Chapter 5-6
Matar Taj Part 1 Complete Hausa Novel · about 23 min read
3 months ago (wata uku da suka wuce)
FCT Nigeria鈥︹€︹€.
Dutsen habuja wani gari ne dake a baya bayan garin abuja, yawancin mazauna garin basuda arzikin zama cikin ainihin garin Abuja,sai ya kasance masu zama a cikin garin zaman rufin asiri sukeyi saboda rayuwar Abuja sai mai arziki.
Acikin garin akwai anguwar datafi fuce a cikin garin wadda ake kira da kayefi, anguwace me qunshe da tarin jama鈥檃 don anguwar a cunkeshe take da mutane, both chiristians da musulmai harma da waenda basuda addini,a bangaren culture kuwa babu wanda babu a aguwar, gwari, yarbawa, igbo, igala duka,haka zalika ginin aguwannin cikin layin kwata kwata basuda kan gado don yawanci gidaje ne na haya barkate don ko hanyar da mota zata kutsa cikin layin babu.
Yawan mutanen anguwan yasa aka samu qarancin tsafta a anguwar saboda yanda mutane ke sana鈥檃 daban daban acikin anguwar don su rufa ma kansu asiri su samu na cin yau da gobe.
Da sallama wata dattijuwar mata ta shigo daya daga cikin gidajen haya a anguwar kayefi anan bayan garin Abujan,dan karamin gida ne daga waje mai kofar karfe, labulen zauren gidan ta dage inda ta sanya kafarta cikin tsakar gidan, hayaniyar da akeyi daga ciki ne ta karade tsakar gidan inda wasu mata da mazan gidan ke hada hadan su kowanne yana abunda ya shafe sa.
Wato daga cikin gidan dakuna ne kusan guda biyar a jere, sai dan tsukeken tsakargidan da bandaki sai wata yar rumfa da alamu anan sukeyin girki.
Ragowar Goron dake hannunta ta wulla cikin bakin ta kafin ta rike sandar dake taimakonta wajen tafiya don tana da kiba sosai gashi girma yazo don kamarma dan dingisawa takeyi, sanye dattijuwar take da atamfa riga da zani sai wani mayafi kore kore.
Tana karasowa tsakar gidan ta soma tari saboda hayaqin daya bade tsakargida inda yake fitowa daga rumfar girkin su.
Matan dake zaune a tsakar gidan sunsha daurin kirji sai faman zazzaga masifa suke tsakanin,daman sun saba, don dawuya ayi wuni guda ba tare da anyi fadan nan ba kamar kaji.
Mazajensu kuwa suna kallonsu ko qala bazasu ce masu ba, mazauna gidan maqotansu kuwa babu wanda yake shiga irin wannan fadan saboda daga hakan yake jawo babbar matsala.
Takalman kafafunta ta soma zarewa ta ture su gefe guda hannunta rike da leda, ta soma takowa daidai hanyar rumfar girki kafin ta dan leka tare da daga murya tace 鈥樷€檏eeee sabeeha?? wannan hayakin fah? Babbake gidan zakiyi ne?鈥欌€
Yarinyar dake tsugunne a bakin wata runfa daga chan tsakar gida sai faman rura wuta take kamar ranta zai fita don iccen kwata kwata bashida cii saboda yanayin garin yau ayi rana gobe ayi ruwa, takai kusan awa guda a tsugunne tana faman abu daya, gashi rana ta fito kwal sosai don rufin langa langa ne wanda hakan yasa zafin ya hadar mata biyu ga zafin rana gana wuta don kusan kowa ya daura tukunyar girkin rana.
Jin sautin muryar kakarta yasa ta saurin juyowa ta mike tsaye don nufin hanyar fucewa daga rumfar,gyaran mataccen hijab din jikinta ta soma yi don yayi mata yawa sosai gashi ya kode,ta wajen wuyan hijab din ta tattaro shi ya rufe rabin fuskarta, babu abunda ake iya hangowa sai hazel eyes dinta da sukayi jaa masu daukar hankali da ido, gashin idanunta sunyi wara wara saboda hawayen dake zubo mata saboda hayakin data shaqa, wajen brows dinta kuwa a cike yake da gashi har yana neman hadewa baqi wuluk dashi.
Saida ta fito sarari sosai na kalleta dakyau, daga ganinta tana da dan haske saidai wahala data kodar da ita, bata da wani tsayi sosai saidai baza ace da ita gajeruwa ba, kana ganinta kaga yarinya danya shataf don bazata wuce shekaru sha bakwai zuwa sha takwas ba, hijab din jikinta yasa na kasa gane yanayin jikinta saidai bata da wani qiba, kafarta sanye da baqin silifas daya soma cinyewa.
