Part ɗin Baba ya nufa in da Mama ma ta ja hannun Nadra suka nufi part ɗin. Nan Baba ya yi masu nasiha sosai Nadra na kuka tana jinjina kai.
Makaho Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 342 min read
Shi dai Fahad bai ce komai ba kansa a ƙasa.
Bayan Baba ya gama ne Mama ma ta ɗaura da nata, Inna ma ta shigo ta ɗaura da nata nasihar.
Sallamar su aka yi kasancewar zuwa lokacin ina shirin kiran sallar Magrib ne.
Suna fitowa falo suka tarar da Aunty Rahama da Rumaisa, sai Farida wacce ita ma ba walwala a tare da ita. Ita kuma Sidra fitowar ta kenan saboda kada a yi tunanin halin da take ciki ya sa ta danne zuciyarta ta fito don yin sallama da ƙanwarta .
Nadra na hawaye ta yi ma su sallama, har Aunty Rahama na ma ta dariya tana cewa.
"Wai kuka sai ka ce amaryar da aka ɗaurawa aure yau."
Rungume Sidra ta yi tana cewa
"Aunty..."
Sauran maganar ta kasa furta wa kuka ya ci ƙarfinta. Sai da Sidra ta yi yaƙi da zuciyarta sanan ta ƙaƙaro murmushin yaƙe tana bubbuga bayan Nadra. Don idan ta ce za ta yi magana to asirin zuciyarta ce za ta tonu.
Da kyar Aunty Rahama ta ɓanɓare Nadra daga jikin Sidra.
Fita suka yi aka yi ma ta tsakiya har wajen motar, Farida ce kawai ba ta motsa daga ina da take ba.
Direba na gaba Fahad na zaune a bayan motar, Aunty Rahama ta bude ma ta bayan motar ta zauna gefensa. Idanun Sidra na kan Fahad ta zuba ma sa idanu.
Shi kuma idanunsa na kan wayarsa da yake sarrafa ta ta cike da ƙwarewa.
Direba ya ja motar suka bar gidan.
Sanyin AC da ƙamshi ne ke tashi a cikin motar, sai kuma sheshsheƙar kukanta.
Yana jin kukan har a cikin ransa ya fahimci yadda take ji, amma jin kansa da mishkilancinsa ya sa shi ya basar da ita kamar bai san tana yi ba.
Ji ya yi kukan na hawa ma sa kai, daidai ana kiran sallar Magrib.
Umarnin tsaida motar ya ba direban, bayan ya yi parking motar ne ya ce wa direban ya fita su yi sallah. Ya yi maganar yana fita. Direban ma fita suka bar ta a cikin motar.
Ruwa suka ɗauka suka yi alwala, daidai za'a tayar da sallah suka shiga jam'i aka yi sallar tare da su.
Sai da suka idar da sallar sannan suka fito zuwa lokacin kanta har yana ciwo sosai yake sara ma ta. Don haka ta dakatar da kukan da take yi sai dai sheshsheƙa take yi.
Har suka ƙarasa kofar gidan tana ajiyar zuciya. Horn horn direban ya yi maigadi ya wangale ma su gate suka shiga.a parking space ya yi parking motar.
Sannan ya zagayo yana buɗe wa Fahad bayan motar ya fito. Sannan ya zagayo ya buɗe wa Ma'eesha.
Ma'aikatan gidan suka ƙaraso suna yi ma su Barka da dawowa. Fahad ne ya amsa Nadra tuni ta nufi hanyar shiga ciki.
Tana tura kofar ta ji a rufe, don haka ta tsaya ta jingina da bango kanta na sara mata idsnunta a rufe.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce✍️
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page5️⃣4️⃣
Tana tura ƙofar ta ji a rufe, don haka ta tsaya ta jingina da bango kanta na sara mata idanunta a rufe.
Karasowa ya yi ya bude ƙofar dama jira take yi don haka ta faɗa cikin falon.
Hijabinta kawai ta cire ba ta karasa upstairs ba ta tsaya a downstairs ta yi amfani da toilet dake cikin falon
Alwala ta ɗauro sannan ta fito ta sanya hijabinta a nan ta ɗauki sallaya ta shimfida. Kasancewar ko ina fesa yake an gyara .
Tana isar da sallar ta kwanta a nan saman sallaya.
_Makaho_
Bayan ya gana waya da Ma'eesha ya shawo kanta ta hakura da zancen ya dawo gida ya ci abincin rana. Abokinsa Khalid na ma sa kallon Mamaki kafin ya bude baki ya ce.
"Jalaluddeen."
Ba tare da ya kalle shi ba ya ɗaga ma sa gira ɗaya alamar ya aka yi.
"Kai da wa kake waya?"
"Ba ruwan ka da ita?"
"Yaushe muka fara ɓoyewa juna sirrin junan mu ne?"
"Da Ma'eesha nake waya."
"Wace ce ita na ji tana kiran ka da mijina?"
"Au hakan da ja ji bai zana ma ka alaman cewa Matata ba ce ita ?"
"Jalaluddeen ka san me kake faɗa kuwa? Na ɗauka bincike da aikin sirri ya kawo ka garin nan sai ka ɓige da aure? To ya za ka yi da Yasmeen da ka bari tana can tana zaman jiran ka?"
Bai tanka ma sa ba ya yi kamar bai ji shi ba. Ya cigaba da cewa.
Iyayenka sun san cewa ka yi aure a nan?"
"Ba wanda ya sani."
"Okay ina fatan ka aure ta ne iya na tsawon zaman da za ka yi a garin nan, da zaran ka kammala aikin ka za ka sake ta ka koma ga Yasmeen ko?"
"Na san ba abin da ya kawo ka kenan ba, so ka yi abinda ya kawo ka ka tafi ina da abun yi."
Mamaki da takaici ya cika zuciyar Khalid, wai aure ba tare da sanin kowa ba.
Tashi ya yi ya fice ba tare da ya sake kallon in da yake ba.
*WAYE MAKAHO?*
Jalaluddeen Kabir Arzika shine cikakken sunansa. Sunan mahaifinsa Alhaji Kabir Arzika (Dad) sunan mahaifiryasa Hajiya Fatima, (Mom)Suna zaune ne a garin Abuja. Alhaji Kabir Arzika baban ɗan kasuwa ne da yana da kamfanonin da suke sarrafa kayayyaki ana fitar da su waje. Mahaifiyarsa Hajiya Fatima kuma Babbar likita ce tana da babban asibitin nata na kanta mai suna *Jasad international hospital* Jamaluddeen shi ne babban Ɗan su da suka haifa. Lokacin da suka haifi Jalaluddeen yana da shekara ɗaya ɗaya mahaifiyarsa ta samu wani cikin da ke matuƙar ba ta wahala tana laulayi sosai wanda ba ta iya komai sai an yi ma ta. Wannan dalilin ya sa ƙanwar Alhaji Kabir mai suna Maryam wacce ake cewa (Ummee) wacce dama shekaru biyar da aurenta ba ta taɓa haihuwa ba ta ɗauki Jalaluddeen ta yaye shi a wajenta ta rike shi kamar Ɗanta. Yayin da Dad ke cigaba da kula da Mom. Jalaluddeen yana wajen ƙanwar Mahaifinsa.
Lokacin da Jalaluddeen ya cika shekaru biyu aka saka shi a makaranta. Lokacin Mom dinsa ta haifi cikin da yake saka ta wahala, ta haifi Ɗa namiji sunan sa Sadik. Har Mom ta haifi Sadik Jalaluddeen na wajen ƙanwar Dad ba ta dawo da shi wajan mahaifiyarsa ba. Sai dai su je ziyara tare da Ummeensa su gaida Mom da Dad su dawo.
Har Allah ya ba Ummee ciki ta haifi Ɗa namiji ranar suna yaro ya ci suna Yusuf.Ta haɗa su ta rene su tare ba ta taɓa banbanta su hasali ma soyayyar da take yi wa Jalaluddeen ya fi son da take yi wa Yusuf yawa. Allah ya jarebe ta da ƙuanar Jalaluddeen tun da aka haife shi, ballantana da yanzu yake hannunta sai ƙaunar ra ƙaru. Kusan lokaci ɗaya Mom da Ummee suka sake haihuwa, Mom ta haifi Sadiƙa da sati biyu Ummee ta haifi Yasmeen.

Har Allah ya ba Ummee ciki ta haifi Ɗa namiji ranar suna yaro ya ci suna Yusuf.Ta haɗa su ta rene su tare ba ta taɓa banbanta su hasali ma soyayyar da take yi wa Jalaluddeen ya fi son da take yi wa Yusuf. Ko mihin Ummee wato Abbee yana ji da Jalaluddeen kamar shi ya haife shi. yawa. Allah ya jarebe ta da ƙuanar Jalaluddeen tun da aka haife shi, ballantana da yanzu yake hannunta sai ƙaunar ra ƙaru. Kusan lokaci ɗaya Mom da Ummee suka sake haihuwa, Mom ta haifi Sadiƙa da sati biyu Ummee ta haifi Yasmeen.
Haka rayuwa ke tafiya Mom na kula da Asibitin ta, Ummee na na zuwa ƙasashe irin su Dubai China tana kasuwancin ta.
Haka rayuwa take ta tafiya Jalaluddeen, Sadik, Yusuf da a ƙasashen waje suka yi karatu har master digri yayin da matan kuma Yasmeen da Saddiƙa suka yi karatun su a nan gida Nigeria don iyayen sun ce ba su yarda ƴa mace su tura ta wata uwa duniya ta yi karatu ba.
A yanzu haka kowa na aiki a cikinsu Jalaluddeen yana aiki a Department of state services(DSS) yana rike da baban muƙami na Senior intelligence officer. Yayin da Sadik kuma Doctor ne yana aiki a asibitin mahaifiyarsu (Jasad international hospital) Yusuf kuma Lauya ne mai zaman kansa. Saddiƙa da Yasmeen kuma yanzu suke karatun Master digiri.
Jalaluddeen wanda aka fi sani da Makaho shi ne Senior intelligence officer a hukumar DSS . Yana jagorantan manyan bincike, yana da iko kan wasu jami'ai, ana ba shi muhimmin missions, albashinsa da alawus suna da yawa sosai . Kuma shi ke jagorantar ayukkan kama criminals, yana shiga aiki da kansa ba dole sai a office ba. Yana da horo na musamman (Fightings spaying tactics) Yana samun kudi sosai sirrin alawus. Ƙwararre ne wajan shiga mutane ya yi mu'amala da su ba tare da an gane shi ba. Yana canza rayuwa a duk yadda ya so yana rayuwa kamar talaka sai yadda ya so, yana samun kudi sosai saboda shiga haɗarin aiki da yake. Yana da allowance na sirri, kuma yana samun lada daga manya missions. Babban jami'i ne yana shiga hatsari da kansa.
Yana daya daga cikin manyan jami'an Department of state services field operations commander da aka fi yarda da shi wajen aikin sirri.
Yana da shugabanni guda biyu da ke sama da shi.
Director General (DG)
Sai kuma Deputy Director su ne manyan shugabanni a sassa daban-daban.
Aikin da ya kawo shi garin Kaduna ba wani binciken wani Attajirin mutum ne wanda yake safarar makamai, yana shigo da bindigogi a ɓoye yana siyar wa ƴan ta'adda Sunan mutumin Alhaji Mamman Daula) yana taimakawa talakawa ana ganin girmansa, amma ba wanda ya san cewa yana safarar makamai. Wannan dalilin ne ya sa Jalaluddeen ya zo garin Kaduna ya yi ɓadda kama a matsayin makaho kuma mai gyaran takalmi. Gidan Alhaji Mamman Daula na kusa da in da makaho ke gyaran takalmi yana kula da duk wani shige da ficensa yana hada rahoto.

Page 5️⃣5️⃣
Gidan Alhaji Mamman Daula na kusa kusa da in da makaho ke gyaran takalmi, yana kula da kula da duk wani shiga da ficensa yana haɗa rahoto.
Wata rana wajan bin bayan daya daga cikin yaran Daula ne ya ga ana ƙoƙarin Illata Mummy mahaifiyar Ma'eesha, wanan dalilin ya sa ya fasa yin abun da ya kai shi ya taimaki rayuwar Mummy ta dauke shi a motarta har zuwa gidanta.
Shi ya sa ko da Mummy ta ce ma sa ya dinga zuwa yana karbar abinci ba saboda komai yake zuwa ba sai dan yana sa idanun ya ga ko ana bibiyar rayuwar ta ne ya ba ta kariya. A cikin lokacin kuma Allah ya yi ma ta rasuwa. Mamy ta sa Daddy ya ba shi auren Ma'eesha don rayuwarta ta tagayyara ba tare da ta san ko waye shi ba.
_Nadra_
Tana nan kwance a wajen saman sallaya har aka kira sallar Isha'i sannan ta tashi ta gabatar da sallar Isha'i.
Har lokacin tana jin ciwon kai sai dai karfin halin da take yi.
Tana idar da sallar Isha'i nan ta sake kwanciya kan sallayar, ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita.
Shi kam ko da ta dawo daga masallaci salar Isha'i nan ya gan ta kwance a saman sallaya tana barci.
Tunawa da ya yi ba ta ci abinci ba ya sa ya ɗauki key din motarsa ya fice daga gidan.
Gasashshiyar kaza ya siyo ya dawo gidan, bayan ya yi parking ɗin motar ya fito hannunsa rike da ledar kazar.
Bayan ya huta kofar falon ya shiga ne ya rufe ƙofar.
Upstairs ya haura da ledar ya ajiye a dinning table.
Ya buɗe fridge ya ciro yoghurt a fridge ya ajiye a dinning table.
Downstairs ya sauka ya karasa in da take kwance a saman sallaya. Durƙusawa ya yi ya daga ya cak ya haura sama da ita .
Yana tsaka da taka step ɗin ta farka.
A hankali ta bude idanunta shi kansa ya ji jikinta da zafi, tsuke fuska ta yi tana cewa.
"Ka sauke ni"
Bai saurare ta ba sai da ya kai falonsu da ke upstairs.
Akan kujera ya dire ta ganin yadda ta tsuke ma sa fuska shi ma ya murtuke fuska ba wasa ya ce.
"Tashi ki je ki yi wanka ki fito ki ci abinci ki sha magani."
"Ni na ƙoshi kuma ba abinda ke damuna da zan sha magani ai."
Ta yi maganar a tsiwace,
Kallonta yake yi don bai taɓa tunanin tana da bakin tsiwa ba, don ba ta taɓa yi a gabansa ya gani ba. Cikin bayar da umarni ya ce.
"Umarni na ba ki ki yi abun da na ce, idan kuma kika ƙi yi to fa ki sani zan shigo na ɗauko ki da kaina ne."
Yana faɗar haka ya zauna a saman sofa yana ɗaukar wayrsa dake saman Centre table.
S hankali ta tashi ta fara tafiya cikin sanyin jiki, idanunsa na kan waya, amma sam ba wayar yake kallo ba har yanzu idanunsa na kanta, a hankali take tafiya har ta shige.
Yana sake mamakin yadda fatarta ta washe ta yi haske kuma ba na bilicin ba, ga fatarta sai ƙyalli da sheƙi take yi, ga wani sihirtaccen kyau da ya ga tana da shi wanda a baya sam bai gani ba.
Cusa hannunsa ya yi cikin gashin kansa yana yamutsawa.
*Abuja*
_Ummee_
Sunan barin gidan ita da Jimoh wanda ke driving ba tare ta ya san in da suka nufa ba ya ce.
"Madam ina za mu je?"
Ba ta ma ji shi ba, hankalin ta na jan photon Makaho da Ma'eesha in da z su je asibiti da inda zasu je siyen waya tana rike da hannunsa, sai na ukun ranar da suka fita siyen Abu a cikin unguwar nan ma tana rike da hannunsa, fuskarta ɗauke da murmushi wanda ya kara bayyana tsantsan kyawunta.
"Madam ina za mu je?"
"Ya sake maimaita wa yana kallonta ta cikin madubin dake jikin motar
"Gidan Yayana."
Ta yi maganar tana ajiye wayar saman cinyarta.
"Yanzu akan kana bibiyar sa shi ne ya yi maka shaƙar mutuwa?"
",Eh Madam dama da suka shiga asibiti ne na tsaya suka fito, bai juya ba amma wai ya san ina bin sa, shi ne ya tare na nape ya sa yarinyar ta shiga, bayan sun wuce ya juyo kaina.
Jinjina kai ta yi tana cewa.
"Ina mamakin yadda Jalaluddeen ya canza, wanda ko baya garin kullum sai mun yi waya duk yawan da wahalar aikinsa, amma wannan karon sai ya yi sati bai kira ni ba, kuma idan na kira wayar ba ta shiga. Na san hakan na da alaƙa da wannan yarinyar ne.
Jinjina kai ta yi ba ta sake magana ba har suka isa gidan Alhaji Kabir Arzika.
Horn motarsu ta yi, sai da security ya leƙo ta karamar kofar, ya tabbatar da su waye kafin ya bude ma su gate ɗin gidan.
Shigar su kafin su kai parking lot ta sa Jimoh ya yi parking motar a harabar gidan.
Fitowa ta yi a cikin motar yayin da ma'aikatan gidan ke gaishe ta, ta amsa ma su sama-sama saboda ranta a ɓace yake.
Jimoh ya zauna cikin motar yana jiran fitowarta.
Door bell ta shiga dannawa ba kakkautawa, cikin ma'aikatan da suke aiki a falon ta nufi ƙofar ta buɗe da sauri, don daga jin yadda aka danna ƙararrawar ƙofar sun san ba na lafiya be ne, zubawa suka yi suna gaishe ta, ba ta ama sa sai dai ta tamabaye su da.
"Dr ta tafi asibiti ko tana ciki?"
"Tana ciki."
Suka amsa ma ta a tare.
Kai tsaye ta nufi part ɗin Mom, bakin kofar ta yi knocking.
Mom tana sauri za ta je asibiti sakamakon ana bukatar ta a asibitin cikin gaggawa.
"Waye?"
"Ni ce."
Ummee ta faɗa cikin ɗaga murya.
Mom cikin mamaki ta ce .
"Hajiya Maryam da safiyar nan? Bismillah shigo."
Ta faɗa daidai lokacin da take saka wayoyinta a cikin handbag.
After dress ta saka saman kayan dake jikinta.
"Assalamu alaikum."
"Wa'alaiki Salam warahmatullah. Hajiya Maryam ke ce da safiyar nan?"
"Eh."
"Allah ya sa lafiya."
"Ina fa lafiya dama ina tafe ne jan zancen Jalaluddeen."
Sai da gaban Mom ya fadi don ta ɗauka wani abu ne ya faru da Ɗan nata ma fi soyuwa a zuciyarta. Dan duk da ba ita ta reni Jalaluddeen ba ba a hannunta ya tashi ba amma ta fi jin soyayyarsa fiye da Sadik da Sadiƙa, ko don yana Ɗan ta na fari ne oho.
"Me ya faru da Jalaluddeen din."
Ta faɗa cike da fargaba kasancewar ta san yanayin aikinsa yana da hatsari.
"Ba abinda ya faru da shi."
Ɓoyayyen ajiyar zuciya ta sauke.
"Tun da yake bai taɓa tsallake kwana ɗaya bai kira ni ba, amma yanzu sai ya yi sati kafin ya kira ni, kuma ko na kira wayrsa ba ta shiga, kuma na san kowane aiki ya tafi ina jin motsin sa, hankalina ya tashi na sa a je garin da yake a bincika ma ni ko yana lafiya, sakamako binciken da aka yi ma ni yana tare da wata yarinya ce a taƙauce ma gida ɗaya yake kwana da yarinyar gidan ma ɗaki daya rak a cikin gidan, wanda ba za'a kira shi gida ba sai dai kango. Kullum yana tare da ya yarinyar suna yawo hannunsa sarƙe cikin na juna suna yawo a gari."
Shiru Mom ta yi kafin ta ce .
"Why ki yi magana da shi ya yi ma ki bayanin komai, duk da na san ba zai aikata wani abun da ba daidai ba."
"Wani magana bayan na faɗa ma ki tsawon sati ba na samun wayarsa, amma ke na san kullun yana kiran wayarki."
Wani kallo Mom ta yi na ta kafin ta ce.
",Wa ya faɗa ma ki kullum yana kiran wayata."
"Ai ba sai an faɗa ma ni ba, tun ranar da ya gane cewa ke ce mahaifiyarsa ba ni ce na haife shi ba ya fara rawar ƙafa akanki komai sai ya ambaci sunanki ni ya rage..."
Dakatar da ita Mom ta yi ta hanyar ɗaga ma ta hannu,.
"Dakata Hajiya Maryam, kar ki soma kawo wani zancen da bai da tushe, har kina zargin kullun sai ya kira ni a waya? Ko kuma kina son ki ce ma ni tun da ya gane ni ce uwarsa yake ƙaunata ko me? To ke idan sati yake yi ya kira ki a waya ni yau kwana goma kenan bai kira wayata ba, na yi ma sa uzurin yanayin aikin da yake yi ne ya sa haka, zanen cewa ta gane ni ce na haife shi yana so na ba ta taso ba. Dan har yanzu irin alkawar da yake ma ni na matar kawunsa haka yake ma ni ban ga abun da ya sauya ba, sai dai a cikin zuciyarsa. Don haka daga ranar da kika ɗauki Jalaluddeen kika tafi da shi na bar ma ki shi na yi addu'ar cikin da nake da shi Allah ya sauke ni lafiya. Na bar ma ki shi a lokacin ne saboda na ga Allah bai ba ki haihuwa ba, ni kuma yana ɗan shekara ɗaya na samu wani cikin. Hatta dangina na sanar da su cewa na bar ma ki Jalaluddeen har abada kada su saka shi a lissafin dangi kuma kada wanda ya sanar da shi ni na haife shi. Haka aka tafi yana ma ki kallon Mahaifiya yana ma Ni kallon Matar kawunsa. Ban so ya sani ba. Har wata rana ya zo gaishe da Alhaji da ya yi rashin lafiya ya tarar da ƴar ƙanwata ya fara son ta suka fara soyayya, na yi farin ciki da haka amma sai kika nuna ba ki son haɗin ya rabu da ita, ni ma na ce ya rabu da ita tun da mahaifiyarsa ba ta so haka ya hakura da ita. Kina bijiro ma sa da zancen za ki haɗa su aure da Yasmeen yarinyar da kika haifa da cikinki, hankalinsa ya tashi domin ya dauka uwa daya uba ɗaya suke, ke ce kika sanar da shi ba kece mahaifiyar sa ba wanda a lokacin ya san ni na haife shi. Ya amince da auren Yasmeen ko da kika sanar da ni addu'ar fatan alkhairi na yi ma ki, ban taɓa ce ma ki komai ba duk hukuncin da kike zartarwa akan Jalaluddeen ba na damuwa Ɗan ki ne kuma yana ma ki biyayya irin ta uwa, bai saba da ni kamar yadda ya saba da ke ba, bai gama sanin dangina ba ko ya zo gidan nan a matsayin baƙo yake zuwa ya gaishe mu ya ba tafi, don haka ki daina zargin na san komai da yake aikatawa ba abun da nasa ni ki nar ni na ji da abun da ke gabana, marasa lafiya na jira na a asibiti."
Cikin ɓacin rai Ummee ta ce .
"Ba zan taɓa yarda da wannan zancen naki ba, duk abinda Jalaluddeen yake aikatawa kin sani, don tun da ya gane kece uwarsa ya canza ma ni yanzu da a baya ne ba zai iya kwana bai ji murya ta ba. Yanzu ya daina jin magana ta, da yana jin magana ta da ba zai saka ƙafa ya bar garin nan ba tare da an yi bikinsu ba, ga shi yanzu da an yi bukin tun last month tun da an gama shirin komai, ya tafi na tsawon watanni ya fifita aikinsa akan aure."
Ta karasa maganar ta na fice wa daga ɗakin.
Mom dafe goshi ta yi tana zama bakin gadon.
Ummee tana fita falo ta hadu da Dad yana saukowa. Dama Yaya kana ciki .
Kallon ƙanwar tasa ya yi yana murmushi
"Eh ina ciki Maryam,.lafiya dai ko?"
"Ba lafiya ba gaskiya."
"Subhanallah me ya faru?"
"Gabadaya Jalaluddeen ya canza, ka duba ana saura wata ɗaya aurensa ya bar garin nan ya ce nan da sati Uku zai dawo, sati Uku shiru wata wata uku shiru har yanzu ba ba wanda ya san me yake yi.A taƙaice ma tare da wata mace yake a can."
"Kin ga Maryam ki kwantar da hankalinki, har ya gama aikin da ya je yi ne sai kuma ya sa kansa wani aikin, idan ya kammala zai dawo. Duk satin da ya dawo a satin za'a ɗaura ma sa aure in sha Allah. Mace da kika ce kuma watakila tana taimaka masa ne wajen gudanar da aiki."
Za ta yi wata ƙorafin ya ɗaga ma ta hannu don ya san halin ƙanwar tasa ba ta raina abun magana, kafin ya ce.
"Ɗan ki yana jagorantan manyan jami'ai, tsara yadda za'a gudanar da bincike ko leƙen asiri, tattara da nazarin bayanan sirri. Bayar da rahoto ga manyan shugabanni, taimaka wa wajan tsara tsaron ƙasa. Shugabannin sa na son sa saboda kaifin basirarsa da hangen nesa, sirri da juriya, jarumtaka da riƙon amana. Ƙwarewar nazari da yanke shawara."
Ɗan ki ba gamagarin mutum ba ne, ba za ki samu lokacinsa a daidai wanann lokacin ba, ki yi ta yi ma sa addu'a Allah ya kare shi a duk in da yake."
"Amma har da matarka ba ta san halin da yake ciki ba take ɓoye ma ni?"
"Maryam kada ki kawo wanan a ranki, domin kuwa Dr ta yi ma ki kawaici da sadaukarwa, shin ta taɓa nuna ma ki wata alama da ke nuna ita ta haifa Jalaluddeen?"
Kai ta girgiza alamar a'a.
" Ko ta taɓa nuna tana da iko akan Jalaluddeen?"
Nan ma kai ta girgiza alamar a'a.
Gajeren murmushi ya yi kafin ya ce.
"Ko kin san cewa lokacin da Jalaluddeen ya haɗu da ƙanwar Dr a gidan nan ya nuna yana son ta ba karamin farin ciki Dr ta yi ba, ganin Ɗan ta zai auri ƴar ƙanwarta . Amma kika nuna iko da isa kika ce bai isa ya aure ta ba kin zaɓa ma sa ƴar ki. Haka ya hakura ya yi ma ki biyayya, Dr ba ta nuna damuwa ba. To me ya sa yanzu kike tuhumar ta a kan lamarin Jalaluddeen bayan ba wata shaƙuwa ce tsakanin su ba, in fact bai fi shekara da sanin cewa Dr ta haife shi ba, wanda bayan sanin bai zo gidan nan sama da sau uku ba."
Shiru Ummee ta yi sannan ta sauke ajiyar zuciya.
"To Yaya ni zan tafi sai anjima."
"Allah ya tsare ki gaida Mutanen gidan."
Daga haka ta fice daga falon in da ta sami Jimoh yana jiranta.
Dad ya nufi ɗakin Mom, da sallama ya shiga, yadda ya ga ta hada tagumi ya san zantukan ƙanwarsa ne suka taɓa ta.
Zama ya yi gefenta ya yana cewa.
"Dr har kin shirya?"
"Eh na shirya."
Ta fada tana kokarin saka farin gilashi a idanunta.
"Ki yi hakuri da abun da Maryam ta yi, kin san ba ta da fahimta ne, amma in sha Allah na san ba wata matsala."
Cikin damuwa ta ce.
"Ni ba ni ce na fitar da sirrin cewa ni ce mahaifiyar Jalaluddeen, ita ta fasa sirrin ta hanyar ba shi auren ƴar ta, ban taɓa saka baki a lamarin da ya shafi Jalaluddeen ba, ita ce take yanke hukunci kan al'amuran shi kame yadda uwa ke yi wa ɗanta. Iyaka ta da shi daga gaisuwa . Sai idan azumi ya zo yake jido ma na kayayyaki na abinci da na sakawa da kyautar kudade, daga nan kuma sai wata shekara. Na san cewa shi yake ɗauke da nauyin gidanta cin su sha da sutura duk a wuyansa yake ya dauke ma su Wannan. Duk shekara sai sun je Umara duka shi ke yi, hatta dangina mijinta da Jalaluddeen yake kallon dangin ubansa ya kai da yawan su Makkah sun sauke farali, dangin ja sun ci moriyar dukiyarsa ne? Duk kawaici da alkunya da nake nunwa ba ta gani har za ta zo tana tuhuma na akan Ɗan da na haifa?"
Dad ya san ranta ne ya ɓaci ɗin idan ba haka ba sama da shekara talatin da uku ba ta kiran Jalaluddeen da Ɗanta .

