← Book details Makaho Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 4 OF 11

Part ɗin su ta koma ta samu Mummy na waya Da Daddy, sai da ta bari sun gama sannan ta kalli Mummy ta ce.

Makaho Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 84 min read

"Mummy hankalina bai kwanta da wannan matar ba, don Allah idan taimakon su za ki yi ki ba su kudi su je su nemi haya su zaiuna, ki ba su kuɗin da za su ja jari amma ba na son zaman su a nan."

Shiru Mummy ta yi tana nazarin maganar ƴarta, ita dai iya sanin ta da Ma'eesha ba ta da ƙyamatar mutane duk yadda suka kai ga lalacewa kuwa. Ta san darajar Ɗan Adam Sosai, amma sam ta rasa dalilin da ya sa hankalinta ya kasa kwanciya da mutanen nan. Cikin sigar rarrashi ta ce.

"Shi kenan zan yi tunani akan hakan, amma ba kya ganin ita nan ta nemi mu ba ta ta zauna ba wai a ba ta kudi ta je ta nemi haya ba?"

"Eh na sani Mummy, amma ba ta da hujjar cewa anan dole za ta zauna, ai taimako ne ko gida aka ba ta a wata unguwar za ta zauna ai."

"Je ki huta za mu yi maganar daga baya."

Tashi ta yi ta nufi bedroom ɗin ta cikin sanyin jiki.

Haka nan su Mamy suka ci gaba da zama cikin gidan, ba abinda suke yi a cikin gidan, kullun da safe ma su aiki za su mai ma su abincin breakfast a part ɗin. Sannan da rana ma a kai ma su can part ɗin haka dare za'a kai ma su .

Ranar da suka cika sati daya a ranar ne Daddy ya dawo daga tafiyar da ya je.

Bayan ya yi wanka ya ci abinci ya huta ne Mummy ta ba shi labarin Mamy da yaranta da yadda suka yi . Kallon ta Daddy ya yi tare da cewa.

"Kin san daga ina suka fito ne?"

"Ban sani ba wallahi, amma dai abu ɗaya na sani shi ne suna bukatar taimako kuma na taimaka ma su."

"To yanzu ya kike son a yi da su?"

"Duk yadda ka ce haka za'a yi yallaɓai."

Murmushi ya yi sannan ya ce.

"A'a duk yadda kika ga ya dace sai ki yi na ba ki wuƙa da nama."

"To me zai hana mu zauna da su a nan gidan?"

Ɗan jim ya yi kafin ya ce .

"Nan gidan kuma?"

"Eh yallaɓai, na ga kamar tana son zama nan ne, don ba ta ce a ba ta wani gidan ko kuɗin siyen gida ko haya ba. Sannan kuma ai tana can BQ ba nan za ta zauna kusa da mu. "

"To ai ba ta da zaɓi muhalli take nema da Abinci, idan ta samu ko ina ne ina ne ai buƙatar ta dai ta samu mu abun da take nema."

"Haka ne, amma zan so a ce ta zauna kusa da mu, tana da yaro saurayi idan bai yi karatu ba sai a saka shi kasuwanci. Macen kuwa sai a saka ta a makaranta."

"Shi ke nan Allah ya mana jagora."

Da Anin ta amsa daidai lokacin da Ma'eesha ke ƙarasowa fakon hannunta da karamar jaka ta fito daga wajan kakarta da ta je yi ma ta weekend.

Ganin Dad ɗin nata ta saki jakar cike da murna ta karasa wajensa ta rungume shi.

"Daddy yaushe ka dawo ba wanda ya sanar da ni?"

"Yau na dawo Mamana ya kika bar su Hajjaju."

Da yake sunan da suke kiran da shi kenan.

"Hajjaju na can na bar ta da masifarta."

Mummy da Daddy a tare suka yi dariya.

"Daddy idan na masifa ba ta za ta ce wai na je na kwaso sauran kayan na dawo gidan nan da zama?"

"Yaushe aka yi hakan?"

Cewar Mummy tana kallon Ma'eesha, duk da ta san cewa Hajjaju ba ta ƙaunar ta har yanzu kuma ba ta nuna ma ta tsana yanzu, domin soyayyar da take yi wa jikar ta ya ɗan saka ya shafi mahaifiyar ta. Domin tana ƙaunar Ma'eesha sosai kamar ranta, ko don Ma'eesha kadai ce jikarta ɗaya da ta fito daga tsatson tilon Ɗants guda ɗaya da ta mallaka a duniya, ga shi ɗan nata shi ma Ma'esha kadai ya mallaka a duniya. Don haka tana ƙaunar Ma'eesha amma ta kasa ƙaunar mahaifiyar Ma'eesha har yanzu , amma tana amsa mata ba yabo ba fallasa idan ta zo gaishe ta sai dai ba ta wani sakin jiki da ita. Ita ma kamata Mummy yanzu abun ya daina damunta.

"To ai ba wani abu idan kin koma gidan nata da zama?"

Cewar Mummy tana Murmushi.

"To idan na koma can da zama ku fa ai ba ku fa kowa a nan, sai ku zauna haka daga ku dai ma su aiki?"

Murmushi Mummy ta yi tana cewa.

"Daga mu sai ma su aiki mana, to su ba mutane ba ne, ga kuma ƙarin wasu ƴaƴan na samu saurayi da budurwa."

"Ok ina suke?"

"Baƙin da kika raka su BQ nake nufi."

Take fara'ar dake fuskarta ta ɓace ɓat.

"Mummy please a ba su wani gidan su zauna can a ba su abinci, amma jikina ya na ba ni zuwansu gidan nan ba alkhairi ba ne.,"

"Ban san me ya sa ba ki ƙaunar mutanen nan ba."

Shiru Ma'eesha ta yi don a ya san me za ta ce ba. Don haka ta mayar da hankalinta ga Daddy ta ce.

"Daddy me ka dawo ma ni da shi tsarabar tafiyar ?"

"Mamana komai na kawo ma ki sai abin da ba ki so ne kawai ban siya ba."

"Thank you so much Daddy."

"You are welcome ."


Daga nan rayuwa ta cigaba da tafiya a hankali sabo da shaƙues ya fara shiga tsakanin Mummy da Mamy. Don ta sa Daddy ya kai Jamil kasuwa a ɗaya daga cikin shagunan ta yana siyar da kaya. Laila kuma an saka ta a makarantar secondary school kasancewar ta gama primary.

Sannu a hankali shaƙuwa ta fara shiga tsakanin Mummy da Mamy wanda kullum a bangaren Mummy mamy ke wuni kullun suna tare, Mamy kan bar BQ ta zo nan main house din su yi ta fira da da Mummy. Tun Ma'eesha ba ta sakin jiki da Mamy har yau da gobe yadda Mamy ke jan ta a jiki ta saki jiki da ita amma ba sosai ba.


Wata ranar talata da misalin karfe biyar na yamma Mummy ta dawo daga kasuwa, sai dai ba tare da dirbanta take ba ita kadai ce take driving. Don ranar direban bai da lafiya yana gida ta ce ya huta.

Kasancewar yanayin unguwar ba yawan mutane da yawa. Tana tsaka da tafiya ta ga mutum ya tsaya a gaban motarta, cikin azama ta taka birkin motar. Su biyu ne suka zagayo gefen me zaman banza ya zauna yana nuna ma ta wuƙa yana cewa.

"Ki bi umarnin da zan ba ki."

Daidai nan ɗayan ya shiga bayan motar ya zauna suka nuna ma ta hanyar da za ta bi, wanda ba ta da wani zaɓin da ya wuce bin maganar su.

Duk hanyar da suka nuna ma ta nan ta bi har suka shiga unguwar da ba mutane don sabbin gine-gine ne a unguwar su ma ɗaiɗaiku ne ba da yawa ba.

"Tsayar da motar."

Ta tsayar suka fito suna waige-waige.

Fitowa suka yi sannan suka ba ta umarnin ta fito ita ma. Fitowa ta yi tana rokonsa da kada su cutar da ita. Don ba ta san nufin su akanta ba, sun yi yi haka ne don su kawo ta wajen da na mutane su kashe ta ko sun yi haka ne don su yi ma ta ƙwace.

Tana ganin wata zabgegiyar wuƙa da suka fito da ita ya sa ta ruga a guje, ganin haka suka mara ma ta baya a guje suka bi ta.

Tana cikin gudu duk ta gaji ga numfashinta kamar za su ɗauke ta ji ta yi karo da mutum a gabanta.

Sai a lokacin ta lura da mutumin da ta yi karo da shi. Saurayi ne maji ƙarfi yana da siffa irin na zaratan maza. Bayansa ta laɓe tana rike rigarsa ta baya, domin ba za ta iya cigaba da gudu ba.

"Saurayi don Allah ka taimaka ma ni kada su cutar da ni."

Dariya samarin da suka biyo ta suka yi sannan ɗaya ya ce.

"Ta ya makaho da ba ya gani zai iya taimaka ma ki?"

Sai a lokacin ta lura da sandar jagoransa dake hannunsa, sannan ga wani baƙin gilashi da ya sa a idanunsa.

Cikin dakakkiyar murya ya ce .

"Ku bar wajan nan."

Dariya suka sake yi kafin ɗaya ya ce.

"Kai makaho ja sandarka ka yi gaba kafin na ƙarasa illata ka."

Cike da ƙwarin guiwa Makaho ya ce wa Mummy.

"Kwantar da hankalinki ba abin da da suka isa su yi ma ki."

Daidai lokacin ɗaya saurayin ya yi kukan kura ya nufo makahon a fusace, yayin da makahon ya ji yakin gudunsa ya ɗaga sandarsa daidai yana kawo wa ya buga ma sa Sandar a kai, wanda ya sa ya faɗi ƙasa yana birgima.

Ɗayan ma na ganin haka ya zo da karfinsa, nan ma makahon ya yi bugu ɗaya ya yi ma sa shi ma ya zube a wajan.

Ganin haka ya sa ta ce.

"Mu je ka bar wajan nan kar su tashi su illata ka."

Ta faɗa cike da tsoro.

"Sai sun ɗauki tsawon lokaci kafin su koma daidai. Ki wuce ki bar nan."

"Kai kuma fa?"

"Kada ki damu da ni."

"Ba zan bar ka anan ba, don Allah ka zo mu ke ka ji."

Haka ya bi bayanta suka isa wajan motarsa ta bude ma sa gefen mai zaman banza ya shiga.

Da sauri ta ja motar suka bar wajan tana godewa Allah.

"Ya sunanka."

"Khalifa."

"Na gode da cetona da ka yi. Mu je gidana duk abinda kake bukata zan ba ka ko meye, zan kai ka asibiti a yi ma ka aikin idanunka ko da ƙasar waje ne."

"Haka idanuna suke, haka aka haife ni ba aikin da za'ayi ya bude kuma."

"Ayyah na ɗauka lalura ce ta same ka."

"A'a."

Ya ba ta amsa a takaice. Ba wanda ya sake magana har suka isa gidan, ta danna horn maigadi ya bude ma ta ta shiga da motar zuwa parking space ta yi parking.

"Hajiya ni zan koma gida, ba na bukatar komai."

"To na ji mu je ka gaisa da iyalina ga mijina ma ya dawo ƴata ma ta dawo ina son na ma su bayanin komai a gabanka."

Daga haka suka fito tana gana yana bin ta da sanadar jagoransa suka shiga ciki.


*Maman Ihsan ce*✍️

09065327995

Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z


*MAKAHO NE*


*NA*

Maman Ihsan ce ✍️


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


page1️⃣6️⃣

Daga haka suka fito tana gana yana bin ta da Sandar jagoransa suka shiga ciki.

Da sallama ta shiga falon, Daddy da Ma'eesha dake zaune a falo suna jiran dawowarta suka mike suna ma ta kallon mamaki. Ganin yanayin ta da kuma wanda take tare da shi.

"Lafiya kuwa Mummy, yanzu Daddy ke shirin kiran wayarki sai muka ji ƙarar motarki."

Murmushi ta yi tare da cewa.

"Na auna arziki ne yau."

Da sauri Daddy ya mike tsaye yana kallonta.

"Subhanallah ba abun da ya same ki ko?"


Murmushi ta yi ta ce

"Ba komai Daddyn Ma'eesha Allah ya kare ni fa ya tura mun wannan bawan Allah ya taimake ni."

Sai a lokacin ne suka lura da Makaho, cikin sakin fuska da fara'a Mummy ya kalli Makaho ta ce.

"Ƙaraso ma na Bismillah."

Sai a lokacin Makaho ya karaso ciki ya zauna a saman carpet.

Nan Mummy ya ba wa Daddy da Ma'eeaha labarin duk abinda ya faru da ita a hanya da haduwarta da makaho.

Sun jinjina lamarin sosai nsannan Daddy ya ɗebi kudi ya mikawa Makaho yana cewa.

"Ga wannan kudin ka damu na kashe wa ko?"

Hannu ya daga ɗaga alamar ba zai karɓa ba. Nan Mummy da Daddy suka yi suka yi ya karba kudin amma sam ya ce ba zai karɓi ko sisi daga wajan cikin kudin da suka ba shi ba. Mamaki suka yi ga shi makaho kuma bai yi kala da wanda yake da kudi ba. Don sai da Mummy ta kare ma sa kallo. Kuma ta rasa me za ta bashi da zai kaba a matsayin tukuicin ceton ranta da ya yi.

Abinci ta saka Ma'eesh ta kawo ma sa. Sai dai ya ce ba zai ci ba.

Kallon Ma'eesha dake rike da tire da ta kawo abinci Mummy ta yi kafin ta ce.

"Mayar da abincin ki hada ma sa take away ya tafi da shi."

"To Mummy."

Ta faɗa tana nufar hanyar kitchen, don dama ba kowane lokaci Mummy ke sanya ma sai aiki yin abu ba, wani lokacin Ma'eesh take saka wa.

Daddy ya kalli Makaho ya ce.

"Bawan Allah ya sunanka?"

"Sunana Khalifa."

"Ma sha Allah, amma me ya saka ba ka karbi kuɗimda la ba ka ba, ko sun ji kadan ne?"

"A'a Alhaji ba haka ba ne, na yi komai saboda Allah ne, idan na karbi kuɗin ku ai ya zama kamar na kudi kuka biya Ni, kuma ba na yi don ku biya ni ba ne na yi saboda Allah ne."

Murmushi Mummy ta yi tare da cewa.

"Iyayen ka suna raye?"

"A'a ba sa raye Allah ya yi ma su rasuwa tun ina yaro."

"Yanzu a ina kake zaune?"

"Gidan wasu bayin Allah ne sauka ba ni ɗaki nake zaunar fisabilillah."

"Za ka iya zama da mu a baka ɗaki can bangaren mazan da ke mana aiki?"

"A'a Hajiya na gode ki bar shi kawai."

Jinjina kai ta yi kafin ta ce.

"Ina neman wata alkfaea a wajen ka."

Faɗi ina dai bai fi ƙarfina ba in sha Allah zan yi ma ki."

"So nake kullun ka dinga zuwa gidan nan ka na karɓar Abinci."

"Eh to kada na ce a'a ki ga laifina komai na ƙi karba, amma dai zan dinga zuwa duk ranar juma'a in sha Allah ina karbar abinci ko na ci."

