← Book details Matar Taj Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 10 OF 20

Chapter 17-18

Matar Taj Part 1 Complete Hausa Novel · about 28 min read

Update!!
Koda ya fito bai ganta ba sai yaji babu dadi aranshi,shiryawa yayi yanda hidaya ta nuna mashi don yana jin maganarta sosai yana gamawa ya zauna bakin gadon.
Tunda ya zauna ya zubama kofar shugowa dakin idanu ko zai ganta, sabeeha kuwa bata koma dakin ba saboda an gindaya mata sharudan shiga dakin, daman zata bashi maganin shi ne saita bashi breakfast daganan kuma saita taimaka mashi yayi wanka daga nan kuma bazata sake shiga dakin ba sai da yamma idan tazo bashi second dose.

Bayan Futar sabeeha daga dakin batayi gigin komawa dakinba saboda koba komai namiji ne kuma yana buqatar privacy bayan wannan ma bata son ta gane ma kanta abunda bai kamata ta gani ba saboda baya cikin hayyacinshi, don tundaga yanda ya soma kokari zame wandoshi kuma ya ganta ta tabbatar akwai gyara sosai a al鈥檃marin.
kasa ta koma bayan ta kakkashe komai yanda head ta fada mata, harta sauko kasa yana ranta, saitaji kamar ta koma don ganin ko ya futo daga toilet din ko bai futo ba ko yana buqatar wani abun.

Jiki a mace ta shiga dakinsu, gaba daya tama manta da cikinta don ko karyawa batayi ba kuma it鈥檚 past 10, yar Ghana da tsegumi ashe tana ankare da ita don ta jiyo lokacin da sauran maids ke gulman ta.
Abuncinta ma itace ta karbi nata ta ajiye mata don a pack pack ake basu kullum safe rana da dinner.

Koda ta shiga ko zama batayi ba saiga yar Ghana ta shugo itama da pack din abuncinta a hannunta,鈥欌€檔ew comer鈥欌€
Yar Ghana ta kirata,juyowa sabeeha dake shirin zama bakin gadon tayi tana mai kallonta, cikin sassarfa yar Ghana ta karaso inda take kafin ta miqa mata pack din data shugo dashi, 鈥樷€檊a break dinky na karba maki鈥欌€
Murmushi sabeeha ta yi duk da ba a ganin fuskanta kafin ta sanya hannu biyu ta karba pack din tace 鈥樷€檔agode.鈥欌€
Murmushi yar Ghana tayi kafin ta soma rage murya 鈥樷€檌na aka kaiki?鈥欌€
Shuru sabeeha tayi tana kallonta kafin ta sauke kanta kasa tace 鈥樷€檚ama wajen madam鈥欌€
Shuru yar Ghana tayi tana kallonta cikin nuna rashin yarda da abunda tace, chan kuma sai tayi murmushi tace 鈥樷€檔a dauka wannan wajen aka kaiki, thank god ba nan bane, bari na koma wajen aikina bye鈥欌€
Girgiza mata kai kawai sabeeha tayi kafin ta zauna nan bakin gadonta,pack din nata ta bude, fries ne sai kwai da aka soya yasha albasa.
Bismillah tayi kafin ta soma turawa cikin natsuwa, duk sanda zata kai bakinta haka zata dan janye mask din ta tura kafin ta maida shi.
Bayan ta gama zamanta tayi anan dakin ta doka uban tagumi, tunanin wannan mara lafiyan ne ya fado mata arai.

Taheels groups鈥..
Zaune take cikin kayataccen office dinta, the most trusted secretary dinta na gabanta, ga kuma wasu file dake ajiye akan table din office din, gaba daya yau ranta a mugun bace yake tun daga gida, ga kuma abunda ta riska anan office.
Kallon agogon dake maqale a hannunsa yayi kafin ya maida dubansa ga madam din nasa, 鈥樷€檓a鈥檃m lokaci yayi fa鈥欌€

Tafin Hannayenta data rufe fuskanta dashi ta sauke kasa, sai kuma fuskanta data dago ta zuba mashi waennan idanuwan nata masu firgitawa, karantar facial expression dinta is so hard don gaba daya bazaka iya tantance a wani yanayi take ciki ba.
Mikewa tayi tsaye tare da ture kujeran dake bayanta kafin ta sagayo 鈥樷€檒ets go鈥欌€
Tana kaiwa nan ta nufi hanyar futa, shikuwa da hanzari ya bi bayanta da wannan files din, cikin takun isa ta fito daga cikin office din nata ma鈥檃ikata duk wanda ya ganta saiya tsaya yadan duqa mata cikin respect dukda bata bi ta kansu ma kwata kwata.
Bata tsaya ko鈥檌na ba sai shareholders hall, secretary yana biye da ita a baya, koda tazo bakin kofar hall din shine ya bude mata kofar kafin ta shige ciki.

Mutanen dake zaune cikin hall dinne wanda akalla zasu kai su kusan guda goma sha biyar ne sukayi saurin mikewa don girmamata, bata tsaya wani amsar gaisuwarsu ba ta nufi hanyar wajen zamanta na musamman a tsakiyan dogon table din.
Zama tayi kafin kowannen su ya zauna suma, shuru ne ya biyo baya baka jin komai sai saukar nunfashin manyan mutanen dake zaune.

Secretary ne yayi opening meeting din kafin ya fara koro masu bayanin progress din da aka samu a wannan shekarar, hidaya dai binsu take da kallo daya bayan daya tana jiran taji wanda zai fara Magana, cikin waenda ke zaune kuwa harda uncle khal don shima shareholder ne sai sauran mutane da sukayi investing kudadednsu da waenda sukeyi partnership dashi.

