← Book details Mar'atussaliha Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 12

Sashe 11

Mar'atussaliha Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Gudu yake taugawa akan titi kamar wan da zai tashi sama har ya karasa bakin katafaren get din gidansu, Yana karasawa me gadi ya bude masa geta ya shiga a guje,ko parking space be karasaba ya ajiye motar ya futo yayi cikin gida a guje,yana shiga yasamu momy a falo tana zaune tana Shan ruwa, bece mata komai ba ya huce sama ya shiga dakinsa ya kwanta tare da Jan bargo me kwauri,ya rufa "momy kam bayansa tabi domin taji lafiya, tana shiga dakin tasameshi akwance a rufe, gefan gadon ta zauna sannan ta ce "abee lafiya kuwa kashigo a hargitse meyasameka" ta yi tambayar cikin damuwa, Habib kuwa jikinsa hauwani rawa yake tsabar sanyi da kaduwa yashiga cewa "momy ki rufeni Dan Allah momy sanyi nakeji "what sanyi "bangane na rufekaba me kake nufi, wannan bargon da ka lulluba fa "momy wallahi sanyi nakeji dan Allah ki rufemun jikina,ni bargonnan babu abin da ya tare mun" momy bansan me yasaba jinake kamar wani abu zai faru Dani "jinake kamar ana caccakar jikina kiyi min addu,a Ina tunanin mutuwa zanyi" momy kam tun da tadau abin na Habib wasa yanzukuma ta fara ganin kamar da gaske bashi da lafiya" kallonsa ta karayi tace "habibu kodai rashin matar ka da kayine ya sa kashiga wannan yanayin eh "uhm momy bazaki gane ba inason nayi bacci ki kwanta a kusa Dani momy"zaro ido mom tayi tare da cewa akusa dakai fa kace na kwanta akan me ,baka da hankali Kato da Kai zakace na kwanta a kusa dakai" please mom wallahi indai nikadaine zanta gani Ana tsoratanine momy tsoro nakeji "mummunnan mafarki zanyi idan na kwanta Nika,dai" au Dan kana mafarki shine zakace na kwana dakai Sabi da agarin mahaukata ake, Ina laifin kace na taimaka maka zuwa dakin yayanka Junaidu ka kwana dashi" a,a momy wallahi yaya juneid bazai rarrasheni ba tsokana ta kawai zai tayi " yayi maganar kamar zaiyi kuka, Tom shikkenan Zan kwanta Amma afalo sai na dinga kula dakai" tana Gama fadar Haka ta Mike tanufi hanyar fita,

Shiko Habib wata kwalla ya goge daga idonsa Yana jin Babu dadi azuciyarsa zuwa yanzu yafara tausaya wa kansa da iyayenka,jibi yadda mahaifiyarsu take tausayinsa kawai sabi da farinciki sa zatazo ta kwana anan,idan ban da mahaifiya Wace zata maka wannan, yanzu kenan da zataji abin da n'a aykata yazatayi,nashiga uku ni Habib duk ranar da momy ta gano Nina batar da saliha..

Itako momy tana fita dakin juneid ta shiga, tasameshi har ya kwanta, tai sallama sannan ta karasa tace" juneid kayi baccci ne" no mom banyi bacci ba Ina hada wani muhimmun abune domin inason a gobe da safe na huce India" "India Kuma Junaidu" Ana tsaka da wannan tashin hankali kana debowa kanka tafiya"haba Junaid sai kace ba matar dan'uwanka ake nema ba" "momy bawai ban damu da batan saliha bane kwai da abin da zanje nayo a India shima yana da amfani Dan Allah mom kadaki hanani tafiya" yakarasa maganar kamar zayyi kuka tare da ruke hannunta, "uhm shikkenan Junaidu Allah ya tsare ya kiyayemin Kai "yanzu inason kaje gurin abbanku ka kwana dashi zanje gurin Habib domin naganshi kamar yafara tabuwa, ina tunanin habib Yana bukatar kulawata dakuma addu,a dan Haka zanje n'a kwana dashi" what momy kije ki kwana dashi fa kikace"Kato dashi zaki je ki kwanta dashi bazanyuwu ba" haba Junaidu ni da dana mezai faru dani abin da nuna tsuguna ba aufeshi "kuma ma idan ban da lalura mezaisa naje ba kwana adakin habibu tsorata fa yakeyi"duk yafita a hayyacinsa" "to tsorata Kuma momy yanzu Wai Ina Habib din bayana gidan saba,?" "A,a Habib Yana cikin gidannan adakinsa"okay tom shikkenan momy duk yadda kika ce ay Haka za,ayi "kije Allah ya tashemu lafiya ni Bari naje dakin dady.....