"Sauran ranakun da?"

"Ba tabbas zan iya zuwa. Amma idan na damu sarari jefi-jefi za ki dinga ganina"

Daidai lokacin Ma'eesha ta karaso rike da leda da ta hadi take away da abin sha da su snacks."

Mummy ta karɓa ta miƙa ma sa ya yi godiya ya nufi hanyar fita daidai lokacin Mamy ta shigo tare da Laila suka yi sallama.

Gabadaya suka amsa ma su sallamar.

Laila na ganin makaho zai fita ta ce.

"Yaushe mabarata suka fara shigowa har cikin gidanmu ne?"

Cak ya tsaya wanda kallo ɗaya za ka yi wa fuskarsa ka san cewa ransa ya ɓaci.

"Ni na mabaraci ba ne, duk da cewar ina da makasa to ba kasashshe ba ne, ina d abun yi kira na aka yi dole na zo gidan nan, kuma ban zo gidanku don a wulakanta ni ba. Na ɗauka gidan karamci da sanin darajar Ɗan adam na zo."

Ma'esha ta yi saurin cewa.

"Ƙwarai kuwa gidan karamci da sanin darajar Ɗan adam ka zo, kuma ka ga yadda muka karrama ka, ita wacce ta yi ma ka maganar ba ƴar gidan nan ba ce cin arziki ta zo, ka yi haƙuri Yaya Khalifa."

Har ga Allah ya ji dadin zancen Ma'eesh sai dai bai ce komai ba ya fita.

Hatta Daddy da Mummy ba su ji dadin zancen da Laila ta yi wa makaho ba, kuma sun ji dadin hakurin da Ma'eesha ta ba shi, duk da ba su so ta ce Laila ba ƴar gidan ba ne don kar ta ji ba daɗi. Mamy kuwa ta ji haushin zancen ma'eesha ko kadan ba ta so a ce An yi maganar cewa ƴaƴanta ba ƴan gidan ba ne, tamkar gori Ma'eesha ta yi wa ƴar ta.

Fuu Laila ta nufi kofar fita za ta fice Mummy ta kira ta.

"Laila zo nan."

",Ta karasa gaban Mummy tana kumbure fuska."

"Kada ki sake irin abun da kika yi yanzu, ki dinga daraja Ɗan adam ban da wulaƙanci ko cin zarafi akan wata nakasa da yake da ita. Ko da a ce haka ne bai kamata ki fadi haka ba. Ko a ina kuma ga mutum duk yadda yake ki daraja shi kada ki wulakanta shi Ɗan adam daraja ne da shi, ba wai idan ka taka wani matsayi sai ka dinga wulakanta mutane ba."

Naj ta ba su labarin Khalifa Makaho da yadda ya taimake ta.

Mamy ta jajanta ma su sannan ta yi Dady Barka da dawowa suka koma part ɗin ta ita da Laila. Ran su a ɓace don idan aka ɓata rana Laila dai Mamy ta taya ta fushi.

Suna zuwa BQ Laila ta fada kan kujera tana kuka.

Mamy ta janyo ta ta rungume.

"Yanzu wai ni ban wuce gori a cikin gidan na ba, kullum cewa kuke na ɗauka nan gidanmu ne amma kalli abun da ma'eesha ta yi ma ni s gaban wannan Makaho."

"Ki kwantar da hankalinki lokaci kadan ya rage daga Ma'eesha har uwar ta za su bar ma na gidan da me gidan dai yadda muka yi da shi. Ko kin mance abun da ya kawo mu nan ne?"

"Ban mance ba, amma sai yaushe za mu yi ta zama a haka ne?"

Lokaci kadan ya rage za su zama tarihi a gidan nan, nan ba da dadewa ba ke ce matsayin Ma'eesha yayin da ni kuma zan maye gurbin mahaifiyarta a wajen Alhaji."

Dariyar mugunta suka saka su duka wanda sautin dariyar ya da ba su ji sallamar Jamil ba.

"Assalamu alaikum."

Shiru ba wanda ya amsa sai dariya suke yi

Ya shigo ya tsaya gabansu sannan suka yanke dariyar da suke yi.

"Lafiya wannan dariyar ai ta wuce na Musulunci."

"Ina ruwanka."

Mamy ta faɗa don ko da wasa ba za ta bari Jamil ya san shirinta, don ba halinsu daya da shi ba ta sani.

Ɗakinsa ya wuce ba tare da ya sake cewa komai ba. Don har ga Allah ya tashi halin mahaifiyar tasa.


*Washegari*

_Ma'eesha_

Ta fito daga cikin bedroom ɗinta tana gyara mayafin abayar da ta yi rolling kanta da shi. Sanye take cikin doguwar rigar Abaya mai ruwa ƙasa. Hannunta rike da makullin motarta .

Part ɗin Mummy ta nufa da niyyar yi ma ta sallama, tun kafin ta karasa ta hango Mamy tana barin part ɗin Daddy cikin sanɗa alamar rashin gaskiya.

Da mamaki take tambayaar kanta.

'Me Mamy ta zo yi nan part ɗin, sannan duk falo bai ishe ta ba ko ɗakin Mummy shi ne za ta zo part ɗin Daddy me ta zo yi. Ga Daddy baya nan ya fita.'

Ƙofar bedroom ɗin Mummy ta yi knocking aka ba ta izinin shiga sannan ta shiga da sallama.

"Assalamu alaikum"

"Wa'alaiki Salam warahmatullah."

Mummy ta amsa yayin da take nannaɗe sallaya kasancewar sallar walaha ta idar.

"Wai har kin fito zuwa gidan su Nasreen ɗin kenan ?"

"Eh Mummy da ita na kwana ba ta da lafiya sosai."

"Allah sarki, Allah ya ba ta lafiya."

"Amin ."

Ɗan jim ta yi har sai da Mummy ta tambaye ta.

"Lafiya alamar kina da damuwa ko?"

"Mummy ."

"Na'am."

Ta amsa tana tattara hankalinta kacokan kan Ma'eesha.

"Me Mamy take zuwa yi nan na?"

Cikin nuna gajiya da zancen Ma'eesha kullun na cewa ba ta son zaman Mamy a gidan."

"Wai me bayin Allah suka yi ma ki ne Ma'eesha? Ban san ki da mugun hali na rashin son jama'a ba."

"Wallahi da na ga Mamy tana sanɗa tana barin part ɗin Daddy ."

Da sauri Mummy ta kalle ta tana cewa

Ban gane ba wai ita da kanta kika gan ta a part ɗin mahaifinki?"

"Eh."

Ta amsa a takaice cike da damuwa.

"Mummy me ya kawo ta ne?"

"Ina zan sani don ban ganta ba. Me yiwuwa nan za ta shigo ta ɓace hanya kin san iyakar ta falo take tsaya wa."

"Wannan fa sanɗa take yi alamar ba ta son wani ya ganta."

Cikin kawar da zancen Mummy ya ce.

"Idan kin je gidan su Nasreen ki gaida ma ni da mahaifiyarta."

"Za ta ji."

Har za ta wuce ta dawo ta ce

"Mummy ba ki tunanin wani mugun abun take ƙoƙarin aikatawa ne?"

"Me ya sa kika ce haka.?"

"Haka zuciya ta ke raya ma ni."

"To ki saƙa alkhairi a zuciyarki."

Cikin sanyin jiki ta yi wa mahaifiyarta sallama ta fice daga part ɗin.

A falo ta tarar da Mamy tana zaune tana kallonta ta washe baki.

"Ƴan matan Mummy ina zuwa haka?"

"Gidan ƙawata."

"Da motarki za ki tafi?"

"Eh."

"Am na ce ba?"

Sai Ma'eesha ta tsaya tana kallon ta don jin me za ta ce.

"Ki dinga fita da Laila tana ganin gari ita ma ko za ta san jama'a."

"Yanzu ina sauri next time za mu tafi tare."

Ba ta jira cewar ta ba ta fice daga falon.

A parking space tana kokarin yin parking motarta kenan ta ga wata sabuwar mota ta shigo cikin gidan.

Ba kowa ba ne face Abdul saurayinta da yake mutuwar son ta.

Bude murfin motar ya yi ya fito daga nasa motar ya nufi nata motar.

Tsaya wa ta yi tana kallonsa da mamaki don ba ta san ya shigo kasar ba.

"Kina mamaki ko?"

Saukar yaushe a garin?"

"Yanzu, ko gida ban je ba daga airport nan na fara zuwa na ga sanyin idanuwana."

Murmushi ta yi tare da cewa .

"Sannu da zuwa, shi ya sa na ji garin na ƙamshin Egyptian, ashe mutanen Egypt ne."

Dariya ya yi tare da cewa.

"Yanzu daga ƙasar Canada nake ."

"Ma sha Allah. Ya kamata ka je gida ka huta kafin ka zo nan k"

"Korata kike yi?".

Dariya ta yi tana cewa.

"Ba haka ba ne, kawai na ga ba ka je gidan ka huta ba ai."

"Okay."

Ya buɗe bayan motar ya fito da wasu manyan jakuna guda biyu ya ba ta. Kin karba ta yi sai da ya nuna ɓacin ransa ta amsa tana godiya.

"Ba zan bar kasar nan ba sai an sanya ma na ranar aure da ke, don haka ki sanar da Daddy zan zo na gaishe shi."

Daga haka ya shiga motarsa direba ya ja suka bar Wajen.

Ba ta kai kayan gidan ba sai ta saka bayan motarta ta yi wa motar key ta bar gidan sai ta kama hanyar gidan su Nasreen.


Ma'eeha na barin gidan Mamy ta hango abincin Daddy a a dinning table.

Tashi ta yi ta kwance haɓar zaninta ta ciro wani kulin magani a leda ta kwance. Sai ta barbaɗa a cikin miyar abincin Daddy ta motsa shi sannan ta motse ta bar wajen bayan ta rufe ta bar wajen in da ta ga Mummy tsaye a falon


*Maman Ihsan ce.*✍️

09065327995

Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z


*MAKAHO NE*


*NA*

Maman Ihsan ce ✍️


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


page1️⃣7️⃣

Tashi ta yi ta kwance haɓar zaninta ta ciro wani kulin magani a leda ta kwance. Sai ya barbaɗa a cikin miyar abincin Daddy ta motsa , sannan ta rufe ta bar wajen in da ta ga Mummy tsaye a falon.

Sai ta hau kame-kame cikin rashin gaskiya ta ce.

"Dama Wai fridge nake so na ɗauko ruwa na sha."

"To ai ga fridge nan a bayanki ko kin manta ba a dinning area fridge yake ba."

"Lah ko me ya hau kaina na nufi can oho, bari na je na ɗauko kawai."

Ta nufi fridge ɗauki ruwa roba guda ta ta dawo falon ta zauna.

Ita ma Mummy zama ta yi ba tare da ta kawo zargin komai a zuciyarta ba, duk da maganar da Ma'eesha ta yi ma ta kuwa.

"Ko abinci za ki kara ci ne akwai shi a kitchen fa."

Cewar Mummy tana kallon Mamy.

"A'a Hajiya ba abinci nake bukata ba, ai an kai ma na ga shi can na baro shi ba mu cinye ba, Allah dai ya saka ma ku da alkhairi ya ƙara arziki, mun gode sosai."

"Haba don Allah ki daina yi ma na godiya, ai mun zama ɗaya."


Ƙarar horn ɗin motar Daddy suka ji da ƙarar bude gate ɗin gidan.

"Bari na tashi na tafi tun da maigidan ya dawo ko?"

"Tashi kuma ki zauna ma na na ga kallo kike yi ai, na manta ban fada ma ki ba za mu tafi aikin Umrah cikin satin nan in sha Allah."

Washe baki Mamy ta yi tana cewa.

"Alhamdulillah Allah ya kai ku lafiya ya karbi ibada?"

"Ke da Alhaji za ku tafi ne?"

"Mun saba duk shekara tare da shi da Ma'eesha muke zuwa mu uku, amma wannan karon ba zai samu zuwa ba ni da Ma'eesha kawai za mu tafi, shi ma wata ƙasar zai tafi."

"Allah ya tsare ku za mu sha kewa."

Dariya Mummy ta yi tana cewa.

"Idan Allah ya kai mu za ku je aikin Hajji ke da yaranki duka."

Kukan farin ciki ta saka tana yi wa Mummy godiya, ita kuma tana cewa ta daina kuka.

Daidai lokacin da Daddy ya shigo da sallama.

"Subhanallah me ya faru ne take kuka?"

"Don na yi ma ta albashir ɗin zuwa aikin hajji ita da ya ranta shi kenan fa."

Murmushi ya yi ya ce.

"Ikon Allah , ai addu'a za ki yi ba kuka ba."

Yana gama fadar haka ya nufi part ɗin sa, duk kukan da Mamy ke yi bai hana ta satar kallon Daddy ta kasan idanunta ba.

Mummy ta bi bayan mijinta ganin cewa Mamy ta yi shiru.

Da harara ta raka ta sanan ta mike ta nufi BQ.

Ko da Mummy ta shiga part ɗin ta ta samu Daddy ya fara rage kayan jikinsa zai yi wanka.

Ta taimaka ma sa ya cire kayan sannan ta haɗa ma sa ruwan wanka.

Kafin ya fito ta cire ma sa jallabiya mai gajeren hannu, kasancewar in dai yana gida to ya fi saka jallabiya.

Ya fito ta taimaka ma sa ya shirya cikin jallabiyar ganin yanayinsa ta san a gajiye yake.

"Ka gaji ko?"

Murmushi ya yi yana cewa.

"Bari kawai aiki ne ya ma ni yawa tun safe har yammacin nan."

"Allah sarki mu je ka ci abinci ka huta na san ba ka ci komai ba."

"Haka ne, a tare suka nufi dinning area yana jin kansa na ɗan sara ma sa.

Abinci ta zuba ma sa ya ci ya sha lemu da ruwa.

Kallon time ya yi.

"Ya kamata a ce Ma'eesha ta dawo gida haka nan, tun yaushe ta kira ni zancen zuwa gidan ƙawarta da ba lafiya shi ne ba ta dawo ba."

"Za ta dawo in sha Allah. Ka san ba ta daɗe da wucewa ba, ka dawo kuma ka san ba ta da ƙawar da ta wuce Nasreen."

Duk da haka sai da ya kira waya ya ce ta dawo gida.


A ranar sai ga Khalifa Makaho ya zo gidan, kamar yadda Mummy ta ce ya dinga zuwa kowace rana, amma bai zuwa kowace rana sai dai duk sati yana zuwa. Ziyarar juma'a, bayan an yi sallar juma'a daga masallaci yakan je gidan ya kaiwa Mummy ziyara. Kuma takan karrama shi sosai da sosai a cika ma sa gabada da abinci kala-kala da abun sha. Wata rana har take away take yi ma sa.

Kamar kullum yau juma'a ya zo gidan, bayan maigadi ya bude ma sa ƙaramar ƙofar m


*Bayan sati ɗaya.*

A ranar ne su Mummy da Ma'eeha suka wuce ƙasa mai tsarki don yin umara. Shi kuma Daddy nan da kwanaki biyar, zai tafi ƙasar da zai je don gudanar da harkokin sa.Farin ciki ya cika zuciyar Mamy saboda yanzu ne lokacin da za ta shirya mummunar kudirin ta kai.