Daya daga cikin manyan mutanen ne ya katse secretary, mutumin kowa yasanshi he鈥檚 so bold kuma shi baya wani rufa rufa, don haka ya soma Magana 鈥樷€檞annan bashine purpose din meeting dinnan ba, munyi鈥欌€
Sai a lokacin hidaya ta dago ta kalleshi, babban ne sosai don a haife zai haife ta kuma yana cikin waenda suka dade sosai suna investing a cikin company ma鈥檃na sune waenda suka dade a cikin company kuma suna bada gudumawa sosai don ganin cigaban company tun marigayi taheel na raye.
Yanda take kallonshi haka yake kallonta, babu wani conering ya cigaba da Magana 鈥樷€檇alilin wannan meeting din shine, munason sanin dalilin dayasa wanda ya kamata ya karbi ragamar wannan company dinnan baiyi presenting kanshi ba har yanxu, yau kusan wata takwas Kenan, a yanda ka鈥檌dar business dinnan take da kowane company shine dole heir din owner of the company ne zai gaji wannan company ko next person In line鈥欌€,
Hidaya najin haka ta maida dubanta ga uncle da ya hade hannayenshi a kirjinshi yana kallon wannan show din,
鈥樷€檓adam munason sanin dalilin presenting dinshi bayan kowa yasan yanxu he鈥檚 30 kuma wannan ne ka鈥欌€檌dar company, we understand your help and contribution in making this company standing on it鈥檚 on, but鈥︹€欌€
At this point idanunta sunyi jaa sosai, shi kuwa bai tsagaita bay a cigaba, 鈥樷€檅ut you鈥檙e not enough madam, you can鈥檛 run the company ko badan ka鈥檌da ba, babu inda aka yarje mace ta rike company anan kasar, a woman can鈥檛 rule the company, that鈥檚 a disgrace to the taheel family and the company reputation as well鈥欌€

Yana kaiwa aya gaba daya office din suka karade da cewa 鈥樷€檡es, that the fact鈥欌€
Kan kace me nan take hall din ya kacame, wannan yace kaza wannan yace kaza, saida hidaya ta bari suka gama tass har lokacin kallon uncle take dake mata wani irin kallo,irin na barki dazu,
Runtse idanunta tayi kafin ta bude su ta daga hannunta biyu ta daki table din dake gabanta, nan take duk sukayi tsit bakajin komai.

Babu tsoro babu fargaba ta daga ma secretary hannu, cikin hanzari kuwa ya miqa mata wannan file din, yana miqa mata ta bude cover din file din kafin ta watso masu shi gaba daya,

Daya bayan daya suka soma dauka papers din don karantawa, 鈥樷€檌dan kun gama karantawa let me know鈥欌€
Tana kaiwa nan ta hade hannayenta a kirjinta tana jiran su gama, nan take kuwa suka soma zuru zuru da idanu don kowa da sunanshi a jikin papers don da duk abubuwan da sukeyi ta bayan fage, sunan uncle ne kawai babu a ciki, wanda yayi Magana ta fara pointing babu tsoron komai ta soma Magana 鈥樷€檡ou!!! with due respect, inason ka fada min waye a cikinku ya kamata na miqa ma company dinnan?鈥欌€

鈥樷€檡ou!!鈥欌€ ta sake fada tana nuni da wani dake gefenta, shi har ya soma balle maballin buttons din suit dinshi tsabar tashin hankali.
鈥樷€檏ai dake da record of molesting workers, da harassment tsakanin ni da kai waye yafi dacewa ya jagoranci wannan company?鈥欌€

Mutumin najin haka ya sauke kanshi kasa, idanunshi sunyi jaa sosai, wannan shine babban embarrassment din da akayi mashi agaban bainar jama鈥檃 kuma manya kamarshi.

Wata iriyar dariya tayi mai bayyanar da hakoranta kafin ta tafa hannunta ta maida dubanta ga dayan dake gefenshi tace 鈥樷€檃nd you鈥 kaida kake da record of homosexuality, gayzism, kana nufi kaine ya kamata yayi ruling wannan company din?, how are you all better than a woman ku fada min鈥欌€

Daya daga cikinsu ne ya dake, daga gani zaiyi kafiya yace 鈥樷€檓u bamuce muna son amsar legacy din family dinku ba, what we just want to know shine maysa har yanxu heir din wannan company din bazai karba muqaminshi ba鈥欌€

Shuru hidaya tayi ta kasa cewa komai sai kuma chan ta saki wani murmushi, 鈥樷€檚eems like you鈥檙e are not understanding this language鈥欌€

Jin haka ya tabbatar masu da abunda take shirinyi, wata bankadar zatayi masu gashi kowa yana tsoron kar ta fidda wani abun nashi don basu taba tsammanin hatsabibya bace ba sai yanxu,
鈥樷€檞e鈥檙e done for today鈥欌€
Uncle ya fada yana miqewa, sauran mutane na jin haka kuwa suka mike kowannensu ya soma fita daga hall din, gaba dayan su tashin hankali ne karara a fuskansu, gashi a junan su ma baqin ciki suke ma juna kuma basa kaunar juna gashi lokaci guda wannan la鈥檃nanniyar ta tona ma kansu asiri a junansu.

