← Book details Matar Taj Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 5 OF 20

Chapter 7-8

Matar Taj Part 1 Complete Hausa Novel · about 17 min read

Washe gari da asuba ta tashi as鈥檜sual kamar kullum, a parlor ta kwana saboda kawu bai kwana a gidan ba, daman yawan ci asabar da lahadi ne kawai yake kwana a gidan, sauran kwanakin kuma achan tasha yake yi saboda sana鈥檃rshi ta tukin motar haya, kano to Abuja line.
Saida ta fara yin sallar asuba kafin ta fara gyaran parlorn nasu inda ta tattara katifar, da dan qyallen zanin da take shimfidawa a kan katifar don katifar soso ne kawai ba bu komai a jikin katifar,sai kuma hijab din da take luluba dashi dayan kuma dashi take sallah.
Ragowar kayan wanke wanken da sukaci abunci dashi ta kwashe ta fita dasu don wankewa.
Gaba daya gidan basu tashi ba sai mazajensu dake futa aiki,wannan yasa take futowa tayi duk wasu ayyukanta da wurwuri kafin sauran matan gidan su fito, don ko dibar ruwan rijiyar gidan ma layi sukeyi.

Zama tayi ta soma yin wanke wanke cikin natsuwa ga sanyi asuba dake busawa, sanye take da hijab din datayi sallah dashi, hijab dai koda yaushe bata rabo dashi, kuma yana nan yanda take sakawa ta rufe bakinta dashi.
Saida ta gama wanke wanken tass ragowar omon kuma ta wanke dayan hijab dinta dashi don gaba daya guda biyun nan ne kawai take dashi kuma shi take sawa koda yaushe shiya duk suka kode saboda wanki dukda wanki ma wani san鈥檌n babu omo take yi saidai ta tsalma cikin ruwa ta dauraye shi.

Tana gamawa ta shanya kan qauren langa langan da take shanya wajen, lokacin har matan sun soma futowa.
Wanke toilet din ta fara yi kafin ta koma dakin nasu, da sallama ta shiga, inna nata sharbar barcinta, mama kuma na gefenta a zaune, da alamu bata dadw da tashi ba, zaman jirata daman takeyi don bata shiga toilet din saita wanke kafin tayi amfani dashi.

Cikin ladabi da biyayya ta tsugunna, har kasa ta soma gaisheta 鈥樷€檌na kwana mama, an wanke bandaki鈥欌€

Kamar koda yaushe bata fiya amsa ta ba, saidai kawai tayi gyaran murya, yau dinma ko gyaran muryar batayi mata, ganin haka yasa ta sake maimaita abunda tace, sai a lokacin maman ta dago ta kalleta kafin tace 鈥樷€檔aji鈥欌€ jikinta ne yayi sanyi don duk a tunaninta har yanxu fushi take da ita, fushinta kuwa ba karamin tashin hankali bane a wajenta.

Sum sum ta fuce daga dakin don daura abunda zasu karya dashi, tuwon jiya ta dumama ta juye a kular, lokacin mama harta futo tay wanka ta koma ciki.
Daga baya ma saiga inna ta futo itama,dakyar take tafiya saboda qibar da take dashi sosai, wani sa鈥檌n ma saboda qibarta cikin dare bata iya futa yin futsari saidai tayi a poo saboda tana da saurin sakin mara saboda ciwon sugar da take dashi.

Dakin ta sake komawa da kulolin tuwon data dumama,tana shiga ta ajiye bayan sun gaisa da inna, kafin ta wuce parlor ta zauna taci nata wanda ta zuba ma kanta.

Bayan yan mintuna qalilan ta koma daki ta kwashe kwanukan da suka gama ci kafin ta fuce dasu.


Kallon inna hadiza tayi kafin ta danyi gyaran murya, 鈥樷€檌nna daga yau sabeeha bzata kara futa tallan nan ba鈥欌€

Wani irin kallo inna tayi mata tana kokarin yin sakacen hakori kafin tace 鈥樷€檚aboda me Kenan?鈥欌€
鈥樷€檌nna ni na haifi yarinyar nan kuma nike da iko da ita, bana son tallan nan saboda haka bazata kara futa yin wani tallah ba ko aike ma karki sake barin ta taje, nitun usuli na nuna maki bana so bansan meysa ki鈥.鈥欌€
Saurin katseta inna tayi

鈥樷€檌ko sai allah, yau ni hadiza kike cewa ke kika haifi yarki?shin idan taje tallan nan ba rufin asirin mu bane?, kuma idan taje tayo tallan nan ay duk rufin asirin mu ne tunda koba komai dai zamu samu nacin yau harda dumame, ke wai hadiza na kasa gane maki, wannan tsawalawan da kike yi akan yarinyar nan na menene ke a ganin ki wannan tarbiyya ce kike mata?鈥欌€

鈥樷€檔i ba wannan maganar nake maki ba inna, inma don ribar da kike samu ne zan dunga baki dubu duk sati鈥欌€
Shuru kawai inna tayi bata sake ce mata komai ba, don talla kam saifa ta tura ta.

