← Book details Mar'atussaliha Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 12

Sashe 6

Mar'atussaliha Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To Habib Yana Isa gida, Afalo ya samu momy da juneid a zaune suna magana,Yana shiga dauke da sallama abainsa yace "assalamualaikum "wa alaikumussalam" momy ta amsa tare da cewa"Dan halaq yanzunna muke zancenka,nakecewa juneid yaje yadubamin Kai lafiya"Murmushi Habib yay yace lafiya kalau momy kawai da saliha ce take tsoron zama agida ita kadai shiyasa nake zama, Kuma dama yau ko Baki kirani ba zanzo domin na gaisheki" jum Junaid yayi Yana tunani anyakuwa ba akwai wata matsalar ba Amma dai shikkenan zai tambaya yaji, tashi yayi tsam ya nufi sama tare dacewa Habib idan kungama gaisawa da mom inason ganinka," okay Babu damuwa "yafada tare da zama a gaban momynsa yace " momy Ina wuni "lafiya kalau abee Ina matar taka kunanan dai lafiya?" Lafiya kalau Alhamdulillah momy" yayi maganar tare da sunnar da Kai.

Zama sukai shuru aguri,tako momy ta zubawa danan ta ido ganinn yadda duk yacanza yayi Baki ya rame sai kace mejinyar kanjamau, gyran murya tayi sanan yace abee a kwanakin Nan Ina fuskantar yanayinka Naga gaba daya duk ka canza meyake faruwa ne? Banaso ka boyemin komai nifa mahaifiyar kace jibi fa duk yadda ka lalace kamar ba Dana Habib ba ,kai da ake ganin ango acikin walwala da annushuwa, dakuma farinciki ,har ma aga yayi kiba yacanza, amma Naga Kai angoncin naka nadaban ne daga ace yau yau kana gadon asbiti, sai ace jibi baka da lafiya gata Kuma naganka ajare" kwallar da ta cicciko ce a idon Habib ta karasa jubowa,ya bude Baki da niyyar yin magana yasaki kuka kamar karamin yaro' Nan take hankalin momy yatashi Dan tun da take da Habib rabon dataga yayi kuka har tamanta sai dai shi yabawa wani kuka,Amma waiyyau shine agabanta take zubar da hawaye sabi da wani abun" habibu fadamin meyake faruwane ? Momy najawo wa kaina masifa da bala'i naje na auro"yar aljanu Dan Allah momy ki taimakeni kice Mata na mutu,Kinga saiki boyeni Dan Allah kinji momy "what!!!!!! "Yar aljanu Kuma bangane inda kadosa ba Habib nifa banfahim ci zancenka ba, kafahim tar Dani akan wa kake magana?" Momy akan saliha mana matata, kiyi hakuri momy banfada miki abin dayasa na takura sauna auri yarinyar Nan ba,kintina wata yarinya da tacemin kashin kare yafini daraja !!!!! "Eh natuna Habib fahimtar Dani saime yafaru "momy nikuma shine naki hakura sai danasan yadda nayi na aureta domin na Rama abin da taimin, Ashe aljana ce dan Allah momy kitaimakeni zata kasheni wallahi ki boyeni kice na mutu" "kujini da shashan rayo sawani abu kake kamar danshekara 10 d'Allah kadawo hayyacinka mana"Kai nake fadawa kabi duniya a sannu, bakomai ne ake ramawa ba dagacikin imanin mutum, akwai haruri amma Kai bazakaji fada ba ida anmaka ko, ka adole dangidan shahararren mekudi, to Bari kaji abee anyi Wanda yaninka mahaifinka kudi mutumin da yakasance besan adadin kudadensa ba,kafadamin ina yake yanzu Hatta iyalansa ina ganin basa aduniyar nan koda tashin labarin su bakaji ayanxu habibu kaji tsoron allah sannan karike addu,,a idan Kai Haka babu abin da zaisame ka"katashi kabani guri dan ni banyarda da wannan zancen nakaba"... Tashi Habib yayi jiki babu kwari tanufi sama gurin yayansa juneid,Yana shiga yasame shi zaune a gefan gado,ya kurawa computer ido, sallama yayi masa sannan ya karasa yanemi guri gefansa ya zauna" yace " Yaya juneid Ina yini "lafiya kalau Habib " yauwa Daman sonake na tambayeka kafin na zo katsina kacemin bakason matarka Kai Sabi da daukar fansa ka aureta dan karama abin da taimaka" nadan zaku iya shiryawa kukoma rayuwa cikin farinciki kamar kowanne ma'airata "bana tunanin kaidai Habib zaka iya hakura kafadamin gaskiya menene yake faruwa agidanka" nasan Haka kurum bazaka kizuwa gidaba bayan kasan bani da lafiya"bama hakaba jibi yadda kabi karame kayi Baki ,Uhm. Habib yayi murmushi yace Yaya kenan bawani Abu bane kawai dai itace take jin tsiran gidan shiyasa bana zuwa nake zama nakula da ita, "dariyace ta kubucewa juneid wadda bemasan lokacin da tafito ba yace "Habib nizaka rainawa hankali bayan nasan ka nasan halinka,Kai tunkafin kazo duniya nazo ta narigaka shan iskar duniya idan zaka fadamin gaskiya kafadamin idan kuma bazaka fadamin ba gahanya nan Allah ya Kara dankon kauna da kurawa "Allah ya barku tare har'abada " what!!! ba aminba Yaya "wallahi sai yanxu natabbatar baka Sona Kai makiyi nane " bangane nu makiyinka bane addu,a fa namaka me kyau"to indai wanan addu'ar ce banaso ni dazama da waccan aljanar har abada bazamu taba zama guri dayaba ,Kai bakasan akan Kaya nakeba shine har dacewa Allah ya barmu tare ,badai Nina wallhai sai dai inkai allha ya barku tare.....

