← Book details Sakata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 11

Sashe 7

Sakata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A'ah, dan Allah ki rage wanan muguwar tsanar."

"Wallahi Sadiya duk safiyar ubangiji, wata sabuwar tsanar Mus'ab ke huda zuciyata."

"Allah ya kawo miki sau™i."Banza nayi da ita, sanan na mi™i zuwa Wakin Ummanah. Wayarta da ke jikim chaji a soket na je Wauka, amma ™walam ba ta nan. "Nasan tana dakin Abbanah, bari na je na ce tabani zanyi karatu." Na faWa a raina tare da fice wa. Ban kai ga Wakin ba naji muryar Ummanah na ce wa. "To yanzu zuwa yaushe zaku jira su?."

"Eyh, zamu jira su zuwa sati ko fi. Dole dai idan su ka gama shawararsu su nai me mu."

"Nima amma Alhaji, ciwon yaron nan ya mugun damana, gani nake kamar zasu Sata mana lokaci. Kasan Likitan yadda ya nuna, yana bu™atar aure cikin gaggawa fa."

"Gaskiyya ne, ciwon nan na shi na bu™atar iyali kusa-kusan nan, Allah dai ya bamu yadda zamuyi." Abbanah ya faWa, dai-dai lokacin da nayi sallama. Ummanh ca ta amsa da faWin. "Salma shigo ma na." shigar nayi kaina a ™asa, sanan na ce. "Ummanah ina son nayi karatun hadda, idan babu damuwa."

"To ai wayar na Waki."

"A'ah Umma, ba ta jikim soket."

"Eyh, ba nan na ajiye ba. Ki duba gefen fulo." Tashi na yi a raina ina ce wa. "Ko mai yasa ban duba nan ba oho." wani Sari da ga zuciyata ya ce. "Rabon kiji wanan maganar ta su." afili na furta. "Mene haWi na da maganar." kasancewar babu mai ba ni amsa, ya sa nayi shiru na ci gaba da tafiya zuwa Wakin mu. Wayar na gefen gadon, hakan yasa na Wauka na fara loda lambar ta shi, wacce tsabar yawan dubawa yasa na hadda ce ta.

Bugun farko ya Waga wayar, kamar ya san ni ce ya fara magana. "Fulani barka da dare." idan na ce banyi mamaki ba, kuma kusan ™arya ne. Domin yadda ya kira sunan da ™arfin gwiwarsa, irin yana da tabbacin ni Win ce."Ba ita ba ce." Na faWa ina murmushi. "Haba Fulani, tun kafin ki kira zuciyata ke cemun Next call is your future wife." Murmushi nayi sanan na ce. "Yakake?."

"Not good." ya bani amsa, a Wan tsorace na ce. "What's going on."

"Fulani I'm missing you, so badly."

"Same here, Vida mia."

"Oh what a sweet name, amma naji dadin sunan." kunya ta ka mani, na ce."Amma Fulani yafi daWi."

"No, wanan ma yayi daWi i really appreciate it."

"Thanks you." na fada, cikin ™arewar magana. "Fulaninah." Sassanyar muryarshi ta sake faWa. "Vida Mia." Nima na faWa, cike da sabuwar soyaya, a raina ina cewa. "Ni kam na dace, a rayuwar soyayya, domin Masrur ko babu ci babu sha, zan zauna dashi ko dan kyakyawar fuskarsa. Duk da Walida ta ce wai rawar kai ce, amma nafishi kyau."

"Fulani, ina da tarin tambayoyi."

"Tambayoyi kuma?." Na faWa kai tsaye. "Yeah Fulani, amma ba tambayoyi masu damuwa ba, na soyayya ne." Murmushi nayi sanan na ce. "Tom ina jinka."

"Fulani mai kika fara ji ranar da kika ganni." Shiru nayi ina sauraron zuciyatah. A hankali na fara ce wa."Ina zaune a harabar gida, na ji kamar ana kirana a waje, na tashi na fito, idanuwa na suka sauka a kan ka. Kyakywar farar fuskar ka ce ta fara burgeni." sai kuma nayi shiru. "Ci gaba mana Fulaninah."

