← Book details Rayuwar Rayhana Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 16

Sashe 9

Rayuwar Rayhana Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

- ZUCIYA (tana son kullum ta yi ta tunanin wannan mace).
- KUNNE (yana so kullum ya ji muryarta).
- HANNAYE (suna so su kai kansu gareta).
- BAKI (yana so ya sumbace ta)
- KWIBI (pelvic girdle) zuwa kafafu (suna so suyi exceptional tarayya ta har abada da ita (sexual need).
-Dr. Norman Vincent Peale
(American Psychologist)
-SegmundFreud (Sociologist/Psycho-Sexual Analyst....)

Wannan shine tunanin Ibraheem, tunanin da ya kusa shekawa dasu jeji su karairaye da dan kyakkyawan jaririn da Allah ya basu.
Suka dauki buri mai yawa suka dora a kansa, musamman hope din ya gaji suna da halin mutum mai daraja da martaba a garesu (Muhd. Mansur).
Karfe tara na dare suka shigo Kano suka doshi Lamido Crescent. Malam Dahiru ya wangale musu kofa suka shiga.
Daddy, Mami, Jawahir, Abida (babu Azizah) suke cin abincin dare tare bisa tebir cikin raha da annashuwa mai yawa wadda su kansu sun mance tun yaushe rabonsu da hakan, a kalla za su iya cewa, tun kafin Khalipha ya ce yana son Rayhanah, soyayyar da ta wargaza musu gida da duk wani farin cikin dake cikinsa.
Ibrahim Mansur da Khalipha Abdullahi Mansur Takai, Matasan Maza masu wata irin baiwa ta zati da kamala da wani kwarjini na daban daga Indallahi, suka yi sallama cikin muryoyinsu na kasaita, Balarabiyar surukar na biye dasu, Ibraheem rungume da jariri.
Gabadaya daga ‘ya’yan har iyayen mikewa tsaye suka yi, suka gigice suka rikice da murna. Yau ga Yaya Khalipha ga Ya Himu......... ga baby da rabon da su same shi cikin gidansu shekara a kalla goma.
Rige-rigen karbar baby ake tsakanin ‘ya’yan da iyayen, ba wanda ya bi ta kan bakuwar fuskar sai Jawahir, ita ta nemota ta rungume, ta yi mata jagora zuwa tebir dinsu tana zuba mata lemo.
Sai da kowa ya dau baby sannan hankali ya dawo kanta. Daddy da Mami “Sannu Mimtaz”. Suke jera mata ba kakkautawa, kanta a sunkuye tana dan murmushi. Ai a take Mami ta mike ta soma shirin jego, abincin da ba ta ci ba kenan.
Su gidansu basu gina shi da safayan daki ba, don basu bukatar bakin kwana. Don haka Mami a dakinta ta sauki Mimtaz. Nan da nan ta yiwa kuku waya ya zo, ta lissafo abubuwa masu yawa na fannin kayan abincin da mai haihuwa take bukata.
Ta hada mata ruwan dumi da dettol ta sanyata a ciki, ta dauki baby ta soma wanke shi sai da ta yi sabi uku tana canza ruwa. Ta shafe shi da olive oil ta sunke shi cikin kayan sanyi farare kal masu kamshin turaren baby mara karfi.
A sannan ne bawan Allah ya soma atishawa. Mami ta hau fada,
“Hala A.C kuka kunna a motar ko tagogi kuka bubbude?”
Ta inda take shiga ba ta nan take fita ba a kan Himu da Khalipha. A.C din gidan ma kashe su ta yi duka kowa ya hakura, ayi jegon tare da shi. Daddy na ta yi mata dariya da zolaya.
“Ba saban ba! Ni Asma’u na zama kaka”. Ai kowa sai da ya dara.
Da Ibraheem ya ji gumi ya fara jika shi sai ya hakura da cin abincin ya yi ta kansa (ya shige dakinsu tun na kuruciya da samartaka ya kure A.C) ya yi kwanciyarshi yana hutawa, zuciyarshi babu sukuni ko kadan, ta cunkushe da tunani.
To wai ina matar da aka aura masan? So ake sai ya tsaga billensa ya tambaya? Ai da nauyi, Daddy na son ja masa rai ne kawai ya wahalar da shi. Shikuma wallahi tunda haka ne ko za’a shekara bazai tambaya ba.
Shima fa yana so ya ga irin wannan farin cikin da tarairayar a fuskar Daddy da Mami a kan nashi iyalin. Da ya ga tunanin na damunsa sai ya kira Sapna suka shiga hirarsu, tana gaya masa kewarsa da take ciki, yaushe zai dawo? Kai tsaye ya ce,
“Sapna na dawo gida kenan mahaifina ya yi min aure!”
Wannan ita ce kalma mafi muni da Sapna ta taba ji a rayuwarta. Ji ta yi kamar ya caka mata mashi a kahon zuci. Sai ta fara yi masa kuka mai girgiza zuciya, ya yi saurin kashe wayar, domin ji ya yi banda ya rungumeta ya rarrasheta ba abin da yake so ya yi.
Ya soma tambayar kansa anya Allah ba zai tuhume shi da hakkin Sapna ba? Ya riga ya mai da ita emotionally disturbed zai yi wuya ta iya fiddashi daga rayuwarta farat daya.
Shima zai dade bai mantata ba a sabuwar rayuwar da ya bude yanzu. Yana rokon Allah ya yafe masa itama ta yafe masa a kan turbar da yasa Sapna, ya gudo ya barta.
Duk da ya san bai taba keta mutuncinta ba, amma yana rage zafi da ita. Ita kuma tana ba da kai ne saboda son da take masa, da kuma tabbacin da take da shi na zai aure ta.
‘Yan’uwana mata musamman ‘yammata ku gane, ku hankaltu kusan irin sarrafawar da za ku yiwa soyayyar saurayi a zuciyoyinku, don maza, musamman yara irin Ibraheem masu tashen naira da kuruciya da zurfin ilimi, wallahi ba kowacce mace suke aura ba, sai innocent.
Za su yi soyayyar wucin-gadi dake ne kawai don amfanin kansu a dan lokacin da suke bukata, in sun gama abinda ya kusanta sure dake su tsallake su barki su nemi ‘yar mutunci mara kyale-kyalen duniya da budadden ido su aura. Yarinya danya jagab wadda ba ta kai shekaru ashirin ba ke kuma (used and dumped)Sunanki.
“Bye-Bye Sapna........!”
Ibrahim ya fada a hankali, wasu hawayen tausayi da sabo cike da idanunsa. “Ni da Illinois (Chicago) watakila sai da yawo”. Abin da yake fada cikin zuciyarsa kenan.

*****
Chapter 9 · 0% Book details