Hhhhhh juneid yayi dariya yace uhm ni dama nasan akwai abin dayake faruwa ,allah sarki dan,uwa kayi Shirin mugunta Kuma abin yakare akanka ,kaikana abinka Ashe aljana ka auro,to Allah ya kiyaye gaba " au yanzu ya juneid abin da zakace kenan kanagani fa yanzu jirana ma take na koma na Dora mata abincin dare yakarasa maganar kamar zaiyi kuka, "hm Habib ni kam babu abin da zan iya cemaka yanzu Dan komai ya faru da Kai kaka jawa kanka, abun da zance maka shine kacigaba da hakuri har lokacin da Allah zaisa tagane gaskiyar kaimijinta ne tafara maka biyya"me wai ni inzaman aure da karuwa allah ya kiyaye inazauna da ita zaman aure ni ka batamin rai wallahi Kai kullum nazo gaisheka sai ka batamin rai,Yana gama fadar Haka ya Mike tsaye yanufi hanyar fita....

********************************abangaren anisa kuwa tanemi yafiyar mahaifiyar ta sunciga ba da zamansu subiyu rayuwarsu sukeyi cikin farinciki da annushuwa musamman yadda hajiya adama taga "yar Tata ta hakura da auren juneid da Habib sai itama hankalinta ya kwanta.

To yau kamar kullum suna zaune a falo suna Hira Anisa ta kalli mahaifiyata tace "Mami "naam Anisa"inason nakoma school nayi digiri tunta dai yanzu Naga ba aure zanyi ba, inason asamamin konda makarantar kwanace a zariya ko kano naje nayi digiri, Ina tinanin zanfi maida hankali nayi karatu can Kuma hankalina zaifi kwanciya, shiru hajiya adama tayi,nadan wani lokacin daga baya kuma ta dago ta kalli anisa tace" Tom shikkenan anisa zan duba magani zuwa gobe idan abin zaiyuwu" murmushi anisa tayi tare da cewa Allah ya nunamana goben darai da lafiya....

8..