Suna fita tayi ma secretary nuni da hannu akan ya basu waje, yana fita kuwa ta kalli khaal kafin ta soma tafa hannayenta tace 鈥樷€檞ow, wow, wow, wonderful, that鈥檚 a great attempt khaal, ni da kai kasan cewa idan mutanen nan suka san cewa wanda suke tambaya akai is not mentaly stable zasu iya komai don ganin sun karbi wannan company din daga hannu mu, kana tunanin zan bar haka ta faru?, no never, this is my parents legacy, my parents hard work, abuh and ummuh, so this is just the beginning khaal鈥欌€
Tana kaiwa nan ta mike ta fuce daga office din ta barshi saqe a tsaye, hannunshi daya dungule yayi jaa sosai kamar gauta.

Hidaya kuwa na futa secretary ya mara mata baya zuwa office, wani irin sign of relief ta sauke kafin ta kalli secretary 鈥樷€檓un tsallake wannan, nasan bazasu hakura ba, zasu ta kawo hari with much questioning, inason kayi providing komai, da yanda mukayi planning komai鈥欌€

鈥樷€檕kay ma鈥檃m鈥欌€ ya amsata kafin ya fuce yana murmushi.

Bayan futarshi Kenan ta, ta bude wata safe locker, wayoyi ne guda biyu sai wasu papers a cikin locker din, daya daga cikin karamar wayar ta zaro kafin ta soma dialing wata number, ana dagawa ta soma Magana anaste 鈥樷€檅ana son dogon bayani, so guda nawa ne suka shigo hannu?鈥欌€
Daga chan ne aka bata amsa kafin ta sake cewa 鈥樷€檕kay!!鈥欌€

Tana kaiwa nan ta kashe wayar ta maidata cikin locker din kafin ta maida dubanta ga papers din dake cikin safe locker, tunani ta soma yi chan kuma kawai sai ta rufe locker din ta cigaba da ayyukan dake gabanta.


Bangaren sabeeha, karfe uku da rabi nayi ta koma dakin nashi, a hankali ta soma bude dakin kamar wata barauniya, dakin duhu dum yanda kasan dare yayi babu haske babu sound din komai kamar babu rai a cikin dakin, ahaka ta dunga rarrafawa ta karasa tsakiyar dakin, sai data karaso bakin gadon ta samu dan hasken bedside lamb,
Bin kan gadon ta soma yi da kallo, barcinsa yakeyi hankali kwance hanunshi rike da wani puzzle solver da ake jujuyawa, ya nado jikinshi da pillow ya rungume.
Tsugunnawa tayi agaban gadon ta zuba ma innocent kyakyawar fuskanshi idanu daga kan lashes dinshi da sukayi zaro zaro ga dogon siririn hancinsa a mike kamar pile zuwa ga lips dinshi da suke a cike sunyi jaa kamar ansa mashi filler ga sexy jaw line dinshi mai daukar hankali sosai, kasa dauke idanunta tayi daga jaw line din nashi don wajen is so attractive duk da bata san attracting dinta wajen yake ba,maido da dubanta tayi ga huge kirjinshi zuwa ga arms dinshi, ya zakalo hannunshi ya rungume pillow a kirjinshi, ya rike wannan puzzle box din da yatsunshi, daga ganinshi yana amfani da musles equipment saboda yanda ya damke pillow din kamar za a kwace mashi pillow din har jijiyoyin hannunsa sun bayyana.
Samun kanta tayi kawai da murmushi ganin yanda yayi wani irin juya bakinshi alamun kosawa da barcin, samun kanta tayi da qin tashinsa saima kallonshi data cigaba da yai harta sakankance lokaci ya kure.

Kokarin tashinsa ta soma yi saidai tsoron yanda zai tashin take don ance yana furgita, wata dabara ce tazo mata kai don haka ta daga dan karamin hannunta ta soma shafa karan hancinsa ba tare da tayi making sound movement ba ko hakan zaisa ya tashi, shuru dai babu motsi saima nunfashi da yake saukewa a hankali, ta dade tana hakan harta maida tafin hannunta kan bare fatar skin din fuskanshi mai laushi kamar na sabon jariri, shafa fuskan nashi ta soma yi ko hakan zaisa ya tashi har zuwa wajen silk gashin sajen fuskanshi daya zagaye fuskan nashi, dukda hakan ma datayi shuru ganin haka kawai yasa ta miqe ta futo daga dakin bayan ta tabbatar yana nunfashi.

Lokacin data futo karfe hudu yayi kowa ya sauka kasa gaba daya maids babu wanda ya tsaya anan saman don wannan dokar ba a tsallaketa.


Hidaya鈥︹€
Bayan wannan shareholder meeting dinnan bata bar office dinba sai wajen yamma liss, school din barad ta fara zuwa suka daukeshi kafin ta dawo gida.
Akan hanyarsu ta dawowa gida ya soma nuna mata medal din da aka bashi na competition din da sukayi kuma yaci second position, kallon medal din kawai tayi kafin ta kalleshi, first tambayar datayi mashi is 鈥樷€檞hy would you take second position, ban haifi danda za a wuceshi a komai ba so buckle up and make me proud next time with a first position, not this rubbish okay鈥欌€
Girgiza mata kai kawai yayi in response,
Bawan allah yana jinta ta gama kanshi a kasa, yau kwata kwata baya cikin jin dadi saboda koda yaushe shi mai faran faran ne, dalilin fushinshi kuwa shine kowanne student parents dinshi na zuwa suyi supporting din yayansu, but shi babu wanda yazo mashi, daman daddyn shi yafi bashi attention akan harkokin nan shiyasa yafi shaquwa da daddyn nashi akan mamanshi, wannan yasa koda yaushe yake missing dinshi sosai.

Koda suka karaso gida kamar koda yaushe maids na tsaye suna jiranta, daya na kula da harkar barad while dayar kuma tana daukan Jakarta da sauran files dinta da sun dawo.

