← Book details Mar'atussaliha Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 12

Sashe 9

Mar'atussaliha Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiko Habib Yana ajiye su dad ya juya yanufi gidan su munir ,Yana zuwa adakinsa yasameshi a kwance Yana danna computer, dasallama dauke a bakinsa yashiga ya zauna a gefansa, yace "barka da wannan lokacin abokina,"barkadai" yafada atakaice, Habib ne ta kara kallonshi yace "wai munir bangane maka ba kwana biyun nan,gaba kidaya duk ka canza meyake faruwa ne?"yanzufa ko gurina bakason zuwa ,Kuma nasan kaji batan saliha Amma ko kazo katayani jaje Wai meye hakane,yanzuma nazo kana wani batarai" kallonsa kawai munir yayi ya kaudakai yace"wani lokacin kasan ni banason kallon mugayen mutane masu bakin hali" au munir kenan nikake nufi mugu me bakin hali" murmushi munir yayi yace"ni kaji nace Kai kawai dai n'a fadi magana tane ko dai ka tsargu?" A,a ni bance maka ba kawai dai Naga ni kake kallo kake fadar maganar Kane shiyasa nazata da ni kake"a,a ni bada Kai nake ba,n'a Isa nace maka Kai mugune,ay idan kewawan hakayene asameka Habib,domin Dani,unka ba duk mazane suke da irunsu ba, Kai dai Allah ya baka ko mutuwa Kai za,ayi maka kekkewan zato"kukukut Habib yahadiyi yawu me dumi tare da saka hannu ya goge zufar data karyo masa,sannan ya runtse ido tare da tunano yadda Babu tausayi Babu imani ya kumawa baiwar Allah wuka aciki,Kai inama,ace yadda munir yakemasa kekkewan zato Haka halinsa yake,ko Babu komai yasan ya more rayuwa cikin jindadi "Yana tsaka da fadawa duniyar tunani munir ya dan tabashiyace" haba Habib ta Ina baka labari kana tafiya tunani, nikasan ma wani labari danajiyo dazu agidan redio" a,a sai kafada Habib yafada yace inajinka" uhm Wai wani mutumine kowa Yana masa kallon me nutsuwa da hankali da Imani, ashe ashe ba Haka yakeba sumu,sumu mugun ice be, Yana da wasu mugayan halaye irinna dabbobi, kanaji ko ayanzu zancen danake fadamaka Wai ya kashe matarsa ya dorawa megadin gidansa sharri akan shiya batar da ita Nan ko ba,ason kasheta yayiba, to dai har yanzu anan ana bincike akai, ance Nan da wata biyu za,a karasa cigaban labarin domin aji makomar Dan,iskar ,wato zurwaja haini kenan"murmushin karfin hali Habib ya kakaro tare da hadiye wani mugun yawu agigice yace" munir dan Allah inakasamo wannan labarin dan Allah kafadamin yanzu"munir ne ta zubamasa ido Yana kallonsa kamar me nazarin wani abu daga bisani kuma yace, Habib kanutsu mené zaka samu kanka akan abin da bakai ka aykata ba,bafa kaine mutumin ba kawai nabaka labari ne,to mené n'a damuwa" dan sosa keya Habib yayi yace am um dama kawai na tausaya masa ne,tab to amma ko wanene wannan yacika azzalumi "uhm hakane Allah dai ya tona asirinsa ,munir ya fada, shiru Habib yayi bece komai ba, munir kuwa ganin Haka yasa yace" Bross banjifa kace ameen ba" am um Ah ay nafada azuciyata Ameen Allah ya tona ashirin Dan banza,am kaga munir tafiya zanyi ina da wani ayki n'a ugila"to shirrar kenan gaskiya ni van yarda ba sai da Shira ta dakko dadi zakace zaka tafi ni dai ka zauna" murmushi kawai Habib yayi ya dau Kee dinsa ya nufi hanyar fita daga dakin,yanaji munir Yana cewa sai kadawo Allah ya kiyaye hanya kakula da tuki fa kada kayi accident"becemasa komai ba ya fuce ya shuga motarsa ya ja ya fuce daga gidan a guje....