"Yauwa dan albarka yazu badaban taki yarda kaje kukwana ba ay da Kai zakaje gurinsa...

**** Kintashi "sannu anisa kinji "allah yadada baki lafiya shalelena"tafada murya a sanyaye.

Anisa ce da Kee ta iya bude baki yace"mami ina su yaya juneid basu zo ba ko uhm ay danan nasan sun tsanemu"

"Anisa kenan Wai har yazu bazaki daina tunanin wadancan mugayan mutanen ba" koni da yake dan'uwana wan da muke uwa daya uba daya na cireshi acikin dangina ballekuma ke"Wai shin Anisa ba kinmun alkawarin zaki hakura da rayuwa acikin suba"bakince keda su har aba da ba?"to yanzu Kuma menene na yimin maganar su ko sokike ki batamin rai"najima da abin da tsukama na "ko sai kin karamin wani bakincikin?"

"Am so sorry mami insha Allah bazan sake Miki zancensu ba idai har nakeji ka dakko zancen ba"mami ay farinciki ki shinakeso Kuma shine nawa"takarasa maganar tare da share kwallar dake mmshirin zubowa....

**(Me duguri)**

In the morning**************

*Best meyasa kafiye matsala ne kabari mana ta Gama karyawa inya so sai na bata wayar kaji muryarta" hm bazaki gane bane Amina"ni dai kawai ki mikanata wayar" ni dai gaskiya bazan bata yanzu ba sai tagama breakfast"in kamatsu sai kaganta kataho yanzu ka ganta da kyau" murya yadan sassauta kasakasa cikin sigar lallashi yace", Amina kinsan idan da ina gari Babu abin da zai hanani zuwa naganta" nayi tafiya yau da safe "naje yin wani atisaye ne bazan dade ba Zan dawo baifi nayi kwana uku ba Zan taho "kekuma inason Nan da 4 days ki kawo saliha hida domin ta fahimci komai yadda ya kamata", okay Babu damuwa yanzu Bari na bata wayar" know nama fasa " meyasa?" Idan taji muryara a yanzu zata iya rudewa nikuma banason haka Dan Allah ni dai ki kulamin da ita sosai" insha Allah zan kula"kuma kada kiyi yunkurin tahowa a mota zan turo jirgi ya daukeku kinji"oh ni Aminatu inaganin fi'ili dacan ba a motar nake tafiya ba Dan tsabar iyayi Sabi da da budurwarka shine zaka wani ce mutaho ajrgii anki to anki din" tana Gama fadar Haka ta katse wayar Kitty....

"India"

*Juneid ne zaune a gaban gadon ya zuba mata ido Tana ta bacci "sai dai haryanzu batadai na ammatar wannan kalmar ta"Abba zasu kasheni' juneid ne ya juya ya kalli doctor ya ce" doctot yaushe zata farka ina son mukoma Nigeria a yau dinnan" eh to Nan da 10 minit zata iya farkawa Amma sir kana ganin idan ka tafi da ita Babu matsala ,domin nifa banason abin da zai Kara taba lafiyarta no nakamu dason ta ,dazakace ma nazo mutafi tare biyoka zanyi" wata uwar harara juneid ya watsa masa sannan ya kauda Kai tare dacewa sai kaje kashirya " murna ce ta ishi doctor da sauri yanufi hanyar fita domin ya je ya shirya.....

