← Book details Matar Taj Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 13 OF 20

Chapter 23-24

Matar Taj Part 1 Complete Hausa Novel · about 23 min read

Update!!!!

Washe gari da safe tun kafin alarm dinsu yayi ringing ta tashi, don yanxu ta fara gane komai na gidan da yanda alamuran gidan ke tafiya, wanka ta fara yi ta saka uniform dinta kafin ta fara nafilfilu, ta dade sosai kanta a kasa tana kiran sunan allah har alarm dinsu yayi kara.

Karfe biyar daidai ta fito daga part din nasu na ma鈥檃ikata kafin ta wuce sama, kamar kullum yauma ko鈥檌na shuru babu motsi saima haske daya bade ko鈥檌na, saman ta wuce cikin natsuwa kanta a kasa, daidai nan daddyn barad ya futo don zuwa sallah, gaishesa tayi kafin ta wuce part din taj.

Koda ta shiga part din batayi gigin shiga bangarensa ba saida ta gama gyaran parlorn kafin ta nufi bedroom din.

Lokacin data shiga yana daga zaune kamar kuwa jiran ta yake yi, murmushi yayi mata wanda ya sata sauke ajiyar zuciya mai nauyi, yau bata shugo ta taddashi yana kuka ba kamar kullum, 鈥渇riend!!!鈥
鈥淣aam friend good morning鈥
Ta amsa shi, murmushi kawai yayi mata kafin yace 鈥渇irst love batazo ba?鈥

Yanda yayi maganar abun tausayi, saida ta karaso ta gane yanayin da yake ciki, he looks so pale, bakinshi ya vushe sosai yayi fariii tarr kamar wadda ke jinya, ga idanunshi sunyi jaa sosai.
Haka kawai taji kamar he doesn鈥檛 sound like yanda yake koda yaushe, 鈥渇riend kayi brush?, ga breakfast na kawo maka鈥
Daidai nan ta karaso bakin gado ta dan duqa don ajiye tray din gefen bedside table.

Kallon corn soup din yayi, take ya soma jin wani abu ya soma zuwan mashi maqogaron shi kamar amai, batama lura dashi ba ta dauka bowl ta miko mashi, daidai nan kuwa ya soma kakarin amai, lokaci guda ya burkice, amai yake son saidai cikin nashi babu wani abun arziki a cikinsa da zai amayar, ganin yanda yake struggle tare da riqe maqogaron shi yasa ta saurin ajiye bowl din hankali atashe.

鈥淪ubhanallah!! Menene? Wani abun ke damunka鈥
Nuni yayi mata da bowl din kafin ya kauda kanshi gefe, 鈥渂ana so鈥
Sai a lokacin ta lura da abuncin ne baya so, gashi batasan ya zata ya ba, abunda aka rubuta kenan a breakfast timetable dinshi kenan, gashi dole saiyaci abunci zaisha magani.
鈥淏aka son wannan?鈥
Ta karashe tana nuna mashi bowl din, girgiza mata kai yayi abun tausayi, 鈥渕eysa baka so?鈥
鈥淚 hate it鈥 ya sake fada
鈥淜ayi hakuri kasha kaji friend saboda ka samu kasha magani Okay?鈥

Juya mata baya yayi a shagwabe tare da nade hannayenshi a kirjinshi 鈥渘o noo banaso鈥
Ya karashe kamar zaiyi kuka.

鈥淔riend dan Allah ko kadan ne kaji? Kaga maganinka ma baka sha ba kar lokaci ya kure鈥

鈥淚 don鈥檛 want to鈥
鈥淚dan baka sha ba first love zatayi fushi dakai鈥 sabeeha ta fada hoping hakan zaisa ya sha, ai kuwa bata gama karashe maganr bama ya juyo ya zuba mata idanunshi, idanunshi da sukayi jaa ya zaro mata shi 鈥渮atayi fushi sosai?鈥
鈥淓h zatayi fushi dakai sosai鈥

Sauke idanunshi yayi kasa irin yanda yara keyi kamar bazaice komai chan kuma ya hadiye wani irin miyau mai daci a bakinsa
Hannunsa ya miqo mata, hakan yasa ta ajiye mashi bowl din a akan lap dinshi.
Kallon bowl din yayi kafin ya runtse idanunshi ya soma diban soup din yana kaiwa baki daga yanda yake sha zaka gane baya so kwata kwata kuma baya mashi dadi a baki, saida yasha kusan rabi kafin ya maido da dubanshi gareta yace 鈥渇riend ya isheni鈥
鈥淪aura kadan friend ka shanye please kaji? Bana son first love tayi fushi okay?鈥

Haka nan ya cigaba da sha harya shanye tas da kyar, sabeeha na ganin haka tayi saurin karban bowl din tace 鈥測auwa friend,鈥
鈥淔riend zanje toilet please i what to pee鈥
鈥淥kay tohm鈥 sabeeha ta amsa shi tana dan yin baya don ta bashi hanya ya wuce.