Tari ta soma yi tana mutsiqa idanunta da sukayi jaa kafin cikin ladabi ta soma Magana tana mai kokarin karbar ledar hannun inna 鈥樷€檚annu da dawowa inna鈥欌€
Kallon fuskanta inna tayi idanunta yayi jaa sosai gashi sai kaurin hayaki takeyi ga uban zufa data tsatsafo mata.
Adan fada fada inna ta soma Magana 鈥樷€檞annan hayaqin fa? Ni mai larurar idanu ay sai ki karashe min ganin nawa 鈥樷€
Inna ta karashe tana mata wani irin kallo, shuru yarinyar data kira da sabeeha tayi tana mai sauraronta saida takai aya tukunna kafin ta soma Magana cikin ladabi.
鈥樷€檌nna iccen ne ba鈥a ci鈥欌€.
鈥樷€檏e har yanxu hada icce ya zame maki wani jan aiki,ina uwar taki鈥欌€
Kanta ta sauke kasa tana mai duban jar kasan dake tsakar gidan don ko sumunti ba ayi ba ,鈥欌€檅ata dawo ba 鈥欌€ ta bata amsa
Saurin runtse idanu inna tayi don yana yanar da idanun nata keyi cikin yan kwanakin nan yasa ganin ta ke neman daukewa dukda bata bari kowa yasan da yanayin da take ciki ba.
鈥榢in gama dahuwar kwan?鈥欌€ ta sake wullo mata tambaya
鈥樷€檈h na gama tun daxu, abunci rana ne nake kokarin daurawa鈥欌€ ta bata amsa a natse.
鈥樷€檢oki bani ruwa mai sanyi in kashe kishirwar dana kwaso,鈥欌€
Tana kaiwa nan ta nufi hanyar dazai sadata da dakin su, kofar dakinsu na daga chan saqo, daga gefe kuma wani daki ne karami.
鈥樷€檌nna ka dawo鈥欌€ wata matar gwari dake kokarin daurama yarta robar dafaffiyar masara ta sayarwa ta soma Magana.
Kallon inda take inna tayi kafin ta washe baki don ita kadaice suke mutunci a gidan dan sauran kwata kwata basuda mutunci 鈥樷€檓aman chidi na dawo, ina chidin yake鈥欌€
鈥樷€檚hege yaro ya tafi yawo鈥欌€ matar ta bata amsa
鈥樷€檡ara daman ba鈥檃 rabasu da yawo, miqon masarar hamsin鈥欌€ ta karashe tana wucewa
鈥樷€檛oh,鈥欌€
Karbar masarar sabeeha tayi kafin ta bi bayan innar har suka zo daidai kan damali kofar dakinsu inda suke yawan zama musamman idan ana kwalla rana saboda wajen akwai dan damshi damshi, tabarmar dake ajiye a wajen sabeeha ta warware ta shimfida kafin ta nufi uwar dakin su, labulen dakin ta daga tare da saka kai ciki, dakin bashida wani girma da alamu ciki da parlor ne don naga harda yan kujeru guda biyu sai ledar daki saidan fridge, daga gefe kuma wata yar yaloluwar katifa ce, ko鈥檌na fess fess babu qazanta sai kamshin turaren tsinke dake tashi.
Direct inda dan mataccen fridge dinsu yake ta nufa ta bude kafin ta zaro pure water guda daya mai dan sanyi.
Tana fitowa a zaune ta tadda inna yanda ta barta tana bude ledar data shugo dashi, yar shinkafa ce ta auno masu ta awo kwano daya sai taliya itama wadda ta auno saidan manja da maggi da kuka.
Anatse sabehaa ta tako inda inna ke zaune kafin ta zauna gefenta cikin ladabi tace 鈥樷€檌nna ga..shi鈥欌€
Kurama fuskar ta ido tayi data danyi duhu, baka ganin komai sai kwayar idanunta sai dan karan hancinta,saboda yanda ta janyo wuyan hijab din daidai wajen bakinta.
Ruwan hannun nata inna ta karba tana mai yin wani tunani da yake bata mamaki tun da sabeeha ta soma tasowa.
Saida ta shanye ruwan tass kafin ta kalleta tace 鈥樷€檍eki karasa abuncin kizo ki tafi, karta dawo ta fara zazzaga masifar fitar ki data saba, ni na kasa gane wannan wani irin abu ne, yoh idan baki futa ba kema kin nemo mana abunda zamu rufama kanmu asiri ya zamuyi?, wallahi bazai yuwu ba kuwa, mun gajii nema don haka kema saikin nema na kanki wallahi,zaman banza bazai yuwu ba, ni yanxu da futa ke neman yimin wahala ga ciwon kafa鈥欌€
Cikin sanyi tace
鈥樷€檛oh鈥欌€
Mikewa tayi ta wuce hanyar rumfar girki, maficin data ajiye a gefe ta dauka ta soma rura wutar, saida ta dauka kusan minti goma ta samu wutar ta kama da kyar, hamadala tayi kafin ta mike da robar shinkafar data tsince tsakuwar ciki ta juye cikin tukunyar.
