← Book details Sanadin Soyayyar Shan Minti Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 16

Sashe 16

Sanadin Soyayyar Shan Minti Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya bani kula kowa kuma na kasa sama raina soyayyar Aminu, idan na tuna da rayuwar da nayi da Aziza nakanyi kuka da nasani sosai Dejja take bani hakuri tana nuna man cewa kaddara tace tazo a haka, watarana zamu kasuwa nida Dejja zamuyi ma su Mama tsaraba dan sun gama exams gobe zamu gida su zasuyi hutun season ni kuma zani dawo level one, bayan mun gama sayen komai muna tsaye bakin titi wata unguwa ce inda ba mutane sosai, dan mun jima bamu samu abun hawa ba, ji mukayi an watsa mana wani abu a fuska daga nan bamu sake sani inda kaimu yake ba, koda muka farka gani na nayi kusa da Nurandeen zaune shida Aziza sai iskancinsu suke da inalillahi na fara magana ina kallon su, nan itama Dejja ta tashi itama inalillahi tace, gani nayi Nurandeen yana son yayi reaping din Dejja wai ita ta hanashi ya ida cima burinshi a kaina, bari itama yayi abunda yakeyi dani, ni kuma hana ina kuka ina bashi hakuri haka nai ta kuka itama Dejja tana kuka nan yace ya hakura amman sai yayi sex dani ko kuma yayi da Dejja, take na yarda dan bansan rayuwar Dejja ta lalace kamar yanda na lalata tawa, da Dejja taso yin gardama da yake nasan halinshi idan yace zaiyi abu sai yayi da naga Dejja tana son ta hanani bashi kaina bansan sanda na wanke ta da mari ba ina cewa “kinfini son kaine Dejja? Rayuwarki nike duba maki ni tawa rayuwar tazo karshe kuma ba zan taɓa barin naga taki ta lalace ba kamar tawa ko kin manta kinsha gaya man haka tawa kaddarar tazo ba? To ki dauka komai ya faru dani a rayuwa kaddara ce." kuka kawai Dejja take, haka Nurandeen ya wulakantani a cikin parlour din gidanshi dan Dejja kasa kallo tayi sai ma juyawa da tayi tana kuka, tun ina kuka ina bashi hakuri har na samai ido, sai yayi yanda yake so sannan ya kyaleni kuma yace kafin ya buɗe idonshi mu barmashi gida ko kuma ya dawo kan Dejja, haka muka kwashi kayanmu Dejja ta kamani tana kuka ina kuka haka muka koma hostel ko Jamila Dejja bata gaya ma abunda ya faru ba, kawai dai tace naped ce ta faɗi damu, haka nayi wanka na kwanta ina aikin kuka take naji na tsani Nurandeen duk duniya ha wanda na tsana kamarshi shida Aziza.

Washe gari muka dawo gida, kowa yayi murna da ganinmu Dejja taso mu wuce gidansu amman ni nace aa gida zani wajen Mama, haka ta kyaleni ba dan taso ba na wuto gida itama ta wuce gidansu, bayan na dawo da sati biyu ba fara ciwo kala kala daga wannan sai wannan haka Mama ta kaini asibiti nan akece muje ayi mana awon ciki, cikin mamaki Mama tace ciki kuma namai bayan ko aure banda shi, amman likita yace aje dai ayi aiko anayi sai gashi ina da ciki na sati biyu da kwana ɗaya tun a asibitin na fara ganin tashi hankali wajen Mama, haka muka dawo gida ni kuka Mama kuka ba irin tsinuwar da Mama batayi man ba, daga karshe Yayata Aisha tazo nan Mama ta gaya mata suka yi man taro suka kama bugu a ranar cikin Nurandeen ya zube a jikina kuma na samu matsalar mahaifa, ina cikin kuncin ciwon da ya samaini naji Mama tace aure zatayi man da wani tsoho a unguwarmu ni kuma naji ban iya dauka shine nazo nan garin har Allah ya hada ni dake, kinji Abun da ya faru dani....

*karku manta na gaya maku litafin sanadin soyayya minti ya faru da gaske, amman ba komai yake gaskiya ba 20%true life ne, Khadija da kanta ta gaya man labarin nata tana son na rubutu akanki shi dan masu irin halinta su daina idan ma akwai masu niyar yi su fasa ni kuma 80%fiction ne na Kara shi dan na kara ma mutane jin tsoron yin abun a zuciyarasu kuma su ƙamaci abun har abada, kuma Khadija tana cikin group din duka biyu da a sanadin soyayyar minti fans da kuma sanadin soyayyar minti 2 duk tana ciki sai dai bata yarda da na bada number dinta ba, dan haka ina maku fatan alkhari kuma ku dauki abu mai amfani da yake ciki nagode*

Share
Comment
And
Vote
Chapter 16 · 0% Book details