← Book details Mar'atussaliha Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 12

Sashe 10

Mar'atussaliha Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Habib kuwa ... Tsawan awa 3 Yana Kiran number wayar doctor faruq Amma shiru kakejj anki dagawa ,Nan take hankalinsa yayi mummunnan faduwa ,Nan danan yashiga tunanin kodai asirinsa ne yake Shirin tonuwa idan ko hakane , shikkenan tashi takare aduniyar Nan domin yasan Babu me fahimtar sa, shiru yayi acikin motar Yana sunanin kodai yaje ya samu munir ya karasa masa labarin mutumin Nan, Dan yaga kusan labarin nasu iri dayane ,Yana tunanin idan yaji makomai wancen mutumin ,shima tashi zata iya kasancewa haka in yaso sai yayiwa kansa kekkewan shiri, dafe kansa ya sakeyi tare da tauna lebe ,yadda har sai da kini ya fito sannan Kuma yadaki sitiyarin motar yace"to ay Kuma yace sai Nan da wata biyu za,a fadi makomar wannan mutumin kash yafada dakarfi"oh my God ni Habib Naga takaina....

12...

MEDUGURI.....

""Namata allurar bacci Amina" yanzu zantafi inafatan dai zaki kulamin da lafiyar ta"nasan kina da kokari akan Haka inaso ki Kara" murmushi Amina tayi tace" to king of the love Insha Allah zankula sosai " ka kwantar da hankalin ka Babu abin da zai samu saliha insha Allah"

"Yauwa Amina nagode sosai Allah ya bar zumunci "yanzu Zan huce gida sai gobe zan dawo ki kuka da lokacin yimata allurar bacci domin zuciyar ta tasamu nutsuwa"

"Tom shikkenan INSHA allah ay naji basai kata maimaitamin ba"sai kace bansan aykina ba ,ko akan ta akafara ciwo"nifa ka isheni"

"Allah ya huci zuciyarki Aminatu "Kinga tafiya ta " yamike tsaye tare da yin hanyar fita, har yakai bakin kofa Kuma sai ya dawo ya Kara zubawa saliha ido kamar zai cinyeta Yana faman murmushi"

Itakon amina rike haba tayi tana kallon ikon Allah agaskiya tayar da da irin. Son da best ya ke nunawa saliha, ta yarda saliha ta mamaye zuciyar best yadda Babu wata "ya mace da ta Isa tasamu gurbi a zuciyarsa Babu ita.

"Gyran murya tayi tace to sarkin love zaka tafine kokuma nasa maka ita a mota ka tafi da ita ?" Dan zaro ido Habib yayi yace "a,a tazauna anan"

"To ay Naga zaka cinye 'yar mutane ne,ko dai kafara maita ban Dani ba?"
Dariya Habib yayi yace "keko sai addu,a haryanzu dai halinki bazai canza ba ,to natafi hankalinki ya kwanta" Yana Gama fadar Haka yajuya yatafi , itako Amina bayansa tabi da kallo zuciyarta cike da tsananin tausayinsa.

Bayan futar best , Amina ce ta dauki katon bargo ta lullube saliha" sanan ta Mike ta nufi cikin kicin ta kunna gas sanan ta dora ruwa akan gas, bayan ruwan yayi zafine ta sauke ruwan ta zuba acikin kula domin karyayi sanyi, bayan ta gama ta dora wani ruwan acikin karamar buta ta karfe,sanan ta zuba citta ,kanimfari, n'a,ana,a , da ganyen shayi e.t.c, bayan shayin ya dahune ta sauke a kasa,sannan ta nufi daki ta Kwan ta "tana kwanciyar ta jiyo rurin wayarta Yana Kara a falo,dasauri ta Mike ta nufi falon ta dauka,tana dubawa taga Ashe best ne, murmushi tadanyi tace uhm "romiyo kenan tafada tare da daga wayar ta Kara a kunne ta tace"...

"Hello"
Daga can bangaren aka amsa da "assalamualaikum"

"Ameen wa, alaikumussalam" best ya akayine har kaje gida"

"Eh wlh naje yajikin madam Dina" dasauki best Wai meyasa ka takurawa kanka Haka"

"Uhm bazaki gane bane shiyasa, bikisan yadda nakeji da itaba" dariya tadanyi tace Niko nasan yadda kakeji da MAR'ATU"

"Adai bar maganar Amina kadan kika Sani "yanzu dai ya jikin nata ta farka" a,a Nan da zuwa 5na yamma zata iya farkawa " okay zuwa anjima zan kara kiranki"

"Okay babu damuwa mujima da yawa"

Tana katse wayar ta saki wata ajiyar zuciya,tadan furzar da iska daga bakin ta tace"Allah sarki so" lokacin da Best ya bar kasarmu muka Gama karatu sau ayi wata uku be kirani ba Amma tun da ruhinsa tazo hannun na shikkenan nashiga siradin takura, tana Gama maganar ta kwanta akan kujerar ta lumshe ido sai bacci...