Kafafunshi ya soma saukewa kasa kafin ya miqe, taku daya yayi ya soma yin baya kamar zai fadi, cikin hanzari sabeeha ta karaso ta kama hannunshi, wani irin zafi taji dayasa ta sakin hannun ta kalli fuskanshi, layi taga ya soma yi wanda ya sata tsorata lokaci guda ta sake taba hannun nashi, yanda kasan daman neman makafa yake gaba daya ya sakar mata jikinshi, wani irin wahalallen nunfashi ta sauke 鈥 wayyo allah na, zaka karyani鈥
Tururin da jikinsa ke fitarwa yasa hankalinta ya koma kanshi gaba daya 鈥渇riend are you okay?, jikinka akwai zafi,鈥
Baya jin abunda take fada ma gaba daya saboda yanda gaba daya yaji wani irin dummm a kunenshi lokacin daya miqe
鈥淶anyi pee鈥

Da taimakonta suka karasa cikin bathroom din, hannunshi har zuwa lokacin yana cikin nata, koda yazo yin pee din ita ta taimaka ta zare mashi mazugin tana kauda ido kafin ta fuce daga bathroom din.

Dakin ta koma ta kwashe bowl din kafin ta fuce zuwa kicin.
Ta dan dade kafin ta dawo cikin dakin saboda wanke bowl din datayi, da mamaki ta karasa bathroom din ganin kamar bai futo ba, knocking ta fara yi, jin shuru yasa ta cewa 鈥渒a gama?鈥
Nan ma shuru babu response, hankalinta ne ya soma tashi,bata tsaya wani dogon tunani ba kawai ta bude kofar ta sa kai ciki, ganinshi a kasa helplessly yasa ta karasowa cikin sauri, babu abunda yake sai kakarin amai gashi aman yaqi zuwa, da sauri ta karasa inda yake ta tsugunnawa, gaba daya ya gigice, babu abunda yake sai kuka, yana jinta a kusa dashi ya nanukota, jikinta har rawa yake.

Daburcewa sabeeha tayi hartama fi shi shiga tashin hankali ganin yanda yake faman tura jikinshi ga nata, aman dake maqale a moqogoron shi ne ya soma zubowa, gaba daya ya amayar da wannan soup din a jikinta wajen gaban rigarta, baiwar allah ko kyankyaminsa bata ji ba saima dabbing bayanshi data dunga yi, struggling sosai ya dunga yi wajen amayar da abunda ke cikinshi tass, ga jikinshi yayi wani irin zumm sosai.
Saida ya gama tass kafin komai ya dan lafa mashi ya kwantar da kanshi a kafadarta jiki a mace ,gaba daya ya gama batasu daga shi har ita, 鈥渇riend i want to see first love please,鈥
Fashewa yayi da kuka don daman idan yana rashin lpy irin wannan indai ba hidaya ya gani ba sai yayi ta kuka.

Wani irin kuka ne ya zo ma sabeeha, allah ya bata wata iriyar raunaniyar zuciya mai rauni, tana da tausayi sosai, musamman idan taga mara lpy, lokacin da aka tafi da inna asibiti kwana tayi tana kuka, duk da zaman su da inna ba wani dadi yake ba hakan baisata tausaya mata ba lokacin da za a kaita asibiti, balle kuma wannnan daya gama shiga ranta saboda lalurar shi,
鈥淚鈥檓 so sorry friend, wallahi bansan ranka baya so ba da bazan baka ba, i鈥檓 so sorry please kaji鈥

Sun jima anan zaune, gaba daya ta zama kamar wata yar tsana a zaune gashi ya rufeta ruff da girman jikinsa daman gata ba tsayin kirki ba ga dan jikin nan nata.
Saida taji ya daina kukan kafin itama ta tsagaita, miqewa ta soma yi ya ruko hannunta 鈥渄on鈥檛 leave me please, karki barni yanda first love ta barni, stay with me, i don鈥檛 want to be alone鈥
Wannan furuci nashi ba karamin narkar mata da zuciya yayi ba don saika rantse mai hankali ne yayi maganar, tasan yana da rashin lpy amma kuma bata san dalilin dayasa kullum yake daki ba dukda ta yanke hakan saboda rashin lafiyarshi amma harga allah yana buqatar yan uwanshi a kusa dashi koba komai shima mutunne kuma yana da zuciya ta dan adam bai chan chanci wannnan ba, saidai tunawa da kaddarar sa kenan yasa ta jin wani irin.