Haka ta karashe shirinta ta fuce daga gidan zuwa gidan matar da take ma aikin abunci, matar babbar event planner ce a cikin garin abuja, sannan tana harkar abincin gidan buki da duk wasu events, da kyar hadiza ta samu matar ta dauketa aiki, inda take bata dubu talatin duk wata.
Yau Friday, yawanci ayuukan ranar sunfi yawa saboda akwai orders din abunci da yawa.


Karfe sha daya daidai kuwa inna ta sata dora dahuwar kwai, tana gamawa ta zuba a roba, saida inna ta kora mata kashedin dawowa karfe daya daya daidai kafin ta fuce, tunda ta fita gabanta ke faduwa babu dalili.

Bata kai karfe dayan bama ta sayar da duka kwan kafin ta dawo gida,
ba karamin dadi inna taji ba kuwa don haka ta daura damara don bata ga dalilin da zaisa ace wai baza a tura ta tallan ba yanda suke fama da talaucin nan, ita dai ba yar gwal bace da za ace ta futa nema ba.
Saida yanma tayi likis hadiza ta dawo a gajiye, gajiyar data kwaso ma baisata ta tambayi inna ko ta bar sabeeha ta futa yau ba don tasan inna akwai taurin kai.

Haka suka shafe sati guda, inda hadiza na futa inna zata daurama sabeeha kwan nan, kafin ta dawo, akwai ranar da sabeeha ta futa da kwan bakin titi kamar kullum, da mamaki Jamila wadda ke shirin tafiya wajen aikinta ta ganta, koda ta ganta ita sabeehan bata ganta ba.
Jamila tayi mamakin ganinta sosai, don batayi tunanin hadiza zata barta ta sake futa ba.
Saida ta dawo daga aiki ta wuce gidan hadizan ko uniform din jikinta bata tube ba,tana zuwa gidan ta samu hadiza a uwar daki, inna kuma tana tsakar gida tana hira da maman chidi, sabeeha kuwa tana bakin murhu ta daura sanwar dare.

Da sallama Jamila ta shiga dakin, a zaune ta tadda hadiza, ganin ta tsaya a bakin kofa yasa hadiza cewa 鈥樷€檏araso mana jamila鈥欌€
Zama Jamila tayi tana fuskantar kafin ta soma Magana 鈥樷€檞ai ni hadiza maisa yanxu kikayi sanyi ne sosai?鈥欌€

鈥樷€檓e kika gani yasa kikace haka?鈥欌€
Hadizar ta tambayeta tana kallonta da mamaki.
鈥樷€檋mm babu komai daxu sai naga sabeeha a bakin titi gaban wata katuwar mota ashe baki hana ta tallan ba allah dai ya kauda bacin rana鈥欌€

A razane hadiza ta kalleta, 鈥樷€檅an gane ba, wace sabeehar ba鈥欌€
Wani irin kallo Jamila ta mata irin kinma raina ma kanki hankali.
鈥樷€檃kwai wata sabeehan ne bayan wadda kika san nake magana a kanta,鈥欌€

鈥樷€檌nnalillahi, wallahi Jamila saida na fada ma inna karta kara bata tallan kwan nan鈥欌€
Miqewa Jamila tayi tare da saba Jakarta a hannu 鈥樷€檚hikenan ay, idan kare na yawo zabo ma na yawo wata rana sai sun hadu, yanxu ya kamata tun wuri kisan abunyi, shawara dai dayace na baki, akaro na biyu ni kinga tafiya ta鈥欌€,
Tana kaiwa nan tayi fucewarta, tun bayan tafiyar Jamila kasa sukuni hadiza tayi, yanda kasan Jamila rura mata wutar tashin hankali tayi, haka kawai ta kasa nutsuwa, washe gari haka sukayi kacha kacha da inna kamar ba mahaifiyarta, itama sabeehar bata barta ba don saida ta daketa sosai kamar zatayi mata illa, duk dan bata fada mata kan cewa inna ta cigaba da daura mata talla ba, ita kuwa baiwar allah bata ma san ta hana inna daura mata tallan ba.
Ranar dai sabeeha taga sauyi sosai tattare da uwar tata, sauyin da tun bayan dawowar su rabon data ganshi, nan take tsoronta ya sake ninkuwa akan na da, abubuwan da suka gabata shekarun baya suka soma dawo mata, don a lokacin ne hadiza ke displine dinta acewarta don wahala dai tasha wahala both emotionally and physically wajen mahaifiyar tata tun kafin ta mallaki hankalinta, sai ayanxu asalin maman nata ya dawo, wato hadiza nada zafi sosai, bata da sauqi, she鈥檚 not soft at all, wata iriyar zuciya ce da ita, ta raini zuciyar ta tsahon shekaru da dama da hatred.


