Sashe 11
Rayuwar Rayhana Part 3 Complete Hausa Novel · about 4 min read
is cool..... sai ka sunsuna za ka ji. Ji ya yi tsoron ya fice daga zuciyarsa, ya samu kansa da kwanciya sosai a gadon ya ci gaba da shakar kamshin yana kara nazarin dakin. Kaya baja-baja a warwatse ga takalma flat da masu tsini masu kyau da jakunkunansu ‘yan gidan Micheal Kors, Nordstrom, Replica, Cloe da Harrods cikin wata jaka ko sa su ba a yi ba. Ya ce a ransa, “Cikin aljanun ita wannan ‘yar gaye ce, tunda har irin kayan Sapna take amfani dasu”. Nan Ibraheem ya lalace a dakin ya kwana, a dakin ya wuni, sallah ke ta da shi da shaye-shayen lemuna da madarar dake dankare cikin firjin dake gefen gadon. Sai da suka nemi karewa yaje store da zummar karo wasu. Tunda ya zo gidan ma bai leka kicin ba, don a koshe yake shigowa barci kawai ke kawo shi sai ruwa da jus da madara yake sha a nashi dakin. A kicin din ma ya kara tsinkewa da lamarin aljanar gidansa. Tukwane a wanke kal-kal an kife su komi tsaf, amma fa ga potatoe ya rube har ya yi tsutsotsi yana ta wari har ya soma busar da kansa. Da ya bude firij sai ya ja da baya cikin dan tsoro yana fadin “Subhanallahi.....!” Kifi ne, nama ne, markade ne, kaji ne duk gasu nan sunyi kankara sun kankare kamar duwatsu. Ai da azama ya fito ya bude kofofin da ya kukkule ya zari mukullin mota ya yi asibitin da yake gudu don ya gayawa Daddy ba zai zauna gida daya da mutanen boye ba. In ba zai barshi ya zauna kusa da uwarsa ba to zai koma inda ya fito. Daddy yana seminar-room da likitocin bangarensa gaba daya wadanda suke karkashinsa, meeting suke yi mai muhimmanci a kan sabuwar cutar da ta iso Nigeria ‘Ebola’. Ibraheem ya fado dakin tattaunawar babu ko sallama, kwarai a firgice yake kira yake “Daddy-Daddy.....” Gaba daya likitocin sama da talatin suka maida hankalinsu da idanunsu gare shi. Ba ta tasu yake ba sai da ya isa jikin mahaifinsa ya rungumeshi jikinsa yana kyarma yana fadin “Wallahi ba zan koma gidan nan ba, in ba auren za ka bani ba to zan koma Chicago, I’m exetremely perplexed.......” [12/26/2019, 13:19] Takori: Hannunsa Dr. Mansur ya kama sannan ya manna shi a jikinsa ya dauki excuse suka fito yana jaye da hannunsa yana yi masa magana cikin lallashi. “Kwantar da hankalinka gaya min me ya faru?Ka ji Ibrahimu?” Ya rungume shi sosai a jikinsa don ya samu nutsuwa, yana jin yadda yake sauke numfashi da sauri. Sai da ya nutsu ya ce, “Muje kawai Daddy ka gani da idonka”. Daddy ya ce, “Ba zai yiwu ba, baka ganin meeting muke yi”. Ya ce, “To bari in jiraka a ofis dinka ka je ku gama”. Ya ce, “Alright”. Mintuna arba’in Dr. Mansur ya yi kamin ya dawo. Shi ya karbi tukin suka nufo Farm Center, Ibraheem ya kame bakinsa ya yi shiru. Daddy ne ya bude gidan da kansa don Ibraheem baya-baya yake yi. Ya kama hannun Daddy zuwa bedroom din ya shiga nuna masa. “Ka gani, ka gani....... akwai spirit a cikin gidan nan”. Yana nuna masa kan mudubin, ya kuma ja shi ya kai shi toilet yana nuna masa su (Pad) har da guntun sabulu dasu maclean din da aka yi amfani da rabi. Ga jakunkuna da takalma ga su brazier, sannan ya ja shi kicin ya kai shi ya yi ta nuna masa, da gaske a rikice yake kamar yadda ya ce dinne...... “He is perplexed.....” Sai a lokacin Daddy ya soma fahimtar me ke faruwa, me Ibraheem ke son ganar da shi? Dariya ce ta kulle masa ciki yana ta kokarin hadiyeta a cikinsa. Ibraheem ya ce, “Na taba tambayarka wace ce Jumah, ka nuna min wata tsohuwa. Ni kuma tabbas na yi magana da wata yarinya mai suna Juma duk da na san sunan tsofaffi ne, amma wallahi Daddy ni da (fresh girl) na yi magana. Ina jin aljana ke son aure na. I cannot live in this house anymore...... sai ranar da Allah ya bani iyali........” Yadda yake maganar ya bala’in baiwa Dr. Mansur tausayi. Ya ji wani abu ya motsa a zuciyarsa, ya kamo Ibrahim ya jingina a jikinsa. “Wace ce ita Juma din?” “Nurse din ofishinka”. “Ce maka ta yi a ofishina take? Yaushe akai hakan?” Ibraheem ya ce, “Wayarka na kira ta dauka, bayan nan ma mun kara magana, har ta tambaye ni wai don Allah nine Ibraheem? Kafin in ba ta amsa wayarta ta mutu. Kuma wallahi da layinka Daddy”. Sai a nan Daddy ya gano komai, ya tuna randa ya manta wayarsa a gidan. Ya gane Rayhanah ce ta amsa mishi waya ta ce sunanta Juma, kuma ya ga received calls na Ibrahim amma bai bi ta kansu ba. Sai ya ce da Ibraheem, “One minute...”. Ya shigatoilet din Rayhana ya yi dariya ya koshi sannan ya fito. Ibraheem ya kulu ya kumbura, don ya gane Daddy abin dariya ya dauki abin. Ganin yanayin da yaron ke ciki sai ya zama serious. “Kwantar da hankalinka Ibraheem...... ba wata ba ce mai suna Juman, RAYHANAH ce MATARKA!!!” ******