Hannunshi da jijiyoyinsa da suka futo rado rado ta zuba ma idanu don fatarsa fara ce tass, samun kanta tayi ta komawa ta tsugunna a gabanshi ta riko hannunshi 鈥渂azan barka ba friend, i promise,鈥
Murmushi kawai yayi mata kafin ta taimaka mashi ya miqe zuwa wajen basin, wanke mashi baki tayi da kanta kafin ta rakashi har bedroom ya kwanta ta jawo mashi duvet ta rufe shi.

Toilet din ta koma ta gyara shi tsaf sannan ta gyara gaban rigarta daya bata mata kafin ta futo, lokacin data fito har ya soma barcin wahala, sai a lokacin ta tina baisha maganinsa ba, don dole badan taso ba sai dan tsoron kar abunda ya faru kwanaki yasa ta soma tashinsa ahankali, maganin ta bashi yasha kafin ya koma,

Zama tayi daga chan gefe a kasa ta hade kafafunta a kirjinta ta zuba mashi idanu.
He look so innocent, daga yanda yake barcin ma kasan a wahale yakeyi don daga ganin yanda yake furzar da numfashi zaka san yana jin babu dadi.

Zaman awa kusan biyu tayi barci ya soma daukan ta tana gyangyadawa har ya fuzgeta, ba ita ta farka ba sai wajen karfe daya, cikin sauri ta tashi zuwa bakin gadon sa, yanda ta barshi haka ta taddashi yana barci peacefully, ko gyara kwanciyar baiyi ba yana mai fuskantar ceiling, jikinsa kwata kwata baya motsawa badan nunfashi da takeji yana futarwa ba zata rantse ko matacce ne, gaba daya jikinsa ya saki.

Taba shi ta soma yi a hankali, don jin ko da zafi jikin nashi, bataji wani zafi ba hakan ya tabbatar mata ya sauka zazzabin nashi, hamdala tayi ta dauke hannunta daga wuyanshi.
,Futa tayi daga dakin ta sauka kasa zuwan part dinsu don gabatar da sallar dhuhur.

Saida ta idar da sallah yar ghana ta shugo bangaren su, murmushi sabeeha tayi mata don yanxu sun saba sosai, 鈥渒in dawo?鈥 Yar ghana ta tambayeta.
鈥淓h na dawo,mouryoum鈥 (sunan yar ghana kenan)
鈥淎y nazo dazu inata nemanki ban sameki ba, ashe baki dawo ba, kinsha aiki鈥

Hijab dinta datayi sallah dashi ta nannade tana mai sauraron yar ghana, 鈥渁yyuka ne sukayi min yawa yau shiyasa ban sauko ba鈥

Kallon dakin yar ghana ta soma yi, ganin sauran yan dakin basa nan yasa ta jan sabeeha zuwa bakin gado ta zaunar da ita kafin tace 鈥渟abeeha niko inason tambayar ki wani abu out of curiosity鈥
Zama sukayi bakin gadon sabeeha kafin yar ghana ta cigaba da magana 鈥渄an allah menene a saman nan?,鈥
Atsorace sabeeha ta kalleta tana mai kokarin karantarta 鈥渕eysa kike son sanin abunda ke saman?鈥
鈥淏a komai, I鈥檓 just so curious, ki fada min kinji鈥
鈥淣i bansan menene a saman ba鈥 sabeeha ta bata amsa tana mai kauda kanta gefe, cije lebe kawai yar ghana Tayi kafin tace 鈥渮an baki kudi in kika fada min鈥

Wani tunani ne ya zoma sabeeha, ta kasa gane wannan yar ghana din da yanda take yawan tambayarta da bugar cikin ta akan al鈥檃muran dake sama, kullum zille mata takeyi ta hanyar fada mata bata sani ba saidai yanxu ta fara bata tsoro don yawan tambayar nata yayi yawa, wata dabara ce tazo mata wadda batama san ta iya ba.