Bakin rigiyar dake hanyar bandaki ta nufa ta janyo ruwa a buta ta wuce bandaki, dakyar ta karasa cikin bandaki kamar zatayi kuka saboda dattin daya yi, kuma da safe saida ta wanke shi tass kafin mamanta ta futa don duk safiya saita wanke mata idan tazo shiga,sha鈥檃nin gidan haya dai sai a hankali, shiyasa yawanci bata shiga bandakin cikin gidan, idan ma zata shiga sai bayan mamanta ta futo nan ne take samun damar yin wanka idan bata samu shiga a wannan lokacin ba haka zata hakura saita futa. Ruwan butar data debo ta tutule ta dauraye inda zatayi amfani dashi kafin ta futo.
A gurguje ta gama dafa dafadukar shinkafa, ta juye cikin kular su dukda dahuwar bataji kayan kamshi ba da nama hakan baisa kamshin abuncin yaqi fitowa ba.
Dakinsu ta nufa da kular lokaci inna ta wuce ciki, ganin bata parlor yasa ta ajiye inda take ajiyewa koda yaushe.
Cikin uwar dakin ta shiga da sallama, a kwance ta tadda inna kan gadon karfensu sai kwasar munshari take, gefenta masarar data gama ci ne ta yasar anan kan gado.
Kauda kanta tayi ta wuce wajen da akwantin kayanta ke ajiye gefen sip, budeshi tayi ta zaro wani hijabi wanda shima yadan soma kodewa, tana zarowa ta rufe akwatin ta fito daga cikin dakin zuwa parlor.
Hijab din jikinta ta soma zarewa daidai nan aka daga labulen dakin nasu, cikin sauri ta sauke hijab din ba tare da ta cire shi ba.
Kamar an wulloshi haka ya shugo cikin dakin, kallo daya tayi mashi yana sanye da riga yar shara sai wani wandon jeans daya dan yage daga kasan wandon, idanun nan nashi jajawur kamar gauta,dauke idanunta tayi da sauri daga kanshi kafin tace鈥樷€檚annu da dawowa kawu鈥欌€ cikin ladabi
Baima tsaya amsata ba yace 鈥樷€檃n gama abinci?鈥欌€
鈥樷€檈h an gama鈥欌€ ta bashi amsa
鈥樷€檢ubo min鈥欌€ ya karashe yana wucewa wajen kujerar parlor,
Abuncin ta zuba mashi kafin ta ajiye mashi a gabanshi sannan ta dauko pure water ta ajiye mashi.
tana gamawa ta janyo robar kwan da take futa sayarwa kafin ta fuce daga dakin, saka hijab din da batayi ba Kenan.
Silifas dinta ta zura ta fuce daga gidan nasu dayayi gaja gaja, haka ta dunga kutsa layikan anguwan kafin ta fito hanyar titi, har lokacin bata cire hijab dinnan daga fuskanta ba.
Saida tazo dadai bakin titi inda suke tsayawa kafin ta dan tsagaita, yara ne da yawa harda waenda basu kaita shekaru ba kowannen su da abunda yake saidawa, masu saida muruci, masara gyada, ayaba da sauransu.
Da ansamu traffic haka zasu wuce wajen motocin nan suna tallata abubuwan da suke saidawa, daman titin yawanci matafiya ne suke wucewa,haka ta dunga bada himma itama wajen saida kwan zabo har saida takai wajen karfe biyu da rabi kafin ta wuce tsallake wajen wani gidan mai inda anan ne take samu ta shiga bandakin wajen don yana da tsafta sosai kuma akwai fanfo da bokiti, wani sa鈥檌n ma anan take yin wanka idan bata samu tayi daga gida ba.
Bangaren mata ta nufa ta wuce bandakin ta dauro alwala kafin ta fito anatse da hijab din nata.
Masallacin kusa da bandakin ta wuce, da sallama ta shiga wajen,kamar koda yaushe yana nan fess fess don ana kula da wajen sosai.
Wata nauyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke saboda wani irin ni鈥檌ma zataji ya sauko mata, tana samun natsuwa da zarar ta zo cikin masallacin nan.
Babu mutane ko daya a cikin masallacin don haka ta nufi wani sako ta tada kabbarar sallah, ta dade sosai wajen sujud tana pouring abubuwan dake cikin ranta, kafin ta salleme.