Saukowa tayi daga cikin motar maids din na mata sannu da zuwa, idanunta ne ya sauka akan motar dake parke a parking lots, barad daya zagayo yana ganin motar kuwa shima ya saki jakarshi a wajen ya ruga da gudu cikin gidan tsabar murna ya soma kiran 鈥樷€檇addy!! Daddy is back鈥欌€
Kwasar jakarsa maid dinshi tayi kafin ta shige ciki, hidaya na gaba suna biye da ita a baya harta shige cikin gida.

Su afiya na zaune a second sitting room suna zaman da suka saba na kallo da ci, barka da zuwa sukayi mata kafin ta wuce, suka bita da idanu, afiya dai har yau a kule take da alamarin yayar tasu, wani sa鈥檌n kuma inta tuna da rayuwar su a baya sai taji wani irin tare da tausayin yayar tata don tun bayan mutuwar ummuh ta koma wata iri gaba daya don tana masifar son ummuh dinsu sosai, yanxu kuwa she鈥檚 not friendly at all,komai harshly take yinshi, dama dama su kannenta ma, suna samun wani soft side of her.

Saman ta wuce direct zuwa, koda ta karaso saman saida ta dan tsaya ta dubi part din big baby, ayanxu ta tabbatar yana barci don haka ta wuce bedroom dinta kawai.

Da sallama ta shugo parlorn part din nata, da barad taci karo da wani babban mutun sak kamar barad din har kamarsu ta soma baci, wasa sukeyi sosai mutumin na mashi chakulkuli barad na dariya yana fadin 鈥樷€檇addy stop daddy!!鈥欌€
Kallonsu hidaya tayi kafin ta kauda kanta gefe ta nufi hanyar bedroom dinta, mutumin da barad ya kira da daddy ne ya kalleshi kafin yayi sqeezing face yace 鈥樷€檞ake squeezing face kamar haka鈥欌€ kyalkyale da dariya barad yayi harda buga kirjin dadyn nashi yace 鈥樷€檛hat鈥檚 mummy鈥欌€ nan take suka kyalkyale da dariya,
Saida suka tsagaita kafin barad ya kalli dadyn nashi yace 鈥樷€檇addy please zan iya ganin uncle taj? I missed him so much I want us to play, daddy Please please 鈥樷€
Shuru dadyn yayi kafin ya shafa kanshi cikin lallami yace 鈥樷€橧鈥檓 sorry barad, uncle baya jin dadi kaji? He needs medical attention ka bashi time tukunna, ka tuna last time abunda ya faru ko?,鈥欌€
鈥樷€檅ut daddy inason naje wajenshi鈥欌€
鈥樷€檔o barad you can鈥檛 mummy zatayi fushi dakai, you can鈥檛 play with him for now, ka manta that little incident daya faru鈥欌€

Sauke kanshi kasa barad yayi cikin rashin jin dadi don shine yayi causing, 鈥樷€檡es daddy,but I鈥檓 sorry bazan kara hakan ba鈥欌€
鈥樷€檡es you made a mistake ka bude kofa ka fito da uncle kunyi wasa ya fadi a bene,shiyasa mummy bazata bari ba, and I鈥欌€檓 hoping bazaka sake hakan ba鈥欌€
鈥樷€橸es daddy鈥欌€
Ya amsa mashi 鈥樷€檊ood boy,鈥欌€
mikewa daddyn yayi yana mai nuna mashi hanyar bedroom dinshi yace 鈥樷€檊o and freshen up boy, kana yin tsami鈥欌€
Dariya sosai barad yayi kafin yace 鈥樷€檇ad sunkuyo na fada maka wani abu鈥欌€
Rankwafowa mutumin yayi barad na ganin haka kuwa ya kama fuskan dadyn nashi ya dannan hammatarshi a wajen, nan take daddyn ya soma kakarin amai da wasa, nan take suka kyalkyale da dariya, yanda suke communication da juna gwanin burgewa don daga gani akwai soyayya mai karfi tsakaninsu.

Yana wucewa daki ya sauke wata ajiyar zuciya kafin ya nufi bedroom din nasu, da sallama ya shiga cikin bedroom din, da ita yayi arba, tana tsaye tana kwance takalmin kafafunta data nannde kafafunta da igiyarsu, karasowa yayi cikin kulawa ya zauna bakin gadon, tunda ya shigo bata dago ba haka zalika ba tace mashi kala ba.

Fuskarshi a hade ya nufi hanyar dresser ya soma kwance tie din dake wuyanshi, saida y agama ya cire agogon hannunshi ya ajiye kan dresser din kafin ya zame belt din kugunshi, yana gamawa ya wuce cikin closet ba tare da yace mata ci kanki ba itama kuwa bata tanka mashi ba saima kokarin zare takalmin nata da takeyi, tana gama warware igiyar ta mike da takalmin a hannunta ta nufi closet room dinsu, juyowa yayi ya mata kallo daya kafin ya cigaba da zame wandon daya rage mashi, itama kallo daya tayi mashi ta wuce wajen closets dinta, duk wani accessories dinta ta soma cirewa kafin ta maida dubanta gareshi yana kokarin daura towel a kugunshi, 鈥樷€檏a dawo ashe鈥欌€
鈥樷€檡es鈥欌€ ya bata amsa kai tsaye kamar bashine y agama wasa da barad ba,
Daga yanda ya amsa mata tasan cewa daga inda suka tsaya Kenan zasu cigaba, kamar yanda ta saba gaslighting akan mutane dukda duk yanda taso tayi akanshi ya gagara don shi baya yin shuru kwata kwata shiyasa take shakkansa sosai, 鈥樷€檞ai meysa bazamu tsaya on a one page ba eh,as my husband abunda nafi buqata shine support dinka bawai ka dunga鈥.?鈥欌€

