← Book details Rayuwar Rayhana Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 16

Sashe 2

Rayuwar Rayhana Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mami dake kwance cikin zazzabi mai zafi a dalilin damuwa da matakin kauracewa da Dacta Mansur ya dora mata, da tunaninsa na cewa ita ta hana Ibraheem daukar wayarshi, bayan ita ma fiye da watanni uku kenan rabonta da jin muryar dan nata.
Abin da basu sani ba shine, Ibraheem ya yi fama da matsananciyar rashin lafiya na (Ulcer). Ba komai ne mujazar rashin lafiyar Ibraheem ba, rashin Cin abinci ne, da tarawa kai aiki wanda ya fi karfin jiki da kwakwalwa su dauka (stress). Kuma ko da wasa bai gayawa Daddy ba, don a lokacin Daddyn ya rikice da murnar maganar da suka yi a waya wai ta zancen aure.
Don haka bai gaya masa ba ko da wasa ya tsallake zuwa wani asibiti a ‘San – Francisco’ ya yi jinya ta lokaci mai tsaho, diyar Ambassadan Nigeria a Amurka ko-ko a ce budurwar sa, Sapna, ita ta yi jinyarsa.
Cikin ‘yammatan bakar fata dake kara-kaina a kan Ibrahim musamman ‘ya’yan Jakadu da zaunannu (wadanda aka haifa a garuruwa daban-daban cikin yankin Amurka da Colombia) Sapna ce kusan a ce ta samu kallon kima daga Ibrahim, itama din a dalilin Babanta ne ya hadasu tun wani aiki da Ibrahim din ya yiwa babban dansa na dashen koda mai suna Ali.
Su mutanen Sokoto ne usul, Hausarsu ce take fallasa hakan. Za’a iya cewa Ibrahim na son Sapna, kasancewarta daban da sauran ‘yammatan sa, mahaifinta ba dattijon banza bane, a’ah, Basakkwacen Dan bokone dake maintaining nationality din sa dana iyalinsa a ko’ina. Yake kuma iya kokarinsa akan tarbiyyarsu.
Sapna ba ta shigar banza, ga kwakwalwa, daliba ce a jami’ar da Ibrahim ya yi (University of Chicago) gata da son addini, ga kyau kamar ita ta yi kanta. Itama baka ce (black beauty), don haka Ibrahim ke son ta. Ba ta da rawar kai da kula maza. Don haka mu’amalarsu ta yi tsayi.
Ibrahim zai iya rantsewa shine namiji na farko da ya kai hannu jikin Sapna, ya sanyata cikin wata rayuwa da baza’ace bata sani ba amma bata yin ta, tayi amanna da itane alfarmar kalmar SO da tasirinta musamman ga diya mace ma’abociyar rauni da gajartar tunani, bai kuma taba keta alfarmarta ba, ba ita kadai ba ma, bai taba ba, iyakacin abin kenan (refreshing).
Ya kuma dade da alkawartawa ransa duk rintsi ba zai taba keta alfarmar diya macen da ba matarsa ba, saboda fadar (S.A.W) a kan zina, idan ka yi da ‘yar wani, babu shakka za a yi da ‘yarka, kanwarka ko uwarka.
Wannan yasa Ibraheem sau tari kasancewa cikin azumi, domin danne sha’awar zuka-zukan matan dake neman cinye shi danyensa, ya kuma daurawa kansa al’adar kin rike waya, wannan kwarai ya taimaka sosai wajen gyara rayuwar Ibrahim.

Don haka ne da Daddy ya kawo zancen aure ya yi saurin amsawa, domin ya iso wani limit na tsananin bukatar auren, saidai ya yi zaton Daddy zai ja abin da dan nisa har ya gama da wasu ‘yan matsalolin dake gabansa, musamman zuwa San-Francisco jinya. Ya kuma fi son zaben Daddyn akan zabensa, don ya san ba zai taba zaba masa matar banza ba.
Ko da nan gaba zai kara da Sapna, a kalla yana da uwargidan da ta san kimar iyayensa; Mamin nan da Daddy da babu kamarsu, za ku ma ta san cewa zaman iyayensa take, kada ta kawo masa wata fiffika idan ta san shi ya ganta ya ce yana son ta.