Tana idarwa ta jingina da bango ta lumshe idanunta, tunanin rayuwarta shekara hudu da suka wuce ta fara, a lokacin idan da za ace mata rayuwar ta zata juya haka zata musa dukda bata samu rayuwar yanci ba, sallamar dataji ne yasa ta amsa ba tare da ta bude idanunta.
Ta dauka kusan minti goma a haka kafin ta bude lumshenshun idanunta ta mike, daidai nan matar datayi mata sallama daxu ta fice daga masallacin, bayanta tabi da kallo kafin ta nufi hanyar futa itama, daidai nan idanunta ya sauka akan purse, kamar bazata dauka ba chan kuma wani tunani yazo mata tunawa da lokacin da ta shigo ita kadaice sai matar data futa yanxu.
Cikin sauri ta dauki purse din ta fuce daga cikin masallacin tare da daukan bucket dinta data ajiye a bakin kofar masallaci.
A gaggauce ta zura silifas dinta tabi bayan matar har tazo daidai wajen da matafiya suke parking motocinsu, ware idanu ta soma yi tana fatan ganin matar, cikin ikon allah kuwa ta hango ta don wani gold peachy mayafi ta saka kuma shi ta gani a jikinta dazu da zata futa daga masallacin.
Ganin matar na shirin shiga zabgegeiyar motar ta yasa tayi saurin hanzarta karasawa wajen motar har tana haki.
鈥樷€檃ssalamu alaikum hajiya hajiya dan鈥sa..ya鈥欌€
Chak matar ta tsaya kafin ta juyo, masha allah, matar fara ce tass ta dan manyata sosai, daga ganinta kasan hajiya ce babba mai ji da nera,kallonta matar tayi kafin ta ajiye wayar dake maqale a kunnenta.
Kallonta sabeeha ta tsaya yi kirjinta na bugawa kafin tace 鈥樷€檋ajiya kinyi mantuwar jakarki鈥欌€
Ta karashe tana miqa mata purse din nata, cikin sauri matar ta kalleta kafin ta kalli purse din, da mamaki matar ta sake ta kallon yarinyar
鈥樷€檚ubhanallahi a ina na yarda purse din?鈥欌€
鈥樷€檃h masallaci ne kika barta鈥欌€ sabeeha ta amsata
Murmushi matar tayi kafin ta amshi purse din ta bude, zunzurutun dollars din dake ciki suna nan intact harda identifications card dinta da atms dinta duk suna nan, mamaki ne ya lulube matar don babu wanda zaiyi irin wannan tsuntuwar ya maidota.
鈥樷€檏ai amma nagode sosai kinji yarinya鈥欌€
鈥樷€檅a damuwa hajiya鈥欌€ ta karashe tare da juyawa
鈥樷€檛saya鈥欌€ matar tsaidata, kafin ta bude bayan motarta, handbag dinta ta bude ta kwaso wasu kudade da bata ma san ko nawa bane kafin ta rufe motar ta fuskanci yarinyar
Kallon kudin da matar ke miqa mata tayi kafin ta dago da fuskanta ta kalleta
鈥樷€檏arba wannan, nagode sosai kinji ko,鈥欌€
鈥樷€檃h ah hajiya basai kin ba..ni ko..mai ba鈥欌€
Matar Bata jira amsanta ba kamo hannunta ta danqa mata kudin kafin ta juya tana mamaki sosai, ashe akwai honest mutane wannan generation din, kuma yar talla ma abun mamaki.
Da mamaki sabeeha ta dago ta kalli matar tare da hannunta, kudi ne masu yawa don akalla zasu kai dubu goma, tana kokarin yin Magana matar ta tada motarta ta fuce daga gidan man.
Kallon kudin sabeeha tayi kafin ta dauka bokitin ta ta fuce daga cikin gidan man, saida ta tsallaka titi kafin ta dan tsagaita, kudin cinikin datayi na kwai ta fara irgawa, dubu uku ne daman, qullesu tayi ta saka cikin robar, kafin ta maida dubanta ga kudin da matar nan ta bata shima irgawa ta farayi tana tunanin me zatace a gida, chak ta tsaya da irgen ganin wani dan passport photograph, kyakyawar fuskar matar nan taci karo dashi, da mamaki take kallon passport din 鈥樷€檞ayyo, yanxu haka batasan ta hado dashi ba鈥欌€ sabeeha ta fada kafin ta ciro passport din sannan ta nannade kudin.
Hanyar gida ta nufa cikin sauri saboda yau tayi yamma sosai, daman tsoronta kar mamanta ta dawo shiyasa kullum inna ke nanata mata akan ta dawo da wuri gashi yau takai har wajen uku da rabi.
