← Book details Rayuwar Rayhana Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 16

Sashe 1

Rayuwar Rayhana Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

 [12/24/2019, 21:48] Takori: RAYUWAR RAYHANAH! 3
Ayadda Mami ta shigo gidan, ya tabbatarwa Jawahir dake zaune tana cin abinci Mami bata cikin nutsuwa. Bata tsaya anan ba ta wuce bedroom dinta ta maida kofa ta rufe ko magana bata yiwa Jawahir din ba, wadda itama bakinta ke cike da tambayoyi fal, data ke so ta yiwa Mamin. Amman ganin babu fuskar da zata yi tambayar yasa ta like bakinta tayi shiru. Tambayoyin data ke so ta yiwa Mamin akan Rayha da Khalipha ne.
Ina Yaya Khalipha ya shiga wata da watanni ta daina ganinsa? Har zuwa wannan lokacin da su Jawahir ke a matakin jami’a iyayensu basu basu iznin rike waya ba, ina kuma Rayha ta shiga? Ta wayi gari ta nemeta sama da kasa ta rasa ta?
Ko kadan zuciyarta bata kawo mata wani abu game da rashin ganin Rayhanah a ranar data wayi gari bata ganta ba, ba, tayi zaton sun je Takai ne da Daddy don shi dama sammako yakeyi in zashi Takai don ya dawo akan lokaci.
To amma bayan wasu yan kwanaki ta koma ganin Daddy cikin gidan bai ce mata komai game da tafiyar Rahane ba.

Wasa-wasa satittika da watanni suka shiga wucewa babu Rahane a gidan. Don haka a yammacin wata ranar Lahadi Daddy yana gida sai ta tambaye shi,
“ni Daddy ina Rayhanah ne?”
Murmushi yayi, yace
“ki kwantar da hankalinki Jawahir, nayi mata AURE!”

Idanun Jawahir duka a waje kamar sa fado abin dariya, cikin kidima da gigicewa. Haka Daddy ya fice ya barta yana dariyar razanarta.
Kwanaki biyu Mami tayi bata je ofis ba, tana fama da ciwon kan barin kai guda (migraine).
Wannan ranar tana kwance a gadonta ta mika hannu ta lalubo wayarta ta kira Ibrahim. Don ta sanar dashi al’amuran da suka cakude mata, suke kuma gallabar rayuwarta ko ta samu sanyin zuciya duk da tasan bazai yi mata maganinsu ba, amma akalla zata ji sauki daga nauyin da zuciyarta tayi, da azabtar da ruhinta ke yi.
Mace ce ta daga wayar, wadda bata tantama baturiya ce, ta sanar da ita cewa Dr. Ibrahim ya daina amfani da wannan layin. Ta nemeta data bata wadda yake amfani da ita tace babu waya hannunsa baya rike waya.
Takaici ya ishi Mami tace “dauki taki wayar ki kai masa har insa yake inyi magana dashi, ni mahaifiyarsa ce”.
Baturiya tace “ya shiga tiyata bazai amsa waya ba yanzu sai bayan awanni goma sha biyu”.
******

(Shekaru goma sha biyu a baya)

Abinda Mamin bata sani ba
shine, matsayin Dr. Ibraheem a yanzu ya zarce tunaninta a nephrology department din overall asibitin Chicago (ILLINOIS teaching hospital). Kai tsaye baka isa kayi magana dashi ba batareda appointment ba, a tun wani aiki da yayiwa shugaban kasar Brunei (sultan of Brunei) na dashen koda, wanda ya bashi damar zama consultant na nephrology department a babban asibitin ‘Illinois’ bayan wani kwas daya halarta na shekara guda a yankin‘Ohio’.

Matashin likitan mai shekaru talatin da uku, mai wasu irin unique akidu da dabi’u da suka hadu suka maida shi wani mutum na daban da sauran al’ummar da yake tare da su. Suka kuma zamo silar mataki iri-iri na cigaba da yake takawa a rayuwarsa at a very young age.
Manyan kasashen duniya ke daukar shi haya yayi musu aiki akan fanninsa, a kuma yi nasara ta ban mamaki.
Zuwa wannan lokacin, I.M Takai, wato IBRHEEM MANSUR TAKAI, ya gama taka duk wani matsayi da Dan Adam din duk da yasan ciwon kansa ke burin samu.
Matsayin da ko iyayen da suka haifeshi basu sani ba, basu zata ba basu san ya taka ba, basu kuma tsammana ba ko a mafarkinsu, kuma bai tsaya neman gaya musu ba, don ba halinsa bane yawan magana ko fadar halin da yake ciki ko abinda yake ciki ga kowa, bayan zuciyarsa, akan wanda aka tambayeshi ma balle wanda ba’a tambayeshi ba, sai ko wanda idanunsa suka gane masa, tunda bashi da halin rufe masa idon.
Yaushe ma ya rike wayar bare ayi doguwar magana da shi? Shekaru uku da suka wuce Mamin ta je Chicago, tayi kwanaki bakwai tare da shi cikin gidansa dake cikin jerin gidajen malaman jami’ar ta Chicago, bayannan Baba Dacta yaje amma bai jima ba alokacin yana lecturing da part time job da asibitin lllinois, abinda suka sani kenan.

