← Book details Makaho Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 8 OF 11

Part ɗin kakarsa Inna ya nufa da sauri.

Makaho Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read

Knocking yake yi a kofar bedroom ɗin ta, cikin barci ta ji bugun ƙofa.

"Waye?"

"Dan Allah Inna ki zo da sauri."

Jin Muryar Fahad ya saka mike da sauri tana kunna hasken torch light din wayar ta. Domin ta san ba lafiya ba duk yadda aka yi .

Buɗe ƙofar ta yi tana kallonsa ta ce.

"Lafiya kuwa Majidaɗi?"

"Ki zo don Allah Inna."

Ba tare da ta sake wata magana ba ta bi bayansa zuciyarta cike da fargaba.

Suna zuwa falo ta kalli Sidra dake kuka ta ce.

"Me ya same ta ne.?'

Ta yi tambayar tana kallonsa .

"Inna ki zo don Allah."

Ya ja hannunta suka nufi upstairs ɗin.

Daga falo ya tsaya ya ce ma ta ita ta shiga ciki.

Duk da ba ta san mene ne dalilin sa ba haka ta shiga ciki zuciyarta cike da wasu-wasi.

Tana shiga idanunta ya sauka akan Nadra dake kwace kan gadon ga jini a ƙafarta har ya ɓata zanin gadon.

",Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. La'ilaha ilallahu Muhammadu Rasulullah Sallallahu alaihi wasalam. Cikinta ne ya zube. Ka yi sauri ka..."

"Ba cikin da take da shi Inna. A taƙaice dai yau ne daren farkon mu da na kasance da ita."

Abubuwa biyu suka haɗu wa Inna lokaci guda, farin ciki da kuma baƙin ciki. Farin cikin na kusantar ta da ya yi, na biyu kuma na baƙin cikin yadda Fahad ya yi wa Nadra daga gani ta sha wahala sosai."

Ba ta yi magana ba ta ɗauki wayarta ta ta kira lambar wayar Mama.

Bugu biyu a na uku ta ɗaga tana cewa.

"Inna lafiya kuwa?"

"Wani lafiya Ɗan ki yana neman yin kisan kai."

Ras gaban Mama ya faɗi ta tashi a firgice tana cewa.

"Me ya yi Inna?"

"Ki zo ɗakinsa ki gani."

Da sauri ta diro daga kan gadon ko takalmi ba ta samu damar saka wa ba ta fice zuciyarta cike da fargaba abun da za ta tarar.

A falo ta samu Sidra na kuka kamar za ta tsaya wajenta amma hankalinta na kan kiran da Inna ta yi ma ta.

Fahad kam tun da ya ji tereren da Inna ta yi ma sa na kiran Mama sai ya ji kunyar Mahaifiyarsa. Don haka kafin ta zo ya sulale ya nufi part ɗin baƙi na gidan.

Inna tana nan tana jiran isowar Mama.

Da sallama Mama ta tura ƙofar ta shiga, ba kowa falon don haka ta nufi bedroom ɗin.

Nan ta ga Inna tsaye kafin ta yi magana ta hangi Nadra kwance a gadon kamar gawa.

Sai da zuciyarta ta harba.

"Me ya same ta haka ta zubar da jini?"

"Ba dole ba saboda rashin imani irin na ɗanki kalli yadda yayi wa wannan ƴar ƙaramar yarinyar aika-aika kamar ya samu guzuma."

Sai da ƙwallar tausayin Nadra ya cika idanun Mama, cikin sanyin jiki ta karasa gaban gadon tana cewa.

"Inna don Allah ki taimaka ma ta mana."

"Ai dole na taimaka ma ta na kira ki ne ki ga abin da ke faruwa."

Inna ta kalli Mama ta ce.

"Ina zuwa bari na je na hado ma ta magungunan da za su taimaka ma ta yadda za ta warke da wuri kuma raɗaɗin ciwon zai ragu kuma za ta koma ta matse.

Tana faɗar haka ta juya ta fice.

Mama ta karasa gaban gadon tana kallon fuskanta da ta bushe da hawaye idanunta sun kumbura.

