← Book details Makaho Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 5 OF 11

Part ɗin Babansa ya nufa in da ya same shi tare da kawunsa.

Makaho Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 106 min read

Gaishe su ya yi sukaasa sannan suka ɗora da yi ma sa nasiha akan zaman aure da hakuri.

Bayan ya bar part ɗin ya nufi part ɗin ya nufi part ɗin Mama. Farida ce kawai a falon daga ganin idanunta ta sha kuka sosai.

Idanu suka haɗa da sauri ta ɗauke kai tana juya ma sa baya. Shi ma kansa ya sani Farida na tsananin son sa da ƙaunarsa amma shi baya son ta, bayan so na ƴan uwantaka da yake yi ma ta ba wani abu a ransa. Da a ce bayan guduwan Sidra iyayen ta ba su bashi Nadra ba to da zai iya auren Farida. Amma a yanzu kam baya jin zai iya aurenta kuma.

Ƙarasa wa ya yi ya zauna kusa da ita. Ta zuba ma sa idanunta tana kallonsa kamar za ta cinye shi. Kafin kuka hawaye ya fara zuba a idanunta sharr kamar an bude famfo.

"Ki yi haƙuri kin ji."

Tashi ta yi a guje ta bar falon ta nufi ɗakin dake kusa da na Mama.

Daidai lokacin Mama ta fito ita da Aunty Rahama.

Bayan sun gaisa ne Mama ta ce.

"Ya za ka fito ka bar ƴar mutane ita kaɗai bayan ka san condition ɗin da take ciki?"

Ka tashi ka koma zuwa gobe iyauenka za su zo ganin gida don jibi suka ce za su tafi, don yau suka ji niyyar zuwa amma na ce su bari sai gobe."

Ya dai yi shiru ba tare da ya sake yin magana ba.

Kallon Baby Zahrah ya yi wacce take ma sa dariya tana kiran uncle.

Alama ya ma ta da ta zo ya zaunar da ita kusa da shi wanda ganin haka ya saka Mama cewa.

"Fahad ba ka da niyyar tafiya ko? Ai bai kamata ma ka bar gidan ba, ka je ka haɗa ni da ita a waya ko ka bani lambar wayar ta.

Sanin cewa ya karɓe wayarta ya saka ya ce .

"Ba ta da waya."

"Kamar ya ba ta da waya?"

"Eh wayar ta ɓace ne."

"To ka siya ma ta wata wayar yau ɗin nan ka tafi ma ta da shi, na san dole za ta so yin magana da iyayenta."

"To Mama."

Aunty Rahama ta ce .

Da take ganin kamar rashin fahimta ce don ita ba ta yi tunanin cewa ƙanin nata zai kusanci Nadra ba wanda daren juya daƙyar ya tafi yana fushi. Ganin shi ma bai ce komai ba ita ma ta yi shiru amma tabbas tana da shakka akan hakan don ta fi kowa fahimtar ƙanin nata.

Sallama ya masu sannan ya nufi part ɗin baƙi ya gaishe da kowa. Sai dai ƙanwar mahaifiyarsa Hajiya Jummai mahaifiyar Farida ce ta share shi ba ta amsa ba, shi ma bai damu ba ya yi ficewarsa


_Ma'eesha_

Tana ɗora girki ta ji sallama daga kofar waje, ta amsa yayin da da take kwarara amai ta taimaka ma ta da ruwa kuma ta gyara wajan a gidan Mallam Liman da aka ba Makaho ɗaki.

Da fara'a ta tarbe su suka shiga cikin ɗaki ta shimfida ma su tabarma.

Bayan sun gaisa ne ta kawo masu ruwan pure water guda biyu.

Nan Dattijuwar take gabatar ma ta da kanta ashe ita ce matar da ta ga za su bar gidan lokacin da Ma'eesha ta fice Makaho na bin bayanta take tambayar makaho ina za su je ya ce suna zuwa.

Yana girki suna taɓa fira don ganin su ne ya saka ta canza tukunyar ta saka babba.

Kafin ta gama Dattijuwar da jikarta mai suna A'isha suka yi ma ta sallama za su tafi.

Ta yi daga da su akan su tsaya ta gama girki su tafi da shi amma ba su zauna ba.

Da ta kammala ta zuba a food flask sauran da ya rage ta zuba a wani food flask shinkafa da wake ne jallop wanda ya ji bisashen kifi.

Tun karfe biyu take jiran Khalifa ya dawo ya ci abinci shiru. Har karfe huɗu sannan ya dawo.

Ta yi ma sa ƙorafin rashin dawowa ya ci abinci akan lokaci. Ƙarshe ma ta ce ya gama su tashi su ke ta siya masa karamar waya.

Ta sanar da shi zuwan Baba mayar Liman da jikarta da suka yi.

Bai so ba haka ta matsa ma sa dole ya yarda suka shirya za su fita don ta siya ma sa karamar waya.

Da zai ɗauki sanadar jagoransa hanawa ta yi ta ce sai dai su tafi haka nan ita ce ƴar jagora.

Duk da bai so ba amma baya son yi ma ta gardama don tana da ƙima sosai a idanunsa.

Hakan ko aka yi bai rike sanda ba ita ce ta rike ma sa hannu suka fita. Tana sanye da doguwar rigar Abaya blue ta yi rolling kanta da mayafin abyarta sannan ta saka facemask da farin glass a idanunta.

Hannunsu na sarƙe cikin na juna suke tafiya duk wanda ya san Khalifa a unguwar sai dai ya saki baki yana kallon su da mamaki. Ganinsa tare da wannan zugegiyar budurwa tana rike da hannunsa suke tafiya.

Sai dai idan har ba idanunta karya suka yi ba ta hangi wata motar a gabansu wani na zaune gefen me zaman banza yana ɗaukarsu hoto.

Cike da mamaki ta yi niyyar nufar motar sai ta ga an figi motar a guje an bar wajen.

"Ka ga wanda ya ɗauke mu photo?"

Ta yi tambayar tana kallon Khalifa.

"Ni da ba idanu gare ni ba da wani idanun zan kalle su?"


Har suka je wani shagon siyar da waya ta siya masa wata karamar waya keypad, duk da ba ta da isasshen kuɗi amma dole ta cire dubu goma ta siya ma sa karamar waya, da sim card mai register

Ka san me ya sa na siya ma ka waya?"

"Ban sani ba don da wani idon zan yi amfani da shi?"

"Ai bai da wahalar koya, ni zan dinga kiran ka idan ba ka gida lokacin cin abinci idan ya yi ba ka dawowa Sai ka zauna da yinwa shi ya sa na siya ma ka da zaran na gama garki zan Kira ka sai ka zo ka ci abinci. Zan nuna ma ka wajen da za ka danna da zaran ka ji ƙara sai ka laluba ka danna wajen ka kara a kunne daga nan za ka ki murya ta."

Bayan sun tsallaka titi kasancewar ba wani nisa da unguwar su.

Suka kama hanyar dawowa gidan wayar da ta siya masa na cikin jakarta, tana tuna mutumin da ta ga suna daukar su photo a waya ɗazu su waye su me ya sa suke bibiyar su?

Daidai lokacin wayar ta ya soma ringing ta duba ta gani ƙawarta Nasreen ce.

Ta ɗaga tare da sallama.

Daga can bangaren ta ji Nasreen na cewa.

"Abdul ne zai yi magana da ke ta wayata tun da kin yi blocking ɗin sa."

"A kan me zai yi magana da ni?"

"Akan yana son ki cika masa alkawarin auren da kika yi ma sa, kuma dama shi ne ya dace da ke ba wannan musakin ba."

A fusace ta ce .

"Nasreen za mu samu matsala da ke wanda ba za mu taba komawa kamar da can baya ba. Kuka ki ja wa shi wanda ya aiki ki kunne ya fita a sabga ta. Wani irin jahilci ne zai saka ya fara neman matar aure, ko mace na auren maza biyu..."

Maganar nata maƙalewa ya yi sakamakon ganin wato motar ta tsaya gabansu.


*Maman Ihsan ce*✍️

09065327995
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z


*MAKAHO NE*


*NA*

Maman Ihsan ce ✍️


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


page2️⃣4️⃣


Maganar nata maƙalewa ya yi sakamakon ya yi sakamakon ganin wato motar ta tsaya gabansu.

A hankali ya sauke glass ɗin motar yana sakar ma ta murmushi.

"? Yaya Jamil."

Ta furta cike da mamakin ganinsa a unguwar su, shi kuma tun ranar da Nasreen ta kira ta a waya bayan ta je gidansu ya so ya zo tare da Nasreen sai dai ba ta bashi damar hakan ba. Don haka ya matsala wa Nasreen akan ta kawo shi gidan amma ta ƙi sai dai ta yi ma sa kwatance.

"Ma'eesaha wancan ranar kin bar gida a cikin fushi kina kuka, na so ki tsaya ki saurare ni amma ba ki tsaya ba. Yanzu ina neman arzikin don Allah ki taimaka ku shigo na ajiye ki a gidanku idan ya so sai mu yi magana."

"Yaya Jamil ina ganin mutuncinka don haka ka bar nan unguwar kafin na saka yara su yi ta jifar motar nan sai sun farfasa ma ka gilashin motar."

Murmushi ya yi tare da da fitowa daga cikin motar ya kalle ta yadda ranta yake ɓace ya ce.

"Idan kin saka an fasa kanki kika yi wa Asara. Domin ɗaya daga cikin motocin da mahaifinki ya mallaka ne na ke amfani da ɗaya. Kuma sakin kanki ne cewa ke kaɗai ya mallaka a duniya. Yau idan ƙasa ta rufe idanunsa ya zama babu shi ke ce mamallakiyar dukiyar da ya mallaka babu wanda ya isa ya canza hakan. Ko Mamy mahaifiyata tuminin takaba akwai za ta samu, ni da Laila da muke Agola ba'a maganar mu. Don haka ki yi hakuri ki zo mu tafi gida na zo ne na ba ki haƙuri a madadin mahaifinki da mahaifiyata."

"Yaya Jamil na daɗe da rasa mahaifina yanzu ba na da kowa a wanann duniyar sai mijina shine fitila ta, domin la kira kowa kansa ya sani da rayuwarsa. "

Ta ji maganar tana damƙar hannun makaho za su fara tafiya ya sha gabanta da sauri ya ce.

"Ki tsaya ki saurare ni Ma'eesaha, kin ga ni ba ni na yi ma ki laifi ba mahaifiyata ce ta yi ma ki laifi kada laifinta ya shafe ni, laifin wani baya shafar wani Ma'eesha.

Sai a lokacin makaho ne ya yi magana ya ce.

"Ki bar shi ki ji da me ya zo?"

"Babu wani abun alkhairi da zai zo da shi, domin kuwa babu alkhairi a tattare da su. Daga ranar da mahaifiyata ta taimake su daga rana ta janyo su inuwa me suka aikata ma ta jefa ta a ranar suka..."

"Ya Isa haka nan Ma'eesha ki wuce mu tafi."

Kamar jira yake dama hannunsa na rike da nata ne.

Take suka fara tafiya yayin da mamaki ya cika zuciyar Jamil, wato duk tana daraja mijinta tun da har ya ba ta umarnin ta wuce su tafi lima take ta wuce ba musu ko gardama. Kenan hakan na nufin ta karɓe shi a matsayin mijin aurenta ne.

Jinjina kai ya yi tare da cewa.

"Ni ina can ina faɗi tashi wajan Daddy da Mamy don su raba auren ma don na yi zaton ba za ta taba yarda da auren ba, nayi zaton za ta saka ya sake ta don ta fi ƙarfinsa, amma sai na gansu tare da alama wani wajen suka Fito."

Shiga motarsa ya yi ya fara bin bayansu ta juyo ta kalli motar amma ba ta damu ba sai ta ci gaba da tafiyar da take yi.

Har suka isa ƙofar gidan ta ciro ɗan makulli daga cikin handbag ɗin ta ta buɗe.

Bayan ta buɗe ne ta ja hannunsa suka shiga bakinsu ɗauke da sallama.

Suna shiga daidai lokacin motarsa ta karaso .

Fitowa ya yi daga cikin motar yana ƙarewa gidan kallo yana jinjina wanan al'amari. Wai kamar Ma'eesha Ibrahim Khalil ce take rayuwa a cikin wanan akulikin gidan. Yarinyar da mahaifinta ke da manyan gidaje na alfarma a garin nan, mutumin da yake kyauta da gidaje da motoci wanda ko gidajen da ya raba wa masu ma sa aiki kamar direba maigadi da sauransu to mahaifin Ma'eesha ya siya ma su lafiyyun gidaje amma a ce ƴarsa ɗaya tilo a duniya tana rayuwa a cikin wannan gidan da bai wuce a ce tana kiwon karnuka ba. Amma ita ke rayuwa a nan lallai ma'eesha Allah ya ba ta karfin zuciya.

Yana tsaye yana kallon ƙofar fale-falen da suka bude suka shiga.

Ya ƙsrasa bakin kofar gidan yana sallama.

"Assalamu alaikum."

Daidai lokacin da ma'eesha ke fitowa da tabarma daga cikin dakin ta ji sallamar sa a kofar gidan.

Makaho ne ya amsa ma sa sallamar yana kokarin mikewa

"Please kar ka fita ka rabu da shi idan ya gani da tafi."

Ta fada tana rike hannunsa.

"A'a Ma'eesha ki yi hakuri wannan bawan Allah ba shi ya yi ma ki laifi ba, ki sauraren shi laifin wani baya shafar wani, don haka ki daina hukunta shi da laifin da mahaifiyarsa ta aikata."

Ya fadi haka yana zame hannunsa daga rikon da ta yi masa ya ɗaiki Sandarsa ya nufa hanyar fita.


Yana fita ya ce.

"Waye ke sallama?"

Jamil ya ce .

"Ni ne wanta Jamil."

"Bismillah ka shigo ciki."

Ya yi maganar yana yin gaba yayin da Jamil ya take ma sa baya.


_Nadra_

Farin ciki duk ya lulluɓe ta sakamakon ganin ƴan uwanta sun zo.

A nan falon dake downstairs suka zauna.

Durƙusawa ta yi ta gaida dangin nata cikin farin ciki.sannannta mike suka gaisa da ƴan matan dangin nasu. Sai tsokanar ta suke wai ta canza a cikin kwana ɗaya ne me Fahad ɗin ya ba ta ne, ita dai ba ta tanka ma su ba.

Ruwa da lemu ta kawo ma su ta na shirin zuwa kawo ma su cincin sai Gwaggo Laraba ta ce.

"Me kuma za ki kawo ma na?"

"Cincin ne zan kawo ma ku."

"A'a cincin da muka baro shi a gida."

"To bari na je na ɗoraa ku girki don na ga Akwai komai na bukatar."

Daidai lokacin aka danna ƙararrawar ƙofa.

Dama tana sanye da dogon Hijabi kamar yadda ya zamar ma ta al'ada.

Tana buɗe wa ta ga Rumaisa ƙanwar Fahad ce sai dai wannan karon iya kaɗai ce.

Murmushi ta sakarwa Nadra tana cewa.

"Antynmu ya kike ?"

Ta faɗa tana Murmushi. Duk da kasancewar ta girmi Nadra sosai amma ba ta da girman kai.

Nadra ma murmushi ta sakar ma ta tana yi ma ta sannu da zuwa .

Rumaisa ta amsa tana shigewa cikin falon ɗin ta hangi baƙi.

Ta shiga da fara'a tana gaida jama'ar da ta gani a falon fuskarta ɗauke da murmushi.

Suka amsa ma ta cikin sakin fuska da walwala.

Kallon Nadra ta yi ta ce.

"Ga abinci Mama ta ce a kawo ma ki ."

"Okay to na gode a gaishe ta."

"Za ta ji."

Ta faɗa nufar hanyar waje bayan ta yia su sallama.

"Am ba ki ji ba."

Nadra ta faɗa tana kallon Rumaisa kasancewar ba ta san sunan Rumaisa ba ta dai san sunanta ba.

Rumaisa ta juyo tana kallon Nadra ta ce

"Da ni kike yi?"

"Eh, dama basket ɗin da kika kawo da safe ne nake so ki tafi da su."

"Okay."

Nadra ta haura upstairs ta nufi kitchen don ɗauko basket da food flask ɗin da aka kawo da safe.

Dama kafin ta wanke su sai da ta fita ta kai wa masu gadi da sauran ma'aikatan gidan.

Bayan ta kawo ne ta ce.

"Ga shi ."

"Sunana Rumaisa."

Jinjina kai Nadra ta yi tana Murmushi. Daga nan ta yi ma ta sallama ta tafi.

Dama ta bar direba a mota yana jiran fitowar ta. Tana fitowa suka bar gidan.

Bayan tafiyar ta ne Nadra ta ce .

"Ga abinci nan an kawo, na san zai ma isa don na ga da yawa kamar ta san za ku zo."

"Dama ta samu ma na, dole wasu za su zo yau su ganki musamman danginki."

Gwaggo Laraba ta faɗa tana karantar yanayin Nadra. Don ta lura jikina a sanyaye yake.

Kallon ƴarta ta yi mai suna Amal ta ce ta zuzuzba abincin ta ba wadanda za su ji. Ita kuma sai ta ja hannun Nadra tana cewa.

"Muje na ba ki sako ko?"

Nadra ta miƙe suka nufi upstairs.

Har cikin bedroom ɗin Nadra suka shiga ta zaunan a saman gadon sannan ta nuna wa Nadra gefenta ta ce ta zauna kusa da ita.

Ba musu ta zauna Kamar yadda ta umarce ta. Sai ta riko hannun Nadra ta ce .

"Daughter akwai matsala ne?"

Shiru ta yi tana wasa da yatsun hannunta da suka sha jan lalle.

"Idan akwai matsala ko sanar da ni, sai na san ta ina da za'a ɓullowa lamarin."

Ƙwalla ne ya cika idanunta a hankali ta ce .

"Ummata."

"Ummar ki kuma?"

Jinjina kai ta yi ta ce.

"Ya jikinta."

Ta ji sauƙi ta warware, yanzu haka ma ta yi ta kiran wayarki ba ta shiga ."

"Eh ya amshe ma ni waya."

"Ya amshi wayarki saboda me?"

Nan ta ba ta labarin duk abinda ya faru.

Shiru ta yi tana nazari kafin ta yi ajiyar zuciya ta ce.

Eh mu ne muka mance ba mu sanar da shi Sayyadi zancen auren naki ba. Amma yanzu na san dole ya sani. Sannan zan ya ma ki wata magana ɗaya. Kada ki sake yi wa Fahad zancen Sidra."

Da sauri ta kalli Gwaggo Laraba ta ce .

"Idan ta dawo ai sai a daura ma su aure ta zo ta zauna ni kuma na je na auri ya Sayy..."

Mugun kallon da Gwaggo Laraba ta yi ma ta ne ya saka ta yi shiru.