Satin sabeeha daya a gida ba tare da taje tallan ba, inna ma dai bata sake bata tallan kwan ba saboda yanda hadizar ta dauko da zafi zafi sosai, bayan wannan ma yanxu innar tayi laushi sosai saboda yanayin rashin lafiyarta dake neman dawo wa.

Akwai ranar da inna ta tashi da tsananin rashin lafiya, gaba daya jikinta ya sage, ranar daga sabeeha sai inna agidan, lokacin da abun ya tsananta sabeeha na tsakar gida tana wankin kayan maman nata, saida ta gama kafin ta daura musu abunci.
Duk wannan hidimar data dunga yi bata shiga daki ba, saboda ayyuka da suka sha mata kai.
Hadiza kuwa ranar taje aiki,don ranar juma鈥檃 ce kuma akwai ayyuka da yawa da zasuyi saboda abuncin sadaka da sukeyi duk sati da ake biyansu sunayi.
Tunda suka fara aikin nan basu suka zauna ba sai wajen karfe uku na rana, dama a daidai wannan lokacin ake zuwa daukan abuncin sadakar鈥.

Karfe hudu daidai ta dawo gidan gaba dayanta kana ganin ta kamar susutacciya, direct dakinsu ta nufa hankali atashe, a kwance ta tadda inna, bata ma bi takan innar ba don duk a tunaninta barci take,cikin sip dinsu ta bude tare da dage kayayyakinta da suke a ninke, chan kasa ta zura hannunta ta zaro wani tsohon hoto, yan mata ne guda uku cikin hoto daga gefe kuma sai wani sauri, ta dan dade sosai tana kallon hoton kafin ta maida hoton cikin drawer, ko tsayawa rufe drawer ma batayi ba ta futa daga dakin.

Bata wani dade ba sai gata ta dawo kuma, this time around tadan samu natsuwa saboda maganganun da sukayi da Jamila.
Ko takan sabeeha batabi ba da ke gaisheta ta wuce daki, sai alokacin ta maida dubanta ga inna dake kwance yashar kamar gawa ga wani kumfa kumfa dake futowa daga bakinta har ya soma bushe, hankali atashe hadiza ta karaso gaban gado kafin ta soma cewa 鈥樷€檌nna, inna, wannan kumfar fa innalillahi wa inna ialihi rajiun鈥欌€
Idanun innar a bude ga hawayen dake saukowa bakinta kuma ya soma karkarcewa gaba daya ta qame gatanan dai tana jin abunda hadizar ke fada saidai ta kasa yin komai, takasa motsawa komai na jikinta ya sandare.

鈥樷€檌nna!!! Innalillahi wa inna ilaihi rajiun na shiga uku ni hadiza鈥欌€ hadiza ta doka ihu hankali atashe, sabeeha data shugo da kwanan abuncin su tana jiyo ihun maman nata yasa ta ajiye abuncin anan dakin ta wuce cikin uwar daki, itama gaba daya hankalinta ya gama tashi sosai tana tsaye baki kofar shugowa dakin, juyowa hadiza tayi ta kalleta hankali a tashe ta soma Magana .
鈥樷€檏e tafi gidan Jamila ki kirawota鈥欌€
Cikin saurin sabeeha ta futa daman da hijab dinta a jikinta, gidan Jamila ta wuce direct dukda batasan gidan ba saida tayi tambaya don bata taba zuwa gidan ba, ana nuna mata gidan kuwa ta shiga da sallama, duk ta burkice, Jamila na ganin shugowarta ta saki baki don mamaki, 鈥樷€檌na wuni鈥欌€ sabeeha ta gaisheta,
鈥樷€檒afiya dai?鈥欌€
鈥樷€檓ama ce tace nazo na kiraki, in鈥nna ce鈥欌€
Jamila najin haka ta zari hijab dinta dake baki kauren kofa kafin ta fuce sabeeha na biye da ita a baya.
Gidan suka shiga a tare, matan gidan har sun fifito saboda ihun hadiza da suka dunga ji tana faman kiran 鈥樷€檌nna ki tashi karki mutu, ki rufan asiri鈥欌€