鈥淣i gaskia ban sani ba, amma nasan head ta sani idan kinaso zaki iya tambayarta saita fada maki鈥
Hankali a tashe yar ghana tace 鈥渁h ah bazan iya tambayarta ba ni fa daman kawai I鈥檓 curious ne鈥

Tabe baki sabeeha tayi kafin ta miqe tace 鈥渒i bari toh ni zan tambayar maki ita鈥
鈥淜i rufa mana asiri, wannan maganar zaisa a koremu daga ni har ke鈥
Toilet sabeeha ta wuce tana kunshe dariyar data zo mata, yanxu ta kara tabbatar da wannan yar ghanar tana da gulma sosai.


Hidaya!!!!
Anatse ta futo daga office, hannunta riqe da jakarta, employees dinta gaba daya babu abunda suke sai gaisheta, ko sau goma kuwa zata sauko sai sun sake gaisheta wannan policy din da kowa ya daukar ma kanshi kenan gudun kar a koreshi, wani baqin shade ne akan fuskanta, tasha mur bakin nan yasha red matte lipstick, yau dai a bossy hidayarta tazo office din, basement ta sauka wajen private parking lot dinta, key din dake hannunta ta danna Nan take blue LV car dinta ta hau kara, tana karasowa inda motar take ta bude tare da shigewa ciki, har zuwa lokacin wayarta ruri takeyi, Jakarta ta wulla gefe kafin ta kunna motar.

Connecting wayarta da motar tayi kafin tayi reverse, maganganu ta soma yi cikin turanci, kafin call ya shiga, harkar smart digital kenan, nan take call din ya shiga, ringing daya akayi picking, 鈥済o and pick up barad鈥
tana kaiwa nan ta futo da haddaiyar motar tata daga basement din, gate din futa daga wajen ma daban ne don an kebar da wajen just for ceo.

With high speed ta hau kan titi tana murza steering, kallon dash board din motar tayi ganin call na sake shigowa da wata unknown number, kara speed tayi kamar zata tashi ranta a mugun bace, tafiyar minti ashirin tayi ta karaso wani beach, sai a lokacin ta rage speed din motar tata, wata hanya tabi daga gefe inda ya kaita har wajen jiragen ruwa na cruise sai na wasu containers, daidai wajen tayi parking kafin wasu armed guard sukazo suka amshi key din don yin parking, bata tsaya amsa gaisuwar su ba ta wuce wajen tafkeken boat dinta, mutanen dake kula da boat din na ganinta sukayi saurin karasowa suna duqa mata, 鈥渨elcome ma鈥檃m鈥 ba tare data amsa su ba tace code 5
Sanin mai hakan ke nufi yasa sukayi saurin bin bayanta, nan take suka soma kunna engine boat din cikin gaggawa,
Ita kuwa tana shiga ciki ta samu waje ta zauna, fadin irin tsaruwar cikin boat dinma bata lokaci ne yanda kasan gida, babu abunda babu aciki ga girma.

Tundata zauna take girgiza kafafunta da yasha zobunan kafa kaf kaf, shade din fuskanta na nan gar zuwa lokaci, bini bini take duban agogon dake hannunta, saida suka dauka wajen awa guda kafin jirgin ya tsaya, kamar jira take kuwa tayi saurin miqewa ta dauki jakarta ta futo cikin qasaita.

Kallon wajen ta soma yi, yau wajen wata guda kenan rabonta data zo wajen nan sai gashi wannan useless mutanen nan suna son su saka mata ciwon kai.
Island ne mai shegen girma sai wani tafkeken gidan guda daya tal da ake hango shi daga nesa, gaba daya ciyayi ya rufe gidan, wajen nada shegen girma kamar daji.

Futowa tayi ta nufi hanyar cikin island din ko tsoron wajen bata ji, ni kaina mai kawo maku rahoto saida na danji tsoro, baka jin komai sai kukan tsintsaye da ciyayi.

Daidai bakin gate faya zagaye gaba daya wannan dajin ta tsaya tare da scanning kanta, nan take gate din ya bude,inda motar dake parke a wajen ta karasa, driver dake zaman jiranta yana sanye da uniform fari kal ne ya bude mata kujerar baya, zama tayi ta hakimce kafin ya rufo kofar.

Hannu ya daga mata ya rissinar da kanshi alamun gaisuwa kamar he鈥檚 deaf baya ji, hannu kawai ta daga mashi yaja motar suka miqi hanyar.
Sun kai wajen minti biyar kafun su karaso gaban wannan babban gidan dana hango daga bakin island din.

