← Book details Rayuwar Rayhana Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 16

Sashe 4

Rayuwar Rayhana Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Karfe biyar na Asubahi tana tsaka da barci sai ga kira again, ta yi dan tsaki ta mika hannu ta dauko wayar tana ganin laifin kanta da ba ta kashe wayar ba tun jiya, ga shi an katse mata barci mai dadi da take yi bilhakki.
Sai dai ita kanta ta san ba laifinta bane, laifin yatsunta ne, sun kasa kashe wayar kada mai Turanci mai dadi ya bugo bata dauka ta sake gillara masa karya ba.
Ai tana ganin lambar ce sai ta nemi barcin da ya cika mata ido ta rasa. Ta amsa da sallama cikin muryar barci, wannan karon tasirin da muryar ta yi a jikin Ibrahim Mansur, Allah ya yi yawa da shi, ta yadda biro na bazai iya rubutawa ba.
Har ta kai ga Ibraheem ya fada cikin wani yanayi na daban. Muryarshi can kasan makoshinsa ya ce,
“Ki yi hakuri na tashe ki daga barci”.
“Don’t mind”. Ta sake cewa.
“Jumah!”
Ya kira sunanta da murya (which is deeply suffering).... Sai ta ji jikinta ya kama rawa, ta yi magana cikin sarkewar harshe.
“Doctor is not yet at office!”.
Ta kashe wayar hannunta yana rawa, gangar jikinta ma gabadayana yi. Irin wadannan mazan sune masu yin zinar murya, me yasa zai rika yi mata magana da irin wannan sauti mai kassara gabban jiki kamar wata matarsa ko budurwarsa? Ba za ta kuma amsa wayarsa ba. Batasan cewa murya ce da Ubangiji Subhana ya halicce shi da ita ba.
Sai kuma ta baiwa kanta dariya, sanda wani bari na zuciyarta ya tambayeta,
“Wa ya gaya miki haka miji ko saurayi ke yin magana da budurwarsa ko matarsa Rayhah?Tunda ke baki da saurayin ko mijin? Babu kuma wanda ya taba yi miki magana hakan including Yaya Khalipha?”
Oho!”
Ta fada tana kyabe baki tareda shigewa cikin lallausan bargonta tana cewa,
“A to, haka dai na ga Daddy na yiwa Mami magana, ita ma in ya yi tafiya tana waya da shi ai haka take yi mishi magana”.
Barci ne mai karfi ya dauke ta. Hasken rana da ya hudo ta farin labulen da ya zagaye dakin barcin nata shi ya ratso ya dallare mata fuska. Ba shiri ta tashi tana mittsike ido ta fada toilet ta yi wanka ta yi brush da yake ta yi sallar Asubahi ta fito falo.
A kicin ta jiyo motsin Inna, don haka ta tasarma kicindin. Can ta iske Inna Juma tana kwabin Alkubus, ta ce,
“Allah ya ja da ran Inna ta, yau Alkubus zamu ci haka?”
Tana buga fulawar ba tare da ta juyo ba ta ce,
“Ni ba ke nake yiwa ba, Baba Likita nake yiwa don jiya ya gaya min yana son shi”.
“Ba kya jin magana Jumah.......! (ta fada da sauti irin na Ibraheem) wanda ita kanta ba ta san sanda muryarta ta karye ta canza ta koma haka ba. Na gaya miki yau ba zai zo ba zai je Takai Asabar din karshen wata ce”.
Inna ta yi dan jim, sannan ta juyo ta dubeta. Abubuwa biyu ne suka sa Innar yin shirun da juyowar.
Na farko kiran sunanta da Rayhanah ta yi da wani irin amo (tune) da ba nata ba, na biyu kuma ba ta ce mata Inna ba kamar yadda ta saba.
Gani ta yi Rayhanah na rawar dari, ta kankame hannunta a kirjinta, murya na rawa idanunta na lumshewa, suna budewa ta ce,
“Inna sanyi nake ji”.
Sai ta tsame hannunta daga cikin fulawar ta rufe ta don ta tashi, ta wanke hannunta ta kama Raihanan, ta soma tofa mata duk addu’ar da ta zo bakinta, domin a tsammanin Inna aljanu ne suka shiga jikin jikar tata yanzu-yanzun nan.
Tabbas muryar da ta yi mata magana da ita, ba tata ba ce.
Daki ta maida ita ta ce ta kwanta, bari ta je asibiti ta kira Dacta (da yake ta san ofishinsa ya taba kaisu).
Rahane ta ce, “Wai Jumah........! (ta kara yin magana da irin sautin dazu) sau nawa zan gaya miki Daddy baya nan ne?”
Inna ta ci gaba da tofa mata addu’a. Haushi ya kama Rahane, don ta ga Inna ta mai da ita mai aljanu kawai don ta ce da ita tana jin sanyi.
“Kinga Jumah..... (ta kara fada da sautin Ibrahim da tune dinsa na yin magana) jeki ki yi Alkubus dinki, ki rabu dani don Allah bana son wannan tofe-tofen da kike mini, fever ne kawai ke son shiga na, rufa min bargo, jeki don Allah”.
Inna ta ce,
“Ba zan tafi din ba, aljani ke son auren ki. Bari Baba Likita ya zo a daddale magana, idan dan American nan baya sonki, to ya sahale miki ki yi rayuwar ‘yanci ki samu wani mai sonki ki aura.
Wannan ba aure bane, watanni goma fa! Ana shirin shiga na sha daya. Babu miji ba dalilin sa”.
Inna babatu take ba ta san cewa Rayhanah ba jinta take ba. Zazzabi mai zafi ya rufeta ruf. Ina ma ba ta kashe wayar nan dazun ba, da watakila ta ji sunan mai wannan poisonous murya wadda ta dura mata virus ta cikin kunnuwanta ta haifar mata da zazzabi mai zafi.
Ita dai fatanta Inna ta fita ta ji da abinda ya sameta, amma Innar ta ki. Sai da ta hada da magiya sannan Inna ta fita tana ta mita, ita wannan aure ya isheta, ba ta san irinsa ba. Bata taba gani ba!
Bayan fitar Inna kira ya sake shigowa, Rayhanah ta daga, duk da ta ce ba za ta kara dagawa ba, zuciyar da gangar jikin sun ki amincewa, cewa suke;