Hankali atashe ta shigo layin nasu har ta karaso gidan, da sallama ta dage labulen zauren gidan, daidai nan aka watso kaya waje, kallon kayan tayi kafin ta maida dubanta ga wanda ke watso kayan.
鈥樷€檊et out ungrateful woman鈥欌€ wani mutumi ya fada
鈥樷€檖apa kemi, why are you doing this to me, wallahi bazanje ko鈥檌na ba, bazan tafi nabar yaya na ba saboda ka kawo yan iskan matanka鈥欌€
Tass bayaraben ya wanke ta da mari, dafe kuncinta matar tayi kafin itama ta dago ta wankeshi ji kake tass,
Karshe dai dambe suka fara babu kunyar ganin idanun mutane da yayansu haka suka dunga jibgar juna, mutanen cikin gidan kuwa babu wanda yace dasu qala, sabeeha dai kauda kanta tayi gefe hankali a tashe don lokacin data shugo har an fara kiraye kirayen sallar la鈥檃sar wanda hakan ke tabbatar mata da mamanta ta dawo.
Fadin irin tashi hankalin dake kwance cikin idanunta bata lokaci ne don kamar har jikinta rawa rawa ya fara.
Tsallake kayan tayi ta nufi hanyar dakinsu, silipas din kafafunta ta cire kafin tayi sallama a natse.
Labulen dakin ta daga tare da shigewa ciki, gabanta ne ya bada dam ganin maman ta a zaune gefenta kuma kawarta ce kuma aminiyarta.
Kamar munafuka haka ta shugo tsakiyan dakin kafin ta tsugunna, 鈥樷€檅arka da hutawa ina wuni mama鈥欌€
Daya daga cikin su ce ta kalleta babu yabo ba fallasa tace 鈥樷€檡auwa鈥欌€
Dayar kuwa ko kallon inda take batayi ba, saima maida hankalinta datayi wajen rubutun da takeyi a cikin memo, ganin haka yasa sabeeha wucewa uwar dakinsu, a zaune ta tadda inna tana ta faman qulle qullenta data saba.
Sallamar da sabeeha tayi yasa ta saurin dagowa ta kalleta, 鈥樷€檏e kuma sai yanxu kikaga damar dawowa?, me kika tsaya yi?鈥欌€
Karasowa tayi kusa da innar ta ajiye bokitin kwan a gabanta kafin ta fiddo kudin dake ciki tace 鈥樷€檡au banyi ciniki ne da wuri ba ne shiyasa鈥欌€
鈥樷€檃y ga uwarki nan zaki mata bayani ne bani ba, miqon kudin, yau nawa kika samu?鈥欌€
鈥樷€檇uka na sayar鈥欌€ sabeeha ta bata amsa.
Washe baki inna tayi tana karbar kudaden kafin tace 鈥樷€檍eki dauki ragowar abunci kici鈥欌€,鈥a toh ta amsata kafin ta mike ta dauki kular, budewa tayi kamar yanda tayi expecting daman ba wani da yawa zata samu ba don haka ta hakura ta zauna kawai ta soma turawa, allah ya taimaka bata fiye cin abunci sosai ba dama dai ruwan lipton ne, bata gajiya dashi, saita sha ruwan lipton kusan sau goma arana indai zata samu ba zata damu da abunci ba.
A parlor kuwa sai bayan wucewar ta ciki suka cigaba da Magana, 鈥樷€檡anxu ke hadiza barin yarinyar nan kikayi tana futa? Ko tsoro bakyaji?鈥欌€ ta karashe tana mai kallon wadda ta kira da hadiza
鈥樷€檍amila ya kikeso nayi toh?, nayi duk yanda zanyi akan inna ta daina bata tallan kwan nan taqi,jiyama da haushi na ta kwana, wai dole ta fita nema itama鈥欌€
鈥樷€檋mm bakya hango risk din dake cikin barinta ta fita ne shiyasa baki tsaya tsayin daka ba, amma idan ta tsohuwar nan ne ko cikin dan kudin kayan da kike sayarwa ay zaki iya fidda yar dubu ki dinga bata duk sati kina toshe mata baki鈥欌€
Nunfasawa hadizar tayi kafin tace 鈥樷€檞allahi bazata karbi dari biyar ba, kinsan cinikin nawa takeyi idan ta daura mata kwan nan kullum?鈥欌€
鈥樷€檔idai wallahi shawara nake baki, karkiga wai yanxu an shafe shekaru wallahi karamin kuskure zakiyi komai zai dawo kanki musamman idan dangin uban鈥︹€欌€
Saurin katseta hadizar tayi ta ta hanyar cewa 鈥樷€檇an allah Jamila kibar zancen nan,kinsan yanda na tsani maganar na,ni yanxu zan samu dubu goman?鈥欌€
Jamila ce ta kalli aminiyar tata kafin tace鈥欌€ gaskiya yanxu bazaki samu ba saidai nanda karshen wata idan anyi albashi,鈥欌€
Shuru hadizar tayi tana wani tunani kafin tace 鈥樷€檞allahi Jamila ina buqatar kudin nan da gaggawa, matar nan bata da kirki indai ba kai mata nayi ba bazata bani sarin kayan nan ba, gashi mun shiga karshen shekara, yanxu zakiji mutumin nan ya fara doka sallama daki daki, 鈥欌€
鈥樷€檛oh gaskia saidai kisan yanda zakiyi don wallahi nidai banida dubu goma yanxu, kema wallahi kinyi rashin tunani da kika sayar da gidanki, yan kudaden da kika dawo dasu da business kika fara dakin rufama kanki asiri, haka kikazo kika dunga kashesu kamar babu gobe, samun muhalli nakai a wannan lokaci ay ba karamin rufun asiri bane yanxu gashi wata nayi duk sai kibi ki rikice akan dubu hamsin a wannan tsinannan gidan,鈥欌€.