Gida ne babba sosai ba karami ba, bata ma jira driver ya bude mata kofa ba ta futo.
Taku dai dai takeyi harta karaso bakin kofar shiga gidan, thump print dinta ta saka kofar ta bude.
Abun mamaki daga waje dai gida ne mai kyau saidai daga ciki babu komai empty, takun tafiyarta yasa suka juyo a rikice, maza ne su kusan hudu gabzaza suna zaune akan kujerun karfe suna cin abuncin, suna ganinta kuwa suka mimike tsaye sukayi layi kafin su soma sunkuyar da kansu, 鈥渨elcome ma鈥檃m鈥
Bata amsa su ba ta tsaya a gabansu, daya bayan daya ta bisu da kallo rai a bace, daya daga cikin su ne ya dauki kujera ya ajiye mata daga gefe kafin ya koma gefe ya tsaya wajen da sauran suke tsaye.

Kallon kujerar tayi kafin ta kaida dubanta ga abuncin da suke ci, lokaci guda taji wani maqoqon bakin ciki ya zo mata, takowa tayi inda suke har gaban wanda ya ajiye mata kujera, babu zato babu tsammani sukaji tasss tass har sau uku, saurin dafe wajen yayi sauran na ganin haka sukayi kneeling a gabanta,
鈥淗ar kuna da time din cin abunci?,shin kunsan problem din dake gaban mu idan har ya tabbata akwai wanda yasan da wannan al鈥檃marin?鈥

Wanda ta mara ne yayi saurin duqawa shima, 鈥渨e鈥檙e sorry ma鈥檃m鈥
鈥淪orry will not fix this? Wani irin useless mutane ne ku da bazaku iya aiki ba tare da kuskure ba? Looks like kuna son nayi wiping dinku ne?鈥

A tare suka soma cewa 鈥渘o ma鈥檃m鈥
鈥淣ow tell me how did you handle it?鈥

Rarraba idanu suka somayi daya bayan daya suna kallon juna, ogan su ne yayi karfin halin cewa 鈥渕adam kinsan bamu taba yi maki kuskure ba, kuma na tabbatar maki wannan karan ma bamu bar any lead da zai nuna cewa intentionally hit and run ac鈥.鈥

Shade din fuskanta ta cire,bacin rai kwance a idanunta, dukda sun tabbatar mata basuyi wani mistake ba tana jin this is not right,鈥

Wani irin disgusting kallo tayi masu a kaskance bayan ta dakatar dashi kafin tayi pointing dinsu daya bayan daya da hannunta 鈥渂e sure of what you said, don wallahi kusan abunda zai biyo baya idan har kunyi wani kuskuren鈥

Tana kaiwa nan ta fuce daga cikin gidan tana furzar da nunfashi mai zafi, idanunta har wani kif kif sukeyi tsabar masifa.
Tana fita kuwa suka miqe taaye suna kabe wandunan su.

鈥淜ai wannan matar fah kamar she鈥檚 a psychopath, zata iya yin komai wallahi,鈥
Ogan su ne ya kalli wanda yayi magana kafin ya shago wuyanshi yace 鈥渂a saida na fada maka kan cewa karkace komai ba? 鈥
鈥淪orry sir鈥
鈥淚na footage din, yau babu wanda zaibar wajennen, inason mu sake duba footage din again and again鈥
鈥淵es sir鈥