______________________________________________________________MEDUGURI_________________

Tun da saliha ta bude idonta Babu abin da take gani sai duhu,Hatta hannayenta idan ta dagasu duhu take gani bata ganinsu,hakanne yasa ta fara addu,a acikin zuciyarta duk wadda tazo bakinta yi takeyi bata tasayawa,ganin yadda take addu,a Babu abin da ya sauya daga cikin daki saima karuwa da duhun yake dadayi,hakan yasa saliha ta soma tunanin ko ta mutune ,wannan duhun da take gani kabarintane a Haka , innalillahi wa'inna ilaihirraju,Mena aykata ,kodai azaftar da Habib danayine ,koba komai mijinane kodai fushin Mala,ikune ke ayki akaine nashiga uku,Allah yasa dai ba gaskiya bane ba, nashiga uku ni saliha inanake nan,runte idon ta tayi tasake budewa nan danan abubuwan da suka faru suka shiga da wo mata filla filla,musamman yadda take kallon Habib ido cikin ido Yana sokamata wuka acikin cikinta ,waiya zubillahi Habib me nayi maka. Allah sarki baiwar Allah da tarasa abin da zatayi kawai sai ta fashe da kuka hawaye masu dumi da azaba sun bin kuncinta kamar ruwa, kuka tacigaba dayi sosai har sai da tayi me isarta sannan tayi shiru da kukan tace"ya allah nasan duk inda kake Kana kallo Kana ganin yadda bawan ka ya wulakanta ni ya tozarta rayuwata da ta "yan,uwana ya lalata komai da yazamana shi mallakinane sannan yake kokarin kasheni "Allah Ina rokonka daka bani tsawan Rai da lafiya domin na ga yadda zaka ramamin abin da ya aykatamin Allah inarokonka ka bani aron rai domin naga karshen Habib ya ubangiji kada kadaukemin numfashina harsai Naga yadda karshen bawannan naka zai kasance, tana Gama fadar hakan tasaki murmushi ,sannan tace"Habib kenan if Allah see yes no body can see know....

Hasken fitila tagani Yana haskawa acikin dakin ,cikin sauri ta dago domin ganin wake nufo inda take,tana daga idonta wazata gani,wata kekkewar budurwace wadda bazata huce shekara 25/27 tana karaso ta Tana sakar mata murmushi,dafarko saliha sai da ta tsorata da ganinta daga bisani kuma sai ta dake data tuna tana da Allah ,Nan take tashiga yin addu,a tana furtawa dasauri da sauri ,matar kuwa Dada tunkaro ta take tana na cigaba da yimata murmushin,sai da ta karaso daf da gadon da saliha take ta tsaya a daidai kanta tace" ki kwantar da hankalinki sunana, Amina "ki yar da Dani bazan cutar da ke ba inason ki bani hadin Kai duk abin da nace kiyishi, kinjini "dasauri saliha ta daga kanta tare da cewa to, a hankula Amina tasaka hannunta ta kama hannun saliha, suka shiga tafiya har suka karaso bakin kofar fita, lokacin da saliha ta saka kafarta a bakin kofar jitai kanta Yana juyawa dasauri da sauri kamar hajijiya,Amina da tafahimci haka tayi sauri tashiga tofa mata addu,a da wani kullun ruwa dayake hannunta, sannan saliha ta dawo hayyacinta suka fito, suna fitowa doctor faruq yace"yawa Aminatu agaskiya na jinjina Miki kinyi kokari ,yanzu zaki iya tafiya kingama aykinki na yau saura gobe Kuma, Amina ce ta bushe da wata mahaukaciyar dariya sannan tace,ku Kuna da hankali kuwa ,ni Aminatu zaku ce zaku hada baki dani kucuci baiwar Allah batajiba bata gani ba ,to muddum Ina Raye sai na ceci wannan yarinyar",tafara tare da Kara damke hannun saliha.