Cike da tausayin yarinyar Mama ta shafa gefen fuskarta tare da cewa.

"Kiyi hakuri Daughter, Allah ya ma ki albarka."

Mamaki take yi saboda Rumaisa da Sahiba sun sanar da ita cewa Fahad ya kusanci matarsa har ba ta iya tafiya to dama karya suke yi ko me?

Fridge ta buɗe ta ciro robar ruwa ta zuba a bakinta ta fesa wa Nadra a fuska da ƙarfi.

Wani gawurtaccen ajiyar zuciya ta sauke tare da fashewa da kuka tana cewa.

"Ya Fahad wallahi zan iya mutuwa."

Tana fashewa da kuma mai tsuma zuciya, daidai dai lokacin da Inna ta shigo cikin ɗakin.

Mama ta kalli Inna ta ce .

"Ta farfaɗo."

"Ma sha Allah, yanzu na haɗa magungunan na ɗora a wuta ki duba a cikin kitchen dake cikin part ɗin nan idan tkya tafasa ki zuba a roba ki kawo mana a banɗaki."

Jin muryoyin su ne ya saka Nadra ta gane ita da su waye a ɗakin. Kuka ta saka masu tana rike hannun Inna tana cewa."

"Inna ki taimaka ma ni ba zan iya tashi ba, wajan Ummata zan koma."

Ta yi maganar tana sake rufe jikinta da bargon da Fahad ya ɗan rufa ma ta.

Mama ta je duba maganin inda ta tarar yana tafarfasa.

Ta juye a wani roba dake cikin kitchen ɗin ta ta bar sayyun magungunan a tukunyar.

Ta kashe gas din ta fito ta wuce zuwa bathroom na Fahad ta ajiye . Inna ta biyo bayanta ta karba ta zuba a roba mai faɗi. Sannan ta zuba wani garin magani dake hannunta.

Sannan ta fita Mama ma ta fice .

"Za ki iya tafiya?"

Cewar Inna tana kallon Nadra.

"Mu taiamaka ma ta dai ."

Mama ta fada tana budar bathroom, ba jimawa ta fito rike da babban towel ta mikawa Inna.

"Ki ɗaura ma ta Inna."

Inna ta amsa ta shigar da shi cikin bargon sannan ta ɗaurawa Nadra.

Sai da suka rirriƙe ta ƙafarta na rawa ta taimakon su suka kai ta banɗaki.

Daga nan Mama ta fita daga bathroom ɗin.

Bayan Inna ta tabbatar da ruwan ya yi daidai yadda take so ta zaunar da Nadra a ciki.

Wani azababben zafi ta ji ya ratsa ta wanda ya sa ta saki ihu. Tana shirin miƙewa tsaye kenan Inna ta danna ta a cikin ruwan wanda hakan ya saka ta sakin kuka tana girgiza kai.

Cikin tausayawa Inna ta ce.

"Na san akwai zafi sosai amma idan kika ɗaure wannan ruwan maganin zai taimaka ma ki wajen warkewa da wuri kuma zai sa ku koma ki matse yadda za ki sake martaba a wajen mijinki."

Ita kam ba ta ma san me Inna ke cewa ba sai aikin kuka kawai da take yi.

Sai da ta ɗauki mintuna talatin a cikin ruwan kafin Inna ga canza ma ta ruwa, sai da ta tabbatar da cewa ta haɗa ta yadda ya kamata sannan ta ce ma ta ta yi wankan tsarki.

Ko da Inna ta fito ta tarar da an cire wannan zanin gadon an sauya wani sabo.

Tana tsaye tana jiran fitowar Nadra, sai wayarta ya soma ruri, tana dubawa ta ga Fahad ne, tana dagawa ya ce.

"Inna idan kun gama ga magani nan na ajiye ma ta."

Jin haka ya sa ta gane cewa shi ne ya shigo ya gyara gadon ya ajiye magani.

Nadra ta fito ɗaure da towel babba a jikinta. A hankali take tafiya ta ji saukin jikinta sosai don tafiyar ta fi ba ɗazu kyau.