"Ke dakata! Ba na son shashancin banza, ko da Sidra ta dawo to sai dai ta auri wani namijin ba Fahad ba, domin dama wani baya auren matar wani haka wata ba ta auren mijin wata. Don haka ki sa wa rabi cewa zaman aure kika zo ba wai kin zo da niyyar wata rana ki fita ki ba wa wata mijin ki da gidanki ba ne, don ba za mu taba aurawa Fahad Majidaɗi Sidra ba, bayan ya aure ki, don haka ki kama mijinli ki yi ma sa biyayya sau da ƙafa. Ba mu kawo ki nan dan ki fita wata rana ba. Sannan kada na sake jin sunan Sayyadi a bakinki ko tunaninsa. Ki cire shi a ranki dama can ba mijinki ba ne."

Jinjina kai ta yi hawaye na bin fuskarsta. Dosa Gwaggo Laraba ta yi ma ya nasiha mai ratsa zuviya da wasu shawarwari kan dabarun zama da miji.

Wasu magungunan mata da na gyaran jiki Gwaggo Laraba ta fito da su daga cikin jakarta sannan ta yi na ta bayanin yadda za ta sha kowane.

Karɓa ta yi ta ajiye su.
Sai ta ga Gwaggo Laraba ta fito da wani kula a cikin leda ta buɗe kazar amarya ce guda aka dafa ma ta da romonta, daga gani ta ji sassaken magani .

Sai da Gwaggo Laraba ta saka ta gaba ta ci rabin kazar ta sha romon maganin sannan ta ajiye sauran da niyyar kafin su tafi sai ta saka ta ta cinye sauran.

sannan suka koma downstairs, don har sun gama cin abinci.

Daidai lokacin ne suka ji horn ɗin mota. Bayan kamar mintuna biyar aka turo ƙofar falon tare da sallama.

Fahad ne ya shigo ya durƙusa cikin girmamawa ya gaida su Gwaggo Laraba.

Upstairs ya haura zuwa part ɗin sa.

A falo ya zauna kan kujera ya faɗa duniyar tunani.

A can falo Gwaggo Laraba ta ce wa Nadra ta tashi ta je ta sami mijinta ta kai ma sa ruwan sha.

Jin haka sai da gaban Nadra fadi, amma sai dake.

Gwaggo Laraba ta tashi ta ce.

"Mu je kitchen ɗin."

Tashi ta yi ta bi bayansa kamar kazar da ƙwai ya fashe wa a ciki. Suna shiga ta fuskanci Nadra ta ce.

"Wato ba ki ji huɗubar da na yi ma ki ba ne? Na ce da zaran ya dawo ki dinga tashi kina tarbarsa, sannan ki bashi ruwa ya sha idan yana da buƙata. Sannan idan wanka zai yi ki taimaka ma sa. Yanzu ɗauki ruwa da cup ki kai ma sa, sannan ku tambaye shi ko akwai abun da yake buƙata ki kai ma sa ko ki yi masa⁷."

Sannan kuma ki daina daka wannan dogon hijab kamar mai takaba ya isa haka nan, daga ke sai mijinkine idan an yi baƙi maza ."

Faranti ta ɗauka ta dauki ruwa roba guda da glass cup ta fito ta nufi upstairs.

Knocking ta yi a kofar falon sai dai ji shiru. Sai da ta sake yi sannan ta ji ya ya ba ta izinin shiga sannan ta shiga.

Yana zaune kan sofa a ƙasan ƙafarta ya fara dauke idanunsa, yatsunta da suka sha lalle ne kawai ake iya gani. Don dogon Hijabinta har ya rufe ƙafarta. Ɗauke idanunsa ya yi ya mayar kan wayarsa yana daddanna wa

Har ƙasa ta durƙusa ta ce.

"Sannu da dawowa."

Share ta ya yi kamar bai ji ta ba ya ci gaba da danna wayarsa.

Duk da haka dai ta sake cewa.

"Ina wuni?"

Nan ma shiru ya ma ta bai amsa ma ya ba.

Glass cup ɗin da ta ajiye ne ta buɗe robar ruwa ta tsiyaya ma sa ta mika ma sa ta ce.

"Yaya ga ruwa."

Ta yi maganar tana mika masa cup ɗin. Sai a lokacin ya ɗago kansa ya sauke idanuntsa kan kamilalliyar fuskarta. Idanunsu ne suka sarƙe cikin na juna, da sauri da janye idanunsa saboda kwarjininsa.

Kamar ba zai karɓa ba sai kuma A hankali ya mika hannunsa ya karɓa tare da cewa.

"Thank you."

Ya faɗa yana kai ruwan bakinsa ya sha.

"Mama ta aiko ma na da abinci na kawo ma ka ne?"

Kai ya girgiza sannan ya ce.

"Am okay, you can go."

Tashi ta yi nufi ƙofar fita ta fice.


*Maman Ihsan ce*

09065327995

https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z


*MAKAHO NE*


*NA*

Maman Ihsan ce ✍️


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


page2️⃣5️⃣


Tashi ta yi ta nufi ƙofar fita ta fice.

Sai dai bayan ta fita kafin ta rufe ma sa ƙofar ya ce.

"Come here."

Dawowa ta yi ciki ta tsaya tana jiran me zai ce.

Kallon Hijabin da ke jikinta ya yi ya tuna duk sanda zai ganta da hijabi ne ko da ya je zance ne a wajen Sidra. Sai ya ɗauka ko don saboda zai shigo ne duk da ita wance yake zuwa wajan nata ba ta saka wa. Har wata rana suna hira da da Sidra a falon saukar baƙi sai ga Nadra ta zo wuce wa ta fito daga ɗaya daga cikin ɗakunan dage part da dogon Hijabinta idanunta ya sauka akan Fahad da Sidra da suke zaune a kujera mai zaman mutum biyu, hannunsa sarƙame cikin na juna ta kwantar da kanta a kafaɗarsa suna kallon wani abu a wayarsa. Girgiza kai kawai Nadra ta yi don ta sha ganinsu rike da juna kuma manne da jikin juna girgiza kai kawai ta yi tana taɓe baki ta zo za ta wuce bayan ta gaida Fahad sai Hijabin ya ja kofin ruwan da Sidra ta ajiye wa Fahad. Ruwa ya zube ran Sidra ya ɓaci har tashi za ta mari Nadra Fahad ya dakatar da ita ta hanyar cewa.

"No."

"Ka bar ni na koya ma ta hankali tun da ba ta da shi kullun tana cikin hijabi kamar mai fita takaba, wani namiji ne zai yi sha'awarki a haka? Yarinya kamar wata bagidajiya sai ƙauyanci, ban ga ranar da yarinyar nan za ta waye ba."

Sai a lokacin da kalli Yayar tata ta ce.

"Aunty Sidra Indai wayewa irin ta ku ne ba na buƙata wayewa ta addinin Muslunci nake buƙata bar ni a haka ban saɓa wa Allah ba."

A fusace Sidra ta wanke wa Nadra fuska da mari wanda sai da ta durƙusa wajen tana kuka.

"Ni za ki yi rashin kunya wani saɓon Allah na yi ko saka hijbi da suturta jiki ne tsoron Allah da ba na da shi? Sau nawa ma su daka hijabin suke aikata ɓarna wanda wacce ba ta saka wa ba za ta iya yi ba?"

Tashi ta yi tana kuka ta bar part ɗin.

"Wai me ya saka kin fiye zafin rai ne?"

"Don Allah Mallam kar ka sake ɓata ma ni rai, ya za'ayi ta Mani rashin kunya na ƙyale ta?"

Ta yi ma sa maganar cikin ɓacin ran da take ciki.

"Ba'ayi ma ni tsawa ki iya bakinki ki san kalaman da za ki dinga faɗa mani, idan ba haka za mu samu matsala da ke."

Jin haka ta sassauta murya tana bashi haƙuri.

Tari da ta ɗan yi ne ya dawo da shi duniyar tunanin da ya lula.

Ya kalle Nadra da kyau wacce ko a mafarki bai taba tunanin ita ce za ta zamo matarsa ba Sidra ba.

Maida idanunsa ya yi kan wayarsa cikin muryarsa mai amo ya ce.

Ba na buƙatar sake ganin ki da hijab matuƙar ba wai namiji ne ya shigo gidan nan ba ko kuma za ki fita zuwa wani waje. Okay?"


Kai ta jinjina ma sa sannan ta fita daga ɗakin.

Kitchen ɗin ta koma in da ta tarar da Gwaggo Laraba tana ƙara gyara wa wasu kayan wajen zamansu.

Ganinta ya sa ta dakata ta ce.

"Abinci za ki kai ma sa?"

"A'a cewa ya yi ya ƙoshi na tafi."

Shiru Gwaggo Laraba ta ce.

"Dole fa sai kin yi hakuri, domin har yanzu akwai tabon da Sidra ta yi masa a cikin zuciyarsa. Domin ba daɗi a ce ranar aurenka matar da kake so ta gudu ta bar ka. Kin ga dole har yanzu ransa ya kasace a ɓace. Ke ce za ki yi ƙokarin dasa ma sa soyayyarki a zuciyarsa. Ta hanyar kyautata ma sa, dama ita zuciya an halicce ta ne bisa ga son wanda ya kyautata ma ta, da kuma ƙin wanda ya munana ma ta. Shin ya nuna ma ki tsana ne ko hantara ?"

Kai ta girgiza alamar a'a kafin ta ce.

"A rayuwar aure ko soyayya, akwai abu guda da ya kamata mace ta gane,
Ko wani namiji yana da irin nasa hali.Kuma yadda yake sonki, haka yake nuna fushinsa idan wani abu ya bata masa rai, ba wai saboda baya sonki ba ne, a’a, saboda ya damu da ke sosai ne.Don haka ke dai ki fahimci irin namijin da kike tare da shi Idan mijin kirki ne, zai yi fushi saboda yana son ki gyaru, ba don ya cutar da ke ba Idan mai saurin ɓacin rai ne, ki gane cewa yana magana ne da zuciyarsa, ba wai yana ƙin ki bane.Idan mai shiru-shiru ne, fushinsa yakan zama nesa da magana, amma zuciyarsa tana cike da damuwa, Idan mai gaskiya da tsauri ne, yana fushi saboda ya san abin da ya dace da abin da bai ya dace ba. Idan mai tausayi ne, fushinsa zai zo da nutsuwa, amma zai so ki gane kuskurenki ba tare da ya takura miki ba, a kowane hali, rarrashi na mace shi ne sirrin da ake so mace ta sani.Ki saurari damuwarsa ba tare da tsawatarwa ba. Ki nuna masa kin gane abin da ya dame shi. Ki yi magana cikin ladabi da natsuwa.Ki yi masa nasiha cikin taushi, ba da jayayya ba, Ki nuna masa kulawa, ko da da kananan abubuwa ne.namiji baya buƙatar mace cikakkiya,
yana buƙatar mace mai fahimta.

Jinjina kai Nadra ta yi cikin gamsuwa ta ce .

"Gwaggo Laraba baya sakar ma ni fuska fa."

"Ya ma ki wani abu ne yanzu da kika kai ma sa ruwa?"

"Cewa ya yi wai kada na sake saka hijabi in dai ba wani namiji zai shigo ba ko fita zan yi."

Murmushi Gwaggo Laraba ta yi sannan ta nuna ma ta yadda za ta zuba da shi da kuma kiyaye abinda baya so.

Sai yamma suka shirya za su bar gidan suna fita harabar gidan dama motoci biyu suka zo da su na Gwaggo Laraba da ta Abba daya wacce daya daga cikin ƴan matan ta yi driving.

Daidai lokacin Fahad ya dawo daga sallar la'asar ya ga suna shirin tafiya. Sallama ya ma su sannan ya ce Nadra ta zo ta karɓar ma su saƙo. Ko da ta ke 200k dubu ɗari biyu ya ba ta ya ce ta ba su yana ma su Allah ya kiyaye hanya.

Ta zo ta ba su suka yi ma ta godiya tare da cewa ta isar ma su da sakon godiya suka tafi.


_Ma'eesha_

Sallamar Yaya Jamil da na mijinta ne ta san cewa ya shigo da shi ne. Don haka ya tsuke fuska ta tashi daga kan tabarma ta koma kan kujerar tsuguno yayin da Makaho ya zauna a gefen tabarma shi ma Jamil ya zauna.

"Ki girma baƙonki hadisin Manzon Allah (s.a.w) ne."

Cikin sanyin murya ta ce.

"Yaya Jamil ina wuni?"

Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke sannan ya amsa mata cike da farin ciki ta sauko.

Tashi ta yi ta je ta kawo ma sa ruwan pure water guda biyu ta ajiye ma sa. Wanda ya san cewa yanzu ne ta fara shan pure water. Don a gidan su ruwan roba ake sha. Shi kan shi tun ranar da suka zo gidan su Ma'eesha suka ji sallama da kowane ruwa sai na roba. Bayan ya sha ruwan pure water leda ɗaya ne ya kalli Ma'eesha ya ce.

"Ina mai ba ki haƙuri a madadin mahaifiyata, na san ta cutar da rayuwar ki cutarwa mafi muni ..."

Kasa karasa maganar ya yi ganin yadda ta mike zumbur.

"Yaya Jamil na roƙe ka dan girman Allah ka tashi ka tafi ba sai ka sake dawowa ba, kuma ba na bukatar ka sake jin an tayar mani da wannan zancen ya riga da ya wuce cutarwa dai an ya mana sai dai sakayyar Allah."

Tana faɗar haka ta shige daki tana fashewa da kuka.

Tana shiga ɗakin Jamil ya cire kuɗi 100k ya ce wa makaho ga kudi nan ya ba wa Ma'eesha amma makaho ya ƙi karba saboda ya ji tsana da ɗaci da a cikin Muryar Ma'eesha ya san ba za ta so kudin ba don haka ya ki karba. Sai ya mayar da kudin cikin aljihunsa sannan ya cire 3k ya ce ka ba ta wannan kudin sadakinta ne da ta ki karba shi ne na karɓa a hannun Laila hakkinta ne ka ba ta."

Wannan kam makaho ya amsa suka yi sallama ya fita.

Ma'eesha na jin fitar Jamil ta fito daga cikin ɗakin ta zauna waje.

Wayar da ta siyo wa Makaho ne ta ciro ta buge wayar don battery akwai caji. Ta saka sim card ɗin da ta siya ma sa ta mika ma sa, nan ta dinga nuna ma sa yadda zai danna idan an kira shi waya. Ta gwada kiran wayarsa sai ta ga ya iya ɗaga kiran kamar yadda ta koya masa kiran na shigowa sai ya ɗaga ta ji muryarsa shi ma ya ji tata muryar.

Sai da aka kira sallar magrib sannan ya tashi ya tafi masallaci. Ita kuma ta kunna gas kasancewar spaghetti sauce za ta yi ma su.

Da misalin karfe takwas da kwata na dare suna zaune a waje ta shimfida ma su tabarma, kasancewar ta fesa maganin sauro sai suka janyo ƙofar ɗakin ta rufe.

Spaghetti sauce din suke ci suna Shan zobo da ta haɗa ma su ta siyo ƙanƙara.

Kasancewar akwai wutar nepa ya saka ta ƙirƙiri wanke-wanke shi kuma yana yi ma ta ɗauraya.

Bayan sun gama ne ta buɗe ɗakin kafin ta ɗaura towel ta shiga wanka. Tana fitowa shi ma ya shiga don yin wanka da kanta ta kai ma sa ruwan wankan a banɗaki bayan ya shiga sannan ta nemi ruwan yin alwalar kwanciya barci.

Tana shiga ɗakin ta fara goge jikinta, ga hasken nepa ya gauraye ɗakin sai dai rashin fanka, Allah ya sa yau garin ba wani zafi.

Yana shigowa ta tana gama shafa mai. Kasancewar ta san cewa shi makaho ne ya saka ta warware towel ɗin a gabansa ta yi tsirara ba komai a jikinta .

Under wear ta saka wata singileti ce da wandonta wanda ya tsaya rabin cinyarta ya tsaya ma ta. Hula ta saka ta yi shirin kwanciya barci ta yi don haka ta kalli in da ya ke tsaye ya ga ashe ya cire rigar da ya yi wanka da ita, jallabiya ya saka ta kalli inda yake zaune kan tabarma da yake kwanciya sai ta ga rashin dacewar hakan ya dinga kwana kan tabarmar ita kuma ta 'na kwance kan katifa mai taushi. Cikin sanyin jiki ya ce.

"Ka zo mu kwanta tare saman katifar za ta ishe mu sai mu kwanta tare a saman katifar ka daina kwana a ƙasan tabarmar. "

Ko ranta gama maganar ta juya sai ya ga jikinsa na rawa yana jijjiga

Da sauri ta mike tsaye tana nufi in da yake tana kiran sunan shi cikin tashin hankali.


*Maman Ihsan ce*


09065327999

Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z


*MAKAHO NE*


*NA*

Maman Ihsan ce ✍️


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


page2️⃣6️⃣

Da sauri ta miƙe tsaye ta nufi in da yake tana kiran sunan shi cikin tashin hankali.

Kansa ya dafe yana cije leɓe sakamakon kansa da yake jin kamar zai zai tsage.

Har lokacin jikin nasa na rawa kafin ka ce me jikinsa ya yi zafi sosai . Hankalin Ma'eesha tashi ya yi saboda jin zafin da jikinsa ya yi .

Rasa ya za ta yi da shi ta yi ga jikinsa sai rawa yake yi.

Ta duba time ta ga karfe goma sha ɗaya na dare ne a yanzu . Ga shi ita ba ta da kudin zuwa asibiti ballantana ta ce za ta kai shi. Don kudin da ke hannunta bai ba su wuce 3k ba, ga kudin abun hawa da za ta kashe kuɗi.

"Sannu ko,bari na je na nemo ma ka magani."

Ta ji maganar tana saka doguwar rigar Abaya ta saka ta yafa mayafin abayar ta ɗauki 3k ɗin da suka rage ma ta ta fice daga ɗakin.

A hankali ta bude ƙofar fale-falen ta fice daga gidan nan tana waige-waige ya sa ta nufi wajen me shagon dake kusa da su.

Ganin ta a rude ne ya dakatar da maso son shigowa shi ya fito .

"Haniya lafiya?"

Mijina me bai da lafiya Bƙan san ina j sa za kawo ma sa magani ba."


Cikin tauSaya ya ce.


"Allah sarki,bayan, Garba dake syar da magani sai dai shi ne ke siyar da magani a nan kusa. Yanzu kam na san ya tashi tun da karfe goma sha sha ɗaya ta yi, don shi karfe goma yake rufe Chemist. Yanzu Sa dai ki je ɗayan layin na san Emeka yanzu yana nan."

Cikin damuwa ta ce.
"Ta ina zan bi?"

