← Book details Matar Taj Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 8 OF 20

Chapter 13-14

Matar Taj Part 1 Complete Hausa Novel · about 20 min read

Update!!!!


Ba karamin dadin haduwa da yar Ghana nan yayi ma sabeeha ba dukda ita bata iya sabo da muamala da mutane ba.Saidai ita wannan akwai jan mutane a jiki sosai hakan yasa ta jin dan sauqin abunda take ji aranta.

Sauran yan dakin kuwa wani irin kallo suke mata,babu wanda yace mata ci kanki a cikin su, daman su uku ne kawai sai ita kuma ta hudu.


Karfe sha daya nayi duk suka fara shirin kwanciya daman saboda sai an gama hidimar gidan kuma sai masu gidan sun kwanta kafin suma su kwanta saboda karsu buqaci wani abu.

Sabeeha dai na kan gado tana rarrabaa idanu har suka kashe fitilian dakin, ganin haka yasa itama ta kwanta cikin fargaba, ga saqe saqen da zuciyar ta ke mata game da maganganun wannan mutumin da bata ma san koshi waye ba, menene aihanin kudirinshi akanta? Meysa sai ita? ga nan wajen da aka kawota da sunan leqen asiri bata ma san taqamaimain mey zatayi anan din ba.

Hawaye ne masu dumi suka soma ambali akan fuskanta, tunawa da mahaifiyarta babu abunda take tambayar kanta akai sai 鈥樷€檓eyzaisa mahaifiyarta ta turo ta nan?, shin haka daman kowa ke rayuwarshi ko kuwa itace rayuwarta tazo a haka? Bata san mene farin ciki ba ko kadan dukda tana masifar qaunar mahaifiyarta, tana farin ciki da ganin mahaifiyar.鈥
Tana cikin wannan tunanin tana hawaye har barci ya zugeta mai nauyin gaske saboda makwancin data samu is confortable, gado ne daidai mutun daya ga bargo harda ac a dakin nasu.

Karfe biyar daidai karar alarm ya karade bangaren nasu na ma鈥檃ikatan gida, afurgice sabeeha ta mike zaune don yanda karar ya sauka a kunenta saida yasa gabanta yayi mugun bugu, hasken dakin nasu ne daya bade ko鈥檌na yasa ta duban dakin da kyau, daya bayan daya waennan maids din suka soma saukowa daga gadajensu cikin gaggawa, bandakin nasu suka fara shiga daya bayan dayan kamar yan boarding kafin suyi shiri ciki uniform dinsu na aiki tsaftsaf, kallonsu sabeeha ta dunga yi har suka gama suka soma fita daga dakin, tana jinsu suna yaren su suna kallonta har suka fice ba tare da sunce mata ci kanki ba.

Ita kuwa da mamaki ta bi kofar da suka fita da kallo,komai looks so weird to her, gashi bata san mey zatayi ba ganin duk sun fita gaba dayan su.
Tana nan zaune wadda ta shigo da ita jiya ta shigo dakin,gasheta sabeeha tayi kafin matar ta soma yi mata bayani, da farko wajen drawer ta nuna mata inda kayanta na aiki suke ajiye dasu toothbrush harda pad da dai sauransu.
鈥樷€檙ule number shine ki kasance cikin tsafta koda yaushe,ki shiga kiyi wanka saiki saka uniform dinki ki fito鈥欌€ matar ta fada
Tana kaiwa nan ta fuce tabar sabeeha a tsaye, kamar yanda matar nan ta umarce ta hakan kuwa tayi, tana yin wanka ta saka uniform din ta zumbula hijab tare da mask dinta kafin ta fito daga dakin.

Koda ta fito rasa hanyar da zatabi tayi don kofofin wajen sunyi yawa, saida ta jiyo hayaniya da karar kwanuka da cokula daga wani saseh daban haka yasa ta nufi hanyar, allah ya taimaketa kuwa hanyar kitchen ne, da sallama ta kara kitchen din muryarta chan kasa kasa, gaba daya maids din kowannen su yana ta hada hadan ayyuka babu wanda yabi ta kanta, wannan matar kuwa na tsaye sai bada orders take, ayi wanchan ayi wannan, daman itace ogansu gaba daya, saida ta lura da sabeeha a gefe tukunna kafin ta doso inda take.
Kallonta daga sama har kasa matar tayi, nan take ta hade rai tamau 鈥樷€檙ule no 2, you cannot dress like this, its so unhygienic, bakisan protocols din aykin ki bane鈥欌€
Kallon bakinta sabeeha ta dunga yi don kwata kwata bata gano inda matar ta nufa ba, saidai yanayin yanda take Magana strictly hakan ya tabbatar mata da kamar tayi abunda ba daidai ba, wannan yar ghanan nan ce ta matso inda suke ta fassara mata kafin ta koma wajen aykin ta don matar akwai masifa.