Page5️⃣6️⃣
Dad ya san ranta ne ya ɓaci dan idan ba haka ba sama da shekara talatin da uku ba ta kiran Jalaluddeen da Ɗanta .
"Ki yi haƙuri Dr "
"Ya wuce amma ka ja wa ƙanwarka kunne."
"In sha Allah hakan ba za ta sake faruwa ba."
A tare suka fito daga ɗakin in da ma'aikatan gidan suka jera breakfast a dinning table.
Ba ta ko kalli dinning area ba ta nufi hanyar fita.
"Dr ki tsaya ki yi breakfast ma na."
"Ba lokaci ana jira na, zan yi a can."
Daga haka ta fice ya raka ta har wurin motarta, da kanta take driving cikin nutsuwa ta bar gidan.
_Makaho_
Yana kammala abun da zai yi da misalin ƙarfe uku da rabi ne ya miƙe tsaye.
Kayan jikinsa ya cire ya saka kayan da ya zo da su a jikinsa. Duka wayoyinsa ya ajiye a nan, ya tafi da guda biyu ƙananu. Ɗaya na amfani domin aikinsa ne ɗaya kuma Wanda yake waya da Ma'eesha ne.
Baƙin gilashinsa ya saka sannan ya saka takalmin soso da zo da su. Ya kashe komai da ke ɗakin sannan ya fito daga ɗakin.
Har lokacin wanann mai nape na zaman jiransa, sai da ya fito ne ya shiga suka bar wajan.
Nesa kaɗan da wajan aikinsa ya ajiye shi, kafin ya fito ya ɗauko sandarsa ya cigaba da dogarawa yana irin tafiyar da yake saba yi.
Wajen sana'arsa ya ƙaraso da sallama, suka amsa ma sa, Bello me yalo yana yi ma sa sannu da dawowa kafin ya ce.
"Na ga ka daɗe lafiya dai ko?"
"Alhamdulillah wajen ne da nisa."
"Allah sarki sannu."
Gajeren murmushi kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba.
Yana nan zaune sai ya ga wata mota ta gifta kan titin.
Makaho ya cire tsohuwar wayrsa daga cikin aljihu, ba waya ce irin ta kowa ba, waya ce ta aikinsa.
Ya yi magana ƙasa-ƙasa a cikin wayar yake cewa.
"Target ya motsa."
Daga ɗaya bangaren aka amsa da .
"Kar ka bari ya ɓace."
Sai ya koma ya cigaba da gyaran takalmin da yake gyarawa kamar babu abun da ya faru.
Daga haka ya ɗan miƙe kasancewar yana da Ɗan tazara tsakanin sa da sauran mutane da suke Zaune kowa na sana'ar sa.
Kiran sallar la'asar ce ta saka ya ajiye komai ya tashi yana cewa.
"Bello don Allah taimaka ma ni da buta na yi alwala."
Kasancewar suna ajiye ruwan sallah a bokiti mai murfi.
Mai suyan awara dake kusa da su ta kalli Makaho ta ce.
"Wallahi shi ya sa Khalifa kake ƙara burge ni, ba ka wasa sa ibada."
Bai ce da ita Komai ba illa ya yi gajeren murmushi.
Bello ya kawo ma sa ruwan,.sai ya karkace hannu yana laluben gefen da ba nan butar take ba, sai da Bello ya rike hannunsa yana cewa .
"Ga ruwan nan."
Ya karba yana godiya. Gefe ya ma tsa ya yi alwala kafin ya ce .
"Jama'a ku tashi mu yi sallah lokaci na wuce wa yanzu za'a tayar."
Wasu sun tashi wasu kuma ko a jikinsu.
Bayan an idar da sallah ya fito daga masallacin gabaɗaya mai suyan awara ifanunta na kansa, tana ganin ikon Allah, cikkaken namiji mai cikar zati da haifa ya hadu ta ko ina sai dai jarabtarsa makanta da talauci.
"Bana son yawan kallo."
Ta ji maganar kamar daga sama, wanda sai da ganinta ya faɗi. Cike da mamaki ta ce.
"Khalifa waye ke kallo ka?"
"Ban san ko waye ba, amma ina ji a jikina ana kallona kuma kallo na ƙurilla."
Wanda yake faci daga can gefe ne ya bude baki ya ce.
"To meye abun kallo a jikin naka, nakasar za'a kalla ko me?"
Kafin ya yi magana mai suyan awara ta ce.
"Namiji ƙira da cikar zati , kyau da kwarjini."
"Dalla rufe wa mutane baki Mallama ina kwarjini ga makaho?"
Ya faɗa a fusace, dama yana jin haushi yana son me awara ba ta son sa, kuma ta yi ta yawan kallon makaho tana jan sa da fira duk da ba wani kula ta yake yi ba. Sai dai yana burge ta amma ba ta jin za ta iya soyayya da makaho talaka.
Mai Yalo da ya sa baki yana nuna wa Mai faci ya daina abun da yake yi , wanda shi kuma Makaho ya ya ɗauki kayan aikinsa ya tafi. Don idan ya tsaya tabbas zai iya illata wannan mutumin kuma za'a san shi waye.
_Ma'eesha_
Ta yi wanka tana jiran dawowar mijinta don tana ta damuwa tun karin safe bai ci komai ba, kamar ta sani kuwa dama bai ci komai ba, don ko ruwa bai sha a hotel ɗin ba.
Da sallama ya shigo cikin gidan, ta ɗago kai ta kalle shi tana amsawa da .
"Wa'alaika salam warahmatullah."
Ta mike fuskarta ɗauke da fara'a ta karbi kayan hannunsa tana yi ma sa sannu da zuwa.
"Yauwa ya gidan."
"Alhamdulillah."
Hannunsa ta riƙe ta taimaka ma sa ya zauna a tabarmar da ta shimfiɗa.
Zama ya yi ta kawo ma sa pure water mai sanyi da ta siyo a kanti ta zuba a jug.
Ya sha ruwan yana yi ma ta godiya.
Abinci ta kawo ma sa yana ci tana yi ma sa fifita har ya gama. A hankali ya furta
" Alhamdulillah."
Murmushi ta yi tana cewa .
"Ma sha Allah."
Kallonsa ta yi na wasu second kafin ta ce .
"Am na ce ba."
"Me kika ce ranki ya daɗe?"
"Na ce maganar sace ka da aka yi fa har yanzu hankalina bai kwanta ba, saboda rashin sanin manufar ma su satar naka, ga shi kai ba gani kake yi ba ballantana idan ka ga wani abu da bai ma ka ba ko makamancin abun da ya faru da kai ka nemi taimako a kowane waje kake. Idan ka fita gidan nan hankalina baya kwanciya sai na ga dwowar ka, ba na so na rasa ka a duniyata da ba na da kowa sai kai."
Ta karasa mgana tana zubar da hawaye.
"Kada ki damu in sha Allah ba abun da zai same ni."
Sallamar mace suka ji daga kofar gidan, suka amsa yayin da ya tashi ya shiga ɗaki kafin mai sallamar ya shigo cikin ɗakin.
Wata mata ce maƙociyarsu ta shigo gidan.
"Sannu da zuwa."
Ma'eesha ta faɗa cikin sakin fuska da walwala.
"Yauwa sannu baiwar Allah."
Matar ta faɗa tana zama a ranarma tare da ajiye madaidaiciyar jakar hannunta. Gaisawa suka yi kafin matar ta ce .
"Sunana Bilikisu maƙociyarki ce duk da ba ki shiga jama'a ballantana a saba da juna."
"Haka ne, in sha Allah zan shigo."
Duka maganar da suke yi yana jin su daga cikin ɗaki, ita matar ba ta san cewa mijin Ma'eesha na gidan ba, don haka ta ce .
"Talla na kawo ma ki ga su nan, kayan gyaran aure ne magungunan mata ma su kara ni'ima da Ɗanɗano "
Shiru Ma'eesha ta yi tana tunani, ita me za ta yi da waɗan nan kayan, ita da ba ta da ko sisi, ko tana da kuɗi ma ai ba za ta siye ba, meye amfanin su mijin da ko hannunta bai taɓa rike wa ba ballantana wata Mu'amalar aure ya shiga tsakanin su. Don sai dai ita ta rike hannunsa amma shi bai taɓa rike hannunta ba, ta lura ko jikinta bai so ya haɗu da nasa, take zai zame jikinsa ta rasa dalili.
Maganar matar ce ta dawo da ita cikin hayyacinta .
"Wanne kike so ga su nan na fito ma ki da su."
Ma'eesha ta kalli magunguna daga na kwali har na roba ga sunanyen su nan da yadda ake amfani da su.
Murmushi ta yi kafin ta ce.
"Allah ya kawo kasuwa."
"Haba baiwar Allah ai yanzu mata ba sa zama ba gyara, idan kina da kyawu sai ki kara da wanka, yadda oga zai samu gamsuwa yadda ya kamata"
Murmushi ta sake yi kafin ta ce .
"Ina da su da yawa ne idan na siye wasu yanzu za su yi ma ni yawa ne."
"Shi ke nan tun da haka kika ce, amma bari ba ba ki wasu kayan kyauta idan kika yi amfani da su da kanki za ki biyo ni."
Magunguna ta dauka kala uku sai wani turare ta ba ta su kyauta. Ba ta da wani zaɓi don haka ta karba tana yi ma ta godiya.
Fitar matar kenan sai ga Nasreen ta shigo da sallama.
"Assalamu alaikum Matar Khalifa na nan?"
Murmushi ta yi tana cewa .
"Ina zan je ƙawata."
Zama ta yi gefenta tana cewa.
"Daga unguwa nake na ce bari na biyo na duba ki."
"Allah sarki aiko na gode. Ya jikin Mama?"
"Mama ta ji sauƙi sosai."
"Ma sha Allah, Allah ya kara lafiya."
"Amin ya Allah."
Kallon magungunan ta yi kafin ta ce.
"Tofah, Ma'eesha kayan mata kike siya?"
Ba ta tanka ma ta ba ta dai yi murmushi.
"To a dai bi a hankali a san irin abun da za'a dinga sha."
"Ke ba fa sha nake yi ba, idan akwai macen auren da kika san tana sha kwashe ki kai ma ta."
"Ban gane ba ke meye na siye to."
"Ba siya na yi ba, ba ni ta yi kuma ba zai ma ni amfani ba kamar yadda ke ma ba zai ma ki ba."
Cikin tashin fahimta Nasreen ta kalli Ma'eesha ta ce.
"Ni da ba matar aure ba ke kuma ai kina da miji."
"Hmmm sunan dai ina da miji ne kawai amma ba wani mu'amala ta aure ya taɓa haɗa ni da shi."
Da mamaki ta kalle Ma'eesha kafin ta ce
"Duk watannin da kuka yi ba wani abu da ya shiga tsakanin ki da shi kuna kwana daki ɗaya? Ko bai da lafiyar mazantaka ne?"
"Ban sani ba wallahi. Kuma kin san wani abu?"
"Sai kin faɗa."
"Ina matuƙar so na ga na samu ciki, saboda ina son yara a rayuwata , burina na ganni rungume da baby na."
"To ba ki tunanin a cikin wannan rayuwa da kike ciki za ku iya ɗaukar ɗawainiyar baby?"
"Za mu iya domin Allah baya ɗorawa bawa abun da ya fi ƙarfinsa. Kuma ba mu fatan dauwama cikin wanann halin da muke ciki."
"Okay yanzu kafin ki yi tunanin cikin da kike so ki fara tabbatar da lafiyar mijinki, idan kuna haɗa jiki wuri guda yanayinsa baya sauya wa?"
"Ai baya yarda mu hada jiki da juna, da zaran na hada jiki da shi zai zame da sauri, ke ko kwanciya baya yarda mu yi a shimfiɗa ɗaya."
Sai da Nasreen ta yi dariyar mai isarta kafin ta ce.
"Ina da tabbacin lafiyarsa ƙalau, kuma yana nisanta kansa daga ke ne saboda baya son wani abu ya shiga a tsakanin ki da shi. Don idan da bai da lafiya ne ba zai damu dan kun hada jiki ballantana ya nisanta kanki da shi, kin ga alamar yana tsoron abun da zai iya biyo baya ne, sai dai ban san dalilinsa na yin hakan ba."
Shiru Ma'eesha ta yi kafin ta ce .
"Ba damuwa sai mu tafi a yadda yake so, don duk yadda nake son haihuwa ba yadda za'ayi ina ƴa mace da aka sani da al-kunya na kai kaina wajan namiji ."
"Ba za ki kai kanki ba amma ai mace ce ke, akwai hanyoyi da yawa da za ki iya saka shi ya kawo kansa gare ki ba tare da ya shirya wa hakan ba."
Murmushi ta yi kafin ta ce.
"Bari na faɗa ma ki a kunne ."
Ta matso dab da Ma'eesha ta matso da fuskarta saitin kunnen Ma'eesha, ta fara yi ma ta magana cikin raɗa.

Page5️⃣7️⃣

Wani kallo Ma'eesha ta yi ma ta kafin ta ce.
,"Ke ni za ki kai ki baro? Wallahi ba zan yi ba sai dai mu yi ta zama a haka, matukar sai na bi wannan hanyar da kika zo ma ni da ita."
"To shi kenan tun da haka kika ce."
Fira suka ɗan taɓa kaɗan kafin ta miƙe bayan ta ciro kayan kwalama da ta zo ma ta da su. ice cream ne da au Chocolate ta ajiye ma ta, sallama suka yi ta fice daga gidan,.ita kuma ta ɗauki ledar kayan da kuma kayan matan da maƙociyarsu ta kawo ma ta su ta shiga ɗakin.
Da sallama a bakinta ta shiga ɗakin , ya amsa mata ta kalle shi ta ce.
"Lafiya ka zauna a ɗaki?"
"Na ga kin yi bakuwa ne shi ne na ba ki waje ku gaisa."
"Ayyah maƙociyarmu ce ita."
"Ayyah me ta zo yi ne?"
Kallon magungunan ta yi wanda shi ma kallon magungunan yake yi, wanda kallo daya ya yi wa magungunan ya ɗauke kai, kuma ya san me magungunan ya ƙunsa amma kasancewar kallon makaho take yi ma sa ya sa ba ya san magungunan yake kallo ba, don duk firar su har da na Nasreen ya ji su.
Murmushi ta yi kafin ta ce.
"Kawai ta zo wai mu gaisa ne da ita kasancewar ban taɓa shiga maƙota mun gaisa, da na zo ya kamata na je na gaida su. Bayan matar ta fita ne Nasreen ta zo ita ma akan hanya yake har ya tafi."
"Ya jikin Maman nata?"
"Da sauki ta ce."
"Ma sha Allah, Allah ya kara ma ta lafiya."
"Amin ya Allah."
"Bari na je masallaci Magrib ta gabato."
"Okay bari na zuba ma ka ruwa a buga."
Daga nan ta fita daga dakin don zuba ma sa ruwa.
_Nadra_
Bayan ta yi wanka ne ta saka kayan barci riga da wando farare na su taushi da santsi , wandon dogo ne shi , ta tufke gashin kanta sannan ya saka hula.
Har za ta yi taurin akbar kwanta kuma sai ya tuna da gargadin da Fahad ya yi ma ta. Don haka sai ta ba nufi ƙofar fita daga ɗakin.
Yana zaune a falo hannunsa rike da waya yana sarrafa ta, tana fitowa ya tsaya yana kallonta sosai, domin kuwa ta yi ma sa kyau sosai fiye da yadda yake tunani, ga kayan barcin su.n zauna ma ta ɗagwas kamar saboda ita aka yi kayan.
Fuskarta a tsuke take, ganin ya tashi ya nufi dinning area ita ma ta tashi ta bi shi.
Ba ta zauna ba ya saka ma ta naman kaza a plate ya zuba ma ta yoghurt a glass cup.
"Zauna ki ci ki sha magani."
"Na ƙoshi."
Ta faɗa tana hade rai. Ɗaya kai ya yi ya kalle ta da kyau , kafin ya ce.
"Ba na son gardama kuma ba na maimaita magana dayay, kar ki bari na sake yi ma ki magana.
Zama ta yi tana tura ba ki , ga shi yunwar take ji amma kuma taurin kanta ya hana ta zauna ta ci. Ganin kallon da ya yi ma ta ne ya saka ta fara ci kamar za ta yi kuka .
Sai da ta ci kusan rabi ta ce ta ƙoshi. Kofin gabanta ya yi ma ta nuni da shi, ta ɗauki yoghurt din ta shanye.
Magani ya ba ta ta karba kamar za ta yi kuka, sai da ta shanye ta bar kasar Wajen. Da ido ya bi ta har ta shiga cikin ɗakinta.
Shi ma ya ci sauran wanda ya rage sannan ya kwashe kayan ya kai kitchen.
Ɗakinsa ya shiga ya yi wanka ya yi shirin barcina ya kwanta kan lafiyayyen gadonsa don yin barci.
Ita ma tana komawa ɗakinta ta wanke baki ta ɗauro alwala sannan ta kwanta barci. Ba jimawa barci ya yi awon gaba da ita.
Amma shi kam Fahad a nasa ɓangaren ba haka ba ne, domin ya kasa barci sai tunanin Nadra ya saka shi gaba. Lokaci zuwa lokaci yake jan tsuki ya kasa gane dalilin da ya sa yarinyar nan ta yi kane-kane a cikin zuciyarsa. Yarinya sai ka ce Mayya. Sai cikin dare barci ya yi nasarar ɗauke shi.
_Ma'eesha_
Kamar yadda ya zame ma ta al'ada kullum sai Khalifa Makaho ya yi ma ta fifita take iya barci yau ma haka ne, yana tsaka da ma ta fifita barci ya yi awon gaba da ita.
Yana ganin ta yi barci ne ya yi sauri ya je ya ɗauko wata ƙatamar fanka a cikin kayansa, ya bude fankar ya ja ta ta ɗan yi tsayi sannan ya kunna ya ajiye ma ta.
Wani abu da ba ta sani ba, a duk lokacin da take yin barci Makaho kunna ma ta fanka yake yi ya fice daga gidan. Yakan je ne ya gudanar da bincikensa cikin dare. Saboda mutanen da yake yin aikin a kansu a dare suka fi yin harkokinsu. Don haka ne ma idan Ma'eeha ta yi barci yake ajiye ma ta fanka ya fice. Sai tsakiyar dare shiyoyin ƙarfe ƙarfe uku na dare yake dawowa, don a cikin awanni biyu yake kammala abun da ya fita da shi yake dawowa.
Kuma ita ba ta san da fankar a cikin gidan ba, don ba taɓa ma sa kaya take yi ba.
Bayan ya ajiye ma ta fankar ya cire kayansa ya sauya daga manyan kaya zuwa ƙananan kaya.
Na'urar ɗaukar sauti ya ɗauka ya maƙala a jikinsa sannan ya ɗauki ɓoyayyer wayarsa ta zuwa aiki ya bar gidan.
Nan Ma'eesha ta cigaba da barci ba tare da ta san baya gidan ba.
Sai zuwa can da misalin karfe uku da rabi ya dawo gidan.
Cikin sanɗa yake tafiya ya shigo cikin ɗakin.
Wasu takardu ya ɗauka a cikin kayansa ya yi rubutu a jiki, ya shigar da wasu bayanai, kafin ya tashi ya karasa in da take kwance tana barci .
Fankar ya dauke ya kashe sannan ya yi saurin zama a gabanta yana yi ma ta fifita .
Baya karfe huɗu ta cika ne ta farka daga barcin, ganinsa ta yi zaune yana yi ma ya fifita, karɓe mafecin ta yi tana cewa.
"Wai Yaya Khalifa me ya sa ba ka tausayin kanka ne?, Ta ya mutum ya zauna tun daga farkon dare har ƙarshen dare bai yi barci ba yana zaune, ko so kake yi ka samu wani ciwon mu shiga uku."
"Na saba babu abun da zai same ni."
"A'a barci ma lafiya ne ga jikin mu, yanzu ka kwanta na awa ɗaya idan ƙarfe biyar ta yi zan tayar da kai ka je masallaci ka yi sallah."
Ganin yadda ta dage har tana ɓata rai ne ya saka shi dole ya amice zai kwanta, ganin yana ƙoƙarin zuwa kan tabarmarsa ne ya saka ta rike hannunsa tana cewa .
"To ai yanzu ba kwanciya zan yi ba ballantana ka ce ba za ka kwanta tare da ni ba. Ka dawo kan katifar ka kwanta kai kaɗai ne za ka kwanta."
Murmushi kawai yayi sannan ya hau kan katifar ya kwanta.
Nan ta dinga yi ma sa fifita cikin mintuna goma barci ya yi awon gaba da shi.
Tana yi ma sa fifita na tsawon awa ɗaya sannan ta fara tunanin tayar da shi don lokacin sallah ya gabato.
Kyakkyawar fuskarsa ta zuba wa idanu tana kallonsa, sannan ta kira sunan sa a hankali.
"Yaya Khalifa, Yaya Khalifa, Yaya Khalifa."
A hankali ya amsa yana mai tashi zaune bakinsa da salati.
"Ka yi hakuri ka ji dadin barci , na ga lokacin sallah ta yi ne shi ya sa."
"Ba komai na gode Allah ya yi ma ki albarka."
Da Amin ta amsa sannan suka fito daga ɗakin don lokacin sallah ya yi .
_Sidra_
Tun da ta ga Fahad ya bar gidan da Nadra ranar ba ta iya barci ba, hankalinta ya kai ƙolololuwar tashi.
Duk ta firgice ta fita hayyacinta musamman da ta ga yadda Fahad ke ta rawar ƙafa akan Nadra yayin da ita ki kallo ba ta ishe shi ba.
Shirya wa ta yi ta nufi gidan Sady baby dan ta ba ta shawarar yadda za ta ɓullowa lamarin nan.
Sallama ta yi wa su Mama da sunan za ta je gidan ƙawarta ba ta da lafiya. Duk da Mama ba ta son yawan fitar da Sidra ke yi sai dai ba ya da yadda za ta yi ta hana ta fita.
Mama ta kalle ta ta ce.
"Direba zai kai ki ko kuma ke za ki yi driving motar da kanki?"
"Mama da kaina zan yi driving."
"Okay ki ɗauki key din motar ga ta can, amma don Allah kada ki daɗe."
"To Mama in sha Allah."
Ta yi maganar tana nufar centat table in da Mama ke nuna ma ta key din motar .
Fita ta yi daga cikin falon kafin ta kira wayar Sady baby.
Daidai tana ƙarasawa wajen motar ne Sady baby ta ɗaga wayar tana cewa.
"Hello ƙawata."
Sidra ta ce kina gida ne?"
"Eh ina gida ina fatan komai na tafiya daidai."
"Hmm gani nan dai zuwa."
Daga haka ta katse kiran wayar ta bude murfin motar ta shiga
Sady baby ta tashi daga cikin saurayin da suke tare kan gado tana cewa
"Ka bar gidan nan kafin ta zo ta same ka."
"Wace ce ita da kike tsoron ta haka.?"
Dariya ta yi kafin ta ce .
"Ba tsoron ta nake yi ba, infact ma amfani da ita nake yi wajen cimma burina na mallakar Namijin da nake so na yake rayuwa da shi."
Ya sauka daga kan gadon Yana cewa.
"Wani namiji ne wannan?"
"Fahad Majidaɗi."
"Fahad Majidaɗi fa kika ce?"
"Ƙwarai kuwa shi, shi ne Namijin da na dade ina so a rayuwata, wanda na san shi tun kafin Sidra ta san shi, a takaice me ni na sanar da ita ko waye shi da kuma irin son da nake yi ma sa. Wata rana mun haɗu da ita a wajan shopping muna magana sai kawai ga motar Fahad ga ƙaraso wajen. Nake sanar da ita ina masifar son sa amma ya wulakanta ni, madadin ta taimaka ma ni shi ne ta kutsa kanta gare shi, da na ga har suna shirin aure ni kuma ba zan taɓa bari ta mallake shi ba sai dai ni ya sa na ba ta gurguwar shawara, don na ga tana masifar son ta yi suna ta ɗaukaka, na muna ma ta damar zai wuce ta don wata shahararriya ta wulakanta, na yi amfani da damar na sa ta gudu ranar aurenta don rasa shi Ni kuma ba mallake shi. Amma cikin rashin sa'a iyayenta suka ba shi auren ƙanwarta a madadinta."
Jinjina kai ya yi tana maida rigar jikinsa ya ce .
"Tab shi ya sa sheɗan ya jinjina wa kaidin mace, to ga shi kin rasa ita ma ta rasa."
Dariya mai sauti ta yi kafin ta ce.
"Ban rasa ba, yanzu haka ina amfani da ita ne wajan ganin ta raba ƙanwarta da Fahad, na ba ta shawarar yadda za ta raba su, idan suka rabu ita ma na tona asirinta wajen iyayensu da shi dole ba za ta rayu da shi ba ka ga na buga wasa na yadda nake so"
"Amma ai ba lallai ya so ki ba."
"Na san hanyoyin da zan bi dole ya so ni."
Ta yi maganar tana nuna ma sa kofar fita, ba musu saurayin ya fice yana jinjina kai
Tashi ta yi ta faɗa bathroom don yin wanka.
Bayan ta fito ta saka doguwar riga daidai lokacin da ta ji shigiwar motar Sidra.
Ta window ta leka ta hange Sidra na fitowa daga cikin motar, sakin baki ta yi tana kallon motar wacce ta san cewa motar Sidra ba ta kai wannan tsada ba.
Taɓe baki ta yi tana karasa shirya wa cikin sauri .
Sallama Sidra ta hi tare da shogjwa cikin falon, zama ta yi kan Kujera daidai lokacin da Sady baby ta fito tana ma ta murmushi.
Oyoyo ƙawata."
Ta faɗa tana rungume Sidra tare da ƙaƙaro murmushin dole.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce ✍️