Kwatance ya yi ma ta nan da nan cikin zafin nama ta bar wajen ta kama hanyar da yake tunanin ya kwatanta ma ta.

Dare ya yi ƙafa sun ɗauke ba mutane da suke kai da kawo.

Tsaya wa ta yi kayan layin dake kke kusa da na su

Har nunfashi take maida wa, kamar wacce ta yi tare gudun tsere.

Ga duhu ba wutar nepa yanzu suka ɗauke don haka duhu ne ya mamaye garin ba ko daya. Ba irin unguwarsu ba ne, da ko dare ne yana mamaye da hasken fitilu.

Tana nan tsaye ta rasa ina za ta kai sai ta hangi wani mutum na dosowa .

Yana zuwa ta tambaye shi sai ya nuna ma ta ashe ma tana kusa da wajen.

Ta karasa shi ma yana gab da rufe wa har ya fito sai ga ta.

Komawa ciki ya yi yana tambayar ta me take so.

Bayani ta yi ma sa ya haɗa ma ta magunguna sannan ta amsa tana tambayar sa kuɗin ya ce dubu ɗaya ne, ta mika masa ta kama hanyar tana gudu-gudu sauri -sauri don hankalinta a tashe yake ba ta san wani hali za ta same shi a ciki ba.

Har ta karasa ƙofar gidan ba ta daina gudu-gudu ba.

Tana shiga ta rufe kofar gidan da sakata sannan ta shiga ɗakin.

Can ta hango shi ya mirgina ƙarshen gadon kusa da katifarta sai rawar sanyi yake yi .

Tana ƙarasa wa ta durƙusa a gabansa tana yi ma sa sannu. Ya amsa da ƙyar kafin ta ɓallo magungunan bayan ta ɗauko ruwa ta ba shi magungunan, daƙyar ya iya hadewa sakamakon jin jikin da yake yi.

Ya dunƙule a ƙasan ɗakin sai ta ce akwai sanyin ƙasa saboda robber carpet ne ya hau katifa ya kwanta.

Sam ya ki yarda ya hau katifa sai da ya ga ta na ma sa magiya sannan ta taimaka ma sa ya kwanta saman katifar jikinsa na rawa kansa kamar zai tsage gida biyu.

Addu'a ta yi ma sa sannan ita ma ta hau kan katifar ta kwanta gefensa tana yi masa sannu, kafin ta janyo wani zanin gadon ta lulluɓe su da shi.


_,Nadra_


Bayan ta yi sallar isha'i tana nan zaune akan sallaya kaɗaici ya ishe ta, Alqur'ani mai girma ta ɗauka tana karatu, sai karfe tara na dare sannan ta ajiye ta yi sallar shafa'i da wuturi.

Bayan ta idar ta yi addu'a ne sai ta rage kayan jikinta ta shiga bathroom don yin wanka.

Ta fito daga wanka kenan ta ta nufi closet ɗin ta. Tana neman kayan barcin da za ta saka. Sai dai cikin rashin sa'a akwatin da aka loda kayan barcin a ciki duk ba rigar arziki da ta ga za ta iya sakawa. Domin dama Sidra ita ce ta zaɓi kayan barci da take so sannan Fahad ya biya kudin aka zuba su cikin akwatin kayan lefe. To duk rigunan irin waɗan da za'a ce da su da babu kusan ɗaya suke don irin ma su shara-sharan nan ne wanda komai na jikin mace a bayyane suke. Kuma ba su wuce rabin cinya ba, ma su tsawon sune waɗanda suka kai guiwa.

Nadra ta dafe kai cike da takaici. Don iya kayan barcin da ta saba amfani da su riga ne da dogayen wanduna.

Ba ta da wani zaɓi da ya wuce ta saka tun da ta san na kowa ne zai ganta da shi ba, idan ta shige cikin bargo ta rufe jiki ta shi kenan. Don haka kawai ta ɗauki wani riga iya kar ta guiwa ta saka, bayan ta shafa turare ta saka pant. Don dama bra din duka ba wanda ya yi ma ta don size ɗin Sidra ne ita kuma tafi Sidra girman nono. Don haka ba ta wahalar da kanta ba ta saka rigar kawai ba tare da bra ba dan rigar irin mai hannun singiletin nan ne kuma tana da ƙoƙon bra don haka daga gabar rigar za ki ɗauka bra ta saka.

Sannan ta daka dogon Hijabinta ta fito daga cikin closet ɗin ta zauna bakin gado.


_Fahad_

Bayan sallar isha'i ya nufi complex ɗin da ake siyar da wayoyi ya siya wa Nadra tsadaddiyar waya ƙirar Samsung.

Bayan ya ba su A.T.M card ɗin sa sun cire kudin yana fitowa kiran Mama ya shigo wayarsa. Sai da ya shiga cikin motarsa ya ajiye ledar wayar gefensa sannan ta ɗaga kiran wayar.

"Hello Mama."

"Kana lafiya?"

"Lafiya lau Alhamdulillah."

"Ina Nadra."

"Tana gida."

"To ka yi sauri ka koma kafa kaɗaici ya yi ma ta yawa. Sannan ka biyo ga abinci ka wuce da a shi."

"Okay gani nan zuwa."

Ya katse kiran wayar a zuciyarsa yana mamakin yadda mahaifiyarsa ke ƙaunar yarinyar.

Bai shiga da motar cikin gidan ba ya bar ta waje ya shiga ta karamin ƙofar bayan ya yi knocking maigadi ya ga shi ne ya wangale ma sa kofar gate ɗin da sauri.


Gabaɗaya suna zaune a falon gidan daga ma su gidan har baƙin da suka zo bikin ba su koma ba.

Don gobe kowa zai tafi Idan aka cire Hajiya Inna wato kakar Fahad, don ta ce sai ta kwana biyu za ta koma.

Don haka kowa na fakon manya da yara don a ƙalla za su kai su goma sha biyar.

Da sallama ya shiga wanda ba wanda ya ji sallamar sa sakamakon fira da suke yi.

Kamshin turarensa ne da a kullum shi yake isar da saƙon wanzuwar sa a wajen.

Abokanan wasan sa na ta tsokanarsa shi dai bai tanka ma su ba. Gaisuwar ma a taƙaice ya yi ma su.

Zama ya yi a inda Rumaisa ta tashi ta ba shi wajan akan kujera mai zaman mutum biyu. Dama ita da Farida ne suke zaune a wajen. Sai ya zaune gefen Farida kallo ɗaya ya yi ma ta ganin yadda take cika tana batsewa ya share ta bai ko sake kallonta ba. Mama ce ta ce.

"Ya jikin Nadra ɗin ta warware Mama."

Karaf kakarsa dama ba kunyar zaro zance take yi ba ta ce.

"Ƙarya kake yi munafuki yaushe ta isa warware wa yarinyar da ka ce ka far ma ta ko tafiya ba ta iya yi shi ne za ka ce ta warware?"

Cije laɓɓansa na kasa ya yi cike da takaicin tsohuwar, sai ta ci gaba da cewa.

"Na ina ce bayan an ɗaura ma ku auren da ita ka ce ba ka son ta tafiya ma gidan naka wajan matar ka ce ba za ka je ba sai da aka saka ka dole shi ne kana zuwa ka haike ma ta shi ma cikin ba ka son ta ne ko?"

Yana jin yadda idanun ta ke yawo a jikinsa ya san ba mai yi ma sa kallon ƙurillar nan sai Farida, don haka ya ɗaga kai ya kalle ta karaf suka haɗa idanu, ta kau da kai tana harararsa. Dariya ta so ba shi ya danne ya mike yana cewa Mama ta bashi abincin zai wuce .

Nan take shaida ma sa cewa baƙi za su zo ganin Amarya gobe saboda jibi za su koma garuruwansu.

"Allah ya kai mu."

Ya faɗa ba tare da ya sake magana ba.

Rumaisa ce ta kawo ma sa basket na abincin ta na cewa.

"Ko na kai ma ka mota ne?"

"Amsa kawai ta yi ba tare da ya ce ma ta komai ba ya yi ma su sallama sannan ya kalli Mama. Ganin kallon ya sa ta gane akwai magana,. don haka ta tashi ta bi bayansa.

A harabar gidan suka tsaya ya kalle ta cikin damuwa ya ce.

"Mama wai me ye makomar wannan Auren ne?"

"Ban gane ba."

"Mama yarinyar nan fa ba wai son ta nake yi ba ita ma ba wai tana..."

"Me ya saka ka amsa wa iyayen ta a lokacin da suka yi ma ka tayin aurenta?"

"Saboda ba zan iya ce ma su a'a ba za su ji ba daɗi. Kuma ni..."

Ɗaga ma sa hannu ta yi alamar dakatar wa kafin ta ce.

"Ka je dare na yi za mu yi magana daga baya."

Ba ta jira cewarsa ba ta juya ta koma ciki. Daga gani ranta ya ɓaci da jin zancen nasa. Cikin sanyin jiki ya ya nufa gate ɗin gidan da basket ɗin a hannunsa.

Bayan ya ajiye a bayan motar ya yi wa motar key ya bar layin.


Ƙarfe tara da mintinan arba'in ya yi horn a ƙofar gidansa.

Maigadin ya wangale ma sa gate ɗin ya shiga da motar zuwa parking space. Ya yi parking motar a parking lot ya fito rike da kwalin wayar sannan ya buɗe bayan motar ya ɗauko basket ɗin abincin ya nufi cikin gidan.

Handle ɗin kofar ya murɗa ya shiga da sallama a bakinsa.

Ba kowa a falon dake downstairs. Sai ƙamshin room freshener spray ke tashi.

Kai tsaye ya haura upstairs ɗin. Nan ya ganta ta fito daga kitchen ta nufi ɗakinta.

Motsin shigowarsa ne ya saka ta juya ta kalle shi.

Shi kuma takaici ya ishe shi sakamakon sake ganinta da zumbulrlen hijabin da ya hana ta saka shi a cikin gidan matukar ba baƙin maza ne ko fita za ta yi ba. Wato ta raina maganarsa kenan .

Fasa shiga dakin ta shi ta juyo ta nufi in da yake ta durƙusa cikin girmamawa ta karbi basket ɗin hannunsa tana ma sa sannu da zuwa .

Dinning area ta nufa da basket ɗin ta ajiye a saman dinning table.

Zama ya yi kan ɗaya daga cikin kujerun dake falon yana kallon ta har ta karaso in da yake, ta buɗe baki za ta yi magana ta ji muryarsa yana cewa.

"Ban hana ki saka hijabi a cikin gidan nan ba?"

Sai a lokacin ta tuna amma sai sai a cikin wannan aniyar rigar barcin dake jikinta ba, don banbancin rigar da shi da babu kusan ɗaya suke.

"Ba kya jin magana ko?"

Kai ta girgiza ma sa alamar a'a.

Miƙewa tsaye ya yi bayan ya ajiye kwalin wayar da ya siya ma ta a Centre table.

"Ke kenan kullun cikin hijb a gida hijab a waje hijab makaranta hijab kasuwa hijabi kin kasa tantance in da ya dace a ce kina saka hijab ko?"

Kafin ta yi magana har ya zare hijabin daga jikinta ya rike a hannunsa.

Mutuwar tsaye ya yi sakamakon sakamakon arba da ya yi da kyakkyawar surar jikinta cikin figigiyar rigar barci da ba ta da maraba da babu.

Yayin da ya ji kamar an zare masa laka daga jikinsa, sam bai yi tunanin haka ba. Yayin da ita kuma ganin yadda yake kallon jikinta ne ya saka ta yi saurin shigewa jikinsa ta ƙanƙame shi yayin da ƙafafunsa suka fara rawa.


*Maman Ihsan ce*✍️

09065327995

Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z


*MAKAHO NE*


*NA*

Maman Ihsan ce ✍️


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


Wannan ƙirƙirerren labari ne ban rubuta shi dan cin zarafi ga kowa ba, idan suka ko hali ya zo ɗaya to a gafarce ni ba da niyyar yin hakan na yi ba. Arashi ne me kashe auren wawa


*SADAUKARWA*

Wannan shafin sadaukarwa ne gare ku masoyana na *MAKAHO NE* Fans group ina jin daɗin comments naku da tarin addu'arku a gare ni Allah ya bar ƙanuna much love


Page 2️⃣7️⃣


Yayin da ya ji kamar an zare ma sa laka da jikinsa, sam bai yi tunanin haka ba. yayin da ita kuma ganin yadda yake kallon jikinta ne ya saka ta saurin shigewa jikinsa ta ƙanƙame shi yayin da ƙafafunsa suka fara rawa.

Wani yanayi da bai taɓa riskar kansa a ciki ba ya ji shi a yau. Tun daga tafin kafarsa har tsakiyar kansa yake jin wani abu na fisgarsa.

Ita kam sai hawaye take yi don wani irin kunyar da ba ta taɓa jinsa ba a rayuwarta sai yau, ji take yi kamar ƙasa ta tsage ta shige ciki ta nitse haka take ji.

Cikin kuka ta ce .

"Yaya Fahad Please ka daina ba na so."

Da ƙyar ya iya fisgo zance ya ce.

"Me na yi ma ki na taɓa ki ne?"ya yi magana yana ɗaga hannayensa biyu sama alamar ba ruwansa.

Kuka ta saka ma sa wanda ya sa shi cewa.

"Me na yi ma ki da kike ma min kuka? Ina kece kika rungume ni, don haka ki sake ni ma na."

Cikin kuka ta ce.

"To idan na sake ka ai za ka ga jikina ne."

"To ya kike so na yi?"

"Ka rufe idanunka sai na sunkuya na ɗauki hijabi na na saka."

"Makaho ne ni da zan rufe idanuna.?"

Sai kuma ya ga gwanda ya rufe idanun nasa domin su rabu lafiya da ita, don idan ba haka ba komai zai iya faruwa a yadda yake jin kansa.

Rufe idanunsa ya yi wanda ya sa ta yi sauri. Sakinsa ta durƙusa ta dauki Hijabin ta saka. Aguje ta bar wajan ta nufi bedroom ɗin ta ta rufe tare da murza key.

Zubewa ya yi kan kujerar yana mayar da numfashi. Dade kansa ya yi cike da takaicin kansa yadda ya kasa controlling kansa akanta.

Tsawon mintuna biyar yana zaune ya kasa ƙwaƙwƙwaran motsi kafin ya iya tashi ya shiga cikin bedroom dinsa.

Wayarsa dake aljihunsa ya ciro sannan ya cire agogon hannunsa. Kayan jikinsa ya fara ragewa sannan ya shiga bathroom cikin rashin kuzari.

Yana tsaye cikin bathroom yana kallon faffaɗan ƙirjinsa zuwa damtsen hannunsa. Ta cikin mirror dake cikin bathroom ɗin sa.

Takaicin wanan zanen Tattoo yake ji ba wai don komai ba sai don sunan Sidra da ya sa aka zana ma sa da photon butterfly.

Tauna lips din sa ya yi kamar zai fasa shi cike da takaici yake kallon zanen da ya fito a kyakkyawar farar fatarsa wanda kallo ɗaya za ka yi fatarsa ka san cewa yana kashewa wa jikinsa kuɗi.

Kansa ya sakarwa shower na tsawon mintuna talatin wanda ba abinda yake tunani sai kyakkyawar surar Nadra. Ya raina yarinyar gani yake yi ƙwaila ce ita sai ga shi gabaɗaya ya susuce.

Tsawon mintuna talatin ya ɗauka yana sakarwa kansa ruwa kafin ya yi wanka ya fito. Body spray kawai ya shafa bayan ya tsane ruwan jikinsa .

Wando three-quarter fari ya saka ba tare da ya saka riga ba ya kwanta haka nan. Sai sai barci ya gagara ɗaukarsa.

Har sai tsakiyar dare barci ya in nasarar ɗaukarsa.


_Nadra_

Tun da ta samu ta kufce daga hannun Fahad ta rufe ɗaki kan gado ta faɗa. Kuka take yi tamkar ya yi ma ta wani abu, bayan ko taɓa ta bai yi ba.

Ƙudundune kanta ta yi a cikin bargo tana hawaye. A haka barci ɓarawo ya yi nasarar ɗauke ta.


_Makaho_


Tun da Ma'eesha ta kulluɓa ma su bargo bayan ya sha magani . Jinjina ya daina rawar jiki amma amma sai dai kansa har lokacin yana jin sa kamar zai rabe gida biyu.

Dafe kansa yake yi yana karanta duk addu'ar da ta zo bakinsa.

Ma'eesha sai jera ma sa sannu take yi kamar ta zubar da hawayen tausayinsa.

Har sai karfe biyun dare kafin ya ji wani zufa ya keto ma sa.

Har zuwa lokacin Ma'eesha ba ba ta yi barci ba. Tsabar tausayinsa. Sai da ta ga yana zufa sannan ta kai hannu saman goshinsa ya ji zazzaɓin ya sauka ajiyar zuciya ta sauke tana hamdala a zuciyarta.

A cikin kunnenta ta ji ya yi ma ta raɗa.

"Na gode Allah ya yi ma ki albarka ya saka ma ki da gidan Aljanna."

"Amin ya Allah."

Ta faɗa tana Murmushin jin daɗi ta kwantar da kanta a saman ƙirjinsa tana kallon kyakkyawar fuskarsa, idanunsa ma suna da kyau da ɗaukar hankali sai sai a juye idanun suke.

Gyara kwanciyar ta ta yi sa sakan faffaɗen ƙirjinsa yayin da take jin wani sihirtaccen ƙamshin da ya saka ta faɗuwar gaba.

Sai ta dake ta dinga cusa kanta a ƙirjinsa saboda ƙamshin ya yi ma ta daɗi.

A haka barci ya ɗauke ta a saman ƙirjinsa

Sai sa ya tabbatar barcin ya yi nisa sannan ya zame ta daga jikinsa a hankali, ya kwantar da kanta kan filo.

Tashi ya yi ta je ya watsa ruwa sannan ya ɗauro alwala ya zo ya gabatar da sallar nafiloli sannan ya koma kan tabarmar da yake kwanciya ya kwanta ba tare da ya koma kan katifar Ma'eesha ba.

Wanda shi ma nan take ya yi barci wanda lokacin karfe uku na dare ne.


_Nadra_

Sai karfe huɗu na asuba ta farka ta je ta ɗauro alwala ta yi sallolin nafila har alfijir ta keto ta shi ta yi raka'atanil fijri.

Aka kira assalatu ta tashi ta je ta yi sallar asuba ta zauna yin azkar. Da karatun Alkur'ani.

Tana son ta fita zuwa falo amma kuma kunya take ji ta haɗu da shi, don haka ta fara wanke toilet Sannan ta gyara ɗakinta ta yi saka turaren wuta.

Falo ta nufa tana addu'a Allah ya sa baya nan, cikin rashin sa'a kuwa tana buɗe ƙofar karaf idanunsu ya sarƙe cikin na juna.