Da kanta ta ɗauko doguwar riga a cikin akwatin kayan da Fahad ya siyo ma ta. Rigar ba ta da nauyi sai pant da ta saka.

Kanta ne ke ciwo ga wani barci da ke fisgarta.

Da taimakon Inna ta kwanta a kan gadon yayin da Inna ta ja ma ta bargo tana yi ma ta sai da safe ta fice.

Lokacin karfe huɗu da kwata na asuba.

Dai da barci ya dauke ta sannan Inna ta bar part ɗin.

Duk abinda ke faruwa akan idanun Fahad dake kallon su ta wayarsa.

Lokacin da ya ga Inna ta fice shi na ya bar part ɗin baƙi ya dawo part ɗin nasa.


*Maman Ihsan ce*✍️


09065327995

*MAKAHO NE*


*NA*

Maman Ihsan ce ✍️


*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION*


Page4️⃣2️⃣


Duk abin da ke faruwa a kan idanun Fahad dake kallon su ta wayarsa.

Lokacin da ya ga Inna ta fice shi ma ya bar part ɗin baƙi ya dawo part ɗin nasa.


_Makaho_

Kwance yake a wani katafaren ɗaki, wanda aka ƙawata shi da kayan alatu Yana kwance saman wani haɗaɗɗen gado wanda aka shimfida tsadadden zanin gado.

A hankali ya fara motsawa, hannun sa ya sa ya dafe kansa dake tsananin sara ma sa.

Wani baƙon ƙamshi da sanyi ne yake ratsa shi. A hankali ya kai hannunsa yana shafa in da yake kwance. Jin laushi ya sa ya tashi zaune yana lalube.

Har kan royal bed ɗin ya shafa ya tabbatar akan gado yake, kuma ba katifar Ma'eesha ba ce.

A hankali abinda ya faru ya fara dawo ma sa a kai. A zabure ya miƙe tsaye yana lalube. Ji ya yi an rike ma sa hannu tare da cewa.

"Ka yi a hankali don Allah jikinka ba ƙarfi."

Cikin ɓacin rai ya ce.

"Meye matsalar ku da ni ne?"

"Ba mu da matsala da kai gaskiya, hasali ma ceton rayuwarka muka yi daga wajen waɗan da suka kama ka, da ba don mun je a kan lokaci ba da sai sun kashe ka."

Shiru yi yi na ɗan lokaci kafin ya nisa ya ce.

"Mutuwa lokaci ne, duk wanda ya mutu kwamansa ne suka ƙare, duk yadda suka so kashe Ni idan kwanakin mutuwa ta ba su cika ba ba su isa su kashe ni ba ko babu ku kuwa, haka kuma idan kwana na suka ƙare ko second ɗaya ba zan kara a duniya ba zan tafi, don haka idan mai kisa ya yi hakuri wanda zai kashe zai mutu. Don haka yanzu zan koma gida na san waɗan da suka damu da ni suna can cikin tashin hankali da damuwa na rashin gani na."

"A gaskiya ka yi yi hakuri yallabai ba zai yiwu ka fita cikin wannan daren ba, sai da safe in sha Allah za mu mayar da kai cikin aminci ."

Table da aka jera abinci ya janyo ma sa ya ajiye ma sa a gaba.

"Ga abinci nan, a gabanka, idan ka mike hannun damarka kuma toilet ne ko da kana bukatar shiga ciki sai ka shiga."

Juyawa ya yi ya bar ɗakin ba tare da ya sake yin magana ba.

Kamar yadda ya ce ma sa kofar toilet na ta hannun damar sa haka ya mike yana lalube har ya ji kofar sannan ya tura ta ya shiga.

Ba jimawa ya fito da alama alwala ya ɗauro ya fito.

Yana fitowa ya ji an ce


"Ga sallaya nan."

Aka rike ma sa hannu zuma saman sallayar.

"Karfe nawa yanzu ?"

"Karfe biyu dare ne?"