Pqge5️⃣8️⃣

"Sannu da zuwa ƙawata ya kike ya hakuri da rayuwa?"
"Alhamdulillah."
"Ma sha Allah."
Zama ta yi gefenta tana cewa.
"Meye labari?"
"Hmmm ke dai bari na kasa gaskata abubuwan da ke faruwa a rayuwata ji nake kamar mafarki nake yi ba gaskiya ba ne."
Tashi Sady baby ta yi ta kawo ma ta ruwar roba da glass cup, zuba ma ta ruwan ta yi ta mika ma ta, karba ta yi ta sha .
_Nadra_
Bayan ta tashi da safe ta fara aikace-aikacen gidan, bayan ta gama da sama ta koma zuwa falon ƙasa. Kasancewar tana da ƙoƙarin aiki ba ta gajiya da aiki ba ta da ganda.
Ɗakinsa ne kawai ba ta shiga ciki ta gyara ba, sai ta shiga kitchen don ɗora breakfast.
Sai karfe tara na safe ya fito ya ji ƙamshi na fitowa daga cikin kitchen ɗin.
A falo ya zauna ta dauki system ɗin sa yana amfani da shi.
Bayan ta gama ne ta fito dauke da babban faranti da aka jera breakfast akai .
Jera su ta yi a dinning table din sanann ta hango shi zaune a falon.
Ƙarasawa ta yi gabansa cikin sanyi jiki ta durƙusa ta gaishe shi.
"Ina kwana."
"Lafiya lau."
Ya amsa idanunsa na kan abun da yake yi.
Tashi ta yi ta nufi bedroom ɗin ta, ya bi ta da kallo, kamar ta san yana kallonta sai ta juyo suka haɗa idanu, kau da kansa ya yi yana jin takaicin kallon da yake yi ma ta har ta kama shi yana kallonta.
Ɗakinta ta wuce kai tsaye ta nufi bathroom don yin wanka.
Ta yi wanka ta shirya cikin doguwar rigar material ɗinkin bubu.
Sanyayyen ƙamshi ke tashi daga jikinta. Kai tsaye ta nufi falon. Yana in da ta bar shi.
"Breakfast na jiran ka Yaya Fahad."
Ta faɗa har yau ba walwala ko sakin fuska a tare da ita.
Bai tanka ma ta ba kamar yadda ba ta saka ran dama zai tanka ma ta ba.
Nufar dinning area ta yi don hada ma sa breakfast. Cikin nutsuwa take yin komai nata har ta shirya ma sa komai.
Tana gama wa ya ƙaraso wajen ya zauna, cin abincin ya fara yi yana mamakin yadda ta iya yin girki haka.
Ita ba ta wani ci komai ba ruwan Lipton wanda ta dafa shi da kayan ƙamshi kawai ta sha.
Bayan ya gama ne ya kalle ta ya ce .
"Idan kin gama za mu je gidanku mu gaida su Umma."
Farin cikin da ta tsinci kanta ciki ne ya kasa ɓoyuwa, cike da farin ciki ta ce .
"Na gode."
Bai ce ma ta komai ba ya tashi har zai bar wajan ya ce .
"Waye zai gyara mun ɗaki?"
"To ina zuwa."
Komawa falo ya yi ya zauna. Ita kuma ta fara tattara kayan da suka yi amfani da su ta kai kitchen, sannan ta dawo ta gyara wajan ta goge.
Kai tsaye ɗakinsa ta nufa, falonsa fes kamar yau aka gyara, daga nan sai ta nufi bedroom. Toilet ta fara wankewa , sannan ta dawo ta gyara ma sa bedroom ɗin har zuwa falo.
Bayan ta gama ne ta fita zuwa kitchen don ta yi wanke-wanke.
Gani ya yi aikin sun yi ma ta yawa don haka take a wurin ya fara tunanin ko a nema ma ta mai taya ta aikin gidan ne.
Ɗakinsa ya shiga don shirya wa, wanka ya fara yi ya fito ɗaure da towel yana tsane kansa da wani karamin towel ɗin.
Shirya wa ya yi cikin manyan kaya, tsadadden yadi mai ruwan sararin samaniya. Yadin irin mai taushi nan ne ya saka hula wacce ta dace da shigarsa.
Sai zuba ƙamshin turare yake yi, ya saka takalmi baƙi wanda shi ma hulɗar ta sa baka ce .
Fitowa ya yi daga bedroom ɗin sa ya nufi ɗakinta dan ya sanar da ita idan ta shirya ta same shi a mota.
_Nadra_
Fitowarta daga wanka kenan tana ɗaure wanda ya tsaya ma ta iya rabin cinyarta.
Nan ya yi tozali da ita wa da hakan ya saka ya tsinci kansa a wani yanayi ma daban. Wani abu ya ji ya tsara ma sa tun daga kansa har zuwa babban yasar ƙafarsa.
Wanda bai san lokacin da ya karasa gabanta, wanda ita kam ba ta ma san ya shigo ɗakin ba sai da ta gan shi a gabanta yana kokarin janyo ta jikinsa neta lura da shi. Taga-taga ta yi baya za ta fadi sakamakon santsi tiles cikin zafin mama ya janyo ta jikinsa sannan ya ɗaga ga can ya nufa gadonta da ita a hannunsa.
Kuka ta saka ma sa tana ture shi amma ko gezau bai motsa ba.
"Ki kwantar da hankalinki kin ji ba zan cutar da ke ba, na yi ma ki alƙawarin zan rayu da ke har zuwa ƙarshen rayuwata, I love you Nadra. Ni za ka yi wa dadin baki saboda kana son ka mori jikina."
"Wallahi ba dadin baki ba ne da gaske nake ba zan iya rabuwa da ke ba ina son ki."
"To shi ne ban ga kana nuna ma ni so myayya ba sai yanzu?"
"Kece ba ki bani dama ba tun dawowa ta kika sauya."
Ya yi maganar da kyar yana yana cikin halin buƙatuwa da ita sosai.
"Shi ne ba ka bani hakurin laifin da ka yi ma ni ba ko? Wato idan jikin nawa wata masifar ce na jiƙa na sha ko?"
Jikinsa na rawa yana ƙara ƙanƙame ta ya ce.
"Na ba ki haƙuri tuba nake ba zan sake ba, ni da kaina zan jiƙa kuma na shanye kin ji?"
Duk da Halin tsoro da take ciki bai hana ta yi ma sa dariya ba, ganin lokaci daya ya canza ba wannan jin kai da yake da shi ko nuna isa da taƙama yana bin ta duk yadda take so.
Tana rike da towel ganin yana ƙoƙarin warware ma ta shi.
"Yaya Fahad kada ka gama morar jikina ka wulakanta ni ka sake ni kamar yadda ka ce, na san ba ka so na ka sake..."
Ya rufe ma ta baki da yatsarsa ya ce.
"Duk abun da na faɗa ma ki yanzu gaskiya ne, zan rayu da ke har ƙarshen rayuwata na amshe ki matsayin matata uwar Ƴaƴana."
"To amma Sunyi Sidra fa?"
"Kada ki sake kira ma ni sunan ta. Please ki ba ni hadin kai na samu abun da yake halaliya ta ba zan iya jurewa ba, kina da ilimin addini kin san hukuncin matar da ta bijirewa bukatar mijinta ko,?"
Hankalinta ya kara tashi ta sani tana cikin tsinuwar Mala'ikun Allah amma ba za ta iya jurewa ba."
"Ka yi hakuri tsoro nake ji."
"Na gane kuma na yi ma ki alƙawarin ba zan dasu da ke ba sai da amincewar ki, amma ki taimaka ki bari na biya buƙata ta da ke ta hanyar wasa da ke ba tare da ba kusance ki ba har sai ranar da kika yarda."
"Kai ta jinjina ma sa tana hawaye."
Rintse ifanunta ta yi tare da sakar ma sa towel ɗin da yake kokarin janye wa .
Bakinsa ya saka cikin nata bakin ya shiga tsotsa kamar ya samu sweet. Yana sarrafa albarkatun jikinta yadda ransa yake so, kasancer ita ma ta sakar ma sa jiki, sai dai ba abun da take tunawa kamar kalaman Aunty Sidra, su ne suke yi ma ta amsa kuwa a cikin kunnenta.
Tambayar kanta take yi shin ya za ta yi? Za ta saɓa wa umarnin Allah ne don ya faranta wa baiwar sa? Ko kuma umarnin Allah za ta bi ta samu lada? Babu biyayya ga abun halitta wajen saɓawa Allah. Wani yanayi ta sake riskar kanta a ciki jin yadda yake tsotsan dukiyar fulaninta kamar jariri yana murnza ɗaya.
Tsawon lokaci ya dauke sarrafa ta, ita kanta ba ta san lokacin da ya cire kayan jikinsa ba kasancewar idanunta na a rufe, ba shiri ga bude idanunta sakamakon jin ya kana hannunta ya ɗora a sanadar girmansa. Cikin tashin hankali ta kalle shi za ta janye hannunta ya matse hannun ya rike yadda ba za ta iya cire hannunta ba.
Zuwa can ta ji ɗumi a cikin hannunta, ta kalli hannun ta ga abun da ya zuba ma ta.
Yamutse fuska ta yi kamar za ta yi kuka yayin da ta mika ma ta toilet peper ta karba tana goge hannunta.
Sumbatar gishinta ya yi tare da cewa
"Thank you."
"Mu je mu yi wanka."
Make kafada ta yi tana cewa
"Ka tafi kai kaɗai."
Murmushi ya yi ma ta ya tashi ya nufi bathroom ya tsarkake jikinsa.
Ko da ya fito ta daura towel ɗin ta tana jiran fitowarsa.
Ya fito ɗaure da wani towel ya nufi ɗakinsa.
Ita ma wankan ta yi sanann ta fito tana gyara gadon ta tattara kayansa da suka yi takure.
Shirya wa ta yi cikin Abaya mafi ruwan toka ta dauki handbag da wayarta ta saka takalmi flat shoe. Ta dauki kayansa ta nufi ɗakinsa.
Ta same shi ya shirya cikin wata ɗanyar shaddar fara yana ɗaura tsadadden agogon hannunsa sai zuba ƙamshi yake yi.
Ta cikin mirror suka haɗa idanu, da sauri ta ɗauke kanta tana sunkuyar da kai.
"Ki saka su a cikin washing machine"
Kai tsaye ta nufi bathroom ɗin sa ta zuba su ciki kamar yadda ya umarce ta haka ta yi sannan ta fito. Har lokacin ta ƙi yarda su haɗa idanu da shi, dan wani kunyarsa take ji sosai ba kaɗan ba.
Key din motarsa da wayoyinsa ya ɗauka sai wasu tarkardu da alama daga can zai je wani wurin ne.'
Shi ya rufe ƙofar shiga don ita tuni ta fice. A wajen parking space ya same ta tsaye don ita ba ta san da wata motar zai tafi ba.
Ma'aikatan gidan na gaishe ta.
Sai a lokacin take lura da motarta sabuwa wanda Baban Fahad ya siya ma ta, duk da ba ta san lokacin da aka kawo motar ba.
Ganin tana kallon motar ya ce
"Motarki ce aka kawo key na falo dan mun dawo sai i na ba ki ."
Ya yi maganar yana buɗe ma ta gaban motar, ta shiga ta zauna sannan ya zagaya wajan zaman direba ya zauna, key ya yi wa motar suka bar gidan.
Ba abun da ke tashi daga cikin motar sai ƙamshin turarensa da sanyin A.C kawai ake ji.
Kallonta ya yi ganin har lokacin kanta a kasa tana wasa da yatsun hannunta da suka sha jan lalle sun yi kyau. Yana mamakin irin kunyar da Nadra ke da shi.
"Nadra."
"Na'am Yaya."
"Kada ki sake kira na da Yaya domin ba Yayanki ba ne, yau na ji kalan dangi."
"To me zan kira ka?"
"Ki zaba ma Ni sunan da kika ga ya dace."
"Ni ban san sunan da ya dace ba."
"Okay to kira ni da Fahad."
"Wallahi ba zan iya ba ."
"To zaɓi suna na masoya ki saka mun. "
"Kunya nake ji "
Dariya ya yi yan cewa.
"Da sannu sai na raba ki da wannan kunyar da kike ji."
"Ta ya ya?"
" Da sannu zan mayar da ke mara kunya."
*Tab wallahi ba na son rashin kunya da fitsara."
"Ba irin wannan rashin kunyar ba, irin kunyar nan nawa da kike ki zan raba ki da shi, don zai iya ciyar da ni."
Ba su yi tafiya mai nisa ba ya ya yi parking a wani gabanb super market.
Kallon wajen ta yi don ba ta san me yake sunyi w wajen ba.
"Me za ki siya wa su Umma tsaraba da su Ammi da Abba?"
"Ba na da kuɗi."
Ta yi maganar kanta a ƙasa, don kam ba ta da kudi ko da suka yi aure kudin sadakinta ne kawai a hannunta, kuma ta ranar wajen sallamar baƙi da ta dinga yi.
"Ba ni account number naki."
Ba musu ta karanta ma sa account number ɗin.
Shigowar alert ta ji na Naira miliyan uku. A firgice ta kalle shi don kudin sun yi ma ta yawa. Za ta yi magana ya ce .
"Fito mu je."
Yana faɗa ya fita daga cikin motar zuwa cikin supermarket ɗin.
_Makaho_
Bayan ya fito da safe zai je wajen sana'arsa, hannunsa ɗaya rike da kayan gyaran takalminsa, ɗaya kuma rike da sandar jagoransa, sai sauri yake yi kasancewar akwai wani jami'in da zai zo karbar rahoto daga hannunsa. Kuma idan jama'a suka taru a wajan za su iya fahimtar wani abu.

Pqge5️⃣9️⃣
Bayan ya fito da safe zai je wajen sana'arsa hannunsa ɗaya rike da kayan gyaran takalminsa. Ɗaya hannun kuma rike da sandar jagoransa, sai sauri yake yi kasancewar akwai wani jami'in da zai zo karɓar rahoto da daga hannunsa. Kuma idan jama'a suka taru a wajen za su iya fahimtar wani abu.
Cikin ƙanƙanin lokacin ya isa wajen sana'ar sa, sai sai akwai mutane duk da bai yi tsammanin zuwan kowa ba.
Ya gaisa da mai Yalo da sauran mutanen da suke wajan .
Zama ya yi bakin aikinsa, sai ga wani karnin yaro ya kawo takalminnsa gyara.
Karba ya yi ya gyara ma sa yaron mai kimanin shekaru shida a duniya. Bayan ya gyara ma yaron takalmi ne yaron ya ba shi dubu ɗaya ya ce .
"Uncle ga shi ka ba ni canji."
"Ya yi maganar yana miƙa ma sa dubu dayan da ke hannunsa. Karba ya yi yana cewa.
"Nawa ne nan?"
"Dubu ɗaya ne uncle."
"Ba na da canji."
Ya yi maganar yana miƙa ma sa dubu ɗayan."
"To uncle Ina za mu samu canji."
Murmushi ya yi saboda yaron ya burge shi ya ce .
"ka tafi ba bar ma ka kudin gyaran."
"To uncle na gode."
Yaron ya tafi yana murmushi, mai faci dake gefe ya ce .
"Dama canji ka nema ka karɓi ko Naira hamsin ce, don na san waye uban yaron nan yana da rufin asiri, kudin da yake samu a rana ɗaya sai ka yi wata ɗaya ba ka tara shi ba!"
Bai tanka ma sa ba ya yi kamar bai ji shi ba. Wani mutum ya zo ya yi sallama .
"Assalamu alaikum."
Gabadaya suka amsa ma sa da .
"Wa'alaika salam."
"Na kawo gyaran takalmi ne."
Ya yi magana yana nuna ma makaho tsakaninsa.
Jarɓa makaho ya yi cikin hikima da basira da Allah ya yi ma sa ya saka hannu cikin aljihun wandonsa ya ciro wani micro SD makaho ya manna shi a ƙasan takalmi da wani ƙarfe kamar ƙugiya a tafin takalmi.
Cikin ƙwarewa ya manna shi da jikin takalmin ya nannaɗe shi da zare ya ɗinke takalmin.
Miƙa ma sa ya yi tare cewa.
"To yallaɓai na gama."
"Nawa ne kudin aikin ka?"
"Naira ɗari ce ."
Ya ciro Naira ɗari daga cikin aljihun wandonsa ya a mika ma sa, makaho ya ba shi takalmin ya karba ya tafi .
Yana barin wajen makahon ya kira waya yayin da yake shiga cikin motarsa.
Ana ɗauka daga can ɓangaren ya ce .
"Hello sir."
Daga can ɓangaren aka ce .
"Ka samu ganin Jalaluddeen?"
"Eh yanzu haka ma bayanan suna hannuna ya ba ni."
"Gud job, aikinsa yana kyau. Ka kama hanyar Abuja yanzu kada ka ɓata lokaci."
"Okay sir."
Ya faɗa yana yi wa motar key ya bar wajan .
_Nadra_
Tana ganin ya ya fita bayan ya ce ta fito su je ta bishi ita ma. Zuciyarta cike da mamakin yadda Fahad Majidaɗi ya tura ma ta Naira miliyan uku.
Ta saka a ranta za ta yi wa Ummanta siyayya da Abba har da Ammi.
Suna shiga ciki ya ce .
"Ki duba tsarabar da kika ga ya dace ki siya ma su."
Jinjina kai ta yi har lokacin tana mamakin sa.
Shi kuma ɓangaren kayan abinci ya nufa. Ita kuma tana bangaren wajen kayan sakawa.
Atamfofi guda biyar da ɗaukarwa Ummanta. Da mayafaiya ma su kyau da tsada, sai sarka da Ɗan kunne ma su kyau kala biyu. Ta ɗaukarwa Abba shaddodi kala uku ma su kyau da tsada.. sai huluna da suka shiga da kowane kaya. Ta ɗaukarwa kakarta Ammi atamfa kala biyu ma su kyau.
Bayan ta gama cire wa ta waiga ta kalli bayanta , sai ta ga Fahad ne yake kallonta .
"Kin gama ne?"
Kai ya jinjina ma sa alamar eh.
"Okay mu je."
Ɗaya daga cikin ma'aikatan wajen ya tura kayan da ta zaɓa.
Ko da aka yi lissafin Kudin tana shirin bude handbag ɗin ta don ta fito da ATM card nata sai ta ga Fahad ya mika nasa ATM card ɗinsa.
Kallonsa take yi da mamaki yadda ya tura ma ta kuɗi har Naira miliyan uku wanda ita a tunaninta da su za ta yi tsarabar iyayenta, amma sai ta ga ya biya.
A bayan mota aka zuba ma su kayan,abun da ya kara ba ta mamaki shi ne yadda ta ga uban kayan abinci da ya siya aka zuba a motar, kama daga kan buhun shinkafa biyu buhun semovita biyu spaghetti da macaroni da cus-cusvhar zuwa indomie komai bibbiyu galan man ja da man gyaɗa haka aka tara komai har zuwa su maggi da kayan tea.
Ta kasa magana har ya bude ma ta gaban motar ta zauna a gefen sa, sannan ya yi wa motar key suka bar wajen.
Kasancewar ba su da nisa da wajan da suka yi siyayya da gidan Abba.
A kofar gidan ya yi horn maigadi ya leƙo ganin Fahad ya magale gate ɗin yana ta fara'a.
Ma'aikatan gidan da farin ciki suka ƙaraso wajen motar suna yi ma su sannu da zuwa. Don sunji kewar Nadra. Fahad ya fara fitowa sanann ya buɗe wa Nadra ta fito fuskarta ɗauke da murmushi tana kallon Baba maigadi da direban gidan da suke nuna farin cikin zuwanta. Cikin girmamawa durƙusa ta gaida su, suka amsa suna ma ta Allah sanya alkhairi ya ba su zaman lafiya.
Ciki suka nufa yayin da ta ɗauki ledar tsarabar su Umma ta shiga falon.
Fahad ya tsaya daga waje yana jiran a yi ma sa iso.
Da sallama ta shiga ciki, ta yi Sa'a kuwa kowa na nan, Abba na gida bai fita ba, Umma na zaune a gefensa, sai Ammi dake kwance kan doguwar kujera mai zaman mutum uku.
Gabadaya suka amsa sallamar fuskar kowa dauke da farin ciki. Nadra ta rungume Umma tana kuka.
"Ikon Allah, to me ye abun kuka kuma?"
Cewar Ammi tana mamakin Nadra.
Ganin haka Abba murmushi kawai ya yi , don duk wanda ya kalli Nadra ya san ba ta cikin tashin hankali. Ta ciko ta yi kyau sosai.
"Ina shi Fahad ɗin yake?"
Kuka kawai take yi ta kasa magana. Su kuma sai dariya suke yi ma ta.
Wacce ke yi wa Umma girki ne ta fito za ta je kasuwa, ta gaida Nadra lokacin da ta tsagaita kuka.
Tana fita ta ga Fahad waje ta dawo take cewa .
"Nadra kika bar mijinki waje ba ki ma sa iso ba?"
Sai a lokacin ta tana da shi yayin da Ammi ke salati.
"Ya kika bar shi waje kuma?"
Cewar Abba yana miƙewa tsaye.
Yana bude kofar ya ga Fahad yayin da Fahad ya durƙusa ya gaida Abba cikin girmamawa.
Ya amsa cikin da farin cikin ganinsa, hannunsa ya ja suka shiga ciki.
Ya gaida Ammi da Umma sannan ya kalli Nadra dake goge hawaye.
"Ka ga sakaryar matarka kukan shagwaba take yi saboda ta ga Ummanta."
Murjushi ya yi tare da cewa.
"Umma ya karfin jikin?"
"Alhamdulillah na ji sauƙi Fahad."
,"Allah ya kara lafiya."
Ya faɗa yana kallon Nadra da take wani narkewa a jikin Umma..
Ruwa da lemu mai aikinsu ta kawo ma su. Fahad ya sha ruwan kawai .
Abba ya kalli Fahad ya ce .
"Ya aiki yaushe ka dawo?"
"Juya na dawo Abba."
"Ma sha Allah, Allah ya taimaka."
"Amin ya Allah."
"Yauwa a kara hakuri da Nadra ka san yarinya ce karama, don Allah ka kara hakuri da ita komai zai yi daidai."
Kafin ya yi magana ne Ammi ta bude baki ta ce.
"Wani hakuri zai yi da Nadra, ai Allah ne ke son sa da gata. Yanzu da ba don Allah yana son ka ba ai da waccen gantalalliyar ya bar ma ka a matsayin matar aure, da yanzu kana nan kana ta fama da ita kila da yanzu na zuwan ka sai ka kawo ƙarar ta. Amma da Allah ya so ka da rahama da kwanciyar hankali ya ba ka Kamilar yarinya ai da yanzu kana nan kana tagumi."
"Umma ta yi shiru tana goge ƙoƙarin ɗauke ƙwallar ta ta je sun cika ma ta idanu.
Fahad ya kalle ta cike da tausaya yana ayyyana girman soyayya irin ta uwa akan ƴaƴanta. Cikin sanyin murya ya ce .
"Mama ki daina damuwa Sidra tana gidan Mahaifina cikin ƙoshin lafiya. Tana sakewa ta yi rayuwata da kowa, yadda ba mai takura ta a gidan nan haka adabi ma ba mai takura ma ta za ta yi rayuwarta yadda yake so , sai dai kewa da ba'a rasa ba.
Jinjina kai ta yi tana yi wa Fahad murmushi ta ce.
."Allah ya yi ma ka albarka."
Da Amin ya amsa yana miƙewa tsaye ya ce .
"Ni xan tafi anjima zan dawo na dauke ta mu koma gidan."
Addu'ar Allah ya dawo da shi lafiya suka yi ma sa ya fice.
_Makaho_
Kasancewar baya son abokan kasuwancin sa da suke sana'a tare su zarge shi ya sa wannan karon bai bar kayan aikinsa a wajen ba, kada su fara zargin ina yake zuwa .
Don haka ya dauki kayan aikinsa ya yi ma su sallama da niyyar da wuce gida ne.
Mai Yalo ya kalle shi ya ce .
"Lafiya za ka tafi da wuri haka?"
",Eh to ba na jin dadi kaina ne yake ma ni ciwo zan je na keanta."
"Subhanallah, Allah ya ba ka lafiya Mallam Khalifa."
"Amin ya Allah."
Mai suyan awara ta kalle shi ta ce
"Sorry kyakkyawa Allah ya sauwake."
Da yake ya san haka take kiransa ya amsa da Amin ya fara tafiya da sandarsa da kuma kayan aikinsa.
Sai da ya yi tafiya mai ɗan nisa sannan ya tsaya cak, mai nape da ke bisa ya tsaya a gabansa, Nan da nan ya shiga suka kama hanyar hotel ɗin yake zuwa .
Bayan sun isa hotel ɗin ne ya bar kayan aikinsa na gyaran takalmi da sandarsa ya shiga cikin hotel ɗin.
Key din dakinsa ya karɓa sannan haura sama.
Ɗakin ya bude sannan ya saka key ya rufe ta ciki.
A.C ya kunna sannan ya nufi bathroom ya sakarwa kansa shower, 🚿 wanka ya yi sannan ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa da wani karamin towel yana tsane ruwan kansa.
Man shafawarsa ya shafa ya saka ƙananan kaya sannan ya karasa ya zauna kan kujera in da kayan aikinsa yake kan table, kama daga laptop ɗinsa da wayoyinsa suke .
Wayarsa ya ɗauka ya lalubo lambar Ummee ya danna ma ta kira, don ya san halinta yanzu haka yana can ta tayar da hankalinta.
*Abuja*
Ummee na zaune a falo tana kwantar wa da Yasmeen da hankali, kan damuwa da ta yi na rashin ji daga Jalaluddeen.
"Ummee tsawon kawanki kenan ban ji daga gare shi ba, yanzu idan muka yi aure haka zai dinga yi ma ni ya share ni ba kiran waya idan yana aiki? A gaskiya ni kan idan aka ɗaura ma na aure sai sai dai duk inda zai je ya yadu tare da ni."
Kafin Ummee ta yi magana kiran Jalaluddeen ya shigo cikin wayar.
Da sauri ga daga daga tana cewa.
"Son lafiya tsawon kwanaki ba kira ina kiran wayrka ba ta shiga kuma ka kasa kira na ko? Ba ka tunanin halin da zan shiga ko don ba isasshen lafiya gare mi ba ko?"
"Tuba nake Ummeena, yanayin aiki ne wallahi , kin san sau da taka tsantsan."
"Duk da haka hankali na zai fi kwanciya idan ina jin motsinka. Na tabbatar kana lafiya."
"Idan kin ji shiru lafiya kenan."
Kamar ta yi ma sa Maganar yarinyar da aka ce yana tare da ita sai kuma ta fasa, ta bari sai ya dawo kafin ta ji daga gare shi.
"Ummee kowa na lafiya ?"
"Eh lafiya lau dai dai Yasmeen ce dai ga ta nan."
Ta yi maganar tana mika wa Yasmeen wayar.
"Subhanallah me ya same ta?"
Tashi Yasmeen ta yi saboda kunyar Ummee ba za ta sake ta yi magana yadda take so ba."
Sai da ta shiga bedroom ɗin ta ta zube a kan gado sannan ta shagwaɓe murya ta ce .
"Hello"
"Yasmeen ya kike ?'
"Ba na lafiya fa Yaya Jalal."
"Subhanallah me ya same ki?"
"Rashin ganinka da ciwon son ka ne za su illata ni."
"Subhanallah, ba na ce ki daina saka damuwa a ranki b"
"Yaya Jalal damuwa dole ne, a satin da za'ayi bikin mu ka tafi wanda dalilin haka aka ɗaga bikin dai ka dawo, da yanzu nuna matsayin ma'urata ko?"
"Haka ne, kin san komai na Allah ne kuma komai da lokacin sa, Allah ne bai yi ba a wancan lokaci."
"Haka ne, amma na damu da rashin ka sosai, amma na san kai ba ka damu da rashina ba da ka dinga nema na a waya."
"Ba haka ba ne, kina raina Yasmeen amma yanayin aiki ne ya sa ba ki samu na."
Fira suka yi a ƙalla mintinan ashirin sannan ya ma ta sallama. Kafin ya katse kiran wayar ta ce.
"Yaushe za ka dawo?"
"Sai zuwa gaba."
"I can't wait wallahi, sai dai na biyo ka in da kake."
"Ko kin zo garin ina mai tabbatar ma ki wahala za ki yi ba za su ki ganni ba."
"To Allah ya dawo mun da mai lafiya my Yaya Jalal"
"Amin ya Allah "
Cikin sanyin murya ta ce .
"I love you."
"Love you too."
Murmushi ta yi wanda sai da ya ji sautin murmushinta sannan ya kashe kiran wayar.

Page 6️⃣0️⃣

Zuciyarta fara tas ta ji muryarsa kuma ya mayarsa hankalinta ya kwanta.
Ta fito fakon tana murmushi daidai lokacin da Yusuf ya dawo. Kallonta ya tsaya yana yi sakamakon ganin kwana biyu tana fama da ƙunci da baƙin rai, yau sai ya ga tana ta fara'a don haka ya ce.
"Ummee wannan kuma fa farin ciki na mene ne?"
Ya yi maganar yana zama kan kujerar da ke fuskantar Ummee yana jiran jin ta bakinta.
Murmushi Ummee ta yi yayin da take karbar wayar da Yasmeen ke miƙa ma ta.
"Bari kawai wai daga Yayanku ya kira waya shi ne duk na wannan farin cikin."
"Okay Yaya Jalal ya kira waya yau kenan ?"
"Eh yanzu muka gama magana da shi."
Taɓe baki ya yi ya kalli Yasmeen ya ce .
"Wallahi kina da aiki in dai Yaya Jalal ne kike ma irin wannan son
"
Kamar za ta yi kuka ta ce .
"Haba Yaya Yusuf me ya sa za ka ce haka?"
"Na ga son naki da kike ma sa ya fi wanda yake ma ki ne, infact ma Yaya Jalal baya da lokacin ki sai na aikinsa kuma..."
Kafin ta karasa maganar da zai yi ne sai Ummee ta dakatar da shi
"Ka ga Yusuf ka kiyaye ni kana ji na ko? Akan me za ka ce ba ya son ta? Ko an tilasta ma sa auren ta ne? Ina da kansa ya amince da zai aure ta ba wanda ya ma sa dole, ka fita a idanuna na."
"Ummee ai ba cewa na yi baya son ta ba, na ce son ta ya fi na sa yawa."
"To sai me ya yi ta fi ma na kai ina mai son naka take?"
Dariya ya yi yana nufar bedroom ɗin sa.
Daga nan ya lalubo lambar wayar Dr mahaifiyarsa ya kira.
Sai dai wayar a kashe take kiran bai shiga ba, don lokacin tana ɗakin tiyata ne za ta cire wa wata mata baby a cikinta. Matar babyn ya mutu a cikinta har ya fara ruɓewa, shi ne Mom take yi ma ta tiyata ta cire gawar babyn.
Ganin kiran bai shiga ba ya tura ma ta text messages.
'AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARE KI MOM. NA KIRA WAYAR A KASHE NA SAN KINA HOSPITAL NE YANZU . FATAN KUNA LAFIYA.'
Bayan ya gama turawa ne ya kira Lambar Mahaifinsa Alhaji Kabir Arzika. Sai dai shi na wayar a kashe.
Tunanin kiran wayar Sadik ƙaninsa ya yi , sai dai shi kuma wayar na ringing ba'a ɗaga ba. Don shi ma Doctor Sadik yana duba marasa lafiya ne wayarsa kuma tana silen ya bar ta a office..
Lambar wayar Abbee ya kira suka gaisa kafin ya tamabaye shi aiki, ya amsa da Alhamdulillah. Daga nan suka ɗan taɓa fira, don shi ma Abbee ba karamin kewarsa ya ji ba. Don shi ma Jalaluddeen yana ƙaunar Abbee wanda sai daga baya ya gane ba shi ne mahaifinsa ba. Don Abbee ya nuna wa Jalaluddeen ƙauna kamar yadda Ummee ta nuna ma sa. Bayan sun ɗan taɓa fira ne ya yi ma sa sallama ya ajiye wayar bayan ya kashe.
_Fahad_
Sai karfe biyar na yamma da Fahad ya kammala abun da yake yi zai je ya ɗauki Nadra.
A kofar gidan ya yi horn maigadi ya wangale ma sa gate ya shiga
Shi sam ya mance da siyayyan kayan abincin da ya yi wa su Abba.
Sai da ya yi parking ya da ma'aikatan gidan suka dinga ɗibar kayan abincin suna kai wa ciki.
Abba saboda zuwan Nadra ya fasa fita ko ina, ya zauna ya ba ta lokacin da suna ta fita .
Sun nuna jin dadin tsarabar da ta siya ma su suna ya godiya ga sanya ma ta albarka .
Suna nan zaune a falon suka ga an fara shigo da kayan abinci. Mamaki ya kama su suna shirin yin tambaya dai diraban su Umma ya ce .
"Mijin Nadra ya ce mu shigo da su ciki."
Store aka ce su shiga da su ciki su ajiye .
Mamaki da al'ajbabi ne ya kama su ganin yawan kayan abincin da ya siya ma su.
Sai da suka gama shiga da su ya ba su kyautar kudi suna ta godiya .
Da sallama ya shiga ciki.
Bayan sun amsa na sa ya karasa ya gaida su.
"Abba ya yi ma sa fadar kayan sun yi yawa ai. Ya ce ba su yi yawa ba ai yi wa kai ne. Godiya da sanya albarka suka dinga yi ma sa.
Umma ta cewa Nadra ta dauki handbag ɗin ta da hijab su tafi.
Marairaice fuska ta yi amma ganin yadda Umma ta murtuke ma ta fuska ya sa ta tashi ta dauki handbag ɗin da hijabi ta saka takalmi suka tafi.
Tun daga ranar suka fara rayuwa mai daɗi, cike da nuna wa juna kulawa rayuwa. A ɗaki ɗaya s gado ɗaya suke kwana.
Sai dai har lokacin Fahad bai sake yunkurin cewa zai yi sex da ita ba. Kamar yadda ya yi ma ta alkawarin cewa ba zai taɓa yi mu'amalar aure da ita ba sai ranar da ta yarda .
Sai dai idan sha'awar ta ta motsa ma sa ya ɗan yi wasanni da ita ya rage zafi. Da zaran ta ga yana neman wuce makaɗi da rawa za ta saka ma sa kuka. Haka zai hakura ya ƙyale ta.
Yau ma bayan ta kammala aikinta da yamma tana zaune a falo ya dawo gidan.
Horn ɗin mota ta ji maigadi ya wangale ma sa gate ya shigo .
Parking ya yi sannan ya fito ya shiga ciki.
Tana zaune a falo ya dawo, yana ganinta ya tsaya daga bakin ƙofa ya ware ma ta hannu alamar ta zo gare shi.
Ba musu ta tashi tana tafiya har ta karasa gabansa ta shige cikin ƙirjinsa ya rungume ta.
Sumbatar ta a goshi ya yi daidai lokacin da wayarsa ta soma ringing.
Ganin bakuwar lamba bai ɗauka ba, ya ja hannunta suka fara tafiya .
"Sannu da dawowa."
Sannu ki ya masa yana zama akan kujera ya zaunar da ita saman cinyarsa.
Kiran aka aka sake yi ta kalle shi ta ce .
"Ka ɗaga ma na ba ka san dalilin kiran ba."
Bai ce ma ta komai ba ya haɗe bakinsu waje ɗaya ya fara aika ma ta da wani zazzafan kiss.
Ba ta hana shi ba sai na mayar ma sa da martani da ta fara yi .
Zare bakinsa ya yi daga nata ya kalle ta da idanunsa da suka fara canza launi zuwa ja ya ce.
"Nadra na gaji da wannan azabtar da ni da kike yi . Idan horo kike yi ma ni akan laifin da na aikata ma ki na horu haka nan ki tausaya ma ni ki ba ni hakkina. Na yi ƙoƙari ai a ce tun daren farkon da muka yi da ke a gidan Baba har yanzu? Kullun idan kika ga ina shirin biyan buƙata ta sai ki saka ma ni kuka? Haka zan haƙura na ƙyale ki. Ba ki tausaya wa halin da nake shiga? Don Allah ki amince ki bari mu raya sunna a wanann daren ki daina tsoro ba zan cutar da ke ba.
Ita kanta ta san ya yi hakuri don haka ta ɗaga ma sa kai alamar ta amince.
Cike da farin ciki ya kara ƙanƙame ta daidai lokacin da kiran wayar ta sake shigiwa wayarsa .
Picking call din ya yi sannan ya saka a hands free.
"Assalamu alaikum."
Suka ji sallamar wani daga cikin wayar.
"Wa'alaika salam."
Ya amsa yana jiran ne na cikin wayar zai ce .
"Kai ne Fahad Umar Majidaɗi?"
"Eh ni ne."
"To ga wata mara lafiya cikin mawuyacin hali take an kawo ta nan asibiti."
"Wani asibiti?"
"Wace ce?"
"Sunan ta Sidra a wayar ta muka samu lambar ka saboda lambar take yawan kira duk da ba mu ga alamar kana amsa kiran nata ba "
Nadra na ji an ce Sidra zumbur ta mike daga cinyarsa tana hawaye.
Kallonta ya yi sannan ya ce.
"Ga ni nan zuwa."
Tana ganin ya mike tsaye ta ce .
"Ɗin Allah zan bi ka mu tafi tare."
Ta yi maganar tana kuka, sanin ba za ta zauna ba ne ya sa ya ce ta dauki hijabi su tafi .
Tana hawaye ta saka hijabi ta bi bayansa suka fice daga cikin falon.
Direbansa ya sa ya kai su yayin da su kuma suka zauna bayan motar yana rarrashinta.
Bayan sun isa ne ya kira lambar da aka kira shi, aka sanar da su cewa tana Aminity word.
Kai tsaye suka shiga suka gan ta kwance kamar gawa.
Nadra ta Fashe da kuka tana tsige bakinta.
Doctor ya kalli Nadra ya ce.
"Wace ce ita?"
"Ƙanwarta ce ita."
"Okay ku same ni a office ɗina."
Bin bayansa suka yi zuwa cikin officer din. Zama suka yi suna jiran jin me zai ce .
"Ina iyayen ta suke ?"
"Ba sa nan za ka iya sanar da mu kai tsaye."
Farin glass din dake idanunsa ya cire ya kalle su daya bayan daya sannan ya ce.
"Ina mai sanar da ku cewa ƴar uwarku Sidra ta kamu da cutar Heart fuilure, da Hausa ana kiran cutar da gazawar zuciya. Saboda zuciya ta daina aiki yadda ya kamata. Gazawar zuciya cuta ce dake faruwa idan zuciya ba ta iya tura jini yadda ya kamata zuwa ga sauran jiki. A yanzu haka cutar ta kai mataki mai tsanani (Advanced stage) zuciyar Sidra ta riga da ta yi nauyi sosai, idan ba ta samu kulawa ko magani ba to rayuwarta za ta iya ƙarewa a cikin watanni. Za ta iya mutuwa a cikin watanni, amma idan ta samu kulawa za ta iya rayuwa fiye da haka sosai. Musamman idan ta samu canjin ruyuwa, magungunan na musamman da kulawar likitoci. Idan har kuna son rayuwar ta ya yi tsayi sosai sai da taimakon ku, yawan saka ta farin ciki to zuciyarta za ta dinga samun sauƙi. Sannan ku dinga ƙara ma ta ƙarfin guiwa. Cin magani abinci mai kyau da kula da ita sosai . Saka ta farin ciki zai taimaka wa jikinta ya yi aiki daidai. Taimakawa ƙwaƙwalwa da zuciya. A guji ɓacin ranta ko shiga damuwa mai tsanani ballantana ta shiga halin bakin ciki ."
Kukan da Nadra ke rike wa tun ɗazu ne ya ƙwace ma ta. Ta tausayawa Auntyn nata sosai .
Ganin haka ya sa Likita ya dinga kwantar ma ta da hankali ta hanyar nuna ma ta cewa wannan fa hasashe ne.
Tashi ta yi a guje ta fita ta nufi ɗakin da aka kwantar da Sidra.
Shi kansa Fahad ya shiga tashin hankali sosai, amma ya aro jarumtaka ya yafa ya sa ba'a gane tashin hankali da yake ciki ba.
Tashi ya yi ya bi bayan Nadra zuwa dakin da 'Sidra take.
_Mom_
Bayan ta fito daga ɗakin tiyata ne ta shiga ɗakunan wasu marasa lafiya ta duba su.
A gajiye ga koma office ɗin ta. Fridge ta buɗe ta dauki ruwan riba mai sanyi ta sha.
Wayoyinta dake kashe ta ɗauka ta kunna su.
Ganin saƙo ya shigo daga babban ɗanta Jalaluddeen.
Jiki na rawa ta shiga bude messages ɗin.
Bayan ta gama karantawa ne ta yi murmushi tare da furta
"Allah ya kare ka ya ba ka nasara a rayuwa."
Soyayyar Jalaluddeen na daban ne a zucuyar Dr, domin ta fi jin sa a zuciyarta fiye da sauran yaranta. Duk da cewar tun yana ɗan shekara ɗaya ta rabu da shi amma har yanzu tana jin sa a ranta ko don ba hannunta ya tashi ba ne oho.
Ko ƙasar idan ta zo tana addu'a Allah ya sa ta zo gaishe su kafin ya koma.
Bayan ta gama duba message ɗin ne ta danna ma sa kira.
Bugu biyu ya ɗauka ta ji sallamarsa cikin muryarsa mai amo.
"Assalamu alaikum."
"Wa'alaika salam."
"Mom ina wuni."
"Lafiya lau Jalaluddeen ya kake ya aikin?"
"Alhamdulillah Mom, na kira bai shiga ba da alama kina asibiti ko?"
"Eh da zan yi operation ne na kashe wayoyin."
"Okay Allah ya sa an yi a sa'a."
"Amin ya rabbil izzati."
"Ka yi magana da Umminka kuwa?"
"Eh mun ji waya yau."
"Okay amma ka dinga kokarin kiranta kullum ka san halinta in dai a kanka ne, dan dole take bari ka yi nisa da su, idan baka kiran wayarta ita ma ba ta samunka takan shiga danuwa sosai .
"To Mom."
"Ka yi waya da Yasmeen?"
"Eh ita ma mun yi waya da ita."
"Ba dai wata matsala ko?"
"Ba komai. Na yi kewar gida."
"To za ka bar aikin ka zo ka gan mu ne ki yaya?"
"Eh zan zo na yi kwana biyu sai na dawo."
"To Allah ya kawo ka lafiya ya kare ka ya ba ka nasara akan abun da ka sa a gaba."
Cikin jin dadi yake amsawa .
Sallama suka yi ya katse kiran wayar.
Daidai lokacin kiran wayar Ma'eesha ke shogowa cikin karamin wayarsa.