Komawa dakin su sabeeha tayi cikin tashin hankali, ita kwata kwata bata saba yawo haka ba ko agida ma, idan ta saka kaya babu hijab dinnan sai taji kamar tsirara take yawo, wannan yasa koda yaushe take yawan saka hijab.
Haka nan ta hakura ta soma zare hijab din nata harda dan hawayenta, tana cireshi ta ninke ta ajiyeshi gefen gadon kafin ta fuce daga dakin.

Kitchen din ta koma, daidai nan daya daga cikin maid din dake futa da abunci a cikin wani serving trolly ta shugo kitchen din, sabanin sabeeha na tsaye daga bakin kofar suka kusa yin karo da juna, wanda hakan ya janyo attention mutanen kitchen din ya dawo kansu 鈥樷€檈xcuse me, watch your step please鈥欌€
Maid din ta fada tana mai kallon sabeeha, itama kallonta sabeeha tayi kafin ta sauke idanunta hannunta na gaban rigarta tana kokarin kare kirjinta.
Gaba daya kitchen din zuba mata idanu sukayi, gata dai bata da kiba kuma itadai bazaace mata doguwa ba kuma baza a kirata da gajeruwa ba saidai allah yayi mata sura mai fuzgar hankali, baga mace bama balle namiji, full option, she鈥檚 well curved and pictured kamar an zana surarta saboda yanayin kayan jikinta riga da wando na aiki Kenan.
Tsugunnawa tayi ta kwashe savage din da suka zube a kasa kafin ta miqa ma maid din dake tura trolly din, 鈥.No wonder take ta fama kakkare kirjinta ashe a cike suke kamar zasu yaga rigar jikin nata kuma daidai jikinta, a hakan ma bata ji hutu ta koshi bama tukunna,masha allah kamar yar Brazilian don sune masu irin perfect shape dinnan da ba kowa keda irinshi ba, one ina million Kenan.

Gyaran murya da akayi ne yasa duk suka koma kan ayyukansu, sabeeha dai na daga tsaye a gefe tana kallonsu suna abubuwan su cikin kwarewa.


**
Cikin isa ta soma sauko daga stair din cikin shigarta mai aji, babu abunda kake ji sai sautin takalminta da kamshinta, hanyar dining ta nufa hannunta rike da Jakarta.

Waigowa sukayi gaba dayansu suna kallonta daya bayan daya harta karaso dining din, itama binsu tayi da kallo, suna zaune har sun fara karyawa, afiya, fadwa da barad.

Wajen zamanta ta nufa kafin gaba daya suka soma gaisheta, amsa su tayi kafin maid din dake tsaye ta soma serving dinta as usual, daman ita bata cin abunci sosai daga coffee sai dan low calories English breakfast.
Baka jin komai sai karar cokula a dining area din, fadwa ce ta fara gama breakfast din kafin afiya, basuyi gigin tashi ba saida hidaya ta gama tukunna kafin ta miqe tana mai duban afiya dake zaune ta hade rai.
Barad ne ya fara futa daga dining din yana mai kissing din aunties din nashi a kuma kafin yabar dining din.


鈥樷€檔aga kinyi requesting for kudade masu yawa,na tura maki approval letter鈥, anything else鈥欌€ ta karashe tana mai dubansu su biyu
Da mamaki duk suka dago suna kallonta, don kwata kwata basuyi expecting haka daga wajenta ba.
Kallon juna fadwa da afiya sukayi kafin suyi murmurshi, godiya sukayi mata kafin ta fuce daga dining din, head of maids na biye da ita da Jakarta a hannu.
鈥樷€橫a鈥檃m yarinyar da aka kawo wadda zata kula da part din sir鈥︹€欌€
Tsayawa chak hidaya tayi tana wani nazari kafin ta dubi head of maids din, 鈥樷€橧 trsut her with you make sure ba a samu matsalar da aka samu ba da previous one鈥欌€,

鈥樷€檕kay ma鈥檃m鈥欌€
Maid din ta bata amsa kafin ta rufe mata matar dake janta zuwa office, barad na daga gefenta don ita ke kaishi school da kanta.

