← Book details Sakata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 11

Sashe 9

Sakata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da mugun mamaki ya Wago ya kalleni, ni kuwa sai haki nake kamar wata zakanya, banyi au ne ba kuwa naji ya kwarfeni da ™afarsa na faWi ™asa Tim!, ai kuwa ya bini da duka. Ya fusa ta iya fusa ta, nima kuma na fusa ta iya fusa ta domin baki na bai mutu ba, faWi na ke. "Shege, mugu, azzalumi, kuma wallahi zai ka ga gatana, wallahi sai munyi shari'a da kai." shi kuwa duka na ya ke amma da ™afa, cikin sa'a na ri™e kafar ta sa, na gan tsara masa wani mugun cizo, kuma nak'i ci kawa har sai da na had'o da fata, da sauri ya janye k'afar tare da matsawa, nan take zuciyata ta ce mun. "FaWan bai k'are ba." ai kuwa na tashi da mugum guda na Wane bayan shi kamar wata biranya, na shiga gantsara masa cizo a wuya, shi kuwa faWi ya ke. "Baki da hankali ne?, sauka a kai na." Salatin da Ummanah ta saki ne ya sa jiki na wani irin mutuwa, kirjina ya shiga bugawa da k'arfi-k'arfi. "Sannu 'yar biri." sai a lokacin na fara ™o™arin dirga ™asa, idanunta suka kai kan ™afarshi da ke fitar da jini, ga kuma shatun ha™orana a wuyansa. "Kashe shi zakiyi kenan." miri-miri nayi da idanu tare da fad'in. "Ina shigowa ya kifa mun mari." Ba ta ko kula ni ba ta shigo Wakin tare da kama hannuna ta shiga jana a ™asa, kamar kayan wanki.

"Nashiga uku na lalace." kawai nake iya fad'a a raina domin nasan yau na bushe har hanjina.

"Ummanah dan Allah kiyi ha™uri, wallahi shine ba shi da gaskiyya, wai sai na share masa d'aki daga na ce bazan share ba shine ya mare ni." Sai da na fad'a kuma, na tuna Saran-b'aramar da nayi, ni a rayuwata kwata-kwata ban iya ™arya ba, komai gaskiyya nake fad'a kai na tsaye. "Shine kika fara gantsara masa cizo ko, ke ga mahaukaciya, karya ko?."

"Wallahi Ummanah ba haka ba ne, mari na yayi." ban ™arasa rufe baki ba, naji saukar mari tare da bulala, ina ihu ina kororoto amma Umma ™ara zanbad'a mun ta ke. Daman Ummanah kwata-kwata ba ta iya duka ba, duk lokacin da ta dake ni sai tayi mun rauni, shi yasa Abbanah yayi mun fad'a kan na kiyaye abinda zai Sa ta ma ta rai, to lokacin da ta da ke ni ma na ™arshe a kan Mus'ab ne, kai Mus'ab ya zama masifa a rayuwata.

Tun ina kuka da bata ha™uri, har na yi shiru gaba Waya duk wani ™arfina ya ™are, sai da ta ga ji dan kan ta sanan ta kyale ni tare da fice wa, ta bar ni kwance ina kuka.

Nayi kusan minti goma a zau ne, zuciyata na ta saka mun abubuwa kala-kala, ta ce mun "in je ina bu ga masa dutse a kai, sai dai ko mene ayi mun.", ta ce mun."In je in ™a re mai tana di, zagi ta uwa ta uba" ko hakan zai kawo karshen zumuncin nan." abubuwa kala-kala, ™arshe na yanke mafita guda d'aya na tarka ta na bar gidan baki daya, na je gidansu Masrur ko a 'yar aiki ya kai ni, daga baya mu yi aurenmu.

A b'angaren Ummanah kam, ta na ga ma duka na ta nufi Sagarensu Mus'ab, ya na zaune kan kujera ya rasa mai ke masa dadi, sallama tayi d'akin ya amsa. "Yanzu kai Mus'ab yarinya k'arama za ka tsaya har ta mare ka, ba ka b'abbalata."

"Ummah kiyi hak'uri, bana son na dake ta nayi mata rauni."

"Da ba ka ballataba, ai ko shi Abban na ku idan yazo ya ji abinda ta yi sai ya Sallata, kuma ya na dawo zan faWamai."

"Ummah dan Allah kiyi hakuri, laifina ne da nasa ta sharar."

"To wallahi daga yau, har zuwa ranar da zaka bar gidan nan ita zata ke maka sharar Wakin, kuma ka ci abinci idan zaka ci." ta faWa ta na ta shi, alamun shi ma ya Sata ma ta rai,a tsakar gida su ka haWu da Maman ciki, ganin yanda ran Ummanah ke haWe Maman ciki ta ce."To mai kuma ya faru da 'ya'yan naki?."

"Bari ke dai, lamarin Salma ya fara isa ta, yarinyar nan kullum rashin arzi™inta ™ara gaba ya ke."

"Salma yarinya ce fa har yanzu, wai bakya tuna lokacin da aka haife ta ne?." wata harara Ummanah ta watsa Maman ciki, sanan ta ce."A'a ban haife ta ba, yawo nake da ita a ciki."

"Allah yabaki ha™uri, yanzu ta na ina?."

"Ta na can ta na jinyar jikinta." daga haka Ummanah ta huce, tabar Maman ciki da sakkaken baki, Waki ta nufa ta ajiye jakar ta tare da shiga bayi, sauri-sauri take ta fito tazo Sangaren namu.

Ni kam tun da na yanke shawarar barin gidan, na shiga haWa kayana, bayan na cika akwatina sanan na jawo wata katuwar jaka na shiga zuba wasu kayan ciki, har da jaka da takalmi na.

