← Book details Mar'atussaliha Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 12

Sashe 8

Mar'atussaliha Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Abu buwa fa sai Kara ta azzara suke inda aka nemi saliha kasa ko sama aka rasa,Abu kamar mafarki,gabakidaya hankalin su juneid ya tashi, musamman ma hankalin safiyya da mahaifiyarsu,komai ya dainamusu dadi abin duniya ya hadu ya musu yawa,tun suna kallon abin kamar wasa yanzu kam sun tabbatar da ba aga saliha ba,gashi gidan t.v da raidio da kadashin kewaye Babu inda labarin batan saliha bejeba ,Hatta cikin gidan saliha an zuba matakan tsaro a cikin gidan ta ko Ina sai bincike akeyi, ayanzu Habib takai takawo yasa ankama megadin gidan sa angarka meshi bejiba be gani ba, Kai natakaice muku ayanzu hajiya adama da yarta Anisa suna hannun hukuma Ana bincike akansu ,sakamakon "yar tsamar da aka samu tsakanin su da su momy akan auren Anisa da juneid da Kuma Habib Ana zarginsu da sace saliha amaryar Habib...

Zaune suke suna faman ganamusu azaba ta kowace irin siga, Hatta jikin su Saïda jini ya fito tukunna sojojin Nan suka daina dukansu, sun dakesu iya karfinsu domin sufadi gaskiyar inda suka Kai saliha Amma amsa dayace suke bayarwa itace"basu da masani ya akan batan saliha, dady dai dayaga za,a kashemasa kanwarsa tilo guda daya yasa aka dakesu,Amma duk da Haka anisa faduwa t'ai agurin sumammiya bata ko motsi, hajiya adama Tana kuka haka aka sata a mita sai asbiti,Babu irin zagin da su Habib Basu Sha agutinta ba, juneid dai yaji ciwon zagin da tamusu ,Amma shi Habib ko ajikinsa saima Kara cewa dayake Bekamata asakesuba sai sunfito masa da matarsa ,Babu tausayi Babu imani agaban idonsa aka yanke yatsan megafinsa guda daya duk Dan yafadi gaskiyar inda saliha take" Allah sarki bawan Allah yamarasa mezaice tsabar azaba da tashin hankali Kira yake kawai su kasheshi,habib kam murmushin gefan fuska yayi ,yakalli sojan yace,ku sakeshi haka,Amma duk da Haka banhakura ba Hutu nabashi zuwanan da sati daya yafadi inda suka kaimin matata...

*Wllhi umma yakasheta kidaina saka ran ganin saliha araye ,yakamata ace umma mu fita miyaki Habib ,umma Habib mugune nafikowa sanin wane Habib Dan Allah umma ki yarjemin naje na kasheshi inyaso Nima akasheni,wallahi umma nagaji daganin zubar hawayenki ,yaushene zakiyi bacci me dadi batare da kinyi mafarki Mara dadiba,yaushene zuciyarmu zata samu Salama ,umma dan Allah kidaina kuka ,kidaina banaso zuciyata tafasa take umma, shikkenan Wai yakashemin "yar,uwata eh umma kiyimin magana mana,ina yakaimin ita ,ni inaso ko da gawarta ce magani naji sanyi, shin kinmanta abin dayafaru ?" Afusace umma ta Mike ta kalli safiyya ido cikin ido ,tace ban Manta ba kuma bazan taba mantawa ba,safiyya ki kwantar da hankalinki nace nayar da da saliha nasan "yata bata mutuba itadin jarumace kyutace wadda ubangiji ya bani, nayi Imani Habib bazai kashe saliha ba nasan shi yanada wayo sosai" yanaso yasan ko ita wacece meyasa tashiga rayuwarsa,wadannan tambayoyin gudabiyu kawai yakeso ta amsa masa ya kashe ta,ayanzu inaji ajikina Habib ya dauke saliha daga wannan garin ,babban abin da Habib be Dani ba da shashancin da yayi saliha bazata taba zama agurinsu ba dole sai ta gudu,wuyarta suce zasu mata Dole ,nasan aljanunta Dole sutashi daganan kuma zata dawo idan kuma tadawo Habib zata fara tunkara.... Safiyya ki kwantar da hankalinki wannan abin da nafada Miki shine zaifaru" safiyyace ta goge hawayen idonta tace,to umma meyasa kinsan da hakan kike kuka ,bayan kinsan zubar hawayenki na dagamin hankali?" Uhmm umma tayi murmushi tace "safiyya kenan, kinsan meyasa nake kuka uhm inakuka ne kawai sabi da hango irin azabar da Habib yayiwa saliha har suka samu nasarar kaita wani gurin,amma bayan Haka da Babu abin da zaisani kuka....

