← Book details Sakata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 11

Sashe 4

Sakata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Eyh shi dake ba da doya akeyi ba ko?."

"A'a Ummah, yafi sau™i ne."

"Ke zanci gidanku wallahi, a gama dafa doyar azo a daka shine zakice yafi sau™i?."

"Wai menene?." Maman ciki ta tambaya, "Yamboll ta yo." Ummanah ta ba ta amsa, " Ai shikenan mu bari mu ci, ku kuma ku fita ku nemo mana tea, da kayan madara." Tashi nayi na amshi kudin, walida ta biyo ni har mun kai bakin kofa, Ummanah ta ce. "Saura ki siyo ruwan sanyi." Dariya nayi na fice, Mus'ab kam zuciyarsa kamar ta fito waje, ji yake kamar ya makeni da duka.

Mun siyo kayan shayin mun dawo cikin asibitin naji ana cewa."³an mata." kamar nasan murya, amma duk da haka naki tsaya wa, duba da yanayin yawan mutanen dake wajen bai zama lallai ni din ake kira ba. "³an mata, bakya jina wai." a ka sake fada kusa dani, da alama mutumin yazo inda muke. A hankali na waigo idanuna suka sauka a kansa, daya cikin matasan da suka zo layin mu jiya, suka tambayi Gidan Alhaji idi me mai. Wanda baiyi magana sosai ba, ina tuna lokacin da yace. "To ina ne gidan naku?." Murmushi nayi masa sanan nace."Ina yini." shima murmushin yayi, cikin zazzakar muryarsa yace. "Lafiya kalau ™anwata; me kikeyi anan?."

"Šan-uwan mu ne ba lafiya, aka kwantar dashi anan."

"Ayyah, Allah sarki muje na duba shi." Wani irin abu naji a zuciyata, amma kuma baxan iya masa musu ba, hakan yasa na ce. "Toh muje." jerawa mu kayi muka fara tafiya, Walida ta shige gaba mu kuma muna baya, duk naji nayi wanan fiyau. Ya cika wajen baki daya, a raina na ce. "Idan wanan yace yana so na, wallahi sai nayi sadaka, sabida yana da kyau, gashi Wan gayu, mai aji, murya mai za™i. Nipa an gama tashin kai na." A haka muka ™ara so da™in, walida ce ta ce. "Bari na sanar da su." gyada kai yayi, ni kuma naji ni a ta kure. Ban yarda da abinda Walida za ta ce ba, hakan yasa na ce. "Bari na bi ta."

"A'ah ki jira mana." kallonshi nayi, idanuna sunyi wani kala na ce. "Ban san me za ta ce ba."

"Mai kike tsoro to?."

"Za fa ta iya ce musu, Saurayina ko wani abu." Murmushi yayi, sanan ya ce. "To menene a ciki, ko ki na da wani saurayin ne?." ™asa nayi da kai na, ba tare da na ce komai ba. Shi kuma ya ™ara cewa. "Ko akwai ne." girgixa kai kawai nayi, dai-dai lokacin da Walida ta fito. Sai a lokacin na fahimci cewa, kofar bata yin ™ara idan a ka bude ta, shine yasa dazo banji lokacin da ummanah ta buWe ba. "Ku shigo." ta faWa, ni kam kamar munafuka haka na zama.

Idanunsa a rufe yana kallon sili muka shigo, Maman ciki ce ta. "Ga waje mana basai ka xauna a ™asa ba."

"A'a Mama bari na zauna anan; ina kwana, ya mai jikin."

"Lafiya ™alau, mai jiki da sau™i." su ka amsa tare. "Allah ya ™ara lafiya."

"Amin, Mus'ab ga ba™o fa." Mama ta faWa, a hankali ya buWe idonsa ya sauke su akan mu, kasancewar ya tsugunna kusa da inda nake zaune. Kallo daya ya gane fuskar gayen, wa'yanda yaganni dasu jiya, tasowa gayen yayi zuwa idan gadon yake, tare da mi ™awa Mus'ab hannu sukayi Musabaha."Ya ™arfin jikin?."

