← Book details Mar'atussaliha Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 12

Sashe 5

Mar'atussaliha Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yauwa daman bawata magana bace kawai dai sonake nace miki wallahi ni dagaske nagaji dazama dake ,kitaimaka ki tafi gidanku ,nafahimci indai nacigaba da zama dake wataran saikin kasheni,dan Allah kitafi indai kuma ba da wani manufa kika aureni ba ,dubeni fa duk yadda nakoma kamar ba ni Habib ba ananfa n'a kwana ina kuka,wallahi Allah ya Isa nashani wannan jarababben auren......

"Au jarababben auren Kuma, hmmm Habib kenan kamanta yadda akai ka aureni, zuwakai fa ka auroni ta karfi kanuna kai wani babban kwarone a tantiranci,harda wani cewa tarbiyya zaka koyamin da hankali, Bekamata kakaraya da yawa Haka ba tunda aykin lada zakayi...

"Saliha kinyi hankali ay wallahi kina ma da hankalinki daman fadamake kawai amma ni bantaba ganin Macé me hankali kamarkiba"

"Wallahi Habib banyi hankali ba dasaura au ,kabari idan kagama koyamin hankali sai natafi gidan tsohona ko,kaga ay yanzu idan natafi ban kwauta makaba sabida kana tsaka da samun lada kuma ace n'a dakatar da samin ladanka ,ah Babu inda zani inan harsai naga kacika littafinka da lada", kwallar dake kwance a idonsa ne yakarasa fitowa zuwa kuncinsa,yace wallahi banason ladan indai saina zauna da bakar kaddara kamarki zansamu, n'a hakura da samunsa,allah natuba na hakura da masoyiyata ta asalima na ci,amanarta balleke da n'a aureki cikin sauki,kodan kinga ina tsoranki,dagayanzuma nadaina jin tsorannanki kiyi duk abin da zakiyi... Ay Yana tsaka da magana Yana hura hanci,yaji saukar wani gigitaccen mari a kuncinsa ,Wanda yayi sana diyyar ganin wasu taurari sun gifta acikin idonsa,tsit yayi har da kama baki,hawayen azaba na fitowa daga idonsa, sannan ya zuba mata su Yana kallonta,itama kallonsa take ido cikin ido fuskarnan Tata a murtike kamar Daren mutuwa,daga inda take tana inya jiyo yadda bugun zuciyar Habib ke harbawa dakarfi,kadan yakejira juciyarsa ta buga sabi da tsananin tashin hankali, ganin Haka yada saliha ta Mike tsaye ta soma tafiya ,sannan ta tsaya cak ta juyo tace masa,na hakura na barka yanzu,amma da sharadi, daga yanzu nice Kai Kaine kakoma ni, duk kannin wasu ayyuka kaine zaka dinga yinsu a gidannan,kuma dagayau kullum kadinga zuwa kagaisheni kafin ka fara aykinka kafahinta!!!!!! Tadakamasa tsawa, ay Habib besan lokacin dayace eh eh na fahimta hajiya saliha "wata tsawar tasake dakamasa tace kull hajiya kurum kada kasake cewa saliha" to to angama hajiya"yafada tare da share zufar da ta karyo masa , murmushin gefan fuska yadanyi sannan tace "Kuma ni dakai babu rabuwa Babu kishiya,mutu karaba, "dasauri ya amshe harda yimata murmushin karfin hali yace Kuma takalmin kazaba, Allah ya jadaren hajiya ta Amarya kuma uwargida a gidan Habib matata tadanan acikin mata, saliha dai bata saurareshi ba ta shige daki tace inajiran yanzu kakawomin breakfast,angama ranki yadade hajjaju"yatashi da sauri ya shige kicin....