Don yanzu wani sabon salo Mamy ta tsiro da shi, sai ta bar BQ da sassafe ta zo man main house din ta ce da ma su aiki su dinga dafa abinci na su kaɗai, ita za ta dafa nata ita da yaranta da na maigidan wato Daddy. Ba yadda suka iya haka suka zuba ma ta idanun take yin abun da ta ga dama. Abincin Dady kuma kullum safe da dare sai ya barbaɗa ma sa magani a ciki. Gabɗaya ya canza kamar ba shi ba. Tafiyar da zai yi ma ya ce ya fasa zuwa.


*Bayan sati biyu*


Motar da ta ɗauko su na tafiya akan titi suna baya direban na zaune mazaunin sa yana driving hankali kwance.

Cikin damuwa Ma'eesha ta ce.

"Mummy tsawon sati ɗaya kenan ba mu ji daga Daddy ba, kuma yana ƙasar nan, abun ya ba ni mamaki shi bai kira ba kuma idan mun kira baya ɗaga wa."

"Kar ki damu me yiwuwa aiki ne ya ma sa yawa."

"Ba na tunanin akwai aikin da zai ma sa yawa da har zai saka shi ya mance da iyalansa. Yanzu haka na ɗauka za mu gan shi a airport ya zo ɗaukar mu."

"Ki yi ma sa uzuri Ma'eesha."

Daga haka ba wanda ya sake yin magana har suka ƙarasa gidan.

Horn direban ya yi maigadi ya bude ma sa kofar gate ɗin ya shiga ya yi parking. Abun da ya kara ba su mamaki ganin motocin Daddy duka a wajen.

Sauran ma'aikatan gidan suka ƙaraso suna yi ma su sannu da zuwa. Mummy ce ta amsa ma su, don Ma'eesha gabaɗaya hankalinta ya koma ga mahaifinta so take yi ta gan shi ta kuma ji dalilin da ya sa ya share su na tsawon kwanaki.

Direban ne ya shigo ma su da kayansu, suna shiga cikin falon ba kowa sai sanyin A.C dake tashi a falon.

Sautin dariya suka ji yana fitowa daga ɓangaren Daddy. A tare suka juya suna kallon ɓangaren Daddy wanda daga nan suke jin dariyar .

Da mamaki suke kallon Mamy tare da Daddy suna fitowa daga ɓangarensa tana rike da jakarsa, alamar tafiya zai yi. Mutuwar tsaye suka yi suna kallonsa. Wanda shi ma su yake kallo sai dai ba za ka iya shaida halin da yake ciki ba.

Cikin rawar baki Ma'eesha ta ce.

"Daddy."

Ba tare da ya kalli kowa cikin su ba ya ce.

"Kun dawo?"

"Ba su iya amsa ma sa ba, shi ma bai sake cewa komai ba ya nufi hanyar fita, Mamy na binsa a baya tana ta wani shu'umin murmushi.

"Yauwa zan yi tafiya maybe zuwa next week zan dawo."

Sai a lokacin Mummy ta yi karfin halin cewa.

"Alhaji ba na ganin dacewar abun da na gani a yanzu, me wannan matar take yi a part ɗin ka?"

"Oh haba!"

Ta jingina kai sannan ta ce.

"Meye tsakanin ku da har za ta fito tana yi ma ka rakiya?"

"Kamar yadda kike matsayin matata a gidan nan to haka ita ma matata ce ita auren ta nake yi."

Rintse idanunta Mummy ta yi sakamakon wami zafi da raɗaɗin kalmar da Daddy ta ki shi kamar an watsa mata ruwan dalma a zuciyar ta.

Ma'eeha kam tamkar saukan aradu haka ta ji.

"Alhaji yaushe hakan ya faru ba tare da sanina ba."

"Ke uwata ce da dole sai na yi shawara dake wajen aiwatar da abun da na yi niyya?"

Jinjina kai ta yi tare da yin murmushi da ya fi kuka ciwo ta ce.

"Haka ne, Allah ya sanya alkhairi."

"Amin, dama ke kika kawo ta kin san halinta kun saba da juna don haka ki karbe ta ku zauna lafiya don ba zan juri tashin hankali da kishin hauka da wasu matan ke yi idan mijinsu ya kara aure."

Yana fadar haka ya fice shi da Mamy tana ma sa Allah ya tsare.

Ma'eesha kuwa sulalewa ta yi a wajen tana kuka, ganin mahaifinta ko kallon arziki bai yi ma ta ba, bayan san cewa ita ce sanyin idanunsa. Yana masifar son ta baya son ɓacin ranta, amma yau an wayi gari ko kallo ta ba yi ba bayan tsawon kwanaki da suka shafe ba su ga juna ba.

Mummy ta yi kokarin danne abun da take ji ta hau rarrshin Ma'eesha. Suna nan da na Mamy ta dawo tana taunar cingum.

Ƙafa ɗaya kan ɗaya ta ɗaura tana danna waya tsadaddiyar wayarta sabuwa fil.

Mummy ta kalli Mamy ta tuna ranar da ta zo ƙofar gidan neman taimako ita da Jamil da Laila. Wai yau ita aka wayi gari ta aure ma ta miji.

Kuka sosai Ma'eeha ke yi ranta na ma ta zafi.

"Aure dai an riga an ɗaura ba yadda mutum zai yi da ikon Allah, ni ma ba son raina ba ne aka aikata hakan. Alhaji ne ya matsa."

Daga haka ta yi shiru tana ƙwalawa daya daga cikin masu aikin gidan kira.

"Inno! Inno! Inno!"

"Na'am Hajiya."

Ta amsa tana fitowa, ganin Ma'eeha na kuka hankalin ta ya tashi ta nufi Ma'eesha tana tambayarta lafiya. Tsawar da Mamy ta daka ma ta ne ya saka ta ɗago da sauri.

"Inno!"

"Na'am."

"Aikin da na saka ki kin gama ne?"

"Eh Hajiya."

Daga nan ta kama Ma'eesha suka nufi ɗakinta da ita.


Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, a cikin gidan, abubuwa marasa daɗi na faruwa. Bangaren Daddy ma gabadaya ya tattara hankalinsa ya mayar kan Mamy da yaranta, su ya mai da madubin sa. Sam bai damu da Mummy ba ballantana ƴarta ɗaya tilo a duniya.

Da abun ya ishe Ma'eesha wata rana da ta je week end gidan Hajiya Turai ta kakarta sai take sanar da ita halin da suke ciki a cikin. Amma sai ta tarar da Hajiyar ita ma ba ta da labarin cewa wai Ɗanta da ta haifa ya iya yin aure ba tare da ya sanar da su ba. Daka jiran zuwa nasa take yi a baya kullum zai zo ya gaishe su, amma tun da ya auri Mamy bai je ya gaishe ta ba.


A cikin kwanakin nan ne Mummy ta dinga fama da rashin lafiya. Yau lafiya gobe ciwo.

Sai dai duk rashin lafiyar ba ta bari a kai ta asibiti ba, a cewar ga wai ciwon ba na asibiti ba ne. Ga Daddy ya fita ba zuwa ƙasar.


_Makaho,_

Kasancewar yau juma'a ne kuma daga masallaci gidan su Mummy yake son zuwa don ya gaishe da Mumm. Kasancewar sun tafi aikin Umara ya san dai yanzu sun dawo.

Don haka bayan ana idar da Sallah kai tsaye ba gidan su Mummy ya nufa don gaishe su kamar yadda ya saba.

Doguwar tafiya ya yi kafin ya ƙaraso gidan. Sai da ya sa hannu ya shafa gate ɗin gidan ya tabbatar gidan ne kafin ya yi knocking.

Maigadi ya bude kofar ya ga Makaho ne ya ce.

"Ma sha Allah makaho ne ke tafi?"

Bai tanka ma sa ba ya yi gaba yayin da maigadin ya bishi da harara.

"Wannan mishkilancin naka Allah ya ga abin da ya gani da ya hana wa jaki ƙaho. Ana ma sa magana yana share Mutane wannan da yana da kudi da an ga gadara."

Makaho kam bai ma san yana yi ba ya nufi cikin gidan.

Daga bakin kofar falon yake knocking, ɗaya da cikin ma su aikin ta fito .

Ganin shi ne ya sa ta ce.

"Bari na sanar da su.

Tana shiga ta yi sallama sai aka amsa ma ta tare da ba ta izinin shiga.

Ta shiga Mummy na barci Family doctor nasu ma hi ma ta ƙarin ruwa.

Ƴar aikin ta kalli Ma'eesha ta ce .

"Aunty wannan makahon da ke zuwa ranar Friday ne ya zo "

"Okay Ina zuwa."

Bayan ƴar aikin ta fita da kamar mintuna biyu sai Ma'eesha ta tashi ta fita ganin Mummy na barci.


A hankali take tafiya har ya buɗe kofar falon.

Yana tsaye a ya jingina bayansa da bango . Tana daga kanta ta sauke idanunta a kansa. Ya nunkuyat da kai ƙada ya haɗa kai da Sandarsa.

Cikin siriryar murya Ma'eesha ta yi masa sallama.

Ya ɗago kansa kamilalliyar fuskarsa mai cike da haiba ta bayyana.


*Maman Ihsan ce*✍️

09065327995

Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z


*MAKAHO NE*


*NA*

Maman Ihsan ce ✍️


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


page1️⃣8️⃣


Ya ɗago fuskarsa kamilalliyar fuskarsa mai cike da haiba ta bayyana.

"Wa'alaiki Salam warahmatullah."

Ya amsa ma ta cikin muryarsa mai amo.

"Ina wuni?"

"Lafiya lau Alhamdulillah."

"Ka shiga ciki."

Tana gaba yana bin ta a baya dama idan ya zo bangaren baƙi Mummy ke cewa a kai sa.

Bayan ta tura ƙofar falon n ta shiga ne shi ma ya zo ya shiga yana mai yin sallama.

Sai da ya ɗan laluba ya ji kujera sannan ya zauna da Bismillah.

Ina Mummyn taki take ne?"

Cikin sanyin murya ta ce.

"Ba ta da lafiya."

"Subhanallah me ya same ta?"

"Zazzaɓi ne."

"Allah ya ba ta lafiya."

"Tana ina ne?"

"Tana bedroom ɗin ta. Ita ce ta ce na shigo da kai."

"Allah sarki, Allah ya ba ta lafiya."

"Amin ya Allah."

Ta amsa tana mai nufar ƙofar fita ta ce.

"Bari na kawo ma ka abinci ko?"

" A'a ki bar shi kawai tafiya zan yi, na zo ne dama na gaishe ta."

"Ka yi hakuri ka zauna zan kawo ma ka abinci ko a cikin take away ne dan idan Mummy ta ji ban kai ma ka abinci ka tafi haka nan ba za ta ji dadi ba."

Tana fadar haka ta fice daga falon.

Ba jimawa ta dawo da leda mai ɗan girma ta mika ma sa.

"Ga shi na zuba ma ka abincin da abun sha sai snacks."

"To na gode Allah ya kara arziki ya ba Mimmy lafiya ."

"Amin ya rabbil izzati na gode."

Ya mike ya fice daga falon tana binsa a baya. Ya nufi hanyar fita ita kuma ta shiga falonsu cikin matsanancin faduwar gaba da sanyin jiki wanda ta ji ya dirar ma ta lokaci guda.

Mamy ne a falon tana waya, amma tana ganin Ma'eesha ta yi saurin katse kiran wayar ta ajiye wayar tana kau da kai.

Ma'eesha dai ba ta kalli gefen da take ba kai tsaye bangaren mahaifiyarta ta koma.

Ta same ta idanunka a lumshe tana tuna yadda Daddy ya canza ma ta, kamar ba mutumin da baya son ɓacin ranta ba, kamar ba wanda yake shiga damuwa idan ba ta da lafiya ba, amma yau ga ta kwance ko ya zo sai dai ya tsaya daga bakin kofar ya yi ma ta magana baya shigowa ciki. Kuma duk a sanadiyar matar da ta taimaka da zuciya ɗaya a a rayuwa. Matar da ta ɗauke ta kamar ƴar uwa take ƙaunarta da zuciya ɗaya. Kalli rayuwar
nan abar tsoro ce.

A hankali ta bude idanunta akan Ma'eesha tana tausayin rayuwar da yarinyar za ta fuskanta bayan babu ita a duniya. Don ba ta da in da za ta je, Daddy ya ma ta shamaki da danginsa, dole ta zauna gidan ubanta. Kuma ba za ta yi rayuwar farin ciki da jin dadi ba. Dama a ce ta aurar da ita ga miji nagari da ba ta da wani damuwa, ta san tana zaune gidan mijinta ba za ta zauna a wannan gidan ba. Ta kira sunanta a hankali.

"Ma'eesaha."

"Na'am Mummy."


"Kar ki sa a ranka duk wanda kike tare dashi a yau ba zai iya rabuwa da ke a gobe ba, dan haka karki sa rai da mutum kowa ki so shi saffa-saffa. Saboda wanda muke tare da su yanzu anjima babu su. Ɗan adam yana iya rabuwa da ke a duk yanda kike da shi, shi ya sa da kowa ma ki zauna da shirin rabuwa da shi ko wane ne, ke dai ki zauna da kowa da zuciya ɗaya, duk wanda ya tafi ko ba yanzu ba wata rana sai ya ga amfanin ki ko ya tuna ki saboda son da kila ma sa da ALLAH da kuma zaman da kika yi dashi dan Allah. Allah ya sa ki dace duniya da lahira, Allah ya haɗa ki da masu son ki da zuciya d'aya wa 'yanda suka san kina sonsu, Allah ya raba ki da wanda duk yanda za ki so su ko daidai da rana ɗaya ba su tuna kin taɓa sonsa ko ka ta6a masa alkhairi ko wani abu naki a rayuwa, in dai mutum ya samu wata dama kai ma sai ya rabu da kai saboda yana ganin ya fi 'karfin ka shi ya sa sai Allah ya kwace daman shi kuma saboda shi da zuciyan kowa yake amfani.

Allah ya haɗa ki da masoyan gaskiya."

Cikin sanyin jiki ta ce.

"Amin Mummy."

Mummy idanunta a kafe kamar tana kallon sama, sai Ma'eesha ta ce.

"Mummy na ba shi abincin ya tafi da shi ya ce yana godiya a gaishe ki da jiki."

Ta yi maganar tana riko hannun mahaifiyarta, sai ta ji hannunta ya saki yaraf.

Gabanta ya tsananta faɗuwa fargaban ya ƙaru.

Ta kira sunanta sau uku shiru, don haka tana kokarin fita ta kira Inno kenan sai ga Inno ta shigo.

Da sauri ta karasa bakin gadon tana kallon Mummy. Shafe ma ta idanun ta yi tana hawaye.

Sannan ta kalli Ma'eesha dake kallon ta kamar wata sokuwa ta ce.

"Sai dai mu yi hakuri Allah ya yi wa Mummy rasuwa ta riga mu gidan..."

Tim ƙarar da ta ji ne ya saka ta juya da sauri, nan ta ga Ma'eesha kwance ta sume a wajen.

