← Book details Rayuwar Rayhana Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 16

Sashe 15

Rayuwar Rayhana Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kararrawar kofa ta soma kara, ai kuwa ta yi fit, ta yi dakinta kamar filfilwa. Inna ta bude kofa, Ibaheem ne a gaba Daddy na bayansa, dukkansu rike da manyan ledojin cefanen da suka yiwowa Inna na African-Food.
Da hanzari Inna ta amshe su tana musu sannu da dawowa. Sai a lokacin Ibraheem ya dube ta sosai, sai ya gane ita ce Juman da Daddy ya nuna mishi hotonta. Sai ya yi murmushi. Ya ce a ransa,
“Lallai yarinyar nan ja’ira ce, wato ita ce Juman”.
Da yake sun yi sallar isha’i kan su shigo a wani masallaci, dining suka hau suka soma cin funkason Inna da miyar ganye da aka yi da manja da kaji zuku-zuku a ciki. Loma biyar Baba Dacta ya kai ya dakata ya soma kwalawa Rayhanah kira.
Ai ji ta yi hanjin cikinta ya nannade waje guda ta kara kudundunewa a cikin bargon ta. Kira har sau uku ta ki amsawa. Sai ya ce,
“Ibraheem je ka zo min da amaryar nan taka. Na lura yau surukuta take yi dani, ko gaisheni ba ta yi ba”.
Ya fada yana nuna masa dakin. Kamar ba zai je ba, ko tunanin me yayi sai kuma ya tsame hannunsa daga plate dinsa ya ciri tissue ya goge, ya sha ruwa sosai sannan ya mike ya nufi dakin.
Murda kofar ya yi ya shiga dakin, tana can karshen gadon ta kudundune cikin blanket mai bala’in taushi kamar curin alkaki, dariya ta kama Ibrahim, gata a Singapore amma ashe bagidajiya ce. Abin da bai sani ba, Rayhanah ko a ina ta tsinci kanta ba abin da zai canza mata akida ko dabi’a, ko al’ada ta kasar haihuwarta.
Ita Rayhanah ba ta yarda da wani abu wai shi wayewa ba, abin da ta sani shine ita musulma ce kuma Bahaushiya, amma tana karatun boko don fita daga duhun jahilci, ba abinda zai canza mata wannan perception (belief). Ba za ta aro wata dabi’a ba wai don ta burge ko a ce mata wayayya, masu yin hakan ma a Informatics Institute mahaukata take kallon su.
Bargon ya kama ya zare shi ta karfin tsiya tana rikewa yana fizgewa ya cillar. Ya zauna a gefen gado ya ce,
“Toh ke Rayhanah kuma haka zamu yi dake? Haka ake tarbar miji? Ko gaisheni baki yi ba Rayhanaah, ga dukkan alamu ma bakin ciki kike da zuwana zan takura miki......”
Shiru kake ji, ta juya bayanta ta cure jikinta.
“Juyo nan, Allah-wallahi kada ki sa in kai hannu jikinki da sunan duka, ko in dauke ki a hannu in kai wa Daddyn ke......”
Nan ma shiru ta yi masa. Bugun zuciyarta na kara tsananta..... tabbas shine suke magana a waya, wanda muryarsa kadai ta yi tasirori masu yawa a zuciya da gangar jikinta.
Ya ce,
“Wato wai ke Jumah ko? To Allah yasa Jummai ce yau gani-gaki, ki kara yi min karya ki gani in ban cinye bakinki ba. Wai ke ga wadda ta matsu miji ya zo har kike tambaya nine Ibrahim???
In ma Ibro ne ga ni, me za ki yi min? Me za ki bani kike nemana???”
Haushi ya kama Rahane, ba ta juyo ba ta ce (cikin kunkuni)
“Ni ban ce ka zo ba, ban ce ina nemanka ba. Tambayarka kawai na yi don in san da wa nake magana ba don wai wani Ibraheem ya zo ba.
Da za ka koma in da ka fito ka sakar min mara in yi karatuna yadda na faro shi ba tare da an takura min ba da na fi farin ciki.......”
Kama baki ya yi da mamaki mai yawa, dariya kuma ta kama shi da yadda take tura baki gaba tana zumbura shi tana cunoshi yana girgiza kai yana dariyar ya mika hannu ya janyo tafin kafarta keeey.... zuwa inda ya ke zaune, ya kama hannayenta biyu ya rike cikin tafin hannunsa na dama ya soma dalle mata baki da yatsunsa na hagu.
Ya ce, “Say it again, ashe baki da ta ido? Watch your words mijinki ne ni ba saurayinki ba....’’
Azaba ta ishi Rahane har leben ta na sama ya dan kumbura..... wasu matsiyatan hawayen azaba suka feso, kamin kuma ta yi aune Ibraheem ya rungumeta gaba dayanta cikin kirjinsa, runguma so calm har baka hango ‘yar Rayhanah cikin physique chest din Ibrahim.
Sannan ya kai bakinsa cikin nata ya soma yin abin da ya fi so a rayuwarsa, wato mouth to mouth kissing. Rikon da ya yi mata mai karfi ne da ta kasa kwatar kanta. Rayhanah ta tsinci kanta a wata duniya ta daban da ba ta taba tsintar kanta a ciki ba.
Abubuwa da yawa ke yawo a kwanya da zuciya da jikin Ibrahim a wannan lokacin. Wadanda shi kansa ya kasa fassarasu, ya kasa daina sumbar kuma ya kasa rabata da jikinsa. A lokacin ta fara kuka na ido, wato zubar hawaye, tunda kamar yadda ya ce din ne zai cinye bakin, ta yarda tareda yin amanna da gaske yake cinyewar zai yi, in tayi la’akari da yanayin yadda yake tafiyar dashi din. Ya ki sakin bakin balle ta koma magiya.
Hawayen da ke fita a idonta su suka sanyayar da jikinsa, ya daina abinda yake yi din ba don ya gaji ko ya gamsu ba, he don’t actually know what he’s deriving in it but it’s something pleasurable ever in his entire life...., amma hakan bai sa ya rabata da jikinsa ba. Data samu hakan sai ta soma ba shi hakuri cikin kuka dole ya karaya ya cikata.
Shi da kansa ya dauko ribbon din daya fadi ya tattara kakkarfan gashin da bai taba ganin relaxer ba ya daure mata...... a ranshi yana ta mamakin yadda mace zata bar gashin kanta in its naturality haka. Shi kuma ya koma da baya ya kwantar da bayansa a gadon kafafunsa na kasa.
Ya nuna mata hanyar kofa.......
“Ki je Daddy na kiranki”.
Ya fada da wani sauti kamar ba nasa ba.
Ta kokarta ta mike amma cira kafa ya gagara. Sai ya yunkura ya mike gaba dayansa yana binta da kallo sosai, ya mika hannu ya kunna fitilar data fi kowacce haske a dakin (ressaince) ta jikin ceiling, wadda haskenta yasa Rayhanah kai tafukan hannunta ta rufe fuskarta.

