← Book details Rayuwar Rayhana Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 16

Sashe 10

Rayuwar Rayhana Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jego sosai Dr. Asma’u ke wa Mimtaz, tana gasa mata jiki da tawul kullum sau hudu a rana, ta sanyata a ruwan dumi sau uku. Har edcuse ta dauka a wajen aiki don an maida ta Murtala Mohammed Specialist Hospital kamar yadda ta bukata, domin raba kanta da duk wata alaka da Dr. Halima. Tana jin yadda ake fadin irin zagin da Haliman ke mata da tonon silili daga bakin Nurses din da suka yi zaman aminci da ita, da mugun alwashin da ta dauka a kanta na sai ta rabata da Dr. Mansur ta aure shi. Wai ita tsohuwar arniyar Jos ce tubabba kuma ba a budurwa Dacta Mansur ya aure ta ba har da dan shege da ta so ta yi kuskuren lakabawa ‘yarta Allah ya cece su. Ire-iren abubuwan da suka tsorata Dr. Asma’u kenan ta bar AKTH don ba ta iya tashin hankali a rayuwarta ba. Ta soma nemawa kanta tsarin Allah daga sharrin mutum da aljan. Ta rage barci kullum sai tsayuwar dare duk da dai hidimar baby Mansur ba ta barinsu suyi barcin kirki daga ita har Mimtaz din, ga shi da kukan dare, ya wuni sur lafiya lau yana barci dare na yi ya bude musu murya ya gigitasu, nonon ma ya ki sha sai kuka, har su Jawahir kwana suke a kansa suna miko wannan suna miko wancan. Dr. Asma’u ta soma bincikensa da kyau, inda ta gano kashi ne baya iya yi da daren saboda tsutsar ciki, sai ta fara treating dinsa da antibiotics masu sa cin abinci, don ko nono da ruwa in dare ya yi baya amsa da sauran magunguna masu kashe tsutsar ciki da narkar da abinci da taimakawa digestive system. Sati bai zagayo ba yaro ya yi ras, cikin koshin lafiya. Tuni Khalipha ya koma bakin aiki ya barsu a gidan karkashin kulawar likitoci har uku, uwa da uba da brother. Ai kuwa cikin wata daya baby Mansur ya zama garjeje dagawa da kyar, goyawa da dan banzan nishi, domin Azizah da ta zo hutu daga Turkish kasa daga shi ta yi. Ita ma mai jegon ta zama sambaleliya mul-mul da ita, sai ka ganta cikin su Jawahir ta takarkare wai tana koyon Hausa za ka ci dariya, sun saba sosai, ta soma koyon amma namiji shine mace, mace ita ce namiji a bakin Mimtaz. Sai ta cewa Jawahir “Dauko Mohd Mansur ki canza mata audugar nan (Pampas).....” Sai su kwashe mata da dariya sai da Mami ta tsawatar. Ibraheem a nashi bangaren, ya zubawa Daddy ido kamar yadda Mami ta zuba masa a kan aurensa. Tunda ya zo ko da subutar baki Daddy bai yi masa zancen matarsa ba, amma fa yana ta janshi a jiki cikin kauna da kulawa. Ya kuma dauke shi a yau ya sada shi da gidan da ya mallaka masa shi da Khalipha a Farm Center, ya bar dakinsu na gidansu ya koma gidansa, shi Daddyn bai zauna ba har yau ya kwashi takardun Ibrahim ne ya mikasu federal. Abin da bai sani ba, kuma miskilin dan nasa bai gaya masa ba, shine cewa ‘nephrology associates’ da sauran ‘medical associations’ da yake ciki suna ko’ina a duniya za kuma su ba shi aiki dai-dai da matsayinshi a (Illinois Teaching Hospital) Chicago sai inda ya zaba. To zaben ne har yanzu bai yi ba, saboda basu zauna da Daddy ba har yau ko ko ya ce Daddy bai ba shi fuskar ya furta masa damuwar tashi ba. Babu zancen da yake masa sai na aiki kamar wani inji babu hutu babu mata babu budurwa saboda shi karfe ne, kullum ya yi ta hada shi da voluntary jobs wato aikin sa kai na neman lada ga marasa karfi masu cutar koda a Najeriya da basu da karfin fita waje kamar wani inji. To ya daina zuwa AKTH, Abdullahi Wase, Murtala Mohammed daga yau zai yi kwanciyarsa a gida ya huta, Daddy ya yi ta boye matar zai koma ya auro Sapna. Wani abin dariya Ibrahim ya tambayi Daddy rannan suna kan hanyar zuwa Abuja. “Plz Daddy wace ce Juma da ta amsa wayata lokacin da ka bar wayarka a office ta amsa kirana?” Daddy ya ce, “Au Juma? Ai ba a ofis bane na bar wayar a gidanka ne. Ita ta amsa ma wayar?” Ya ce, “Eh”. Cikin fargaba ya ce da Daddy, “Don Allah Daddy zan iya ganin hoton ta?” Fuska a sake Dacta Mansur ya ce, “Why not?” Ya yi parking a gefen titi ya fiddo dalleliyar wayarsa yabude gallery ya fiddo hoton Inna Juma da ya taba daukanta ita kadai lokacin da za a yi mata passport din tafiya Singapore ya nuna masa. Ibrahim hannu na kyarma jiki na tsuma ya karbi wayar ya duba. Me Ibrahim zai gani? Wata bakar tsohuwa ce da a kalla ta ba saba’in baya, ta sha dauri da Adiko ta kawata idonta da farin kwalli ta yi ras!. Haba! Ai ba shiri Ibrahim ya jefa wayar Daddy a kan titi yana haki kamar wanda ya tiki gudun cetar rai. Ya ja bakinsa ya yi shiru