Juyawa ta yi da a sauri za ta koma ciki sai ta ji muryarsa mai amo ya ce.

"Come here."

Ya faɗa babu wasa a fuskarsa.


*Kuyi hakuri da wannan ba na da caji ne alƙawarin da na yi na tuna ya sa ɗan yi shi*🙏🏻


*Maman Ihsan ce*✍️

Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z


*MAKAHO NE*


*NA*

Maman Ihsan ce ✍️


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


page2️⃣8️⃣


Juyawa ta yi da sauri sauri za ta koma ciki sai ta ji muryarsa mai amo ya ce.

"Come here."

Ya faɗa babu wasa a fuskarsa.


Ba yadda ta iya haka ga dawo cikin takunta na nutsuwa ta karasa gabansa, durƙusawa ta yi ta motsa laɓɓanta cike da karsashi ta ce.

"Ina kwana?"

Banza da ita ya yi kamar bai ji ta ba, har ta fidda ran zai yi magana ta ji ya ce.

"Dodo kika gani da za ki gudu ko meye?"

Kai ta girgiza alamar a'a.

"Me ya saka ba ki jin magana ne?"

"Tura baki gaba ta yi kafin ta ce.

"Ina jin magana."

"Ban ce ki daina zama mani da wannan ƙaton nan a gida ba."

"Na saba da shi ne?"

"Dole ki daina don ba na nuƙata."

Ya faɗa cike da izza.

Ba ta ce komai ba ta miƙe tsaye sannan ta ce.

"Zan shiga na gyara ma ka ɗaki ."

Bai yi magana ba ya yi kamar bai ji ta ba, ita ma ba ta sake cewa komai ba ta nufi ɗakin nasa.

'Ma sha Allah.'

Ta faɗa a zuciyarta sannan ƙarasa ciki tana ƙarewa falon kallo. Don falonsa kalar fari ne hatta kujeru da Centre carpet da Centre table da labulaye tiles komai fari ne

Bedroom ta nufa nan ma ya haɗu sosai komai dake cikin ɗakin white colour ne komai fari ne na ɗakin kama daga kan fenti labulaye, tiles, carpet, gado, mirror bedside drawer, zanin gadon, bargo, closet ɗin sa komai fari ne kuma da alama mutum ne shi mai tsafta.

Toilet ta fara da shi don shi ma nasa fari ne komai na ciki. Duk da tsaf yake kamar an wanke shi amma haka ta wanke shi tas sai ƙamshi yake yi sannan ta fita zuwa bedroom ɗin sa.

Gyara gadon ta yi ta sannan ta gyara ɗakin ta share ta yi mopping, room freshener da ta gani ta fesa a ɗakin sannan ta nufi hanyar fita.

Falonsa ta gyara ta gyara ta saka ƙamshi sannan ta fita zuwa babban falon.

Kamar yadda ta bar shi zaune haka ta same shi zaune sai dai wannan karon laptop ne a gabansa yana danne-danne.

Falon ta zo tana kokarin gyarawa ya mike tare da laptop dinsa a hannunsa ya nufi nasa bangaren.

Ledar da ya shigo da shi ta ɗauka za ta kawar ya juyo ya ce wayarki ce na siya ma ki, anjima zan kai ki a yi i ma ki register na sim card.

Kafin ta ce komai har ya rufe kofar.

Buɗe ledar wayar ta yi ta ciro kwalin wayar, ba tare da ta buɗe kwalin ta ga wayar ba ta mike tsaye ta fara gyaran Falon.

Sai da ta gama tsaf sannan ta sauka downstairs ta gyara falon ta goge komai ko ina tsaf hatta toilet dake cikin falon sai da ta wanke ta kunna turaren wuta da sannan ta haura upstairs nan ma ta saka turaren wuta .

Tana shirin komawa bedroom ɗin ta kenan ta ji ta ji ƙarar ƙararrawar ƙofa.

Sauka ta yi ta je ta buɗe, sai ta ga Rumaisa ce da basket a hannunta.

Murmushi suka sakarwa juna kafin Rumaisa ta ce .

"Barka da safiya Aunty?"

"Don Allah ki daina ce ma ni Aunty ki kira ni da Nadra, don kin girme ni ni ce ya kamata na kira ki da Aunty."

Murmushi Rumaisa ta yi ta ce.

"Ko na girme ki yanzu ke ce sama da ni, sabi'oda Yayana kike aure kenan kin zama Yayata."

Mika ma ta basket ɗin ta yi tana cewa.

"Sauri neke yi sai Anjima kuma."

"To don Allah ki ce wa Mama ta daina aiko ma na da abinci mun gode sosai, zan fara shiga kitchen da kaina."

Kai Rumaisa ta jinjina tana cewa.

"Zan fada ma ta in sha Allah."

Sallama suka yi ta juya ta tafi ita kuma ta shiga da abincin ciki, a dinning table ta ajiye ta shiga bedroom nata.


_Ma'eesha_

Farkawa ta yi da asuba cikin barci take ta laluben katifar ko za ta ji shi, amma sai ta ji wayam ba alamar mutum a kusa da ita, bayan ta san a jikinsa da ta kwanta.

Kunna torchlight ɗin wayanta ta yi sai ta hango shi can kan tabarma da yake kwanciya akai ya kwanta ya dunƙule jikinsa waje ɗaya.

Mamaki ya kama ya kama ta domin ita dai a iya saninta yadda ta yi masa gata ta kawo shi kan katifa ta lulluɓe shi amma bai masa ba ya tashi ya koma kan tabarma.

Taɓe baki ta yi daidai lokacin ne kuma aka kira sallah.

Shi ma kiran sallar ne ya farkar da shi ya buɗe juyayyun idanunsa wanda suke ajuye sai dai ba sa da amfani tun da baya gani da idanun.

Ƙoƙarin tashi ya fara yi ta yi sauri ta sauka tana miƙa ma sa sandarsa.

"Ga sandarka nan."

Ta mika masa sandarsa ya karba tare da cewa.

"Na gode Allah ya yi ma ki albarka."

Da Amin ta amsa tana ɗaukar buta ta ba shi buta.

"Ya jikin naka?"

"Na ji sauƙi."

"Allah ya kara sauki."

"Amin na gode, matata maganin kukana."

Bayan ya yi alwala ya je masallaci yayin da ita kuma ta yi sallar ta a gida.


Sai karfe bakwai ya dawo daga masallaci zuwa lokacin har ta kammala breakfast.

Doya ta soya ma su sai ta yi source ɗin ƙwai. Da ruwan Lipton wanda ya ji kayan ƙamshi.

Don kudin da suke hannunta sun ƙare ƴan canji ne suka rage ma ta.

Ruwan Lipton kawai ya iya sha bai ci doyar ba, hakan ya saka ta damu Kasancewar ta san ruwan Lipton ba zai ɗauke shi ba.

"Ko na siyo bread ne na haɗa ma ka tea ka sha?"

"Kada ki damu hakan ya ishe ni, ba na jin cin wani abu a bakina ne."

Cike da tausayawa ta ce.

"Ayyah sorry."

Kai kawai ya jinjina ma ta ba tare da ya yi magana ba.

"Bari na je na kawo ma ka maganininka."

Tana fadar haka ba ta jira cewarsa ba ta tashi ta ɗauko ledar maganinsa ta ba shi.

Pure water ta fasa ta zuba a cup ta bashi .

"Ka sha maganin sai ka kwanta ."

Ta fada tana ɓallo ma sa maganin ta bashi, ya karba ya sha.

"Zan yi wanka."

Ya faɗa yana dafe kansa.

"Okay bari na kai ma ka ruwa."

Tashi ta yi ta je ta haɗa ma sa ruwan wanka ta kai ma sa banɗaki.

Yana zaune ta dawo ta ce.

"Na kai ma ka ruwan a banɗaki."

"To na gode Allah ya yi ma ki albarka."

Amin ta amsa yayin da da shi kuma ya fara lalube cikin jakar kayansa.

"Me kake nema?"

"Jallabiyata."

"Okay bari na duba ma ka."

Kafin ya yi magana sai hannunsa ya kai kan jallabiyar sakamakon tana da santsi ne ta fita daban da sauran kayan, hakan ya saka da ya kai hannu yake gane abinda ya taɓa.

Ɗauka ya yi ya yayin da ita kuma ta fita daga ɗakin.

Bayan fitar ta sai ya cire kayan jikinsa ya saka jallabiya.

Kayan da ya cire ya fito da su yana cewa.

"Ina son na wanke kayan kafin na shiga wanka."

"Saboda me za ka yi wanki bayan ba ka da lafiya ?"

"Kar ki damu zan iya yi."

Nan ta dai suka fara jayayya akan za ta wanke masa ma sa shi kuma ya hana ya ce shi zai wanke.

"Kana son na samu lada?"

"Eh sosai kuwa Ma'eesha."

"To idan har kana son na samu lada to ka bar ni na yi wankin kayan ka domin lada za'a rubuta ma ni."

Hakan ya saka ya ce.

"Ke me ya saka idan zan wanke ma ki kike hanawa?"

"Saboda ni na fi cancanta na yi ma ka ba kai za ka yi mani ba."

"Ni kuma ba na son ki wahala bisa la'akari da gidan da kika fito ba ki saba da waɗan nan aikace -aikace ba."

Murmushi mai ciwo ta yi tare da cewa.

"Haka ne, ka yi gaskiya, tabbas ban saba ba don ma su aiki ke yi ma ni amma hakan ba yana nufin ban iya ba ne. Don haka ko da a ce mijina kana da kudi ka aje ma su aiki to ka sani duk wani aiki naka ba zan taba bari ƴar aiki ta yi ba domin kwaɗayin ladan da zan samu wajan kyautata ma ka."

"Kin tabbata?"

"Of course, ka jira lokaci za ka ce na faɗa."

Murmushi ya yi kafin ya ce.

"Wani lokaci zan jira kuka yaushe lokacin zai zo, na so na ga wannan lokacin."

Kallo da ta yi tana ɗauke ƙwallar da ta ji ya gangaro ma ta da yatsanata ta ce.

"Lokaci yana tafiya a hankali ga masu jira, yana gudu da sauri ga masu tsoro,yana zama dogo sosai ga masu korafi, yana zama gajere ga masu murna,
Amma ga masu ƙauna lokaci shi ne madawwamiya."

Cikin sanyin jiki ya nufa banɗaki ba tare da ya yi magana ba, saboda yanayin maganar na ta tana gab da yin kuka. Domin ya ji ƙuna a cikin kalamanta.


_Nadra_

Ta gama shirinta zuwa register da zai kai ta na sim card ɗin da zai siya ma ta. Haka kawai ta tsinci kanta cikin farin ciki domin ta san ko ba komai za ta ji Muryar Umma da Abba.


Fitowa ta yi dan sanar da shi ta shirya, baya Falon don haka sai ta yi knocking da a ƙofar falonsa. Jin shiru ya saka ta yi tunanin cewa yana cikin bedroom ɗinsa.

Don haka ta tsaya bakin bedroom tana knocking.

Izinin shiga ya ba ta ta tura ƙofar bedroom ɗin ta shiga bakinta ɗauke da sallama.

Yana tsaye a gaban dressing mirror ɗaure da towel a ƙugunsa ta shigo. Ganinsa haka nan ta juya da sauri tana barin ɗakin.

Ta jikin mirror ya kalle ta ganin yadda ta fita kamar wacce ta ga abin tsoro take guduwa.

Tsane ruwan jikinsa ya cigaba da yi.

Ita kuma ba ta tsaya ko ina ba sai bedroom ɗinta.

Don saura kadan dogon Hijabinta ya haɗe ma ta ƙafa ta faɗi, sai Allah ya taimake ta ba ta fadi ba.


Tana nan zaune bayan wasu ƴan minutes ya shigo sanye da farin yadi mara nauyi.

Sai ƙamshin turarensa yake tashi a jikinsa.

Ganinsa ya sa ta mike da sauri tana kallon sa cike da fargaba, ganin take yi kamar wani laifi ta aikata ma sa ganinsa da ta yi ɗaure da towel.

"Ke."

Kallonsa ta yi ganin yana kallonta ya saka ta ɗauke idanunta da sauri.

"Ina ganin akwai motsi a cikin kanki ko?"

Ba ta gane me yake nufi ba don haka ta ce.

"Motsi a cikin kai kuma?"

"Eh ina nufin ba ki da cikakken hankali ko?"

Tura baki ta yi tana kau da kai.

Da kika shiga ɗakina me ya saka kika fita a guje?"

"To da ka san ba ka da kaya a jikinka me ya saka ka bari na kalle ka haka nan ai bai dace ba."

Mamaki ta bashi don haka ya ce.

"Shekarunki nawa?"

"Goma sha takwas."

'18 years no wander ta fiye shirme da yawa, ashe akwai tazara tsakaninta da Sidra, don Sidra yanzu shekarunta ashirin da biyar, an dauki yarinyar da ba ta gama mallakar hankalin kanta ba an hada ni da ita.'

Tsuki ya ja a fili wanda sai da ta ɗaga kai ta kalle shi. Sai ta ɗauka shigar da ta yi masa ɗaki ne ya ba shi haushi, don haka ta ce.

"Ka yi haƙuri zan kiyaye."

"Za ki kiyaye me?"

"Ba zan sake shigar ma ka daki haka nan ba ganka ba kaya a jiki ba wannan ma akasi ne."

Dafe kansa ya yi ya rasa ya zai nuna ma ta daidai da ba daidai ba.

"Kina zuwa islamiyya?"

",Eh mana har walima fa sai da na yi."

"Me aka sanar da ku akan hakkin aure?"

Shiru ta yi kanta a ƙasa, ya ce

"Akwai inda aka ce ma ku ya haramta don miji ya kalli matarsa ba kaya ne ko kuma shi ya kalle ta ba kaya sun aikata wani babban laifi ne?"

Girgiza kai ta yi alamar a'a. Sannan ta ce.

"An ce mu dinga rufe tsiraicinmu."

"Okay to waye aka ce ku baiyana wa tsiraicinku ?"

Tura baki gaba ta yi tana kau da kai.

"Ni ma ban sani ba."

"Okay to bari na nuna ma ki yau za ki sani."

Ya faɗa yana nufo tana ja baya, da sauri ta ce.

"Mazajen aurenmu ne za su iya ganin surar jikinmu."

Ta fada kamar za ta yi kuka, shi kuma ya yi dariya ya ce.

"Oh ashe kin sani kike yi kamar wata..."

Rurin wayarsa ya saka ya dakata da maganar da yake yi ya duba ganin Mama ce ya ɗaga da sallama.

Bayan sun gaisa ne ta cikin wayar take sanar da shi zuwan dangin mahaifinsa zuwa Anjima. Ya ce to ya sani zai kai Nadra ta yi register layi ne ya siya ma ta waya. Mama ta ji daɗin hakan sai sanya masa albarka take yi, ta ce ya ba Nadra su gaisa ya ce tana cikin dakinta idan ta fito zai kira. Ya fadi haka ne don ya ga ta kasa motsi kunya ta ishe ta ba lallai ta yi maganar ba.

"Ki same ni a mota."

Yana fadar haka ya fice daga ɗakin, ita ma ta bi bayansa.

Tsaye ta gan shi a ƙofar fita, tana fitowa ya rufe kofar, har lokacin ba ta yarda ta kalle shi ba.

Motar da ya nufa ta bi bayansa, direbansa ya taso ya zo ya buɗe ma sa bayan motar ya shiga ita ma ya bude mata dayan gefen ta shiga sannan ya zagaya ya zauna mazauninsa, ya yi wa motar key suka bar gidan bayan maigadi ya wangale ma su gate.


*ABUJA*

_Sidra_

Ta fito daga cikin gidan hannunta rike da handbag ɗin ta da wayarta. Wajen motar dake harabar gidan ta nufa. Direban ya saka trolly ɗin ta a but motar yayin da ta zauna bayan motar.

Fuskarta ba walwala duk yadda Sady baby ke ta yi ma ta magana ba ta wani kula ta ba, don haushin ta take ji. Kasancewar ita ta ba ta goyon bayan abinda ta aikata, a lokacin da Khadijah ke hana ta gani take yi Khadijah ba ta ƙaunar ta, sai ga shi sanadin biye wa Sady baby komai ya lalace ma ta.

"Ƙawata Sa mun yi waya, don Allah ki yi hakuri kuma da za ki bi shawara ta ki hakura da Fahad tun da an bashi ƙanwarki ya aura."

"Fahad nawa ne ni kaɗai babu macen da za ta mallake shi sai ni kuma zan iya aikata komai a kansa, babu wanda ya isa ya ma ni shamaki da abun so na ciki kuwa har da ƙanwata Nadra"

Ta fada cike da ƙasaita.

"Direba mu tafi sauri nake yi."

"Allah ya tsare hanya."

"Amin idan kuma har wata matsala ta biyo baya to fa ki sani ba zan ɗauki fansa ta akanki ba zan taɓa saurara ma ki ba ko kaɗan."

Direba ya ja motar suka bar gidan suka kama hanya don zuwa Kaduna.


*Maman Ihsan ce*✍️

09065327995

Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z


*MAKAHO NE*


*NA*

Maman Ihsan ce ✍️


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


page2️⃣9️⃣


"Amin. Idan kuma har wata matsala ta biyo baya to fa ki sani zan ɗauki fansa ta akanki ba zan taɓa saurara ma ki ba ko kaɗan."

Direba ya ja motar suka bar gidan suka kama hanya don zuwa Kaduna.

Amma a zuciyarta fargaba ce ta yadda za ta tunkari iyayenta da maganar dalilin da ya sa ta gudu ranar ɗaurin aurenta. Tabbas ta san mahaifnta na da zafi, idan ya dauki zafi ya hau to saukowarsa abu ne mai matukar wahala cikin sauƙi. Sai yanzu take nadamar wasikar da ta rubuta ta ajiye, domin kuwa da ba ta rubuta ta ajiye ba za ta iya ƙaryar cewa sace ta aka yi yanzu aka sake ta. Amma wannan wasikar shi ne babban kuskuren da sai yanzu ta san ta tafka ta.

Cike laɓɓanta ta yi tabbas ba za ta tunkari gidansu ba sai ta fara zuwa wajan ƙawarta Khadijah ta ba ta shawarar yadda za ta yi, wanda a baya ta yi kokarin hana ta guduwa amma ta kasa.

Wayarta wacce har yau take kashe ta kalla sai ta kau da kai tana kallon hanya.


_Fahad_

Yana zaune a bayan motar Nadra na gefensa , idanunsa na kan wayarsa yana danne-danne ya ce.

"Za mu yi baƙi yau, dangin mahaifina ne za su zo ganin ki zuwa anjima."

"To Allah ya kawo su lafiya ."

Ba wanda ya sake yin magana a cikinsu har suka ƙarasa office na kamfanin MTN don ya siya ma ta sim kuma ta yi register.

