← Book details Rayuwar Rayhana Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 16

Sashe 5

Rayuwar Rayhana Part 3 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Shi din kuwa ta shiga yi mai yawa, sai da ta yi ya isheta. Wannan mutumin da take waya da shi, da matsayin da zuciya da gangar jikinta suka baiwa muryarsa, suka kuma karbeta, da tasirin muryar cikin gangar jikinta da kwakwalwarta, da wata tsoka guda daya dake tsakiyar kirjinta (zuciya) ya fi gaban na wani mutum kawai, wanda yin waya da shi kawai zai haifar da wadannan emotions. He must be the HUSBAND.
Ba ta tantama ko shakkar cewa shine mijinta IBRAHEEM MANSUR TAKAI....
Zazzabin na karuwa, sanyin da take ji na daduwa. Har Azahar ba ta fito ba kuma ta ki bude kofarta kada Inna Juma ta dameta sai ta ci alkubus.
Ita yau ko naman Dawisu (Peacock) aka gasa aka kyafe mata aka ce ta ci da gida da mota (in return), baza ta iya ci ba.
Muryar Ibraheem kawai take son sake ji, da son ganinsa a zahiri. Wata murya data haifar da wasu bakin abubuwa agareta da bata taba ji ba a rayuwarta, ba kuma zata iya fassarasu ko fasaltasu ba da kowacce irin siga don wani ya gane ko ya fahimta.
Zazzabin kuma sai ta ji yana sauka a hankali, a saboda lallashin da zuciyarta ke mata da cewa,
“Watakila shine angon Rayhanah! Amma anya Rayhanah baki kamfato da yawa ba?
Daga ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaki?
Idan kuma ba shi bane hatta wannan tunanin da kike da bari da kike muryarshi na tasiri a gangar jikinki da zuciyarki, kina aikata haramun ne fa, a matsayinki na matar aure!!!
“Astagfirullah!”
Rayhah ta fada a hankali. Ta debo kuzari da karfi ta zubawa jikinta, ta mike cikin zafin nama, ta bude bed-side fridge dinta ta dauko gorar ruwan FARO mara sanyi ta soma kwankwanda. Sai da ta sha rabin doguwar robar sannan ta ajiye.
Ba ta mantawa wannan horon Mami ne, ba ta bari su karya kumallo sai sun sha fresh water sun koshi. Sannan ta adanawa Daddy wayarsa, ta bude kofa ta nufi falo wajen Inna.
Ba ta falon, don haka ta wuce dakin da ya zan mallakin Innar a kasan benenta.
Sanda ta shiga Inna na sallar Azahar, sai ta shiga bayin Innar ita ma ta yi alwalar ta fito ta tada sallah.
Ko da Inna ta idar ba ta kulata ba laziminta ta ci gaba da yi kasancewarta mai son ibada, ba ta zama haka kawai, inda abokin hira ayi hira ayi dariya, in babu a yiwa Ubangiji tazbihi ayiwa Annabi salati.
Ta gane lamarin na Inna yau har da fushi a cikinsa. Ko don ta rufe kofa ne ko don ta ki cin Alkubus ita ba ta sani ba. Sai ta ji ranta ba dadi, ta gurgusa ta kwantar da kai a cinyoyinta, cikin murya mai ban tausayi ta ce,
“Inna idan laifi na yi miki don Allah ki yi hakuri”.
Girgiza kai Inna ta yi alamar a’a. Sai da ta kai laziminta ta ja addu’a ta shafa ta shafawa Raihanan, sannan ta ce,
“Ni baki yi min laifin komai ba, auren nan ne dai nake so a kawo karshensa in ba mai nasara bane”.
Rayhanah ba ta gane abinda Inna ke nufi ba, cikin mamaki ta ce,
“Inna kamar ya ya idan ba mai nasara bane?”
Inna ta ce, “Eh, idan ba mai nasara bane, abin nufi idan yaron baya so, ba zan zuba ido ki kare kuruciyarki a haka ba har jinnu su soma kokarin auren ki.
Daga yau daki daya zamu dinga kwana. Bari Baba Likita ya zo, wannan zaman jiran tsammanin warabbuka ya ishe ni”.
Chapter 5 · 0% Book details