← Book details Rayuwar Rayhana Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 16

Sashe 16

Rayuwar Rayhana Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abin da Inna ba ta sani ba shine, ita Rahane ba jinta take ba don ta yi nisa cikin tunani mai zurfi. Da ta gaji da zaman falon sai ta lallaba ta shige daki. Kwanciya ta yi a gadonta don ta samu barci, amma idanun sun ce basu san wannan ba.
Duk motsin da ta yi, duk juyin da ta yi, jinta take a kirjin Ibraheem. Gaba dayanta ma in fact, kamshin Ibrahim take, wani irin kamshi da ba ta taba jin mai sanyi da dadinsa a duniya ba, ba ta kuma iya tantance kowanne turare ne ba. Ta kasa barci sai juyi a kan gado.
Jikinta, zuciyarta da kwakwalwarta ke karbar wani sabon sako mai kassara gabban jiki. Cikin wannan halin, wayarta da Ibraheem ya aje a bed-side ta soma kira. Ba ta yi niyyar dagawa ba, domin dare ya mika sosai, amma da kiran ya isheta sai ta mika hannu ta daga.
Sabuwar lamba ce, amma ta nan Singapore. Daddy ba zai kirata a irin wannan lokacin ba sai dai in ba lafiya ba.
Wannan tunanin da ta yin shi yasa ta daukar wayar ta amsa cikin sanyi. Wajen minti biyu ba a yi magana ba, za ta kashe ya ce,