Futar matar nan ce daga kitchen din ya baima yar Ghana daman jan sabeeha, gaisawa sukayi kafin yar Ghana ta soma tambayarta akan aikin da aka bata.
鈥樷€檃 bangaren ina aka saka ki?, girki ko gyare gyare?鈥欌€
鈥樷€檅ata fada min ba鈥欌€ sabeeha ta bata amsa cikin nutsuwa

Nunfasa yar Ghana tayi kafin tace 鈥樷€檋mm ina maki fatan dai a wannan bangare guda biyu zaki yi aiki don鈥︹€欌€
Zuba mata idanu sosai sabeeha tayi don jin abunda take shirin fada, ganin haka yasa yar gana rage murya don suna da dan yawa a kitchen din 鈥樷€檏inga ayki a gidan nan yana da wasu qalubale daban daban,鈥欌€

Samun kanta tayi da cewa 鈥樷€檓enene qalubalen?鈥欌€
Nunfasawa yar Ghana tayi kafin tace 鈥樷€檃kwai wani part a sama wanda muke kira da demon palace, mudai da muke aiki anan kasa bamu taba zuwa saman ba kuma basusan menene a saman ba, saidai muna kallon duk wadda aka tura aiki chan saman bata wuce kwana daya biyu tabar aiki a gidan nan, a yanda naji ma wadda ta dade da ayki a bangaren bata wuce sati guda ba tabar gidan nan a burkice, shiyasa na tambaye ki don sanin inda zakiyi aiki鈥欌€

Wani tunani ne ya fado ma sabeeha nan take ta danji gabanta ya fadi, 鈥樷€檓enene a saman to?鈥欌€
Yanda tambayar ma ta futo daga bakinta ita kanta batayi tsamanin haka ba.
鈥樷€檋mm babu wanda ya sani, saboda duk waenda sukayi aiki acahn din basa fadin komai game da part din, mudai musan nothing comes good daga part dinnan, wata qila wani mummunan abu ne a wajen鈥欌€


Bata kaiga idawa ba sukaji alamun matar ta dawo kitchen,lokacin wajen karfe tara na safe, kallon inda sabeeha take matar tayi kafin tace 鈥樷€檓uje鈥欌€
Binta abaya sabeeha tayi har suka fuce daga kitchen din, girgiza kai kawai yar Ghana tayi tana mata fatan allah yasa dai ba saman za a kaita ba, don idan da anan kasa zatayi aiki da tuni head(head of maids) ta nuna mata ayyukanta, bangare su sabeeha kuwa zuba idanu ta dunga yi don ganin inda za a kaita don ba karamin tashin hankalinta yar Ghana tayi ba da batun part din saman nan da babu wanda yasan menene a saman, binta kawai take a baya har suka shiga cikin gidan tana sauraron bayanan da take mata.
鈥樷€檓adam bazata samu ganinki ba, so ni zan maki bayanin ayyukanki鈥欌€
Girgiza mata kai sabeeha tayi kanta a kasa har suka soma hawa sama, ita tunda suka shigo ma ta burkice don baza ta iya cewa ga daga inda suke fito.

鈥樷€檃ikinki ba kamar kowanne aiki bane, record dinki ya nuna kin kware ta bangare caregiving, so ina fatan baza a samu wata maatsala ba, sannan akwai rules din ayyukanki, abu na farko da zaki kiyaye dashi shine your job is confidential, you can not tell anyone irin aikin da zakiyi da condition din sir, idan kika kuskura kika fada kuma鈥欌€
Dan tsayawa matar tayi kafin ta juyo ta maida dubanta ga sabeeha,鈥欌€檅a sai na fada maki mai zai buyo ba, just keep that in mind鈥欌€