"Alhamdulillah." Mus'ab ya fada a da ™ile. "To Allah ya™ara afuwa."

"Amin."

"Zan huce, Allah yakara lafiya."

"Amin-Amin, an gode." Su Umma suka fada, shi kuma ya nufi ™ofa. Walida ce tayi magana da ™arfi yanda kowa zaiji."Salma kije ki raka shi mana." kamar mara laka haka na tashi, ina raba idanu nayi waje.

A bakin ™ofa na tarar dashi. "Salma..." ya faWi sunan, tare da ja cikin wani irin salo mai dadi. Sai naji kamar shi kadai ya iya kiran sunana. "Zan tafi, ngde da kulawa. Sunana Masrur, sanan wanan asibitin na mahaifina ne, kuma yana karkashin kulawata saboda haka, an dauke muku komai."

"Mun gode, amma da ka barshi dan wallahi ban san ta yadda zan fadawa iyayena haka ba."

"Salma..." ya ™ara kiran sunan na, a nutse na Wago na kalleshi. "Ina sonki." Kara Wagowa nayi na kalleshi, idanunsa suna kaina, da sauri nayi kasa da nawa a raina na ce."nima ina sonka." amma afili kuwa shiru nayi na kasa cewa ko uffan."Bazan ta kureki ba, zanbaki lokaci kiyi tunani. Ga lambata nan." ya faWa yana mi™omin wani kati, hannu nasa na amsa sanan nace. "Nagode." ka Wa kai yayi ya tafi, ni kuma na koma ciki.

Kamar wata Sarauniyar da tayi sata aka kamata haka na shiga cikin Wakin. Sai dai duk cikinsu babu wacce tace da ni ko uffan, hakan yasa nayi matu™ar damuwa. A hankali na ce."Umma, mai walida ta ce muku?." banza Umma tayi dani kamar ba taji ni ba, kuma nasan taji, hakan yasa na koma ga Mama. "Mama mai walida ta ce?."

"Mai kikaji wani yace miki?." Na girgiza kai na ce."Bakomai."

"To kuma, ko kinyi wani abun ne?." na girgiza kai kawai, can 'yan mintina na ce. "Walida ta so mu tafi." ba ta kai ga magana ba likita ya shigo Wakin. Bayan sun gaisa yace da su Ummah.

"Ban san wane likita ke duba Mus'ab ba, kuma ko ma wane akwai matsalal da ba daga likitan mu take ba, dagashi yaron ku take."

"Matsala kuma likita?." Mama da Ummanah suka tambaya, har wani hade baki sukeyi. Ni kam a raina na ce. "Allah yasa matsalal mutuwa ce." maganar likitan ce tasa na dago na kalleshi.

"Eyh matsala, domin gaskiyyya ba aina hin ciwon dake damunshi ake fada ba, kuma da masaniyar sa domin ko magungunan da ake bashi, na asalin ciwon sa ne. Kunga kuwa sun hada baki da likitan suna Soye muku.

Wani daWi naji a raina, domin nasan babban ciwon ne kadai ake boyewa iyaye ba'aso su ji sabida kadan hankalinsu ya tashi.

"To yanzu likita wane ciwo ne, na gaskiyya dan Allah." Ummanah ta fada kaman zatayi kuka, wani ™ululun abu ya tsayamun a ma ™oshi yanda matarnan ta damu da Mus'ab ko ni bata damu dani ba, ji yanda take magana kaman zatayi kuka.

Abban ciki ne yayi sallama, tare da Kawu mudi da kuma Yaya ilyasu. Shigowa sukayi baki dayansu, nida walida muka koma can gefe muka basu basu waje, kasancewar dakin babbane.

"Kai ka sa tsohuwar mutane cikin damuwa." Yaya ilyasu ya faWa. Likitane ya ci gaba da cewa."Kamar yanda na fada muku, matsalal shi ba ciwon kai bane kwata-kwata." da sauri Abban ciki yace. "To menene?."