💪 𝙅𝘼𝙅𝙄𝙍𝙏𝘼𝙏𝙏𝙐 𝙒𝙍𝙄𝙏𝙀𝙍'𝙎 𝘼𝙎𝙎𝙊𝘾𝙄𝘼𝙏𝙄𝙊𝙉💪✍️
(𝙅.𝙒.𝘼)

Page6️⃣1️⃣
Daidai lokacin kiran Ma'eesha ya shigo cikin karamin wayarsa.
Sai da kiran ya katse sannan ya sake bi bayan kira.
Kiran na shiga wayar ta ta ɗaga tare da yin sallama.
"Assalamu alaikum."
"Wa'alaiki salam."
"Ina wuni ya aikinn?"
"Lafiya lau Alhamdulillah."
"Ma sha Allah."
"Ina fatan kina lafiya, kuma ba wata matsala ko?"
"Gaskiya ba zan samu kwanciyar ba sai na ga dawowar ka gida?"
Murmushi mai sauti ya yi kafin ya ce.
"Ki kwantar da hankali in sha Allah ba wata matsala da za ta biyo baya. Gobe ma in sha Allah zan yi tafiya ta kwana biyu?"
Cikin tashin hankali ta ce.
"A'a, a'a, a'a don Allah, ina za ka je wa kake da shi?"
"Yanzu ne nake jin labarin an samu wasu da suka dawo a ƙauyen mu,.ina son na je na duba ko akwai dangina a cikinsusu."
Shiru ta yi kafin ta ce.
"Amma ai bai kamata ka tafi kai kadai ba cikin halin da kake ciki, bugu da ƙari kuma ai ba ka da kuɗin mota."
"Eh haka ne ba na da kuɗin mota, amma akwai motar ɗaukar kaya da za ta tafi Adamawa . Zan bi motar na zauna ko a samun buhuhunan kayan dake bayan motar ne?"
"Shiru ta yi kafin ta yi wani tunani ta ce."
"Ma su motar za su bari ka bi su ne?"
"Eh suna bari ai, har mun yi magana da direba motar."
"Gaskiya bai kamata ka tafi kai kaɗai ba sai dai mu tafi tare."
"Bari na dawo sai mu yi magana."
"Okay sai ka dawo."
Daga haka nan ya katse kiran wayar yana tunanin hanyar da zai ɓullowa Ma'eesha.
Tashi ya yi yana kokarin barin wajen hotel ɗin don zuwa shawo kan Ma'eesha.
_Nadra_
Tana zaune saman kujerar gaban gadon da Sidra take kwance. Tana rike da hannun Sidra ta zuba ma ta idanun ta da suka rikiɗe zuwa ja sakamakon kukan da ta sha. Sidra tana barci ba ta ma san me ke faruwa ba, yayin da Fahad yake tsaye jingine da bango ya rungume hannayensa a ƙirji ya zuba ma su idanu.
Turo ƙofar aka yi da sallama. Gabdaya suka amsa Nadra na ƙokarin goge hawayen da ke idanunta.
Baba, Mama, Inna, sai kuma Rumaisa su ne suka shigo cikin ɗakin. Fahad ya yaushe su suka masa suna yi ma sa ya mai jiki. Sai kuma Nadra ta gaishe su suka amsa suna tambayar ta ya mai jiki.
Tambayar ba'asi suka yi Fahad ya yi ma su bayanin da Doctor ya yi ma su. Tabbas hankalin su ya tashi matuƙa kuma sun tausaya wa Sidra.
Baba ya kira Abban su Sidra yake sanar da shi halin da Sidra take ciki .
Buɗar bakinsa ya ce Allah ya ba ta lafiya. Daga haka ya yi ma sa sallama ya kashe wayarsa. Baba yana matukar mamaki irin zafi da kafiya da Abba yake da shi.
Kwanan Sidra uku a asibiti Nadra da Fahad ke tare da ita. Sai dai kullum sai su Mama sun zo gaishe su, kuma su suke aiko da abincin safe da rana da kuma dare.
Ranar da za'ayi discharging nasu daga asibiti kowa na nan. Baba, Mama, Inna. Bayan likita ya ba su shawarwarin yadda za'a kula da ita da kuma da kiyaye ɓacin ranta ya kuma rubuta ma su magunguna.
Sidra ta kalle su ɗaya bayan ɗaya, ta san gidan Baba za ta koma wanda ba za ta so hakan ba, don haka ta kalli kowa sannan ta fara magana cikin sanyin murya.
"Ina ji a jikina kamar ba zan daɗe a duniya ba, iyayena sun juya ma ni baya. Don haka ina son na rayu tare da ƴar uwata Nadra. Ina son na ganni a kusa da ita don idan na mutu ina tare da ita buƙatata ta biya, ta wani ɓangaren zan ji kamar ina tare da ajalinsa ne "
Shiru ɗakin ya ɗauka na tsawon mintinan biyu ba wanda ya yi magana, kafin ta sake yin magana ta ce .
"Baba, Mama, da kuma Inna, don Allah ku yi hakuri ban raina abun da kuka yi ma ni ba amma ina neman alfarma ku bar ni ta koma gidan Nadra da zama zan yi farin ciki da hakan."
Caraf ina ta yi saurin cewa.
"Ta ya ya za ki koma gidan ƙanwarki da zama? Nadra fa ƙanwarki ce ba Yayar ki ba, ai abun ba tsari."
"Inna ku yi hakuri ku bar ta ta koma gidan nawa, tana son kasancewa da ni, kuma ga halin da take ciki ko kin manta abun da Doctor ya ce ne na a dinga yi ma ta abun da take so?"
"Ke dalla maganar Doctor maganar Allah ce?"
"Inna tun da ita ma ƙanwar ta goyi bayan hakan ki bar su kawai Allah ya ba ta lafiya."
Shi dai Fahad bai ce komai ba ya kau fa kansa gefe. Nadra ta kalle shi ta ce.
Yaya Fahad ka amince ta koma gidanka da zama? Zan yi farin ciki ni ma ita ma haka za ta yi farin ciki da hakan, a halin yanzu ba ta da wanda ya fi ni , Please ka amince ma ni."
"Duk yadda kike so ki yi ai gidanki ne."
Ba ta san lokacin da murmushi ya suɓuce ma ta ba ta shiga yi ma sa godiya. Ita dai Mama ba ta ce komai ba, amma fa dukkan alama ba ta so hakan ba.
_Makaho_
Da sallama ya shigo cikin gidan. Ma'eesha dake zaune kan tabarma ta haɗa tagumi tana tunanin tafiyar da ya ce zai yi.
"Amin wa'alaika salam."
Ta amsa tana mikewa tsaye ta nufi in da yake.
"Sannu da zuwa."
Ta ce tana amsar kayan aikinsa dake hannunsa.
"Yauwa sannu mar'atussaliha."
"Ka zauna ga tabarma nan a gabanka."
Ita kuma ta nufi ɗaki ta ajiye ma sa kayan shoe maker nasa.
Pure watar dake cikin leda ta ɗauko ta kawo ma sa, sannan ta kawo ma sa abuncin da ta dafa. Shinkafa da wake da mai da yaji ta dafa.
Ruwan ya fara sha sannan ya fara cin abincin. Tana yi ma sa fifita tana yi ma sa fira cike da shauƙi.
Sai da ya ci kusan rabin abincin sannan ya yi hamdala tare da yi ma ta godiya .
"Na gode Allah ya yi ma ki albarka ya kawo ranar da zan saka ma ki hidima da sadaukarwar da kika yi akaina."
Murmushi ta yi tana cewa.
"Amin Mijina. Dama ina son mu tattauna kan zancen tafiyarka ne, yanzu tafiya za ka yi ka bar ni ni kaɗai?"
"Ki yi haƙuri Ma'eesha ba daɗewa zan yi ba zan dawo, in sha Allah ba zan wuce kwana biyu ba zan dawo."
"To kana da tabbacin cewa su ɗin danginka ne wadan da aka ce sun dawo?"
"Eh to ban sani ba sai na je na tabbatar."
"Idan ba danginka ba ne fa?"
"Sai na dawo mu cigaba da rayuwa a haka."
"Idan kuma ya kasance su danginka ne za ka dawo ka ɗauke ni mu koma can ne da zama?"
"Ba zancen komawa can da zama, domin garin da babu kwanciyar hankali me ake yi da shi? Ko su na ba barinsu zan yi ba za mu dawo nan ne su nemi sana'ar yi."
"Amma ina tsoron zama gida ni kaɗai ba kowa a kusa da ni."
Shiru ya yi yana nazarin abun yi kafin ya ce .
"Zan yi magana da Mallam Liman ya taimaka ma na da jikarsa A'isha, na ga jininki ya haɗu da yarinyar sosai har takan shigo ko?"
Jingina kai ta yi tana cewa
"A'isha mutumiyata ce ita takan shigo ita da kakarta, lokacin da nake siyar da gawayi ita take ɗaura mun."
"Haka ne, zan nemi Alfarma wajen Mahaifinta ."
"To na gode."
Ta faɗa tana murmushi.
"Yauwa kina ji na ko?"
"Eh ina ji."
Ta tattara hankalin ta da nutsuwar ya zuwa gare shi.
"Akwai wata mata da take ba wa mata tallafin kuɗi domin su yi kasuwanci, jiya mun je tare da abokan zamana na wajen sana'ar. Mun same ta ta kuma yi alƙwarin taimakawa ma na, wato za ta ba Matayen mu jarin da za su yi sana'a. In sha Allah ina saka ran kina ciki. Na bayar da sunan ki da lambar wayarki za ki iya jin kira kowane lokaci.
Cike da farin ciki take kallon sa tana murmushi.
"Allah ya sa mu ji alkhairi."
"Amin ya Allah."
"Bari na je masallaci idan na hadu da Mallam Liman zan sanar da shi komai .
Ruwa a buta ta kawo masa a buta ya yi alwala ya nufi masallaci.
A daren ranar bayan an gama sallar isha'i ya sanarwa Mallam Liman zancen A'isha .
Kai tsaye ya amince ma sa tare da yi masa addu'ar Allah ya sanya alkhairi.
Washegari tun da asuba ya yi wanka ya shirya. Ya nufi masallaci don yin sallar asuba.
Ana idar da Sallah bai zauna Kamar yadda ya saba zama ba, kasancewa tafiya da zai yi.
Duk wasu muhimman abubuwan da zai bukata dama tun cikin dare ya haɗa su a cikin jakar kayansa .
Sai kayan sakawar sa kala ɗaya ya ɗauka, su ma kayan ya ɗauka ne saboda kada Ma'eesha ta yi magana kai.
Ba ta yi kokarin haɗa ma sa breakfast ba kamar yadda ta so, shi kuma ya ɗauka saboda zai yi asubanci ne ba ta yi ba, yayin da ita kuma ta ɓangaren ta babu komai a gidan na ci ne da za su ci ya saka ba ta yi wani yunƙuri ba. Kuma ta san ko da ta faɗa ma sa babu abun da za su ci a gidan bai da kudi sai dai ya kara shiga damuwa.
Don haka ya yi shiru ba tare da da nuna damuwa ba.
Ta rike ma sa jakar yayin da shi kuma ya lalubi sanadar jagoransa ya fara tafiya.
Suna zuwa kofar gidan ya haka ta fita ya ce ta koma ba sai ta raka shi ba. Gani take yi kamar idan ya tafi ba zai dawo ba.
Har ya fara tafiya sai ta rike hannunsa, ya kalli hannun ya kalle ta.
"Gani nake yi kamar idan ka tafi ba za ka dawo ba, ina tsoron wani abu ya same ka yadda ka bani labarin garinku na tsorata da shi, idan na rasa ka ya rayuwa ta za ta kasance a wanan duniyar fa ba na da kowa?"
"Kina da kowa Ma'eesha, ki jira lokaci in sha Allah wata rana sai labari, na yi ma ki alkawarin zan nemo ma ki dangin mahaifiyar ki s duk in da suke a faɗin duniyar nan."
Murmushi ta yi tana goge hawaye ta ce .
"Ta ina za ka fara neman su? Wacce ko ita mahaifiyar rawa ba ta san komai ba akan ta, tun tana yarinya karama aka kai ta gidan marayun, wanda ita ma bude ido ta yi ta ga kanta a cikin gidan. Kada ka yi ma ni alkawarin da ka san ba za ka iya cika shi ba."
"Zan iya ."
Ya faɗa cike da kwarin gwiwa.
Murmushi kawai ta yi don ta san ba abu ba ne mai sauƙi.
Sai da ya tabbatar ya kwantar ma ta da hankali ta samu nutsuwa sannan ya yi ma ta sallama ya tafi.
Yana tafiya rataye da jakar da ya karba a hannun ta fatan hannunsa da sanadar jagoransa.
Tana kallon sa har sai da ya ɓacewa ganinta sannan ta koma cikin gidan tana fashewa da kuka.
Yana fitowa daga layin kasancewar gari bai yi gama haske ba, don haka ba mutane.
Wata baƙar baƙar mota ce take gefen titi, kai tsaye ya nufi motar, kafin ya karasa matuƙin motar ya fito da sauri ya zo ya bude ka sa bayan motar.
Shiga ya yi sannan ya rufe masa murfin ya zagaya mazaunin direba ya shiga tare da yi wa motar key.
Kai tsaye hotel suka nufa, yana shiga ɗakinsa ya yi wanka.
Ya shirya cikin tsadaddun suit black shirt din ciki White me sai tie Black and white. Sai ƙamshin tsadaddun turarensa yake yi, ya daura agogon hannunsa ya sanya takalmi.
Ba jimawa ya gama shirin sa. Sai dai ya canza jaka, ba wacce ya bar gida da ita zai tafi ba, sannan kayan da ya dauko a can gidan ma ya bar su a can bai zo da su ba. Wayoyinsa da mahimman abubuwan da zai bukata ya ɗauka.
Wayarsa wacce Ma'eesha ta siya ma sa ce ya ɗauka yana kallon wayar kafin ya kashe ta.
Futowa ya yi ya nufi motar kai tsaya, direban ya bude ma sa da sauri cikin girmamawa.
Kai tsaye suka nufi airport, wanda isar su ba jimawa jirgi ya tashi.
Direban ya juya da motar ɗin don komawa, bayan jirgin su ya ɗaga.
Ba wanda ya sanar wa zancen dawowar sa, don haka ba wanda ya yi tunanin dawowarsa.
Sai bayan saukar jirgin su ne ya fito daga cikin jirgin. Cike da mamaki da al'ajabi yake kallon motar gabansa. A hankali ba cikin motar ya ziro ƙafarsa wajen yana sakar ma sa sanyayyen murmushi.

Page6️⃣2️⃣
Sai bayan saukar jirgin su ne ya fito daga cikin jirgin. Cike da mamaki da al'ajabi yake kallon motar gabansa, a hankali na cikin motar ya ziro ƙafarsa wajen yana sakar ma sa sanyayyen murmushi.
"Sadik?"
"Na'am Yaya Jalal."
"Wa ya faɗa ma ka tasowa ta?"
"Babu na dai ritsa ka ne. Tun shekaranjiya da kuka yi waya fa Mom ka sanar da ita za ka dawo nan fa kwanaki biyu, shi ne yau na ce ko kwana ne sai dai na yi a airport amma sai na je na ɗaukoka."
Ya yi maganar yana rungume Yayan nasa, hakan ya sa shi ma ya rungume shi .
Sake juna suka yi yayin da da Sadik ya karɓi jakar hannun Jalaluddeen ya sa a bayan motar. Sannan ya bude wa Jalaluddeen gaban Mota wajen me zaman banza yayin da shi kuma ya zagaya mazaunin direba ya yi wa motar key suka bar airport ɗin.
Yana tsaka fa driving yayin da shi kuma Jalaluddeen ya ya kunna wayoyinsa, amma bai kunna na wajen Ma'eesha ba.
Hankalinsa na kan waya ne ya ɗago yana kallon Sadik, saboda ya san airport da gidan Ummee ba nisa, ya ci a ce sun karasa gida.
Da mamaki yake kallon Sadik yana kuma kallon hanya,."
"Kai Mallam ina za ka kai Ni ne?"
"Gida mana."
"Wannan ne hanayar gidan?"
"Eh ma na, hanyar gidan iyayen asali ba na iyayen riƙo ba. Haka kawai kullum idan ka dawo daga tafiya sai ka sayka can?"
"Sadik kana da rigima, yi ina kake so na sauka idan ba can ba?"
"A'a gaskiya Yaya Jalal tun da Allah ya sa ka san cewa ba Ummee ba ce ta haife ka Mom ce ko? To ya kamata ko sau ɗaya ka yi ma ta abun da za ta ji cewa ita ma uwa ce tana da kai, ba komai ba nake so ka yi illa iyaka ka sauka a gidan kuma ka kwana tare da mu, mun gaji da sai dai ka zo ka gaishe mu na mintinan ka tafi. To yanzu ba wanann zuwan kana tare da mu dai gobe ka tafi can gidan. Amma fa ka kashe watoyin ka."
Kafin ya yi magana har sun iso gidan
Horn Sadik ya yi a kofar gidan , yayin da wani security taso ya wangale ma su katafaren tangamemen gate din gidan.
Ya cinna hancin motar a katafaren gidan, kai tsaye parking lot ya nufa, in da aka tars manyan motoci na alfarma. Ke wajan .
Fitowa ya yi bayan Sadik ya bude ma sa murfin motar
Sadik ya ɗauki jakar kayansa suka nufi cikin gidan..
Ma'aikatan na ma sannu da zuwa ga hannu kwanan yake amsa ma su.
Yana tura kofar tare da sallama. Mom wacce ta fito don uwa asibiti ta amsa tana kallonsa da mamaki.
Don ba ta san ya iso ba, kuma ba ta yi tsammanin ganinsa a gidanta ba, don ko da ta faɗawa Sadik dawowar Jalal ta ɗsuka asibiti ya tafi ashe shi ɗauko Yayansa ya je ba.
Ganin Sadik da jaka ya sa ta game cewa ɗaukimo Jalaluddeen ya tafi.
"Mom ba ki ga yae8n ki ba, can na tafi na ce ko zan kwana a can sai na je na ɗauko shi na kawo shi nan zuwa gobe ya tafi can."
"Yaushe wanna Gwaggon ta ku Maryam za ta bar shi ya kwana s nan."
"Ba za ta san ya zo ba, ko ta sani ma menene ne ai ina ce nan ne guda. Mahaifinsa na asali ta isa ta hana shi shi ne?"
"Amma yanzu ...."
Sai ta fasa maganar da za ta yi .
"Ya karasa har cikin falin Mom na kallonsa duk da ta ga ya nufo ta amma ba ta san nufin sa ba sai da ta ji ya rungume ta.
Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta saki, shi ma wani ƙaunar mahaifiyar tasa ne yake Ratsa zuciyarsa .
Ya durƙuda kasa ya gaishe ta, ta amsa tana tambayar da aiki, ya amsa da Alhamdulillah.
"Ka je ka yi wanka ka fito ka ci abinci."
"Ina Sadduƙa?"
"Ta tafi school."
Ya nufi ɗakin da ya ga Sadik ya kai ma sa kayansa. Ta bi shi da kallo tana jin ƙaunar ɗan nata har ranta.
_Fahad_
Bayan an yi discharging na Sidra a asibiti ya dauke ta ita da Nadra zuwa gida, kamar yadda Nadra ta buƙata. Baba da Mama da Inna kuma suka nufi gida tun da Sidra ta ki yarda ta bi su kuma Nadra ta roki Fahad ya amince ta bi su, ba shi da wani zaɓin da ya wuce ya amince ko don farin cikin Nadra.
Yana driving Nadra na gefen sa yayin da Sidra ke bayan motar.
Shiru ba abun da kake ji a cikin motar sai sanyin A.C da mayen turaren da Fahad ke amfani da shi.
Har suka karasa gidan kowa ya kasa cewa komai.
Horn ya yi Maigadi ya wangale ma sa ƙofa ya cinna hancin motar a cikin gidan.
Bayan ya yi parking ne Nadra ta fara fitowa daga motar, sannan ta bude wa Sidra ta fito.
"Sannu Aunty."
Ta faɗa cike da kulawa. A hankali Sidra ta fito tana jinjina ma ta kai ba tare da ta amsa ba.
Kayan da suka dawo da su daga asibitin Nadra ta dauka a bayan motar.
Fahad ya fito ba tare da ya ce komai ba ya nufi kofar shiga fakon. Sai sam babu walwala s fuskarsa .
Bude ƙofar ya yi ya matsa gefe alamar su shiga ciki.
Da sallama a bakin Nadra ta shiga Sidra na bayanta, shi kuma ya take ma su baya.
Kai tsaye upstairs ya nufa suna bayansa ƙarar taka step ya ji ya juyo ya kalle su. Ganin alamar cewa a sama Nadra ke niyyar ba wa Sidra masauki ne ya sa shi cewa.
"A ƙasa masaukin baƙi yake ko kin manta ne?"
"Yaya Fahad Aunty Sidra ce fa Yayata ce?"
"Na sani shi ya sa nake tunatar da ke a ƙasa masaukin baƙi yake, ba wai don yayarki ba ko Yayata ce ta zo a ƙasa za'a sauke ta. Nan saman iya na ma su gidan sai ɗakunan yaran da za mu haifa in sha Allah."
Yana gama faɗar haka ya ci gaba da tafiya zuwa ɗakinsa ya shige.
Murmushi Nadra ta ƙaƙaro don son ta kwantarwa da Sidra hankali ta ce.
"Na tuna ma Aunty ba ɗaki a nan sai ƙasa mu sauka na raka ki?"
Wani kallo Sidra ta yi wa Nadra kafin ta ce .
"Ban gane ba ɗaki ba, ko kin manta ni na faɗi irin tsarin da nake so sannan aka bi tsarin da na so wajen gina gidan . Ko kin manta da suna na aka gina gidan? Ɗakuna biyar ne a ciki, ɗaki ɗaki ɗaya naki ɗaya nasa sauran ɗakuna uku ba kowa a ciki shi ne ba za ku iya bani ɗaya na, ta yadda za ku dinga jin motsina ba? Ba komai na gode."
Tana faɗar haka ta juya da sauri ta fara sauka daga matattakalar kai tsaye ta nufi ɗakin baƙi ta shige da sauri.
_Jalaluddeen_
Yana shiga cikin ɗakin ya zube kan tangamemen gadon dake cikin ɗakin. Sanyin A.C da ƙamshin room freshner na ratsa shi. Kasancewar Sadik ya gyara ma sa ɗakin.
Sai da ya kwashe tsawon mintuna ashirin kafin ya mike ya fara rage kayan jikinsa.
Bathroom ya shiga ya wanda shi ma kansa abun kallo ne, tsaya wa ya yi yana kallon kansa a jikin tangamemen mirror dake jikin bangon banɗakin.
Shi kansa ya san ya ɗan rame. Daidaita ruwan 🚿 dake bathroom din ya yi daidai yadda yake so bai yi zafi ba kuma bai yi sanyi ba .
Shower gel ya ɗauka ya yi wanka da shi. Dai fa ya kammala wankan sannan ya fito sanye da bathrobe sai wani karamin towel da yake goge ruwan kansa.
Jakar kayansa ya bude ya fito da ƙananan kayan da zai saka.
Ya shirya cikin ƙananan kayan da ya zo da su a jaka ya fesa turarensa mai ƙamshi.
Babu tunanin da yake yi kamar na Ma'eesha yadda ya fito daga gidan take kuka. Tausayinn ta mai tsanani ne ya kama shi .
Ɗaya daga cikin wayoyinsa ya ɗauka ya lalubo wata lambar ya danna ma ta kira.
Bugu ɗaya aka ɗaga daga can ɓangaren aka ce.
"Barka da rana yallaɓal."
"Barka dai Adamu ya kake?"
"Lafiya lau sir."
"Yauwa kamar yadda na faɗa ma ka za ka nemi mata guda biyu wadanda kake mu'amala da su, ka ba su Naira dubu ɗari biyar ₦500,000 su kai kuɗin zuwa ga gidan da na sanar da kai su faɗa wa matar gidan cewa tallafi ne wanda mijinta makaho ya sanar da ita za'a ba su."
"Okay sir, yanzu ba sa nan sai zuwa yamma za su shigo garin, in sha Allah zuwa gobe da safe saƙon ka zai isa zuwa gidan da ka ce."
"To na gode."
"Ba komai Yallaɓal."
Sallama suka yi ya katse kiran wayar.
Yana ajiye wayar sai aka turo ƙofar da ƙarfi, ba kowa ba ce illa Sadiƙa ta shigo aguje ta shigo rungume shi cike da murna.
"Yaya Jalala you are welcome."
"Thank you."
Sakin sa ta yi tana murmushi tare da cewa.
"Wallahi yanzu Yaya Sadik ya kira ni yake sanar da ni, ai tuni na bar school na dawo gida saboda kai."
Daidai lokacin Sadik shi ma ya shigo yana cewa
"Food is ready."
Gabadaya suka fita daga ɗakin suka nufi dinning area.
Mom na zaune tana kallonsa yadda suka fito a jere fuskar kowannen su ɗauke da annuri. Farin ciki ne yake ji har kasan ranta.
Masu aiki biyu ne tsaye a wajen suna jiran ma su gidan su buƙaci abun da za'a zuba ma su sai su zuba ma su.
Sadik ne ya ja wa Ya Jalal kujera ya zauna sanan suka zazzauna.
Ma su aikin ne suka yi serving na su bayan sun faɗi abun da suke so su ci.
Kasa cin komai ya yi sakamakon tuna Ma'eesha da ya yi, shin ta samu abun da ta ci ko ba ta samu ba, don ya lura kwana biyun nan sai kame-kamen abinci take yi.
Tsintar kansa ya yi cikin yanayi na rashin jin dadi wanda take komai nasa ya sauya.
Tashi ya yi daga dinning area din ya nufi ɗakinsa. Da kallo suka bi shi ganin yadda ya sauya nan take.
_Ma'eesha_
Bayan tafiyar mijinta ta zauna ta ci kuka ta ƙoshi, babu mai rarrashinta. Har sai da ta ji kanta ya fara ciwo sannan ta dakata, hatta idanun ta a kumbure suke. Gani take kamar za ta rasa shi, kuma su ma su motar duk da ya ce ma ta motar kaya ne a saman kaya zai zauna shin zai iya kula da kansa a matsayin sa na makaho a wanan doguwar tafiyar.
Da wanan tunanin ta yini har rana ta fito ba ta yi breakfast ba.
Bugu da ƙari ba ta da komai a gidan da za ta ci, kuma ba ta da ko sisi da za ta siya abun da za ta ci.
Wasa-wasa har karfe biyu na rana ba ta ci komai ba, karshe ma zazzaɓi ne ya rufe ta ta kwanta saman katifarta. Wayar ta ta janyo ta lalubo lambar makaho amma switch off. A haka har ya fara rawar sanyi ta duƙunƙune kanta.
Addu'o'i kawai take yi a cikin zuciyarta tana addu'ar Allah ya yaye ma ta ya kare ma ta mijinta a duk in da yake.
_Sidra_
Tana nufar ɗakin baƙi maganar Fahad ne ke yi ma ta amsa kuwa a cikin kunnenta.
'Nan saman iya na ma su gidan ne dai ɗakunan yaran da za mu haifa in sha Allah.'
Tana shiga dakin ba ta rufe kofar ba ta zube a ƙasa, Nadra da ta kasa motsi ta jiyo sautin faɗiwar abu timm.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce✍️
https://chat.whatsapp.com/E8JgnaAUG13CRwJbYeXImE?mode=gi_t
🌲🌳🌿☘️
*TALLAH!*
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*