Suna parking a wajan da aka tanada don ajiye motoci direban ya fito da sauri ya bude ma su bayan motar .

Suka fito sai ga wani mutum sanye da Suit ya ƙaraso in da suke cike da girmamawa ya ce wa Fahad.

"Ambassador Barka da zuwa."

Hannu Fahad Majidaɗi ya mika ma sa suka gaisa.

Sannan ya kalli Nadra ya ce.

"Madam Barka da zuwa."

"Ina kwana?"


Ya amsa sannan ya ma su jagora zuwa ciki.

Ba ɓata lokaci aka yi ma ta duk abinda ya dace, gabɗayansu san san waye Fahad.

Har da ihsani ya yi ma su sannan suka bar wajen suka kama hanyar gida.

Ganin sun kusa zuwa ta hanyar da zai sada Nadra da gidan iyayenta ta kalle shi ta ce

"Don Allah ka kai ni gida na ga Umma ta ko na mintuna biyar ne."

Ka kallonta bai yi ba ballantana ya amsa ma ta. Har suka wuce hanayar unguwar tana kallon hanyar idanunta na cikowa da ƙwalla sakamakon ba ta da lafiya ko ranar auren a kwance take.

Horn direban ya yi maigadi ya wangale ma sa gate ya shiga da motar, parking space ya nufa ya yi parking sannan ya fito ya bude ma su.

Bayan sun fito ne ya rufe sannan suka shiga ciki.

Bayan sun haura upstairs ne ya kalle ta ce.

"Ki haɗiye wannan hawaye naki na faɗa ma ki, idan kuma kukan kike sha'awar yi zan saka ki yi mai dalili."

Ya faɗa yans jinjina kai alamar tabbatar wa.

Na fada ma ki muna da baƙi idan kika kuskura kika aikata abun da zan ji kunya akan akan gidadanci suka bar gidan nan sai na hukunta ki a cikin gidan nan"

Tura baki ta yi tana magana ƙasa-ƙasa tana cewa.

"Ni kam ba bagidajiya ba ce, idan mutum baya irin rayuwar da kuke yi sai ku dinga ma sa kallon bai waye ba, to ba na son wayewar ta ku."

"Me kike cewa ne?"

"Ba abinda na ce da kaina nake magana."

Ta faɗa tana kallon wayar dake ajiye a Centre table, ta dauki wayar ta tuna ba ta yi ma sa godiya ba.

Ta kalle shi ta ce .

"Na gode Allah ya saka da alkhairi ya ƙara ma ka buɗi."

Tana fadar haka ta shiga ɗakinta da wayar a hannunta.

Shi ma ɗakinsa ya wuce.

Tana shiga ta daka sim card ta yi settings komai, tana gamawa ta ga ya tura kofar ya shigo mika ma ta kati ya yi ba tare da ya ce komai ba. Karɓa ta yi ta ga recharge card ne na 10,000 ya siya ma ta cike da murna ta yi godiya ya fice bai amsa ma ta ba.


_Makaho_

Bayan ya fito daga wanka hannunsa ɗauke da bokitin ya ajiye a tsakar gidan.

Ma'eesha na zaune a tsakar gidan ta ce.

"Ka yi a hankali."

"Na gode."

Ya faɗa yana laluben ƙofar ɗakin kafin ya shiga da sallama.

Sai bayan kamar mintuna talatin ta shiga cikin ɗakin da sallama a bakinta.

Ya amsa ma ta yana zaune kan tabarm kansa a ƙasa.

"Lafiya dai ko ciwon kan ne?"

"Ba komai."

Shiru ta yi kafin ta ce.

"Zan je can bakin layi na dawo?"

"A dawo lafiya?"

Ya amsa ma ta sannan ta ɗauki gyalen ta yafa ta fice daga gidan.

2k ya rage ma ta a hannunta ga shi yanzu mijin baya jin dadi tana son ta siya ma sa nama ta ɗan yi masa farfesu ko zai ci tun da ya kasa cin abinci.

Dubu ɗaya ta cire ta siye naman dubu ɗaya ya rage ma ta dubu ɗaya. Abun da ba ta yi tsammani ba shi ne ganin naman dubu ɗaya yanka biyar ya yi ma ta cikin sanyin jiki ta dawo gidan tana tunanin wanan. 1k da ya rage ma ta idan ya kare ya z su yi, ga shi tana son ta siye Omo da sabulu na wanki.

Kafin ta shiga gidan ta tsaya wajen me shagon ta fiye Omo na ɗari biyu da dabulun wanki na ɗari uku aka ba ta canjin Naira ɗari biyar.

Ta koma gida gidan in da ta tarar har ya yi barci, don cikin magungunan da aka ba shi akwai wanda zai saka shi barci.

Gass ta kunna ta ɗora tukunya ta haɗa ma. Sa farfesun naman wanda ya ji kayan ƙamshi.

Ko ɗaya ba ta ci ba ta zuba masa a bowl ta rufe ta ajiye ma sa. Jira take yi ya tashi ko zai samu abinda ya saka a baki, domin rashin cin abinci da bai yi ba ya dame ta


_Nadra_

Sabuwar wayarta da Fahad Majidaɗi ya siya ma ta Samsung Galaxy S23 ultra wayar kudinta ta kai kimanin miliyan ɗaya da dubu dari biyu 1,200,000.

Kallon wayar take tana Murmushi cikin ledar wayar ta duba ta zaro idanu sakamakon ganin zunzurutun kuɗin wayar wanda ba ta yi zato ba.

Umma ta kira don ta ji muryarta amma sau biyar kiran na katsewa ba'a ɗaga kiran ba, sai ta saka lambar Abba ta danna ma sa kira, kasancewar ta haddace lambobin wayar a cikin kanta.

Abba ya ɗaga kiran wayar tare da yin sallama.

"Assalamu alaikum."

"Abba."

Ta faɗa muryarta na rawa kamar za ta yi kuka.

"Nadra ke ce?"

Kai ta jinjina kamar yana ganinta.

"Kina lafiya?"

"Lafiya lau Abba."

"Ma sha Allah, ina mijin naki?"

"Yana ɗakinsa?"

"Ba wata matsala ko?"

Hawaye ta goge kafin ta ce.

"Abba nan zan cigaba da zama da shi har zuwa lokacin da Aunty Sidra za ta ..."

Tsawar da Abba ya daga ma ta ne ya saka ta fashe da kuka. Tabbas ta san cewa mahaifinta na da zafin zuciya kuma wannan alama ce da ke nuna har yanzu yana fushi da Sidra."

Jin sautin kukanta ya saka ya sassauta murya cikin sigar rarrashi ya fara magana.

"Nadra, ashe ba na faɗa ma ki cewa kada ki sake yi ma ni maganar Sidra ba, ki mance da ita tun da ta guje mu ta zabi wasu akan mu to ki ɗauka ta mutu. Na san mancewa da ita ba, amma wannan ne karo na karshe da za ki yi ma ni maganar ta. Tabbas ta so ta kunyata ni ta tozarta ni a idanun duniya Allah ya sa ke ce kika fidda mu kunya , hakika ina alfahari da ke Allah ya yi ma ki albarka ƴaƴanki za su yi ma ki fiye da yadda kika ma na."

"To Abba."

Ta faɗa tana goge hawaye.


Kiran wayar Farida ne ya shigo wayar Fahad, nan take sanar da shi sun ƙaraso suna harabar gidan.

Nan yake sanar da ita yana zuwa.

Fita ya yi in da ya same su a harabar gidan, ƙannin mahaifinsa ne da yayyunsa, sai da wasu dangin mahaifinsa, sai Rumaisa da ta yi ma su jagora Da Farida wacce ta na ce sai ta zo ita ma. Duk da mahaifiyarta Hajiya Jummai ta hana ta zuwa don kada ta zo ta ga abun zai ɓata ranta.

Motoci uku suka yi don sun kai su goma sha biyar.

A falon dake downstairs suka yada zango. Sai ya gushe su cike da girmamawa abokanan wasansa na tsokanarsa

Farida ba ta shigo ba ta tsaya a harabar gidan tana ƙarewa gidan kallo. Tana ina ma ita ce aka kawo wannan gidan a matsayin mayar Fahad Majidaɗi. Cike da ƙunar rai ta shiga falon tana karewa falon kallo.

Tabbas ya tsaru gidan Fahad gida ne da kowace mace mai hangen nesa za ta yi fatan ace ita ce matar gidan.

Bayan sun gaisa da kowa ne ya kalle su ya ce

"Mu haura sama sai ta fito ku gaisa ko?"

Ya fadi haka yana haurawa upstairs ɗin wacce ganin haka ya sa Farida ta bi shi a baya.

"Yaya."

Ta faɗa cikin shagwaɓa wanda ya sa ya tsaya daidai kofar ɗakin Nadra.

"Ya aka yi ne Farida, kin gama fushin naki?"

Hararar wasa ta yi ma sa tana cewa.

"Duk ranar da aka ce na mutu to son ka ne ya yi ajalina."

Basar da ita ya yi kamar bai je me ta ce ba, daidai lokacin da zai shiga ɗakin Nadra ta yi saurin rike hannunsa suka shiga tare.

Da sallama a bakinsa suka shiga ita kam ko sallamar ba ta yi ba. Hannunsa na cikin na Farida suka shiga, shi a ganinsa ba wani abu ba ne kamar yadda Rumaisa ke rike shi haka Farida ke ma sa duk da kasancewar ita ba maharramarsa ba ce akwai aure a tsakaninsu.

Daidai lokacin da Nadra ta ɗago kai tana kallon ƙofar, ta sauke idanunta a kansu ta yi saurin goge hawayenta. Hannunsu dake sarƙe cikin na juna ta kalla sannan ta kalli fuskar Farida sai ta ga ba ta san ta ba kuma ba Rumaisa ba ce wacce suke uwa daya uba ɗaya, iya saninta Rumaisa ce kawai ƙanwarsa.

Harara mai cike da tsana Farida ke jifan Nadra da shi.

Nadra kam ba ta ma san tana yi ba, dan kallo ɗaya ta yi ma ta ta kalli hannunta da take rike da na Fahad ta ɗauke kai.

Wayar Fahad ce ta fara ruri ya kalli Nadra ya ce.

"Sun iso suna falo."

Daga haka ya daga kiran wayar yana mai zame hannunsa daga cikin na Farida.

Fita ya yi daga ɗakin yana amsa wayar.

Farida ta tsaya ta rike ƙugu tana ƙare wa ɗakin Nadra kallo.


_Ma'eesha_

Bayan ta gama duk wasu aikace-aikace da take da su har wankin kayan ta da na Makaho sai da ta wanke su. Ta shiga ɗaki ta same shi zaune ya haɗa tagumi.

"Ka tashi ?"

Ta fada tana zama a gefensa. Hannun ta ta daura a saman goshinsa zuwa wuyansa ta ji ba zafi.

"Alhamdulillah da alama ka ji sauki ko?"

Kai kawai ya jingina ma ta ba tare da ya ce komai ba.

"Na san kana jin yunwa ko?"

"Eh."

Ya faɗa a takaice.

"Bari na kawo ma ka abin da za ka ɗan fara ci."

"Bari na wanke baki."

Ya faɗa yana mikewa tsaye.

"Ina na ajiye Sandar tawa ce?"

"Ga shi nan gabanka ai bai yi nisa da kai ba."

"kin san ban gani nake yi ba, kuma ban laluba ba."

"Allah sarki wata rana za ka gani, in sha Allah wata rana idanunka za su buɗe ka ganni ka ga yadda wannan duniyar ta mu take."

Ɗan jim ta yi kafin ya ce .

"Ba na jin zan iya gani, domin Wannan lalurar da ita aka haife ni, kin san kuka duk wata lalura in dai har da ita aka haife ka to ba wanda zai iya ba ka magani ko aiki ka samu lafiya. Sai dai wadanda suka samu lalurar daga baya ne to ana iya dacewa."

"Ikon Allah ya fi gaban mamaki."

Fita ya yi ya je ya wanke baki, ko da ya dawo ta ajiye ma sa farfesun naman nan da ruwa sai lemu na gora da take da shi ajiye.

Da sallama a bakinsa ya shigo cikin ɗakin, don haka ta amsa tare da cewa


"Na ajiye ma ka abinki ka yi a hankali."

Ta fada tana rike hannunsa da taimakonta ya zauna.

ƙamshi ya daki hancinsa ya yi shiru kafin ya ce.

"Me kika dafa."

Farfesun naman rago ne."

"Ina kika samu nama?"

Murmushi ta yi tare da cewa.

"Siya na yi ma na, ina zan samu nama?"

"Na ɗauka kudin ki ya kare."

"Eh ya ƙare yanzu haka ma ɗari biyar ne ya rage ma ni."

Dafe kansa ya yi tare da furta kalmar.

"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un."

Ga ni yake yi ya gaza tun da har kudin hannunta suka kare bayan ɗawainiyar da take yi na gidan da shi kansa, yanzu ina zai shiga ya fita don samawa kansu mafita, yadda kudin suka kare haka wata rana ma kayan abincin da ta ajiye ma su a gida za su ƙare."

Ganin lokaci ɗaya ya shiga cikin damuwa sosai daga jin kuɗinta sun ƙare ta ce.

"Komai ya yi zafi maganinsa Allah, a cikin tafiyar rayuwa babu wanda ba ya fuskantar ƙalubale. Wani lokacin abubuwa sukan yi zafi har mutum ya ji kamar ya kasa, ko kuma ya fitar da rai, talauci, rashin aikin yi, bacin rai, ko rashin lafiya na iya sanya zuciya ta yi nauyi, amma babban sirrin samun natsuwa shi ne haƙuri. Komai yayi zafi maganinsa Allah hakuri ba yana nufin gazawa bane, yana nufin jiran lokacin da Allah ya sanya maka ne cikin natsuwa da yaƙini.Ka tuna dukkan waɗanda suka yi nasara a rayuwa sun sha wahala kafin su sha daɗi, Wahalar yau ita ce labarin gobe. Watarana idan ka waiwaya baya, za ka yi murmushi ka ce Alhamdulillah, domin duk waccan wahalar ta zama tarihi. Kada ka bari halin da kake ciki yau ya sa ka manta alkawarin Allah ci gaba da hakuri, ci gaba da addu'a, kuma ci gaba da aiki tukuru, Allah ya sa mu wanye lafiya, ya kuma canza mana kuncinmu zuwa farin ciki."


*Maman Ihsan ce*✍️


09065327995

Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z


*MAKAHO NE*


*NA*

Maman Ihsan ce ✍️


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


page3️⃣0️⃣


"Komai ya yi zafi maganinsa Allah, a cikin tafiyar rayuwa, babu wanda ba ya fuskantar kalubale. Wani lokacin abubuwa sukan yi zafi har mutum ya ji kamar ya kasa, ko kuma ya fitar da rai, talauci, rashin aikin yi, ɓacin rai, ko rashin lafiya na iya sanya zuciya ta yi nauyi. Amma babban sirrin samun natsuwa shi ne hakuri, Komai yayi zafi maganinsa Allah haƙuri ba yana nufin gazawa ba ne, yana nufin jiran lokacin da Allah ya sanya maka ne cikin natsuwa da yaƙini.Ka tuna dukkan wadanda suka yi nasara a rayuwa sun sha wahala kafin su sha daɗi wahalar yau ita ce labarin gobe. watarana idan ka waiwaya baya, za ka yi murmushi ka ce Alhamdulillah, domin duk waccan wahalar ta zama tarihi, kada ka bari halin da kake ciki yau ya sa ka manta alkawarin Allah. Ci gaba da hakuri, ci gaba da addu'a, kuma ci gaba da aiki tukuru. Allah ya sa mu wanye lafiya, ya kuma canza mana kuncinmu zuwa farin ciki."

Cike da burgewa yake sakin murmushi saboda kalaman ta na hikima da burge wa, wanda ke sanya da cikin shauƙi a duk lokacin da ya ji fararen zantukanta ma su daɗin saurare, yakan tsinci kansa cikin farin ciki.

"Bismillah ka ci kada ya yi sanyi."

"Ke kuka fa?"

"Kada ka damu na riga na ci nawa naka ya rage."

Shiru ya yi kamar mai yin wani nazari kafin ya ce.

"Ina son yau na lallɓa na fita na san ko ba yawa dai zan ɗan samu. Akwai wasu canji a aljihun wata rigata ina ganin za su iya kai ɗari uku ki riƙe su duk da na san ba waya amma ba za ki rasa abun siye ba. Tun da ni ba na siyan komai ballanta na yi amfani da kuɗin."

"Jinjina kai ta yi tare da cewa

"To Allah ya sa ma su albarka."

Da Amin ya amsa sannan Don haka iya guda uku ya ci ya ce ya ƙoshi, ta ce za ta rufe ma sa zuwa Anjima ya ce A'a. Ya ishe shi.

Dole ta bar shi ita sai ta cinye sauran .

Cewa ya yi zai zo ya shirya ya fita, ita ce ta hana shi ta ce sai ya gama warware wa bai kamata ya fita a haka ba. Ta ce masallaci kawai za ta iya barinsa ya tafi.


_Farida_

Matsawa ta yi dab da Nadra tana kallon ta cikin idanu bayan ta gama ƙarewa ɗakin kallo. Wanda kallo ɗaya za ka yi ma sa ka san cewa iyayenta ma sun yi bajinta sun siya ma ta kaya ma su tsada kama daga furniture har komaib dake cikin ɗakin .

Taɓe ba ki ta yi kafin ta ce.

"Amarya ta ango."

Nadra dai ba ta tanka ta ba, don tun da ta lura da mugun kallon da Farida ke ma ta ne ta gane ba arziki ya kawo ta ba.

Idanun Farida ya sauka akan sabuwar wayar Nadra da Fahad ya siya ma ta.

Zare idanu waje ta yi tana mamaki kafin ta ce.

"Au har matsayinki ya kai ya siya ma ki wayar Samsung Galaxy S23 ultra wayar da kuɗin ta ya kai miliyan ɗaya da dubu dari biyu ko fi ma?"

Baƙin ciki takaici ya ishe ta, wayar ta ɗauka tana dubawa, irin wannan wayar ita ce take mafarkin mallaka a yanzu. Burinta da samu wayar, sai dai ta yi mamaki yadda take tunanin Fahad ba haka ba, a baya da ta ji sanyi a ranta lokacin da ta ji an ce ba da ɗin ransa aka yi ma sa auren ba baya son yarinyar. Sai dai hankalinta ya tashi ne da su Rumaisa suka faɗa cewa Fahad ya yi karɓi budurcin Nadra har ta kasa tafiyar Sa bya ɗauke ta. A wannan lokacin ta ji guiwarta ya yi sanyi. Ta ji ta sare sai kuma yanzu da ta ga wayar nan da ya siyo ma ta .