Dakin Jamila ta shiga, inda ta tarar da hadiza na faman jijiga inna, har lokacin idanunta a bude suke tarr, karasowa Jamila tayi don dubata, tabbas abinda tayi hasashe ne ya tabbata, ita ma gaba daya lokaci guda hankalinta ya tashi
鈥樷€檋adiza mu kaita asibiti yanxu kafin abun ya tsananta鈥欌€
Tana kaiwa nan suka fara kokarin daukan inna, kasa daukanta sukayi saida Jamila ta fita, allah yao baban chidi na nan, shine ya shugo ya goyo innar, hadiza dai babu abunda take sai kuka, haka suka fito gaba dayansu har waje, ga anguwar a chunkushe take babu motoci, haka suka fito bakin titi hankali a tashe.
Daidai nan motar taxi din kawu ta shawo kwana,daman ya dawo ne yaci abunci ya koma kan aiki, hadiza na ganinshi ta tsaidashi, bata ma tsaya yi mashi bayani ba suka shiga gaba daya cikin taxi din yaja suka wuce wani asibiti dake nan duten habujan.

Asibitin government ne saidai kuma yaji jiki sosai, don kwata kwata babu kayan aiki, haka suka dunguma da inna cikin asibitin.
Da kyar aka samu likita guda daya ya fara dubata, tashin farko yace masu wannan matsalarta tafi karfin asibitin da basu da ayyukan da zasuyi mata taimakon gaggawa, don kamar ta samu paralyze,jin wannan kalma ta daga ma hadiza hankali sosai, haka suka sake dungumar ta suka wuce cikin garin Abuja.

Daidai federal hospital suka tsaya, Jamila ce tayi masu jagora inda kawu ya goyo inna dake nan jikinta babu progress ko kadan saima idanunta daya soma rufewa alamun shima yana gab da qafewa.

Taimakon gaggawa aka fara yi ma inna inda manyan likitoci suka shiga da ita wani daki emergency, sun dauka kusan awa guda suna kokarin gano daga inda matsalar ta fara, saida sukayi mata wata allura wadda zatayi stabilizing system dinta kafin su fara yi mata test.

Bayan awa gudan nan saiga likita ya futo, nan ya soma masu bayani, inna na dauke da liver cancer wanda taci taci ta sosai, wanda dole sai an cire mata wannan hantar don ta lalace, na biyu kuma tana dauke da diabetes wanda shima yayi mata tsanani.
Cikin kidima hadiza ta soma kuka, saida Jamila ta bata baki kafin tayi shuru, nan doctor ya cigaba da yi masu bayani.
鈥樷€檏amar yanda nace, dole sai an cire mata wannan hantar zata rayu inba haka ba zata iya mutuwa Indai ta kara kwanaki talatin ba tare da an cire ba, don cancer ce kuma spreading takeyi.鈥欌€

鈥樷€檒ikita nawa ne kudin aikin?鈥欌€ jamila tayi saurin tambayarsa
鈥樷€檇ubu dari takwas ne鈥欌€
Dafe kirji hadiza tayi tsabar kidima, ina zata samu dubu dari takwas yanxu, matarda ko dubu dari da zata ce nata ne na kanta bata dashi.

Tsabar tashin hankali zaman dirshen tayi a wajen sai Jamila c eke bata baki.
Ranar dai sun kwana cikin tashin hankali, ga kudin asibiti da kudin gado da aka kira masu kusan dubu talatin, a rana guda Kenan fah.

Kwanan inna uku ta farfado,gaba daya jikinta yanda suka kawo haka yake, abunci ma saita roba ake dura mata,ga chachar kudin asibiti, don tsakanin kwana ukun nan sun kashe wajen dubu tamanin.
Maganar kudin aiki kuwa babu inda zasuje su samu wannan kudin, tashin hankalin hadiza Kenan, ranar da kawu ya zauna da innar hadiza ta samu ta koma gida don ta dan huta don ita ke zama da ita tsawon kwanakin.
Sabeeha dai kullum tana zaune a gida tana jimamin rashin lafiyar inna don kwata kwata mamanta bata bata fuskar zuwa asibitin bama.