“Rayhanah kada ki kashe min waya, zamu bata”. Da muryar da ta kasa amincewa cewa ta Ibraheem ce.
A hankali ta ji idanunta sun lumshe da kansu. Ya kara cewa,
“Hira nake so muyi, Rayhaanah za ki yi min?”
Ta girgiza kai kamar yana ganinta. Amma ba tayi magana ba.
“Ba za ki amsa ni ba Rayhanahhh?”
Ya fada tun daga karkashin zuciyar sa in a subdued.
Ji tayi sunan yafi dadi a bakin sa fiyeda bakin kowa, fiyeda bakin duk wani Dan Adam data taba jin ya furta sunan a kunnenta, tun bayan da Allah ya yayemata lalurar ta, jama’a suke ambaton RAIHANAH!!!
“Ni fa barci nake yi, hirar me zan maka da tsakiyar dare haka Ya Himu?”
“Karya kike idonki biyu!”.
Ya fada kai tsaye. Kamin ta ce wani abu ya ce.
“Hira irin wadda mata take wa mijinta, kamin yayi barci”.
Ji ta yi kamar ya kinkimo katon dutse ya dora mata aka. Don haka ba ta amsa mishi ba ma wannan karon. A sanyaye ya ce,
“Rayhanah haka zamu yi da ke ko?”
Da likitan zai tsaga jikinta a wannan lokacin da ya ga yadda jininta ya daina ratsawa a jikinta. Mene ne haka? Yau wane irin dare ne a rayuwarta? Me ke shirin faruwa da ita?
Shirun nata ya matukar tuke Ibrahim, ya ce a dan zafafe.....
“Allah idan ba za ki bude baki ki yi min magana ba zan zo yanzu Rayhanah mu kwana tare, cikin bargo daya. Kin san kuma Inna ba za ta ki bude min kofa ba”.
Hawaye ya cicciko idanunta, wannan shine abin da ta fi tsoro a rayuwarta kenan yanzu (sake kadaicewa da Ibrahim).
Cikin ‘yar rawar murya da karkarwar jiki ta ce,
“To me..... me zan ce maka Ya Himu?’
“Labarin rayuwarki ta baya, da saurayinki Yaya Khalipha.......”
Hannu ta kai ta toshe bakinta.... ta fidda ido alama razana.
“Ka daina irin wannan maganar don Allah..... babu kyau Ya Himu”.
Ibraheem ya lumshe idonsa a hankali ya ce,
“Na bari, to amma samarinki nawa a Kazaure?”
Da sauri ta ce,
“Allah mu bamu da saurayi, Daddy baya bari”.
Dariya ya yi, domin yadda ta yi maganar kuruciyarta ta fito sosai. Sai ya kara tausasa murya,
“Ai an gaya min ne wai da Yaya Khalipha ne zai aure ki......”
“To Allah bai yarda ba”.
Ta fada da sauri. Ta ce a ranta “ko da yake son nawa nima nake son sa, ai kai nake gani a matsayin miji cikin mafarkaina, don haka ban mika masa soyayyar zuciyata gaba daya ba”.
Ba ta san cewa a fili ta fada ba.
Ibrahim ya runtse ido, cikin mamaki da hardewar harshe da nauyin American-accent dinsa ya rinjaya ya ce,
“Har mafarkina kike yi Rayhanahhh?”
Sai a lokacin ta ankara da subutar bakinta, ta ce,
“Lah! Ni fa ba da kai nake ba”.
Ya ce,
“To na yarda ba da ni kike ba, tadin zuci ne ko? Amma ya ya kike ganina cikin mafarkin? Da ‘ya’ya, da jikoki ko Rayhahhh?”
Muryarta na rawa cikin kidima da daburcewa ta ce,
“Don Allah zan kwanta, gobe (8 am) ina da test”.
“Da izinin wa za ki je yin test din?
Da kam kina bisa umarnin Daddy albarkacin cewa bana nan, amma yanzu na dawo, babu inda za ki kuma zuwa ba da amincewa ta ba, goben barin kasar ma zamu yi gobe insha Allahu......”
Ai dama kiris take jira, sai ta soma magana cikin son kecewa da kuka....,,
“Idan ka yi min hakan ka zalunce ni Ya Himu, na wahala a kan karatun nan, ga shi na ci karfinsa watanni tara suka rage min...”.Sai kuka.
Kyaleta ya yi ta yi ta yin abinta, bai kashe ba ita ma ba ta kashe ba. Gidan waya na ta kwasar kudi. Saida ta yi shiru don kanta, sannan ya sassauta murya.
“Na ce zan rabaki da karatunki ne?”
“Eh, ba haka ka ce ba?”
Ya ce cikin ‘yar dariya,
“Ni ban ce haka ba, barin Singapore na ce”.
“Eh mana, am not a kid, barin kasar na nufin barin karatun!”.
Murmushi ya yi mai sauti.
“Rayhanah bani da wannan amsar yanzu, muyi hirar da na ce muyi”.
Jikinta ya yi sanyi kamar ta soma rokonsa amma kawai sai ta fasa, muryarta abin tausayi ta ce,
“Tohh”.
“Has he ever held your hand?”
Da sauri kuma a razane ta ce,
“Wa?”
“Yaya Khalipha!”.

Wuta ta daukewa Rayhanah, ta rasa abin da za ta ce masa. Ba ta san sanda ta ce,
“Kai ka taba rike hannun Aunty Nabilah? Saboda kai ne ba ta so na!!!”.
Very shocked Ibrahim ya zama, ya dauke wuta dif! Ashe da wayonta take yin abu irin na yara, gidadawa. Kuma ashe har tayi masa farin sanin da har ta fahimci akwai wani abu tun tana karama tsakanin sa da Nabilah Abdulqadir. Yayi ta maza Ya ce,
“Ai ni namiji ne mijin mace hudu ne, ko na rike hannunta bani da laifi, tunda zan iya karawa da ita. Ke kuwa tare kuka balaga da Khalipha gida daya, ga soyayya da kusanci mai nisa a tsakaninku, INA KIIISHIIII Rayhanah.......!!! Has he ever did it???”
Duk da amsarsa ta farko ta bugi kirjinta, amma yadda ya yi sentence din karshe ya gigitata...... tana kokarin kashe wayar ya fadi da karfi.
“Kada ki kuskura ki kashe min waya Rayhanah..... zamu yi mummunar sabawa. Na ce Khalipha ya taba rike hannunki ko wani abu makamancin haka?”
Cikin rawar murya ta ce,
“Eh”.
“Sau nawa?”
“Sau daya ne Allah”.
“A ina?’
“A kafar benen gida”.
“Sai kuma me?”
“Wallahi Allah shi kenan”.
Sai ta fara kuka tun karfinta. Bata taba ganin irin wannan mutumin ba mai neman kada a zauna lafiya da titsiye no rhym no reason (babu gara babu dalili). Sai kawai ta ji ya kashe wayar.
Ba a jima ba ta ji shigowar mota harabar gidan, wayarta ta yi kara, shi din ne. Ta sake dagawa hannunta da jikinta duk suna rawa.