Karfe uku da rabi daidai sabeeha ta koma part din, dakinsa ta wuce direct bakinta kunshe da sallama, tundaga bakin kofar dakin ta soma jin fitar nunfashinsa kamar yana battling da breath dinshi.
Karasowa inda yake tayi hankali a tashe, yana nan kwance kamar an qame shi, nunfashi sa ne kawai ke fita da kyar tsabar zazzabin dake cinshi.
鈥淔riend friend are you okay鈥
Duvet din ta yaye mashi, ya jike jargab gaba dayanshi,tabashi ta soma yi don ya tashi don duk a tunanin maybe mafarki yake yi saboda ayanda yake nunfashin da yanda zufa ta wankeshi saida taji zafin ne ta gane cewa zazzabin da yayi dazu ne ya dawo mashi.
鈥淔riend friend鈥 ta soma kiranshi, shuru babu response, at that point hankalinta ya gaba tashi, gaba daya tama rasa ya zatayi, takai wajen kusan 30mins shuru babu response, wani tunani ne yazo ranta, to kodai ya suka ne? Ta tambayi kanta, bata jira bama kanta amsa ba ta wuce bathroom ta debo ruwa a bowl ta dawo bedroom din, wash cloth ta tsoma cikin bowl din kafin ta soma shafa mashi a fuskanshi, nan ma dai shuru, ta dade sosai tana goga mashi tana hawaye har ruwan yayi sanyi, lokacin ana maganar wajen karfe hudu, kamar da wasa ta dago taga idanunshi sun soma budewa, idon yayi jaa sosai,
Hamdala tayi kafin tace 鈥渕eysa Kaqi tashi? Hankalina duk ya tashi na dauka wani abu ne ya sameka鈥
Da hausa tayi maganar so bai gane abunda take nufi ba don haka kawai ya zuba mata idanu, wannan ruwan data goga mashi a jiki ya sashi jin sanyi sosai, saida ya farka nema zazzabin yayi doubling, take ya fara karkarwa kaf kaf, hakoranshi na gogayya dana juna, burkice dai sabeeha ta burkice sosai don unexpectedly ya fara jijiga ba kamar dazu da yake barci ba kwata kwata baya motsawa, 鈥渋nnalillahi wa inna ilaihi rajiun鈥 ta furta ganin idanunshi na neman qafewa, 鈥渘a shiga uku don Allah meke damunka? Ka fada min menene?zazzabin ne?鈥
Ta sake tambayarshi hankali a tashe, burgimar daya farayi ne yasa ta shiga wani sabon hankali, kankace me bata ankara sai ji tayi dimm ya fado kasa, cikin sauri ta nufi hanyar fita daga dakin harma part din gaba daya, karar dataji na futowa daga sitting room dake saman ne yasa kawai ta nufi wajen hankali a tashe kamar an jeho ta, fadwa dake zaune tana waya afiya kima na daga gefenta tana cin pizza tana kallo suka zuba ma sabeeha ido da mamaki, jikinta na kyarma ta shugo bedroom din.
Kallonta sukeyi afiya ce tayi saurin cewa 鈥渒e bakida hankali ne, wannan illiterate dinfa ko harda mahaukata ne suke mana aiki鈥

Fadwa ce data gane ta tayi saurin katse wayarta ta kalli afiya tace 鈥渢hats new maid din big baby鈥
鈥淥h da alamu itama haukan ya taba kanta kenan鈥 afiya ta fada sounding so annoyed
Fadwa ce kawai ta kalleta tace 鈥渕e ya shugo dake?
鈥淢adam, frien鈥. Sorry sir ne bashida lafiya鈥
Afiya ce tayi saurin cewa 鈥渄aman wayace maki shi mai lafiya ne? Ni bansan wake kawo irin waennan africans din nan ba? They are the stupidest people鈥
Sauke kai sabeeha tayi hawaye na gangaro nata, fadwa ce ta sake cewa 鈥済o and do your job properly鈥
Jiki a Mace sabeeha ta juya ta fito daga part din, gaba daya ta rasa ya zatayi, wajen wa zataje? Tunawa da head yasa ta saurin sauka kasa tana hawaye, daidai hanyar dazai kaita ga dakin head tayi karo da yar ghana, kallonta yar ghana tayi ganin duk ta burkice yasa ta cewa 鈥渟abeeha? Are you okay?鈥
Sabeeha batama lura da ita ba ta wuce dakin head, ciki ta shige ta rufo kofar, duve dube ta soma yi ganin bata nan yasa ta saurin fitowa, a bakin kofa ta sake tadda yar ghana a tsaye, 鈥渋na head?鈥

鈥淚 dont know but maybe tana kitchen鈥
Kitchen din sabeeha ta nufa hankali a tashe, tana shiga ta hangota cikin sauri ta karasa inda take ganin babu kowa a kitchen din.
鈥淗ead, please ki taimaka min, sir bashida lafiya鈥

A burkice head ta soma duban kitchen din kafin ta janyo hannunta suka fuce daga kitcehn din, wani corridor sukabi inda take tabbatar da babu kowa a wajen kuma babu wanda zai jisu
鈥淜e bakida hankali? Wayace maki zaki iya wannan maganar a ko鈥檌na? Shin kin manta you鈥檙e not to disclosed abunda ya shafe shi ba?鈥

鈥淚鈥檓 sorry head, wallahi bashi da lafiya he鈥檚 sick鈥
Buge mata baki head tayi 鈥渁nd wayace maki daman mai lafiya ne shi? Ina mai baki shawara idan har kinason rayuwarki da lafiyarki dole sai kinbi yanda aka kayyade maki, dont ever step down and say a word about abunda ke sama鈥