Ihu ta saka wanda ya janyo hankalin Mamy dake zaune a falo. Kuma daidai lokacin ne Daddy ya shigo falon.

Yana jin abun da Inno ke fada ya yi hanzarin nufar ɗakin .


Wajen Mummy ya nufa ya duba ta sosai ya tabbatar rai ya yi halinsa ya sa shi lulluɓe ta har da fuskarta yana mai zubar da hawaye. Yana jin kamar ya dawo da hannun agogo baya da ya mayar ya canza wani abu.

Ruwan sanyi ya ɗauka a cikin fridge dake cikin dakin, ya watsa wa Ma'eesha.

Ba ta farfaɗo ba har da aka yi sau uku sannan ta farfaɗo tana matsanancin kuka.

Faɗa wa ta yi jikin mahaifiyar tata tana kuka mai tsuma zuciya. Tana rungume da gawar tana surutai.

"Mummy ta za ki tafi ki bar ni cikin wannan duniyar mai cike da tarin kalubale? Mummy ba zan iya ba, ke ce gatana, ban san ya zan yi ba. "

Haka ta dinga ihu tana sambatu Inno na rarrshin ta.

Mamy kam ko magana ba ta yi ba ta juyabta bar ɗakin.

Daddy ya kira mutane ya sanar da su.

Lokacin da Alhaji Shamsuddin ya ji labarin rasuwar Inno ya shiga tashin hankali sosai ba kadan ba. Yana tuna rayuwar da ta yi a gidan marayu da yadda take yi ma sa addu'a idan ya kawo ma su abu. Dole ya shirya ya bar ƙasar dak da cewar yana fushi da ɗan nasa Daddy.

Domin gabadaya sauyawar da Daddy ya yi ya shafe su har da su ma. Domin ya daina kiran su a waya ko sun kira baya ɗaga wa. Ba don komai ba yake ma su haka sai don sun nun ba sa son auren nan fa ya yi musamman da bai sanar da su ba sai bayan bikin da yadda Ma'eesh ta ba su labarin yadda auren ya kasance, da kuma wace ce ita Mamyn da yaranta da zo da su. Dalilin haka ya saka Mamy ta ce wa Daddy ya hana Ma'eesha zuwa gidan kakannin nata tana week end. Duk yadda Daddy ke tsoron iyayensa yanzu ba ya yi sai tsoron Mamy da bin umarnin ta. Sai abun da ta ce yake yi.

Ko da Hajiya ta yi ma da maganar Ma'eesha ta daina zuwa week end gidanta ya ce wai ta daina zuwa daga yau ya raba ta ya gidan ya kuma yi wa Ma'eesha gargadi sosai akan zuwa gidan kakannin nata har cewa ya yi bai yafe ma ta ba.


Nan da nan labarin rasuwar Mummy ya karade unguwar. Ta yi jama'a sosai har daga wasu unguwannin da dama sun zo .

Bayan an yi ma ta sutura za'a kai ta makwancinta anan Ma'eesha ta dake rike cewa har tana kokarin fita waje za ta bi su Sai da Inno ta rike ta.

Daga nan ta sai ta liƙe wa Inno a jiki, don ko kakarta Hajiya Turai ba ta lyarda ta je kusa da ita ba, saboda Daddy ya yi ma ta iyaka da ita.

Ta canza kamaar ba ita ba, gabadaya ta yi sanyi duk da cewa dama ita ba mai hayaniya ba ce.

Har aka yi kwana bakwai ba ta wani iya cin abinci, Inno ke kokarin ba ta abinci ba ta ci sai dai ta sha ruwan tea idan ta matsa ma ta ma ne take sha.

Kasancewar ba ta da dangin uwa na uban ma Mamy ta sa Daddy ya yi ma ta shamaki ita da danginsa.

Ba ta taɓa jin ciwon rashin dangin uwa ba sai yanzu, da tana da su to ba shakka can za ta je ta nemo su.


*Bayan sati ɗaya*

Yau juma'a ya yi daidai da ranar da Mummy ta cika sati biyu da rasuwa. Gidan kamar ba gidan mutuwa ba, sai harkokin su suke yi, idan aka cire Ma'eeha da Inno. Don su ne ka kalle su har yanzu ka san suna cikin damuwa. Sai kuma Jamil babban yaron Mamy shi ma mutuwar ta shige su, amma iya su ne suka da mu sauran sai a hankali. Haka dai rayuwa take ta tafiya .


*Bayan sati Uku.*

_Makaho_

Tafiya yake yi rike da sandarsa ta jagora ya tsaya a ƙofar gidan su Ma'eesha.

Maigadin baya nan don haka direba ne zaune a bakin gate ya ji ana ƙwanƙwasa kofar ya buɗe.

Ganin makaho ne ya ce .

"Mallam Khalifa kana lafiya?"

Don haka ya ji Mummy da Ma'eesha na kiransa da Khalifa ba su ce ma sa makaho.

"Ya amsa da lafiya lau ya ƙoƙari?"

"Alhamdulillah."

"Ma sha Allah."

Ya haƙurin Hajiya kuma?"

Cewar Makaho.

Direba ya ce.

"Haƙuri namu ne duka."

Daidai lokacin mota ta yi horn sai Direban ya bar makaho ya tafi ya bude gate.

Laila ce ta shigo da motar ta yi parking space.

Idanunta ya sauka akan motar Ma'eesha dake gefe.

"In sha Allah wata rana sai na raba ki da wannan motar ta zama mallakina. Wato saboda ke ƴarsa ce ya siya ma ki tsadaddiyar mota, amma ni kuma ya siya ma ni mai sauƙin kuɗi. Mu ba je zuwa komai ma sai na raba ki da shi ba iya motar ba."

Fitowa ta yi tana yi wa Khalifa wani ƙasƙantaccen kallo ta ce.

"Shi kuma wannan makahon me ya kawo gidan nan, bayan wacce ta ce ya dinga zuwa ta mutu sai dai idan kabari zai bi ta can ta bashi abincin da take ci."

Muryarta kawai Khalifa ya ji ya gane ita ce ranar ta yi ma sa maganar mabarata.

Kafin ya yi magana sai Direban ya ce.

"Ina ganin wajan Hajiya Ma'eesha ya zo."

Laila ta yi ɗan jim sannan ta ce.

"Ma sha Allah."

Daidai lokacin Mamy ta fito tana kallon su kafin ta ce.

"Lafiya kika tsaya a nan?"

"Wai ina ganin baƙon Ma'eesha ne."

Sai a lokacin Mamy ta lura da Makaho, ta kalle shi sama da ƙasa. Wasu kuɗaɗun kaya ne a jikinsa ma su arha, dai hula taɓa ni ka ji hadisi da ya sanya a kai, sa hankali silifas a ƙafarsa. Wani tunani ya zo wa Mamy ta yi dariyar mugunta ta ce .

"Wajen Ma'eesha ka zo ko?"

"Eh na zo ne na yi ma ta ta'aziyya da bankwana don daga yau na gama zuwa gidan nan, tun da Hajiya Allah ya karbi abinsa Allah ya jikanta da rahama.

Direba ne kawai ya amsa da Amin.

Kallon Direban ta yi ta ce.

A kai shi ɗakin baki, yanzu zan tura ma sa ita .

Daga haka ya bar wajen Laila ta mara ma ta baya.

Suna shiga falon ta damu Daddy ta ce .

"Dama Alhaji akwai maganar da nake so mu yi ne."

Ya ajiye wayarsa ya ce

"Ina jin ki."

"Ya kamata a tausaya wa yaron nan kullum sai zuwa zance yake yi, tun uwar na da rai har ta rasu , bayan rasuwar ma kullun yana zuwa ɗebe ma ta kewa yanzu haka ga shi can ɗakin baƙi."

"To ai Ma'eesha ta fi karfinsa makaho ne fa."

"Kamar ya ta fi karfinsa makaho ba mutum ba ne, ai idanunsa ne kawai ba sa aiki, amma idan aka aura ma sa ita an samu lada taimako ne ai za ta taimaka ma sa tunda ita mai kula da gida tana gani, kuma idan suka haifi yara ita ce mai kula da su ba shi ba."

Shiru ya yi cikin rashin yarda da zancen, ganin haka ta ɓata rai cikin bayar da umarni ta ce.

"Ina son daga yau juma'a gobe Asabar a ɗaura auren makahon nan da Ma'eesaha."

Shiru ya yi tana tunani ta sake cewa.

"Ko ba ka ji ba ne?"

"Na ji shi ke nan duk yadda kika ce haka za'ayi."

Laila dake tsaya tana jin su ta wuce ɗakinta cikin farin ciki.

To ba damuwa ka je ka sanar da ski gobe ya nemi sadaki ya kawo a ɗaura ma su aure, idan bai da kudin a bashi sadaka kawai kowa ya huta. Don gobe ko ana ha maza ha mata sai an ɗaura wa yarinyar nan aure da makahon nan."


*Maman Ihsan ce*✍️

09065327995

Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z


*MAKAHO NE*


*NA*

Maman Ihsan ce ✍️


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


page1️⃣9️⃣


To ba damuwa ka ke ka sanar da shi gobe ya nemi Sadaki ya kawo a ɗauara ma su aure, idan bai da kuɗin a bashi sadaka kawai kowa ya huta. Don gobe ko ana ha maza ha mata sai an ɗaura wa yarinyar nan aure da makahon nan."

Da mamaki Daddy ke kallon ta amma ya kasa yi ma ta musu. Don duk abinda take so ko ta furta sai ya tsinci kansa da bin Umarninta ko da ba ya son hakan, amma ba ya iya yi ma ta gardama.

"Ka tashi mu ke ka same shi ya san da zancen."

Tashi ya yi ba don ya so ba sai don zuciyarsa na azalzalarsa da ya bi umarninta.

Ko da ta tura ƙofar falon baƙin ba ta yi sallama ta shiga, a tunaninsa Ma'eesha ce amma yanayin takun ƙafarta da kuma ƙamshin turaren ya ji ba irin na Ma'eesha ba ne. Muryar Daddy da ya yi sallama ya saka shi ya amsa da.

"Wa'alaika Salam warahmatullah. Daddy Barka da rana."

"Yauwa Barka dai."
"Khalifa sunan ka ko?"

"Eh Daddy."

"Kana da mata ne?"

Sai da ya ɗan yi jim yana mamakin dalilin tambayar kafin ya ce.

"Ba na da mata Daddy."

"Shi kenan faɗuwa ta zo daidai da zama."

Cewar Mamy tana Murmushin mugunta.

"Na ba ka auren Ma'eesha gobe ka nemo sadaki ka kawo za'a ɗaura ma ka aure da ita."

"Sai da ya kike tsaye daga zaunen da yake, tsabar mamaki da al'ajabi."

",Daddy Ma'eesha ba sa'ar aurena ba ce, ta fi ƙarfina, ni fa makaho ne, faƙiri wanda ba shi da cin yau bare na gobe, ta ya zan iya ɗaukar ɗawainiyarta, bayan ina makaho ballantana a ce zan iya yin wani aikin da zan riƙe ta."

Mamy ta yi saurin cewa.

"Ba mutum ke yi ba Allah ke yi, baƙin da Allan ya tsaya baya hana ma sa abincin da zai ci. Kai dai ke nemi sadaki ka kawo ko nawa ne, idan ma ba ka samu ba ka zo za'a ba ka ita Sadaka."

Tana gama fadar haka ta ce

"Ko ba haka ba Alhaji, sannan a wannan masallacin za ka so kafin sallar azahar, don ana idar da sallar sai a ɗaura aure kawai."

"To na gode Allah ya saka da alkhairi."

"Mu je Alhajina."

Cewar Mamy tana jan hannunsa ganin ya karaya kamar ba yadda zai yi ne.

Suka fice suka bar shi cike da mamaki. Yana cikin wannan mamaki ne ya ji sallamar Ma'eesha cikin siriryar muryarta.

"Assalamu alaikum."

"Wa'alaiki Salam warahmatullah."

"Sannu da zuwa ina wuni?"

"Lafiya lau Alhamdulillah."

Ya amsa yana tunanin abun da mahaifinta ya ce ma sa. Kafin ya buɗe baki ya ce.

"Ya ƙarin haƙurin Mummy."

"Alhamdulillah."

"Allah ya jiƙanta da rahama ya sa Aljanna maɗaukakiya ce makomar ta. Sannu da imani kin ji Ma'eesha."

"Amin na gode."

Ta amsa tana goge ƙwalla.

Muƙe wa tsaye ya yi yana cewa.

"Dama na zo ne na yi ma ki ta'aziya tare da sallamar bankwana, don ba zan sake zuwa gidan nan ba, dan wacce ta kawo ni nake zuwa yanzu babu ita a doron duniya. To me zai da na ci gaba da zuwa, sai dai kuma yanzu Daddy ne ya zo da wani al'amari mai girma."

"Wane Daddy ya zo da al'amari mai girma?"

Ji ya yi ba zai iya fada ma ta ba, don haka sai ya ce.

"Cewa ya yi na zo gobe."

"Ma sha Allah, to sai ka ci gaba da zuwa ai tun da ya baka dama. Bari na je na kawo ma ka abinci."

"Ba na jin zan iya cin abinci yanzu."

"Okay bari na kawo ma ka snacks da lemu ka tafi da su ."

Tana gama faɗar haka ta fice, bai tsaya jiran ta ba shi ma ya fice, don ya shiga damuwa sosai.

Ko da ya dawo ta yi mamakin rashin ganinsa, ta tambayi maigadi ya ce ya ga ya fice.

Komawa ciki ta yi ta tarar da Daddy zaune shi kaɗai.

Bayan ta yi masa sallama ta ce tana son gobe ta je saloon, kai ya jinjina ma ta kawai ya kasa magana .


_Makaho_

Yana barin gidan su Ma'eesha ya nufi unguwar da yake , kasancewar masallaci yake kwana dama. Bayan an idar da sallar la'asar ya keɓe shi da limamin masallacin ya sanar da shi abun da Daddy da Mamy suka ce na ba shi auren Ma'eesha.

Mallam Liman ya yi mamaki sosai ba kaɗan ba, kasancewar ya san cewa Ma'eesha ita ce ƴa ɗaya tilo da Alhajin ya mallaka, to wane dalili zai sa ya aurar da ita ga makaho talaka. Ya san cewa za ta sha wuya sosai ba kadan ba, ya kuma san wannan ba an yi ba ne dan farin cikin yarinyar sai dai bakin cikinta.

"To yanzu na ga a masallaci kake kwana, to kana da ɗakin da za ka ajiye ta ne?"

"Ba na da shi ."

Ya fada cike da damuwa.

"To akwai wani gidan haya nawa da nake da shi, akwai wani ɗaki guda ɗaya can ƙarshen cikin gidan. To zan ba ka ka zauna da ita a ciki sai dai ba'a shafa siminti ba, zan saka a yi wata dabara da za ku zauna cikin rufin asiri."

"To na gode Allah ya ƙara arziki."

"Amin ya Allah, kana da kudin sadaki?"

"Sun ce wai na je ko nawa ne na kawo, idan ba na da shi ko sadaka za su bani, don haka zan duba ƴan kudin da nake turawa ko nawa ne zan bayar."