“........ ba zamu samu sauki ba in bamu ji shi ba, ba zamu barki ki zauna lafiya ba sai mun ji ko shine IBRAHEEM!!!
[12/25/2019, 15:42] Takori: Ya tabbata ta amsa kiran, amma ba ta yi magana ba.
Ya dade shima bai ce komin ba, sai da ya saisaita kansa ta hanyar yin ajiyar zuciya akai-akai, sannan a sanyaye ya ce,
“Am now not to ask for Doctor, (yanzun ba Dr. Zan tambaya ba) don haka don Allah kar ki kashe min waya.
I want to know more about you..., Concerning you. ...”
Ta ce, “You can ask me anything (za ka iya yi min kowacce tambaya) insha Allahu ba zan kashe ba”.
Ta fada da muryar da ta kara kassara Ibraheem.
Ya ce, “Meye alakarki da Doctor Mansur?”
“Likita da mai taimaka masa”.
Ta amsa kai tsaye.
“Wannan matsayin da kike ikirari bai yi isar da zai sa ya baki wayarsa ba. Don Allah!Ke wace ce dinsa???”
Tunda ya ce ALLAH! Sai ta ji ba za ta iya yi mishi karya ba. Kuma jikinta yayi wani irin sanyi, da wata muryar again da Ibrahim ba zai taba mantawa ba, ta ce,
“Kafin in amsa maka, nima ina so in tambayeka don ALLAH! Ko kai ne IBRAHIM.....???”

Shiruuuu! Ya bakunci kunnenta. Da ta duba sai ta ga cajin wayar ne ya mutu. Don haushi sai raunanniyar zuciyarta ta ce da ita,

“Ki rushe da kuka........”
Chapter 4 · 0% Book details