Page6️⃣3️⃣
Tana shiga ɗakin baƙin ba ta rufe kofar ba ta a ƙasa. Nadra da ta kasa motsi ta ji yi sautin faɗiwar abu timm.
Da hanzarin ta sauko daga matattakalar, ɗakin ta nufa kai tsaye har da ɗan gudun ta, tana shiga ta yi tozali da Sidra kwance ba ta motsi .
Durƙusawa ta yi akan ta tana kuka tana jijjiga ta tare da kiran sunan ta .
"Wayyo Allah na Aunty Sidra ki tashi don Allah Aunty Sidra ."
Ta mike daga durƙuson da take ganin Sunyi Sidra ba ta mike ba ya sa ta nufi upstairs tama ihun kiran sunan Fahad.
_Jalaluddeen_
Tun da ya kasa cin abinci a dinning area ya shiga ɗakinsa ya zauna kan gadon. Sai kuma ya mike ya tashi ya rufe kofar ta hanyar mirza wa kofar key ya bar key din a jikin ƙofar.
Wayar da Ma'eesha ta siya ma sa ne ya ɗauka tare da lalubo lambar wayar ta.
Kira ya danna ma ta zuwa lokacin gabansa ya ji yana faɗuwa.
_Ma'eesha_
Tana nan kwance tana rawar sanyi ne ta ji ringing din wayar , duk da dai ba ta ga ko sunan waye ba amma dai ta lulubi wayar ta sannan wajen amsa kira tana kara wayar a kunne.
"Assalamu alaikum warahmatullah."
Ta ji saukar muryarsa mai amo a cikin dodon kunnenta.
Ba ta san lokacin da ta bude kumburarrun idanunta ba tana cewa.
"Wa'alaika Salam warahmatullah."
Muryarta da ya ji ba ta fita sosai kuma tana wayar kamar wacce take a galabaice ya saka shi cewa.
"Ma'eesha lafiya kike kuwa?"
Da kyar ta iya cewa .
"Lafiya lau nake kada ka sami damuwa ba komai."
"Kamar ua ba komai bayan muryarki ma ta nuna cewa kina cikin mawuyacin hali , ba ki tana yi ma ni karya ba kada ki soma a yanzu ."
Dafe kanta dake sara ma ta ta yi kafin ta ce.
"Kaina ke ciki amma kada ka damu zan wartsake In sha Allah."
"Kin ci abinci ne?"
"A'a ban ci ba."
Shiru ya yi kafin ya ce.
"Ba abuncin ko?"
"Eh."
Ta ba shi amsa a taƙaice. Wanda take idanunsa suka sauya ya katse kiran wayar .
Daya daga cikin wayoyinsa ya ɗauka ya kira wata lamba, ana ɗagawa cikin bayar da umarni ya fara magana .
"Adamu ba lokacin da zan tsaya jiran sai wasu sun dawo. Yanzu ba sai an jima ba ka nemi wasu matan guda biyu ja ba su saƙon ka sanar da su yadda za su yi sannan idan sun fito daga gidan ja biya su hakkin aikin da suka yi. A tare za ku je ka jira su a wajen gidan.
Yana gama faɗar haka ya kashe wayarsa ya ajiye gefe, tausayi da kewar Ma'eesha suka addabe shi.
Ma'eesha kam dama da kyar take amsa ma sa don haka ta saki wayar tana dafe kanta
Bayan kamar mintinan arba'in kenan sai ta dinga jin sautin sallama a tsakar gidan ,
Da ƙyar ta iya amsawa da muryarta da ba ta fita sosai.
Ta yunƙura ta tashi zaune, hijabiinta ta laluba ta saka, sannan ta dafe bango tana tafiya .
Ta bude kabulen daidai lokacin daidai lokacin da suke sake yin sallama.
Ta amsa suna haɗa idanu da matan guda biyu.
"Sannun ku bayin Allah."
"Yauwa sannu."
"Nan ne gidan Khalifa Makaho?"
"Eh nan ne."
"To ina fatan ya sanar da ke zancen tallafin kuɗi da ake ba wa mata don su yi sana'a su dogara da kansu."
"Eh ya sanar da ni ya bayar da sunana ina sha Allah za mu samu."
"Haka ne."
Wata karamar jaka suka mika ma ta suna cewa ta samu dana'ar da za ta yi don dogaro kai.
"In sha Allah.."
Ta karba tana yin godiya zuciyarta cike da murna
Komawa ta yi cikin ɗakin ta juya kuɗin.
Bandir ɗin Naira dubu ɗaya ne guda biyar, wato Naira dubu ɗari biyar kenan.
Farin ciki ya cika ta ta ɗebi wasu daga cikin kuɗin ta mayar da saura.n a leda ta saka cikin akwatin kayan ta .
Daidai lokacin ta ji sallame A'isha. Hamdala ta yi tana jingina da bango ta amsa sallama.
A'isha ta shigo tana cewa.
"Sannu Aunty ina wuni ."
Ta amsa na ta sanan ba kuma ma ta dubu ɗaya ta ce .
"Ki siyo mun milo da madara da sigar."
"Aunty bread fa,?'
"Ba zan iya ci ba ku siyo mun kawai na sha yunwa nake ji ban karya ba."
,"subhanah har rana ta yi?"
"Ba na jin dadi ne."
Da hanzarin A'isha ta fita daga gidan don zuwa siyo manta kayan tea.
Ba jimawa ta dawo ta shigo da kayan tea din a cikin baƙar leda.
Ta duba flaks cikin ikon Allah ta samu akwai ruwan zafi a ciki. Nan da nan ta haɗa ma ta tea.
Ita ta taimaka ma ta ta je ta wanke baki, sanan ta ba ta ruwan tea ɗin ta sha.
Kallon A'isha ta yi kafin ta ce .
,A'isha bari na kira Yaya Khalifa a waya na sanar da shi zan tafi asibiti."
Ta ji maganar tana jingine jikinta da bangon ɗakin
"To Aunty Ma'eesha."
Lambar wayarsa ta lalubo ta danna ma sa kira amma ba ta shiga ba. Dai da ta gwada kira har sau uku kiran bai shiga ba, kallon A'isha ta yi kafin ta ce .
"Wayarsa ba ta shiga bari ba aike ki Chemist ki ce ya haɗa ma ki maganin zazzabin maleria."
Ta yi maganar tana janyo kuɗi ta ba ta 3k ta ce ta je da shi. Karɓa ta yi tana yi ma ta sallama ta tafi.
"Ba jimawa sai ga ta ta dawo da ladar magunguna.
Zuwa lokacin ta tarar har ta fara barci . Sai da ta tayar da ita sannan ta tashi ta sha magungunan ta ba ta canjin Naira ɗari biyar.
Tana gama shan maganin ta kwanta barci ya dauke ta nan da nan.
A'isha ta tashi ta awa taya ta gyaran gidan.
Ba iya zazzaɓi ne ke damu ta ba, har da tafiyar makaho ya dame ta, domin kuwa kewar sa na daya daga cikin abun da ke sa tana jin wani iri a tare da ita .
Shi ma a nasa bangaren haka ne, domin kuwa tun da ya tuna ya ya kasa cin abinci. Ji yake yi kamar ya rufe idanu ya tsinci kansa a gaban ta. Sai ya ji farin ciki da yake yi da tafiyar duk ya rasa. Duk da cewar yanzu yana a lafiyayen gida na alfarma. Ga komai da ake bukata na more rayuwa amma ji yake yi rayuwa a wancan. Akulkin gidan tare da Ma'eesha yake bege.
*Jan hankali.*
Wani lokaci mace tana jin kamar idan ta biya wa mijinta bukatu, yi masa girki kala-kala, gyara jiki, , ta tsaftace jikinta ciki da waje girmamawa, ladabi biyayya, kwantar da kai… to zata iya gamsar da mijinta 100%.
Sai dai gaskiya ɗaya ce
Mace ba za ta iya cika dukkan muradan mijinta ba, kamar yadda shima ba zai iya cika nata ba.
Saboda dan Adam bashi da iyaka a bukata. Yau yana son shiru, gobe yana son hira. Yau yana son tuwo, gobe yana son noodles. Yau yana so ki zauna da shi sosai, gobe yana buƙatar sarari. Yau yana so ki yi masa magana da tausayi, gobe yana fushi saboda wani abu da ba ki yi ba, Zuciyar mutum tana canzawa. Rayuwa tana da nauyi.
Ki yi niyyar kyautatawa saboda Allah, ba don yawan yabo ba.
Ki fahimci cewa mijinki ba kullum yana buƙatar abu iri ɗaya ba, yau soyayya, gobe space.
Ki gina kwanakinki da basira ki dinga karanta sauyin yanayinsa.
Ki yawaita addu’a sosai. Saboda ko kina da niyyar gamsar da shi, idan ALLAH bai sa kin gane hanyar ba, zai zama kamar ba kya yi.
Mace mai basira ba wadda ta iya komai ba ce,
Ita ce wadda ta san iyakokinta, amma tana kokari da zuciya ɗaya.
Ita ce wadda ta mayar da gida masaukin salama, ko da mijin yana da tabo.
Kuma hakan yana da girma fiye da zama kammalalliyar mace. Girmama ƙoƙari shine soyayya.
Shi kansa ya san tabbas Ma'eesha na son sa kuma so na haƙiƙa
Knocking ƙofar da aka yi ne ya dawo da shi cikin tuanin da ya lula.
Mom ce ta shigo da sallama , ya amsa ma ta yana zaune kan gado, yayin da ta zauna saman bed side tana karantar yanayinsa.
"Wace ce ita?"
Da sauri ya kalle ta yana mamakin tambayar da ta yi ma sa.
"Na ce wace ce ita?"
Nan ma sake kallon ta ya yi ya kasa cewa komai.
"Mom wai akan wa kike magana ?"
"Akan wacce kake tunani da har ka kasa cin komai saboda ita ."
"Ni Mom ba wacce tunanin ta zai hana ni cin abinci."
"Ga shi kuwa na gani."
"Eh to ni wace mace zan yi tunanin ta bayan Yasmeen da kika sani, ita kadai ce."
Ya yi maganar kansa a ƙasa ya kasa hada idanunsa da mahaifiyar tasa.
Murmushi irin ta su ta manya ta yi kafin ta ce.
"Idan har tunanin Yasmeen ne a cikin zuciyarka to da ka tashi yanzu ka karasa in da yake ka gan ta, saboda gari daya kuke a yanzu. To ya kamata ka sani ka cire tuanin kowace mace a zuciyarka ka san meye a ƙasa ba sai na faɗa ma ka ba. Ba ka isa ka fito da wani zancen wata mace bayan Yasmeen ba don haka kada ka fara abun da ka san ba zai yiwu ba."
Wayar ta ta ɗauka ta danna kira bugu ɗaya aka ɗaga.
"Kawo wa Yayanku abinci a ɗakinsa."
Daga haka ya katse kiran wayar .
"Ba jimawa sai ga Sadiƙa ta shigo da farantin abinci da aka ɗaura kan tire da robar ruwa ruwa da glass cup sai lemu na kwali.
Mom ce ta karɓi abincin ganin haka ya sauko daga saman gadon ya zauna akan carpet dake ɗakin.
Sadiƙa ta kalle shi ta ce.
"Big bro are you okay?"
"Am okay"
Daga haka ta fita ta ba su waje .
Abincin Mom ta ajiye ma sa a gabansa ita ma ta zauna tana fuskantar sa ta saka shi gaba kamar yaro.
Sai da ya ci rabin plate ɗin abincin sannan ya sha ruwa lemu ma bai sha ba.
Kallonsa take yi tana yi wa Allah godiya, domin kuwa rabon da ya kwana a gidan nan tun bayan da Gwaggonsa ta dauke shi yana ɗan shekara ɗaya, sama da shekaru talatin kenan bai sake kwana gidan ba sai yau. Sai dai ya so ya gaishe su ya tafi .Amma ta san hakan na da nasaba da rashin sanin ita ce mahaifiyarsa sai a cikin shekarar nan da zancen aure sa da Yasmeen ya fito. Kuma zuwa lokacin ba wani zama yake yi ba, ko, amma yanzu ga shi ita da shi nan ya fara sauka kafin ya je gidan Ummeen tasa.
Horn ɗin mota suka ji sanan suka ji ƙarar buɗe gate. Hakan ya tabbatar ma su da isowar Dad.
"Dad ne ya dawo ko Mom?"
"Eh shi ne."
Ta faɗa tana tashi ta dauki farantin da plate da ya ci abinci da shi. Ta fita daga ɗakin ya bi ta da kallo.
_Fahad_
Ya rage kayan jikinsa kenan zai yi wanka daga shi sai gajeren wando da singileti. Nadra ta turo ƙofar dakin cikin tashin hankali.
Da sauri ya juya ya kalli ƙofar ya ce .
"Lafiya me ya faru!"
"Aunty Sidra ce ta faɗi?"
Shiru ya yi kamar bai ji ta ba, ganin ya yi shiru ta karasa dab da shi ta rike hannunsa tana kuka ta ce.
"Ka taimaka ma na don Allah Yaya Fahad."
"Ni fa ba na ƙaunar ganin wanan yayar taki na tsane ta, amma kin goyi bayan ta dawo gidanki ta zauna, ba yadda na iya Amma wallahi ba da son raina hakan ta faru ba."
"To ba yadda zan yi ne shi ya sa, ta nuna nan take so kuma ga abun da Doctor ya ce a guji ɓacin ranta."
Jallabiyarsa fara ya ɗauka ya ɗauka ya saka sannan ya nufa hanyar fita ta bi bayansa.
Yana zuwa ɗakin baƙi ne ya ganta kwance ba ta motsi kamar wata gawa. Durƙudaws ya yi a gabanta ya zuba ma ta idanun na wasu sakanni kafin ya kalli Nadra ya ce.
"Ba ni ruwa a fridge."
Da sauri ta zuwa falo kasancewar fridge dake nan ɗakin a kashe yake.
Nan da nan ta dawo da robar ruwa ta mika ma sa. Ya ɓalle marfin ya yayyafa ma ta amma shiru ba ta motsa ba, hakan ya sa ya ka ya watsa ma ta da ƙarfi wanda ya da ta ja ajiyar zuciya tare da rike hannunsa da ƙarfi tamkar wani zai kwace ma ta shi daga hannunta.
Tsuki ya ja a ƙasar ransa kafin ya fusge hannunsa da ƙarfi ya fice daga ɗakin.
_Jalaluddeen_
Bayan fitar Mom kenan ya tashi ya fice daga ɗakin shi ma.
A falo ya tarar da ƙannen nasa suna zaune sun zubawa tangamemen plasma t.v wanda ya kusa rabin rabin bangon Falon.
Sai sanyin A.C da wani sanyayyen ƙamshin turaren wuta da ke tashi a falon
Ɗaya daga cikin lafiyayun royal chair dake Falon ya zauna. Kasancewar kujera ma i zaman mutum uku ce nan take Sadik da Sadiƙa suka taso suka zauna kusa da shi suka sanya shi a tsakiya.
Fuskar kowannen su ɗauke da murmushi, Sadik ya ce
" Yanzu fa daga gobe ka zama ango."
Kallon rashin Fahimta ya yi ma sa ya ce .
"Kai ba na son shirme fa, waye zai zama ango gobe."
"Kai ma na Yaya Jalal, ai Dad ya ce duk ranar da ka dawo garin nan a washegarin ranar za'a ɗaura auren ka da Yasmeen kowa ya san da wanan zancen."
"
Wani gumi ne ya ji ya karyo ma sa shi da sanyin A.C dake ratsa falon.
,*Maman Ihsan ce✍️
09065327995
Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z

Page6️⃣4️⃣
Gumi ne ya ji ya karyo ma shi duk da sanyin A..C dake ratsa falon.
Ba wanda ya sake magana, su ma ganin yanaynsa ya sauya ne ya sa kowa .
Mom ce ga karasa falon ta kalle shi ta ce..
"Ka zo ga Alhaji na son ganin ka."
Ta faɗa tana nazartar yanayinsa.
"To Mom."
Ya amsa tana tashi ya bi bayanta don zuwa amsa kiran Dad.
Yana shiga ya tarar da Dad da Mom zaune saman kujerar mai mai zaman mutum uku.
Da sallama ya karasa falon ya zube a kan carpet ya gaida Mahaifin nasa.
"Barka da dawowa Dad."
"Barka dai Jalal ya kake?"
"Lafiya lau Alhamdulillah."
"Ma sha Allah, ya kuma aikin?"
"Alhamdulillah aiki sai an daure."
Dariya Dad ya yi yana cewa .
"Ya su Ummeen taka?"
"Dad ai ban je can ba nan na sauka."
"To fa, nan ka sauka?"
"Eh na yi kewarku ne Dad."
"Allah saekiy, Ummeen taka ta san kana nan."
"Ban faɗa ma ta ba Wallahi, don idan ta sani za ta saka ni na koma gidan yau ne, ka san halin ta yanzu za ta iya aiko direba ya ɗauke ni idan ma ban tafi ba."
Murmushi Dad ya yi tare de cewa .
"Ƙwarai kuwa na san halin ta ba ta san ka yi nesa da ita sai dole. Shi ya sa ba ta ƙaunar wanan aikin da kake yi kullun cikin ƙorafi take. To amma idan ka yi aure ai dole ka bar gidan."
"Yauwa Dad ka je kai da Mom kuwa kun ga yanayin tsarin gidan ko?"
"Eh mun je gidanm ya yi kyau ma sha Allah, tsarin gidan kamar ba a Nigeria ba a kasar Turai aka yi shi."
Cewar Mom tana dariya. Kafin ta ce .
"Allah ya kara arziki ya kare ka a duk in da kake, gaskiya ka yi ƙoƙari irin wannan gidan haka?"
",Gaskiya kam Jalal ka narka dukiya a gidan nan Allah ya da yawan rai aka yi wa."
Cewar Dad yana jinjina kai.
Nan suka cigaba da fira har dare ya yi don karfe sha daya ne a lokacin. Kafin ya yi ma su sallama ya koma part ɗin sa.
Wanka ya yi sannan ya kwanta kan gadon daga shi sai gajeren wando da singileti. Har ya dauki waya zai kira Ma'eesha ganin karfe goma sha daya da mintuna arba'in ya sa ya fasa don yana tunanin yanzu tana barci.
_Nadra_
Tun da ta ga Sidra ta yi ajiyar zuciya ta dawo hayyacinta ta saki murmushi tana goge hawayen da ke kwance a idanunta.
Fahad da ya fice daga ɗakin ta zuba wa idanu har sai da ya banko ƙofar da ƙarfi sannan ta dawo da kallon ta kan Sidra.
"Sannu Aunty Sidra."O
Ba ta tanka ma ta ba ta kau da kai tana kallon yadda jikinta take jin sanyi. Don gabaɗaya Rigar jikinta sun jiƙe, kamar da gayya ne Fahad ya watsa ma ta ruwan.
Ba tare da ta damu da yanayin yadda Sidra ta tsuke ma ta fuska ba ta kama hannunta ta janyo ta tana cewa.
"Sannu Aunty ba ki ji ciwo da faɗuwar da kika yi ba? Ba abun da ya same ki ko?"
Zare hannunta ta yi daga na Nadra tana kokarin barin wajen kenan sai Nadra ta riƙe ta tana cewa.
"Bari na taimaka ma ki muje banɗaki daga nan sai ki yi wanka."
"Ba ta ce ma ta komai ba, ta shige banɗaki ta bar ta tsaye. Nadra ta nemi mopping stick ta goge wajen da ruwan ya zube.
Sannan ta sanya ma ta sabon zanin gado ta gyara gadon. Sidra na fitowa ta kalli Nadra ta ce .
"Sannu da aiki."
"Yauwa sannu Aunty ya jikin naki?"
"Da sauki Alhamdulillah."
"Ma sha Allah, duk da yamma ta yi bari na je na samu abun da zan sarrafa ki samu ki ci na san yunwa kike ji ko?"
Kai kawai ta jinjina ba tare da ta yi magana ba.
"Yauwa Aunty don Allah kada ku saka wa ranki wani tunani ko damuwa, maganar Doctor ba maganar Allah ba ne, don haka ina sha Allah muna tare da ke har jikokin ki sai mun gani. Kuma ina son mu je mu roki Abba ya yafe ma ki kura-kuranki ki koma gida ki ci gaba da rayuwar farin..."
"Nadra!"
Yadda ta kira sunan ta sai da gabanta ya faɗi. Ta kalle ta da sauri ba tare da ta karasa maganar da take yi ba.
"Na'am Aunty."
"Tun ba'a je ko ina ba har kin gaji da ni kina kora ta na koma gida na yi rayuwar farin ciki, saboda na zo gidanki gidan aro ko?"
Cike da mamaki Nadra ke kallon ta tana nanata zancenta a zuciyarta, wato zancen cewa su je su nemi yafiyar Abba ne ba ta so ta ce tana korar ta . Sannan kuma me take nufi da gidan aro, wato duk da ba ta gaban Fahad da yanayin ta take nuna ma sa bai saka ta ta shiga hankalin ta ta fita daga lamarinsa ba, har yana cewa gidan aro.
Murmushi kawai Nadra ta yi kafin ta ce.
"Allah ya ba ki haƙuri Aunty ya huci zuciyarki ba haka nake nufi ba. Bari na je na nema ma na abun da za mu ci ki samu ki sha magungunan ki."
Tana faɗar haka ta fice daga dakin tana murmushi.
_Jalaluddeen_
Washegari da safe bayan sun kammala breakfast ya shirya don zuwa gidan Ummeensa.
Sanye yake cikin cikin cikin cikin wani tsadadden yadi mai ruwan sararin samaniya. Ɗinkin ya zauna ma sa a jikinsa ya ma sa kyau.
Sallama ya yi wa mutanen gidan gidan sannan Sadik da ya shirya zuwa asibiti ya dauke shi a motarsa, da niyyar idan ya kai shi gidan sai ya wuce asibiti daga can.
Horn ya yi a ƙofar gidan, security ya leƙo ganin su ya sa ya wangale gate ɗin da sauri, kasancewar ya san motar Sadik.
Bayan ya yi parking kusan a tare suka fito daga cikin motar . Ma'aikatan gidan na ganin Jalaluddeen suka nufo shi da sauri suna gaishe shi. Ya amsa ma su cikin sakin fuska da walwala.
Suka nufi ƙofar da za ta sada su da ƙofar shiga babban falon gidan.
Kararrawar ƙofar Jalaluddeen ya danna wanda ya sa gabaɗaya ilahirin jama'ar dake ciki suke kallon ƙofar cike da mamaki. Saboda sun san idan har suka ji yanayin bugun kararrawar Jalaluddeen sun san shi ne.
Ummee da Abba sai Yusuf da suke a dinning table suna breakfast suke kallon ƙofar. Ma su aikin da ke falon ma suna kallon ƙofar suna mamakin yaushe ya dawo.
Hatta Yasmeen da yanzu farkawar ta daga barci kenan ta ji ƙarar ƙofar masoyinta sai da ta miƙe zumbur.
Da sauri Yusuf dake cin abinci a dinning area sai ya tashi kafin ma su aikin su buɗe har ya riga su isa ya buɗe.
Cike da mamaki yake kallon Jalaluddeen ya ce.
"Yaya Jalal kai ne yanzu haka?"
Gajeren murmushi ya yi tare de cewa.
"Ga shi kuwa kana gani."
Ba su hanya ya yi suka shigo cikin sannan ya rufe kofar daidai lokacin da Yasmeen ta fito daga part ɗin ta. Daga ita sai rigar barci wacce ta tsaya iya guiwarta, kanta babu ɗankwali kanta babu ɗankwali sai kitso calaba da ke kanta.
Ganin da gaske ba ƙarya kunnen ta yi yi ma ta ba ta nufe shi da gudu za ta rungume shi ya yi saurin dakatar da ita da hannu ya ce.
"Koma ki saka kaya!"
Ya faɗa babu wasa a fuskarsa . Da sauri ta juya tana tura baki Dariya Yasuf ya yi don ya san a fadin gidan nan Jalal ne kawai zai yi ma ta magana sau ɗaya ta aikata abun da ya umarce ta ba tare da gardama ba.
Ummee ta kalli Jalaluddeen ta kalli Sadik dake rike da jakar kayan Jalaluddeen dake hannun Sadik.
"Daga ina kuke haka da safiyar nan? Na san dai ba ka isa a ce har ka bar garin Kaduna ka iso nan ba ."
Kafin ya yi magana sai Sadik ya ce .
"Daga gidanmu yake, tun jiya ya iso na je na dauke shi a airport na yi ma sa bazata. Daga airport na kai shi gida ya kwana yanzu na dawo da shi gidansu."
Ya yi maganar yana dariya. Su ma dariyar suka yi ban da Ummee. Kafin ta ce.
"Son za ka dawo ko ka sanar ma na dawowarka sai dai na gan ka daga sama wasu ne ka sanar."
'Wasu?'
Sadik ya faɗa a ransa yana mamakin Gwaggon tasu. Gaida su ya yi sama-sama ya ce zai tafi aiki yana sauri, daga nan ya fice daga falon.
Yasmeen ce ta dawo sanye da rigar after dress ta saka hula a kanta. Cikin farin ciki ta ƙaraso wajensa da niyyar ta rungume shi. Da idanunsa kawai ya gargaɗe ta wanda gane nufin sa ya sa ta tura baki tana fushi.
Zama ta yi akan kujera mai zaman mutum biyu dake Falon.
Kasancewar ba wanda ya san abun da ya haɗa su ya sa Abba cewa.
"Yasmeen ba ki ga Yayanki ba ne?"
Kamar tana jira sai hawaye dariya Yusuf ya yi yana cewa.
"An dai ji kunya."
"Ke lafiya me yake faruwa ne haka, ba na son sakarci."
"Ummee bar ta ni da ita ne."
Jin haka ba su sake magana ba, ya gaida su cikin girmamawa, sannan Yusuf ma ya gaishe shi.
"Tun jiya kake garin nan Son shi ne ba mu sani ba?"
"Ummee ki yi haƙuri ke ma kin san ban saɓa sanar da tafiya ta ko dawowa ta ba, muna waya da Mom ne nake sanar da ita dawowa ta anan Sadik ya ji shi ne ya je ya taro ni."
"To me ya sa da muka yi waya ba ka sanar da ni ba?"
"Bayan mun gama waya da ke lokacin ban yi tunanin dawowa ba."
Murmushi ta yi kafin ta ce.
"You're welcome."
Murmushi kawai ya yi yana kallon Yasmeen dake cika da batsewa.
"Amma ya kamata ka canza wanan aƙidar taka Son, a ce ba ka sanar da kowa duk abun da ya shafe ka? Yanzu fa iyali kake shirin ajewa ko ba haka ba, duk rashin damuwa da mutane idan kana aiki dole za ka canza ko don iyalinka."
"In sha Allah Ummeena."
"Yauwa Ɗan gidan Ummeensa."
Gabaɗaya suka saka dariya. Ta kalli jakarsa ta ce wa Yasmeen.
"Kai ma sa jakarsa ɗakinsa."
Ta ɗauki jakar ta nufi part ɗin nasa dake upstairs.
Da kallo ya bi ta kafin ya kalli su Ummeen ya ce .
"Bari na fito Ummeena."
Murmushi ta yi kafin ta ce.
"Ya aiki ya hanya?"
"Lafiya lau Ummee aiki ba sauƙi."
"Shi ya sa ba na son wanann aikin naka, ka ajiye shi ka fara kula da Kamfanin..."
"A'a kin san kowa da hanyar cin abincin sa, na san dai saboda rashin zamansa ya sa ba ki son aikin."
"Ki kwantar da hankalinki Ummeena."
Ya faɗa yana nufar part ɗin sa.
Yana tura ƙofar falon ya yi kiciɓis da Yasmeen dake ƙokarin fitowa. Kau da kanta ta yi gefe idanunta na kara cikowa da ƙwalla.
Hannunta ya rike yana cewa .
"Meye kuma na kuka?"
"Ka daina so na ka daina ƙauna ta."
Ta saki kukan da take riƙe wa , kafin ya kalle ta ya ce .
"Me ya sa kike tunani na daina son ki?"
"Ai a baya ba ka ƙyamata ta dai yanzu, da idan ka dawo za ka yarda na yi ma ka oyoyo idan na ji kwarara amma yanzu sai ka hana."
Dariya ya yi kafin ya ce.
"Da da yanzu ba daya bane Yasmeen, a baya ina na ki kallon jini daya ne ni da ke ina ma ki kallon Muharrama ta amma daga baya sai muka fahimci ba haka ba ne, daga ranar da na fahimta cewa ba Ummee ta haife ni ba na canza yanayin zamantakewar da nake yi da ke, domin akwai iyaka tsakanin mu. ga shi har ana shirin yi ma na aure, ai addini bai yarda na haɗa jiki da ke ba har sai kin halatta a gare ni. Ina fatan kin fahimce ni?"
Kai ta gyaɗa ma sa alamar eh kafin ta ce.
"Za ka raka ni wajen bikin ƙawata?"
"Wata ƙawarki?"
"Maryam da ka sani Aminiya ta."
"Har bikin ya zo?"
"Eh kuma mun shirya taro kowace za ta je da saurayinta ko mijinta, dama saboda ba ka nan na ce ba zan je ba, tun ja ka dawo dai mu tafi karfe biyar na yamma."
Shiru ya yi kafin ya ce.
"To Allah ya kai mu. Amma ba na son zuwa irin Wuraren nan fa."
"Please Yaya Jalal ka raka ni."
"Okay Allah ya kai mu."
Da murna ta daka tsalle tana yi ma sa godiya.
Fita ta yi daga part ɗin zuciyarta fara tas.
Tsaye yake yana ƙarewa ɗakin nasa kallo wanda ya ƙawatu da kayan more rayuwa, babu wani wadataccen haske a cikin dakin, ya ɗauki wani remote ya danna, take ɗakin ya gauraye da hasken wasu fitilu da suka ƙara ƙawata ɗakin.
Tangamemen gadonsa wanda aka gyara ya kalla gadon circle ne a zagaye yake ba irin gamagarin gadon da kowa ya sani ba ne. Jakar kayansa ya ɗaura kan gadon ya cire wayoyinsa na aiki da kuma wacce Ma'eesha ta siya ma sa ya ajiye saman gadon ya rage kayan jikinsa ya shiga bathroom don yin wanka.
Shower 🚿 ya sakar wa kansa yana wanka yana tuna yadda Ma'eesha take dafa ruwan zafi ta kai ma sa banɗaki ya yi wanka.
Sauri-sauri ya yake yi ya fito domin ya kira ta a waya domin ya ji halin da take ciki.
Ummee ce ta yi sallama ta yi knocking ƙofar ɗakin nasa, jin shiru ya sa ta tura kofar da sallama. Sai dai ta ga baya cikin bedroom ɗin nasa. Amma jin saukar ruwa a banɗaki ya sa ta gane cewa wanka yake yi.
Har za ta fita sai ta ji ƙarar waya kamar calculator ta juya ta kalli wayar dake kan gado yana ruri.
Kallon wayar ta yi cike da mamakin yadda aka yi mutum kamar Jalal yake amfani da wayar da talakawa ke amfani da su.
Ƙarasawa ta yi jikin gadon tana kallon wayar.
Ganin sunan da ke jikin wayar ne take kiransa wato MAR'ATUSSALIHA ya sa ta cika da mamaki.
Kiran ya tsinke take wani kiran ya sake shigowa wayar, da sauri ta kai hannu kan wayar...