Akwai dai abinda ya taba takura zuciyarsa a can baya, wani lokaci can da ya shude na kuruciya.....Yeeeesss... kuruciya mana..... Amma mai GIRMA!!! It goes far beyond mere or casual assumption! Wanda ya yiwa yakin zuciya da kwakwalwa, har ya samu yayi fata-fata da shi ya fatattakeshi daga rayuwarsa, domin ya fahimci ba karamin barazana bane kuma kalubale ga ci gaban rayuwarsa, da abunda ya raboshi da gida, iyaye da yan uwansa.
Ya tabbata barin abin ya habaka ko ya fito sarari (a wancan lokacin) da yake determined matashi (matashi mai kuduri) zai rugurguza ginin da yake son yiwa rayuwarsa ne da burin iyayensa akansa.
Kuma yanada burirrika da al’amuran da yasa gaba da suka sha gabansa (al’amarin) suka dameshi suka shanye a muhimmanci.
Tun daga wancan lokacin Ibraheem bai kara takurawa zuciyarsa a kan diya mace ba. Kananan kura-kuran da yake yi ma (Lamamu), ya na rokon Allah ya yafe masa as soon as ya aikata. Domin a ganin Ibrahim da wautarsa a wancan lokacin (it’s something that a healthy human being cannot do without), ya na da kyakkyawan hope din cewa, daga ranar da Daddy ya ba shi auren da yake ikirari, babu shi babu lamamun.
Abu daya ma yasa yake refreshing din (bakin Sapna), labbanta da tsagar bakinta su ke fizgar hankalinsa kamar ita ta yankawa kanta, take kuma ba shi a araha, saboda son da take masa. Shima kuma yana jin zai iya aurenta ko a nan gaba, amma ba a matsayin uwar ‘ya’ya ba.
Dalilinsa shine gata ya yiwa rayuwarta yawa, ba za ta iya yiwa ‘ya’yansa irin tarbiyyar da yake so ba, irin wadda uwa da ubanshi suka dora su a kai.
*****
[12/24/2019, 21:48] Takori: Hankalin Ibraheem ya yi kololuwar tashi jin Mami na kuka. Ya kara rike wayar a kunnensa da kyau, sai ya ji cikin shesshekar kuka Mamin na fadin;
“Daddy no longer love me now........ a kan wani dan kuskure kalilan.... HEEMU ya zan yi???”
Ta ci gaba da rusa masa kukan da bai taba ji ko ganin ta na yi ba.
Abin da ya sani shine, Mami da Daddy na matukar son junansu, ta yadda har daya baya iya jure bacin ran daya na lokaci mai tsayi, ba tareda ya shiga tashin hankali ba, ba kuma ya daukar fushin dan’uwansa da sauki ba tare da ya yi exaggerating al’amarin ba fiye da kima.
“Cool down Mamee....... take it easy, kukan ki na gigita ni. Ban son in ji ko& laifin na mene ne, amma zan bai wa Daddy hakuri.
Nima ba cikakkiyar lafiya ce dani ba, last week akai discharging dina from bed a SanFrancisco. Zan kira Daddy yanzu........”
Ai sai Mami ta manta da nata damuwar, muryarta na rawa ta ce,
“Me ya sameka?”
“Ai na ji sauki Mami, ulcer na ce ta motsa irin motsawar da ba ta taba yi min ba. Ban gaya muku bane don kada na tada muku hankali ku zubar da aiyukan ku ce za ku taho wajena. But am more than fine now. Luv u Mum!
Kuma fa ya kamata zuwa yanzu ki dinga kiyaye lafiyar zuciyar Daddy, shekaru sun tura, yana bukatar stable family care.
A abubuwa da dama kuna da ra’ayi daya amma ya ce yanzun kin canza, saboda rudin kawaye. Kin zabi bin ra’ayin kawayenki akan nasa.
Kin daina bin ra’ayinsa, sai dai ke ya biki, sai abin da kawayenki suke so kike yi wadanda kin kasa gane ba masoyanki bane, anya Mami??? Ina nan tahowa Nigeria nan da wata daya”.

Dr. Asma’u ta kawo doguwar ajiyar zuciya. Wane irin zurfin ciki ke da Dacta Mansur da babu mai jin zuciyarsa sai Ibraheem? Hatta ita MATARSA Asma’unsa!!!
Ita ko a fuska bai taba nuna mata tana yi mishi ba dai-dai ba, duk da ita akan sanin kanta tasan ta yi mishi ba daidai din ba, kawai ya daina yarda ya kadaice da ita, ya daina zaman gidan sam-sam.
Abinci ko ta mance yaushe rabon ya zauna su ci shi tare da ‘ya’yansu, wanda a da yake da kakkarfar akida a kan hakan.
Domin ya kan ce, hakan na kara kauna a zuciyar ‘ya’ya da iyayensu. Yana hana yaro ya zama mai kwadayi, yana kara jin kai da hadin kai tsakanin ‘ya’ya da iyayensu.
Abin da Mami ba ta sani ba shine, can a (Farm-Center) yake cin abinci in yana da bukata wajen Inna Juma da suruka, ayi hira ayi raha, ya cikasu da shopping sannan ya dawo (Lamido Crescent) ya nemi gadon barcinsa ya kulle da mukulli, duk don ya hora Asma’un, a bisa sababbin halayen da ta tsiro masa dasu wadanda ba zai dauka ba ko daya.
An ce kukan kurciya jawabi ne, in tana da hankali sai ta gane. Ba ta gane din ba, sai yanzu da dan cikinta ya ankarar da ita.
Ita kanta ta san mai laifi-kan-laifi ce a wajen Dr. Mansur, bai taba tambayarta ina Rayhanah ba, tun ranar da ta kore ta.
Wanda a yanzu take cikin fargabar ina yarinyar ta shiga babu ko duriyarta, amma Dacta bai tambaya ba, bai tambaye ta ina Khalipha ba, ina kuma zancen aurensa da ta hana ya kwana? Ina wadda ta aura masan? Me take ci? Me take bata tunda Khaliphan baya nan?
Ita kanta ta fi son kada ya tambayetan, don ba ta da amsar ba shi. Sosai yake sakar mata fuska a falo in sun hadu gaban ‘ya’yansu, sai dare ya yi ya garkame kofarsa. Wannan ya fi komi tada hankalin Dr. Asma’u wadda ke son gyara kuskurenta, amma Dacta ya ki bata dama. Babu fuska ma bashi da lokacinta.
Ba don yana kwana a gidan ba ma (if he is not on-call) da sai ta ce wata ce ta janye shi, kasancewarsa mai farin jinin mata a wajen aiki, manya da yara, masu aure da marasa aure, duk da ya manyanta saboda yadda Allah ya suranta shi, ya kuma yi masa ado da kirki da tausayi har ma da nuna kulawa ta musamman ga marasa lafiyansa da kananan likitoci da ma’aikatan dake karkashinsu.
Wadatar zuci da rikon addininsa sun shafe shekarunsa a jiki da fuska, sun ba shi shekaru arba’in da biyar na magidanci mai kananan ‘ya’ya.
Chapter 2 · 0% Book details