"Shikenan." Na faWa, shi kuma yayi dariya. "Ni kam Fulani idan na faWamiki ranar da na fara ganinki za ki yi mamaki sosai."

"Yaushe?." Na tambayeshi. "Fulani, wajen 3weeks back. Na gan ki ke da ™awayenki, kun dawo daga school. Tun lokacin na fara bin ki, ina ganin ki." Murmushi nayi mai sauti sanan na ce."Kasan maganar da nayi da ku, sai da Mus'ab ya ja a ka dake ni."

"Fulani, wai mai kika yiwa Mus'ab ne?."

"Nima ban sani ba, kawai dai na san ya tsane ni, nima haka."

"Amma ya kama ta ku daina haka, ba kya ganin yadda kuke kama ne."

"Ni kam har abada ba zan so Mus'ab."

"Nima bance ki so shi ba, amma ku fahimci juna." cike da jin haushi na ce."Ko da a kwai wani abu da fahimtar juna dashi za ta yi mun?."

"Šan-uwan ki ne fa."

"Dan Allah mu bar maganar shi haka." Na fada kamar zanyi kuka."Shikenan, yanzu tambaya ta gaba. Mutum nawa kika yi dating kafin ni?." Shiru nayi ina son tuna wa, sai kuma na ce."Wani yaro ne Hafiz, tun muna aji biyu a islamiya daga baya kuma mu ka rabu."

"FaWa kuka yi?." Ya tambaye ni. "A'a, kawai yau da gobe da kuma girma."

"Okay, Wa kika fi so a ™awayenki?."

"Ai ni bani da ™awaye da suka huce 'yan uwana, Walida da Sadiya."

"Wacece wacca nagan ku tare a asibiti?."

"Walida, na bashi amsa."

"Okay, yanzu yi mun naki kafin na ciga ba."

"A wacce unguwa kake?." tambayar da ta fara zuwa bakina ba tare da na shiryawa fitarta ta ba.

"Gwari avenue." Na girgiza kai, alamun naji."Akwai wata?." ya tambayeni, na ce."Eyh, mai ya baka kwarin gwiwar zuwa layin mu."

"Zuciyatah." Dariya nayi sanan na ce."Na gama."

"Ina da wasu masu yawa, amma naga dare yayi."

"Uhm." Na faWa, sabida bana son wayar ta kare. "Ki kwanta, sai Allah ya tashe mu. Kisani ina matu™ar ™aunarki."

"Nima haka." Na faWa tare da gyara kwanciyatah, fuska ta Wauke da murmushi ya katse wayarshi. Haka na kwanta ina ta murmushi, kamar wata sabuwar kamun hauka.

Washe gari..

Da sassafe na tashi, sabida ina son zuwa boko duk da ba wani abu ake mana ba, sabida muna Ss2 ne kuma anyi exam Win third term har angama. Boko dai ajin mu Waya da Sadiya, amma Walida ta na Science ne, ni da Sadiya Muna art. Ita sadiya ma commerce take, kawai wasu subject Win mukeyi tare. Ni dai na ce ba zan wahalal da kaina a kan Karatun boko ba, dan yanzu ba wani aiki a ke samu ba, gwanda na karanci har kar kasuwanci abu na.

Zaune nake a cikin class, na ware gefe na zauna hirar mu da Vida mia nah ta na dawomun ina murmushi ni kadai abu na. Safiyya ce ™anwar Samira wacce Mus'ab zau aura ta shigo ajin mu, wata muguwar dariya ce ta tawo mun, ganin ta na tafiya kamar cokali. To a haka ma tafi Samira ™iba, ga mamaki naga ta na yo inda nake, kau da kai nayi daga saitin inda take tawo wa."Salma Galadima." ta faWa, bayan ta ™ara so inda nake, cike da haWe rai na ce. "Ya a ka yi?." murmushi tayi sanan ta ce. "Lafiya ™alau, ai yanzu mun zama 'yan uwa."

"kun dai zama 'yan uwa, ni mene alaka ta da ku, har da wanda zaku aura."

"Ai ko ba komai Wan uwanki ne ko."