Page6️⃣5️⃣
Kiran ya tsinke wani kiran ya sake shigowa wayar, da sauri ta kai hannu kan wayar da niyyar ɗauka sai ya riga ta ɗauka cikin zafin nama. Kallonsa ta tsaya tana yi yana sanye da rigar wanka kansa na ɗigar da ruwa da towel a hannunsa.
Yana ɗaukar wayar sai kiran ya tsinke, ya kalle ta ya ce.
"Ummee kina buƙatar wani abu ne?"
"Wace ce mar'atussaliha?"
"Abokiyat aikina ce ita."
"Ba ta da wani suna se wannan?"
"Tana da shi, amma haka ake kiranta saboda kyawun halinta da nagartarta."
"Okay ka fito ka ci abinci na ga ba ka fito ba ne na biyo bayanka."
"Ummeena yanzu na ci abinci a gidan Mom, sai zuwa anjima."
"Okay ka huta, ko kana bukatar wani abu ne?"
"Ba na bukatar komai Ummeena."
Murmushi suka yi wa juna a tare sannan ta fita tana cewa.
" ka kwanta ka huta kada ka takura kanka da zancen aikin nan."
Yana dariya ya amsa sannan ya goge kansa da towel na hannunsa.
Kiran Wayar ne ya bi ya danna ma ya kira .
"Bugu biyu da ga tare da yin sallama cikin nitsatsiyar muryarta.
"Assalamu alaikum warahmatullah."
"Wa'alaiki salam warahmatullah Mar'atussaliha mayar mijinta."
Murmushi mai sauti ta yi wanda sai da ya ji sauti nan cikin kunnensa.
"Ina wuni'
"Lafiya lau ya kike"
"Alhamdulillah ga ni ina gama da kewar ka, har ciwo.n kai na yi sai da A'isha ta zo ga siyo Mani magani na sha. Bayan na tashi barci ne sai na ji sauƙi.
"Ya Salam, to yanzu ya kike ji a jikin naki?"
"Alhamdulillah na ji sauƙi sosai wallahi."
"Ma sha Allah. To meye labari ?"
"Labari mai daɗi kuwa."
"Fada mani ina jin ki."
"Wadanda ka ce za su ba mu tallafin nan ne suka kawo ma na kudi ma su yawa har Naira dubu ɗari biyar."
"Cikin nuna jin dadi da murna ya ce.
"Alhamdulillah Allah ya saka ma shi da alkhairi."
"Amin Mijina."
Yanzu abun da za'ayi ki ɗauki kamar dubi ɗari uku ki shiga da su kasuwa ki je ki siyo kayan abinci ma su kyau da inganci. Kamar yadda kika yi a baya lokacin da kika siyar da wayarki."
"A'a wanan fa an ce mu yi sana'a ne aka ba mu jari."
"Dubu ɗari biyu da ya rage sau mu yi shawarar sana'a da za mu yi idan na dawo ko?"
"To shi kenan yadda ka ce haka za'ayi."
Ka isa lafiya? Ka samu danginka cikin wadanda aka ce sun dawo?"
"Ba sa ciki ba kowa nawa."
Cikin sanyin jiki ta ce.
"Allah ya bayyana ma ka su a duk in da suke, Allah ya haɗa fuskokin ku."
"Amin na gode."
"Yanzu yaushe za ka dawo?"
"Ina ganin zuwa jibi motar da na biyo za ta dawo, don haka ita zan biyo."
Fira suka tana daga bisani ya yi ma ta sallama ya kashe kiran wayar.
_Nadra_
Tana barin ɗakin Sidra koma ɗakin Fahad, ta ji saukar ruwa a bathroom alamar yana wanka.
Kitchen ta nufa don ɗora ma su abun da za su ci. Nan da nan cikin ƙanƙanin lokaci ta dafa ma su jallop ɗin superghetti da ya ji kayan lambu da bisashen kifi. Sai farfesun kayan ciki wanda ya ji kayan ƙamshi.
Bayan ta zuba a cikin kula ne ta kwashe su ta jera a dinning table.
Daidai lokacin ana kiran sallar magrib kenan ta kammala. Fahad wanda ya fito da niyyar zai je masallaci ya ji ƙamshi girkinta.
Tana kokarin barin dinning area suka hadu. Murmushi suka sakar wa juna kafin ya ce.
"Sannu da aiki."
Madadin ta amsa sai ta ce ma sa a dawo lafiya, kafin ta nufi ɗakinta. Wanka ta yi sannan ta ɗauro alwala ta gabatar da sallar magrib.
Tana nan jan sallaya ba ta tashi ba, karatun Alkur'ani take yi har sai da aka kira sallar isha'i ta tashi ta gabatar da sallar isha'i ta yi addu'o'i sannan ta mike tsaye ta cire hijabiñ da ya yi sallah da shi .
Rigar material ne a jikinta ɗinkin doguwar riga ce.
Kai tsaye ta nufi falonta daidai lokacin yana dawowa sallah.
Nadfah yunwa nake ji."
Kallonsa ta yi alamar ba ta bane sunam danya kira ta sa shi ba ne
"Wa na ji ka kira ne?"
"Ke na kira ma na, ba ki ji na ce Nadfah ba?"
"Shiru ta yi tana nanata kalmar a ranta.
'Nadfah.'
Wato farkon sunan ta na nasa ya haɗa kenan NAD+FAH =NADFAH.
Nurmushi ta yi sakamakon sunan da ya yi ma ta daɗi sosai da sosai ta ce.
"Ga abinci na jiranka. Mu je dinning area na zuba ma ka, daga nan sai na kira Aunty Sidra ta fito mu ci abinci ."
Ji ya yi ransa ya ɓaci sakamakon kiran sunan Sidra da ta yi. Amma gudun kada ya ɓata ma ya rai tun da ya fahimci tana son ƴar uwarta sosai ya sa ya ce.
"A gajiye nake ba zan iya fitowa zuwa dinning area ba please ki kawo mun nawa a ɗakina, amma fa dai kin taya ni ci."
Ya yi maganar yana murmushi.
"Ayyah sorry, to bari ba kawo ma ka ko?"
Ta yi maganar tana wucewa don kawo ma sa abincin nasa.
Shi kuma ya shiga cikin bedroom ɗin sa.
Bayan kamar mintuna biyar sai ga ta ta dawo da ba tire a hannunta wanda ta jera abincin da abun sha da kofi da spoon.
Yana zaune yana jiranta daga shi sai singileti da gajeren wando.
Yana zaune kan sofa dake cikin bedroom ɗin nasa. Ajiyar abincin ya yi kafin ta janyo stool dake gefe ta ajiye a gabansa danna ta ɗora abincin. Jallop ɗin superghetti ne da ta dafa ya ji kayan lambu fa busashshen kifi. Ta zuba ma sa lemu da ruwa sannan ta ce.
"Ina zuwa?"
"Ai tare za ki zauna mu ci ."
"Okay just 5 minutes zan dawo."
Ta faɗa tana murmushi ta fice daga ɗakin hannunta rike da wayar ta.
Ƙasa ta sauka ta nufi ɗakin baƙi. Nan ta samu Sidra na ta kai wa da komowa.
"Assalamu alaikum."
"Wa'alaiki salam."
Zama ta yi bakin gadon tana cewa.
"Sannu Aunty Sidra."
"Yauwa sannu. Na ga kin dade baki dawo ba ko kina tare da Fahad ko?"
"A'a Aunty da na bar nan kitchen na je ba yi girki, da na gama ne na aka kira sallar magrib na je na yi, kuma kin san baka tashi daga magrib sai na yi isha'i. Yanzu na fito don na tambaye ki nan zan kawo ma ki abincin ki ne?"
"Ku a ina za ku ci?'"
"Ya ce tare za mu ci a ɗakinsa?"
Sai da ta ji zafi a zuciyarta kamar an watsa ma ta garwashin wuta kafin yi ƙoƙarin daidaita nutsuwarta ta ce.
"Yanzu zuwa wajansa za ki yi?"
"To Aunty Sidra ya zan yi?"
"Hmm yanzu haka za ki bar ni ki je can wajensa ki bar ƴar uwarki da take cikin halin jinya tana bukatar taimakon ki? Kuma kin san bai kamata ki bar ni na kwana ni ƙaɗai ba, saboda ba'asan me zai faru cikin dare ba ko ciwon nawa zai iya tashi ba kowa a kusa da ni, wata kila ma sai dai ki ga gawata da safe."
Ta yi maganar tana fashewa da kuka.
Cikin rauni Nadra ta rungume ta tana rarrashin ta.
"Dan Allah Aunty Sidra ki daina fadar haka ba abun da zai same ki ina tare da ke in sha Allah."
Tana gama faɗar haka ta fice daga cikin ɗakin yayin da Sidra ta zauna sai cika take yi tana batsewa. Ba jimawa sai ga ta ta dawo da tire a hannunta wanda ta jera wa Sidra abinci.
"Aunty ga abincin nan ki fara ci kafin na dawo."
Sai da ta buɗe ma ta abincin ta saka ma ta fork ta zuba ma ta ruwa da lemu sannan ta fice daga ɗakin.
Da sallama ta shiga ta samu Fahad na zaune waya yake yi abincin na nan gabansa bai fara ci ba. Zama ta yi gefen sa tana kallon sa har ya gama wayar sannan ta ce .
"Yaya ba ka ci abincin ba."
'Ke nake jira."
Murmushi ta yi kafin ta saka fork cikin plate ɗin abincin. Shi ya dinga ba ta a baki har sai da ta ƙoshi. Ganin haka ita ma ta fara ba shi suna fira har ya ce ya ƙoshi.
Tattara kayan ta yi ta kai kitchen ta wanke sannan ta dawo.
Sanin halin ta yanzu za ta yi ma sa zancen Sidra ko ta ce za ta tafi wajen ta ya sa ya rufe ƙofar ya murza key.
Za ta yi magana ya ce.
"Na yi ma ki dukkan wasu alfarma da kika nema akan Yayar ki. To yanzu lokaci na ne, dama ai kin yi ma ni alƙawari kin tuna? Rashin lafiyar Yayarki ya tsayar da komai."
Shiru ta yi tana tuna kalaman Sidra.
Ba ta ankare ba ta ji ya ɗauke ta ya yi sama da ita, kai tsaye bathroom suka nufa.
Wanka suka yi a tare sannan suka fito daga banɗaki ya naɗo ta cikin towel kamar baby.
_Jalaluddeen_
Da misalin ƙarfe huɗu da rabi na yamma bayan ya dawo masallaci, wanka ya shiga ya yi sannan ya fito sanye cikin bathrobe (Rigar wanka) yana tsaye a gaban dressing mirror yana kallon kansa.
Wayarsa ya ɗauka gaban dressing mirror ɗin wacce yake waya fa Ma'eesha.
Kira ya danna ma ta bugu biyu ta ɗaga. Cikin zazzaƙar muryarta ta yi ma sa sallama .
Sai da ya lumshe idanu cike da kewarta ya amsa ma ta sallamar.
"Ina wuni mijina?"
"Lafiya lau ya kike ya gidan?"
"Gaskiya duka ba lafiya ba. Don ta ina zan yi lafiya ba ka tare da ni, sannan kuma gidan ma duhunsa nake gani domin fitilar dake haska ma ni gidan baya tare da ni?"
"To ina fitilar ya faɗa ai sai ki neme shi?"
"Kai ne fitilar ai, idan ba ka nan gidan Lami ne, sai yanzu nake jin maraici a tare da ni."
"Kuyi hakuri zan dawo in sha Allah. Kin siya abincin ?"
"Wani abinci ?"
"Kin manta na ce ma ki cikin dubi ɗari biyar din nan ki cire dubu ɗari uku ki siye kayan abinci kamar yadda kika siye da kika siyar da waya."
"To an ce mu yi sana'a ne, idan ba mu yi sana'ar ba kuɗin karewa za su yi."
"Allah na nan, kuma ba haka za mu dawwama ba."
"Na sani amma Allah ya ce ka tashi in taiamake ka, kai ga ka ba gani kake yi ba, ballantana na ce za ka yi sana'a da kuɗin, mutane cutarka kawai za su yi . Sai dai..."
"Ma'eesha."
"Na'am."
Ta amsa tana sauraron abu zai fito daga bakinsa.
"Ki yi abun da na ce ma ki."
"To sh ke nan, yadda ka ce haka za'ayi ."
Sallama ya yi ma ta ya katse kiran wayar.
Ya shafa tsadadden man shafawarsa sannan ya shiga ciinin closet ɗin sa .
Ba nunawa ya fito sanye da cikin rigar suit baƙa na cikin fari ya ɗaura tie Black and white. Sai ƙamshi yake bazawa. Ya ɗaura tsadadden agogon hannunsa. Wayarda Samsung Galaxy Z fold 5 wacce kuɗin wayar Naira miliyan biyu da dubu ɗari Shida. 2, 600,000. Ya saka a aljihun rigar suit ɗinsa. Bayan ya saka Safa da makami ne ya saka baƙin glass a idanunsa.
Daidai lokacin Yasmeen ta yi knocking. Izinin shigowa ya ba ya ta shigo da sallama.
Ya amsa ma ta ba tare da ya kalle ta ba, yana duba sako a cikin wayarda ta aiki. Reply ya yi sannan ya sa wayar a aljihun wandonsa.
Kallon Yasmeen ya yi ta yi shirin ta cikin material fari da baƙi don shi ne ankon da suka yi . Ganin kayan ya matse ta ne ya sa ya ce.
"Ki ke ki sauya kayan jikinki ?"
Kamar za ta yi kuka ta ce .
"Yaya Jalal wallahi wanan ne ankon ka yi hakuri don Allah."
"Ban hana ki fita da kayan da suka matse ki ba?"
"Ka hana?"
"Ban isa ba kenan shi ya sa ba ki daina ba."
"Wallahi ka isa ka yi yawa ma, amma wanan ne ankon kuma tailor din ne ba ni na ce ba."
"Ki je ki saka after dress."
Da sauri ta fita sanan ya nufi hanyar fita. A falo suka hadu ya yi gaba ta bi bayansa. Don Ummee ba ta gidan ma.
Ɗaya daga cikin motocinsa wanda ya sa aka wanke ma da ne ya shiga. Ita ma ta shiga ta zauna gefensa, sai dai ba walwala a fuskarta ganin ta rufe adonta.
"Ina ne wajen taron?"
Ta sanar da shi tana ɓata rai. Kamar bai san tana yi ba ya yi wa motar key yayin da maigadi ya wangale ma su gate ya fice daga gidan.
Kai tsaya wajen taron suka nufa. Ya yi parking a wajen da aka tanada na parking motoci.
Daidai yana fitowa daga cikin motar suka yi idanu biyu da Nasreen ƙawar Ma'eesha, tana sanye da ankon irin na Yasmeen ,wacce fitowar ta kwanan daga wata motar da aka yi parking. Sakin baki ta yi tana kallon Jalaluddeen da matsanancin mamaki.

Page6️⃣6️⃣
Daidai yana fitowa daga cikin motar suka yi idanu biyu da Nasreen ƙawar Ma'eesha, tana sanye da ankon irin na Yasmeen, wacce fitowar ta kenan daga wata motar da aka yi parking. Sakin baki ta yi tana kallon Jalaluddeen da matsanancin mamaki.
'Khalifa Makaho?'
Ta faɗa a ranta idanunta akansa. Tabbas ya shiga ruɗu sakamakon ganin aminiyar Ma'eesha. Amma dai ya dake ya basar kamar bai taba sanin ta ba. Yanayinsa ba zai taba nuna halin da ya shiga ba, amma tabbas ya yi nadamar zuwa wajen nan.
Kau da kansa ya yi ya rufe murfin motarsa ya yin da Yasmeen ta fito ta zagayo gefensa tana murmushi.
"Mu shiga ciki."
Ta yi maganar tana rike hannunsa suka fara tafiya.
Dariya Nasreen ta yi har yana tafa hannu tana kallon su har suka shige ciki.
_Fahad_
Bai sauke Nadra ko ina ba sai tsakiyar gadon. Daga nan ya haura saman gadon shi ma ya ja ma su bargo ya rufe su. Towel din jikinta ya warware za ta yi magana ya haɗe bakinsu waje ɗaya. Hannu ya kai jikin kan gadon ya rage hasken ɗakin, take duhu ya mamaye ɗakin.
Tsoro da fargaba suka ziyarce ta amma idan ta tuna huɗubar da Aunty Rahama ta yi ma ta sai ta fara kokarin kawar da tsoron da take ji. Bakinsu ya haɗe waje guda ya fara aika ma ta da zazzafar kiss, wanda babu ɓata lokaci ta fara mayar ma sa da martanin abun da yake yi ma ta.
Take saƙon ta ya fara isa gare shi ya kuma yi tasiri a jikinsa. Tsawon mintinan shida suka dauka suna yi tsotson bakin juna cikin raɗa ya ce .
"I love You Nadra."
"Love You too Yaya Fahad."
Hannunsa ya sa ya shiga shafa fatar jikinta daga sama har ƙasa ta ko ina a jikinta. Musamman ƙirjinta da yake cike da dukiyar Fulani masu ɗaukar hankalin mai kallon su. Ya kai bakinsa ya fara tsotson su har jikinsa na rawa kamar mazari. Ita kanta yau ta ji tana bukatar mijinta, don magungunan gyaran da Sunyi Rahama ke ba ta ne yake yi ma ta aiki. Don ba karamin ni'ima ya sakar ma ta ba. Duk ta gama jiƙewa.
Sai da suka kai junan su ƙololuwar buƙatuwa da juna sannan ya karanto addu'ar saduwa da iyali ya shige ta. Sai da suka yi ihu tare ita na zafin da ta ɗan ji shi kuma na daɗi ya yi.
_Sidra_
Jin Nadra shuru ba ta dawo ba ya sa Sidra hankalin ta ya tashi. Don yanzu ta fara tsorata da wanan lamari. Don tabbas ta fara hango soyayyar Nadra a idanun Fahad kamar yadda ta ga soyayyar Fahad a idanun Nadra. Ta tasa yaushe ne suka kamu da soyayyar juna. Don kama yanzu ba tsana ko ƙiyayyar ɗaya daga cikin su akan ɗaya.
Haka kawai ta ji jikinta bai ba ta ba wanda hakan ya sa ta tashi da sauri ta fita daga ɗakin.
Ta baya ta zagaya daidai saitin window na ɗakin Nadra jin shiru ne ya sa ta zagaye ta window na ɗakin Fahad.
Abun da kununuwan ta suka jiyo ma ta ne ya yi sanadiyar ɗaukewar numfashinta na wucin gadi. Domin numfashin su take ji gami da gurnanin mai haɗe da ihu da Fahad ke yi ya wanda hakan ya sa Sidra shhga tashin hankali.
Toshe bakinta ta yi dan kada sautin kukan nata ya fito ta bar wajen a guje.
Ikon Allah ne ya kai ta ɗakinta wanda shigar ta kenan ta faɗa kan gado tana fashewa da matsanancin kuka mai ƙona zuciya.
"Shi kenan ta ƙare mun na shiga uku na lalace. Ya mafarkina ke shirin rugujewa lokaci daya ne? Dama na zo gidan nan ne don na kwashi bakin ciki da kunci?"
Kai ta girgiza da sauri tana cewa.
"Ina ba zai yiwa ba Wallahi hakan ba za ta faru ba, Nadra ba za ta taba yin nasara ni kuma na fadi ba. Saboda ba abun da ta fi ni da shi."
Haka ta dinga kuka tana Surutai ita kaɗai kamar wata mahaukaciya.
_Nasreen_
Cike da mamaki da al'ajabi na Khalifa Makaho da ta gani a wajen taron Centre ta ciro wayar ta a jaka.
Lambar ya wayar Ma'eesha ta lalubo ta danna ma ta kira, sai dai cikin rashin sa'a har sau biyu tana kiran wayar Ma'eesha ba ta ɗaga kiran wayar ba.
Saurayin da suka zo tare ne ya ce .
"Lafiya kuwa?"
Sai da ta yi dariya sanan ta ce .
"Kada ka damu, ƙawata ce aka yaudara aka cuce ta nake son sanar da ita gaskiyar da ba ta sani ba."
"Ban gane ba."
"Ba za ka gane ba dama. Ka manta kawai ba zai amfane ka da komai ba."
Tana gama faɗar haka ya ja hannunta suka shiga cikin wajan taron.
Suna shiga ciki ta hangi Angon na dosowa wajan Jalaluddeen, yana isowa ya rungume shi yana cewa.
"Jalaluddeen kana ƙasar nan dama?"
"Wai dama kai ne kake aure yau?"
"Eh ma na na ɗauka saboda ni ka zo."
"A'a rakiya kawai na yi ban san mai ne ango ba ma."
" Tun da muka gama karatu fa ba ku sake haduwa ba ko? Mun hadu ma na sau ɗaya a ƙasar Canada."
"Haka ne to ya aiki ya iyali?"
"Ban yi aure ba har yanzu ina dai kan hanya."
"To ma sha Allah, Allah ya kawo lokaci na alkhairi."
Daga nan suka rabu ango ya koma wajen da aka tanadar dan shi da amaryarsa. Yayin da Jalaluddeen ya koma ya zauna kusa da Yasmeen.
Yana zama sai ya lura da Nasreen na ɗaukar su photo. Ya basar kamar bai ganta ba.
Ana ta Shagali mawaki ya waƙe amarya da ango an yi rawa da waka. An yi wa amarya da ango liƙin kuɗaɗe ciki kuwa har da Jalaluddeen. Don ba karamin kudi ya yi ma su liƙi ba kuma ƴan dubu ɗaya ne kuɗin da ya yi ma su liƙi.
Bayan wani lokaci an fara cin abinci yayin da kowa ke cin abin da ransa ke so ne Nasreen ta zagaya ta wajan Amarya.
"Ke kalli wancan Mutumin kin san shi ne?"
"Ta yi maganar tana nuna ma ta Jalaluddeen wanda ke kare da waya a hannunsa tana magana."
Dariya ta yi sannan ta ce
"Okay Jalaluddeen kike nufi ki? Kin ga handsome guy kin ƙyasa ko? To ki cire rai domin ana shirin aurensa kwanan nan ne. Da ba don tsaiko da aka samu ba su da yanzu ya dade da angocewa ba."
"Ba sunan sa Khalifa ba? Sanan yana gani ba Makaho ba ne?"
Sai da ta yi dariya kafin ta ce
"Wani Khalifa kuma wani Makaho kuma? Ko dai ya yi ma ki kama da wani ne?"
"Ba wani kama na tabbatar shi ne kuma sai na toni asirinsa ."
Dariya kawai ta yi don tana yi wa Nasreen kallon wacce ba ta cikin hayyacinta.
Kafin a tashi taron Jalaluddeen ya ce wa Yasmeen ta tashi su tafi yamma ta yi. Ba musu za su bar wajan duk idanun Nasreen nan kan su.
Ita kanta ta matsu su bar wajan saboda ta lura da yadda Nasreen ke yi wa Jalal kallon ƙurilla wanda ya da ran Nasreen ɓaci. Don kishinsa take yi, a tunanin ta Nasreen na kallon Jalaluddeen ne saboda tana son sa.
Har sun yi nisa ta juyo ta watsawa Nasreen wani banzan kallo mai haɗe da gargadi sannan ta bar wajan.
_Mamy_
Cikin tashin hankali take bincike a cikin ɗakinta. Gabaɗaya gwala-gwalai da ta tara babu ko ɗaya, hatta kuɗaɗen da take ɓoyewa a ɗakinta ba ko sisi.
Cikin tashin hankali ta nufi in da ta ajiye ƙadarorin Dady. Kasancewar yanzu baya da kataɓus a gidan sai abun da ta ce ya da ta karɓi takardun fiye da ƙadarorinsa da ta mallaka. Wasu ma sunan Ma'eesha ne a jikin takardun.
Ɗora hannu ta yi a saman kai tana fadin ta shiga uku. Domin ta san ba mai shigo ma ta cikin ɗaki sai Laila. Ita kadai ce take shigo ma ta ɗaki don ko Jamil bai cika shigo ma ta ɗaki ba.
Cikin tashin hankali ta lalubo lambar wayar Laila ta danna ma ta kira, sai dai har ya katse ba ta ɗaga ba. Sau uku tana kira ba ta ɗaga ba.
"Allah ya sa yarinyar nan ba ta salwantar da ƙadarorin nan ba."
_Laila_
Tana zaune a gaban motar Taj ta kalle shi ta ce .
"Wai yaushe za mu bar ƙasar nan ne mu tafi ƙasashen da aka ce yawon shaƙatawa. Sannan kuma yaushe ne za mu yi auren?"
"Kada ki damu idan kin gama tattaro duka dukiyar muka tara su na tabbatar za mu ishe mu mu yi rayuwar mu a can ba tare da har jikokin mu sun yi talauci ba."
"To zan dai sake bincikawa amma na tabbatar na kawo ma ka kaso saba'in na dukiyar gidan."
"Ba iyakar su kenan ba ki sake gwada wa ki tabbatar kin gama kwashe komai kuɗaɗe da kadarori da gwala-gwalai. Ba kin ce yanzu ba komai a wajen Dady ba duk Mamy ta amshe komai?"
"Eh na kawo ma ka duk wasu takardun duk rabi na takardun sunan ƴarsa Ma'eesha ya saka, kuma yanzu na Mamy ta raba shi da ƴarsa Ma'eesha ka ga ba mai gadon dukiyar ko?"
"Mu za mu gaje su mu je mu yi bushasha"
"Don Allah kada sai na gama tattara komai na mallaka ma ka don mu je mu yi rayuwar mu a can kamar yadda ka ce daga baya ka juya ma ni baya ka guje ni"
"Haba ni ba bututu ba ne, ki daina tunanin hakan ?"
Murmushi ta yi tare da cewa.
"I love You?"
"Love you more."
Kallon takardun da ta kawo na sa yau ya yi sannan ya ce.
"Ana jira na zan iya tafiya?"
"Eh za ki iya sai gobe idan mun hadu sai mu sake tattaunawa."
Fitowa ta yi daga cikin motar ta shiga motarta wacce a baya mallakin Ma'eesha ce kafin su raba ta da shi .
Tana fita ya fara duba takardun sannan ya kira Jalaluddeen a waya."
Lokacin Jalaluddeen na driving za su koma gida shi da Yasmeen, ya ga kiran yaron aikinsa ya shigo wayarsa.
Parking ya yi a gefen hanya sannan ya fito daga cikin motar ya bar Yasmeen a ciki.
"Hello Taj."
"Hello sir, barka da yammaci sir."
"Yauwa Barka dai , an kara samun wasu abubuwa daga yarinyar ne?"
"Eh Yallaɓal ga wasu takardun nan yanzu ta kawo, wasu sunan Ma'eesha ne a jiki, wasu kuma sunan Mahaifinta bai Mallaka ma ta su ba."
Jinjina mai Jalaluddeen ya yi kafin ya ce .
"Da kyau Taj aikinka ya yi kayu, dama na san za ka iya shi ya sa na saka ka. Ka ajiye takardun zuwa jibi zan dawo sai ka kawo ma ni su na haɗa su tare da waɗan can da ka karɓo.."
"Okay Sir."
"Yanzu a cikin waɗan nan takardun da ka kawo ma ni ba takardar Kamfani a ciki?"
"Gaskiya babu."
"Zuwa gobe ka bincike ta ta nemo ma ka wannan takardar, don Ma'eesha ta taɓa ba ni labarin kamfanin, duk da ya zama mallakin Mahaifiyarta ne shi mahaifin dama ko da ya siye kamfanin fama kamfanin ya mutu sai an raya shi, kuma amma takardun suna gidan duk yadda za'ayi ka saka ta nemo wannan takardar."
"Ina tunanin daga ita har Mamy ba su san da kamfanin ko takardun su ba."
"A yadda suka mayar da Dady ba zai ɓoye ma ta komai ba, don haka ka sa ta nemo shi yana da mahimmanci sosai."
"Okay sir, in sha Allah zan saka ta kawo su."
Sallama suka yi ya katse kiran wayar sannan ya shiga motar ya yi ma ta key ya fara tafiya. Kallonsa Yasmeen ta yi ganin lokaci daya yanayinsa ya sauya sai ta fasa ma sa maganar da ta yi niyya, don ta san halinsa idan ransa ya ɓaci ba za ta ji dadi ba, barinsa shi ne mafi sauki."
Har suka isa gidan ba wanda ya yi magana, horn ya yi maigadi ya wangale ma sa gate ya shigar da motarsa ciki.
Satar kallonsa ta yi kafin ta ce .
"Thank you my husband to be..."
Kallon ta ya yi ta fita da sauri tana murmushi.
Tura hannunsa ya yi cikin suman kansa yana yamutsawa. Sannan ya kifa kansa kan sitiyarun motar.
Tsawon mintuna biyar har motar Abbi ya shigo direban Sa ya yi parking ya buɗe ma sa ya fito. Har zai wuce ciki ya lura da motar Jalal da ke kunne. Ya karasa jikin motar ya yi knocking glass ɗin.
Sai a lokacin Jalal ya ɗago tare da sauke glass ɗin motar. Ganin Abbi ne ya sa ya bude murfin motar ya fito. Cikin kulawa Abbi ya ce .
"Son kana lafiya dai ko?"
"Alhamdulillah Abbi ."
"Ka tabbata ba wata matsala?"
"Bo komai Abbi kawai dai na gaji ne."
A tare suka jera suka shiga cikin gidan suna fira.
*Washegari*
Suna zaune a babban falon gidan suna fira. Abbi, Ummee, Jalaluddeen, Yusuf, da kuma Yasmeen. Fira suke yi cikin nishadi, kafin suka ji horn ɗin mota.
"
Ganin karfe uku ne ya sa Ummee cewa.
"Ko Yaya ya iso ne?"
Ta yi maganar tana kallon Abbi.
"Ina ganin ya iso don lokacin da ya faɗa kenan yanzu."
"Lafiya dai ko Abbi?"
Cewar Yusuf yana kallon Abba.
"Lafiya lau Alhamdulillah, abun farin ciki ne ma za mu ƙulla."
"Alhamdulillah. Wani abun farin ciki muka samu?"
"Muna son gobe a ɗaura auren Jalal da Yasmeen yake so a tattauna."
Da sallama Dad ya shigo cikin falon suka amsa ma sa, sannu da zuwa suka yi ma sa dukansu. Ya amsa sannan ya zauna suka gaisa.
Ummee da kanta ta jawo ma sa abun sha ya sha sannan ya yi gyaran murya.
"Duk da ba na da lokaci ina kan hanya ne, sai dai sanin gobe ne Jalaluddeen zai tafi ya sa na zo."
"Haka ne Yaya."
"Cewar Ummee."
"Don haka rashin sanin cewa idan ya dawo washegari za'a ɗaura ma su aure. Na ɗauka cewa sai ya kammala aikinsa zai dawo, to sai aka samu akasi ba yadda na yi tunani ba ne, don haka ya kuke gani."
"Kawai a ɗaura ma su aure ya tafi da matarsa kowa ya huta!"
Cewar Ummee tana kallon Yayan nata.
"A'a ku bari a ji daga bakinsa duk yadda ya ce haka za'ayi. "
Cewar Abbi yana kallon Jalaluddeen.
"Son ya ke ce shin a ɗaura ma ka aure kana da ra'ayin tafiya da matarka ba za mu takura ma ka ba?"
"Abbi ina neman alfarma a yi hakuri a bari na karasa aikin da na je yi idan na dawo sai a ɗaura auren ko da kuwa ranar da na dawo ne."
_Nasreen_
Bayan an kai amarya gidanta ta samu isasshen natsuwa sun koma masaukin su sannan ta dauki waya ta kira lambar wayar Ma'eesha.
Bugu biyi ta ɗauka cikin nitsatsiyar muryarta ta yi ma ta sallama.
"Assalamu alaikum ƙawata."
"Rike sallamar ki ina son ki saurare ni da kyau."
Cikin mamaki Ma'eesha ta ce.
"Ikon Allah sallama bushara ne da saƙon aminci, amincin shi ne ba ki so?"
"Duk ba wanan ba, ina mijinki yana gida?"
"A'a ya yi tafiya."
Sai da Nasreen ta yi dariya sosai kafin ta ce .
"Idan kika wayi gari wanda yake tare da ke kika yarda da shi kika ba shi amana ya ci amanarki ya yi ma ki karya fa?"
"Ba sai kin tambaye ni ba, na tsani ƙarya na tsani yaudara na tsani mai aikata su ko ma waye! Ai ke ma kin sani ba na son ƙarya idan na kama mutum da wanan halayyar zan iya rabuwa da shi kin sani. Amma me ya sa kika yi ma ni wanann tambaya?"
"Amsar yaba tare da ni ko ba faɗa ma ki ba za ki yarda ba dan idanun ki sun rufe, amma idan na zo na nuna ma ki video da photo hakan zai tabbatar ma ki da gaskiyan lamari, ki gode wa Allah da na je biki a Abuja don zuwan ki ne."
Daga haka ta katse kiran wayar yayin da Ma'eesha ta bi wayar da kallo cikin rashin gane in da zancen nata ta dosa.