鈥樷€檋mm Jamila kinfa san dalilin sayar da gidan da nayi, shikennan zan hkura har zuwa lokacin, inkin karba albashi saiki bani鈥欌€ hadiza ta bata amsa
Daga nan wata hirar suka shiga sai wajen yamma liss jamila tayi masu sallama.
Sabeeha dai bata fito ba tana nan zaune a dakin nasu kusa da inna don tsoron haduwa take da maman nata.
Tunawa da wanke wanken dake jiranta yasa ta miqe jiki a mace ta tattara na cikin dakin kafin ta fuce, anan parlor ta tadda maman nata, fuskan nan nata a hade, kallo daya tayi ma sabeeha ta watsa mata wani kallo dayasa ta dauke idanunta cikin gaggawa kafin ta sunkuyar da kan nata.
鈥樷€檢o nan鈥欌€
Takowa sabeeha tayi ta karaso kafin ta durkusa gefe 鈥樷€檇an ubanki me kika tsaya yi kika dade?
Shuru sabeeha tayi jikinta na kyarma don duk a tunanin yau dukanta zatayi saboda yanda ta hade fuskarta sosai, 鈥樷€檏i amsa ni nace dan ubanki, me kika tsaya yi har kika kai wannan lokacin?鈥欌€
Bakinta da kyarma dan tsoro ta soma Magana, 鈥樷€檞allahi ban tsaya komai ba, sallah kawai na tsaya nayi bayan na sayar da kwan, shi..ne shi..ne鈥欌€
Sanin tana kakarewa wani sa鈥檌n cikin Magana musamman idan a tsorace take yasa hadiza saurin cewa 鈥樷€檚hine mai?鈥欌€
鈥樷€檞ata mata ce ta yarda Jakarta shine na tsinta na bata, dalilin daya tsayar dani kenan鈥欌€ ta kaarshe tana sheshekar kuka kasa kasa
鈥樷€檓atso nan鈥欌€ hadiza ta umarceta babu alamun wasa a tattare da ita
Rarrafawa tayi ta karaso dab da maman nata, tana kaarsowa ta damko gaban hijab dinta kamar zata shake mata wuya tace 鈥樷€檞allahi idan baki fada min abunda ya tsayar dake ba sainaci ubanki, ba karfe biyu kike dawowa ba meya tsaidake har akayi la鈥檃sar? Idan kikamin karya wallahi ranki sai yayi mumunan baci,wurin wa kika tsaya?鈥欌€
鈥樷€檔a rantse da allah mama ban tsaya ko鈥檌na ba, wallahi gaskia na fada maki, inbanda matar nan wallahi ban hadu da kowa ba, kingama har kudi ta bani鈥欌€
Sakinta hadiza tayi ganin tana kokarin zaro kudade, wani irin kallo ta jefe ta dashi bayan ta kalli kudin da take miqo mata hannunta har karkarwa yake saboda tashin hankali 鈥樷€檜ban waye ya baki wannan? Dama ke yar iska ce ban sani ba yaushe kika fara iskanci?鈥欌€
Saurin runtse idanu sabeeha tayi daman tasan haka zata kasan ce don tsoron hakan ne yasa ta boye kudin, 鈥樷€檌dan baki daina kukan munafurcin nan ba saina kashe ki anan wallahi, daman iskanci kika fara ban sani ba? Ke ko iskanci kike yi saiki bari na sani eh?鈥欌€
鈥樷€檞allahi mama bana iskanci, kinga hoton matar ma, acikin kudin na tsinta鈥欌€
Ta kaarshe tana miqa mata passport photograpy din, karba maman tayi kafin ta kurama picture din idanu, saida ta dauka kusan minti biyu babu ko kiftawa tana kallon hoton, nan take idanunta yayi jaa sosai ta maida kallonta ga sabeeha wani sabon tashin hankali ya wanzu a fuskarta
鈥樷€檌na kika samu wannan?鈥欌€
鈥樷€檃 cikin kudin da matar ta bani naga hoton,鈥欌€ ta amsata da gagagwa
鈥樷€檇ama chan kinsanta ne?鈥欌€
鈥樷€檞allahi ban santa ba, a masallaci ta yarda purse dinta shine na dauka na bata, shine tayi min godiya ta bani kudi鈥欌€
鈥樷€橞a nace karki sake kiyi mu鈥檃mala da mutane ba?uban waye yace maki idan aka yarda abu ana tsinta a baiwa mai shi,ko na taba ce maki idan kin dauki abu ki maidawa maishi inama ruwanki da abun wani? 鈥樷€ ta karashe tana daka mata uban tsawa dayasata qamewa kyam, tana masifar tsoron mama kamar ranta.