"Nadra kike ko wace ce oho dai, bari na ba ko wani labari. Ni sunana Farida kuma ni ƴa ce a wajan ƙanwar mahaifiyar Fahad. Kuma soyayya muke yi da shi, ke a taƙaice dai sabada mu yi kusanci da juna me ya je ya ɗauko ni daga wajan iyayena ya kawo ni gidansu don mu shaƙu da juna soyayyar mu ta yi karfi kuma..."

Kasa ƙarasa maganar ta yi sakamakon tura ƙofar da aka yi aka shigo.

Kallon su ya yi ɗaya bayan ɗaya kafin ya ce.

"Lafiya kuwa?"

Murmushi Farida ta yi ta ce.

"Lafiya lau ina gabatar ma ta da kaina ne."

"Why not ki bari ku tafi can gaban kowa sai ku yi gabatar wa an bar su zaune suna jira."

Nadra dai ko kallonsa ba ta yi ba ta mike tsaye ta nufi hanyar fita sanye da hijabinta har ƙasa wanda suka dawo da shi daga yin register na sim card.

Da sauri ya rike hannunta wanda sai da ta ji faɗuwar gaba. Kallon su Farida ta yi wacce ta ji kamar ya soka ma ta mashi ne a ƙahon zuciya.

"Farida ki je muna zuwa."

Kamar ta yi ta kurma ihu haka take ji, q fusace ta fita.

Kallon Nadra ya yi ya ce.

"Ke wai ba na faɗa ma mi kada ki sake sanya hijabin nan ba. Da muka dawo ne ban cire ba."

Kai tsaye ya ce.

"Cire Hijabin nan."

Ba musu ta cire, doguwar riga ce a jikinta na atamafa ɗinkin ya zauna ma ta cif a jikinta, atamfar irin me aikin nan a jiki ce kuma ta ji Stone work.

Sun ɗan kama ta amma na sosai ba, kallonta ya fara yi wanda cikar halittar ta ke ba shi mamaki a iya shekarunta.

"Haka zan fita? Ban saba ba fa."

"Daga yanzu dole ki saba."

Mintuna biyu ba ba ki kada ki bari na dawo na tarar da ke a cikin ɗakin nan ba tare da kin fito ba."

Yana gama fadar haka ya fita daga cikin ɗakin.

Tana nan tsaye ta ga lokacin da ya ba ta ya kusa cika, kuma ya hana ta saka hijabi ba t da wani zaɓi dole ta fito


Suna nan zaune suna fira suna yaba kyawun gidan Fahad, shi kuma idanunsa na kan ƙafa yana jiran ta fito kafin su yi ƙorafi.

Ƙarar ƙofar ya sa suka juya suka kalle ta.

"Ma sha Allah."

Wasu daga cikin su suka faɗa. Don tabbas Nadra ba ta da makudan tana da kyau da kuma diri mai ƙyau sai dai a ce ma ta baƙa ce ita.

Kanta a ƙasa cikin natsuwa da kunya take takun ta. Shi kansa ya kasa ɗaukeidanunsa daga kanta, domin shi kansa idan ya ganta ba hijabi sai ya yi ta kallonta saboda surar jikinta mai ɗaukar hankali ne.

Durƙusa wa ta yi ƙasa ta fara gaiahe su suna amsawa. Ƴan matan da su Rumaisa suka gaiahe ta a matsayin ta na matar Yaya.

Kitchen ta nufa ta buɗe fridge ta ɗebo bottle water da lemukan roba sai da ta ciki tire sannan ta kai ma su ta ajiye ma su. Sannan ta kawo ma su cincin da dubulan da Alkaki ya yawa .

Kitchen ta koma tana tunanin me za ta sarrafa ma su mai sauki ne.

Ta duba kitchen ɗin duka akwai komai na buƙata.

Sanin spaghetti ya fi sauki ya sa ta fara ƙokarin girka ma su.

Nam da nan kuwa ta fara ma su girki ɗin .

Ƙamshin turarensa ya da ta juya bayan ta blending na kayan miya.

"Me za ki yi anan?"

"Girki zan yi ma su."

"Ba bukatar sai kin yi ma su girki don a yadda kiken nan da ƙauyanci ba wani girkin da kika iya, ki zo ki kawo ma su kwamacalar da za ki saka a yi ta magana akai. Idan sun tafi ki girka iya cikinki ke kaɗai."

Maganar ta yi ma ta zafi amma sai ta yi Murmushi ta ci gaba da aikinta.

Ƙamshi har cikin falon wata daga cikin matan na cewa

"Sai mun ci girkin amarya kafin mu tafi.

Shi dai Fahad na mamakin taurin kai irin na Nadra yake yi, wato ba ta daina ba ta ci gama da yi kenan.

Cikin ƙanƙanin lokaci ta dafa ma su jallop ɗin spaghetti da ya ji kayan lambu da bisashen kifi. Sai Pepe chiken don kan gas biyu ta yi amfani da su.

Babban food flask ta zuba ciki ta kawo ma su . Sannan ya kawo ma su Pepe chiken.

Ta ƙara kawo ma su ruwan sanyi da lemu, sai plates da forks ta kawo ma su suna ta yi ma ta godiya .

Miumushi ta yi tana cewa.

"Ba komai, ku yi hakuri don ban san da zuwan na ku da wuri ba."

Rumaisa ce ta dinga zuba ma su taliyar da pepe chicken ɗin .

Don ganin suna da yawa ya saka Nadra ba ta kai ma su dinning table ba.

An zuba wa kowa Rumaisa ta kalli Fahad ta ce.

"Yaya daga yanzu in dai Aunty Nadra na wuri Sai dai ta za ta zuba ma ka abinci."

"Am okay."

Ya faɗa ya tashi ya koma can gefe kan sofa yana danne-danne a wayarsa. Shi a ganinsa ba ta iya girki ba kwamacala ce kawai .

Sai ya ji kowa na santin abincin.

"Aunty Ashe haka kika iya girki mai daɗi?"

Murmushi kawai ta yi don ba sabon abu ba ne don a yaba girkinta. Don ko gida duk ranar da ta yi girki sai an fi ɗokin cin girkin nata fiye da na Sidra. Farida ce kawai ba ta ci abincin ba ta koma gefe tana danne-danne a wayar ta.

Bayan sun kammala Rumaisa da sauran ƴan matan suka gyara wajan suka yi wanke-wanke.

Har lokacin Fahad bai ci komai ba, don ko breakfast na safe bai yi ba.

Sai karfe shida suka bar gidan. Nadra ta ba ƴan matan turarurruka iyayen kuma ta ba su dubu hamsin 50k cikin kudin sadakinta da aka ba ta.

Bayan fitar su Fahad ma ya bar gidan, ba shi ya dawo ba sai karfe goma na dare.

Yunwa duk ta addabe shi, don ba wani abun da ke cikinsa in ban da biscuits da lemu.

Ɗakinsa ya nufa kai tsaye, a gajiye ya rage kayan jikinsa ya shiga bathroom. Wanka ya yi ya fito sanye da rigar wanka.

Bayan ya shafa turarrukansa ne ya sanya wando three-quarter Blue da farar singileti.

Ji ya yi ba zai iya kwana bai ci abinci ba, ga shi ko da ya je gidan Mama daddare nan ya ce a kawo ma sa abinci cewa ta yi ya je matarsa ta ba shi. Shi kuma baya iya cin abincin restaurant daga na mahaifiyarsa sai sai kuma ya yi ta fama da kayan snacks.

Bai da zabi dole ya nufi part ɗin Nadra don yunwar yake ji sosai.

Da sallama ya shiga ɗakin nata, tana zaune kan sallaya sanye da hijabi tana karatun Alkur'ani.

Karfe goma da mintuna arba'in lokacin, tana karanta suratul Maryam.

Zama ya yi bakin gadon nata har ta kai karshen surar. Don dama ta kusan idar wa.

Juyo wa ta yi ta kalle shi yana zaune abakin gadon.

"Sannu da dawowa."

Kai kawai ya jinjina ba tare da ya amsa ma ta ba.

"Please ki nema mani abun da zan ci yinwa nake ji."

"To me kake so na girka ma ka?"

"Komai mai sauƙi dai da ba zai ɗauki lokaci ba."

"Na dafa ma ka indomie ne don ya fi sauƙi."

Bai tanka ma ta ba, tashi ta yi ta je ta ajiye Alqur'ani ba tare da ta cire hijabinta ba ta fita zuwa kitchen. Don ita ta saba da saka hijabinta mancewa ma take da wai ya hana ta.

Daga nan zaune da yake ya ɗan kishingiɗa ya kwanta kan gadon, ƙafarsa na ƙasa yaba kallon saman ɗakin.

Lumshe idanunsa ya yi cike da gajiya nan da nan barci ya ɗauke shi a nan saman gadonta.


_Maeesha_

Da misalin karfe goma na dare ta gama shirin kwanciyarta. Tana sanye da rigar barci iya guiwarta.Makaho kuma ya fito daga wanka kenan. Hannunsa rike da sandarsa ɗayan hannunsa kuma rike da kayan da ya cire, ya saka jallabiya. Da alama a cikin banɗakin ya sauya kayan jikinsa.

Da sallama ya shigo Cikin ɗakin.

"Assalamu alaikum"

"Wa'alaika Salam."

Ta amsa tana mai zuba ma sa idanun kasancewar akwai hasken wutar lantarki nepa sun bar ma su wuta.

Zama ta yi a saman katifar tana kallonsa

"Akwai abun da kake bukata me yanzu?"

Ta tambaye shi sakamakon barci da ke idanunta tana son ta kwanta.

"Ba na buƙatar komai, Allah ya yi ma ko albarka."

"Amin ya Allah."

"Ka zo ka kwanta saman katifar."

"Ke ina za ki kwanta idan na kwanta saman katifa?"

"Zan kwana ni ma a katifar mu kwanta tare ai ba wani abu ba ne matarka ce ni fa ta sunnah to mene ne don nun kwanta a wajen ɗaya, na tausaya ma ka ne fa saboda ganin ba dadin kwanciya ƙasan kake ji ba, sannan kuma ba isasshen lafiya ce da kai ba. Idan na ce na bar ma ka katifar ni ma ba zan iya kwanciyar a ƙasa ba jikina ciwo zai yi, ka sani ba wai sai an sanar da kai ba ma'aurata muke to me ye dalilin ka da ba ka son ka raɓi jikina, ba wai ina son wani abu ya shiga tsakanina da kai ba ne don Mun kwana a shimfida ɗaya amma na duba dacewar hakan ne sakamakon ba mu da wajen kwana sai wannan kayifar don ko bargo ma da za ka ji taushi babu. Amma sai gudun haka kake yi, na saka ka ka kwana tare da ni ranar da ba ka da lafiya bayan na yi barci ka zame jikinka ka sauka ka bar ni me hakan ke nufi? Ba akan daidai nake ba kai ne kake kan daidai?"


_Sidra_

Da misalin karfe takwas na dare motar da ta kawo ta ta faka a ƙofar gidan Mahaifinta.

Sakamakon motar ta k lalace a hanya ya saka suka yi dare.

Sallama ta yi wa mai motar yayin da ya fito ma ta da trolly ɗin ta tana jansa ta nufi bakin gate ɗin.

Knocking take yi kafin maigadi ya ce .

"Waye a wajen."

Ba ta tanka ba har ya taso ya bude.

Ganin ita ce ya sa ya bude baki cikin mamaki ya ce.

"Hajiya Sidra Kece daga ina?"

Ba ta duba darajar farin gemu da ya haife ta ba ta ce.

"Daga gidanku."

Baki ya sake yana kallonta don bai yi mamaki ba kadan ne daga rashin mutuncinta, Don har marinsa ta taɓa yi.


*Mamman Ihsan ce*✍️


09065327995

Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z


*MAKAHO NE*


*NA*

Maman Ihsan ce ✍️


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


page3️⃣1️⃣


Baki sake yake kallon ta don bai yi mamaki ba, kadan ne daga rashin mutuncinta, don har marinsa ta taɓa yi.

Da idanu yake kallonta har ta ɓace wa ganinsa.

A hankali ya fara tuna wata rana ta dawo daga unguwa tana danna horn ɗin mota tana jiran ya bude ma ta gate. Shi kuma ya zagaya banɗaki sai da ya gama uzirinsa ya fito da hanzari ya wangale ma ta gate ɗin gidan.

A guje ta shigo da motar kamar za ta bi ta kan Baba maigadi da motar.

Ita ce ke driving sai Nadra dake zaune wajen me zaman banza.

A fusace Sidra ta fito daga cikin motar ko kashe motar ba ta yi ba, Nadra ce ta kashe motar ta zare key.

Baba maigadin yana kallon Sidra ta nufo shi a fusace sai da ya tsorata. Cikin kwantar da murya ya ce.

"Ki yi hakuri Hajiya ina banɗaki ne lokacin..."

Kafin ya kai karshen zancen ta ɗauke shi da mari wanda sai da ya yi baya kamar zai fadi.

Tsoro da firgici ne ya bayyana akan fuskar Nadra.

Idanunta cike da ƙwallar tausayin tsohon ta ce.

"Baba don Allah ka yi haƙuri na san ba ta kyauta ba ɓacin rai ne, ba ta iya sarrafa fushinta ne."

Ta yi maganar tana ɗauko ma sa hularsa da ta fadi ƙasa.Kallon Nadra ya yi tare da cewa.

"Allah ya yi ma ki albarka."

Da Amin ta amsa sannan ta sake ba shi hakuri ta nufi cikin gidan wanda Sidra ta riga ta shiga.

A falon ta tarar da Sidra ita kaɗai sai huci take yi.

"Aunty Sidra sam ba ki kyauta ba, ta ya ya za ki dubi wannan dattijo da ya haife ki za ki iya ɗaga hannu ki mare shi?"

"Na mare shi akan me zai bar ni cikin mota ina jiransa? Ba aiki yake yi ba albashi ake biyansa ?"

"Amma wannan ba shi zai ba ki lasisin da za ki taka wanda yake ƙarƙashinki ba, domin ɗan Adam daraja ne da shi kuma..."

"Shut up!"

Ta sakawa Sidra tsawa tare da cewa.

"Ki fita a sabga ta idan ba haka ba wallahi yanzu zan ma ki marin da ya fi wanda na masa."

Tana fadar haka ta nufi ɗakinsu ita kuma Nadra ta nufi part ɗin Ummansu.


Sauran ma'aikatan gidan da suke gefe suna kallon yadda Sidra ta faɗawa Baba maigadi magana su ma suka shiga taitayinsu don na Baba mai gadi ma sauki ne.

"Ita kuma wanan daga ina kamar wata korarriya ta dawo a wanann daren?"

Direba ne ya yi maganar, sai mai ba wa fulawa ruwa ya ce.

"Ai ta yi wa kanta sagegeduwa don da yanzu ita ce a gidan miji cikin rufin asiri, amma yanzu ga shi ta dawo ta tarar da mijin da take so ya auri ƙanwarta."

Nan dai suka dinga firan Sidra a tsakaninsu.


_Abba_

Tsaye yake a ɗakin Umma yayin da Ammi ke ta fama da Umma akan ta ci abinci amma ta ƙi ci. Don tun lokacin da ta yi arba da wasikar da Sidra ta rubuta ta ajiye ta gudu. To daga nan ba ta sake lafiya ba, abinci ma sai na matsa ma ta take ci.

Saboda tana cikin tashin hankali na rashin sanin halin da ƴarta take ciki, ba ta san hannun waye za ta faɗa ba, kuma ba ta san in da ya shiga ba, don ko anan haka kawai idan suka fita unguwa daga ita har Nadra to Umma ba ta taɓa samin nutsuwa da sukuni har sai ta ga sun dawo gida hankalinta yake kwanciya, amma yau ga shi an wayi gari ba ta san in da Sidra ta tafi ba ko sanin halin da take ciki ba.

Abba ya kalli mahaifiyarsa da take ta fama da Umma ya ce.

"Ammi ta sha maganin ta kuwa?"

"Ina fa ta sha Abdallah wannan yarinyar taka wallahi mu dai ba ta taɓa yi ma na rana ba, Allah ya wadaran halin Sidra ga shi ta saka mahaifiyarta ta cikin halin jinya, me yiwuwa tana can hankalinta kwance. Tun da yarinyar nan take ba abun arzikin da ta taɓa yi ma na, akan me za ki damu da yar da ba ta damu da ke ba, idan ta damu dake za ta tafi wani wajen ta bar ki ne?" Duk a cikin jikokina Sidra ce ta fita Zakka wallahi da ina da dama da na..."

Sallamar ta da turo ƙofar da ta yi ne ya saka sauran maganar Ammi maƙalewa. Tana kallon Sidra da maɗaukacin mamaki, a hankali ta ce .

"Sidra!"

Umma dake kwance tana fama da jinya ta buɗe idanunta tana ƙokarin tashi zaune. Abba ya haɗe fuska kamar zai yi Aman wuta yana ma ta kallon bakin ciki da takaici.

Trolly ɗin hannunta ta sake ta ƙaraso gabansu tana kuka. Tana ƙoƙarin zubewa akan guiwar ta kenan cikin zafin nama da tafasar zuciya Abba ya saka ƙafa ya yi balla da ita wanda sai da kanta ya haɗu da bango Ya bugu, ta zube a wajan tana sakin Maryan kuka.

"Tashi ki bar mani gida tun kafin zafin zuciya ta ɗebe ni na yi ahalinki."

_Ma'eesha_

Har ta gama zancen da take yi makaho bai tanka ma ta ba. Ita mamaki ma yake ba ta, meye a ciki don sun kwanta a katifa ɗaya tana matarsa yana mijinta.

Ba ta gama mamaki ba ta ga ya kwanta akan tabarmar ya shafa addu'o'i a jikinsa ya juya ma ta baya.

Takaice ya ishe ta don sai yanzu take nadamar yi ma sa magana da ta yi akan su dinga kwanciya a katifa ɗaya, sai ya ɗauka ko tana bukatar kasancewa da shi ne a shimfiɗar ma'aurata wanda abu ne mawuyaci ne ga mace budurwa kuma Hausa Fulani.

'Ba zan sake yi ma sa magana akan ya zo su kwanta a katifar ba in sha Allah.'

Daga haka ta kwanta tana ta mita cike da takaici har barci ya ɗauke ta.


_Nadra_

Indomie ta dafa ma sa wanda ta yi wa haɗi sai ya ji kayan lambu su carrot da sauran su ta dafaffen ƙwai da naman kaza.

Ta ɗora plate ɗin indomie a tire ta rufe da wani plate ta saka fork sannan ya saka bottle water me sanyi da kofi .

Cikin natsuwa take tafiya a hankali ta nufi ɗakinta don ba ta ji motsin fitowar sa ba da alama har yanzu yana ciki kenan.

Ko da ta shiga da sallama a bakinta, ba ta ji ya amsa ba don dama shi sai ya ga dama take magana idan bai ga dama ko kana ma sa magana ba zai tanka ma ta ba.