Page6️⃣7️⃣
Na tambaye ka wace ce ita ba ka sanar da ni ba, yanzu ka shirya faɗa ma ni ne?"
Juyo wa ya yi ya kalle ta ya n da take ƙaraso wa cikin ɗakin. Zama ta yi gefensa ta dafa kafaɗar sa tana cewa.
"Na ji an ce uwa tana iya karantar idanun ɗanta, tabbas na yarda da wanann domin kuwa tun ranar da ka iso garin nan na lura da hakan. Amma sai ka ce ma ni ba haka ba lokacin da na tambaye ka, har na yi ma ka maganar nan ka nuna ma ni cewa ba komai."
Shiru ya yi ya dauke kansa daga duban mahaifiyar tasa don ta yaya zai iya sanar da ita cewa yana da mata bayan ba su suka sura ma sa ita ba ba su san da zancen ba. Tabbas wata zuciyar na ingiza shi akan cewa ya sanar da ita komai amma yana gudun abun da zai je ya dawo. Don haka a ƙasan ransa ya ji cewa gara ya bari idan ya kammala aikinsa da ya kai shi can garin ne sai ya dawo tare da Ma'eeha ya ajiye ta gidan Mom tare da gabatar da ita ya sanar da ita komai. Zuwa lokacin ita ma Ma'eesha zai fara sanar da ita ko shi waye kafin ya sanar da danginsa. Da wanan tunanin ya saki murmushi yana cewa.
"Mom kin dawo?"
"Na dawo ya kake ya mutanen gida?"
"Suna lafiya lau Alhamdulillah."
"Ma sha Allah. To meye labari ?"
Ta faɗa tana zuba ma sa idanu .
"Mom ba komai fa kamar yadda na ce, idan ma akwai zan sanar da ke idan lokaci ya yi?"
Jingina kai ta yi tare da cewa .
"Allah ya kawo lokacin na alkhairi."
"Amin ya Allah."
Shiru ne ya biyo baya kowa da abun da yake ransa, kafin ta katse shirun ta hanyar cewa.
"Gobe ne tafiyar taka ko?"
"In sha Allah."
"To Allah ya kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya ya kare ka a duk in da kake ya ba ka nasara."
"Amin ya Allah Mom. Na so na a ce na ƙara kwana biyu saboda Sadik ya kai ni wajen dangin ki da ban san su ba mu ga juna da su. Musamman mutanen Katsina ya dace na gan su har da wanann rigimammiyar tsohuwar da nake jin labarin ta wajen Sadik. "
Dariya ta yi tana cewa.
"Mahaifiyar tawa ce rigimammiyar tsohuwar sau nawa ka ganta ?"
"Na gan ta ai lokacin da kika taɓa samun accident din nan ta zo a lokacin har ta addabi jama'ar asibiti idan an ce ta yi shiru ta fara masifa."
Dariya ya yi suka cigaba da fira har Saddiƙa ta yi sallama ta shigo ɗakin.
"Wato Yaya ka shigo ko ka neme ni ko?"
"Afuwa sis ya kike, ina Sadik."
"Yanzu ya shigo ya ce bari ya yi wanka ya zo ya same ka. "
"Ke kina gidan dama?"
"Eh ina nan kawai dama na shiga ɗaki ne ina jiran shigowar Mom, da ba fito Dad ke sanar da ni kana ciki."
Zama ta yi kan carpet tana cewa.
"Zan iya zama ayi firar da ni?"
"Eh za ki iya ma na, tun da gulma kike son ji."
Dariya Jalal ya yi yana kallon yadda take tura ba ki. Zuwa can ta ce.
"Yaya Jalal wai ka fasa auren Yasmeen yanzu sai ka dawo tafiya kuma, to me ya sa bayan ni da ita duk mun gama sanar da kowa zancen ga shi har kuka sai da ta yi."
"Ai na san giulma ce ta kawo ki nan yanzu."
"Mom na tambaye shi ne fa na ga ƴar uwata ƙawata na cikin damuwa na rashin auren da ya sa aka ɗaga, ya bar ƙawata cikin damuwa da zullumi."
"Kar ki damu sis komai lokaci ne, idan Allah ya kawo ranar sai ku ga komai sai ya zama tarihi, na fi son na kammala abubuwan da na saka a gaba a halin yanzu."
"To Yaya Jalal Allah ya taimaka ya yi jagoranci."
"Amin ya Allah."
Sadik ya shigo da sallama a bakinsa, suka amsa ma sa ya gaishe da Yaya Jalal kasancewar tare da Mom ya dawo aiki shi.
Zama ya yi suka cigaba da fira cikin farin ciki da nishadi har karfe sha daya na dare ta yi ba su sani ba. Daidai lokacin Yusuf ya shigo ɗakin da shi da Dad. Bayan sun yi sallama sun shigo ne Jalal ya kalli Yusuf yana cewa.
"Har ka dawo ne?"
"Eh yanzu fa karfe goma sha daya na dare."
Duk sun yi mamaki sosai ba kadan ba, don ba su yi zaton lokaci ya tafi har haka ba. Sallama Jalal ya yi ma su amma kafin nan sai da ya turawa Sadik kuɗin ma su yawa a account din sa ya ce ya yi siyayyan gida kayan abinci da kayan bukata.
Godiya da sa albarka Mom da Dad suka yi ma sa sannan ya yi ma su sallama, har wajen motat Yusuf suka raka su, sai da suka bar gidan suka koma ciki, sai dai zuciyar Mom na ayyana ma ta akwai abun da Jalal ke ɓoyewa.
Ko da suka koma gida Ummee da Abbee na zaune a falo suna sai Yasmeen da ke can gefe.
Da sallama suka shigo yayin da Abbee ke cewa .
"Yauwa ga su nan ƴan halak sun bayyana, hankalinki ya kwanta?"
Kallon su Jalal ya yi yana cewa.
"Ga Ummeenku ta damu ba ku dawo da wuri ba ga dare ya y,i har za ta kira ku na hana ta na ce dare ya yi na san duk in da kuke yanzu za ku dawo. Ya su Dad din da Mom."
"Kowa na lafiya suna gaishe ku."
Cewar Yusuf yana zama kan kujerar mai zaman mutum ɗaya.
"Son ba wata matsala ko?"
Ta yi maganar tana kallon Jalaluddeen.
"Ba komai Ummeena, in sha Allah kuma tafiyar safe zan yi."
"Ba damuwa Allah ya kai mu ya tsara mun kai a duk in da kake ."
"Amin Ummeena."
Abbee da Umme suka tashi suka shiga ciki yayin da Jalaluddeen ya tashi ya koma gefen Yasmeen ya zauna.
"Meye matsalar ki."
Shiru ta yi ma sa tana wasa da wayarta.
"Ki yi hakuri na fahimce ki, ni ma nan da kika gani dole ta sa na ɗaga auren saboda na fi son idan na kammala aikina na dawo sai ayi auren hankali na ba zai rabu biyu ba. "
Cikun karaya ta ce.
"Na ga kamar gujewa auren kake yi ne."
"Wa?"
Ya faɗa yana fito fito da idanunsa.
"Kai ma na Yaya Jalal."
"Wane ni? Waye za'a ba sa zugegiyar mace kamar ki ya ce baya so.."
Madadin ta sauko sai ta sake tunzura tana cewa.
"Wato ba ka ni aka yi ba cewa ka yi kana so na ba ko? Na sani ba sai ka nanata ma ni ba na san kai ba ka ce kana so ka ba aka ba ka ni."
"Ya Salam ba haka nake nufi ba, kada ki juya mun zance ki fahimce ni."
Tashi ta yi tana kuka wanda ya san kukan baya rasa nasaba da burin da ta ci na auren wanda shi kuma ya ruguza shirin nata. Bedroom ɗin ta ta nufa tana kuka. Bin bayanta ya yi zuwa ƙofar bedroom ɗin nata, ya tura ya ji ta rufe da key ta ciki.
Barin wajen ya yi Yusuf ya bi shi da kallo yana dariya, hararar sa ya yi ya wuce bedroom ɗin sa.
Ita kuma jin bai yi ta knocking yana roƙon ta ta bude ma sa ƙofar ba ne ya saka ranta ya kara ɓaci.
Yana shiga cikin bedroom ɗin sa ya ci karo da kiran wayar Ma'eesha na shigowa cikin wayarsa.
Kiran ya bari ta katse sannan ya bi bayan kiran nata.
"Assalamu alaikum warahmatullah."
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya amsa ma ta.
"Wa'alaiki salam warahmatullah mar'atussaliha."
Murmushi ta yi cike da nishadin jin muryarsa.
"Na'am mijina ina wuni."
"Lafiya lau Alhamdulillah ya karfin jikin?"
"Na warke dama zazzaɓin rashin sanin halin da kake ciki ne tun da na ji muryarka na warke."
Murmushi ya yi yana mai jin dadin kalamanta da suke kwantar ma sa da hankali.
"Me kika shirya mun za ki tanadar ma ni gobe idan zan zo?"
"Komai da na san kana so na tanadar ma ka shi ."
"To godiya nake mar'atussaliha, Allah ya yi ma ki albarka ."
Da Amin ta amsa ma sa , daga nan ta ce ma sa .
"Bari na bar ka haka nan na san ba kudi ne da kasa ba ballantana ka saka kati a waya."
"Waye ya ce ma ki ban da kudi ?"
"Na san a yadda ka yi tafiyar nan ba ka da kudi ai. Ms ce ba?"
"Kika ce me?'
"Na ce ko za ka samu wanda ke da account number sai ka tur mami na saka kudin da Z ka karamar mota. Kasancewar da za ka tafi wata babbar motar kaya fa ka bi na san ka sha bakar wahala sosai to hakan ya sa na ce bari na tura ma ka kuɗin motar cikin kuɗin tallafin da muka samu."
"A'a kada ki damu wanann karon ba babbar mota zan bi ba, ƙaramar mota zan bi na samu wadan da suka bani kudi na san za su ishe ni."
"To shi kenan Allah ya sa hakan ne mafi alkhairi, Allah ya dawo mun da kai lafiya ."
"Amin ya Allah na gode sosai Allah ya ma ki albarka ."
"Amin mijina."
Sallama suka yi sannan ya katse kiran wayar yana tunanin idan ya tashi gobe yin da jirgi zai bi kuma ki awa daya ba zai cika a jirgi ba zai isa, don haka ya yanke shawarar zai sauka a hotel ɗin sai zuwa yamma ya isa gida gudun kada ta zarge shi. Da wannan tunanin ya kwana.
_Nadra_
Bayan ya gama ayyukan gidan kamar yadda ta saba, ta share ko ina ta gyara, ya saura daura ɗakin Fahad wanda ta san yana kwance tama jira ya tashi.
Kitchen ta shiga don haɗa ma su breakfast, nan da nan ta kammala ta je ta yi wanka. Riga da siket ta saka na atamfa wanda ya zauna ma ta ya yi ma ta kyau sosai a jiki.
Ɗakimsa ta nufa ta ji saukar ruwa a bathroom, hakan ya tabbata ma ta fa yana wanka kenan.
Ɗakin Sidra ta tafi ta tarar da ita har ta yi wanka ta shirya cikin ƙananan kaya riga da wando.
"Ina kwana Aunty."
"Lafiya lau."
Ta amsa ma ta ba yabo ba fallasa.
"An tashi lafiya ya jikin naki."
"Da sauki Alhamdulillah."
"Ma sha Allah, Allah ya kara ma ki lafiya.,"
"Amin ."
"Dama na gama haɗa breakfast ne shi ne na zo na kira ki za ki fito ne ko na kawo ma ki naki a nan?"
"A'a zan zo nan na ci tare da ke."
"Okay to mu je.
A tare suka fita har suka haura sama , a dinning area suka karasa in da Nadra ta ja ma ta kujera don ta zauna ."
"Bisimillah ki zauna ina zuwa ."
"Me zan zuba ma ki Aunty?"
"Ke ma kin san na fi Shan tea da safe da soyayyan ƙwai da hankalin turawa."
Murmushi ta yi ta fara hada ma ta tea ta haɗa ma ta komai da komai da take buƙata.
"Bari na je na duba ko Yaya Fahad ya gama shirya wa."
"Hmmm da alama dama can kina son Fahad munafurci ne ya sa kika nuna ba ki so ko, yayin da kika ma ni alkawarin cewa za ki rabu da Fahad ni kuma ya aure ni shi ne kika yi kane-kane , amma ku saurari abin da zai biyo baya daga ke har shi mayaudarin ."
Daidai lokacin suka ji ƙarar buɗe kofa kamar mutum ba fitowa. Ƙamshin turarerensa ne ya fara iso wa gare su. Yana sanye cikin suit farar takaminsa baki da farin glass da yake sanye da shi.
Sai da zuciyar Sidra ta buga amma kallo ɗaya yi ma ta ya dauke idanunsa daga kallon ta . Ganin hannunsa time da wasu file ne ya saka Nadra ta mike tsaye tana cewa .
"Barka da fitowa Yaye Fahad."
"Barka dai Nadfah."
Ya faɗa yana rungumo ta jikinsa, kunya ce ta lulluɓe ta don ta tabbatar Aunty Sidra na kallon su.
"Kokari. Zame jikinta ya yi yana ce w.
"Bisimillah ka zo ka yi breakfast."
''ina sauri ne ana jira na yanzu n nan idan Na dawo zan ci."
Jinjina kai tai ta yi tare da cewa a dawo lafiya.
"Ba za ki raka ni ba.?'"
Ya yi maganar yana nufar hanyar sauka yana kuma cewa .
"Aunty Rahama za ta zo anjima ."
Cikin farin ciki da jin dadi ta ce Allah ya kawo ta lafiya.
Yana fita wayarsa ta fara ruri, Aunty Rahama ce take kiransa. Ya daga yayin da ya isa wajen motarsa.
"Hello Aunty Barka da safiya."
"Barka dai ya kake ya Nadra."
"Muna lafiya duka."
"Na ga message naka kana sanar da ni Sidra na gidanka, yanzu haka su Mama suka bar ta?"
"Eh wallahi abun ya dame ni."
"Ka kwantar da hankalinka ina nan zuwa wallahi yau sai ta bar gidan nan, sai dai ta koma gidan ubanta ko yanka naman jikinta zai yi sai dai ya yi. Kai kafin ma na zo ma sai na biya na sanar da iyayenta halin da ake ciki kuma na sanar da su yau sai ta bar gidanka."
Cike da gamsuwa ya jinjina kai yana yi ma ta godiya, sallama suka yi ya katse kiran wayar ya shiga motarsa tare. Da yi wa motar key ya bar gidan.

Page6️⃣8️⃣
Cike da gamsuwa ya jinjina kai yana yi ma ta godiya, sallama suka yi ya katse kiran wayar ya shiga motarsa tare da yi wa motar key ya bar gidan.
Nadra kam zama ta yi suka fara yin breakfast. Bayan kamar mintuna ashirin suna zaune wajen sai ga text message ya shigo cikin wayar Nadra. Ganin sunan Fahad ya sa Sidra ta yi saurin ɗaukar wayar da sauri kafin Nadra ta ɗauki wayar.
Bude messages ɗin ta yi ta fara karantawa kamar haka.
*Hi my Nadfah ya kike? Am sorry na bar gida ba mu yi gaisuwar safe yadda ya kamata ba ana jira na ne shi ya sa. Ya gajiyan daren jiya na gode sosai zuma ta. Tabbas daren jiya kin jiyar da wanan majidaɗin daɗi mara misaltuwa thank you so much, I love you more than anything*
Sidra na gama karantawa sai zuciyarta ke tafarfasa ta juya ta kalli Nadra ta ga ita ma kallon ta take yi. Don dama ta ji ba daɗi daukar ma ta wayar da ta yi. Don haka ta fara jifar Sidra da wani kallo mara misaltuwa.
"Munafukar banza kawai ke sa muka yi za ki rabu ma ni da saurayi na amma kika yi shiru kika sakar ma sa jiki jiki har ya kika samu kansa ko?"
"Aunty Sidra maganar gaskiya ya kamata ko hakura da Yaya Fahad tun da ba shi kadai ne namiji a wanann duniyar ba. Matar mutum kabarin sa, wata ba ta auren mijin wata hakazalika wani baya auren matar wani, aure nufin Allah ne shi. Ban taɓa tunanin zan zauna inuwar aure da Yaya Fahad ba, haka shi ma bai yi zaton ni ce zan zama matarsa ba, amma da Allah ya ƙaddara ba ga shi mun yi aure ba muna zaune lafiya ya yarda da ƙaddarar sa ya karɓe ni matsayin abokiyar rayuwarsa, ni ma haka na yarda da shi a matsayin abokin rayuwata. To ke me ya yasa ba za ki yarda da ƙaddara ba a matsayin ki ba musulma ki nemi zaɓin Allah. A gaskiya da ba na ƙaunar Yaya Fahad amma a halin yanzu ina jin sa har ƙasar raina, ban san yaushe ne na kamu da son sa ba amma tabbas na san yanzu ina son sa. Shi ma yana so na don haka ki haƙura ki fauwala wa Allah lamuranki zai taimake ki, don Yaya Fahad bakya gabansa ko ganin ki ba ya son yi, kamar yadda ya ce idan ya bar abu ya bar shi kenan har abada ba zai dake waiwayar sa ba to haka ne. Fata na Allah ya ba ki mijin da ya fi Yaya Fahad."
Tana faɗar haka ta tashi da niyyar za ta bar wajen, ita ma Sidra ta yi saurin mikewa tare da cewa .
"Ni kike faɗa wa wadan nan maganganun saboda na zo gidan aro?"
"Aunty Sidra wannan gidan ba gidan aro ba ne gidana ne na har abada sai mutuwa ce z ga fitar da ni daga cikkin...."
Kafin ta mai zancen maganar ta Sidra ta ɗaga hannu da niyyar kai wa Nadra mari. Cike da zafin nama Nasara ya yi saurin riƙe hannun Nadra salqfin ta ce .
"Kada ki kuskura hannu ki taɓa jikina, domin yanzu ba da ba me. Kika mare Ni sai na rama wallahi sai dai mu yi kare Juni biri jini wallahi."
Cike da mamaki take kallon Nadra domin ba wacce ta sani ba ne, ba wacce ta saba rayuwa da ita ba ne, domin da ita ce, ba wacce ta saba zagi har ta mare ta ba ce, sai dai yi kuka ta ba ta hakuri. Ba wacce ta saba ba ce. Yau wata ce take gani a gabanta ba waccen Nadra ba ce."
Nadra ta tashi ta bar wajan dan ta fara gajiya da magana ɗaya da Yayan take yi ma ta. Kullum zuga ta take yi akan ta rabu da Fahad ta yi ma sa wulakanci ko zai yi zuciya ya sake ta. Ita kuma ba za ta iya ba gaskiya ba za ta iya ba domin saɓawa Allah ta sabawa Iyayenta don ta faranta wa Aunty Sidra ba.
Saman gadonta ta faɗa tare da sakin kuka , gabaɗaya ta rasa yadda za ta yi da rayuwarta, ga shi lokaci guda ta kamu da soyayyar Fahad ba tare da ta shirya wa hakan ba. Ga Aunty Sidra ta ƙwallafa wa ranta dole sai da shi za ta rayu.
_Aunty Rahama_
Bayan ta gama shirin ta na zuwa aiki yara shi an kai su school ne ta fito daga gidan.
Driving take yi a motar cikin nutsuwa duk da ta makara da zuwa aiki amma da safen nan ne take da tabbacin cewa za ta samu Abba a gida.
Tana isa ƙofar gidan ba ta yi horn ba ta fito daga cikin motar, knocking ƙaramar ƙofar ta yi nan da nan maigadi ya taso ya buɗe.
"Barka da aiki Mallam."
"Yauwa Hajiya ina kwana?"
"Lafiya lau, Alhaji yana ciki kuwa ko ya fita?"
"A'a yana ciki?"
Ya yi maganar yana matsawa gefe don ba ta hanyar shiga.
Ta shiga ciki har zuwa ƙofar falon za ta yi knocking kenan dai ga Abba ya bude kofar zai fito.
Tana ganinsa ta durƙusa cikin girmamawa ta ce.
"Ina kwana Abba.?"
"Lafiya lau, Rahmatuko ?"
"Eh Abba."
"To suna ciki ki shiga ni za fita?"
"Ai wajen ka na zo Abba."
"To bisimillah shigo."
Ya yi maganar yana komawa ciki Aunty Rahama ta bi bayansa.
Da sallama suka shiga falon Umma da Ammi dake zaune a falon suka amsa.
Aunty Rahama ta gaida kowa cikin girmamawa sannan ta zauna ta kalli Abba ta ce.
"Da farko dai Abba ba maganar Sidra zan yi ma ka ba kasancewar ba ka son a yi zancen ta. Amma ina son sanar da kai ne matuƙar ba ka dawo da Sidra gidanka ba to haƙiƙa za ta kasance barazana ce ga rayuwar auren Nadra."
Da sauri suka kalle ta cike da mamaki, Abba ya shiga tashin hankalin jin cewa rayuwar auren Nadra zai iya samun tangarɗa akan Sidra."
"Meke faruwa?"
Cewar Ammi tana kallon Rahama.
"Sidra ta dage ba za ta zauna a gidan mahaifin mu ba sai gidan Nadra a halin yanzu a can gidan Nadra take zaune wanda na san zaman dole matsala za ta biyo baya."
Nan ta ba su labarin abun da ya faru daga rashin lafiyar Sidra har zuwa komawar ta gidan Fahad.
"Ta ina hakan za ta faru wallahi na tabbatar ba alkhairi ne zai kai Sidra gidan Nadra ba sai don ta kashe ma ta aure, dama tana jin baki cikin an aura wa Nadra Fahad.
Abba kasa magana ya yi illa ya dauki wayarsa ya kira ƙanwarsa Laraba.
Bugu biyu ta daga ya fara magana cikin ɓacin rai da takaici
"Laraba ina son idan kin gama abun da kike yi ki tafi gidan Maimaina ku hadu ku je gidan Nadra ku dawo da Sidra gidana ƙafarta ƙafarku, tana can ta tare a gidanta."
Daga haka ya katse kiran. Wayar, daidai lokacin Aunty Rahama ta yi ma su sallama ta tafi. Idanun Abba kawai za ka ƙalla ka san cewa ransa a ɓace yake .
_Jalaudeen_
Fitowa ya yi daga cikin gida yayin da gabaɗaya mutanen gidan suka fito don yi ma sa rakiya..
Mota ɗaya za su tafi airport da ita, miyar Yusuf ce
"Yusuf ya shiga mazaunin direba yayin da da Jalaluddeen ya zauna gefensa. Bayan motar kuwa Abbi da Ummee ne a baya sai Yasmeen da take zaune a gefen Ummee.
A hankali suke tafiya yayin da Yusuf ke cewa.
"Amma idan ka dawo wanan karon shi ne dawowar ka ta kammala aikin ko?"
"In sha Allah, don na riga na gama haɗa bayanan da zan haɗa, kama su shi ne abun da ya rage, da kuwa wasu abokan harkar ta su da nake so na tabbatar."
"Allah sarki bro kana kokari ma Allah ya bada nasara."
"Amin ya Allah."
"Umme da Abbi suka hada baki wajan amsa wa.
Har suka isa airport fitar fitar aikin nasa suke yi. Bayan sun fito daga motar ne Yasmeen ta tsaya a gabansa tana ma da wani kallo mai wuyar fassara.
Komawa ya yi gefe wanda gane abun da yake nufi ya sa ta bi shi ta tsaya a gabansa fuska ba walwala.
Murmushi mai sauti ya saki kafin ya ce .
"Yasmeen rigima ko gaishe ni fa ba ki yi ba."
Shiru ta yi masa wanda ganin haka ya sa ya ce .
"Okay."
Yana kokarin barin wajen.
Rigarsa ta rike tana girgiza kai.
"Me zan yi ma ki bayan fushi da ni kike yi?"
"To ka tsaya na daina."
Zuba ma ta idanu ya yi ya rungume hannayensa a ƙirjinsa.
"Kin ga na fahimce ki ba yadda kike tunani ba ne, na ina nuna ma ki halin ko in kula ba ne, kawai dai yanayin aiki ne ya sa ba na da lokacin da zan dinga kiran ki ko kuma ke ki kira ni ki same ni. Amma ai ba dole sai ta haka nan ne za ki yarda ina son ki ba, ita soyayya a zuciya take, fatan kin fahimce ni, kina zuciyata kowane lokaci kowane hali kar ki manta da wanan ."
"Son lokaci ya yi fa jirgi baya jira."
Ya ji Muryar Abbi yana ma sa magana.
Wayarsa ya ɗauka ya yi ma ta transfer na kudi a account din ta sannan ya ce.
"Sai mun yi waya ki kula da Kanki."
Murmushi ta yi sanan ta bi bayansa suka koma wajen da su Abbi ke jiran su.
_Nadra_
Bayan kukan da ta yi akan abun da Sidra ta yi ma ta ne sai barci ya ɗauke ta a wajen. Kasancewar daren jiya ba ta yi isasshen barci ba.
Sidra kuwa mamaki da al'ajabi ya hana ta cewa komai kuma ta kasa barin wajen. Mamaki take yi shin har ta yi lalacewar da Nadra za ta kalli idanun ta ta yi ma ta magana yadda ranta yake so? Shin sanyi ta yi ne? Ina zafin nata yake, yarinyar da idan ta yi ma ta abun da bai yi ma ta ba za ta ɗaga hannu ta mare ta amma yau ta rike ma ta hannu yayin da take da niyyar marin ta? Sanann ta faɗa ma ta zancen da ranta yake so. Tabbas tura ta kai bango dole ta nema wa kanta mafita kuma ba ta jin za ta iya hakura da soyayyar Fahad.
Tsawo lokaci ta ɗauka a wajen ba ta motsa ba, har aka dinga danna ƙararrawar ƙofar, ba ta ji ba daga farko Sakamakon ta yi zurfi a duniyar tunanin da ta lula.
Daga baya ta sauka downstairs ta nufi kofar da niyyar budewa a tunanin ta Fahad ne Nadra ta sanar da shi abun da ya faru.
Sai dai tana buɗe kofar mutanen da ta gani tsaye a bakin ƙofar ne suka saka hanjin cikinta kaɗawa. Ja da baya ta yi tana kallon Gwaggo Maimaina da ke jifanta da wani mugun kallo, dama tana tsoron ta kasancewar ita ma tana da zafi sosai .
"Ja da baya ta cigaba da yi yayin da Gwaggo Maimaina ta finciko wuyar rigarta tana cewa.
"Munafuka me ya kawo ki zama gidan ƙanwarki, kashe ma ta aure kike so ki yi ko?"
Nan ma girgiza kai ta yi ba tare da ta ce komai ba.
"Tattara kayan ki yanzu ki zo mu tafi."
"Gaskiya ba in da zan ta..."
Kafin ta kai karshen zancen Gwaggo Maimaina ta wanke ma ta fuska fa marin da ya sa ta hantsilawa. Ita dai Gwaggo Laraba ba ta ce komai ba ta yi shiru tana kallon su.
"Har kina da bakin magana eye fitsararriya mara kunya. To wallahi tun da ubanki ya ce ki dawo gida wallahi sai kin tafi."
"To wai shi ya kore ni daga gidansa, kuma kuma danginsa har gidajen ku na ce kuka kore ni sannan wasu sun karɓe ni ina zaune a gidansu a ce na tafi? Sai dai idan wadanda suka ce na zo na zauna suka kore ni daga gidansu shi ne zan tafi ."
"Ƙarya kike yi Sidra ƙafata ƙafarki sai kin tafi kin bar gidan nan ehe!"
Gwaggo Laraba dai ba ta ce komai ba ta haura sama ta nufi ɗakin Nadra.
Knocking ta yi ta ji shiru sai ta tura kofar da sallama a bakinta.
Hango Nadra ta yi kwance saman gado tana barci, ga busashshen hawaye a idanunta da alama sai da ta ci kuka kafin ta yi barci. Cike da tausayin ta Gwaggo Laraba ta karasa cikin ɗakin.

