Sashe 8
Rayuwar Rayhana Part 3 Complete Hausa Novel · about 3 min read
shiru Yaya Khalipha, akwai girma da kimar Dacta Ibraheem da yawa a idaniyata”. Khalipha da Ibraheem basu san sanda suka sa dariya ba saboda yadda ta yi maganar tsakaninta da Allah da darajjawa mai yawa cikin murya da idanunta. Sun shigo Zaria take tambayar Khalipha cikin rada, “Matarsa baka ce ko fara?” Allah ya yiwa Ibraheem ji mai karfi, saboda cin gasasshen nama, don haka Mimtaz ba ta san ya jita ba. [12/25/2019, 19:13] Takori: Khalipha da ba a sirri da shi ya kara rungume wankan tarwadan jaririnsa ya ce da karfi yadda Ibraheem zai ji, “Yadda yake baki, haka take baka sidik. Aradun Allah nawa jaririn zai washe kwana biyu idan ya fara shan nonon farar mace, amma ‘ya’yan IBRAHEEM da RAYHANAH sai an rufe ido don muni. Ni wannan yaron ma ba don ina son mai da shi little Mansur ba, ai Ibrahim zan sa masa tunda ya nuna min da shi yake uban ba dani ba”. Ibraheem bai tofa musu ba.......ya yi nisa a cikin tunanin kalmar da Khalifa ya ambata...... RAYHANAH! RAYHANAH!! RAYHANAH!!! A ina ya taba jin wannan sunan???????? So Khalipha na nufin sunan matarsa Rayhanah.... kamar ya san sunan..... tabbas ya taba jinsa.....amma a ina? Ba zai iya tunawa ba. Shekaru masu yawa sun shude, abubuwa da yawa sun shude, wasu kuma da yawa sun shigo in one’s life journey of struggle toward achievements........ ya takurawa kwakwalwarsa da umarnin ta tuno din, amman ga dukkan alamu ta kasa! Sabida yawan sababbin abubuwa da al’amuran da aka dura mata cikin shekarun da suka gabata din. A dai-dai garin Tiga sitiyari ya kwace masa motar ta yi jeji....... cikin wani mugun zafin nama ya kama akalarta ya maida ta kan titi. Dukkanninsu sai da suka jirkito don ma Allah yasa da belt a jikinsu. Sannan yadda Khalipha ya kankame jaririnsa bai kankame Mimtaz haka ba. Wuta ta daukewa Khalipha da matarsa, tabbas yau sun ga mutuwa kusa. Sai Khalipha ya sassauta murya ya ce “Man! Am not ready to die now. Life began at fourty....” Murmushi ya yi, wani irin murmushi mai nufin amsoshi da dama ga statement din Yayansa Khalipha. Shi kansa ai bai son mutuwar yanzu, gara Khalipha tunda shi har ya ajiye mai yi masa addu’a. Shi me ya cimma a rayuwar? Just his proffession...... Akwai sauran bukatun sa masu muhimmanci bayan wannan..... SOYAYYA..... AURE.... ‘YA’YA.... TARBIYYAR ‘YA’YA..... son binciko hakikanin ko wace ce JUMAH!. A kalla ko ya karbi auren da Daddy ya ke ikirarin yayi masa, yayi alfarmacikin dimbin alfarmominsa da basa karewa agareshi, ya kara masa da ita. Muryarta kawai ya ji.... amma ta tabo wani al’amari mai girma a can tsakiyar zuciyarsa. Zai iya hakura da son bakin Sapna, ya kara da JUMAH NURSE. Wata bakuwar halittar da bai taba gani ba data shigo cikin rayuwarsa in an era of global communication...... (waya), ga auren iyaye mai albarka, ga kuma na son rai, wanda zai karairaya akidar nasara ta zama da mace daya dake zuciyarsa zuwa karbar na sunnah (polygamy) na Musulmi, musamman Bahaushe. “To an taba son mace ba a ganta ba Ibraheem?” Zuciyarsa ta jefo tambaya. “Eh.....” Shima ya ba ta amsa. Akwai wani abu “Soyayyar zuciya” da ba ido ne yake gani ba. Ita wannan soyayyar Allah ne yake yin dalilinta ba ido ba, wanda ke gina tashi soyayyar akan kyawu ko (personality). Wato kyan mace da yadda Allah ya suranta ta ko halinta da dabi’unta. Shi soyayyar zuciya kuma, zuciya ce take so da gangar jiki gaba daya. Wasu daga cikin physical parts (bangarorin jikin dan adam wadanda Allah ya halicceshi dasu) su suke so ba ido ba........ sune.....