Tsagaitawa yayi daga abunda yake ya juyo ya mata kallo daya kafin ya girgiza kanshi ya cigaba da abunda yakeyi, tana ganin haka ta cigaba da Magana鈥..
鈥樷€橧 made you who you are today Jamid, your parents your siblings, kowanen su suna under my wealth shelter meysa kai bazan juyawaka yanda nake so ba? Why can鈥檛 you support me kodan saboda鈥︹€..鈥欌€

鈥樷€欌€檋idaaaaaaayaaaaa!!!
Ya daka mata wata uwar tsawa daya sata yin gum ta zuba mashi idanunta da sukayi jaa sosai,
鈥樷€檖oint of correction, you don鈥檛 owe me, because I鈥檓 your husband, and we have two different personalities, bazaki taba sakani abunda banyi niya ba, I will never work for you nor under you,kuma duk abunda nasan kinyi ba daidai ba saina fada maki, so keep that in mind鈥欌€ yana kawai ya fuce daga dakin.

Yana futa ta doka wani uban tsaki kawai ta cigaba da abunda take, what she wanted from him was just an apology 鈥樷€橧鈥檓 sorry鈥欌€ saidai bata jin zata taba samu daga wajenshi, don tana masifar shakkarsa sosai, bata kawo mashi wargi ko kadan ita kanta ta rasa dalili.

Karfe tara daidai ta fito daga closet room cikin shirinta na kwanciya,yau ko sauka kasa yin dinner ma batayi ba, babu abunda take sai kamshi mai dadi sosai, tana sanye da sleeping dress baqa mai sirirn hannu kamar vest wadda ta sauko mata har wajen gwaiwarta
Akwance ta taddashi ya bata baya don he鈥檚 not ready for her drama, itama kuwa kwanciyanta tayi ta juya mashi baya.

Sunyi nisa sosai cikin barcin wayarta dake gefen bedside ta soma ruri,karar wayan yakai kusan minti goma yana yi saida jamid ya mike zaune ya dubi inda take kwance 鈥樷€檋idaya!! Hidaya!!鈥欌€
鈥樷€檜hm鈥欌€ ta amsashi don barcin nata baiyi nisa ba,
鈥樷€檏i tashi mana, bakiji wayanki na kara bane鈥欌€
Tsaki tayi kafin ta miqa hannunta ta miqe zaune, duban screen din wayar tayi kafin ta shiga app din dake detecting warning alert din gidan, rai adan bace tace 鈥樷€檞hat sort of nonsense is this鈥欌€
Dubanta yayi kafin yace 鈥樷€檞hats the issue鈥欌€
鈥樷€橞ig baby ne鈥欌€ ta bashi amsa kai tsaye rai a bace.
Yana jin haka hankalinshi ya tashi lokaci guda ya mike tsaye ya zura bedroom slippers dinshi 鈥樷€檋aba hidaya, yanxu kinsan cewa warning alert din dakinsa ne shine kika zauna calmly kamar ba komai ba? What if wani abu ne ya faru?鈥欌€ yana kaiwa nan baima bi ta kanta ba ya fuce daga dakin rai a bace.
Yana fita saida ta dauki kusan minti biyar kafin ta miqe ta bi bayanshi.

Direct part din big baby ya nufa kai tsaye, yana zuwa a gaggauce ya danna pin din dakin ya shige ciki.
Daga yanda yake sassarfa zaka gane hankalinshi a tashe yake, dakin ya bude tare da danna light din dakin, nan take ko鈥檌na ya bade, jefa idanunshi ya soma yi cikin bedroom din nan take ya soma jin sound din kukan shi sosai, yana daga zaune bakin gado daga chan sako ya nannade jikinshi gaba daya.
Karasowa daddy barad yayi inda yake kafin ya tsugunna a gabanshi,
鈥樷€橳aj!!! Taj!!!, calm down okay?鈥欌€
Dagowa taj yayi jikinshi sai faman kyarma yake kamar wanda ya kwana yana zazzabi, idanunshi gam ya kullesu, farar rigarshi kuwa ta baci da jini da alamu ya yanke hannunshi da wani abun ne,

Dafa kafadar shi daddyn barad yayi kafin yace 鈥樷€檛aj open your eyes, it鈥檚 me, uncle jamid鈥欌€
Saida yaji hakan yayi saurin bude idanunshi, dukda ya gane uncle jamid din hakan bai sashi ya dawo daidai ba, hakoranshi sai faman gogayya suke da juna kaf kaf tsabar tsoro.
Ture hannunshi dake kafadarsa ya somayi bakinshi na karkarwa ya soma ihu 鈥樷€檔o no, I鈥檓 scared, first love please help me鈥欌€

A daidai nan hidaya ta shugo dakin, tun daga nesa ta tsaya ta harde hannayenta tana sauraron yanda jamid keta faman rokonshi akan he should calm down don gaba daya ya hade jikinshi waje daya kamar wanda za a yanka, saida ta shafe yan sakanni kafin ta karaso inda suke.
Zama tayi bakin gadon nashi kafin ta soma Magana 鈥樷€檅ig baby鈥欌€
Yana jin sautin muryarta ya bude idanunshi tar akanta, rarrafawa ya somayi har zuwa inda take kafin ya rungume kafafunta, gaba daya y agama burkicewa babu abunda yake sai kuka 鈥樷€檉irst love don鈥檛 leave me alone, stay with me please, I鈥檓 scared.鈥欌€

Tunda ya soma Magana bata ce kala ba saima kallon suman kanshi data soma fitowa datayi, ga kafarta daya qanqame kamar her life depend on it, ga laps dinta daya jiqa da hawaye.