Stool ta janyo ta ɗira tire ɗin a gabansa.

Ga mamakinta sai ta ga ya yi barci. Kamar ta tayar da shi kuma sai ta fasa tayar da shi. Don ba ta san yanayinsa ba, ba kowa ke son idan yana barci a tayar da shi ba, don haka ta fasa tayar da shi.

Tsaye take tana kallonsa ta rasa ya za a'a yi.

Don haka ta fara ƙokarin shiga wanka don ita ma barci take son yi.

Hijabin jiki ta ta cire ta ninke shi ta ajiye a saman sallayar.

Bathroom ta nufa don yin wanka.

Wanka ta yi da shower gel ɗin ta mai ƙamshi sannan ta zuba wani turaren da Gwaggo Laraba ta kawo ma ta ta ce ta dinga zuba wa a cikin ruwan wanka yana da kanshi mai dadi kuma yana kama jiki ya daɗe yana kamshi a jikin mutum.

Towel ta ɗaura a kikinta wanda ya tsaya ma ta iya rabin cinyarta, sai ta fito sam ta mance da wai Fahad na cikin ɗakin.

Gaban dressing mirror ta tsaya tana goge jikinta da wani ƙaramin towel tana goge ruwan jikinta.

A hankali ya fara bude idanunsa a cikin barci da ya ɗauke na mintuna.

Saman ɗakin ya kalla kafin ya tashi daga zaunen da yake a hankali ya sauke idanunsa akan ta.

Tana tsaye ta gama goge jikinta. Idaninsa na sauka a kanta sai da ƙirjinsa ya buga da ƙarfi. Tun daga kan zara-zaran yatsun ƙafarta yake kallonta Yana sama da idanunsa har zuwa santala-santalan cinyoyinta da suke sheƙi ga alamar cikar hips ɗin ta a bayyane. Kallonta yake yi cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara.

Man shafawarta take shafawa hankali kwance tana rera wakar larabci.

Bayan ta shafa man a hannayen ta ne sai ta fara ƙokarin zame towel ɗin jikinta.

Kamar an ce ta kalli madubin sai ta hango Fahad ya zuba ma ta rikitatun idanunsa yana kallonta.

Da sauri ta mayar da towel ɗin da take ƙoƙarin kwancewa ta janyo hijabi da sauri ta zura ta rufe jikinta.

Kau da kansa gefe ya yi cike da takaicin rashin kwancewar towel ɗin ba ta yi ba. Don baj taɓa ganin mace mai diri da ta jan hankalinsa ba kamar idan ta kalli Nadra ba hijabi a jikinta. Ko dai ta san cewa tana da sura mai jan hankali ne ya sa take rufe jikinta kullun cikin hijabi.

Tabbas yarinyar ta kusan ruɗar da shi, amma saboda mishkilancin irin nasa ya basar kamar bai kalle ta ba.

Fuska ba walwala ya kalle ta cikin tsare gida ya ce.

"Ina abincin?"

Kallon stool ɗin da ke gabansa ta yi tare da cewa .

"Ga shi nan, na ga kana barci ne na ajiye ma ka."

"Ina barcin zan ci da kina ajiye kika kama gabanki ?"

"Ka yi hakuri na ɗauka ba za ka so na tayar da kai ba ne."

"Okay."

Ya faɗa yana miƙe wa ya nufi kofar fita ya fice daga cikin ɗakin.


_Sidra_

Wani azababben zafi ne ta ji ya ratsa tana zaton kanta ma ya fashe.

Duhu ta fara gani ga wani jiri da take ji yana ɗibarta daga kwancen da take. Muryar Abba ta ji cikin kakkausan marya ya ce

"Ba na bukatar sake ganin ki a cikin gidan nan, ki tashi ki koma inda kika fito, ki je wajen da ya fiye ma ki nan."

Cikin kuka ta ce.

"Abba ka yi hakuri ka yafe ma ni wallahi sharrin shaidan ne."

Idan ba ki tashi kin fita ba sai na illata ki kuma na saka a yi waje da ke yanzu kuwa."

Sai a lokacin ta yi kokarin kiran sunan mahaifiyarta mai tausayin ta. Uwa mafi uba ko da Uba sarki ne."

"Umma ki taimaka ki saka baki Abba ya saurare ni."

"Ba abinda zan saurara ki tashi na ce.

Sai a lokacin ta ji sautin kukan mahaifiyarta, don kuka ne ya ƙwacewa Umma q wanann lokacin.

"Umma don Allah ku saurare ni, ki saka banki Abba ya sauko."

Kallon kakarta ta yi tana cewa.

"Ammi please ki saka banki ɗanki ne Abba yana ma ki biyayya kuma..."

Kafin ta rufe baki Ammi ta ce .

"Ko kashe ki zai yi ba zan ce komai ba mara mutunci kawai."

"Na ji ko ba za ku yafe ma ni ba don Allah ku daura ma ni aure da Fahad idan bai aure Ni ba zan iya rasa rayuwata."


Mamaki ne ya kama kowannen su domin kuwa da alama ba kukan nadamar abun da ta aikata take yi ba. Kuma babu nadama a tattare da ita, ba ta yi nadamar wuce wa ta bar iyayenta cikin tashin hankali ba, ba ta damu da halin da suka shiga ba a'a ita ta saurayin ta take yi ma.

Cikin takaice Ammi ta ce .

"Ai sai dai ki mutu domin Fahad yana can tare da matarsa Nadra."

Kuka ta sake mai haɗe da kururuwa Abba ya ja ta ƙeee taka ihu bai saurare ta ba sai da ya kai ta har baƙin gate bayan ya ce maigadi ya buɗe ma sa gate ya cilla ta waje. Sai ga Ammi ta cillo ma ta handbag ɗin ta da trolly sun rufe gate ɗin ta ciki.


*Maman Ihsan ce*✍️

09065327995

Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z


*MAKAHO NE*


*NA*

Maman Ihsan ce ✍️


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


page3️⃣2️⃣


Kuka ta sake mai haɗe kururuwa Abba ya ja ta ƙeee tana ihu bai saurare ta ba sai da ya kai ta har bakin gate, bayan ya ce wa Maigadi ya buge ma sa gate ya cilla ta waje. Sai ga Ammi ta cillo ma ta handbag ɗin ta da trolly sun rufe gate ɗin ta ciki.

Kuka sosai Sidra ke yi tana tuna ranar haɗuwar su ta farko da Fahad.

Ta fito daga cikin super market tana tsaye tana magana da wata ƙawarta da suka daɗe ba su haɗu ba sai yau da ta zo shopping. Sady baby ta kalli Sidra ta ce .

"Na gaji da zuwa gidanku tun da ke ba ki zuwa gidan mutane dai dai ayi ta zuwa gidanku Ni ma na kama kaina."

Sidra dake sanye cikin fitted gown na less ɗinkin ya zauna ma ta a jiki less ɗin dari ne da ratsin golding sai ƙaramin gyale golding colour da ta rataya a gefen kafaɗarta sai baƙin glass da ta saka a idanunta tana jingine a jikin motarta sai ta buɗe bayan motar ta saka ledar siyayyen da ta yi, kallon Sady baby ta yi ta ce.

"Ki yi haƙuri ƙawata wallahi Abba da Muna ba su bari muna yawon gidajen ƙawaye, Khadijah ƙawata kawai suke bari na je ita ma sai da dalili.

Wata galleliyar mota ƙirar Lexus ( Lc series higher trims) ce ta ƙaraso wajen kyawun motar da tsaruwarta ya saka hankalin wadanda ke wajen ya koma ga motar. Hatta Sidra da ke sanye da bakin glass idnsunta na kan motar, sai dai ba za ka taba gane me take kallo ba.

Murfin motar mamallakin motar ya buɗe, a hankali ya ziro fararen ƙafuwansa waje wanda yake sanye da takalmi kambas masu tsada ƙirar Gucci sneakers. Kafin ya fito yana sanye da tsadadden kaya na alfarma Tshirt mai tsada da wando jeans.

"Fahad Majidaɗi kenan, I like the guy."

Cewar Sady baby tana kallonsa.

Jin shaka ya saka Sidra cewa.

"Kin san shi ne?"

Ba ta amsa ma sa ba, don gabaɗaya hankalinta ya koma kan Fahad.

Cikin takunsa na ƙasaita yake taku har ya shiga super market.

Sai da ya shiga sannan Sidra ta ce .

"Waye wanan guy din?"

Sady baby ta ce .

"Sunansa Fahad Umar Majidaɗi. Shi Ambassador ne Yana wakiltar ƙasarsa ne a ƙasar America (united state) yana yawan zama a ƙasar America , yana aiki a matsayin hadin gwiwa tsakanin tsakanin Nigeria da America. Yana jagorantar harkokin diplomasiyaz yana ƙarfafa dangantakar ƙasar da yake wakilta, da kuma kulawa da al'amuran ƴan ƙasarsa da suke zaune a American yana Magance matsalolin siyasa da tattalin arziki tsakanin ƙasashen guda biyu."

Murmushi Sidra ta yi kafin ta ce .

"Yana ƙoƙari."

"Na taɓa nuna ma sa ina son sa ya yi rejecting ɗina."

Cewar Sady Baby cike da takaici

Murmushi Sidra ta yi wanda ita kadai ta san ma'anarsa . Sallama Sady baby ta yi ma ta ta shiga motarta ta bar wajan.

Sidra ta matsa jikin motar Fahad ta jingina tana jiran fitowarsa. Ba jimawa ya fito tare da wani ma'aikacin super market din ta riko ma sa kaya.

A bayan motar ya saka ma sa Fahad ya dunƙule kudi ya ba shi, zagayawa ya yi wajen direba sai ya ga Sidra ta jingina da mirgina motar tana waya, tana pretending kamar da gaske.

"Wallahi Umma na gaji sosai ga Direban bai dawo ba yamma ta yi ban san yadda zan yi ba ga shi ba na iya shiga abun hawa na kasuwa."

"Excuse me."

Ya faɗa kamar wanda aka yi wa dole.

Sai ta yi kamar ba ta ji ba, kamar za ta yi kuka take magana akan rashin abun hawa. Kafin ta katse wayar ta kalle shi ta yi Murmushi.

"Oh sorry."

Ta fada tana matsawa.

"Nevermind."

Ya ba ta amsa yana kokarin shiga motar.

"Oh Allah yanzu ya zan yi na koma gida."

Kin haka ya ce.

"Ki shiga na kai ki idan ba za ki damu ba."

"Toh na gode."

Ta fada tana mai zagayawa mazaunin direba ta shiga ta zauna.

Tsawon lokaci mintuna ba wanda ya yi magana kafin ta ce .

"Na gode fa."

Bai amsa ma ta ba yana driving ɗinsa.

"Da ana samun mutane irin ku marasa girman kai masu saukin kai ai da an gode."

Sai a lokacin ya kalle ta yana cewa.

"Ke ce mutum ta farko da ta ce ina da sauƙin kai wai ba na da girma kai, kowa cewa yake ina ji da kaina ke kika fita daban."

Dariya ta yi tana cewa .

"To ma sha Allah na zama ta daban a wajen ka."

Kwatance ta yi masa ya kai ta har ƙoafar gidansu. Za ta fice ta ce.

"Sai yanzu ta daban za ta sake ganinka."

"Duk sanda kike bukatar gani na in dai ina kasar za ki ganni."

Ya faɗa yana miƙa ma ta katinsa ta yi godiya, sai da ta jira wucewarsa ta shiga cikin gidan,.

Direban su ta ba key ɗin motarta ta sanar da shi in da zai je ya dauko motar sannan ta shiga ciki.

Tun daga nan ta ke kiran Fahad a waya suna gaisawa har wata rana ya zo ya bayyana ma ta yana son ta. Ranar kamar za ta zuba ruwa ƙasa ta sha , daga nan suka ƙulla soyayya cike da kulawar juna, in dai yana ƙasar yana yawan zuwa ko da bai daɗe ba.

A hankali Sidra ta share hawayenta bayan ta gama tunanin ranar da suka fara haɗuwa da Fahad tana dafe kanta inda ta bugu da dukan da Abba ya yi ma ta.

"Ba zai yiwa a raba ni da shi ba Fahad nawa ne dole ya saki Nadra ya aure ni."

Da ƙyar ta tashi ga dare ya yi ta nufi bakin titi kasancewar ba nisa da gidansu da gidan Gwaggo Maimuna. Tana ganinta ita ma ta kore ta don ta dauki zafi kamar yadda ƙaninta Abba ya dauki zafi.

Daga nan sai ta nufi gidan Gwaggo Laraba lokacin karfe goma sha ɗaya na dare.

Gwaggo Laraba ta yi ma ta faɗa sannan ta kira Abba ta ba shi haƙuri akan ya yi haƙuri. Kwancewar shi ne dama da Gwaggo Laraba ya yi ma ta fada ya ce idan ba ta kori Sidra ba ta bar gidan nan idan ba haka ba sai ta hadu da ɓacin ransa. Ba ta da wani zaɓi dole ya ce ya tafi.

A ranar Sidra ta ga tashin hankali sosai ba kaɗan ba.

Ƙarshe ta yanke shawarar zuwa gidan iyayen Fahad don ta nemi alafarmar Baban Fahad ya je ya roƙi Abba ko Allah zai sa ya hakura kasancewar yana jin kunyar Baban Fahad yana ganin ƙimarsa.

Ƙarfe ɗayan dare ta yi ba abun hawa ga shi dama ba da motarta ta tafi Abuja ba. Yanzu na ina take ta mota.

Ƙarfe ɗaya da kwata ta isa ƙokar gidan su Fahad a jikace sakamakon dogon tafiyar da ta yi .


_Makaho_

Bayan ya tabbatar da Ma'eesha ta yi barci don dama shi ma ba barci yake yi ba idanunsa biyu. Tashi zaune ya yi tare da lalubar sandarsa ya ji ya riko ta ya mike tsaye.

Hanyar ƙofar ya nufa yana lalube har ya buge sakatar ya fita daga cikin ɗakin.

Bayan ya ɗauro alwala ya zo ya fara sallolin nafila. Ba shi ya kwanta ba sai karfe uku na dare.

Yana zaune kan sallaya yana addu'o'i kafin ya shafa.

Kwanciyar sa ya yi wanda ba jimawa barci ya yi awon gaba da shi.

Kiran sallar asuba ya farkar da shi daga barcin da ya soma ɗaukarsa.

Fita ya yi daga ɗakin ya nufi banɗaki.

Wanka ya yi ya fito ya yi alwala sannan ya koma dakin.

Jin tsit sai saukar numfashinta ya tabbatar ma sa da cewa .

Har yanzu barci take yi ba ta farka ba.

Kayan jikinsa ya sauya zuwa wata jallabiya kafin ya nufi in da katifar da Ma'eesha ke kwance.

Pillow ya buga yana kiran sunanta.

"Ma'eesha."

A hankali ta bude ida wanda daka a lumshe suke kamar bairci.

"Na'am."

"Lokacin Sallah ya yi ni zan shiga Masallaci, ki tashi ki yi sallah.

,"toh"

Ta fada hana tashi daga zaunen da take.

Fita ya yi shi ma ya je masallaci yayin da ita kuma ta gabatar da sallar a gida.


_Fahad_


Bayan ya bar indomie da Nadra ta dafa ma sa ɗakinsa ya koma. Kwanciyar rud da ciki ya yi yana cije lips ɗin sa ba tsakiya.

Ba abinda ke ma sa yawo a kansa sai yadda ya ga Nadra ɗaure da towel.

Gabaɗaya abun ya tsaya masa a cikin kansa ya yi kane-kane ne.

Cike da takaici ya ce .

"Oh Fahad wai tunanin me kake yi haka ne, ba dai waccen ƴar karamar yarinyar je neman birkita masa ƙwaƙwal.


Da sallama ta turo kofar ɗakinsa ta shigo, bayan sallamar da ta dinga yi a bakin ƙofar falon

Yana jin sallamar amma bai bude idanunsa ba kuma bai tanka ba .

Tire ɗin ta ajiye wanda ta jera ma sa abincin akai .

"Ga abincin nan na kawo maka."

Kamar ba zai amsa ba kafin ya ce

"Okay thank you, sai da safe za ki iya tafiya."


"To Allah ya ba mu alkhair."

Har ta kai bakin ƙofar ta ji ya ce .

"Zo mana."

Yadda ya yi maganar sai da gabanta ya fadi, don haka ta juyo cikin sanyin jiki ta karasa wajensa.

"Ina za ki je?"

"Kai ka ce na tafi ."

"Okay kuma yanzu na ce ki dawo"

Shiru ne ya biyo baya kafin ya ce .

"A nan ɗakin za ki kwana."

Ya faɗa kamar ba shi ya yi maganar ba.


_Makaho_

Dawowarsa daga masallaci kenan ya yi sallama, Ma'eesha na zaune a barandar ƙofar ɗaki tana hada ma su abun breakfast a gas ta amsa sallamar da ya yi .

Cikin sanyin murya ta ce .

"Ina kwana?"

Ya amsa da lafiya lau ya aiki ya ƙoƙari ?"

"Alhamdulillah, ya karfin jiki?"

"Alhamdulillah."

Sallama suka ji yaro ya yi ya shigo.

Suka amsa ma sa ya ce

"Wai ana sallama da Ma'eesha."

Cikin mamaki ta ce.

"Waye ?"

Yaron ya ce .

"Wani ne ya zo da mota yana waje."

A tunanin ta Yaya Jamil ne, amma duk da haka yya ce.

"Ka je ka ce waye?"

Yaron ya fita ba jimawa ya dawo ya ce.

"Wai ya ce saurayinki ne Abdul ya dawo ."

Mamaki da al'ajabi ya kama ta ya aka yi ya san tana nan , shin ba ta yi blocking nasa ba kuma ta fada ma sa ta yi aure.

Tashi ya yi cikin ɓacin rai ta dauki hijabin ta ta saka ta lallai makaho ta ce.

"Ina zuwa don Alaihi minti biyu."

Daga haka ya nufi kofar gidan ta fice.


*Mamman Ihsan ce*✍️


09065327995

Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z


*MAKAHO NE*


*NA*

Maman Ihsan ce ✍️


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


page3️⃣3️⃣

Daga haka ta nufi ƙofar gidan ta fice.

Wata baƙar motar ce ta hango a ƙofar gidan, tinted glass ne ba ta iya hango na cikin motar.