Tana kaiwa nan ta fuce, sabeeha dai hawaye bata bar yinshi ba anan tsaye, wannan wani irin masifa ne haka, ayanda take ganin yanda yake wahala zai iya mutuwa wallahi, tunawa da kalamanshi da yayi mata dazu inda yake ce mata karta barshi yasa ta komawa zuwa saman, a daidai nan ta bakin kofar kitchen din ta hango yar ghana a tsaye ta labe,bata ma tsaya bi takanta ba don ba wannan ne agabanta ba yanxu ta wuce sama.
Koda ta karaso sama tana jiyo yanda fadwa da afiya ke hirarsu suna kallo, tsugunnawa kawai tayi ta soma hawayen takaici, dukda batasan alakarshi dasu ba amma yanda taga kammanin su ta tabbatar yan uwansa ne suma, ranta yayi mugun baci da yanda suka amsa ta lokacin data shiga wajen su, wannan wani irin ahali ne? Ta soma tambayar kanta? Ita tasan mara lafiya zama ake dashi shi kuma wannan gudunsa akeyi saboda wani dalilin daban wanda bata san koma menene ba saidai tana jin harga allah ba ayi mashi adalci ba.

Tana nan tsugunne dadyn barad ya karaso saman shida barad, daman shi yaje ya daukosa yau, tun daga bakin stairs ya fara jin sheshekar kukan nata, da mamaki kuma ya ganta a zaune bakin kofar dakin tana kuka.

鈥淲hat鈥檚 going on here?鈥
Cikin sauri sabeeha ta dago kanta, ganin wanda ke gabanta ya sata miqewa cikin gaggawa, 鈥渁kwai wata matsala ne?鈥 Ya sake tambayarta

Kamar jira kuwa take ta girgiza mashi kai 鈥渟ir please friend bashida lafiya鈥
Shuru yayi yana wani nazari, ganin yanda take kuka yasa shi kallon barad yace 鈥済o and freshen up okay?鈥
Yana kaiwa nan ya nufi part din taj, kofar ya bude sabeeha na biye dashi har cikin bedroom din, tun daga nesa ya hangoshi a kasa kamar matacce ga hannunsa daya ballaqe shi gefe, cikin hanzari kuwa jamid ya karasa inda yake ya juyoshi, jikinshi ya koma jawur, har zuwa lokacin karkarwa yake,
鈥淚nnalillahi, whats going on here? Me ya sameshi?鈥
Jiki na bari sabeeha ta soma bayani, 鈥渟ir tun safe yake zazzabi bayan na bashi medication dinshi sai yayi barci By 3 na dawo zan bashi second dose shine naga baya motsi.

Duk rikicewar sabeeha bata kai jamid ba, jijiga taj din ya soma yi 鈥淭ajudeen hey hey!!! Open your eyes鈥
Ay Inaaaa taj baya ji kwta kwata, idanun nan sun rufe ruff, rasa abunyi jamid yayi, tunani kala kala Na yawo a ranshi, karshe dai kawai yayi deciding daukarshi gaba daya,
鈥淶oki taimaka min鈥
Matsowa tayi ta kama hannunshi don taimaka mashi, dakyar take jan hannun tana zufa harda nishi, haka nan jamid ya daukeshi duk da shi namiji ne dakyar ya daga shi ya sashi a bayanshi don yana da girma sosai masha Allah.

鈥淏ude kofar鈥 ya umarci sabeeha,
Kofar ta bude ya fito dashi a bayansa, sabeeha na biye dasu tana kuka har suka fito daga part din, suna nufin sauka kasa saiga hidaya ta hauro last stair,da mamaki take kallon abunda idanunta ke ganar mata, tabbas big baby ta hango a bayan jamid.
Ganin yana neman wuceta yasa ta saurin damqo hannunshi ta daka mashi tsawa kamar ba mijinta ba
鈥淛amiddddddd鈥hats going on here whats this? Are you out of your mind ina zaka kaishi?鈥

Yasan halinta don haka ya amsa ta 鈥渂ashida lafiya he鈥檚 in a critical condition?鈥

鈥淲ait what? Ina zaka kaishe then?鈥
Wata iriyar tsawa ya daka mata 鈥淪hin bakiji me nace bane? He鈥檚 in critical condition and you鈥檙e still questioning me?鈥

鈥淭oh daman wa yace yana da lafiya? Look jamid babu inda zaka kaishi, zan kira medical team dinshi suzo yanxu鈥

鈥淗idayaaaa!!! Meysa bakida tunani ne? Whys your heart sore? Shin kina jin abunda kike fada kuwa鈥

鈥淢ajid!!!!!鈥 Itama ta daka mashi tsawa, su fadwa tuni suka fito suka tsaya suna kallon ikon allah
鈥 how dare you? How dare you? Kai waye nashi? Who are you to him? His guardian angel or what? Ni ce guardian dinshi? He鈥檚 under my care saboda shi kadai ne kanina, kana son ka nuna min ka fini sonshi ne ko ka fini damuwa dashi? You鈥檙e making me look at you as a hypocrite,鈥

Yanda kasan ta buga mashi arrow a kirji haka yaji, yau hidaya da bakinta ke fadin mashi cewa tana kallonshi a matsayin hypocrite?