"Kinga Safiyya, tashi ki bani waje." Na faWa a tsawa ce, saukar da murya tayi sanan ta ce."Kiyi ha™uri, tambayar ki na zo yi fa."

"Me zaki tambayeni?."

"Dan Allah KifaWamun gaskiyya, nasan ba kya ™arya kuma ba za kiyi ba." kallonta nayi sanan na ce. "Wai me zan fada miki."

"Nasan kin san Mus'ab su na soyayya da Samira, to amma tun farko ba wata soyayya ba ce ta a zo a gani, dan bai taSayi ma ta maganar aure ba. Kawai dai soyayyar tasu ta bazo ne, kowa ya sani to kwatsam su Abbanku su ka zo da maganar aure, bayan su Babban mu sunyi shawarar ba shi, sai ga wani zance ya fito. Wai Mus'ab yana dauke da wata cuta, kuma duk macen da ya aura za ta sha wahala a kan wanan cutar tashi, dan Allah ki faWamun gaskiyya, nasan ba zaki Soye ba, sanan kin san Yayata ba wani kiSa gare ta ba, kuma wallahi ba xan taSa cewa daga bakinki na ji ba, ko a gidanmu."

Legends pen.

(08165383931/ 08129553971).

Daga page 10 zamu gama free pages, mu shiga paid pages, ¦ 500 kacal ne sai kuma masu bu™atar complete ¦ 1000.

Payment via.

8129553971

OpaY

Sani Muhammad lawan.

Shaidar biya.

08165383931.

*SAKATA*d'þ“&þ

<Ø;ßStroy and written<Ø;ß

By

Sayyid writer (Legend)


*FUTURE WRITERS ASSOCIATION*

*(FUWA)=Ø‹Ýþ=ØÚÜ*

*The Fearless Writers Team*

_Marubuta masu tsage gaskiyya_

SHAFI NA TAKWAS.

(P.08).

(3E 'DDG 'D1-EF 'D1-JE

"Nasan kin san Mus'ab su na soyayya da Samira, to amma tun farko ba wata soyayya ba ce ta a zo a gani, dan bai taSayi ma ta maganar aure ba. Kawai dai soyayyar tasu ta bazo ne, kowa ya sani to kwatsam su Abbanku su ka zo da maganar aure, bayan su Babban mu sunyi shawarar ba shi, sai ga wani zance ya fito. Wai Mus'ab yana dauke da wata cuta, kuma duk macen da ya aura za ta sha wahala a kan wanan cutar tashi, dan Allah ki faWamun gaskiyya, nasan ba zaki Soye ba, sanan kin san Yayata ba wani kiSa gare ta ba, kuma wallahi ba xan taSa cewa daga bakinki na ji ba, ko a gidanmu."

Tsuru-Tsuru nayi da idano, tabbas nasan komai da ta faWa gaskiyys ne, Amma idan na fad'a mene makoma ta, nayi munafunci, ko nayi taimako?.

"Wallahi, Salma ba zan ta Sa cewa a bakin ki naji ba." Wata nannauyar ajiyar zuciya na sauke, sanan na ce."Kin san bani da alak'a kyakyawa da Mus'ab, abubuwan shi ba su shafe ni ba, kuma ba na saka kaina, domin nasaka SAKATA na kulle duk wata ™ofa da za ta had'a wani abu tsakani na da abinda ya shafi Mus'ab."

"Nasani, Amma ba zaki rasa sani wani abu a kai ba, bani zaki yiwa ba Salma, 'yar uwata da rayuwarta." Shiru nayi ina tunani a cikin zuciyata, mai zai sa na Soye gaskiyyar nan, mene ruwana da tonan asirinsa, idan ma na rufa mai aairi ban tsane shi ba, gwanda na to na masa asiri ko mutuwa ne ma yayi, karewa.

"Duk abinda na fad'a miki, idan har kika fad'awa wani ni ce na fad'a miki. Ubangiji ya gama ki da Masifa a rayuwa." da sauri ta gyad'a kai sanan ta ce. "Na yarda wallahi, babu wanda zaiji ke ce kika fad'amun."
Chapter 7 · 0% Book details