Amma shi yana ganinta ya bude murfin motar ya fito ya jingina da jikin motar yana kallonta da maɗaukacin mamaki a fuskarsa. Don ko da Ma'eesha ta faɗa ma sa a waya cewa ta yi aure bai yarda ba, sai da ya tambaye Nasreen ta faɗa ma sa gaskiya ne, daga nan ya matsa ma ta akan sai ta bashi address na Ma'eesha. Da farko ta hana ma sa sakamakon Ma'eesha ta yi ma ta gargaɗi akan haka wanda har da barazanar cewa idan ta sake ma ta zancen Abdul ko kuma ta ƙara ƙalubalantar auren za ta rabu da ita. Amma sai Abdul ya ruɗe Nasreen da maƙudan kuɗaɗe wanda ya sa ta ba shi address n gidan. A tunanin ta ba zai gane gidan ba saboda yanayin unguwar ta talakawa ne kuka gine-ginen gidajen ba wani tsari ne da su ba.

Fuska Ma'eesh ta ƙara tsuke wa kafin ta isa wajensa.

"Abdul meye haka, me ka zo yi a nan bayan na faɗa ma ka cewa ni yanzu matar wani ce, amma saboda rashin sanin darajar aure ya sa za ka zo kofar gidan matar aure ka ce a yi ma ta sallama ta fito?"

Gajeren murmushi ya yi kafin ya ce.

"Wai yanzu Ma'eesha Ibrahim Khalil ce ta dawo haka? Look at you, kin yi baƙi kin rame duk wanda ya san ki a baya idan ya ganki yanzu ya san kina cikin wahala. Wannan rayuwar ba ta dace da ke ba, ba za ki iya ba kuma ba ki saba ba. Don haka wannan musakin mijin naki kuma faƙiri ki sa ya sake ki ki zo mu je ki cika ma ni alkawarin aurena da kika yi. Zan ba ki jin dadi da kwanciyar hankali zan mayar da ke..."

"Ya isa haka Abdul!"

"Kina da baƙin da za ki hana ni na yi magana ne? Bayan a baya ina ma ki kallon mai gaskiya ashe ba haka kike ba, bayan kin yi alƙawari ki saɓa an ba ki amana kin yi ha'incin? Ko kin manta ke da kanki kika yi ma ni alkawarin aure? Ke fa kika ce da zaran na dawo daga ƙasar Canada na dawo Nigeria za ki tura ni wajan mahaifinki na gama da shi a yi zandan aure kawai sai da na kira ki a waya ki ce ma ni wai kin yi aure haka yarda da amana take, bayan kin yi ma ni alƙawarin aure ashe yaudara kika shirya, Ni ina can ina tsara mana rayuwar da za mu yi bayan auren mu idan na ɗauko kin mun bar Nigeria, ashe sha sha sha kika mayar da ni ko?"

Goge hawayen dake kan fuskarta ta yi kafin ta ce .

"Ni ban zamo daga cikin munafukai ba da suke ɗaukar alƙawari su saɓa ko kuma su yi karya ko su ci amana. Ban yi ko daya daga cikinsu ba."

"To idan ba ki yi ba me ya sa kika yi aure bayan kin yi ma ni alkawari?"

"Ni ma kaina ban san da zancen aurena ba kwatsam lokacin ɗaya ake shaida ma ni wai an ɗaura ma ni aure ba tare da sani na ko shawara da ni ba ballantana neman yarda ta. Ka ga ta ina nake da laifi akan hakan?"

"To na ji ba ki da laifi amma ai Nasreen ɗin ta fada Mani wanda kika aura musaki ne kuma faƙiri to me ya sa za ki yarda ki zauna da shi? Ai kin fi karfinsa nesa ba kusa ba, ai zaren ba kalar yadin ba ne. Kina da ikon da za ki saka ya sake ki ko ta ƙarfin arziki ko ta tsiya tsiya , bai isa ya yi jayayya da ke ba, idan kuma ba za ki iya saka wa ya sake ki ba ki bar ni da shi ina da hanyoyi da yawa da zan saka ya rabu da ke ko yana so ko baya so ki bar ni da shi."

Ɗaga ma sa hannu ta yi alamar dakatarwa kafin ta ce.

"Ba ruwanka da shi?"

"Da mamaki yake kallon ta kafin ya ce.

"Kar dai a ce wai son sa kike yi, kina nufin kina son makaho mabaraci ina fatan dai ba ki taɓa bari ya raɓi jikinki ba?"

A fusace t ce.

"Abdul!"

Sai da ya kalle ta da kyau bai amsa ba ya dauke kansa yana kallon gefe.

"Ka fita a sabga ta domin yanzu ni matar aure ce, kuma zaman aure nake yi na ibada har abada ba don na fito wata rana ba. Khalifa mijina ne har a aljanna in sha Allah, ina son mijina ba abinda zai saka na rabu da shi mutuwa kaɗai za ta raba ni da shi, idan ka sake zuwa ƙofar gidan nan wallahi sai na tafka ma ka rashin mutunci, don sai na sa yara sun dinga jifanka da duwatsu sun farfasa ma ka mota. Wanda bai san darajar aure ba.

Makirin murmushi ya saki kafin ya ce.

Kika ce ba abun da zai sa ki rabu da shi ba ko? Sai kuma kika ce mutuwa ce kaɗai za ta raba ki da shi to ai ko akwai abun da zai raba ki da shi ɗin domin kuwa mutuwar rigar kowa ce kuma mutuwar tana nan tana jiransa idan kin isa sai ki hana mutuwar zuwa gare shi. Kuma ki jira ni ina nan dawowa gare ki

Yana faɗar haka ya juya ya bude murfin motarsa sai dai kafin ya shiga ya juya ya kalle ta ya ce.

"Kalli yadda kika rame kika yi baƙi kika lalace ba wanda zai gan ki yanzu ya ce wai Ma'eesha Ibrahim Khalil ce ta dawo haka."

Yana gama faɗar haka ya shiga motarsa ya yi ma ta key ya bar ta nan tsaye. Hawaye duk sun gama wanke ma ta fuska.


Hanyar shiga gidan ta nufa ta shiga cikin sanyin jiki. In da ta bar makaho tsaye a nan ta same shi.


_Nadra_

Da mamaki da kuma fargaba take kallon Fahad, Majidaɗi jin ya ce wai a nan za ta kwana.

Tsaye take tana kallonsa yana cin abincin sa hankali kwance.

Duk yunwar da yake kira yana ji bai cinye rabin abincin ba.

"Ka ce anan zan kwana?"

"Eh ko kina da matsala ne?"

"Eh ina da ita."

"Okay meye matsalar?"

"Ba na iya barci tare da wani a kusa da ni."

Dariya ta so ba shi anan sai ya danne. Tsaye ya mike yana cewa .

"Amma ai ke sa Sidra ɗaki ɗaya kuke kwana ko?"

"To ai ita Yayata ce."

"To ni ma ai mijinki ne?"

Cike da yarinta ta ce.

"To ai kai ba wai mijina ba ne, ka ga ka ce wai za ka rabu da ni ya Sayyadi ya aure ni tun da ba ka sona shi kuma yana so na. "

"Idan kika sake kira mani sunan wannan mutumin ba?"

"To ka yi hakuri."

"Okay na ji zancen rabuwa da na ce ma ki za mu yi lokaci nake jira."

Kafin ta yi magana ma ya ce.

"Ki ɗauke kayan nan ki kai kitchen, ki dawo da shirin barci ina jiran ki"

Tura baki ta yi ta ɗauki kayan ta fice daga ɗakin

Tana ajiye kayan kitchen da sauri ta nufi ɗakinta ta saka key ta mirza ta ciki . Ita kaɗai take magana a zuciyarta.

'Tab ai na gane nufinsa wato ya ce baya so na kuma zai sake ni ne nan gaba na je na auri Ya Sayyadina. Amma shi ne zai ce na je na kwana ɗakinsa ya yi Mani wayau ya kwashe albarkatun jikina sannan ya sake ni lokacin da zama fanko sannan zai bar wa Ya Sayyadi fanko, to ta Allah ba taka ba, masoyina mai so na tsakani da Allah ne kadai zai samu budurcina ba kai...'

Maganar ce ta maƙale sakamakon jin ƙamshinsa da ta yi, gane gabanta ya faɗi ta juya ta kalli ƙofar.

Tsaye ta gansa yana ma ta wani kallo da ta kasa gane ko na mene ne.

Yana kallon ta yana kuma kokarin hana zuciyarsa shin da take so, don tabbas tun da ya lyalle ta ɗaure da towel gabɗaya kansa kwance a kanta. Matsanancin sha'awarta yake yi, sai dai yana kokarin hana kansa zuwa gare ta. Musamman da ya san cewa ba ya jin son ta a ransa, kuma idan har ya ya aikata wani abu da ita raina shi za ta yi, don kallon ƙaranar yarinya yake yi ma ta, a ganinsa raini ne zai ja wa kansa kuma yana ganin ya fi karfin haka nan a wajen ta yana ganin ba ta da ajin da zai haɗa jikinsa da nata.

Tsuki ya ja cike da takaici ya harare ta sannan ya fice daga ɗakin.

Ganin haka ya saka Nadra ta yi Murmushi tare da cewa.

"Alhamdulillah na ji dadin wannan girman kai da ji da kai da kake da shi. Ya gani yana so amma Jin kansa da mishkilanci ya hana shi ya nuna, hakan ya Mani kyau kai kuma ya yi ma ka muni."

Haka ta kwana zuciyarta fara tas.


_Sidra_

Karamar door din gate ɗin ta ƙwanƙwasa, security dake bakin gate ɗin gidan ya duba agogo ya ga karfe ɗayan dare.

Don haka daga cikin ya ce.

"Waye?"

Ta waje ta ce

"Ni ce."

"Kece wa?"

"Ni ce Sidra matar da Fahad na gidan nan zai aura."

"Tofa yallaɓai da ya yi aure abin sa."

"Eh ƙanwata ya aura."

"To ai ba nan ya zauna da ita ba ki je gidansa ma na."

"Wajen mahaifinsa na zo, ka ce ma sa wai Sidra Abdullahi Maitama ce ta zo wajensa."

"Gaskiya yanzu dare ya yi Alhaji na barci ba zai yiwu na tayar da shi ba."

"Don Allah ka taimake ni ka sanar da shi ba zan iya kwana a haka ba ga ni a waje wani abu zai iya samu na, ba ni da in da zan je."

Daidai lokacin ne wayar security ya yi ringing, ya duba ya ga maigidan ne, ya dauka cikin girmamawa ya ce .

"Barka da dare yallaɓai."

"Ka bude ma ta gate ta shigo ciki."

Abun da Alhaji ya faɗa kenan sanan ya lashe kiran wayar.

Dama lokacin Alhaji Umar Majidaɗi bai yi barci ba, ya gama duba wasu document kenan yana shirin kwanciya ya duba CCTV camera ya ga Sidra tana tsaye jikin gate ga trolly ɗin ta a gefenta tana magana da maigadi.

Duk da ba wai ya gane ko wace ce ba amma tabbas ya san cewa ya san fuskar yarinyar ya taɓa ganinta amma ba zai tuna ina ba ne ya san ta.

Bayan ya ba security damar shigowa da ita ne ya juya ya kalli kan gadonsa da Mama ke barci.

A hankali ya kira sunanta yana shafa fuskarta. Bude idanunta ta yi a kansa ta ce .

"Alhaji lafiya kuwa?"

"Ki je ki bude main door akwai yarinyar da ta zo yanzu, tana tare da trolly me yiwuwa daga wani gari take dare ya ma ta a hanya."

"Wace ce ita?"

"Ba zan iya tuna wace ce ba amma na san za ki gane ta ke, mu tafi tare."

Shiru Mama ta yi kafin ta sauko daga kan gadon ta saya hijabi suka fita shi kuma Bana yana sanye da jallabiya a jikinsa.


Bayan security ya ba wa Sidra damar shigowa ta shigo tana kalle-kallen don gidan ko ina fitilu ne.

Main door ta nufa tana tsaye tana shakkar yadda za ta buga ma su kofa, sai ta ga an bude kofar. Baba da Mama ta gani tsaye suna kallonta.

Durƙusawa ta yi tana kuka yayin da Mama ta ce.

"Sidra?"

Sai a lokacin Baba ya gane ta .

Cikin kuka ta ce.

"Baba dan Allah ka taimake ni Abba ya kore ni, ƴan uwansa na sun kore ni ba na da wajen zuwa, dan Allah ka taimake ni ka ba shi hakuri ya yafe ma ni na koma gida."

Shiru Baba ya yi kafin ya ce.

Yanzu ransa a ɓace yake akan abin da kika aikata , ba zai saurare kowa ba, don haka ki zauna a nan zuwa wani sati idan na dawo daga ƙasar Germany zan je na roƙe shi ya yafe ma ki."

"Na gode Baba Allah ya saka da alheri. "

"Amin ya Allah, gobe da safe zan bar kasar idan na dawo sai kin fada mani in da kika je da kuma dalilin da ya sa kika tafi kafin na je na roƙe shi."

Kallon Mama ya yi tare da cewa.

"Hajiya a kai ta ɗakin baƙi a ba ta abinci ta ci ta kwanta."

"To Alhaji "

Mama ta fada tana cewa Sidra.

"Tashi mu tafi."

Baba ya nufi part ɗin sa yayin da Mama ta yi wa Sidra jagora zuwa daya daga cikin ɗakunan da suke saukar baƙi.

Daki ne wanda aka komai da komai na buƙata gado wardrobe mirror T.V da fridge. Ga toilet a ciki.

Mama ta kalli Sidra ta ce.

"Nan za ki zauna, bari na kawo ma ki abinci."

Daga haka ta fita don zuwa kitchen, ruwan semovita ya rage a cikin kula kuma tuwon da zafi da da miyar egusi da ya ji nama da ganda.

Kawo wa Sidra ta yi sannan ya ce .

"Akwai ruwa da lemu a fridge, don dama an zuba komai saboda baƙi da suka wuce yau."

Godiya Sidra ta ya wa Mama sannan mama ta fita.

Dama yunwa take ji ta buɗe fridge ta dauki bottle water da lemu ta wanke hannu ta ci tuwo.

Bayan ta gama ne ta ajiye kayan q gefe ta shiga bathroom ta yi wanka. Ta fita ta sanya kayan barci ta kwanta.


*Washegari*

Bayan Nadra ta gama aikin gyaran gidan da ta saba yi ya rage ɗakin Fahad ya rage ta gyara.

Kitchen ta nufa don ɗora breakfast sai ta ji alamar tafiyar mutum.

Tana juyawa ta gan shi yana fitowa ɗakinsa hannunsa rike da waya yana cewa.

"Ka yi hakuri Baba na macen yau ne tafiyar ta ka, da na kawo ma ka ita ka ganta. Amma duk da haka akwai sauran lokaci bari mu zo yanzu sai ta gaishe ka kafin ka tafi."

Daga nan ya katse wayar ya karasa kitchen ɗin .

Yana tsaye bakin kofar kitchen ɗin ta juyo suka hada idanu ya kalle ta daga sama har ƙasa. Kuma lokacin ma hijabi ne a jikinta.

Durƙusawa ta yi ta gaishe shi cikin girmamawa.

Bai amsa ba ya basar da ita. Cigaba ta yi da kokarin wanke tukunya za ta kunna gas ya ce .

"Ki je ki shirya za mu je ki gaida Baba zai yi tafiya da safen nan."

"To."

Ta ce tana ajiye tukunyar ya fito ita ma ta bi bayansa.

Ɗakinsa ya nufa ita ma ta nufi ɗakinta.

Rigar Abaya ta saka kasancewar kayan lefen ba hijabi ko ɗaya, kasancewar Sidra ba ta saka hijabi.

Ita kuma hijabin da ta zo da shi dama guda ɗaya ne na jikinta da ta zo da shi. Don ko kayan gidan iyaye Sidra ba ta ɗauki hijabi ba.

Ganin babu hijab ya saka Nadra ba ta da wani zaɓi saka Abaya mai ruwan ƙasa ta yi rolling kanta da mayafin abayar.

Ba ta yi kwalliya ba powder kawai ta shafa sai lips glow ta yi kyau ta fito kamar baƙar balarabiya.

Handbag ɗin ta ta dauka ta saka wayarta a ciki da wasu ƴan kuɗaɗe cikin na sadakinta ne ta ɗauka.ta zo wajen ɗaukar takalma, sai dai duk takalmomin zaɓin Sidra ce don dogaye ne ma su tsini, wanda ita kuma Nadra ba ta iya tafiya da dogon takalmin ba.

Tana tsaye tana neman mafita ya shigo ɗakin, kallonta ya yi ganin ta shiga har handbag ta dauka ya ce.

"Me kike jira?"

"Takalmin da zan saka nake nema. Ƙarasowa ya yi ya kalli takalmomi da ke wajen da sun kai kala goma sha biyar ya ce.

Duk takalmin da suke nan ba wanda ya ya ma ki, sun yi amma suna da tsini ba zan iya tafiya da su ba."

Hannu ya saka ya ɗauki wani bakin takalma ya ajiye q gabanta.

"Ki koyi tafiya da su daga yau."

Za ta yi magana ya wurga ma ta wani kallo wanda ya saka dole ta yi shiru ta saka haka nan, tafiya ta fara yi kamar mai tausayin ƙasa.

Ya yi gaba tana binsa a baya suka fice .

Har ya suka fito ya rufe kofar gidan yana zaune cikin motar yana jiranta ta karaso tana tafiya kamar mai yanga.

Yana zaune a mazaunin direba ta shiga ta zauna gefensa.

Ba tare da wani ya yi magana cikin su ba ya yi wa motar key suka bar gidan.


*Mamman Ihsan ce*✍️

09065327995

Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z


*MAKAHO NE*


*NA*

Maman Ihsan ce ✍️


https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️


page3️⃣4️⃣

Ba tare da wani ya yi magana cikinsu ba ya yi wa motar key suka bar gidan.

Driving yake yi cikin nutsuwa yana kallon hanya, har suka ƙarasa gidan bai ce uffan ba, haka ita ma ba ta ba har suka ƙarasa bakin tangamemen gate ɗin gidan.

Horn ya yi security ya zo ya wangale ma sa gate ɗin gidan, ya shiga ya yi parking lot.

Kusan a tare suka fito daga cikin motar, ma'aikatan gidan da suke nan suka fara gaishe su, Fahad ɗin kam bai amsa ba ita Nadra ce take amsawa cikin girmamawa kasancewar ta ga duk sun girme ta.

Tafiya take yi a hankali sakamakon takalmin da ba ta saba amfani da irin su ba.

Ƙararrawar ƙofar ta danna, sai ga ɗaya daga cikin masu aikin gidan ta zo ta buɗe ma su ƙofar.

Ganin Fahad da Nadra ya saka ta gane cewa ita ce Amaryarsa.

"Sannu da zuwa yallaɓai ."

Bai amsa ba sai kokarin shiga ciki yake yi, ganin bai amsa ba kuma dama sun saba da halinsa. Cikin sakin fuska ta gaida Nadra.

"Sannu da zuwa Aunty."

Murmushi Nadra ta sakar ma ta tare da cewa.

"Yauwa Barka da safiya ya kike?"

"Alhamdulillah."
Chapter 5 · 0% Book details