"Matsala shi a ciki take."

"To amma mai yasa duk bayanan ku na baya yake nuna kai."

"A'ah ranka yadaWe, ko a file na asibiti cike ne, sanan magungunan da yake sha ma na ciwon ciki ne, kawai su na ambatar kai ne domin Soye muku."

Ina daga gefe na fara addu'ar, Allah yasa afendes ne yanda za'a yanka shi karshe a ce ya mutu.

"To yanzu likiti menene cutar?." Abban ciki ya ™ara tambaya, Likitan ne ya fara duba takardun hannusa, nikam hankali na kanshi.

" I need you to stay calm, please. Cutar tashi ba wata babba bace, amma kuma lokutan da ta dauka a jikinshi ta kara girma.

"Doctor, kana firgita mu Menene matsala?"

Legends pen.

(08165383931/ 08129553971).

Daga page 10 zamu gama free pages, mu shiga paid pages, ¦ 500 kacal ne sai kuma masu bu™atar complete ¦ 1000.

Payment via.

8129553971

OpaY

Sani Muhammad lawan.

Shaidar biya.

08165383931.

*SAKATA*d'þ“&þ

<Ø;ßStroy and written<Ø;ß

By

Sayyid writer (Legend)


*FUTURE WRITERS ASSOCIATION*

*(FUWA)=Ø‹Ýþ=ØÚÜ*

SHAFI NA BIYAR

(P.05).

(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE

" I need you to stay calm, please. Cutar tashi ba wata babba ba ce, amma kuma lokutan da ta dauka a jikinshi ta kara girma.

"Doctor, kana firgita mu Menene matsala?"

" He have been diagnosed with a rare condition called Hypersexual Hormonal Disorder HHD. It means His body produces an unusual level of sex hormones beyond control. That s why kake yawan jin wani irin zafi, idan kana ciwon cikin. Kuma irin wannan sha'awar ba irin wacce ake iya da ™ilewa ba ce,da ™ile ta da yayi na kwanakin baya yasa ta zama babba har haka."

"Wannan wace irin cuta ce haka, nifa bangane komai ba?." Mama ta tambaya cike da ruWani. "Nima dai." Ummanah ma ta faWa.

Yaya Ilayasu ne, ya kallemu ni da Walida yace."Ku fita." Sim sim sim kamar munafukai muka fice, ni dai burina a ce mutuwa zaiyi.

Bayan munfita ne likitan ya kalli su Mama yace.

"Yana fama da wata irin cuta mai suna Hypersexual Hormonal Disorder. (HHD). Ma'ana jikinsa yana fitar da wani nau'in sinadarin sha'awa fiye da kima. Wanan ne dalilin da yasa yakw yawan jin wani irin zafi, da kuma wata sha'awa mai ™arfi wacce har ta kan iya kayarda shi ™asa."

"Inullahi wa'inna illahir rajiun." su Mama suka shiga maimaitawa, likitan yakara da cewa."Tun farko bai bari anyi dogon bincike ba, a kan rashin lafiyar tashi, gashi har abun ya zama worst haka, ko kunyar ku yake ji oho."

"To amma fisabillillahi, ko da yanajin kunyar mu bashi da 'yan uwa maza. Kawai sabida rashin kula da lafiya." Ummanah ta fada cike da damuwa.

"To yanzu likita menene ai nayin maganin cutar?." Abban ciki ya tanbayeshi.

"There s no drug-based cure yet. But in most studied cases, emotional stability and natural intimacy especially within marriage. help the body regulate the hormones over time. Auren na iya zama magani a gareshi."

"Shikenan likita, insha Allahu za'ayi." Abban ciki ya faWa, likitan yakara da cewa."Yanzu za'a rubuta mishi drugs da zai na amfani dashi, zasu taimaka sosai da sosai."

"To mungode." Ummanah ta fada, likitan yasa kai ya fita, Mus'ab kam idonshi a kulle angama to na mai asiri yanzu kowa sai yasan halin da yake ciki.
Chapter 4 · 0% Book details