Zufar dake keto mata ta sharce kafin ta sake jero mata tambayoyi 鈥樷€檃 haka kika futa yau?, me matar tace maki?鈥欌€
鈥樷€檈h haka naje, godiya kawai tayi min鈥欌€ ta amsata
鈥樷€檛ashi kije鈥欌€
Sabeeha najin haka ta mike tsaye ta tattare kwanukan parlor wanda kawu yaci da wanda maman taci duka ta fita dasu.
Tana fita kuwa hadiza ta miqe tsaya, babu abunda ke kwance a fuskanta sai furgici da tashi hankali, hannunta har karkarwa yake saboda tsabar tashin hankali mara misali, hijab dinta dake gefe ta zura kafin ta fuce daga cikin parlor.
Koda ta fito batabi takan mutanen tsakar gidan ba ta fuce daga gidan gaba daya kamar zata tashi sama.
Hanyar gidan su Jamila ta nufa don yana dan nesa dasu, cikin mintuna qalilan ta karaso gidan, shima gidan haya ne saidai baikai nasu yawa ba don dakunan haya uku ne kawai a gidan.
Ko sallama batayi ba ta wuce bangaren Jamila, kamar daga sama kuwa Jamila ta ganta hankali atashe
鈥樷€檋adiza lafiya inace yanxu nabar gidanku ko nayi mantuwa ne?
Hannunta hadiza taja suka zauna akan kujera mai zaman mutun biyu kafin ta mika mata hoton da sabeeha ta bata.
Kallon hoton Jamila tayi tana tunanin ko lafiya don bata dago komai ba kwata kwata, muryar hadiza ce ta katseta 鈥樷€檔a shiga uku Jamila,duba kiga鈥欌€
鈥樷€檞ace wannan din鈥欌€ Jamila ta tambayeta
Kallonta hadiza tayi kafin tace 鈥樷€檏i duba da kyau mana鈥欌€
鈥樷€檏inga dan allah kimin bayani, wacece wannan din鈥欌€ Jamila ta karashe tana gyara zaman dan kwalin kanta
鈥樷€檅ata maki kama da yan gidan su ba?鈥欌€
zaro idanu Jamila tayi cikin kidima tace 鈥樷€檛oh fa, ina kika samu wannan to?鈥欌€ ta karashe tana kallon idanun Jamila, bata ma kaiga jin amsarta ba ta gane abunda take hasashe.
Cikin kidima itama ta miqe tsaye, 鈥樷€檔a shiga uku ni Jamila, kinga abunda nake fada maki ko?鈥欌€
Jan hannunta hadiza tayi ta zaunar da ita kafin tace 鈥樷€檇an allah Jamila ki bani shawara ya zanyi eh?鈥欌€
鈥樷€檃y saida na fada maki hadiza, wallahi da kanki zaki jefamu cikin masifa, sau nawa na fada maki ki daina barin yarinyar nan tana futa, wallahi idan dagin ubanta suka鈥..鈥欌€
Saurin toshe mata baki hadiza tayi idanunta yayi jaa sosai lokaci guda kuma bacin rai ya dabaibaiye fuskarta 鈥樷€檇an allah karki mana bakin fata, ay wallahi bazan taba barin haka ba ko bayan raina wallahi har abada, a yanxu dai yata ce ni kadai nina haifeta kaf duniya babu wanda ya wuce ni, kuma babu wanda ya isa ya rabani da ita tunda duniya ta shaida hakan nina tsugunna na haifeta kuma na rantse da wanda ke busa min rai bazan taba sakin ta ba, wannan alwashi ne dana dauka鈥欌€
Ganin haka yasa Jamila sauya zancen tace 鈥樷€檛oh yanxu ya zakiyi kennan鈥欌€
Nunfasawa hadiza tayi tana kumfar baki 鈥樷€檅ani kiga saida safe鈥欌€
Ta karashe ta nufi hanyar futa daga dakin jamila bayan ta karbi passport din, ko amsa gaisuwar yayan Jamila da suka dawo daga islamiyya batayi ba ta fuce daga gidan.