Jamid dai kallonshi yake cikin tausaywa da kaunarsa, aduniyar nan bai bata ganin wanda ke qaunar yar uwarsa kamar yanda taj ke kaunar hidaya ba tun kafin wannan lalurar ta sameshi, tun tasowarshi da girmashi bashida kamar hidaya gaba da baya, babu wanda ya isa yayi comparing hidaya da kowa don tana da space na musamman a zuciyarshi dukda yanxu ya samu wannan amnesia din hakan bai sashi identifying dinta ba, kaunarta kuwa taa nan daram a cikin zuciyarshi.
Haka zalika har a yanxu ma babu wadda ya yadda da sai hidaya, ita kadai ke iya controlling dinshi.
Sun dauka kusan minti biyar a haka kafin hidaya ta soma shafa kanshi, 鈥樷€檚huuu, stop crying I鈥檓 here鈥欌€ ..Ta fada tana mai dago fuskanshi da yayi gaja gaja, 鈥樷€檞ipe those tear鈥欌€ ta bashi umarni, nan take kuwa ya soma goge hawayen nashi yana gamawa ya kamo hannunta ya riqe gam cikin nashi, har zuwa lokacin yana tsugunne a gabanta, wayarta dake rike a hannunta ta dauka ta soma dialing number head.
Head dake ta faman sheka barcinta tana jin karar wayarta tayi zumbur ta mike, ganin sunan madam yasata saurin daga wayar cikin hanzari tana kokarin goge miyau din dake yawo a gefen bakinta.

鈥樷€檡es madam鈥欌€
Daga chan bangaren ne aka soma Magana, tana cikin sauraron madam din tayi saurin miqewa hankali atashe, dan blanket veil dinta ta janyo ta yafa akan rigar baccin dake jikinta kafin ta zura takalminta ta fuce daga dakin da take kwana,
Bangaren maids din gyare gyare ta nufa direct, tana shiga ta kunna futilar dakin kafin ta buga masu kofar dakin yanda duk zasu tashi
A furgice kuwa duk suka tashi, kallonsu ta soma yi daya bayan dayan kafin ta maida dubanta ga gadon sabeeha 鈥樷€檞here鈥檚 this new maid, you!!鈥欌€ ta yi nuni da sabeeha dake faman rarraba idanu,
鈥樷€檉ito鈥欌€
Ta bata umarni, hankali a tashe sabeeha ta miqe, sanye take da hijab dinta sai janyoshi datayi ya rufe mata fuskanta ya rage idanunta ne kawai a bayyane,
Futa head tayi kafin tabi bayanta hankali a tashe, sauran maid kuwa babu abunda suke sai tsaki bayan futarsu saboda tashinsu da akayi cikin tsakar daren nan wajen karfe uku, gashi zasu tashi da wuri,

Suna fitowa head ta dubi inda sabeeha take tace 鈥樷€檞hat mess have you caused? Matsalata da irin ku black people dinnan idan kuna abu kamar marasa kai, just simple instruction baku iya bi ba?, now what stupidity have you done?鈥欌€

Tunda suka fara tafiya head take surfa mata masifa ita kuwa baiwar allah gaba daya hankalinta baya kan maganganun head din don hankalinta a tashe yake, babu abunda take sai tambayar kanta shin me tayi? Gaba daya jiya ta fara aikin fa? Hartayi abunda ba daidai ba.

Suna karasowa part din headmaids ta fara shiga ciki sabeeha na biye da ita, zuciyarta na faman lugude tsabar tsoro, koda suka karaso bedroom dinshi head ta tsaya 鈥樷€檏i shiga鈥欌€
A tsorace sabeeha ta sanya hannunta kan mabudin kofar kafun ta shiga bakinta dauke da sallama, jamid ne kawai ya amsa sallamarta da mamaki, kallonta yayi daga sama har kasa kafin ya dauke idanunshi daga kanta.
Mikewa hidaya tayi, taj na ganin haka shima ya miqe yana mai kokari kamata da kyau, kallonshi tayi 鈥樷€檅ig baby seat down鈥欌€
Tana fadin haka kuwa ya zauna anan kan gadon idanunshi na kanta don baya son ta tafi, takowa ta somayi har inda sabeeha take kafin ta daga hannu ji kake tasss tass tass, ta kwashe sabeeha da maruka both sides din fuskanta, cikin sauri jamid ya karaso inda suke ya janyo hidaya baya rai a bace yace 鈥樷€檋idayaaa鈥欌€

Hannu ta daga mashi rai a bace, akan me zai jata baya tana kokarin saitama wannan dumbhead din kai, lokaci guda sai bacin ranta ya koma kanshi, bata kaunar irin abubuwan da yake mata wanda babu wanda ya isa yayi mata irin haka sai shi, Taj dake zaune kukan sabeeha na mashi eco a kunne, kasa hakura yayi dole ya miqe tsaye baima san ya tashi ba ya nufi inda suke,take shima ya soma hawaye yana jan hannun hidaya 鈥樷€檉irst love please I鈥檓 sorry, don鈥檛 hit her please, she鈥檚 our friend remember?鈥欌€
Haka ya dunga maganganun da baima san me yake cewa ba yana jan hannun hidaya irin yanda yara keyi, 鈥樷€檚top it鈥欌€ ta daka mashi tsawa, 鈥樷€檊o back and seat down鈥欌€
Wannan tsawar datayi ba karamin abu bane a wajen taj, don baya kaunar yaga tana fushi dashi ko kadan, nuni tayi mashi da gadon shi,

Saurin sakin hannunta yayi ya nufi gadon ya zauna kanshi a kasa, har wani irin zazzabi ne ya rufe shi lokaci guda, ga wani azababben ciwon kai daya kawo mashi ziyara, jikinshi har rawa yake ga jijiyoyin kanshi da suka fito rado rado.