Bai sake yin wata magma ba ya fara gabatar da sallolinsa.

Bayan ya idar da sallolin ne ya ya yi addu'o'i sannan ya tashi. Ya sake jin Muryar mutumin na cewa

"Allah ya karba ya bada lada."

"Bai amsa ma sa ba ya ji ya rike ma sa hannu yana cewa

Suka karasa bakin gadon sannan ya zauna sannan ya janyo ma sa karamin table da aka jera ma sa abinci akai.

"Bismillah ka ci abinci."

"Ba zan ci komai ba."

"Me ya sa yallaɓai?"

Kwanciyarsa ya yi ba tare da ya ce ma sa komai ba, domin ya san cewa Ma'eesha na can cikin damuwa ba za ta iya cin abinci ba, don haka shi ma ba zai ci abinci ba."

Duk yadda aka dinga rarrashin sa bai motsa ba, dole ya fita ya bar ma sa ɗakin.


_Ma'eesha_

Da sallama ɗauke a bakinta ta shiga cikin gidan. Cike gidan yake da mata da yara. Wasu Na hura wutar murhu wasu na share kofarsu wasu na wanke-wanke wasu na zaune ba sa komai yayin da yara kuma suna wasa. A hankali ta sauke idanunta kan kofar ɗakin da makaho ya kai ta a matsayin ɗakinta, wanda ta kasa zama, har lokacin yara na zaune kofar dakin sun jeru a dama Po suna bayan gida.

"Lale marhaba da zuwan matar makaho."

Cewar Larai Dillaiya kenan.

Baba ta fito daga ɗakinta tana washe baki ta ce.

"Amarya sannu da zuwa, ke ce da safiyar nan?"

Murmushi Ma'eesha ta yi tare da durƙusawa ta yi ta gaida Baba.

Ta amsa mata cike da farin ciki.

Ta gaida sauran matan gidan suka amsa mata cikin dakin fuska.

Baba ta yi murmushi ta ce.

"Ƴata ko za mu shiga daga ciki ne?"

Ma'eesha ta kalle ta tana murmushi ta bi bayanta suka shiga ciki.

Bayan ta shimfida ma ta tabarma ta zauna ne ta ce.

"Yanzu kuwa Liman ya fita yana cewa wai ya ji ana raɗeraɗen an kama Khalifa mijinki juya da yamma, shi ma bai sani sani ba sai yau a masallaci yake ji da asuba. Har ya ce na je na duba ki. Ina shirin fita ne sai na ji na uryar ki."

Murmushin karfin hali Ma'eesha ta yi kafin ta ba ta labarin abun da ya faru, kafin ta kara da cewa.

"Yanzu ina jiran ɗan anjima ne na koma wajen ƴan sanda. Amma kafin nan ina son ki bani aron jikar ki A'isha ta nuna mani yadda ake kunna wutar murhun gawayi ne."

Dariya sosai Baba ta yi kafin ta ce.

"Ba ki iya ba ne dama?"

"Eh ban ma taɓa gwadawa ba sai yau, na fi gane wa Gas ne don shi na taso na gani a gidanmu."

Cike da tausayinta Baba ta ce.

"Allah Sarki rayuwa kenan, wannan ma zai wuce in sha Allah."

Ta mike ta fita waje tana kiran Mahaifiyar A'isha. Matar ta shigo dakin Baba suka kara gaisawa da Ma'eesha, kafin Baba ta ce .

"Ina A'isha?"

"Ba ya dawo daga islamiyya ba amma yanzu na san suna hanya."

"To dama za ta je ne ta taya Matar Khalifa wani aiki a gidanta."

Daidai lokacin A'isha ta yi sallama ta shigo cikin gidan.

"Ma sha Allah gata nan ta dawo."

"Assalamu alaikum."

Ta yi sallama ƙofar ɗakin kakarta ta shigo.

Ganadaya suka amsa mata ta shigo ciki, tana ganin Ma'eesha ta faɗada fara'ar ta ta ce.

"Aunty sannu da zuwa."

"Yauwa A'isha ya kike?"