__________________Tom bayan Habib ya Isa gida,azaube ya samu saliha ta sha kunu,ta hade girar sama data kasa Tana jiran dawowar sa,Yana shiga yayi sallama" shiru bata amsaba saima masifa da ta fara masa da kwandon bala'i tace"Habib Ina kaje ,banace kadawo dawuri zaka doramin abincin dare ba,saibi da tsabar ka ajiye shanyani sai karfe ,10 na dare zaka dawo Ina katsaya" Tana magana Tana hura hanci kamar wata uwarsa,Habib kam zuwa yanzu yagama tsorata da lamarin saliha, sannan ya fahimci inda ta dosa,sotake kawai ta kashehi ta huta,to ko indai hakane maganarsa gwara ta kasheshi kwai ya bi masoyiyarsa hankalinsa yafi kwanciyar" saliha kuwa ganin yadda ya tsareta da ido Yana kallonta ne yasa tace" Habib tunanin mekakeyi da bazaka iya cemin nayi hakuri ba!!! Rausayar da muya yayi yace"Dan Allah kiyi hakuri hajjajuna wallahi ban iya girki bane,shiyasa naki dawowa da wuri,ni abu buyu naiya girkawa daga taliya sai indomi, bayannan ban iya komai ba, Dan Allah kiyimin afuwa kafin inshigo gidannan sai da na tsaya gurin wani maisai da abinci natambayeshi idan zai koyamin,kuma yace zai koyamin gobe na fara zuwa..

Memakon wannan abin da yayi yasa saliha ta tausaya masa ,saima ta juyar da kanta gefe tasaki murmushi tace "Allah ya kaimu, oya muje mu kwanta,"agigice Habib ya dago ido ya kalleta yace,"mukwanta Kuma Aina zan kwanta tab Allah ya kiyaye na kwanta dake"

"Au Allah yakiyaye ma zakace "banace kadainamin taurin kaiba,saikuma na dagaka na doka dakasa kafi kowa zama abin tausayi"to ba irin kwanciyar aure nake nufiba ,Wace zata Kwanta da Kai Allah ya kiyaye Nima na kwanta da Kai gado daya,Kai da ba mijina ba kaifa bawanane ,yanzumma bautar zamuje kayimini bawani abuba ay bacci agidannan kadainashi, zamuje ka dauki mifici kamin furfita harnayi bacci"

"Furfita fa kikace, naga akwai fanka adakin sannan akwai AC meyasa bazaki kunnaba "

"Banyi ra,ayiba kuma bansaba da fanka ko AC ba gidanmu babu damifici nake fifita agida Dan Haka Dole kamin furfita da wayasa kaje hargidan iyayene ka dakkoni dan bazance auroni kaiba, idan da kasan bazaka jurewa wahalaba da baka auro "yar talakawa ba, kaje ka auro "yarmasu kudi,wadda ubanta ya Tara,Kai nifa bada banba ma sainace aje ayo odar sauraye akawomin sudinga cizona sabi da nasaba kwana acikinsu, wallahi ko kazaba na kaika dakin kiwona da kasa Aka ginamaka/ kokuma ka kwana kanamin furfita,zabi daya...

Runtse ido Habib yayi ya bude tare da furzar da iska daga bakinsa, ya daga Kai ya kalli saliha wadda ke tsaye ta kuramasa ido Tana kallonsa Tana hura hanci,uhm yayi murmushin karfin hali yace" shikkenan naji Zan kwana adakin can Amma ni bazan kwana inamiki furfita ba" oky tafada tare da juyawa ta dauki Kee din dakin tafita Habib Yana gaba Yana binsa abaya harsuka karasa wannan dakin me duhu Wanda Habib yasa Aka Gina domin kiwon saliha ,bude dakin tayi yashiga,sannan ta kalleshi tace,"to habibty na sai dasafe ko "batare da tajira me zaiceba ta datse dakin da kwado ta juya jiki Babu kwari tashiga part di ta,daki tashiga ta dakko fulo tadawo falo ta kwanta ,runtse idonta tayi,amma ta kasa bacci,kawai sai ta Mike Zane ta hada Kai da gywa tasaki kuka,tana tunanin irin halinda habib zai shiga awannan dakin mekama da kurkuku,Harcikin zuciyarta tana tausayinsa Amma Babu yadda ta iya dolene ta koyamasa tarbiya tun da tafuskanci islamiya bata ratsashi ba...
Chapter 6 · 0% Book details