Dam dam gaban sabeeha ya bada, idan har batayi kuskure ba wannan aikin da za a bata shine aikin da aka turo ta tayi liken asiri akai ko menene?, maganar mutumin nan ce ta fado mata arai 鈥樷€檌dan kinje zaki san irin aikin da zakiyi鈥欌€
Tabbas wannan ne abunda yake nufi Kenan, hannunta har wata irin zufa ne ke tsatsafo mata, sai a lokacin ma ta lura da stairs suke hawa.
Haka suka dunga hawa stairs din mai tsayi kafin su iso saman, kallon wajen sabeeha tayi kirjinta na tsananta bugu kamar ana buga ganga, bin matar ta dunga yi kamar raqumi da akala har suka karaso petion din dake tsakanin part din guda biyu.
Nuni head tayi mata da bangaren hannunta na dama 鈥樷€檅abu ruwanki na nan bangaren, sannan chan鈥欌€
Tayi mata nuni da dayan part din, 鈥樷€檃nan ne zaki yi aikinki as a caregiver鈥欌€

Takowa suka soma yi har zuwa part din kafin head din ta dannan security pins, 鈥樷€檞annan ne pin din shiga ciki, daga ni sai wadda zata kula da wajen sai madam ne kawai muka san pin din, kin gane me nake nufi?鈥欌€
Girgiza kai kawai sabeeha tayi kafin su shige ciki, suna shiga maid ta rufo kofar, nan take haske ya bade ko鈥檌na hanyar walkway zuwa cikin part din, gefen wajen kofar maid din ta dan latsa wani electric dispenser nan take sanitizer ya futo, hannunta tayi sanitizing kafin ta umarci sabeha datayi hakan itama.
Tana gamawa ta soma cire takalmin kafarta daga gefe akwai wani rack da aka jera crocs, daya head ta dauka kafin ta bama sabeeha dayan.


鈥樷€檙ule number 2, you should be very clean sosai, sannan duk sanda kika shugo ki tabbatar kin saka mask and kinyi sanitising hannunki, uniform dinki should be clean as well,ko digon datti a kayanki is not allowed鈥欌€

Girgiza mata kai tayi alamun gamsuwa dukda a tsorace take sosai,ciki suka fara shiga, haske ne ya gauraye ko鈥檌na bau nan take komai ya bayyana, parlor ne mai girma da kyau fari qal komai is organise babu wani karikice sai camera鈥檚 ta kowanne lungu da sako acikin parlorn.
Sabeeha dai bata ma tsaya duban parlorn da kayu ba don tunaninta yayi nisa da abunda matar nan ke fada ma da wanda yar Ghana ta fada mata ga kuma wanda aka turo ta akai.

Saida suka zo dan nesa da kofar dakunan cikin part din matar ta tsaya, 鈥樷€檏arfe shida zaki fara aikinki, sannan daga inda karfe hudu tayi ki tabbatar kin gama komai kin sauka kasa, daya daga cikin ayyukan da zakiyi shine gyaran part din nan, akwai kitchen da duk wani abubuwan buqata,鈥欌€
鈥樷€檛he most important part of your job shine,kula da movement din sir,da abuncinsa, sai medication dinsa,sannan akwai timetable din abunda yafi buqata on a daily basis zaki samu wannan a kitchen, and lastly I will advice you duk abunda zakiyi kiyishi cikin natsuwa banda hayaniya saboda baya son hayaniya.鈥欌€

鈥樷€檞aye kuma sir?鈥欌€ abunda ya fado ma sabeeha arai Kenan, tasan me caregiver ke nufi, saidai abunda bata gane bane shine dalilin da yasa aketa wannan boye boyen da wannan ka鈥檌dojin, komai looks so strange.
Kofar dake facing dinsu suka nufa, nan matar ta bude ta soma mata bayani, 鈥樷€檔an ne activity room din sir, duk ranar Friday zaki dunga kawoshi nan鈥欌€
Kallon wajen sabeeha tayi, wajen cike yake da kayan wasa na yara, babu abunda babu mota ne jirgi da keke dadai sauransu da mamaki take kallon wajen har suka fito daga dakin.