*


Da sallama hadiza ta shugo gidan Jamila, tana zaune a parlor tana cin taliya, ganin yanayin hadiza yasa ta ajiye taliyar gefe, ta miqe ta wank hannunta kafin ta dawo parlor.

鈥樷€檇uk kin rame wallah, ki dai na sama kanki damuwa, insha allah zamu samu mafita.
鈥樷€檍amila wace mafitar Kenan? Wata guda fa akace? Ina zan samu wannan uban kudaden?
Nunfasawa Jamila tayi kafin ta soma Magana cikin hikima 鈥樷€檌nada mafita guda daya, koba komai zatayi maki maganin matsalolinki guda biyu a duniyar nan鈥欌€
Gyara zama hadiza tayi tana sauraronta, haka kawai sai taji sanyi aranta.
鈥樷€檌n kin tuna kwanaki na baki wata shawara ko?, mezai hana ki amince kawai ni zansan yanda zanyi ayi chuku chukun da akeyi鈥欌€

Shuru hadiza tayi tana nazarin shawarar data bata, 鈥樷€檛oh ya zamuyi kenan?鈥欌€

鈥樷€檏inga baban jamilu (mijinta kenan) yana harkar agency din matafiya, yasan komai game da abubuwan daya shafi matafiya da yanda wassun su suke chuku chuku ta hanyar shiga kasashe waje daban daban, akwai wata agency da take kai yara aikatau zuwa kasashe daban daban a fadin duniya har sai wanda kika zaba,鈥欌€
Dan tsagaitawa tayi don karantar yanda hadizar ta bata attention sosai.
鈥樷€檋adiza mai zai hana ki turata aikatau itama, kinga kudin da ake samu wallahi da yawa ba kadan bane, don yana kaiwa wajen dubu dari uku ko yafi haka ma, duk wata, idan har kin amince zan tambayr maki baban jamilu saiki zabi kasar da sukafi badawa da yawa ki tura ta kawai, kinga kin huta da damuwar ganinta a gabanki, sannan kuma zuwanta chan zai magance maki matsalar inna da matsalar mu, ko ba komai dai tabar maganar dangin ubanta ta kau, kije kiyi tunani akai 鈥欌€

Nunfasawa hadiza tayi kafin ta dubi Jamila, 鈥樷€檍amila ay babu maganar zuwa nayi tunani, na amince kawai, ki mashi maganar, aturata da gaggawa, bamuda lokaci鈥欌€

Wani irin murmushi Jamila tayi kafin tace 鈥樷€檡anxu kika dauko hanya, karki damu ay tunda kin amunce Magana ta kare, zansa yayi mata komai, abunma zaizo da sauqi tunda an taba mata passport, idan na mashi bayani zan aiko ki bada tsohon passport dinta wani sabo za ayi mata kawai yanxu鈥欌€
Wani irin sanyi hadiza taji jin wannan shawarar da Jamila ta bata, haka ta koma gida tana mai jin sauqin abunda ke ranta.

Bayan mijin Jamila ya dawo nan ta mashi bayani, da murnarshi kuwa ya amince wajen taimaka masu don daman su kamar masinjoji ne a harkar, idan ka kawo mutane zaka samu kaima naka kason, wannan yasa yaji dadi shima,nan ya buqaci ta karbo passport din yarinyar kawai don shi za a buqata, da daddare kuwa Jamila ta aika hadiza ta bada passport din.

Cikin kwana biyu mijin Jamila y agama komai, daga kan passport dama a kungiya za a kaisu, ana tara yara kamar guda sha biyar haka sai a tura su, acikin kudin aikinsu za a zari kudin kawosu da za ayi sannan agency zata zari nata kason sauran kuma sai a turo ma iyayen yara.
Bayanin daya shafi inda za a kaita da aikin da zatayi duk bai shafi hadiza ba kawai tunda taji mijin Jamila yace agency din suna bada albashi kusan dubu dari uku wani sa鈥檌n ma yana fin haka, hakan yasa ta amince kawai.

