shima zaƙewa yayi yana ɗibar kaya, dan kuwa duk abunda na dauka shima sai ya dauka kuma ba ɗaya ko biyu yake ɗauka ba sai ya dauki guda uku zuwa hudu, haka muka gama siyayarmu akayi mana total kafin na fiddo kudi naji yace "ka dauki kudin harda nata." yana miƙa mashi atm dinshi, kallonshi naɗago inayi kafin na fiddo kudin nima nace, malam ka haƙinka ka saman kayana cikin shopping bag sauri nike yi, murmushi guy din nan yayi sannan yace "haba yan'mata wa yake maida hannun kyauta baya? Ni nayi niyar biyaki ba tambayata kikayi ba." harararshi nayi sannan nace "nagode sosai, amman ka barshi zan biya da kaina, haka ya matsa sai da ya biya sannan yasa aka kwashe kayan aka kai a boot din motarshi kallon shi nayi sannan nace"ya haka Malam."?
Chapter 2 · 0% Book details