Nuni da kofar tsakiya matar tayi kafin tace 鈥樷€檔an ne kuma bedroom din sir,first thing first by 8 dot yake tashi so duk abunda kikeyi na gyara ki tabbatar kin gama kafin lokacin, idan zaki shiga bedroom din ba鈥檡in knocking saboda baya son any sound ko karar komai, zaki bashi first medication dinshi by 8:30 dot, sannan kafin yaci abunci zaki taimaka mashi yayi wanka ya shirya by 9 zaki bashi breakfast, sai second dose of medication dinshi鈥欌€

Jin haka yasa sabeeha shiga tunanin waye wannan sir din, kalaman matar dataji ne da yanda komai suke yin shi cikin tsari da ka鈥檌doji yasa ta soma tunanin to kodai raino aka sake kawota, to amma rainon da zatayi ne leken asiri?, ita gaba daya ma kanta ya burkice da ala鈥檃marin,

鈥樷€檛hat鈥檚 all for now, zuwa gobe zaki fara鈥欌€ matar ta karashe tana mai nufar hanyar futa daga part din sabeeha na biye da ita a baya.
Kasa suka sauka, maids din dake gyara gyare suna kallonsu ta wutsiyar idanu kamar hankalisu baya kansu, saida sukaga head ta wuce kafin daya daga cikin su ta soma Magana kasa kasa 鈥樷€檔andini, ayna fada maki, wannan a sama zatayi aiki kai amma I pity her,鈥欌€
Dayar da aka kira da nandini ce tace 鈥樷€檛o me she looks like she鈥檚 happy, bata san inda ta jefa kanta ba, ki duba kiga yanda last maid dinnan ta gudu, ta bani tausayi ko kwana biyu bata yi, ni im curious wallahi, menene a saman nan鈥欌€
Matsowa dayar tayi ta rada ma nandini wani abu a kunne鈥︹€︹€

Bayan sun sauko daki sabeeha ta koma na bangaren su, tana shiga babu kowa a dakin don koda suka sauko daga sama ta gansu suna aikace aikace anan kasa, daman yan dakin nasu bangaren aikace aikace suke handling.
Zama bakin gadonta ta doka uban tagumi, tunani kala kala na yawo a kwanyar kanta.


California鈥︹€
Envision academy high school鈥︹€.
School Bus ce ta fito daga cikin school din, dauke da student, babu abunda ke tashi a cikin bus din sai hayaniyar yara, maya da gang dinta na zaune daga gefe su uku ashe wata yarinya suka saka a gaba suna bullying,yarinyar na gabansu a tsugunne maya ta daura kafar ta akan labs din yarinya, su kuma student me zasuyi banda dariyar mugunta, saida aka zo first stop kafin wasu few daga cikin student din suka fita daga cikin motar ciki kuwa harda maya da kawarta inda suka shige cikin yaran da suka futa don kar a gansu.
Suna fitowa maya da kawarta kloe suka yanki wata hanya cikin sauri gudun kar driver yayi noticing din futar su, saida sukayi ma bus din nisa kafin su dan tsagaita, dariya kloe ta fara kafin ta maida dubanta ga maya 鈥樷€檏ai babes this is the toughfest part of running away from school, I can鈥檛 wait to be 18 and free muyi mu gama exams鈥欌€
鈥樷€檋mm, nima kaina na gaji da guje gujen nan just to have fun, meysa sai lallai mutun ya zama 18? Other countries baa yin haka鈥欌€
Daidai nan suka karaso kan titi inda wata mota ke parke daga gefe, cikin hanzari suka karasa wajen motar, maya na gaba while kloe kuma na daga baya.
Suna shiga wanda ke zaune mazaunin driver ya miko hannu zai rungumeta, 鈥樷€檆ome here babe鈥欌€檞ani irin kallo ta watsa mashi wanda ya sashi komawa mazauni yana mai kunna mota, saurayi ne white American yasha wasu kananun kaya, daga baya kuma kloe ce ita ma da nata saurayin black American,
Wanda ke bayan ne yace 鈥樷€檊irls where are heading to?鈥欌€
Maya ce tayi saurin cewa as usual, tana kaiwa nan wanda ke tukawan ya zugi motar suka bar wajen.
Basu tsaya a ko鈥檌na ba sai a wani wajen shakatawa, wajen kamar restaurant, ciki suka shiga, inda daga nan basu tsaya ko鈥檌na ba sai wani sirrintaccen bangare dake cikin restaurant din, kamar koda yaushe zaida wannan black American din yayi Magana da mai wajen don abokin yayansa ne kafin abarsu su shiga ciki don ba a yarda underage su shiga.

Wurin so very dim sai blue light kamar dare, maza da mata na zazzaune kowanne yana harkarshi da drinks a gabansu wasu kuma na cin abunci wasu kuma hayaki suke busawa.