Saida ya zauna hidaya ta maida dubanta ga sabeeha kafin tayi kwafa ta fuce daga dakin rai a bace.

Bayan futarta jamid ya dubi sabeeha dake kuka innocently harda shesheka abun tausayi, 鈥樷€橧鈥檓 sorry about that okay?bansan me kikayi ba but Please be careful next time okay?, ranta ne ya baci sosai that鈥檚 why tayi acting that way鈥欌€
Tsagaitawa sabeeha tayi da kukan tana sauraron yanda yake Magana anatse cikin mutunci, girgiza mashi kai kawai tayi alamun gamsuwa
鈥樷€檡ou鈥檙e the new caregiver right?鈥欌€
鈥樷€檡es sir鈥欌€ ta amsa shi.

鈥樷€檖lease work on his injuries okay?鈥欌€
Girgiza mashi kai sabeeha tayi kafin ya fuce daga dakin ya barta a tsaye.
Sauran hawayen dake kan fuskanta ta goge, kafin ta maida dubanta ga inda yake zaune a bakin gadon ya runtse idonshi gam jikinshi na faman karkarwa.
Takowa ta soma yi anatse har zuwa inda yake zaune, tsugunnawa tayi a gabanshi tana mai kallon fuskanshi, kawai saita fashe da kuka ganin yanda fuskanshi yayi jaa sosai ita a tunaninta shima ko bugunshi akayi, har zuwa lokacin bata san taqamaimain laifin datayi ba saidai koma menene ta yanke shi ne a dalilinshi ne.

Idanunshi ya bude ya sauke akanta yana kallon yanda take kuka, hannunshi ya dago ya dora akan fuskanta, hannun nashi dake kan hijab din fuskanta tabi da kallon, wani irin dumi ne taji ya ratsa fuskan nata wanda ke futowa daga tafin hannun nashi 鈥樷€檇on鈥檛 cry for me friend鈥欌€
Runtse idanun ta tayi ta dora hannunta akan nashi dake fusknta, wani irin zafi taji sosai kamar wuta, hannunshi is so soft kamar bai taba amfani dasu ba.
Sun dauki kusan minti biyu a haka, ta kasa sauke hannunshi daga kan fuskanta, ga wani mixed feeling dake shiga cikin jininta, lokaci guda ya shiga ranta sosai, tausayinshi ya gama yi mata katutu arai, da zuciya daya taji tana son shiga cikin rayuwar shi ta hanyar taimakonshi da kulawa dashi don iya abunda zatayi mashi Kenan.
Bakinta na rawa ta soma Magana ahankali cikin muryarta mai kwantar da hankali
鈥樷€檚ir, you鈥檙e burning up,鈥欌€
Zame hannun nashi tayi daga kan fuskanta ta maida dubanta ga hannun nashi, jinin data gani ne yasa ta tuna da maganar wanda ta tarar tare da madam wanda take tunanin shine mijinta,
Mikewa tayi tsaye yana ganin haka shima ya miqe yana mai jan hijab dinta, kallon hannun nashi tayi kafin ta daga kanta don ganinshi, 鈥樷€橧鈥檓 scared friend bazan iya zama ni kadai ba鈥欌€
鈥樷€檢aka rakani?鈥欌€
Girgiza mata kai yayi kafin ya sauke mata murmushin sa mai tsada, wanda ya sata kasa dauke idanunta akanshi, yanda yake murmushi zaka rantse lafiyar kalau, he looked so matured.

Batace komai ba ta nufi hanyar fita yana biye da ita har suka wuce zuwa kitchen, bin hanyar ya dunga yi da kallon kamar yau ya taba shiga wajen, suna shiga kitchen ta nufi wajen da taga first aid box, janyowa tayi ta soma budewa kafin ta zaro spirit da cotton wool harda wound plaster.
Komawa sukayi dakin yana biye da ita a baya har suka karaso bakin gadon, 鈥樷€檚eat down friend鈥欌€
Tana fada kuwa ya zauna, tsugunnawa tayi tana mai kallon hannun nashi, mika mashi hannunta na dama tayi yana ganin haka kuwa ya daura hannunshi akan nata, goge mashi hannun ta soma yi da spirit, 鈥樷€檕uch鈥欌€ ya furta
A dan furgice sabeeha tace 鈥樷€檚orry, sorry akwai zafi ko鈥欌€
Girgiza mata kai yayi, haka ta gyara mashi hannun kafin ta saka mashi plaster, tana gamawa tace 鈥樷€檏a kwanta kayi barci friend鈥欌€
鈥樷€檔o I don鈥檛 want to, nasan tafiya zakiyi kamar yanda first love ta tafi, I鈥檓 scared don鈥檛 go please鈥欌€ ya fada cikin rada, ganin haka ya sata zama a kasa tace 鈥樷€檅azan tafi ba friend, ka kwanta to鈥欌€