Addu'a da fatan alkhairi Mallam Liman ya yi ma sa


Sannan makaho ya sa nemi alfarma yi ma sa wakilci ya karba ma sa auren Ma'eesha ya amsa ma sa .

A yammacin ranar Mallam Liman ya tura iyalinsa ta je ita da maƙociyarsu suka je da buhun siminti aka shimfiɗa suka yi ƴan dabaru sannan suka ja kofar suka tafi.

A daren ne Mallam Liman ya kai Makaho gidan nasa har ɗakin da za'a saka Ma'eesha ya raka shi. Godiya sosai ya yi masa suka fito a tare.


Washegari aka ɗaura auren Khalifa da Ma'eesha akan sadaki Naira dubu uku da Khalifa ya bayar.

Ɗaurin auren da ya ba wa jama'a mamaki da al'ajabi, kamar Alhaji Ibrahim Khalil ne zai aurar da ƴar sa ɗaya tilo ga wani makaho kuma faƙiri.

Ya koma cikin gidan cikin sanyin jiki ya ke sanar wa da Mamy kuma komai, wanda duk maganar da yake yi na auren a kunnen Inno. Wacce ta kaɗu da jin zancen, ta shiga kitchen tana goge hawayenn tausayin Ma'eesha.

Wayarta ta fara tunanin ɗauka ta kira Ma'eesha ta sanar da ita kada ta dawo ta gudu.


*Cigaban labari*

Ƙarfe huɗu na asuba Ma'eesha ta farka daga barci da take yi. Sautin muryarsa mai amo ta ji ta ji yana karatun Alkur'ani mai girma. Yana zaune saman sallaya da alama sallama sallah ya idar.

Sauraron muryarsa take yi yadda yake ba wa kowane harafi hakkinsa, yana karanta suratul Yasin.

Lumshe idanunta ta yi tana jin wani sanyi da nutsuwa na ratsa ta. Ya idar ya kama wata surar. Har sai da aka kira sallar assalatu ya juya bangaren da Ma'eesha ke kwance kamar wanda idanunsa suke gani.

Ita kuma sai ta yi saurin lumshe idanunta kamar mai yin barci da gaske, ko ta mance makaho ne baya gani oho.

Tashi ya yi ya karasa bakin katifar bayan ya yi lalube.

Da ya ji ya taɓa pilow ne ya bubbuga pillow ɗin a hankali.

Dama ba barci take yi ba hasalima ta buɗe ifsnunta da ta ji takun tafiyarsa.

"Ma'eesha."

"Na' am."

"Ki tashi ki yi alwala ki yi sallah lokaci ya yi ."

"To zan tashi."

"Allah ya baki iko."

Ya fada yana laluben Sandar jagoransa.

Bayan ya taɓa ta ne ya saka ya ce.

"Ni zan tafi masallaci."

"A dawo lafiya."

Tashi ta yi tana jin alamar cizon sauro a jikinta.

"In sha Allah gobe ba zan manta ba zan siye maganin sauro in sha Allah. Ko ma na nemi zanin sauro."


_Nadra_

Ta kasa haɗa idanunta da nasa saboda wani irin kwarjinin da yake yi ma ta. Sai ta ya kamar za ta kalle shi sai ya kasa saboda kaifin idanunsa gare ta.

Kallon ta ya yi ba yabo ba fallasa ya ce.

"Ki shanye shi duka, ki ba ni kofin."

"Gabaɗaya tea din jinsa take kamar tana shan magani. Bakinta ba daɗi don jin zazzaɓi take yi ma a jikinta, ga kanta dake bala'in sara ma ta, kuma baya rasa nasaba da kukan da ta sha.

Hawayenta ya gani yana sauka a hannunta da take rike da tea.

"Wai ke kuka baya yi ma ki wuya ne, yanzu me na yi ma ki daga ba ki abinci shi ne za ki dinga yi ma ni kuka?"

Kai ta girgiza ma sa alamar a'a.

"To me aka yi ma ki na kuka ne haka?"

Shiru ba ta ce komai ba.

"Saboda an aurar da ba ke ba ga wancan ustazun ba ko?"

Shiru ta yi ma sa ko motsin kirki ta kasa yi tana dai rike da kofin a hannunta.

"To idan ma don ba'a ba ki wanda kike so ba ne ya saka kike kuka to ai ba ke kadai ke da kuka ba, ni ma da kukan zan zauna na yi ta yi, saboda masoyiyata Sidra da nake so ta gudu aka aura ma ni ke kin ga ni na sai na zauna mu yi kukan tare ko?"

Sai a lokacin ta ɗaga kai ta kalle shi, ta ga ya zuba ma ta rikitatun idanunsa yana kallon ta. Kafin ya ci gaba da cewa .

"Ban taɓa kawo wannan ranar a tarihin rayuwata ba."

Cikin kuka ta ce .

"Yaya Fahad."

"Na'am."

Ya amsa yana kallon ruwan tea dake hannunta, don kazar ma ta ce ba za ta iya ci ba.

"Ina neman wata alfarma a wajen ka."

"Ina jin ki?"

"Na san kuna son juna kai da Aunty Sidra, kuma ban san dalilin da ya sa ta tafi ranar aurenku ba, amma na san tabbas za ta dawo. Kuma soyayyar da take yi ma ka ba za ta iya cire shi daga cikin zuvuyarta ba. Ina son duk ranar da ta dawo matukar ta nuna tana son zama da kai to ka sauwaƙe ma ni sai ka aure ta, ni ma na je na auri Ya Sayyadina."

Shiru ya yi yana kallon ta kafin ya ce.

"Na ji alfarma da kika nema, zan yi ma ki ɗayaba cikin biyu. Ma'ana zan sake ki sai ki je ki auri Ya Sayyadi da kike so, amma ban ma ki alƙawarin Auren Sidra ba."

Za ta yi wata magana kenan ya ɗaga ma ta hannu. Dole ta yi shiru. Ba tare da ya kalle ta ba ya ce.

"Gud night."

Ya fita daga cikin ɗakin bayan ya rage hasken ɗakin ya ja ma ta kofar ɗakin ya rufe.

Ajiye kofin shayin ta yi ta fashe da kuka mai cike da ƙunci.

"Ta ya zan iya za zaman gidan nan da aka gina da sunan Yayata, na yi amfani da kayan ɗakin da ka ajiye da sunanta, sannan na yi amfani da kayan lefenta sannan na mallaki masoyinta da tafi kauna fiye da komai a rayuwar ta, yau a ce shi ne mijina anya za ta fahimce ni kuwa da wani ido zan kalle ta ?"


*Maman Ihsan ce*✍️

09065327995
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z


*MAKAHO NE*


*NA*

Maman Ihsan ce ✍️


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


page2️⃣0️⃣


Ta ya zan iya zaman gidan nan da aka gina da sunan Yayata,na yi amfani da kayan ɗakin da aka ajiye da sunanta, sannan na yi amfani da kayan lefenta, sannan na mallaki masoyinta da ta fi ƙauna fiye da komai a rayuwar ta, yau a ce shi ne mijina za ta fahimce ni kuwa da wani ido zan kalle ta.


_Fahad_

Yana komawa part ɗin sa kai tsaye ya nufi bedroom, bai tsaya ko ina ba sai bathroom. Don shi baya gajiya da yin wanka.

Kayan jikinsa ya cire ya tsaya jikin babban madubin dake cikin bathroom ɗin, ffaɗan ƙirjinsa ya zuba wa idanu yana kallon zanen Tattoo da ya sa aka yi ma sa , daga gefen ƙirjinsa har zuwa damtsen hannunsa. An yi ma sa zanen butterfly da kuma sunan sa haɗe da na Sidra.

Wani ɗaci ya ji a ƙasar ransa ji yake yi ina ma a ce zai iya goge wannan zanen Tattoo dake jikinsa da ya goge ko ya daina ganin sunan Sidra a jikinsa.

Wanka ya yi don shi akwai shi da yawan wanka sosai.

Almost 30 minutes ya ɗauka yana sakawar wa kansa ruwa kafin ya yi wanka da shower gel din sa mai ƙamshi.

Towel ya ɗaura a ƙugunsa dai wani ƙarami da yake tsane ruwan kansa da shi.

Gaban dressing mirror dake cikin bedroom dinsa ya tsaya. Yana kallon kansa a jikin madubin, da alama shi mutum ne mai yawan don kallon kansa a madubi.

Body spray ɗin sa ya shafa sannan ya shiga cikin closet ɗin sa. Bai sanya wasu kaya ba sai wando three-quarter fari da ya saka, ya zo ya hau saman tangamemen gadonsa ya haye daidai lokacin da wayarsa ta soma ruri.

Dubawa ya yi still number wayar ɗazu ce, kamar ba zai ɗaga ba sai kuma dai kuma ya ɗaga har lokacin bai yi magana ba.

Jin shiru ya saka ya kashe wayar gabaɗaya ya kwanta.


_Sidrah_

Gabaɗaya daren ranar ba ta yi barci ba sai kuka da ta kwana tana yi. Ta yi danaasanin tafiya ya bar aurenta, ga shi yanzu ta yi biyu babu, ba ta ga tsunsu ba ta ga tarko. Ita ba ga samun abinda ta fito nema ba don yin suna da ɗaukakar da take so ta yi. Sannan auren da ta tsallake ta baro da niyyar idan ta koma ta ba iyayenta haƙuri su haƙura da sake saka ranar ɗaurin auren sai ga shi an maye gurbin ta da ƙanwarta. Ko da a mafarki yadda ta san Fahad wayayyen mutum ɗan gaye ji da kansa ba zai taɓa amincewa ya karbi Nadra ba, amma abun mamakin sau ta ga ya amince da ita yarinyar da yake cewa kamar ba ta waye ba shi ne ya amince ya aura. Har yana iya keɓe wa da ita kenan a wanann daren, wa ya san me suka yi?

Wannan tunane-tunanen ne ya hana ta barci yake saka ta zubar da hawaye.

Fatan ta gari ya waye ta ɗauki hanyar komawa gida. Ta roki iyayenta kuma dole Nadra ta bar ma ta Fahad Majidaɗi.


_Nadra_

Bayan fitar Fahad daga ɗakin ta dinga riskar kuka kamar ranta zai fita. Don har sai da ta ji kanta na sara ma ta kamar zai fashe sannan ta yi shiru, don idanunta ko gani ma ba ta yi saboda tsabar kumburin da suka yi ma ta.

A haka ta ƙudundune waje guda da misalin karfe ukun dare ne barci ya yi nasarar ɗaukarta.


Da misalin karfe biyar na asuba wayarta ta fara ƙara kamar yadda ta saita ta. A hankali ta motsa tare da kokarin bude kumburarrun idanunta da suka yi ma ta nauyi sosai.

Addu'ar tashi daga barci. Ta tashi zaune tana dafe kanta da hannayenta biyu, dan ciwon kan nata sosai ya ƙaru.

Saukowa ta yi daga saman gadon tana rike da kanta ta nufi bathroom ɗin dake cikin ɗakin. Tana shiga ta ji jikinta na rawa sanyi take ji sosai.

Tana kakkarwa ta tashi daga duƙen da take, ta lallaɓa ta yi wanka da ruwan zafi sannan ta sake amfani da ruwan ɗumi ta gabatar da alwala ta fito ɗaure ta towel.

Da kyar take yin tafiya har ta karasa cikin closet. Komai na kayan sabo ne a ciki.

Tun daga kan kayan lefe har da kayan da aka ɗinka wa Sidra wanda iyayen su suka ɗinka ma ta, sai waɗan da Fahad ya kawo ma ta ya ce sun burge shi ne.

Cikin kayan da aka kawo ma ta daga gida ta duba bayan ta saka underwears sai sai sun matse ta kasancewar ta fi Sidra cikar halitta. Don ta fi Sidra nono da hips. Dan ko tela ma idan zai yi ma su ɗinki na Nadra yakan fi na sidra kaɗan.

Don haka pant ɗin dai ta saka ya shiga ma ta, amma bra bai shiga ba don rabin nononta a waje suke kuma sai ya maste ta, kasancewar da sunan Sidra aka ajiye komai to komai size ɗinta ne ita kuma ba ta da nono Sosai ƙanana ne da ita.

Don haka Nadra ba ta wahalar da kanta Wajan saka bra din ba ta bar nononta haka nan, kasancewar nonon nata irin ma su kan tasa ɗin nan ne a tsaye suke ƙyam.

Wata doguwar rigar material mara nauyi ta saka bayan ta sa turare sannan ta saka dogon Hijabinta ta ɗauki sallaya ta fito ta shimfiɗa.

Sallar nafila ta yi kafin ta yi sallar asuba ta zauna tana azkar.

Duk da kasancewar ta mai yawan karanta Alkur'ani ne da safe amma Yau kam ba ta jin za ta iya karatun Alkur'anin nan da ta saba.

Kwanciya ta yi a nan saman sallayar da ta yi sallah. Don ciwon kanta nan nan ba ta daina jin sa ba, ga sanyi tana ji. Don haka sai ta ƙudundune kanta cikin Hijabin a nan saman sallayar ta yi barci.


Da misalin karfe takwas na safiya a cikin ɗan barcin da ya ɗauke ta ne ta ji ƙamshin turarensa ya ziyarci hancinta.

Wani faɗuwar gaba ta tsinci kanta a ciki. Duk da ba ta son bude idsnunta da suka yi ma ta nauyi amma sai ta ɗan tashi zaune daga saman sallayar ta kalle shi da kyar.

Sanye yake da farar jallabiya a jikinsa ya tsaya a tsakiyar ɗakin yana kallon ta.

Daidai lokacin da wayarta dake kan gado ta soma ruri, tana son ta miƙe amma ta kasa.

Sai ta ga ya nufi gadon ya ɗauki wayar.

Sunan da ya gani a screen ɗin wayar yana yawo shi ne an rubuta YA SAYYADINA. Sannan aka saka emojis na love da kuma emoji na heart a gaban sunan.

Miƙa ma ta wayar ta yi ba tare da ya yi magana ba. Kuma ya tsaya a saman kanta.

Har kiran ya katse wani ya sake shigowa sannan ta ɗaga tare da yin sallama.

"Assalamu alaikum Ya sayyadi"

"Wa'alaiki Salam warahmatullah ya Sayyadata."

Shiru ba ta sake magana ba, sai dai tana da yaƙinin Fahad ɗin ma ya ji maganar Ya Sayyadi, dan wayar sauti na fita wanda ke kusa da kai zai ji maganar na cikin wayar.

"Sayyadata an watse taron biki lafiya ko?" Ban samu zuwa..."

Sai kukanta ya ji ta fashe da shi.

"Subhanallah, subhanallah ya sayyada me ya faru ne, ki faɗa ma mi make faruwa ne?"

Ya faɗa a ruɗe saboda jin kukanta.

Fahad ya karbi wayar daga hannunta ya ce.

"Kai daga yau kada ka sake kiran wayar nan?"

"A'uzubillahi me ya haɗa Sayyada da rijalu kuma, ke sayyada waye Wannan kuma? Subhanallahi A'uzubillahi minash shaiɗani rajim ƙato da wayar Sayyada da sanyin safiyar nan. Wa'iya zu billahi a'uzu billahi."