Zama sukayi wajen da suke zama koda yaushe inda sukayi nasu order drinks din, wannan white ameriacn dinnan dai yana kusa da maya, da alamu saurayinta ne don daga yanda yake ta faman bata hakuri kamar yayi mata laifi ne.
鈥樷€檚hut up u cheater,鈥欌€ ta daka mashi tsawa wanda yasa hankalin kowa ya koma garesu

鈥樷€檓aya please鈥欌€ kloe ta fada tana kallonta don suna zaune opposite dinsu.
Hannunshi ya sake sanyawa ya riko nata 鈥樷€檅ebz please im sorry, there nothing between us, its just accidental kiss please鈥欌€

Ajiye juice din maya tayi ta maida dubanta gareshi, 鈥樷€檡ou鈥檙e a cheater and a liar, you think I鈥檓 stupid? Kiss by accident? For goodness sake rick Zara is my friend, how could you kiss her and call it by accident, I see both of you with my 2 eyes鈥欌€

Shima saurayi harzuka yayi yana mai kallonta 鈥樷€檒ook, I don鈥檛 fucking care about the kind of thought you have on this, how many times do I have to apologies, I鈥檓 done please鈥欌€
Kallonsu kloe tayi da saurayinta don ganin yanda zasu kare, kamar yanda sukayi hasashe kuwa sai gani sukayi maya ta sauko lokaci guda, don bata taba taba yarda yayi fushi shima don tana masifar son nick kamar ranta, shiyasa duk abunda yakeyi take daga mashi kafa, gashi bai wani girmeta sosai ba, he鈥檚 just 22.
鈥樷€檕kay but promise this should be the last time鈥欌€
Amsata yayi yana mai hugging dinta so tightly, ganin haka yasa kloe gyaran murya tana mai duban saurayinta tace 鈥樷€橧 told you, bazata iya hakura dashi ba鈥欌€
鈥樷€檞hat are you gossiping?鈥欌€ maya ta karashe tana duban kloe da saurayinta, kafin ta tabe baki ta maida dubanta ga black American dinnan tace 鈥樷€ I cant stay long guys, daddy nay a dawo and its been a week now bai koma ba, my phone has been seized, so lets just do what we have to do, how far with the?鈥欌€
Bata gama fada bama ya zura hannunshi cikin aljihunsa ya zaro wata yar takarda ya ajiye a gabansu kowa ya tura mashi gabansa harda maya.

Wani irin murmushi maya tayi mai wuyar fassara kafin ta dauki nata nannadaddiyar paper ta soma warwarewa jikinta har tsuma yake鈥..


**
Abuja Nigeria.
Gidan Marigayi alhaji santuraki..
Safiyar juma鈥檃 Kenan, yau gidan a cike yake tam saboda dama duk Friday ake taruwa a cikin main house bangaren Anne duk da estate daya suke kuma kowa da part dinshi.
Matan uncle Sameer babban dan gidan anne kennan da aunty fadila da iyalanta duk sun hallara ga jikoki harda da yaya ma.
Rana irin ta yau ta zame masu kamar double celebration saboda ayau uncle Sameer zai dawo daga Europe after shekara daya Kenan da tafiyarshi zuwa wani course.
Yaran duk suna zaune a sitting room na kasa don gidan nada girma sosai while iyayen su kuma suna sama wasu kuma suna kitchen ana hidimar girki dasu.

Anty Laila (uwar gidan uncle sameer)ce ta shigo dakin da sallama don zuwanta Kenan gidan, don bata samu tazo da wuri ba saboda ta dan tsaya don shirye shiryen tarbar mai gida don anan gidan ta zai sauka,

Da sallama ta shugo cikin dakin, anne dake zaune akan gado da wasu tarkacen takardu a gefenta ne ta dago ta kalleta tare da amsa sallamarta fuskanta babu yabo ba fallasa, nanna ce ma dake zaune kan kujera tana cin dambun sadakar Friday da aka kawo ne ta kallata cikin fara鈥檃 tace 鈥樷€檃h ah matar babban yaya sai yanxu鈥欌€

Sunkuyar dakai anty Laila tayi harta karaso tsakiyar dakin ta zauna kan carpet tace 鈥樷€檅arka da hutawa nanna, barka da huta wa anne鈥欌€