IN the morning....

Wani gurine Wanda koda dabba dayake da Rai tsoran shiga jejin yake ya zauna, Sabi da tsabar mugganan abubuwan da ake aukatawa agurin yayi yawa, agurin daki dayane wan da dagashi Babu wani,dakin yakasance bashi da maraba da kurkuku,gashi da duhun gaske,daga cikin abin da suke a dakin n'a farko akwai hayakin tumfafiya da mangelo dakuma wata bakar laya wadda suka kasance tsarine daga muggan aljanu kowane irin aljajune Babu yadda za ayi sutashi harsai anfito dakai daga cikin dakin, wannan dakin idan Kai mutumne me aljanu kana saka tafin kafarka aciki to kayi bankwana da aljani harsai ka an fito dakai tukunna zasu dawo jikinka, idan kuma mutum yakasance shi aljanine ba mutumba to idan yariga tashi ga yayi bankwana da duniyar mutane, wannan dalilin shiyasa Habib yakirawo doctor faruq yasa yayi mata allurar bacci tunkafin su karasa...

. Ton su doctor faruq harsun ido cikin jejin zasu shiga kenan saiga Kiran Habib yayigo Kai tsaye, doctor ya daga tare dacewa "yallabai mun isofa, murmushi Habib yayi tare da cewa , "ba kun iso din ba tana hayyacinta ko kum haryanzu bacci take, dariya doctor ya kwashe da ita yace"hhh ay ita data tashi sai karfe 10 na safiyar gibe" "yauwa doctor aykinka Yana kyau yanzu Ina son kusaka ta acikin wannan dakin" doctor ne ya zaro ido yace" yallabai asata anan dakin fa kace damatsala fa indai Aka sata zamu iya rasata "bangane ba mekake nufi Habib yayi tambayar "ina nufin zata iya mutuwa ,wannan dakin dakin hatsarine kaikanka kasani, muddum aljani yashiga baya dawowa balle ita " dariya Habib yayi yace badamuwa kusaka ta akwai aljanu ajikinta Babu abin da zai sameta sai dai ku ne matsalar,yanzu abin da zakuyi duk inda Macé me aljanu take kunema a garinnan ,sai na biyata ta dinga fito da ita duk lokacin da zaku sata tafadamana gaskiya, okay na gane Babu damuwa za,ayi yadda kace, Yana Gama fadar Haka ya katse wayar tare da janyo gadon daga bayanmotar asbitin,ya gara tayoyin gadon zuwa cikin dakin saiga saliha aciki a kwance ko motsi batayi baywar allah

Tirkashi ana wata ga wata...