Cike da takaici Fahad ya ce.

"A'uzubillahi akanka. Kai bari na yi ma ka gargadi na karshe, idan har ka sake kiran wayar nan sai na sa an koya ma ka hankali, za ka san waye Fahad Majidaɗi."

Da sauri Ya Sayyadi ya ce.

"Fahad Majidaɗi da na sani mijin Sidra?"

Bai ba shi amsa ba ya ce.

"Ina mai maka gargadi wallahi ranar da ka sake kiran wayar nan duk inda kake a faɗin ƙasar nan sai na saka an kamo ma ni kai, ban damu da wanzuwar soyayyar dake tsakanin ka da Nadra ba, amma a halin yanzu ta yi ma ka nisar da ba zai ka iya kamo ta ba, watakila dai nan da lokaci kaɗan idan na sallame ta za ka iya zuwa gidansu ka ci gaba da alaƙa da ita ko ka aure ta wannan ba damuwata ba ce, amma a halin yanzu tana ƙarƙashina kam ƙarya ne na bar ka ka yi wata alƙa da ita, idan za ka iya jira ka je ka ci gaba da jiranta har zuwa lokacin da za ta fito, amma kam sake kiranta bayan tana ƙarƙashin iko na shi ne kuskure ma fi muni da za ka tafka a rayuwarka."

Yana gama fadar haka ya katse kiran wayar tare da yi wa Nadra wani mugun kallo."

"Ke!?"

Ya kira sunanta da kakkausar murya.

Idanunta da suka yi nauyi ta daga ta kalle shi da kumburarrun idanunta.

"Idan kika sake magana da wani ƙaton gardi a cikin gidan nan bayan kin san akwai igiyar aurena a kanki sai na shayar da ke madaran mamaki."

Ba tare da ya sake magana ba ya fice rike da wayar a hannunsa bai ba ba ta wayar ba.

Kuka ta sake fashe wa da shi wanda ya ƙara sa wa ta ji kanta na barazanar tarwatse wa.

Yana zuwa falon ya ji ƙarar ƙararrawar ƙofa, sauka downstairs ya yi ya nufi ƙofar ya zai buɗe.


_Makaho_

Ko da ya dawo daga masallaci sallar asuba ƙarfe bakwai na safiya.

Zuwa lokacin Ma'eesha ta kammala aiyukan gidanta. Ta gyara ɗaki ta share ta yi mopping ta yi wanke-wanken ta wanke toilet sannan ta yi wanka.

Dadai lokacin da ta fito da Gas da za ta hada ma su abun breakfast kenan ta ji sallamar sa ya shigo gidan.

Ta amsa ma sa sallamar ya shigo ta zuba ma sa idanun tana kallonsa.

Sai da ta durƙusa cikin girmamawa ta gaishe shi duk da baya ganinta.

"Ina kwana?"

"Lafiya lau Mar'atusaliha."

Murmushi ta yi ba tare da ta ce komai ba.

"Kin tashi lafiya?"

"Alhamdulillah."

"Ma sha Allah, sannu da ƙoƙari Allah ya saka ma ki da gidan Aljanna Firsausi."

"Amin ya rabbil izzati."

"Me kike yi ne haka, na ɗauka za ki kwanta sakamakon juya ba ki samu isasshen barci ba jiya."

"Ai na yi barci kai ne dai ya kamata ka wanta ka huta ko za ka samu barcin da ba ka samu ka yi ba."

"Ni da zan fita neman na kai ne zan kwanta na huta?"

"Wai nawa kake samu a rana wajan gyaran takalmin da kake yi ?"

"Eh to mutane da yawa ba sa yarda su ba ni aiki, kasancewar ni makaho ne ba na gani to ba sa yarda su ba ni aiki, sai su ce wai ba aikin da na iya, sai su kai wani wurin, amma wasu na bayar wa sai dai ba su da yawa. Abun sai sa'a ne wata rana ma bai wuce na samu ɗari biyu wata rana dari biyar amma ban taba samun dubu ɗaya ba. Shi ya sa nake ganin cewa ba zan iya riƙe ki ba, ban cancanci na ajiye mata ba, saboda ba na da halin ciyarwa da me zan ciyar da ke? Sam na kasa dalilin da ya sa iyayenki suka aura ma ni ke, bayan kin saba da cin abinci mai kyau mai tsada, ruwan sha mai tsada sutura mai tsada kayan kwalliya ma su tsada ta ya zan iya yi ma ki duk abubuwan da kika saba da su?"

Murmushi ta yi tare da cewa.

"Dama haka rayuwa ta gada, ba komai yake tafiya a yadda yake a da ba."

Haka ne Ma'eesha, amma na rasa gane me kike son ki ci ma wa a rayuwa, ko me kike so ki zama meye burin ki?"

Murmushi ta yi kafin ta ce.

"Ina son na zama mace tagari mai tsoron Allah a fili da ɓoye, tare da biyayya ga manzon Allah
mai biyayya ga iyayenta ɗari bisa ɗari da kyautatawa, mai biyayya ga mijinta, idan ya hana ta hanu, idan ya sa za tayi. Wacce take ɓoye adonta ga mazan waje, ta bayyana shi ga mijinta. Wacce take da kunya, gaskiya, adalci da tausayin mijinta. Wacce ba munafuka ba, ba ta sharri dan ta jingina karya a mijinta. Mace mai girmama iyayen mijinta da yan uwansa saboda Allah mace mai gudun duniya da neman na kanta kamar Nana Khadija.
Mace mai tallafawa mijinta da dawainiyar gida kamar Nana Fatima. Mace mai kishin mijinta kamar Nana Aisha."

Allah sarki ƴar aljanna, yanzu kina ganin za ki iya karɓa ta a matsayin mijin aurenki, za ki rayu da ni a cikin kowane hali?"

"Me ya saka ka yi Mani wanan tambaya?"

"Saboda na ga kin fi ƙarfin na, ke ba ajina ba ce kin wuce sa'ar aurena, a matsayina na nakasashshe miskini ta ya ke da kika rayu cikin daula da wadata za ki iya zama da ni?"

"Me za hana na zauna da kai idan ƙaddarar aurena da kai ne Allah ya tsara?" Ba na son na fita daga cikin salihan bayi ma su godiya da duk abin da Allah ya aiko ma su da shi? Mai daɗi ko mara daɗi, ma su jiran ƙaddara duk daɗinta duk raɗaɗinta su haɗiye ta, ko ba ka san cewa Allah ya fi mu sanin abun da ya dace da mu ba?"

Jinjina kai ya yi tare da cewa.

"Haka ne?"

Murmushi ta yi kafin ta ce.

"Ina son ka ba ni tarihin rayuwarka ban san kowa naka ba, ina son sanin Asalinka?"


*Maman Ihsan ce*✍️

09065327995

Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z


*MAKAHO NE*


*NA*

Maman Ihsan ce ✍️


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


page2️⃣1️⃣

Ina son ka ba ni tarihin rayuwarka ban san kowa naka ba, ina son sanin Asalinka.

Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce.

"Yanzu aiki kike yi, ki ci gaba da yin aikinki idan muka b zauna ba ki aikin komai ni ma ba na komai sai na baki."

"To shi kenan, bari na haɗa ma na breakfast."

Shiga cikin ɗakin ya yi ya bar ta nan tana kiciniyar ɗora girki.

Tana nan zaune ta ga ya fito daga ɗakin rike da wasu kayan a hannunsa, da alama wanka zai shiga.

"Ka bari na sa ma ka ruwan zafi ka yi da shi don akwai sanyin safiya."

Murmushi ya yi tare cewa.

"Ma'eesha kenan, ni da na saba da ruwan sanyi me zai dame ni kuma yanzu? In dai wannan ne na saba da shi kar ki damu kanki, babu irin rayuwar da ban gani ba."

"Na sani amma ya kamata ka san cewa tsakanin da da yanzu akwai banbanci, da ba ka da aure ba ka da wacce za ta dafa ma ka ruwan zafi ka yi ji wanka, yi yanzu Allah ya ba ka ya kamata ka san cewa akwai banbanci tsakanin lokacin da kake da aure da yanzu. Yanzu fa ɗan gata kake mai cikakken iko, ka saka ayi ka haka a hani ai kuwa ka ga da banbanci ko?"

"Haka ne."

"To ba ni mintuna biyar kaɗai zan dafa ma ka ruwan zafi yanzu."

Zama ya yi akan dangaramar ƙofar ɗaki ta zuba ruwa a cikin tukunya ya yi zafi sannan ta juye ma sa cikin bokitin ta mai ma sa har cikin ɓanɗaki."

"Na mai ma ka ruwan cikin banɗaki."

"Na gode ma ki Ma'eesha Allah ya yi ma ki albarka."

Da Amin ta amsa sannan ya shiga banɗaki, ta fara kiciniyar haɗa ma su breakfast.

Bayan ya gama ya fito sanye da wasu kayan a jikinsa, waɗanda ya cire kuma suna a hannunsa.

Kallonsa ta yi sannan ta ce.

"Wai me ya saka da ka yi wanka kake saka kaya ne, kar ka damu ko da ba ka gani na ai idan za ka canza kaya zan fito daga cikin ɗakin na ba ka wuri ka shirya ne, amma ace daga yin wanka ba ka tsane jiki ba kuma ba ka shafa man shafawa ba kawai sai ka ɗauki wasu kaya ka saka?"

"Za'a daina in sha Allah."

"Da ya fi."

Ta faɗa tana mai cigaba da fere dankalin turawar da take yi.

"Bari na tso na ba ka man shafawa da turare ka shafa."

Ta mike ta bishi cikin ɗakin.

Man shafawar da ta ba shi ya shafa ne ya shafa ya kuma ya shafa turaren da ta ba shi.

Tana nan zaune ya fito yana yana cewa.

"Aikin me zan yi ma ki ne na fara yin yanzu kafin na fita ."

"Ka fita ina?"

"Neman na kai mana."

"Yau da alama za'ayi rana a garin nan, ka je kana ta wahala a cikn rana bai fi ka samo Naira ɗari biyar ba. Don haka cinikin yau na siye zan ba ka Naira dubu ɗaya ka ga ai na ba ka fiye da cinikin da kake yi ."

Ga mamakin ta sai ta ga ya tsuke fuska alamar ransa ya ɓaci.


_Fahad_

Kafin ya karasa bakin ƙofar har an dake danna wata ƙararrwar.

Yana bude ƙofar ya ga ƙanwarsa Rumaisa ce rike da basket na abinci.

Sai wasu ƴan mata guda biyu tare da ita, yan matan duk danginsu ne da suka zo biki daga wani garin.

Basket ɗin abinci ne a hannun Rumaisa. A tare suka haɗa baki wajen cewa.

"Yaya Fahad ina wuni?"

Bai amsa ma su gaisuwar da suke yi ma sa ba, hannu ya mika wa Rumaisa alamar ta ba shi basket ɗin hannunta.

Ta mika ma sa ya karba zai mayar da ƙofar ya rufe ta ji saurin cewa.

"Yaya Please za mu ga Amarya."

Tsuke fuska ya yi kafin ya ce.

"Wani lokacin za ku ganta."

Marairaice fuska suka yi suka hada baki wajen cewa.

"Yaya Please."

Rumaisa ta ɗora da cewa .

"Kuma dama Mama ta ce idan mun zo mu shiga mu gaishe ta mu ce kuma tana gaishe ta."

Sauran suka hada baki wajem cewa.

"Eh haka ne."

Ba su hanya ya yi alamar su shiga ba tare da ya ce komai ba.

Suna shiga ya mayar da kofar ya rufe. Suka Zazzauna a fakon kan kujerun dake downstairs.

Upstairs ya haye sannan ya ajiye abincin a dinning table ya nufi ɗakinta.

Kuka take yi har lokacin tana kuɗudune kan sallayar.

Ba ta ji shigowarsa ba sai ƙamshin turarensa da ta ji ya ne ya sa ta tsaida kukan nata, ta ɗago kumburarrun idanunta ta kalle shi. Tana ɗan dafe kanta.

"Tashi ki fito ƙannena suka zo kawo abinci Mama ta ce su gaida ke idan sun zo."

Tashi ta fara yinƙurin yi tana cije lips din ta na ƙasa.

"Ki shiga bathroom ki wanke fuska ba na bukatar sake ganin wannan hawayen."

Bathroom ta shiga ta wanke fuska kamar yadda ya umarce ta.

Bayan ta fito ne ya yi hana tana bin sa a baya suka fita.

A tunaninta suna nan upstairs ne, ganin ya nufi downstairs ta na tafiya a hankali tana jine lips sakamakon ciwon kan da ya sa ta gaba.

A hankali take tafiya tana sanye da hijabinta har ƙasa sai flat shoe dake ƙafarta.

",Zuba ma su idanu suka yi suna kallon su. Musamman Nadra da da duk wanda ya kalle ta ya san tasha kuka.

Cike da ƙarfin hali take tafiya don har wani jiri take ji.

Daf da za su sauka daga matattakalar kenan ta ji kanta na juyawa ta yi kamar za ta faɗi.

Ganin haka ya saka ya yi saurin rike ta ya ga ta yi luu za ta yi baya.

Cikin zafin nama ya taro ta ya ɗaga ta cak ya koma da ita sama ba tare da ya karasa da ita wajen su Rumaisa sun gaisa ba.

Kallon kallo aka fara yi tsakanin Rumaisa da cousin sister ɗin ta guda biyu da suka zo tare.

Ɗaya daga cikinsu ce ta saka dariya yana cewa.

"To fa, Yaya Fahad ya ɓaro aiki kenan, to amma ba an ce baya son ta ba? To ya hakan ta faru?"

Rumaisa ta kalle ta tare da cewa.

"Me kenan ya faru?"

"Ba ki ga alamar Yayanki ya sha romon amarci ba daren jiya, ki kalli yadda idanunta suka kumbura tsabar kuka, sannan tafiya ma ta kasa yi sai da ya ɗauke ta."

Cike da tausaya wa Rumaisa ta ce.

"Allah sarki."

Ɗayar wacce ba ta yi magana ba ta ce.

Ku ga fa da yake cewa baya son auren har jiya fa da ƙyar Mama ta saka shi gaba ya bar gida, da cewa ya yi ba zai zo nan gidan ba Sa sanya ga ɓacin ran Mama sannan ya zo ya tare, amma da ke namiji munafiki ne har ya iya azabtar da ƴar mutane ta kasa tafiyar don jaraba.

Gabaɗaya suka saka dariya da shewa. Dadai lokacin ne suka ji ƙamshin turarensa suka juya suka kalle shi.

"Ku tashi ku tafi kun zo kuna ma ni ihu a gida."

Kamar suna jira kowacce ta mike suka nufi hanyar fita.

Komawa ya yi sama ya shiga kitchen ya haɗa ma ta tea sannan ya nufi ɗakinta don kai ma ta, ya dawo ya zo dinning ya ɗauki basket ɗin da Mama ta aikio ma su da shi, sannan ya ɗauki plate a kitchen ya wanke da cokali sannan ya koma ɗakinta.