"Malan Wai ko kaji batan wannan matar da kaje cire mata aljanu" eh naji wallahi amma ina tsoron zuwa gidan karda naje ina shiga ta dawo,inason naje nayiwa Habib jaje Amma Babu dama" haba Malan ay a Haka zaka daure kaje "idan bakaje ba Habib bazaiji dadi ba" hm shikkenan Zan je amma kafin natafi zan yi ban kwana da ku bansani ba ko mutuwace ke bina,"dariya ce ta subucewa matar malan batasan lokacin da ta kwashe da ita ba harda kwanciya a kasa tsabar dariya...

To juneid ne zaune a dakinsa Yana dan daddanna wayarsa" danna wayar yake amma hankalin sa na can wani gurin tunani kawai yakeyi" Yana tsaka da Haka yaji wayan na ruri bugu daya ya daga tare da Kara wayar a kunne yace "assalamualaikum"doctor wa, alaikumussalam sir barka da wannan lokacin" barka dai yakake ya me jiki" lafiya kau sir daman nakira Kane n'a sanar da Kai wannan yarinyar ta samu lafiya" Dasauri juneid yace alhamdulillah"yanzu ina take" sir sai dai matsala daya dole saika zo India Sabi da kullum cikin furgici take da kokarin guduwa" okay Babu damuwa Nan da two weeks Zan iso yanzu Ina da San wani ayki danake son karasawa da nagama Zan shigo insha Allah,inason kacigaba da kuka da ita Dan Allah,sannan kadinga kwantar mata da hankali" okay sir angama,ya katse wayar tare da sakar ajiyar zuciya...

Shiko doctor juyawa yayi inda take a kwance, idanuwan ta lumshe da alama bacci takeyi" Masha Allah kekkewar budurwace wadda akalla zatayi shekara 24 a duniya farace doguwa sosai,gashinta ya barbazo kan fuskarta gabadaya ya lullube fuskar,da alama andanyi dambe da ita kafin asamu ta nutsu tayi bacci, bacci takeyi Amma sai faman sauke ajiyar zuciya take,kanta kuwa daure take da farin bandeji Wanda ya karamata kyau da kwarjini,sai Dana Kara kurama fuskarta ido sannan na tabbatar da cewa idonta ne kawai arufe amma kamar ba bacci takeba sakamakon bakinta danaga ni Yana motsawa Yana furta karma biyu sune"Abba Zan mutu "Abba zanmutu"Abba Zan mutu"cikin tausayawa doctor yake bin budurwar da kallo,Yana mamakin yadda akai yarinya budurwa ",yarshekara 16 akayiwa wannan mummunan tabon da baya taba gogewa har tsufanka,kumama bayan haka sabo da tsabar rashin Imani irin na mutum,kwakwalwar tatama baza,a Bari ta zauna kalauba sai da aka nakasata "jibi fa tsawan shekara 8 muna zaune da ita anan asbitin bata iya furta komai sai Abba zanmutu" ankawota tana shekara 16yanzu gashi tacika shekara 24 bansan Kuma Nan gaba adadin shekarun da zata dauka a kwanceba, Allah sarki baiwar Allah ...

__tom Amina sai bata tashi daga bacci ba sai karfe 4:30 shima saliha ce ta tashi tana Kiran sunanta" zumbur ta Mike ta nufi gurinta tana mata sannu"daker take iya cewa yauwa" murya a sanyaye saliha ta kalli Amina tace" kina da kirki Dan Allah ki fadamin me wacece?"murmushi Amina tayi tace"ki kwantar da hankalin ki saliha indai nice karki wani tsorata, ni d'un da kike gani kawar best ce "shinenan yakirani yace naje n'a taimakeki" best Kuma saliha tashiga maimaita sunan abakinta ,tashiga duniyar tunanin Ina tataba Jin me sunannan, runtse ido tai ta bude Amma ta kasa tunano inda tasan me sunan, sai kawai ta Kara kallon Amina tace please waye best" murmushi kawai Amina tayi tace kinsan shi idan kika Gandhi zaki ganeshi"yadda Amina take magana saliha ta kuramata ido tana kallonta" Kallonta take kamar tataba ganin ta Amma Kuma sai ta kasa Tina ainada tasan ta ,hakanne yasa saliha ta dafa kanta tace oh my God" Amina ce ta kalleta tace"lafiyar ki kuwa" marda kanta tayi ta kwanta tace "lafiya kalau "oky Bari naje na hadamiki ruwan wanka ko inyaso sai na kawomiki ko ruwan zafine Kisha domin cikinki ya sarware,Dan na fuskanci kina kin yunwa...

13...

"Tashi tayi ta je ta hada mata ruwan zafi sannan, tazo ta kamata zuwa bathroom"bayan ta shigar da ita ne sannan ta fito ta jawo kofar ta koma falo,

Saliha kuwa bayan ta shiga bathroom zama tayi dirshe a kasa ta shiga duniyar tunani tana cewa azuciyarta "kenan da Habib soyayi ya kasheni" to amma menene nufinsa akaina da yasa aka sani awannan dakin kuma akamin dinki aciki" kodai soyake ya azaftar Dani" Kay a,a to idan ba Haka ba meyakeso ya min" shiru ta danyi tana bin bandakin da kallo kamar meshirin tunano wani abu can Kuma kamar an tsikareta ta Mike tashiga yin wankan...
Chapter 10 · 0% Book details