Koda ta fito nan take taji wani irin ciwon kai ya saukar mata, zuciyarta a cunkushe don nan take komai ya soma dawo mata, wannan baqin cikin, hatred dinnan da ta kwashe shekaru da dama tana dakonshi ya dawo mata fill a zuciyarta.
Take bakar zuciyarta ta dawo kamar sabuwa, babu abunda jikinta keyi sai karkarwa don tana da zafin zuciya sosai daman yanxu ne ta danyi sanyi saboda girma dayazo mata.
A wannan yanayi ta karaso gida lokacin har an soma kiraye kirayen sallar magrib, a tsakar gida bakin dakali ta tadda inna, ko kallon inda take batayi ba balle ta amsa tambayarta daga inda take.
Uwar daki ta shige ta zauna bakin gado tare da zare hijab din jikinta da zufa ta wanke shi tass, ta shafe wajen awa guda tana saka da warwarewa a cikin zuciyarta har akayi sallar isha鈥橧 kafin ta samu ta mike dakyar ta dauro alwala.
Sabeeha kuwa taga lokacin futarta da dawowarta don tana runfar girki ta daura masu abuncin dare tuwo da miyar kuka, mamakin maman nata take koda yaushe, baka taba iya contemplating mood dinta kwata kwata, yau she鈥檚 soft gobe kuma she鈥檚 opposite, maganganun da sukayi dazu ya tsaya mata arai sosai, ayau da ace iskanci take to fa babu wanda zai fara sani sai mamanta saboda ta santa ciki dabai, don ko kalar nunfashin da take futarwa mamanta ta sani ballatana kuma motsinta.
Ko tsoronta dake kunshe a cikin ranta bazaisa tayi iskancin bama, don a duk duniyan nan babu wadda ta zagaye rayuwarta kamar mahaifiyarta, duk wani motsinta akan mahaifiyarta, shiyasa tun bayan dawowar su Nigeria bata kara futa ba da sunan zuwa makaranta ba, gashi ta haneta mu鈥檃mala da kowa don ko qawa bata dashi, bata ma san menene qawance ba saboda she has a very dark experience lokacin tasowarta saboda halittarta, kowa is just a stranger to her hatta maqotansu da suke zaune gida daya mamanta bata yarda tayi mu鈥檃mala dasu ba kwata kwata, daga inna sai mamanta sai kawu wato qanin mamanta Kenan, shiyasa take nan kamar mai rayuwar qunci mara freedom.
Tun tasowarta da girmanta bata taba barinta ta zama socialize ba, bata taba barinta ta shiga cikin mutane ba, she hid her to the world gaba daya, tun bayan da ta fara zama budurwa, bata taba koda taka kofar gidan suba lokacin suna tsohon gidan su kafin yanayin yau da kullum yasa zaman nasu ya gagara a cikin gidan 鈥..
A lokacin da suka koma gidan haya ko tsakar gidansu bata futa kwata kwata, bata isa tayi koda dogon nunfashi ba saboda how highly strict with movement dinta da maman ta take,duk wani motsinta saida izinin mahaifiyarta abun yakai hatta kalar nunfashin da zata futar da duk motsin da zatayi saida izinin mahaifiyartaa, shin wannan so ne ko kuwa wani abun ne daban? Haka take yawan tambayar kanta koda yaushe.
Free page
7-8
MATAR TAJ(Destined with you馃┑馃)
鉂わ笍馃敟Romantic love story鉂わ笍馃敟
Written by QueenMarh
Da sunan Allah mai rahama mai Jinkai鈥
Gargadi!! Ban yarda wani ya chanza min koda kalma daya bane daga cikin littafin nan batare da amincewa ta ba, sannan littafin nan na kudi ne,idan kinaso ki biya Saina tura maki And lastly bazanyi free page da yawa ba.
I hope you鈥檒l enjoy this master piece guys, zaku tsinci tsaftattaciyar tsantsar soyayya aciki wannan littafi hade da cin amana da qiyyaya.
The suspense and the plot twist is a top notch馃檭馃檭
Enjoy!!!!!
Matar Taj (destined with you馃┑馃)