Food flask ɗin ya bude ɗaya, farfesun kan rago ne, ya zuba ma ta. Sai ya bude wani ya ga wainar shinkafa ce sai miyar taushe daban.

Tea ya miƙa ma ta.

"Karɓi ki sha."

Ba ta jin shan komai don haka ta ce.

Ta girgiza ma sa kai ba tare da ta yi magana ba.,

"Ba na son sake maimaita magana ɗaya."

Ya faɗa cikin tsare gida. Karɓa ta yi ta fara sha.

"Na kawo ma ki bread?"

Kai ta girgiza alamar a'a, sai ya miƙa ma ta farfesun.

Da ƙyar ta iya cin guda uku ta ajiye.

Bayan ya karbi kofin da plate ɗin ne ya fice da su, sannan ya dawo tare da magani a hannunsa. Ruwa ɗauka a cikin fridge dake nan cikin ɗakin.

Ya ɓalli magani ya ba ta sannan ya zuba ruwa a glass cup ya ba ta ta sha.

Jingina ta ji da kan filo da ke kan gadon, ba tare da ta kwanta ba.

Fita ya yi daga cikin ɗakin bayan ya ɗauki basket ɗin abinci ya fita da shi ya ajiye a dinning table.

Bedroom ɗin sa ya nufa ya ciro wayar Nadra da ta karɓa ya kunna yana dubawa.

Ba ta amfani da social media sosai don what's up kawai ya ga tana yi, ya shiga ya duba shi ma daga ƴan uwanta sai ƙawarta da Ya Sayyadi ne suke yin chatting da shi. Ba ta da groups har wurin text message sai da ya duba. Nan ma ya ga ba wani abu ba rashin daidai da take yi.

Ya tuna idan ya karbi wayar Sidra ita ce TikTok, Instagram, Facebook, twitter da sauran su, ga tarin groups kamar Hauka groups ɗin na na maza da mata ba wai iya mata zalla ba. Kuma bai ga group ɗin ƙaruwa ba ko na faɗakarwa sai irin su. Manyan mata, ƙasaitattun mata, mata ma su aji, ma su ji da kansu, wayayyun mata. Da sai sauran su.

Amma nan wayar Nadra ya ga ba ma kullun take hawa what's up din ba, wa'azuzzuka na ma manyan malamai ne suka cika wayar video da Audio.

Kashe wayar ya yi gabaɗaya ya bude side drawer ya saka ta a ciki.


_Rumaisa_

Bayan direba ya ajiye su a gida ne suka fita duka su uku ne dama suka je gidan. Rumaisa, Rahina da Sahiba.

Suna fita daga motar jikinsu na rawa suka shiga cikin falon.

Nan suka ga gabaɗaya mutanen gidan suna falo har da ɓaƙi da suka zo daga wasu garuruwa. Dariya suka shiga suna yi gabaɗaya mutanen suka mayar da hankali suna kallon su.

Inna wato kakar su Fahad ta kalle su ta ce .

"Waɗan nan sabbin mahaukatan fa?"

Sahiba ta yi saurin cewa

"Wallahi ba hauka ba ne Yaya Fahad ko?"

"Me ya yi Fahad ɗin?"

Cewar Hajiya Jummai mahaifiyar Farida.

Rahina ta ce.

"Jiya nan ya dinga cewa baya son auren nan, har sai da aka kore shi daga gidan nan ya tafi wajan Amaryarsa. To ga Amarya can idanunta sun kumbura tsabar kuka tafiya ma ba ta iya yi sai ya ɗauke ta kinga yadda ta koma yake wani tarairayarta ko tafiya sai ya ɗauke ta Allah ya sa bai illata ta ba."

Rahina ta yi maganar kasancewar bazawara ce ta yi aure shekara ɗaya auren ya mutu.

Gabɗaya falon aka yi shiru Mama ko ta yi farin cikin jin haka yayin da bakin ciki ya kama Hajiya Jummai saboda tana taya ƴarta Farida kishi.

Farida ko kasa haɗirye ƙincinta ta yi sai kawai ta tashi ta bar wajen tana kuka

Dinning area ya nufa ya zauna ya ci waninar da Mama ta kawo ya sha farfesun kaɗan sannan ya tashi.

Yana shiga bedroom ɗin sa ya ga wayarsa na ruri. Ya duba ya ga Mama ce.

Ɗauka ya yi tare da yin sallama.

"Assalamu alaikum."

Daga xan bangaren ta amsa tare da cewa.

"Ya kuke?"

"Alhamdulillah."

"Ya Nadra take ƙannenka sun ce ba ta da lafiya ko?"

"Eh haka ne."

"To ka kula da ita, ta zauna cikin ruwan zafi ba wanda zai kuma yi ma ta illa ba, sannan ka bar ta ta huta a ƙalla ko na sati ɗaya ne kar ka takura ma ta, don Allah ka bi ta a hankali, na tabbata da daren jiya ka bi ta a hankali da ba za ta jigata haka nan ba."

Shiru ya yi bai iya cewa mahaifiyar tasa komai ba, don bai gane in da zancen ta ya dosa ba,kafin ya yi magana ya ji ta katse kiran wayar.

Maganganun nata ne suka fara yi ma sa yawa a ƙwaƙwalwarsa. Me zai saka ta zauna a cikin ruwan zafi, kuma akan me zai ɗaga ma ta ƙafa na sati ɗaya. Mama tana magana ne kamar ya kusanci Nasra alhalin ba abinda ya shiga tsakaninsa da ita. To me ya saka ta ce haka. Ya san dai haka nan kawai Mama ba za ta ji zargin wani abu a tsakaninsu da Nadra ba. Tuna zuwa ƙannensa da suka yi kawo ma su breakfast ya sa shi tunanin akwai maganar da suka yi. Mai yiwuwa don sun ga alamar ta sha kuka ne, to me zai saka su faɗi abin da ba su da tabbas akan sa.

Daga nan ya tashi ya shiga bedroom ɗin sa. Kayan jikinsa ya rage ya shiga wanka.

Yana tsaye yana kallon kansa a madubi kamar yadda ya zame ma sa ɗabi'a. A da idan ya ga Tattoo dake jikinsa ya kalli sunan Sidra da butterfly yakan yi Murmushi.

Amma yanzu ji yake yi da zai iya da ya goge sunan daga jikinsa. Ji yake yi kamar ya samu reza ya ya kankare fatar jikinsa.

Wanka ya yi da shower gel din sa mai ƙamshi sannan ya ɗaura towel ya fito yana tsane ruwan kansa.

Man shafawarsa ya shafa ya fesa body spray ya shiga closet ɗin sa.

Shirya wa ya yi cikin ƙanan kaya farar Tshirt mai tsada da wando jeans, ya duba ɓangaren takalmominsa kambas masu tsada, saidesigner sneaker ya saka a ƙafarsa shi ma fari ya ɗaura tsadadden agogonsa Rolex GMT- master ll pepsi sannan ya fesa turarensa Bleu de Chanel (farfum) duk wanda ya gansa ya ga gentleman na gaske mai tsafta da kuma classy.

Fitowa ya yi daga cikin closet ɗin ya ɗauki wayoyinsa da makullin motarsa ya fice cikin takunsa na ƙasaita.

Har zai wuce sai ya tuna da ita ya koma ɗakinta


_Maeesha_

Ganin makaho ya tsuke ne ya ba ta mamaki don ita a fahimtar ta ba ta san ta jmyi ta yi wani abu na rashin daidai ba.

"Ka yi hakuri idan na faɗi wata magana da ba ta yi ma ka daɗi ba."

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce.

"Ma'eesha mutane suna raina sana'ar nan da nake yi ba na jin daɗi, domin ni albarkarta nake nema. Amma yau ke da kanki kike raina sana'ar?

"Ka yi hakuri ba yadda ka fahimta ba ne, ni so nake ka huta saboda ana rana, ina tausaya ma ka ne shi ya sa na ce kudin da kake samu bai fi ɗari biyar ba zan ba ka dubu ɗaya ka zauna ka huta a gida."

"Ba na so ki rike kudin ki ni zan fita na nemi gumina da kaina. Ba son raina ba ne na zauna a ce kina ɗaukar nauyin da ya rataya a kaina, na san ba zan iya ɗaukar nauyin ki ba, amma ina son ɗaukar ko da kwatankwacin nauyin ki ba, zan kwatanta, domin ma wata rana zan yi alfahari da cewa na yi wa matata wani abun kuma ta karɓa ta yi amfani da shi. Ki yi hakuri idan kin ji ba daɗi kinji ƴar aljanna ."

Murmushi ta yi tana cewa.

"Allah ya buɗa ma ka hanyar samu mijina."

"Amin matata."

Tea ta haɗa ma sa ta bashi bread sai soyayyen dankalin turawa da ƙwai.

Suna ci suna ɗan taɓa fira sama-sama. Kafin ya ce.

"Yanzu Ma'eesha idan aka wayi gari kayan abincin da kuma siyo sun ƙare, musamman waɗan nan na ku na gayu da kika saba ci kuka ya kasace ba na da kuɗin siya ma ki irin su fa?"

"Ba damuwa Allah ke ciyar wa ba mutum ba, duk abinda Allah ya hore ma ka ka kawo zan karba na yi godiya ga Allah, tare da maka addu'a buɗi daga wajensa.

Nan suka cigaba da fira har suka kammala sai da ya yi niyyar yi ma ta wanke-wanke ta hana. Dole ya fita bayan ya ɗauki kayan aikinsa na ɗinkin takalma.


Yana tsaka da tafiya ya ji kamar ana binsa bayan ya yi nisa da layin, kuka da dukkan alamu mota ce ke bin bayansa. Jin hakan da ya ji ne ya saka shi ya tsaya daga tafiyar da yake yi, motar ma ta tsaya, wata baƙar mota ce tinted glass.

Bayan ya fita daga layin ne ya shiga wani layi sai ya tsaya cak da tafiyar da yake yi, motar ma ta tsaya daga bin sa da take daidai lokacin da ya saki sanadar hannunsa.


*Maman Ihsan ce*✍️


09065327995

Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z


Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z


*MAKAHO NE*


*NA*

Maman Ihsan ce ✍️


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


page2️⃣2️⃣


Bayan ya fita daga layin ne ya shiga wani layi, sai ya tsaya cak da tafiyar da yake yi, motar ma ta tsaya daga bin sa da take yi daidai lokacin da ya saki sanar hannunsa. Sannan ya saki kayan aikinsa na gyaran keke.

A fusace ya juyo bayansa tamkar mai gani, yayin da matuƙin motar ya yi arba da shi dai ya figi motar a guje tamkar mai gani.

Jin motar ta bar wajen Khalifa Makaho bai yi magana ba ya lalubi sandarsa da basket na kayan aikinsa ya yi wucewarsa in da za shi.

Ya ɗan yi tafiya mai nisa sannan ya ƙarasa bakin wata karama titi. Da sallama ya ƙarasa wajen, yayin da wasu dake wajan suka amsa tare da cewa.

"Ka iso Khalifa?"

"Eh ina kwanaku?"

"Lafiya lau Alhamdulillah."

"Ma sha Allah."

Mutane ne a wajen duk da ba sosai ba, don wajen karamar titi ne, kuma akwai hanyar da za ta sada ki unguwar masu kuɗi wanda hanyar suke bi zuwa cikin unguwanninsu.

Ba Makaho ba ne kaɗai a wajen, akwai mutane ma su kananan sana'o'i a wajen suke zaune. Akwai mai siyar da yalo a wajen, da mai siyar da kifi gangariya a wajen da wani mai baro dake sigar da Aya sai wata mace mai suyan awara a wajen, daga gefe kuma ga mai shinkafa da wake da mai da yaji.

Duk suna wajen saboda babban bishiyar mangwaro ce a wajan ta yi inuwa mai fadi.

Nan ne wajen sana'ar Khalifa nan take zama ƙasan bishiyar. Wata rana kuma yakan bar wajan ya yi ta yawo yana neman wanda takalminsa ya tsinke.

Mai awara ta kalli Khalifa ta yi Murmushi dama ta saba tsokanarsa a wajen.

"Kyakkyawa ya kake?"

Ta fada tana Murmushi.

"Kyakkyawa don Allah ka dinga sakin fuska ma ma kai kenan fuska ɗaure tamau ba murmushi ba dariya kamar wanda aka aikawa saƙon mutuwa."

Bai tanka ma ta ba kamar kullum dama baya tanka ma ta ita ma ba ta fasa tsokanarsa.

Mai siyar da yalo ne ya yi magana ya ce.

"Wai ke Laure ba za ki ƙyale wannan bawan Allah ba ne, kullum sai kin dame shi da surutu, kuma baya tanka ki ."

"Ilu mai yalo ka bar ni, ina son ya yi magana ce na ji muryarsa. Ka san Allah makatntar nan tashi ce kawai cikas ɗinsa. Amma da ba don makaho ba ne wallahi ba na aure shi ko da bai da kudi kuwa. Don ko kyakkyawar surarsa na kalla zan ji daɗi saboda ya haɗu iya haɗuwa rashin idanunsa ne matsalarsa, kuma gaskiya ba zan iya auren makaho ba, don makantar idanun ai mutuwar tsaye ne ba zan iya ba don wahala zan yi da kai. Amma wallahi kana da siffar da kowace mace za ta so ka."

Shi dai Khalifa bai ce komai ba yi ya yi kamar bai ji ta ba.

Tunanin Ma'eesha yake yi, ga wata da ba ƴar kowa ba ƴar talakawa tana cewa tana son sa amma ba za ta iya auren makaho ba. Ta ɗauki makantarsa a matsayin kasawarsa. Amma Ma'eesha gata can ƴar masu kuɗi wacce ta taso cikin kudi da gata da kayan more rayuwa kamar ta amma ba ta ɗauki makantarsa a matsayin kasawarsa ba a haka take son da take faranta ma sa rai ba ta damu da makantarsa ba tana rayuwa cikin farin ciki da walwala.

Bai san lokacin da ya yi wani sanyayyen murmushi ba tare da sanya ma ta albarka a zuciyarsa.

Wani matashin saurayi ya zo wajen sakamakon hangen kayan gyaran takalmin da ya yi ne ya zo.

"Ina mai gyaran takalmin?"

Khalifa ya ce ma sa baki nan."

Ya kalle shi ya mika ma sa takalmin daga ɗan nesa da shi.

Sai ya ga yana lalube yana cewa.

"Ina takalmin yake bawan Allah ka matso kusa mana."

Ganin yana lalube ya saka shi cewa.

"Ban gane ba wai makaho ne yake lalube ko me? Bai ma ganni ba ko?"

",Eh makaho ne amma ya iya aiki sosai zai yi ma ka yanzu."

Cewar Ilu mai yalo yana kokarin karbar takalmin don ya mikawa Khalifa.

"Dalla Mallam bar ni, hauka nake yi ne, ko na yi ma ka kama da mahaulaci ne da zan ɗauki takalmi na ba wa makaho salon ya mayar ma ni da takalmin nakasashshe kamarsa ko? Wannan nakasashshen sai dai ya nakasa tsakalmi ba dai ya gyara ba."

Yana fadar haka ya figi takalmimsa yana barin wajen.

Cike da tausayinsa Ilu mai yalo ya dafa kadarsa ya ce.