Daya daga cikin "yan daban gurin ne ya taso a hargitse yayo kan Amina da wata doguwar wuka a hannunsa yace,ke muzakiyiwa taurin kai" yan zunnan nan zan hullaki inda ba,a dawowa ,ya daga wukar zai caka mata" yaji anyiwa wukar kekkewan ruko,yaja yaja yakasa kwacewa ,take ya juyo Dan ganin wanene,Yana juyowa suka hada ido da saliha wadda idon ta yakada yayi jajur kamar garwashi Nan danan fuskarta ta canza kala tazama wata iriya idan ka ga saliha wannan lokacin abin sai ya baka tsoro" afusace", ta ja wukar Nan danan ta fede masa hannu ta wukar sannan tayi wulli dashi gefe yaje ya daki wata bishiyar tsamiya ,dayan ne yatashi da gudu zai gudu,cikin zafin nama saliha ta damkoshi tare dacewa " ni zaku kashe akanme "menayi muku!" Ta shararamasa maruka har hudu wan da yayi sana diyyar murdewar kansa gefe daya" amma duk da Haka saliha bata barshiba tacegaba da marinshi tana cewa me tayi musu,tana tsaka da Haka ta hango doctor faruq har yayi nisa ya gudu tun tuni,wayar tashima a gurin ya wurgar da ita Sabi da tsabar tashin hankalin da yagani, jikin saliha harrawa take ta kama hanya tanufi inda doctor yayi "sai dai kashe tana daga kafarta ta fadi a gurin sumammiya ,Nan take Amina ta durkusa tashiga Kiran sunan ta Amma shiru, da sauri ta dakko wayarta a aljihun wandonta tashiga contact ,ta danna wata number wadda akayi seven da my best friend ,sannan tashiga Kiran number bugu daya ya daga,tare da cewa" my best da matsala fa" bakinsa harrawa yake wajen cewa matsalar me fa,meya faru da,ita ?" Ka kwantar da hankalin ka kawai dai ta tada aljanune kasan tana da dinki acikinta yanzu ansamu matsala dinkin ya bude kana kusane ka karaso, pleace my best ka nutsu dan Allah,ka debo Kayan ayki cikin nutsuwa kada ka manta abu ko daya ,yanzu Zan dauketa na huce da ita gida kasamemu acan" okay thanks ya fada tare da katse wayar,yashiga debo kayayyakin ayki,daganan kuma yafito ya shiga mota ya Sona tuki,abin takaicin shine ban gane wanene Shiba sakamakon lullube fuskarsa da yayi ,Ina dai iya gano launin idanuwansa daga cikin hiramin daya yafa......

Tom tuki yakeyi sosai be tsaya ba har sai da ya Isa,wani Dan madaidai cin gida,wan da yake shi kadaine a bangaren sai wasu tsillatsillar gidaje agefansa, parking yayi a bakin gidan,sannan ya saka hannu ya debo kayan aykin ya rufe kofar ya shiga cikin gidan da sauri, Yana shiga Kai tsaye wani saki yashega wan da yake tunanin Yana suna ciki, Yana shiga yasamesu a falo, inda saliha take ya kalla ,tanakwance saman kujera 3ster idanuwan ta a lumshe,fuskarnan tayi suwet ta rame,sabi da tsabar ciwon da yake cin ta,gurin da Habib ya caka mata wukar ya kalla da sauri ya runtse idonsa ya bude tare da karasawa gurin da sauri, ya durkusa a gabanta tare da zubamata ido hawaye na bin fuskarsa,zuciyarsa cike da tsananin tausayinsa, Aminace ta saurin dakatar dashi dacewa" mené Haka best, bakuka zaka zauna yiba ka fara ceto rayuwarta tukuna ,idan yaso saika cigaba da kukan, murmushi sakar mata yace"Amina nagode sosai Allah ya saka Miki da alkairi, " Amina dole nayi farinciki kasancewar MAR'ATU na bata mutuba" Amina mekikeso na Baki kifadi duk abin da kikeso nikuma na amince Zan Baki duk abin da kikeso" murmushi Amina tayi tace" kafara ceto rayuwarta tukuna,kar katsaya soyayya Kuma soulmate din taka ta mutu" don wannan yarinyar idan baka sameta ba mutuwa Ina tunanin zakayi, dariya yayi sosai sannan ya dauki kayan aykin yashiga gyra gurin ciwon, yanayi Amina tana taimaka masa ,Sabi da shi akwai tausayi da soyayya daker yake aykin,ahaka dai suka samu suka gama gyramata gurin sannan hankalin best ya kwanta.....
Chapter 9 · 0% Book details