Abangaren Anisa da mahaifiyata kuwa"kullum cikin kuka hajiya adama take sakamo kon abinda Habib ya sa akamusu abin yayi mata ciwo sosai ,koda barene akasaba dashi yazama dan,uwa Bekamata ayimasa irin abin da akamusu ba, balle ita da take kanwar mahaifinsa, tabbas bazata taba mantawa da wanan abin ba ,Kuma bazata taba yafe duk wani cinkashi da akamata akan abin da batasan hawa ba batasan sauka ba, tana tsaka da wanan tunannin taji sallamar su momy a asbitin da ita da juneid da Kuma Habib da dady, karasowa sukayi kusa da inda gadon da aka kwantar da anisa take suka tsaya tare da cewa "Mami ya me jiki" cikin masifa hajiya adama ta Mike tace bansani ba"mugaye kawai bansani ba anfada muku muna bukatar sananuku ne bamaso, kodai kunzone kukara tozartamu, to Bari kuji ni adama daya akemin ba,a nabiyu dan Haka kufita kokuma namuku ihun zaku kashemin "yata, duk dama bansan dawace tsiyar kuka zoba ,bansani ba ma zuwa kukayi ku karasa min ita, to wallahi munfi karfinku namanmu daci gareshi ,kumatsa daga kan ta karnaje kunyi guzirin wani sharrin tafada a fusace!!! Kwallar da ke kwance a idon dady ce ta karasa fitowa ya kurawa kanwar tashi ido yace" yanzu ni Adama kike kora daga inda kike, karki Manta nifa dan'uwanki ne ciki daya muka fito amma kidinga aybata dani da zuri,a ta akanme zamucutar da ku" rufemun baki !!!!!!! Tafada tare da zaro ido,kamar wata aljana tace ni zakayiwa dadin baki" au ashe kamanta ni din"yar,uwarka ce danka agaban idonka yasa akadin ga ganamana azaba akan abin da bamu aykata ba ,narasa menayiwa yaranka sun tsanemu to tunka fin ku kashemu nayenke alakar da ke tsakanin mu daku ,dagayau ni Adama bani da kowa sai Allah sai Kuma yata daya da Allah ya bani "ko a hanya kada kasake nuna kasanni kufita !!! Tanuna musu hanyar fita.... Dady kam jin wadannan bakaken maganganun da take jifansa da sune yasa kansa yashiga juyawa, yafara ganin bijibji" luuuu yatafi zai fada dasauri juneid ya rukoshi tare da nufar hanyar fita daga dakin dashi, suma ragowar binsu sukai, suka shiga mota suka dauki hanyar gida kowannensu jiki Babu kwari Amma Banda mutum daya shine Habib da hakanma yafi masa dadi ,Sabi da dole yasan tunda dady rashin lafiyarsa tatashi Babu yadda za,ai acigaba da bincike akansu ,harsai dady yasamu lafiya,kafin Nan Kuma yariga da yagama bincikensa akan saliha ,yakasheta kawai Adawo musu da gawarta, kokuma ya hullawa namin daji gawar sucinye....

11.....

****su juneid suna Isa gida ,sukayi parking din motar sannan suka fito, kama dady yayi suka nufi part dinsa dashi Yana masa sannu,itama momy bayansu tabi har suka Isa bedroom din dady aka kwantar dashi, bayan anwantar dashine juneid yasamu guri a kasa yazauna ,yazubawa dadyn Basu ido ganin yadda zafafan hawaye kefita daga cikin idonsa ko tsayawa basayi,ya kurawa saman silif Yana kallo, momy ce ta soma magana ta n'a kallonsa tace "haba abban juneid meyasa wannan abin zai dameka harya kusan tada maka da ciwonka ,Dan Allah ka kwantar da hankalin ka" uhm dady yadanyi murmushi yace "Bazaki gane ba ,itafa din kanwa tace jinina wadda mukafito ciki daya,tun kafin iyayenmu su rasu suka bani amanar adama to meyasa zatace kada nakara nuna nasanta, meyasa inason "yar,uwata,dady yasa hannu ya goge hawayen fuskarsa yacigaba da cewa "haryanzu adama yarinyace batasan komai ba ,batason ratuwar duniya ba,kwai dai tana cikintane Amma idan Banda abin ta tayaza,ai tace ni alhassan bana sonta meyasa kowani taji ya fadi wannan maganar ay ta karyatashi, juneid ne ya dafa kafadar abbansa yace" dady ka kwantar da hankalin ka insha Allah mami zata fahimceka kuma ni juneid inama ka alkawar da cewa duk abin da yake faruwa insha Allah,komai yakusa zuwa karshe,Bari natashi na fita akwai abin danakeson yi yanzu, dagamasa Kai kawai dady yayi yabi batansa da kallo har juneid ya futa...
Chapter 8 · 0% Book details