"Lafiya lau Alhamdulillah."

Daga nan ta gaida kakarta da mahaifiyarta. Sannan Baba ta ce ta je ta taya Ma'eesha aiki."

Jakarta da Alqur'ani ta ajiye ta bi bayan Ma'eesha suka fice bayan Ma'eesha ta yi ma su sallama.

Suna tafiya suna fira a hanya duk da dai Ma'eesha ƙarfin hali kawai take yi, damuwar dake zuciyarta ma kaɗai ta ishe ta.


_Fahad_

Shigowarsa kenan bayan ya bar part ɗin baƙi. Tsaye yake yana ƙare ma ta kallo.

Karon farko a rayuwarsa ya ji wani abu game da ita a zuciyarsa.

A baya baya jin komai akanta a zuciyarsa, amma a yanzu da wani mu'amala ta shiga tsakanin sa da ita sai yake jin ta a gefen zuciyarsa, tabbas ba zai iya cewa ya kamu da soyayyar ta ba amma kuma ya ji yana tausayin ta a zuciyarsa. Sam ya kasa gane dalilin da ya sa har ya ji ya kwaɗaitu da son kasancewa da ita ba. Wanda ko bayan aurensu bai taɓa saka wa a ransa akwai ranar da wata mu'amala ta aure ya haɗa shi da ita ba, kwata-kwata babu wanann a tsarin zamantakewarsa da ita ita, amma lokaci ɗaya komai ya sauya ya ji ba zai iya hakuri da ita ba.

Shafa gashin kansa ya yi har zuwa gefen kwantaccen sajensa zuwa gemunsa. Yana jin nishaɗi sakamakon tuna yadda ya tsinci kansa a yanayi dai bai taɓa jinsa a ciki ba sai dalilinta. Ta mallaka masa mutuncinta da ƙimarta da darajar ta na ƴa mace, wanda a wannan zamanin ba kowace mace ba ce ke kai mutuncinta gidan aurenta ba.

Murmushi ya saki yana nufar bathroom.

Jallabiyar jikinsa ya cire yana tsaye gaban madubi yana kallon jikinsa. Idanunsa suka sauka akan damtsen hannunsa zuwa gefen ƙirjinsa da ke da sunan Sidra. Ɓacin rai ya ji ya ziyarce shi lokacin guda.

Shower 🚿 ya sakar wa kansa idanunsa suna sauya kala zuwa ja.

Take ɓacin ran da Sidra ta cusa ma sa ya dawo ma sa sabo.

Har ya gama ya ɗaura towel da wani karamin towel a hannunsa yana tsane gashin kansa.

Alwala ya ɗauro ya fito daga bathroom ɗin.

Jallabiya ya saka ya ya gabatar da sallolin nafila.

Sai da aka kira sallar asuba ya tashi zai tafi masallaci ne ya kalle ta.

Yana son ya tayar da ita amma yana tsoron tashin ta.

Fita ya yi ba tare da ya tayar da ita ba ya nufi masallaci.


Cikin barci ta ji ana sallah a masallaci, Kasancewar ta saba tashi a daidai wannan lokacin, to da zaran lokacin sallah ya yi duk nauyin barcin da ke kanta sai ta farka daga barci.

Tashi ta yi daga kwancen har lokacin tana jin jikinta na ma ta ciwo sosai, sai dai ƙasanta ya rage zafin da yake yi ma ta.

A hankali ta fara tafiya ta nufi bathroom.

Gasa jikinta ta sake yi da ruwan ɗumi sannan ta yi wanka ta fito

Wata doguwar riga mara nauyi ta saka ba ta tsaya sa komai ba ganin Lokaci sallah ya tafi.

A daddafe ta yi sallar asuba ta yi wasu azkar ɗin sannan ta koma ta hau gado ta kwanta. Don ko karatun Alkur'ani da ta saba yi kowace safiya yau ba ta samu damar yi ba ta shige cikin bargo.

Lokacin da gari ta fara haske Fahad ya dawo daga masallaci.
Chapter 8 · 0% Book details