Yana shiga kicin din ya samu guri ya zauna,ya saki kuka zuciyarsa kuwa kamar ta fito waje Sabi da azaba"sai dayayi kuka me isarsa sannan ya share hawayensa ya Mike,yashiga malkada kayanmuya,sannan ya tafi ya kunna gas yadora ,indomi domin ita kadai ya iya girkawa, bayan yadora ne, ya dakko albasa yafara yankawa,Yana tsaka da yankawa ya zaftare hannunsa,saiga jini ya fara zuba,Nan take hankalin Habib ya tashi,ya shiga neman abinda zai kulle,can gefe ya hango wani audiga da sauri ya dauka ya baybaye gurin da ita,sannan ya dakko albasar yashiga wankewa bayan yagama ya zubata a indomin, yakoma gefe ya Dora da kukansa Yana tsaka da yin kukan yaji kamar indomin tana kamawa,ay dasauri ya nufi gurin ya sa hannunsa wai zai sauke,nan take ya kone,wata uwar Kara ya kwada ya koma gefe ya zauna yagama hucewa sanan ya dawo ya dauki tumma ya sauketa, gabakidaya acikin plate ya juye aciki,sanan ya kashe gas din,yasa cokali a ciki,ya nufi dakin saliha Yana shiga yasameta zaune a kan kujera idonta n'a kan t v dake manne ajikin bangon dakin,karasawa yayi ya dora plate din akan table din dake gabanta,sana ya koma ya dakko shayi hadin kauri ya kawo mata,juyawa yayi zaitafi ya tsinkayo muryarta tana cewa "Ina zaka ay baka gamaba dasaura,kashiga bedroom Dina ka gyramin kafin nagama inaso zandan kishingida, batare da yace komai ba yazo ya huce ta gabanta zuwa bedroom dinta yashiga aykin gyrawa.....

Yana tsaka da geran dakin saliha ta shigo ta kwaso masa fant da bureziya nata da kuma Kayan bacci ta kawo maso ta wanke, Habib ne ya tsaya ya kafeta da ido can Kuma sai yace "ay Naga da injin wanki a gidannan meyasa bazan ki wankeba sai ni zanwanke, batarai tayi tace " to bazan wanke ba Kai nakeso kawankemin ko baza ka wanke bane, jiki n'a Bari Habib ya karbi kayan ya ajiye yace ,"wa ni na Isa nace bazan wankeba ni awa, "oho dai kuma wallahi da hannunka nakeso ka wanke,yau inason ka wanke fant da bureziyar karuwa", a gigice habib ya dago ya kalleta yace " da hannnafa kikace, Wai Dan Allah bakije islamiya ba,kinmanta namijine sama da mace,ko kinason tsinuwar mala'ku ta tabbata akankine, ko dai kinmanta ni mijinkine" "au au kamanta kace har aba da bazan taba zama matar kaba kawai ni baiwa ce ka auro,ba matar aureba" to aynima yanzu bawa na aura ba mijin aureba, tanakai wa Nan amaganar ta tayi taki ta fuce ta bar gurin, shiko Habib zama yayi ya zabga tagumi domin yamarasa meyake damunsa,izuwa yanzu kam yayi danasani yafi a'irga tabbas bature yayi gaskiya dayace idan kasan abin da zaka fada wa mutum,to bakasan irin abin da za a dawo maka dashiba ,shiyasa ubangiji yakecewa,idan kaga bawana Yana aikata barna to karka muzanta shi koka zageshi, idan zaka iya kayimasa addu,a...

MAR'ATUSSALIHA BOOK 2

7...

Tom bayan Habib yagama gyran dakin, ya kwashi wanki ya futa harabar gidan, zama yayi ya soma wankin,yanayi Yana yayyatsine fuska shi adole me kyenkemi,jiyayi anyi hown megadi ya bude kofa dasauri ya daga kansa ya zubawa get din ido gomin ganin Wanda zai shigo, motar munir ce ,bayan ya shigo yayi parking,ya fito,karaf idonsa ya Kai kan Habib da yake Daman wanki Yana zufa, abin mamaki yatsaya Yana kallon ikon Allah,megadine ya karaso kusa da shi yace ranka ya Dade ,Naga katsaya kana kallon yallabai,da sauri munir yace" kai uban me kake daba zaka karbi wanki kayiba kabarshi Yana wanki sabi da bakasan aykinka ba" "wallahi naje nace yakawo nayi masa ya dakamin tsawa har da cemin idan nasake ko kallon inda yake saiya koreni daga ayki" munir besake cemasa, komaiba ya nufi inda ya ga Habib,Yana karasawa daf dashi gamamakin sa saiga Kayan mata yake wankewa,cikin mamaki munir yace "Bross mezangani Haka wayasaka wankin Kayan mata" shuru Habib yayi masa daga bisani kuma ya dago tare da yimasa murmushin karfin hali yace "aykin lada nake..