Kasa motsawa kawai yayi, badan taj yana da special waje a tarihin rayuwar shi ba daya barshi da ita kawai saidai bazai iya ba dole ya zama strong and komai zata ce bazai taba saka shi giving up akan taj ba saboda karfin alqawari.

Wayarta ta daga ta soma dialing heath team din dake kula dashi.
Bawan allah taj yana nan ya gama galabaita sabeeha kuwa kukan da take ya wuce musali dukda kunshe kukan takeyi don karya futo fili, fadwa da afiya kuwa kamar suna kallon tv, yau wata takwas kenan rabon da su ganshi sai yau, ya chanza sosai kamar bashi ba, Taj mai kwalisa mai class da girman kai da aji shine ake fada akanshi, idan ance masu he will look helpless kamar yanxu zasu rantse karya ne,tabe baki afiya tafi ita ranta ya gama baci ganin yanda ake ta fada akanshi, sai taji tsanarshi na ninkuwa a ranta, whys the world revolve around him? Kowa is trying to protect him, abunda yafi damunta shine yanda hidaya ta tsaya akanshi, ita wannan abun yana damunta sosai.

****
Cikin yan mintuna kadan saiga health team sunzo, lokacin jamid ya maidashi daki ya kwantar dashi.
Cikin gaggawa suka soma dubashi suka sa mashi ruwa da allurori irin nasu na masu matsalar amnesia, wani irin special care aka bashi na gaggawa har aka samu ya soma dawowa daidai.

Saida doctor ya tabbatar masu cewa zaiji sauqi kuam he鈥檚 stable kafin ya fita da team dinshi.

Sabeeha na rabe daga gefe ta kasa tafiya, baiwar allah ta tsorata sosai.

Hidaya ce ta futa ba tare da ta kalli inda sabeehar ke tsaye ba, tana fita jamid ya miqe shima, 鈥減lease take care of him dan Allah karki bar kusa dashi i trust you okay?鈥
Girgiza mashi kai tayi alamun gamsuwa kafin ta karasa bakin gadon ta zuba mashi idanu abun tausayi.

Majid na fita dakin su ya wuce, yana shiga ganin bata dakin yasa ya wuce closet room, kofar ya banko ya shiga, yana shiga ya ganta tana kokarin rage kayan jikinta,
鈥淗idaya!!!鈥
Wani irin kallo tayi mashi, 鈥 please bani da time din wannan surutan naka? Na fada maka whatever comes around matiqar yayi involving big baby ne babu ruwanka, don babu ruwana da kai mijina ne duk abunda nayi鈥︹€

Dakatar da ita yayi ta hanyar cewa 鈥淲ow,hidaya, you always don鈥檛 fail to amaze me so impressive, bazan tsaya muna jayayya dake ba but inason ki sani, babu wanda ya sanki sama dani? Ciki da waje, i know all your movements da intentions dinki, kina ganin wannan abubuwan da kikeyi shi zai rufe abunda ke zuciyarki dana karanceshi tun shekaru da suka wuce? Idan har zaki yaudari duniya ni bazaki taba yaudarata ba, i鈥檓 warning you, don鈥檛 try my patience, mu tafi a haka har allah ya bashi lafiya, saidai ina so kisan cewa ko me zakice bazai taba hanani shiga al鈥檃marin taj ba, you can never stop me, duk abunda zakiyi kiyi,鈥
Yana kaiwa nan ya fuce rai a bace.

Saurin runtse idanunta tayi da sukayi jaa sosai, ya zatayi da jamid, ya zatayi da jamid, kamar mahaukaciya haka ta soma watsar da kayan dresser dinta, me yake nufi kenan? Dole yasan da wani abu kenan,? Whats in his mind?
Tabbas tasan jamid shi yafi kowa saninta da halinta tunda shike zaune da ita saidai bata taba tsammanin zaiyi threatening dinta ba,

Zarya ta soma yi tsakanin dakin tana tunani, 鈥渋 need to do something, kafin lokaci ya kure鈥
Ta fada ma kanta鈥︹€..


Matar Taj (destined with you馃┑馃)
Written by
Queenmarh鉁嶏笍

Free page
Chapter 13 · 0% Book details