Washe gari da safe kuwa da asubah hadiza ta tashe ta baiwar allah bata ma zan meke faruwa ba., 鈥樷€檔a baki minti biyar jekiyi wanka ki futo kisa kayan nan鈥欌€ hadiza ta bata umarni tana mai yi mata nuni da wani koren kaya da hijab.
Saida ta gaisheta kafin ta fuce tsakar gida cikin sauri, duk sanyin asubar nan haka ta debi ruwa a rijiya tayi wanka, ko tsayawa dauraye bandakin batayi.
Tana gamawa ta maida hijab dinta tundaga bandakin kafin ta wuce cikin daki, kayan da maman nata ta bata ta fara saka wa, dakin kwata kwata babu haske dim dim, hakan yasa na kasa ganin yanayin jikinta, yawanci itadai koda yaushe tana cikin hijabi,

Tana gamawa ta ganin maman nata bata dakin yasa wuce tsakar gida don daura dumamen da za akai asibiti.
Bata ma kaiga dora tukunyar ba maman nata ta futo daga daki, sanye da hijab.

鈥樷€檃jiye tukunyar nan kizo mu wuce鈥欌€
Ajiye tukunyar tayi ta nufi inda maman nata take, daman already da silifas dinta a kafarta.

Lokacin da suka fito haske ya bayyana don gari ya soma washe wa,
Gidan Jamila suka wuce direct, da sallama suka shiga,Jamila ce a tsakar gidan tana hidimar abuncin yan makarnta.

Sama sama suka gaisa da hadiza kafin su wuce cikin daki, wasu yan maganganu sukayi sabeeha dai na daga tsaye ta raqube a gefe har suka fito, kallon inda take hadizar tayi kafin tace 鈥樷€檏i zauna anan鈥欌€
Cikin girmamawa ta amsa da toh kafin hadiza ta fuce.

Anan tsakar gidan ta samu waje ta zauna, har gari ya washe sosai, karfe takwas daidai mijin Jamila ya futo tare da jamilar suka wuce.

Sabeeha dai binsu take da idanu duk ta soma tsorota har suka zo wani waje inda aka rubuta Aj agency service, cikin wajen suka shiga, wajen cike yake da mutane ga wasu yan mata da maza kamar ta harda wasu manyan mata dukkansu da irin kayan jikin da mamanta ta bata,idanu ta soma zaro wa tana tunanin ko menene dalilin kawo ta da akayi nan, mijin Jamila shima anan yake aiki so yana zuwa already yayi masu bayani daman sunsan da zuwanta, nan wani mutumi yayi mata nuni da inda sauran yaran suke don ta zauna.
Shikuma mijin Jamila da ita jamilar suka shiga wani office,wani mutumi ne a zaune, gaisawa suka farayi kafin mijin Jamila ya soma Magana 鈥樷€檃lhaji mun taho da yarinyar, zaku iya ajiyeta na shekara goma ma idan kunaso babu matsala saidai kudin da aka bamu ne, shine nace tunda ita ba鈥檃 yanke mata lokacin dawowa ba ko za a kara mana鈥欌€

鈥樷€檏aifa masinja kasan yanayin aikin nan, dubu dari fa muka baka, gaskia bazan iya kara wani abunba鈥欌€

Jamila ce tayi saurin tsomo baki 鈥樷€檋aba alhajin allah, mu fa bamuda matsala, ce maka akayi ku riketa, idan ma shekaru dari zatayi tana aiki karkashin ku mu bamuda matsala, ko dan wannan ya kamata a kara mana wani abun mana鈥欌€

鈥樷€檃h toh mu gaba ta kaimu, zan kara maku dubu goma鈥欌€
Godiya sukayi mashi kafin ya irga kudaden ya basu suka fuce daga wajen.

Samun waje tayi daga gefe chan ta zauna gaba daya ta fara furgicewa da tsoro, don bata taba shiga cikin hayaniyar mutane haka ba.
Su kuwa Jamila da mijinta suna amsar kudin su suka kara gaba abunsu suka barta tana zare idanu.

Tana nan zaune cikin yaran har wajen karfe goma kafin a fiddo dasu waje inda akayi parking wata katuwar bus.
Daga nan aka basu umarnin shiga cikin bus din, sai a lokacin sabeeha ta tabbatar da something is wrong? Ina ne nan ta tambayi kanta, ina za a kaita, nan take ta soma hawaye.
Har suka shiga cikin bus din bata bar hawaye ba.

Shin ina za akai sabeeha?
Ku biyoni don sanin wata duniyar sabeeha zata shiga, Siyar da ita su Jamila sukayi? Da sanin mahaifiyarta kuma? Ko kuwa Da gaske aikatau din za a kaita wata kasar daban? Inda bata san kowa ba? Gashi bata iya mu鈥檃mala da mutane ba.


Matar Taj (destined with you馃┑馃)
Free page
Chapter 5 · 0% Book details