****umma kitaho muje gidan su Habib ,yakamata ace zuwa yanzu yafito da saliha Amma jikike shiru, Dan Allah kitashi yanzu sama da wata biyu kenan Babu saliha Babu labarinta "umma ce ta Dan numfasa sannan tace" banki tatakiba safiyya yakamata muje can domin ni zuwa yanzu n'a soma karaya "yauwa umma ko kefa tashi muje mu shirya" bayan sun tashi sun shirya ne suka nufi hanyar gidan su Junaid....

Abangaren su Amina kuwa, sunshirya tsaf da ita da saliha kamar ba itaba gabaki daya ta yi kyau ta Dada haske lafiya tasamu duk wannan ramar datayi yanzu Babu ita, kallon Amina tayi race anty Amina Ina Kuma zamuje?" Ki kwantar da hankalinki saliha zamuje gidan su best ne domin kiga wata kekkewar bazata wadan da ko da kudi bazaki iya samun bazatar Nan ba sai ikon Allah" murmushi saliha tayi tace"to Allah yasa muji alkairi Ameen sannan suka fita daga gidan zuwa bakin titi don yakaisu airport su hau jirgi Sabi da best yayiwa Amina takarar karsu taho a mota zai turo da jirgi ya daukesu.....

Bayan mint goma yacika ne ta farka karaf sukayi ido hudu da juneid dake zaune"a gigice ta Mike tashiga ferta yaya juneid"dasauri ta cakumi wuyansa tashi ga girgizashi tana kuka tana cewa" Yaya juneid Ina abbana ,Ina ummana" karkacemin sun mutu" Yaya Ina kannena suna Ina Dan allha Yaya kafada min suna Ina ,kadai na mutune bana duniyar" yay kaima kamutune ?" Girgizamata kaiyayi zuciyarsa tab cike da tsananin tausayinta 'idonsa tab da kwalla yace" Basu mutuba sunan da ransu kema bawai kinmutu bane kinan aduniya, "maza tashi mutafi na kaiki gurin ummanki a,a Yaya bakafada min Ina kanwata jery ba kaboyemin wani abu nasan tazo gurin alokacin taga komai yakasheta ko Yaya " jijjiga Kai juneid yayi yace" wanan ce bansani ba ko tamutu ko tana Raye Amma Ina da tabbbacin Bata mutuba etama" a,a Yaya kafadamin gaskiya karka fadamin Don in kwantar da hankali na yanzu idan kuma nake natarar da basa rayé?" Short up !!! Ya daka mata tsawa yace zanmiki karyane ko nataba Miki karyane banason shashanci ki nutsu!!!! Kuka ta fashe dashi tare da cewa in nutsufa kace Yaya acuce ni sanna kuma acemin n'a nutsu yaya anyako baka manta abin da akamin ba yay ancuceni anzalinceni " menai kawai don nakasance nidin me hakurice "bazan taba yafewa ba harsai andau Karmin fansa .....

"Okay ki tashi mutafi gida "yafada tare da mikewa ....

Bayan tatashi ta shirya doctor shima ya shirya suka nufi inda jirgin yake suka shiga sukadauki hanyar komawa gida Nigeria....

"Bayan su safiyya sun Isa gidansu juneid,afalo suka tarra da momy tana zaune ,aytana fanin safiyya tamike tsaye tace"saliha tafada da karfi" shiko Habib Yana daga daki yajiyo maganar momy da sauri ya fito "Yana sakkowa suka hada ido yayi mutuwar tsaye Yana nunata da hannu " jijjiga Kai yashiga Yi Yana cewa"no momy no wanan ba saliha bace" to idan ba saliha bace uwarka ce momy tafada afusace" murmushi safiyya tayi tace au bakisan ni ba itabace" to zuwa mukai kufito Mana da "yar,uwarmu Ina saliha take" kan momy ne ya kulle shiko Habib hanyar fita yanufa yashiga mota ta figa betsaya a ko Ina ba sai a gidan munir....
Chapter 11 · 0% Book details