“Zo ki bude min kofa, bazan danna‘doorbell’ ba, kada in tada Inna”.
Ba karamin razana ta yi ba, da ta mike tsaye don cika umarninsa ji ta yi hajijiya na dibar ta. A haka ta bi bango ta fita daga dakin ta ratsa ta falo ta bude mishi kofar.
Kayan barci ne farare sol a jikinsa masu dan kauri. Ta ba shi hanya ya wuce cikin falon, amma ita ba ta matsa daga inda take ba, ta rabe a jikin kofar.
Ibraheem zama ya yi cikin tausasan kujerun falon ya nutsa hannuwansa cikin tarin sumar kansa, ya sunkuyar da kai ya yi shiru. Shudewar mintina goma a hakan sannan ya dago idanunsa jajir ya dube ta.
Tana rabe a jikin kofar kamar mai jiran ya gama abin da zai yi ya fita ta rufe kofarta. A zafafe ya ce,
“Ki daina yi min wannan kauyancin da gidadancin da kike mini, a Turai na ganki kina rayuwa cikin Singaporeans, har shigarsu kin iya, ba a Takai na dauko ki ba. Am not here for what you think, o.k?”
Ta sadda kai kasa. Hannunshi na dama ya mika mata......
“Zo mu yi hira!”
Jikinta na makyarkyata ta ce,
“Ni barci nake ji”.
“Tunda na kasa kema ba za ki iya ba”.
“Ya Himu don Allah ka zo ka tafi, Inna na fitowa alwalar asubahi, don Allah ka rufa min asiri, cewa za ta yi ni na kirawo ka.....”
Halin da yake ciki bai hana shi yin dariya ba, gaba daya ta gama firgicewa kamar mai fargabar kada mijinta ya kamata da kwarto.
A tausashe ya ce,
“Zan tafi, but on one condition....”
Ido ta zazzaro masa tana jiran jin condition din. Hannu ya kara miko mata.
“I only want to kiss you again! Rayhaanah don Allah.....!! Zan miki addu’a Allah ya saki a aljanna!!!”.

Ba ta motsa daga inda take ba, sai shi din ne ya taso ya tako a hankali ya tadda ita har inda take. Irin rikon da ya yi mata da amsar da yayiwa bakin nata, ya tabbatar mata he will go far beyond abinda ya roka din, za ta gayawa aya zakinta idan ta sake ta bashi dama.

A lokacin ne Inna ta fito don yin alwala, ta kuwa yi kyakkyawan gani, sai ta juya a hankali da baya da baya har ta buge keyarta da kofa.
Sai karfe shida Ibrahim ya bar gidan. Jikinta babu sauran kuzari ta zauna a kujerar falon tana nemo consciousness din ta da diminishing gigicewarta. Sai da Inna ta tabbatar ya tafi sannan ta fito ta yi alwalarta ta wuce daki ko uffan bata ce mata ba.
A ranta addu’a take musu tana kuma roqon Allah da ya bawa Rahane soyayyar Ibrahim cikin sauki. Ba kamar yadda suke tararrabi ba itada Baba Dacta. Yasa abinda ta ganewa idonta yanzun haka yake har zuciyar Ibrahim!!!

Littafi Na 4 na dauke da karashen labarin kuma tare suke da Dan uwansa. Taku har abada;
Sumayyah Abdulqadir
( TAKORI).
Chapter 16 · 0% Book details