To bayan dawowarsu ne al’amuran Ibraheem Takai suka ci gaba da bunkasa. Manyan kasashen duniya dai-dai ne bai jefa kafarsa ba ya yi private aiki dasu ba. Musamman Ohio, Columbia, Bruce da Brunei.To kamar yadda yake ga kowanne lafiyayyen dan Adam, kaddara da nauyin aljihu kan canza da yawa daga halayen dan Adam, duk irin tarbiyya da tsantsenin iyayen da mutum ya tashi a ciki kuwa, Ibraheem is not exempted.

Da fari, wahalar karatu da kujuba-kujubarsa basu sa Ibraheem waiwaye ga al’amarin mata ba, duk da yadda suke binsa kamar kaza da ‘ya’yanta. Ina ya ga lokacin yin wata mu’amala ta soyayya ko akasinta, karatu yake ka’in da na’in kamar bai da sauran wani buri a rayuwarsa sai shi.
Amma da ya hattama karatun, ya samu nutsuwa da hutu, ya kuma soma jefa kafa (outside Chicago) don aiki da samun hutu, duk tsantsenin sa sai da wasu daga cikin tarbiyyar Uwa da Uba suka canza.
As a Proffesional Medical Doctor, Ibraheem bai kurba giya, baya zukar sigari balle wani abu da zai gusar da hankalinsa ko ya sa shi maye. To amma ‘yan mata fa (barin rayuwar kowanne lafiyayyen da namiji), musamman wanda bai da aure kuma jikakke kamar Ibraheem, yaro matashi mai cike da koshin lafiya da tarin ilimi da duk wata alfarma ta rayuwa.
Ya dade da fita daga gidajen malamai ya sayi nasa na kansa (American – mansion) a North-Eastern Chicago bayan wata kyautar bajinta daya samu daga (Sultan of Brunei) akan aikin dashen kodar da yayi masa ya samu lafiyar da yayi shekaru yana fama, da duk wata alfarma da manyan likitocin Amurka ke tinkaho da ita.
Duk da haka Ibrahim ba zaune yake wuri guda ba ko a cikin Chicago, sai ya yi watanni uku baya cikinta yana yawon (private jobs) a duk inda aka gayyace shi aiki tare da kungiyar (nephrology associate). Ita wannan kungiya ita ke tallata members din cikinta da ayyukansu da kwarewarsu ga duniya kuma ta kan turasu su wakilceta idan an bukaci likitocin koda daga cikinta. (It’s not a profit making organisation but for the benefit of its members). Abin nufi, ‘nephrology associate’ ba’a ginata don samar da riba ga kungiyar ba sai don amfanin ‘ya’yan cikinta. Haka da yawan kungiyoyin likitocin Amurka da Africa Ibraheem na cikinta, irin su AAPS (Association of American Physicians and Surgeons), NAD (National Association of Doctors), Alberta Medical Association, AMA (American Medical Association) Flying Doctors Society of Africa, AAD (African-AmericanDoctors Association), WAMA (West African Medical Association) da sauransu.
Cikin shekarun da Ibrahim ya yi a lllinois-Chicago, bai wani kara jiki ba, yana nan yadda yake (Dogo mai kirar karfi). Ma’abocin zati da kamala. Kalar fatarsa ce kawai ta canza sai karin hankali da nutsuwa bayyananniya da shekaru da zurfin ilmi suka karawa fuskarsa.
Baki ne shi kamar Dacta Mansur, jikinsu iri daya, tsayinsu iri daya, zubin jikinsu iri daya, amma a halin yanzu Daddy ya fishi kauri da cika ido na jikin girma. Amma idan ya juya baya yana tafiya ko yana wani abun daga tsaye tsammani zakayi Dr. Mansur ne.

*****

Ya fito daga dakin tiyatar ya shiga (Doctor’s Changing Room) yana cire koren kyallen dake hancinsa da cire korayen kayan tiyatar dake jikinsa ya sanya wadanda ya zo dasu. Yana wanke hannunsa da sabulu a sink din dake cikin ofishinsa bayan ya zare ledar hannunsa, sakatariyarsa Rita ta nemi izinin shigowa, ya amsa mata, ba tare da ya juyo ba.
Ta shigo cikin tarin girmamawa ta mika masa wayar dake hannunta domin ita take hada mishi appointment kuma ita yake baiwa wayarsa take amsa mishi in ya ga mai muhimmanci ce a gare shi ya amsa, in ba hakan ba, ta ce a bada sakon a fada masa, ko voicemail ya hanata sanyawa a wayar.

“Your Mum has called......”

Ta fada cikin tarin girmamawa tare da mika masa wayar.
Ya karba ya duba ya tabbatar Mamin ce. Rita ta juya ta fita ta rufo masa kofar. Ya zauna a kujerar dake fuskantar tebirinsa, cikin nutsuwa ya kira lambar Mami.
Chapter 1 · 0% Book details