Doguwa ce sosai amma ya fita, siririya ce amma kirjinta da kugunta a cike suke. Har yanzu sanye take da suturarta ta dazu (belted -waist -shirt) da dogon bakin wandon jeans. Ta zargo belt din tsakiyar rigar ta daure. Sai ya kamo hannunta suka fito suka tadda Daddy da Inna suna hira a falo, tuni ya gama cin abincin.

Rayhanah ba ta taba jin kunyar Daddy a duniya irin yau ba. Ga kanta babu kallabi, sai ta cure a gefe daga can bayan Inna wai gaishe shi take, shi sam ma baya jiyota, balle ya San magana take ya amsa mata.
Abin da ya ce shine,

“Rayhanatu yau Allah ya yanke mana komai ga Ibrahimu ko?”
Daga mishi kai ta yi ba tare da ta dago ta kalle shi ba. Ya yi murmushi na jin dadi da samun kwanciyar hankali cikin kulawa yace
“Babu wata damuwa ko?” Ta sake daga mishi kai again. Da hanzari ya ce,
“Ki bari Rayhanah, kada ki bullo da wannan sabuwar mu’amalar tsakaninmu, wai saboda Ibrahim ya zo.
Ni ban san shi ba ke na sani a matsayin ‘yata, in kuma kin canza min matsayi daga uba zuwa suruki ne, ehh to ki gaya min?”.
Nan ma girgiza kai ta yi. Ya dai tabbatar yau Rayhanah surukuta ta musamman take yi da shi ba zai samu matsayin baya da yake so ba.
Sai ya hakura ya mike a lokacin Ibrahim yana wajen socket ya kunna wayar Rayhanah a inda tasa chaji ya dau lambarta ya zuba nashi lambobin a ciki na layin da ya saka anan Singapore, amma bai sa suna ba.
Daddy ya ce, “To Ibrahim mu tafi masauki, tunda ka yi min firraqu ni da ‘yata, kaima ba zan barka a gidan ba, wuce muje”.
Shi Ibraheem murmushi kawai ya yi ko Rayhan bai kara kallo ba ya yi gaba, ka rantse da Allah ba shine wancan mai deep kisses din ba.
Shi yake tukasu zuwa otel din su, sai dai ya karanta hira tsakaninsu, ya fi mai da hankali ga tukin.
Daddy ne kadai yake ta zuba yana gaya masa don Allah ya rike masa ‘ya amana, ya ji kanta ya tausaya mata, ya tausayawa maraicin ta da raunin ta, ba ta da uwa ba ta da uba sai shi a yanzu. Duk abin da ta nuna ba ta so don Allah kada ka takura mata.
Ibraheem ya ce a ransa,
“Saboda ni ba Da bane, tsinto ni ka yi a bola?”
*****
[12/27/2019, 17:59] Takori: Sabon dare a wajen Rayhanah! Bayan fitarsu ta dade ba ta motsa daga inda take ba, wato bayan Inna Juma. Ita Juman kicin ta shiga ta ci gaba da ‘yan kaye-kayenta da su wanke-wanke, tana yi tana ‘yan wakokinta.....
Wai “duk wayon amarya sai an sha manta....... na zama dauko riga, na zama dauko wando, na zama dauko hula.... shekara mai zuwa war haka zan fara goyo da wankin kashi da share tumbidi........”
Chapter 15 · 0% Book details