"Kar ka damu abokina Allah ya sa ba rabonka ba ne, Allah zai kawo ma ka rabonka ka ji."

Murmushi ya masa tare da cewa.

"Ba komai."


_Nadra_

Tana nan zaune saman gadon sakamakon zufa da ta ji ya karyo ma ta bayan maganin zazzaɓi da Fahad ya ba ta. Ta ji ba wani ciwo garau take ji.

Hakan ya saka ta cire hijabinta ta ajiye a gefe. Ta ji kewar gida tana son ta yi magana da Umma da Abba amma ga Fahad ya karɓe ma ta waya

Tana nan zaune ta yi jigum sai ta ga an turo kofar dakin, ta daga kai ta kalle shi ta ga yana shigowa kai tsaye. Da sauri ta janyo hijabinta ta na sakawa tare da ƙudundune jikinta waje ɗaya.

Mamaki ya cika shi ganin yadda duk ta taburce wurin saka hijabinta bayan tana da riga a cikinta ba wai tsirara take ba, kuma bayan haka nan ai shi mijinta ne halak ɗin sa ne ko da ya ganta tsirara ba ai ta halatta a gare shi amma sai wani noƙe wa take yi cikin hijabi.

Zuba ma ta idanun ya yana tsaye hannayensa suka biyu cikin aljihun jeans ɗin dake jikinsa.

Jin ba ta sake jin takusana ba kuma bai yi magana ba sai ta ɗaga kai ta kalli in da yake. Idanunta ne suka sarƙe cikin nasa.

Ya zuba wa kyakkyawar fuskarta idanu, sam ba ta kama da masoyiyarsa Sidra. Don ita Sidra fara ce sol kuka fuskarta doguwa ce idsnunta madaidaita hancinta dogo ne sai bakinta wanda shi ma madaidaici ne ba za ka kira ta mai ƙaramin baki ba kuma ba za ka kira ta mai babban baki ba. Ita kuma wannan Nadra baƙa ce amma baƙinta mai kyau ne irin mai sheƙin nan fatarta tana glowing ne, round face ne da ita, don fuskarta a zagaye yake, idanunta dara-dara ne hancinta dogo ne haka bakinta ma ƙarami ne laɓɓanta pink ne don a zahirin gaskiya ta fi Sidra kyawun fuska, sai dai kasancewar ta baƙa ba kowa ke ganin kyawunta kamar yadda ake ganin kyawun nata ba Ita kuma Sidra hasken fatarta yake kara haska ta don ita Sidra doguwa ce ba ta da cikar halitta sosai saɓanin Nadra dake da hips da kuma manyan nono. Amma kasancewar kullun tana cikin hijabi ya sa ba'a ganin dirin jikinta, ita kuma Sidra ba ta saka hijabi mayafin ma sai ta ga dama take saka shi.

Tura baki ta yi ganin yadda yake kallonta kuma kamar tunani yake yi.

Kara ƙanƙame jiki ta yi cikin Hijabin tana tura baki.

"Ya jikin na naki?"

"Da sauƙi."

Ta fada tana sunkuyar da kai ƙasa."

"Me ke ma ki ciwo yanzu?"

"Ba komai."

Jinjina kai ta yi kafin ya ce.

"Akwai abun da kike buƙata ne?"

"Ba komai."

Daga haka ya nufi hanyar fita, sai ya juyo ya ce.

"San fita na san Mama za ta aiko ma ki da abinci."

Daga haka ya nufi hanyar fita ya fice daga ɗakin.

Daga haka ya nufi kofar fita in da ya nufi parking space, motorsa ya nufa ya shiga.

Tun kafin ya danna horn maigadi ya wangala ma sa gate ɗin gidan.

Yana fita ta mike ta fara ƙokarin gyara ɗakin.

Toilet ta wanke sannan ta zo ta gyara ɗakin tas.

Falo ta nufa kai tsaye duk da ba wani gyara amma haka ta gyara shi, sannan ta shiga kitchen ta yi wanke-wanke ta gyara shi ta goge wajen da ya dace.

Ɗakinta ta koma ta yi wanka ta fito mayyukan shafawar da ta gani an jera ma ta ma su tsada ta shafa, sannan ta saka underwears don singileti ta saka da wando ta duba kayan ta rasa wanda za ta saka. Domin ita tana son saka rigar Abaya ce ko kayan da ya ke rufe jiki kuma ta sake a ciki ba tare da ta takura ba. To nan kayan kuka duk kaya ne da Fahad ya siya da sunan Sidra don irin kayan da take son sakawa kenan ma su kama jiki, sai kuma na gida wanda iyayen su suka siya ma ta ta kai wa tela duk irin kayan da take so ta saka aka yi ma ta.

Rasa kayan da za ta saka ta jan tsuki cike da takaici.

Wani riga da siket ta saka duk da ya kama ta amma sai ta bar shi kasancewar ta san za ta saka hijabi.

Hijabi ta dauka ta saka sannan ta fita zuwa falon.

Ba ta wuce mintuna biyar ba ta sauka downstairs.

Kallon gidan take yi wanda ya haɗu iya haɗuwa. Komai na gidan na musamman ne, gini ne mai kyau da tsari na zamani.

Tuna Sidra ta yi kawai sai ta goge ƙwallar da ta ji ya cika ma ta idanun.

"Ƴar uwa ina kika shiga ne, me ya sa kika gudu kika bar takarda meye dalilin hakan. Ga ni a gidan da ya dace a ce kece kike ciki tare da masoyinki Yaya Fahad. Don Allah ki dawo akan lokaci Abba da Umma suna fushi da ke."

Ta yi maganar tana goge hawayenta.

Ƙarar ƙararrawar ƙofa ta ji ya saka ta gyara zaman Hijabin jikinta ta nufi ƙofar ta buɗe.

Cike da murna ta ce.

"Gwaggo Laraba."

Ta rungume ta tana dariya. Sannan ta kalli saura mutanen duk danginsu ne da suka zo daga ƙauye bikin auren.

Cike da murna ta tarbe su ta yi ma su iso zuwa ciki.


_Ya Sayyadi_


Tun da Fahad Majidaɗi ya yi masa gargaɗi akan Nadra ya kasa ƙwaƙwaran motsi. Shin me ye zai saka Fahad da da yake auren Sidra ya ma sa haka, yana da wannan ikon da zai ma sa barazana. Me ya taka ne ko iyayen Nadra sun san da zaman sa amma ba su ma sa shamaki da ita ba sai shi bare a wajenta, kawai don yana auren Yayarta. Har yana cewa zai saka a Kamo shi duk in da ya shiga a faɗin ƙasar nan.

Jiki ba ƙwari ya shirya cikin jallabiya da ɗagaggen wando ƙwaurin ƙafarsa a waje.

Babur ɗinsa ya ɗauka ya tayar ya nufi gidan su Nadra.


*Maman Ihsan ce*✍️

09065327995

Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z


*MAKAHO NE*


*NA*

Maman Ihsan ce ✍️


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


page2️⃣3️⃣


Babur ɗin sa ya ɗauka ya tayar ya nufi gidan su Nadra.

A ƙofar gidan ya tsayar da babur ɗinsa sannan ya tsaya yana danna horn. Maigadin na jinsa ya share shi har sai da Direban ya yi magana .

"Ba ka ji ana horn ba ne?"

"Rabu da ɗan wahala."

"Waye wai?"

Direban ya sake tambayar maigadi.

"Oh kai ba ka gane ko waye ba, ai ni tun da na ji wannan ƙarar babur ɗin kamar an tayar da injin ɗin markaɗe na san wannan Ustaz ɗin ne dake son Nadra. Ni idan ba shi da tsarin idanun ba ina shi ina neman aure a wannan katafaren gidan. Ai ruwa ba sa'an Kwando ba ne, yana talaka da shi ko sutura arziki bai da ita kayansa fa kala uku ne jallabiya uku yake da su daga wata fara sai baƙa da wata Blue su kenan kayan nasa sai hular taɓa ni ka ji hadisi da wani takalmin robarsa da ta so ta yi ma sa yawa."

Dariya direban ya saka yana cewa.

"Kai Mallam Musa ba ka da dama, haka ka sa wa Ya Sayyadi idanu?"

"Ba dole ba, saboda ina jin takaici a ce wai kamar ƴa a gidan nan ba ƴar aiki ba ƴar ma su gida a ce ita yake so. Ita kuma Nadra da yake ba ta damu da rayuwar duniya ba kuma ba ta duba girma da ta fito ba amma ta yarda ta karbi soyayyarsa haka zai zo ta fito har ta kawo ma sa ruwa da Abinci. Idan da Sidra ce ya isa ya ce yana son ta ai wargi ma wuri yake samu."

Dariya direba ya yi ya ce.

"Har ka tuna ma ni ranar da Sidra ta mare shi saboda ya bugar ma ta mota ."

Maigadin ya saka dariya ya ce.

"Dama ita Sidra ai ba ta da hakuri ban san yadda aka ji aka fasa auren Sidra ba aka ɗaura da Nadra."

Kafin ya yi wata magana suka ji ana buga gate ɗin gidan da ɗan ƙarfi, hakan ya saka maigadi ya tashi da sauri yana cewa.

"Waye ke damun mutane a wajen?"

Ya faɗa yana buɗe karamar ƙofar.

"Assalamu alaikum warahmatullah."

Ya faɗa yana miƙa wa Maigadi hannu don su yi masabaha.

Maigadin ya mika ma sa hannu tare da cewa

"Wa'alaika Salam."

"Ma sha Allah, ya lokaci ya kuma aiki?"

"Ga shi Muna ta yi."

"Ma sha Allah, Allah ya taimaka ya yi jagora."

"Bai amsa ma sa ya ce.

"Ustaz ka shigo."

Ya fada yana ba shi hanya, ya shigo da babur ɗin nasa ciki ya ajiye a harabar gidan daga gefe.

Sannan ya ƙarasa wajen da Direban yake suka gaisa. Maigadin ya ce .

"Ka zo ka yi bankwana da mu ne?"

Cikin rashin fahimta Ya Sayyadi ya ce .

"Bankwana aka me fa?"

"To dama me za ka sake zuwa yi a nan, tunda wacce kake zuwa dominta ta yi aure."

Wani kallo ya yi wa Maigadi kafin ya ce.

"Amma ba ka cikin hayyacinka ko? Yarinyar da babu wanda take so sai ni ne ta yi aure? Wannan da'ifin labari ne bari na je na ji sahihin labari daga bakin da baya ƙarya.

Ya tafi zuwa cikin gidan yana tafiya kamar zai kife a ƙasa.

"Assalamu alaikum."

Daidai lokacin da LUBE mai aiki ta buɗe kofar, ganinsa ya sa ta gaida shi, bai amsa ba ya ce ta sanar da Abba ya zo yana son magana da shi.

Ta nufi part Abba ta same shi shi da Gwaggo Maimuna da Ammi.

Ta gaishe su sannan ta sanar da su saƙon ya Sayyadi. Sai da suka kalli juna Abba da Gwaggo Maimuna sannan Abbabyq ce a sanar shi ya shigo.

Bayan ya shigo ya gaida su suka suka amsa cike da kulawa.

Nam yake sanar da Abba Fahad Majidaɗi ya yi masa rashin mutunci har da ka sa barazanar idan ya sake kiran wayar Nadra sai ya sa a ɗauko ma sa shi a fadin ƙasar nan, wai idan bai daina ba ba shi ne kuskure mafi muni da zai tafka a rayuwarsa.

Ajiyar zuciya mai ƙarfi Abba ya sauke sannan ya ya yi wa Ustaz ɗin takaitaccen bayanin abin da ya faru, sannan ya bashi haƙuri akan cewa ba su da wani zaɓi ne da ya wuce su aura ma sa Nadra a madadin Sidra. Ba za su bari alsu kunyata ba a idanun duniya mutuncinsu ya zube taron da jama'a suka zo wasu daga wasu garuruwa a ce sun watse haka nan ba tare da an yi ɗaurin auren da suka taro domin sa ba.

Kuka wiwi Ustaz ke yi na rashin Nadra da ya yi a rayuwarsa, yarinya mai hankali da tarbiyya, wacce ta so shi duk da tana gidan ma su rufin asiri shi kuma gidan talakawa ba ta ƙi shi ba, ya san ba zai samu mace kamar Nadra a rayuwarsa ba.

Ba tare da ya cewa kowa komai ba ya nufi kofar fita yana kuka har da majina. Ammi ta raka shi da harara don dama ba ƙaunarsa take yi ba. Kullum sai ta zuga Nadra akan ta Kore shi amma ba za ta yi ba sai dai kasa ta yi ma sa murmushi.

Dama daga Ammi sai Gwaggo Maimuna suka rage a gidan, don su Gwaggo Laraba da sauran dangi sun tafi gidan Nadra su ga gida kuma su yi ma ta sallama don gobe za su watse zuwa garuruwansu.


_Sidra_

Ta gama haɗa kayanta a cikin akwatin kayanta tana jiran Direban da zai kai su Sady baby ya zo ya ɗauke ta su kama hanyar Kano. Amma sai ta ji shiru tun da suka fita da sunan zai kai su Sady Unguwa ya dawo shiru.

Ta kira wayar Sady baby bai shiga ba. Don ba ta son shiga motar haya, don haka ba ta da wani zaɓin da ya wuce ta ta jira su. Ba ta da wani zaɓin da ya wuce ta jira su har sai sun dawo.


_Fahad_

A kofar gidan Mahaifinsa ya tsaya yana yin horn ɗin motarsa, yanayin sannan horn din da Maigadin ya yi ne ya gane cewa Fahad ne ya iso.

Da gudu-gudu ya nufi gate ɗin gidan ya wangale ma sa.

Parking lot ya nufa ya yi parking motarsa. Gidan har yanzu akwai baƙin da suka zo bikin don ga motocinsu nan a jere.

Fitowa ya yi daga cikin motar yayin da ma'aikatan gidan ke gaishe shi.

Ya amsa ma su ba yabo ba fallasa.

Tun daga ƙofar da zai sada ka da falo yake ji yo hayaniyar ƴan matan da ke cikin falon.

Firarsu kawai suke yi suna dariya.

Mirɗa handle ɗin kofar ya yi ya shiga wanda ƙamshinsa kaɗai ya isar da saƙon zuwansa.

Kowace ta nutsu suka fara gaishe shi, ya amsa ma su ba yabo ba fallasa. Ya kalli Rumaisa ƙanwarsa da Rahina da Sahiba da suka je gidansa suka dawo suka ce wai Nadrah ba ta iya tafiya ya kasance ta.

Ganin kallon da ya yi masu ne suka sha jinin jikinsu. Daidai lokacin wayarsa ta yi ringing.

Ya duba ganin abokinsa Sadik ne ya saka ya yana cewa.

"Ya aka yi ne?"

Maganar mintuna biyar suka yi sannan ya katse kiran wayar .

Ko da ya duba bai ga su Rumaisa da Sahiba da Rahina ba sun sulale sakamakon ganin kallon da ya jefa ma su.

Sauran ƴan matan duk ba garin suke ba zuwa bikin suka yi. Amma duk ƙannensa ne.
Chapter 4 · 0% Book details