"Aykin ladafa kace,Kai yanzu Habib duk ayyukannan na duniya da,akesamun lada bazakai ba,sai dai wankin Kayan mata" "tukunnama Wace shegiyar ce ta saka ka wanki!!!!! ?" Dasauri Habib ya rufemasa Baki ,Sabi da sauri ma harda kumfa ya watsamasa a Baki,yace" Kai baka da hankali wacece shegiyar kakulla ba,acewa mutum shege ,kadaina " baki da hanci munir ya saka Yana kallonsa cikin mamaki,domin shi yanzu lamarin Habib tsoro yake basa,gaba kidaya ya zama kamar zararre gawani Baki da yayi,ya rame,magana yafarayi yace",waini bross meyake faruwa ne gaba kidaya ka canza "why" hmm kawai yace yayi masa banza yacigaba da wankinsa har yagama minir Yana binsa da kallo..

Yana Nan zaune ya tsinkayo muryar saliha tana cewa "Wai baka Gama bane,tun dazu Ina jira kazo ka gyra falonnan yayi datti,murya narawa Habib yace,Kiyi hakuri hajjajuna sabi ,hudu nayi sabo da sufita sosai Bari nazo nayi sharar, ",

Munir dake zaune yayi mutuwar tsaye kallon abin yake kamar a mafarki yamarasa me zauce,hakanne yasa yamike tsaye,ya kalli Habib yace,bross ni zan huce idan kagama bautar kaje Momy na kiranka tace tun shekaranjiya take kiranka wayarka a rufe,danhaka tana son ganinka,ni kaga tafiyata"sai anijima Jani talau, murmushi Habib yayi yace ,"nafika ko agirin Allah tun da ni yanzu aykin lada nake,kaikuma nasa ido "Yana kaiwa Nan a maganarsa ya shige cikingidan...

Yana shiga cikin gidan ya dakko tsintsiya yashiga share falon bayan yagama ya shiga yin mopping sannan ya koma gefan kujera ya zauna ya huta...

Tashi yayi ya shiga bathroom yayi wanka ,bayan ya Gama yafito ya saka doguwar riga milik me kwai da sheki,gaban mudubi ya karasa,yadan shafa Mai daga Nan Kuma ya fesa turare ya fito,afalo yasameta a zaune,wannan karon ba kallo take ba karatun qur,Ani mwgirma take cikin voice dinta me dadin gaske,karasawa yayi gabanta ya zauna har ta kammala ayar karshe ashafin tacikin suratul Maryam" dago ido tai ta kalkeshi ko kiftawa Babu tace "lafiya inazaka" kodai gurin Amaryarka zaka?" Tayi maganar tare da sakar sa murmushi, murmushi ya danyi sannan yace"a,a momy ce takeson ganina" kinsan dai n'a miki alkawarin babuke babu kishiya hajjajuna, "au hakane rom shikkenan Adawo lafiya,kuma karka dade don inaso kazo ka doramin abincin dare" oky badamuwa insha Allah bazan dadeba ,Yana gama fadar Haka ya Mike ya nufi hanyar futa daga falon.

Bayan futar Habib saliha ce zaune tana tinanin irin abin da ya faru da ita da Habib ayau tabbas tasan Bata kyauta masaba, Amma Babu yadda ta iya idan ba ita ba Babu wan da zai iya koyawa Habib hankali,yanzu gashi ko banza ya Dan fara hankali,tafada a kasan zuciyata tare dacewa hm yanzu muka fara wasan..

__________________________________________________malan ke zaune acikin iyalansa Yana bawa matarsa labarin abin da yafaru dasu a gidan Habib ba Karan tsorata matar malan taiba, sannan taci dariya,Amma Babu damar yin dariya yadda zata isheta,Sabi da malan Yana zaune karyace tamasa rashin kunya, kallonsa tayi race " Amma dai maln zaka koma kataimakeshi ko da Basu Gama barin jikinta ba,me Wai me kike nufi"? "Ina nufin aljanun baiwar Allah Nan tana bukatar taimakon kafa malan "wani inkinganni alahira kaini akai ay ni dazuwa gidan habibu har abada,ke koyanzu n'a hadu da wannan yarinyar me suffar aljanu saina gudu wllhi,hmm dan bikisan wahalar danasha bane..
Chapter 5 · 0% Book details