Tana fadin haka kuwa ya kwanta, dan motsawa tayi yana jin haka yayi saurin kamo hijab dinta ya riqe gam,
Haka suka zauna yana kallonta tana kallonshi, gashi idanunshi tarr yaqi yin barcin saboda baya iya barci dole saida maganinshi shiyasa ba a skipping lokacin maganinsa, ganin kusan har karfe hudu yasa ta miqe tsaye,yana ganin ta miqe kuwa shima ya mike har yana kokarin karo da ita, matsawa tayi baya kadan kafin tace 鈥樷€檛oh ka bari nayi sallah鈥欌€
Da mamaki yake kallonta yace 鈥樷€檔o firnd zaki tafi ki barni ne, lets go together鈥欌€
Shuru sabeeha tayi tana tunanin yanda zatayi dashi, don taso ya barta ta futa ta koma part dinsu ko alwalar ne ya barta ta dauro saita dawo nan, ganin hakan bazaiyuwu ba kawai ta nufi hanyar bathroom dinshi a tsorace.
Yana biye da ita a baya ta tsaya tana bin bathroom din nashi da kallo, kallonda batayi ba bathroom din ba daxu, komai fari qal qal ya hadu ba kadan ba, zata iya rantsuwa akan bata taba ganin bathroom mai girma sosai kamar daki irin wannan ba,.. wajen wash hand basin ta nufa yana biye da ita, alwala ta dauro yanata kallonta hart agama, tana idawa ta juyo sauran kiris su gwaru don suna dab da juna.

鈥樷€檓uje toh鈥欌€
Matsa mata yayi ta wuce kafin yabi bayanta kamar jela har suka kaarso tsakiyan dakin, da kyar tayi indicating kibla kafin ta kalleshi tace 鈥樷€檏a zauna a bed dinka toh, babu inda zanje I promise zanyi sallah ne鈥欌€
鈥樷€橲allah鈥欌€?? ya maimaita abunda ta fada confusedly, da mamaki ta kalleshi tace 鈥樷€檡es sallah,鈥欌€

Yanda tace kuwa hakan yayi ya samu waje a bakin gadon ya zauna, bai yarda ya dauke idanunshi akanta ba harta tada kabbara, ta dade sosai tana jero salloli tana addua harta sallame.
Hannayenta ta daga tana mai kai kukanta wajen allah kamar kullum ta dade sosai tana addua.
Duban agogon dakin tayi ganin wajen kusan biyar da kwata hakan ya sata mikewa ta fara sallar raka鈥檃tainul fjir, tana idarwa ta dubi inda yake zaune, yana kallonta har wani tagumi ya doka ya zuba mata idanu.
鈥樷€檉riend kaje kayi alwala鈥欌€
鈥樷€檃lwala?,鈥欌€ ya sake tambayarta
Nunfasawa sabeeha tayi tana tunanin how he react, tambayr kanta ta somayi kodai bai iya bane, bata kawo wani negative thinking aranta ba ta nufi inda yake tace 鈥樷€檉riend muje toilet鈥欌€

Da saurin shi kuwa ya mike suka wuce bathroom, 鈥樷€檇uk abunda nayi kaima saikayi okay? Wannan ibada ne, idan kanason allah ya baka duk abunda kake so sai ka dunga yi lokacin ta okay?鈥欌€
鈥樷€檡es firnd鈥欌€ ya fada da murnarsa, alwala ta somayi yana kwaikwayonta ita kuwa tana mashi bayani har suka gama, suna idawa suka fito, anan kan carpet ta tsaya yana gefenta 鈥樷€檏aga sallah danayi dazu? Irin shi zamuyi yanxu okay?鈥欌€
鈥樷€檡es firnd鈥欌€ ya fada sounding so excidetedly,
Tada kabbara tayi yana kallonta shima ya yayi, haka ta soma karatu a bayyane shima yanayi har suka idar, suna idawa ta kalleshi 鈥樷€檏aga yanxu allah will answer all your prayers duk abunda kake so you can ask allah鈥欌€
鈥樷€檢an roki allah yasa first love kartayi fushi dani, I want to be seeing her everyday鈥欌€ ya karashe sounding childish

Murmushi kawai sabeeha tayi batace komai ba haka suka zauna, tana lazimi tana koya mashi wani abubuwan, abunda ta lura dashi kamar koyon abubuwa yake, and it looks like ya mance da wasu abubuwan daya shafi addininshi.
Suna nan zaune ya soma gyangyadawa, surprisingly don da wuya yake iya bacci idan bai sha magani ba, kan kace me sai kawai jin kanshi tayi akan shoulder dinta, saita zama wata yar dul a gefenshi, juyoda kanta tayi tana kallon tsakiyan gashinsa dake shoulder dinta, curly gashinsa babu abunda suke sai wani irin kamshi mai dadi, wani ririn murmushi ne ya subce mata kawai, saita samu kanta da tofa mashi addu鈥檕in data iya da ayar allah.
Shiko barci ne mai nauyi ya dauke sa peacefully, sun dan dade a haka ta soma yin hannunta ya qage saboda yana da girma sosai,
Rasa abunyi tayi ganin bata da wani option yasa ta soma mashi Magana cikin rada bayan ta riko hannunshi da hannayenta gudun karya furgita 鈥樷€檉riend, friend, tashi ka kwanta鈥欌€
Kunnenshi ne ya soma jiyo mashi muryarta, take kuwa ya bude idanunshi ahankali da suka soma yin jaa ya zuba mata su, a shagwabe ya tabe baki ya soma miqewa, da taimakonta ta ya kwanta a kan gadon don barci ne mai karfi ya soma fusgarshi.
Yana kwanciya ya kama hannunta yaqi saki haka nan ta hakura ta zauna a bakin gadon idan barcin nasa yayi nisa saita zame ta futa.
Tana nan zaune itama tana zabga hamma har barcin ya sureta ta lafe akan gado hannunshi na cikin nata鈥.


Matar Taj (destined with you馃┑馃)
Written by
Queenmarh鉁嶏笍

Free page
Chapter 10 · 0% Book details