Bayan na gama na shiga d'akinta, inda take ajiye kudinta na nufa, naira dubu uku na dauka, sai kuma nayi tunanin dubu uku tayi mun yawa, nan da Gwari avenue baifi 2500, haka yasa na ajiye dari biyar na fito, ina kokarin janyo jaka da akwati na ta shigo, kallo na kawai tayi ba tare da ta ce."Ci kan ki ba." ta huce ciki, ni kam na ci gaba da jan kayana. Ina daf da bakin ™ofa naji an cafke ni, juyuwar da xanyi na ganta da wayar charger ta computer Abbanah, ba wata-wata ta hau zabga mun, ni kuma ina rusa ihu.

Mamam ciki ta shigo da sauri ta na fad'in."Innullahi wainna illahir rajiun, Menene haka dan Allah?."

"Barni na targad'a yarinyar nan, nayi mata rau ni."

"Kiyi ma ta rau ni, sabida me, haba dan Allah." Nikam narkewa na ™arayi a jikin Maman ciki, ina faWin."Wallahi sai na bar gidannan ba za'a kasheni ba."

"kiyi shiru ke kuma." Maman ciki ta faWa, Ummanah kam ajiye bulal tayi tare da shigewa Wakin, kallona Maman ciki tayi sanan ta ce. "Je ki mai da kayan, kuma kar ki sake irin wanan abun ko da wasa."

"Wallahi Mama bazan ko ma ba, duka na zata ci gaba, ni kawai a bar ni."

"Ki je ki mayar na faWa mi ki." Maman ciki ta sake faWa. "Wallahi ko kin mayar sai na dake ki, kuma har can Sangaren zan zo." Kuka na fara, maman ciki ta ce. "To ai ba Sangarena zan kai ki ba, muje." tunda ta ce haka, Sangaren Hajja zata kai ni. Ai kuwa can Winne, Hajja na gani na haka ta fara sababi. "Amma wanan uwarta ki ba ta da hankali, to wallahi ahir Winta." Ni kam wata tsanar Mus'ab ce sabuwa ta sake fidda rashe a cikin zuciyata, a kan shi anyi mun dukan da ba'a taSa kwatanta mun ba, an kira mahaifiyata sa mara hankali, duk a kan Mus'ab, kai Mus'ab ya zama tauraruwa mai wutsiya a inda nake." Maman ciki ce tai ta ba Hajja ha™uri, sai da ta ga tay shiru sanan ta ta shi ta tafi. "Tashi ki haWa ruwan Wumi." Hajja ta faWa tana kallona, bayan fitar Maman ciki, ba musu na mi™e nayi Kitchen, a heater na Wora ruwan Wumin, sai da yayi sanan na sauke na shiga na watsa ruwa, naji daWi sosai a jikina, na zo nabi lafiya kujera na kwanta, banko sassauta da tsinewa Mus'ab, har bacci ya Wauke ni.

Sai wajen la'asar sanan na tashi, zaune na ganshi kan Waya kujera dake kallon tawa, amma hankalinshi na kan wayarsa yana dannawa, inaga ma baisan ni ce kwance kan Waya kujerar ba, mi™ewa nayi ina turu baki, ina hararshi ™asa-™asa, Allah ya gani na tsani Mus'ab, bana ko ™aunar ganinshi domin a yanzu na fuskanci Mus'ab so yake ya rabani da Ummanah, domin a kwanciyar nan ta wa na ™ara tabbatar da hakan, indai nasamu saSani da Ummanah tofa a kan lamarin Mus'ab ne, ko mene ribarsa oho, wani Sari na zuciyata ya ce. "Mutumin da baya sonki, mene ribarsa idan bai rabaki da iyayenki ba?." a fili na furta. "Kurwata kur, mai Wa ya ci Wanshi mara Wa ya ci ™o™on tsuliyarshi." Wani kallo ya watsamun, sanan ya ci gaba da danna wayarsa, nima na mayar mai da kallon da hausawa suke cewa. "Harara a duhu." tun da bai san inayi ba.

Bayi na shiga na Waura alwala, na fito na ta da sallah, har na kamalla yana zaune, yana danna waya."Mai bautar waya." na faWa a raina, tare da shiga Wakin da Hajja ke ciki. "Hajja abinci." Na faWa daga tsaye. "Ke fa matsalata dake rashin kunya da rashin mutunci, haka ake yi a gidanku." na cuno baki gaba sanan na ce. "Ke kuma matsalal ki mita da sababi."

"Nayi mita nayi sababin, na rantse yanzu zaki ficemum a Sangare." Shiru nayi nasan zata aika, kaddam ne daga aikin Hajja."To yanzu Hajja mai zan ci?."

"Shiga kitchen, ki dafa taliyar yara ina da ita lodi-lodi." Kicin Win na nufa, na shiga haWa indomie na, ina mamakin yadda Hajja ke cin indomie, a yanzu haka akwai sama da katan biyar a cikin kicin Win, ina tsaye har ta kamalla, na juye a faranti na dawo falon, yana nan zaune kaman mutun-mutumi, yana faman bautar waya. Bayan na ajiye na shiga Waki, nayi narai-narai da fuska na ce. "Hajja tawa." Baki buWe take bina da kallo, kamar ta ga sabuwat hallita. "Hajjana, dan Allah wayarki zaki bani, na kira malamin mu na sanarshi bani da lafiya ya sa banzo ba." ita Hajja ba ta wami damu da waya ba, kuma kullum wayarta cike da katin waya, haka su Sadiya za su zo da Walida suyi ta Wauka suna kiran samarinsu, ni kam bantaSa ba sai yau, ko da yake yanzu na fara soyayyar.
Chapter 9 · 0% Book details