鈥樷€檅arka dai鈥欌€ suka amsata a tare
鈥樷€檡a iyali, yau mai gidan naku zai dawo ko鈥欌€ nanna ta fada tana mai kallonta
鈥樷€檈h yau zai dawo insha allah鈥欌€
鈥樷€檛oh masha allah ga dambu bismillah鈥欌€ nanna ta fada tana mai kallonta
鈥樷€檃lhamdulillah nanna, sai zuwa anjima zan diba鈥欌€
Shuru ne ya biyo baya adaidai lokacin fadila ta shugo dakin hannunta rike da mubin, yaron(aunty mubina) amaryar uncle sameer kenan.
鈥樷€檓ubin dai akwai barci yaron nan shiyasa yake burgeni鈥欌€
Jin muryarta yasa suka dago suka kalleta banda anty Laila da kanta ke kasa, kallon inda take fadila tayi kafin tace 鈥樷€檃she kin iso鈥欌€
Kamar anty Laila bazatyi Magana ba tace 鈥樷€檈h yanxu na shugo鈥欌€
Tana kaiwa nan ta mike 鈥樷€檅ari na sauka kasan鈥欌€
Nanna ce kawai ta amsa ta da toh, anne kuwa hankalinta na kan pappers din dake gabanta, anty fadila na kwantar da mubin ta dubi hanyar futar da anty Laila tayi kafin ta tabe baki tace 鈥樷€檋mmm鈥欌€
Kallonta nanna tayi fuskanta ya dan sauya tace 鈥樷€檋aba fadila, har yanxu dai bakwa jituwa da yayar taki?鈥欌€

鈥樷€檔anna bazaki gane bane, Tsakani na da ita waye ya kamat ya gaisar da wani?鈥欌€
Rai adan bace nanna tace 鈥樷€檒allai fadila, karkiga wai don tare kuka taso, matar wan k ice kuma uwar yayansa, dole ki bata respect dinta, anne kina kallon wannan shashanci da girmansu鈥欌€
Sai a lokacin anne ta dago ta kallesu cikin glass din dake fuskanta 鈥樷€檃y sun san daidai basai nayi Magana ba, and besides ita da take babba itace ya kamata taja girmanta鈥欌€

鈥樷€檃nne please karki goyi bayan kowa a alamarin nan saboda wani abu chan daya faru a baya wanda ya zama tarihi鈥欌€
Kallon yar uwar tata anne tayi tace 鈥樷€檋ajara!!鈥欌€

Jin yanda anne ta kira nanna yasa anty fadila fucewa daga dakin, tana futa kuwa anne ta kalli nanna tace 鈥樷€檅ana son a sake maimaita maganar nan, bana bin bayan kowacce a cikin su, laifin shi Sameer dinne daya bar hakan ta kasance shiyasa bana Magana akai鈥欌€

Nunfasawa nanna tayi kawai kafin ta maida hankali wajen abuncin da take ci.

Fadila na futa daga dakin kuwa ta sauko kasa zuwa kitchen, a tsaye ta tadda anty mubina da masu aiki suna ta hidima, karasowa tayi har inda suke tayi kafin tace 鈥樷€檃maryar babban yaya, baki koma daki kin hutaba?, kije ki huta tunda mubin yayi barci nakaishi dakin anne鈥欌€

Juyowa mubina tayi hannunta duk flour gashi tasha apron da alamu dai aykin takeyi bil hakki da gaskia, 鈥樷€檃nty fadila ay mun kusa gamawa, cake dinne kawai ked an daukan lokaci鈥欌€

鈥樷€檛oh shikenan, bari naje na dubo ko hamad sun dawo daga kai sadakar tunda naga an sauko daga masallaci, wannan yar banzan yarinyar ashe guduwa tayi ta barki鈥欌€
Dariya kawai mubina tayi kafin ta maida dubanta ga ayyukan dake gabanta.

Anty Laila kuwa bayan ta futo kasan ta sauko ta hakimce akan kujera, tana nan zaune fadila ta sauko ta wuce kitchen harta futo daga kitchen din ta sake komawa sama, su inti da amla da kareem sai wasansu suke鈥.

Basu suka bar gidan ba sai wajen karfe tara da rabi bayan kowacce taje tayi ma anne sallama.
Part din anty Laila yana opposite na anty mubina, sai part din anty fadila dake chan nesa dasu sosai, sai kuma wani part din daban, duk sun zagaye bangaren anne dake a tsakiya鈥︹€.


Matar Taj (destined with you馃┑馃)
Written by
Queenmarh鉁嶏笍

Free page
Chapter 8 · 0% Book details