kirjinsa na ta bugawa.. Daddy ya bude murfin motar ya dauko wayarsa har ta tsage tawargajeakan titi, ya kuwa ce da wa Allah ya hada shi ba da Ibrahim ba. Fadi yake, “Wane irin wulakanci da iskanci ne wannan? Ba kai ka ce in nuna maka hotonta ba? Don ka ganta talaka sai ka wulakanta hotonta har ka fasa min waya? Ka ci gidanku, ka ci kaniyarka.Wannan tsohuwar mai daraja ce a wajena.....” Shi dai ya yi gum da bakinsa ya rasa inda zai sa kansa da mamaki da takaici. Tsohuwa ce da muryar danyar yarinya har da Turanci? Saboda bakin ciki har suka zo Abuja bai kara yin magana ba. A lokacin Khalipha da iyalinsa sun tafi Hurghada har da Azizah da Jawahir da Abida za a kai wa dangi Muhd Mansur su ganshi. Ya iya zama har da kokarin mikewa bul-bul da shi a lokacin watanninsa hudu. Kamanninsa da Mami da duhun fatarsa basu canza ba da ka ganshi ka ga half caste, very cute da shi. Yau kwanan Ibrahim Mansur goma a gidansa na ( Farm Center ) wanda ya yi dai-dai da cikar sa watanni na hudu a Nigeria, bai taba damuwa da wai ya shiga daki-dakin dake a kulle ya ga yadda suke ba, iyakancinsa ya shigo ya wuce bed room dinsa ko ya zauna a falo ya kalli labaran tara ko CNN. Amma a yau Asabar kulle wayarsa ya yi ya kuma kulle kansa a gidan kada Daddy ya neme shi ya hadashi da aikin dashen kodar nan. Shima tashi ba ta da lafiya it's now weak and delicate to such an extent that it fails to perform its normal functions properly, in zasu dasa mishi mai kwari shima yana so. Daddy yana wujijjiga shi, ba don ubanshi ne ma ba cewa zai yi rainin hankalin ya isa. “I need a life partner, ina sha’awar rayuwar Khalipha, ina bukatar mace, I’m at the Zenith of my thirty (30)”. Abin da yake fada kenan cikin zuciyarsa, yana daga kwance ciki sofa din dake gefe guda a mayalwacin dakin barcinsa, pjamas ne kawai a jikinsa ruwan toka, wadanda basu rufe faffadan kirjinsa ba. Lallausan gashi ne baki sidik kwance luf a kirjinsa. A wannan lokacin Ibrahim rufe idonsa ya yi, muryar yarinyar da ta kira kanta da (Jumah) ta soma amsa kuwwa a kwanyarsa. “Dacta ba ya tare da wayar fah..... Dacta is not yet at office.......” Ya Allah! Wannan wane irin bala’i ne ya same ni? Dana sani da ban yi maka waya ba....... watakila aljana ce ta yi min magana ta dasa min wannan bala’in. Bari kawai na mai da kaina busy na yi sanitary ko na samu sa’eedah. Da nashi dakin ya soma, ya canza bedsheet ya hada kayan wankinsa cikin kwando ya turasu laundary ya goge ko ina ya fesa insecticide ya kullo dakin. Yasa injin shara yana zuke kurar (center carpet) dake tsakiyar wawakeken falon. Yasa duster ya karkade kujerun da plasma da sauran tarkacen kayan lantarkin dake dakin. Sai ya koma daya dakin dake bude wani bedroom din ne shake da kayan wasan yara da gadajensu da study table na yara da katifu, kekuna, babur, toys, teddies da ‘yan tsanoni masu aiki da batir. Sai ya samu kansa da yin dariya, dariya mai yawa da ya dade bai yi ba, ya kara kaunar mahaifinsa. Komai ma sabo ne ba a fiddashi daga kwalinsa da ledarsa ba, don haka dakin baya bukatar wani gyara amma duk da haka sai da ya sharo yana ya fesa Rambo. Daki na karshe wanda shine a kulle da mukulli sai da ya yi ta gwada bounch of keys sannan ya samu guda ya bude. A nan ne Ibraheem ya daskare cikin mamaki. Ibrahim na da masaniyar cewa, wannan gidan da Dacta ya mallaka musu, gina shi ya yi ba sayen shi ya yi a gine ba, don kafin a fara ginin ma sai da ya nemi Ibraheem din da ya turo sample na irin ginin da yake so. Shi ya turo samfur daga San Francisco da Daddyn ya yi amfani da shi, don haka bai sa ‘yan haya ba. Zai rantse shine mutum na farko da ya fara kwana a gidan, amma wannan dakin ya karyata haka. Daki ne yalwatacce mai dauke da fararen Italian furnitures, ga bargo ba a ninke ba, ga kayan kwalliya da turarukan mace da su deo-spray a jere a kan mudubi, a gefe ma wasu jakunkuna ne shake da kayan ado na mata sababbi da alama ko sa su ba ayi ba, ga braziya da pantis farare kal an wanke an shanya a bayi (toilet) ba’a kwashe ba, ga su brush da maclean da turarukan wanka har da audugar mata (pad), da alama an cira ne an aje ragowa ba sabuwa ba ce. Ibraheem kidimewa ya yi da tsoro, firgici da mamaki don ya tabbatar kam ba shi kadai yake kwana cikin gidan nan ba, duk da bai taba jin motsin dan adam a cikin gidan ba. Tabbas akwai aljana a tare da shi, amma fa yana son kamshin dakin aljanar nan idan ma aljanar ce. Sai ya zauna a bakin kyakkyawan gadon ya dauki bargon yana sunsunawa, kamshin
Chapter 10 · 0% Book details