Page6️⃣9️⃣
Hango Nadra ta yi kwance saman gado tana barci, ga busashshen hawaye a idanunta, da alama sai da ta ci kuka kafin ta yi barci. Cike da tausayin ta Gwaggo Laraba ta karasa cikin ɗakin.
"Ta san wanann hawayen ba zai rasa nasaba da Sidra ba, domin kuwa ta ɗan Fahad da wuya ya saka ta kuka. Don ko farkon aurensa da ya nuna baya son ta bai saka ta kuka ba ballantana yanzu da yake son ta.
Sunkuya wa ta yi tana shafo fuskarta daidai in da hawayen ya bushe.
A hankali Nadra ta buɗe idanunta ta sauke su akan Gwaggo nata.
"Gwaggo ke ce ko mafarki nake yi ?"
"Ni ce Nadra ba mafarki kike yi ba. Tashi zaune ta yi wasu sabbin hawaye na zubo ma ta .
"Daina zubar da hawayenki kin ji?"
Ai kamar ta ce ta kara ne don kuka ta saka ma ta wiwi. Cikin tashin hankali ta zauna bakin gadon tana rungume ta tare da bubbuga bayanta alamar rarrashi.
Ajiyar zuciya take saukewa kafin ta fara magana cikin rauni.
"Gwaggo meye lafin ƴaƴan da suka yi biyayya ga iyayen su wajen cika ma su burin su? Ya sa hakan zai janyo ma su ƙasƙanci da wulaƙanci a duniyar ma'abota sadaukarwa? Shin laifina ne ko kuma ni ce na ce Abba ya aura ma ni Yaya Fahad ballanta har Aunty Sidra ta ɗora alhakin hakan a kaina?"
Kuka ne ya ci karfinta wanda hakan ya saka Gwaggo Laraba sake rungume ta.
"Gwaggo wallahi Yaya Fahad baya son Sidra yanzu ya tsani ganinta ko maganar ta baya so ina yi ma sa, tana zaune a gidan nan ne don saboda na nemi hakan daga gare shi, wanda shi kuma ba zai ki amince wa bukatata ba. Da a ce na ga yana son ta ko kuma zai iya auren ta wallahi zan hakura na bar ma ta shi su yi rayuwar auren su kamar yadda suka tsara. Amma shi ya ce ya hakura da ita har abada ba zai iya auren ta ba. To meye amfanin na bar ma ta shi bayan ba aurenta zai yi ba?"
Ɗan bubbuga bayanta Gwaggo Laraba ta yi tana cewa.
"Daina kuka ya isa haka nan kin ji, ai ba zai taɓa yiwuwa ba ne a ce ya sake ki sannan ya zo mu ba shi auren Sidra ba, idan ba rashin hankali irin nata ba da rashin tawakkali irin nata ba ai hakan ba mai yiwuwa ba ne."
Nadra ta share hawayenta sannan ta kalli Gwaggo Laraba ta ce.
"Gwaggo me za ki ci ne daga ma ki ne?"
"Hutar da Kanki Nadra mun zo ɗaukar Sidra ne bisa umarnin mahaifinku."
"Abba ya yafe ma ta ne ko?"
Ta yi tambayar cike da farin ciki, dama ita birninta bai wuce Abba ya daina fushi da Sidra ya yafe ma ta ba. Don fushin iyaye masifa ne akan ƴaƴan su.
A tare suka fito daga ɗakin suka sauko downstairs daidai lokacin da Gwaggo Laraba ta tasa Sidra a gaba tana jan akwatin kayan ta .
Cikin girmamawa Nasara ta gaida Gwaggo Maimaina , ta amsa mata cike da murna.
"Nadara ya hakuri da rayuwa ya mai gidan?"
"Lafiya lau Alhamdulillah ya fita."
Kallon Sidra dake jifanta da wani kallo ta yi kafin ta ce.
"Aunty Sidra da alama Abba ya sauko ya yafe ma ki,na yi farin ciki da haka, Allah ya..."
"Dalla rufewa mutane baki munafuka, kin sanar da shi ina gidanki saboda a fitar da ni da..."
Ba ta kai ƙarshen maganar ta ba Gwaggo Maimaina ta finciko wuyar rigarta ta hankada ta waje, sai da ta faɗi. Sannan ta koma ciki ta dauko akwatin kayanta ta fito da shi. Gwaggo Laraba na biye da ita a baya Nadra na n take ma su baya.
"Daughter juya ki koma gida Allah ya yi ma ki albarka, ku gaida mijin naki idan ya dawo."
Tana so ta yi wa Sidra magana amma ta kasa, don ko ta faɗa ma ya cewa ba ita ce ta samar da Abba zaman ta gidan ba yarda za ta yi ba. Don haka ta yi shiru idanunta na cika da ƙwalla, har direba ya ja motar suka fice daga gidan.
Komawa ta yi ciki tana rusa kuka wanda ita kanta ba ta san ko na mene ne ba.
_Ma'eesha_
Da taimakon A'isha wacce ta taya ta aiki ta gudanar da komai. Girki kaloli suka yi saboda tarbon Makahon mijinta. Bayan sun kammala ne ta zuba a kulolli tana kiran dawowarsa. Kasancewar ya ce ma ta garin da nisa dai yamma zai iso. Ta zuba wa A'isha ta ce ta ɗauka ta tafi da shi gida, sannan ta ba ta kudi 5k cikin kuɗin tallafin da aka kawo ma ta.
A'isha na barin gidan dai ga Nasreen ta yi sallama ta shigo kamar an jefo ta daga sama.
"Assalamu alaikum ina Ma'eesha take ?"
"Wace'alaiki Salam warahmatullah . Lafiya wannan kiran haka Nasreen."
Ba ta ce komai ba ta janyo hannun Ma'eesha suka shiga cikin ɗalo .
Ita dai ma:eesha ya tsaya na kallon ikon Allah.
Wayarta ta danna sai ga photon Makaho shi da Yasmeen.
Sannan ta ga video shi da Yasmeen ta rike ma da hannu sune tafiya . Sai ta ga na washehari.
"Na gani amma gaskiya Allah ya yi halitta kin ga wani kamanni da na gani? Gaskiya kamar ta yi yawa."
Wani banzan kallo Nasreen ta yi ma ta kafin ta ce.
"Wani irin kamanni to ba wani kama wanan mijinki ne Khalifa Makaho ."
"Ba yadda haka. Za ya yiwu mijina makaho ne baya gani kuma tallka ne wanda idan muka samu abun da muka ci na yau na gobe sai mun nema, ba don da Allah ya rufa ma na asiri muka samu kudin tallafin nan ba har muka samu wadata ai da sai dai kawai hamdala. Ki duba wanan na jikin hoton hutu da jin dadi sun nuna a jikinsa. Ki dubi ko kayan jikinsa sun fi karfin miliyan ɗaya, kalli takalmin da agogon sa, kalli wayarsa fa kalli motar da ya fito ciki a ƙalla za ta miliyan ashirin. Don Allah ki bar wannan zancen mara tushe."
"Ba yadda za'ayi kama ta yi yawa haka, ki bude idanun ki da kyau , wanda duhu da makantar zuciya ta sa kike yi wa kallon haske. Ni dama tun ranar da na fara ganinsa bai yi kama da mutumin da ya sha wahala ko kuma wata gwagwarmayar rayuwa kamar yadda ya yi ma ki ƙarya ba. Domin hutu da jin dadi abu ne wanda ba sa ɓoyuwa. Duk wanda ya taso cikinsa sai ya nuna kansa. Mijinki ki kiyaye shi ba makaho ba ne, wata manufa yake da ita a Kanki da ya sa ya yi ma ki basaja a matsayin makaho, yana da wata mummunar manufa a Kanki ki zama mai taka tsantsan wajen kula da kanki, don gaskiya hankali na bai kwanta da shi ba maƙaryaci ne mayaudari ne..."
"Ya isa!"
Ta faɗa a tsawace. Wanda sai da Nasreen ta kalle ta da sauri .
"Dan Allah ki tashi ki tafi idan abin da ta kawo ki kenan. Mijina mai gaskiya ne ba zai yi ma ni karya ba."
Ba ta ce komai ba ta bude handbag din ta sanan ta ciro wasu hotuna guda biyu na kati da aka yi. In da yake zaune tare da Yasmeen da wanda yake fitowa daga cikin mota Yasmeen na rike da hannunsa.
Ga waɗan nan ki ajiye a wajen ki za su yi ma ki amfani.
Daga nan ta mike ta nufi bakin kofar fita sanann ta juyo ta kalle ta.
"Na yi ma ki alkawarin sai ba binciko abun da yake ɓoye wa."
Daga nan ta fice daga cikin gidan ranta a ɓace.
_Jalaluddeen_
Bayan ya sauka a airport Taj ya je ya ɗauko shi. Kai tsaya ya bashi umarnin ya kai shi hotel.
Ba su zame ko ina ba sai hotel ɗin da yake zama. Ba ɓata lokaci suka fito daga cikin motar Taj na rike da jakar uban gidan nasa.
Suna shiga ciki ɗakin Taj ya ajiye ma sa jaka, cikin girmamawa ya ce .
"Barka da dawowa sir."
"Barka dai ya aikin da na saka ka komai ba tafiya daidai?"
",komai na tafiya yadda ka tsara. A yanzu haka ta kawo ma ni kaso ma su yawa a cikin dukiyar mahaifin Ma'eesha. A yanzu haka akwai wasu takardun da za ta kawo ma ni a cikin kwana biyu."
Jinjina kai ya yi alamar gamsuwa sannan ya ce.
"Thank you, za ka iya tafiya."
Taj ya fita ya bar masa ɗakin.
Laptop ɗin sa na aiki ɗauka ya fara amfani da shi.
Sai yamma ya shiga wanka ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa, wsyarsa wacce Ma'eesha ta siya masa ya fara kunnawa.
Take kuwa kamar tana jira sai ga kiran Ma'eesha ya shigo cikin wayar.
Amsa kiran ya yi tare da yin sallama. Ta amsa ma sa tare da cewa.
"Ina wuni mijina."
Murmushi mai sauti ya yi sanan ya ce .
"Lafiya lau mar'atussaliha."
"Kana ina ne yanzu?"
"Yanzu motar mu ya sauka ga ni nan zan nemi abun hawa ba iso gida."
"Alhamdulillah na gode wa Allah da ya dawo mun da kai lafiya. Allah ya dawo da kai gida."
"Amin ya Allah."
Daga haka ya katse kiran wayar. Sauri -sauri ya shirya cikin kayan yadinsa ma su arha cikin wanda ya saba sawa.
Sannan ya dauki jakar kayansa da ya ajiye a hotel ɗin ya tafi Abuja da wasu. Sanadar jagoransa ya ɗauka da baƙin glass da aka fi sanain sa da shi. Sannan ya dauki jakar kayan ya ya fito daga cikin ɗakin rike da wayarsa ta wajen Ma'eesha. Takalmin soso ya saka da hularsa taɓa ka ji hadisai ya fito daga hotel ɗin .
Yana fita zuwa titi ya tara mai keke nape, bayan ya sanar da shi in da zai kai shi.
Shiga ya yi mai nape din ya ja keke nape ɗin suka bar wajen.
Har ƙofar gidan ya sauke shi. Ya biya shi kudinsa sannan ya shiga cikin gidan bakinsa dauke da sallama.
Ba ta tsakar gidan don haka ya ya shiga dakin yana dogara sandarsa.
Tsaye ya yi yana kallon ta da mamaki, ganin yadda ya dinga sallama ya ji shiru ba ta amsa ba. Da a da ne yana sallama za ta fito ta tare shi. Abun da ta zuba wa idanu yake kallo, kara zaro idanun ya yi yana kallon hotunan da tasa a gaba tana kallo da maɗaukakin mamaki a kan fuskarta. Ɗago da jajayen idanunta ta yi tana ma sa wani kallo mai wuyar fassara.

Page7️⃣0️⃣
Tsaye ya yi yana kallon ta da mamaki,ganin yadda ya dinga sallama ya ji shiru ba ta amsa ba. Da ada ne yana sallama za ta fito ta tare shi, abun da ta zubawa idanu yake kallo , kara zaro idanun ya yi yana kallon hotunan da ta sa a gaba tana kallo da maɗaukacin mamaki akan fuskarta . Ɗago da jajayen idanunta ta yi tana ma sa wani kallo mai wuyar fassara..
Ganin kallon da take ma sa ne ya sake jefa shi cikin tashin hankali. Sai ya yi ya maza ya dake kasancewar tana yi ma sa kallon makaho ne ba ta san yana gani na shi ha sa ya share ya ɗaga murya yana ƙwala ma ta kira.
"Ma'eesha !" Ma'eesha!" Ina kiks shiga? Ko tana banɗaki ne!"
"Na'am gani nan a gabanka."
"Gaba na kuma kuma?" Lafiya nake ha sallama ba ki amsa ba?"
"Ka yi hakuri ban ji ba ne na tsaya kallon wani abun mamaki ne?"
"Wani abun mamaki?"
"Duba ka gani."
Ta yi maganar tana nuna ma sa hotunan sa da na Yasmeen. In da ya fito daga motarsa Yasmeen ta rike ma sa hannu sa kuma,. Kallo ɗaya ya yi hoton ya cije lips din sa na ƙasa kafin ya ce.
"To ni fa nake makaho fa wani idanun zan gani sai dai ki bani labari."
"Mu bar zancen kawai, sannu da dawowa Mijina."
Ta yi maganar tana karɓar jakar da ke hannunsa. Yayin da ya fara lalube da sandarsa har ya zauna kan tabarma da ke shimfide a ɗakin ya zauna.
Yana lura da yanayin ta duk taa shiga ruɗu, ruwan sanyi da ke cikin jug wanda A'isha ta siyo ma ta ta ajiye a gamda sannan ta zuba a kofi ta mika masa.
"Bisimillah ga ruwa ja sha.*
Ta yi maganar tana kai ma sa ruwa saitin bakinsa ya buɗe ba ki ya sha har cikin ransa ya ji sanyi.
"Na gode." Ya faɗa yayin da yake kau da kansa gefe.
Hakan ya sa ta gane ya ishe sa Kenan. Ajiye kofin ta yi sannan ta ɗauko farantin da ta jera ma sa abici ta ajiye a gabansa.
"Ga abinci wanne zan zuba ma ka?"
Ta kalle shi tana murmushi tana tuna mutum na cikin hoton. Amma kasancewar ta yarda da mijinta ɗari bisa ɗari.
"Na yi ma ka masa da miyar tasushe sanann ga tuwon semovita da miyar kuɓewa. Na san kana son su ko?"
Murmushi ya yi yana sa ma ta albarka yayin da ya buƙaci ta saka ma sa tuwon ya ci.
Har da kunun aya ta ta saka ma sa ƙanƙara ya yi sanyi ta zuba ma sa.
Fitowa waje ya yi ya zauna saboda ɗakin zafinsa yake ji kamar gidan biredi.
A tare suka ci abincin suna ci tana yi ma sa fira. Sai dai ya lura da cewa duk da Nasreen ta kawo ma ta pics din su da Yasmeen bai yi tasiri a wajen Ma:eesha ba, saboda ta yarda da shi sosai kuma ta yarda da kalaman sa.
"Wai na tambaye ka ma na Yaya Khalifan."
"Ina jin ki."
Ya ba ta amsa cike da fargaban tambayar da za ta yi masa.
"Wai dama ana ana samun mutane biyu da kamanni ɗaya, komai na su iri ɗaya kuma ba tagwaye ba ne?"
"Eh ana samu sosai ma kuwa. Ai kowane mutum a duniya akwai irin sa a wani wurin?"
Shiru ta yi kafin ya ce.
"Da ace kana gani da na nuna na ka wani hoton wani mutum mai kama da kai kamar an tsaga kara."
"Allah sarki, sai ya kasance ba na gani ballantana na san meye banbancin mu."
"Wata rana in sha Allah idanun ka zai bude za ka fara gani tamkar yadda kowa ke ganin ka "
"Allah ya nuna ma ni ranar da idanun mijina za su buɗe ya kalle Ni na kalle shi."
"Amin ya Allah"
Ya amsa ma ta da shi sannan ya tashi yana yi ma ta godiya tare da yaba girkin nata.
Zai shiga ɗaki kenan ya ji muryarta tana cewa.
"Kana bukatar wani abu ne?"
"A'a lokacin sallar magrib ya yi zan je na yi sallah."
"Okay Ina zuwa .
Ya tsaya bakin kofar ga shiga ta dauko ma sa sandar jagoransa. Ta zuba ma sa ruwa a buta ya je ya shiga banɗaki.
Bayan ya fito ya yi alwala ya ya nufi masallaci don yin sallar magrib.
_Sidra_
Kuka take yi a bayan motar Gwaggo Laraba na gaban motar yayin da Gwaggo Maimaina ke baya ita da Sidra.
Ba abun da ke tashi a cikin motar sai sautin kukan Sidra. Ba wanda ya kula ta ballantana ya ce ta yi shiru ko ya ba ta hakuri.
Har suka isa gidan ba wanda ya yi magana a cikinsu.
Horn direban ya yi maigadi ya wangale ma sa gate ya shigo da motar ciki ya yi parking.
Gwaggo Laraba ta fito daga gaban motar yayin da Gwaggo Maimaina ke dakawa Sidra tsawa wanda ya sa dole ta fito, don ta san idan ta yi ma ta taurin Kai ba wani abu ba ne a wajen Gwaggo Maimaina sai ta gaura ma ta mari a gaban ma su aikin gida .
Fitowa ta yi ta nufi hanyar shiga ciki fuuu.
"Uban waye kika ajiye da zai ɗaukar ma ki akwatin kayanki?"
Gwaggo Maimaina ta yi maganar ranta a ɓace..
Tura baki Sidra ta yi saboda ba ɗabi'ar ta ba ce ɗaukar kaya idan ta dawo ko ba nauyi sai dai ta saka a shigo ma ta da shi.
Kamar za ta yi kuka ta zo ta ɗauki akwatin kayan ta shiga da shi ciki.
Ko da ta shiga ta same su duka a falo.
Abba, Umma, Ammi, Gwaggo Laraba da Gwaggo Maimaina.
Ta yi sallama yayin da take shiga ciki, gabaɗaya suka amsa ma ta. Kallon fuskar Abba yake sakawa hanjin cikinta kaɗawa.
Ajiye akwatin kayan ta yi tare da zubewa akan gwuiwoyinta.
Tsawon lokacin ba wanda ya yi magana a falon sai shiru. Kafin Abba ya bude baki ya yi magana.
A baya na yanke hukuncin cire ki daga cikin zuri'a ta sakamakon abun da kika yi ma ni na kunyatawa da kuma tozarci. Ko sunan ki na hana a kira mun a cikin gidan nan, na zo kowa ya fita harkar ki. Amma abin takaici ashe kin koma gidan ƙanwarki da zama Nadra. Kuma na san zaman ki a gidan ta ba alkhairi ba ne. Sai kin haddasa ma ta masifa ita da mijinta, tabbas za ki addabi rayuwar su ne. Don haka na yanke hukuncin dawowar ki a cikin gidan nan. Kuma ko ƙofar gida ban yarda ki taka ki fita ba, sanan kuma nan da wata ɗaya zan aurar da ke sadaka ga duk wanda na ci karo da shi idan na tafi ƙauye a cikin satin nan."
Yana gama faɗar haka ta ɗora hannu biyu akai ta rushe da kuka tana fadin ta shiga uku ta lalace, don Allah Abba ya rufa ma ta asiri kada ya ma ta haka, amma bai saurare ta ba haka ya fice daga gidan.
Hararar ta Ammi ta yi tana cewa.
"Wannan hukunci da Abdullahi ya ɗauka ya yi ma ni daidai wallahi. Ya ma yi ma ki sassauci ne albarkacin mahaifiyarki da kullum take cikin damuwa akan ya yafe na ki ki dawo. Darajar ta kika ci hukuncin ya tsaya iya haka, amma hukuncin da ya so ɗauka a kanki ai sai kin tsani kanki da kanki."
Tana gama faɗar haka ta juya zuwa ɗakinta, ƴaƴanta Gwaggo Laraba da Gwaggo Maimuna suka mara ma ta bayan.
Aka bar Umma tsaye Sidra na durƙushe tana kuka tana roƙon Umma da ta ba Abba hakuri ya janye hukuncin da ya yi niyyar ɗauka kanta .
Umma ta kasa cewa komai ta yi tsaye kamar wacce aka dasa, amma da zaran ka kalli cikin idanun ta za ka hango tsantsar tashin hankali da take ciki.
_Daddy_
Yana zaune a bedroom ɗin sa ya saka hoton Mummy da Ma'eesha yana kallo yana zubar da hawaye.
"Kiyi haƙuri Hajiya na kasa rike amanar da Allah ya ba ni. Ƴa ɗaya tilo da Allah ya ba ni ina ji ina gani aka waufantar da rayuwar ta amma na kasa cewa komai. Yarinyar da muka haife ta mika rene ta cike da so da ƙauna, muka yi burin inganta rayuwar ta da bata farin ciki mai ɗorewa. Sai ga shi lokaci daya abubuwa suka dagule. Na san cewa kafin rasuwar ki ban yi ma ki adalci ba, na tauye ma ki hakkin ki ga ƴar da kika haifa ina ji ina gani aka mayar da rayuwar ta zuwa matakan rugujewa. Ban san a wani halin take ciki ba. Wasu abubuwan duk ba na iya tuna su tun bayar zuwan Mamy da yaranta gidan nan. Ki yafe ma ni don Allah, Allah ya yi ma ki rahama ya sa aljanna Firdausi ce makoma a gare ki. Ma'ee..."
"Alhaji!"
Ya ji Mamy ta kira sunan sa a tsawace. Da sauri ya juya yana goge hawaye.
Ƙarasowa ta yi cikin isa da taƙama ta ce.
"Me kake yi da wanan hoton, kuma kukan me kake yi ne? Wani sabon mutuwa aka yi ma ka ne, ko Ma'eesha ce ta muyiy. Da sauri ya girgiza kai ya na cewa .
"Ma'eesha na nan da ranta ba ta mutu ba in sha Allah."
Taɓe baki ta yi tana cewa.
"Ko ta mutu wa ya sa ni ko yunwa da wahala ta gama da ita, don wanan makahon mijinta ba wata sana'a da zai iya ba, sai sai idan bara za su dinga zuwa tare tana yi ma sa jagora. Ta yi maganar tana dariyar mugunta.
Wani tsabar Mamy ya ji a zuciyarsa amma ba zai iya yi ma ta komai ba.
"Alhaji."
Ta kara sunan sa tana ɗauke hoton Ma'eesha da mahaifiyarta akan cinyarsa. Ajiye su gefe ta yi tana tabe baki.
"Alhaji na ce ba wasu kuɗade ko dukiyar da suka rage a hannunka. Ka san yanzu girma ya kama ka ya kamata a ce kana hutawa Jamil ne yake kula da komai naka. Ko ba haka ba?"
"Eh haka ne "
Haka kawai ya tsinci kansa da bin umarnin ta. Duk abun da ta ce baya iya yi ma ta gardama.
"Sauran wadanda ke hannunka ina so ka kawo su na bayar a kula da su ka huta ko saboda bawan jinin ka."
Kai ya jinjina alamar gamsuwa da maganar ta.
"Za ka bayar ?"
Kai ya daga kafin ya ce .
"Eh zan kawo."
Murmushi ta yi tana cewa.
"Bari na kawo ma ka coffee din ka ko?"
Ta faɗa tana murmushi ta nufi hanyar fita tana cewa.
"Ina zuwa ka jira ni yanzu."
Ta fita tana murmushin cin nasara a ranta. Duk da ita kamata yanzu ta rasa meke ma ta daɗi a duniyar nan, ko barci cikin natsuwa ba ta iya wa.
_Sidra_
Umma don Allah kada ki bari Abba ya yi ma ni auren dole ba zan iya zama ba Wallahi. Umma kauye fa ya ce zai aurar da ni, Umma ta ya zan iya rayuwar ƙauye ko na wuni ɗaya ba zan iya ba duk kyawu na da karatuna har matakin digiri a ce wai za'a kai ni ƙauye a bayar da aurena sadaka ga duk wanda aka ci karo da shi. !"
Tana cikin wanan halin ta zube ƙasa sumammiya.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce✍️
*SADAUKARWA GA*
AMMEY LAYLERH

Page7️⃣1️⃣
Umma don Allah kada ki bari Abba ya aura da ni auren dole ba zan iya zama ba wallahi. Umma ƙauye fa ya ce sai aurar da ni, Umma ta ya zan iya rayuwar ƙauye, ko na wuni daya ba zan iya ba. Duk kyawu na da karatuna har matakin digiri a ce wai za'a kai ni ƙauye a bayar da aurena sadaka ga duk wanda aka ci karo da shi!"

Cikin tashin hankali Umma ta yi ihu tana kiran sunan ta, wanda hakan ya janyo hankulan su Ammi da yaranta suka shigo falon da hanzari.
Ganin abun da ke faruwa ya sa suka fahimci dalilin ihun Umma. Gwaggo Laraba ce ta ɗauko robar ruwa a fridge ta yayyafawa Sidra. Wanda nan take ta ja ajiyar zuciya mai karfi. Sannan ta Fashe da matsanancin kuka.
"Kukan me kike yi ai baki ga komai ba akan abun da kika aikata ."
"Cewar Gwaggo Maimaina tana mata wani banzan kallo.
Umma dai ba ta ce komai ba ta kama hannunta ta yi suka nufi bedroom ɗin ta.
Suna dab da shiga ciki suka tsaya cak ba wanda ya ji ƙara ko fa taku daya.
"Ba na buƙatar ta a tare da mu. Domin ganinta na ba na son ba yawaita kallon ta . Ɗin haka ta tattara kayanta ta bar part ɗin nan, ta koma ɓangaren baƙi da zama."
Cikin takaici Umma ta ce .
"Haba Alhaji ai hannunka baya ruɓewa ka yanke ka yar.
"Ni kam tuni zan yanke hannuna na yar idan dai ya ruɓe, don idan ban yanke na yar ba tuni zai fara cin sassan jikina!"
Yana gama faɗar haka ya juya ya nufi ɗakinsa.
Umma ta saki Sidra ta bi bayan Abba a ɗakinsa. Yana tsaye ya juya wa ƙofar baya.
Za ta yi magana ta ji muryarsa ya ce.
"Dama ba abun da kike so kenan kullum kike roƙon na dawo da ita gida ba, to ta dawo me ya rage kuma?"
Za ta yi magana ta ji ya ce .
"Bissalam."
Ta fita daga ɗakin ba tare da ta sake cewa komai ba, don ta fi kowa sanin halin mijin nata. Don haka ta bashi lokaci kafin ya huce don ta ga ɓacin ran da ke kan fuskarsa.
_Makaho_
Wayarsa ta aiki ya fito da ita daga cikin jakarsa, lokacin Ma'eesha ta tafi gidan Mallam Liman kai wa Baba abinci.
Waya yake yi da ogan sannan wajen aiki, nan take sanar wa headquarter din su yana kokarin kama daya daga cikin yaran Alhaji Daula. Fatan nasara ya yi ma sa daidai lokacin da ya ji sallamar Ma'eesha tana shigowa gidan . Da sauri ya katse kiran wayar ya kashe wayar ya sa a aljihun wandonsa. Sannan ya amsa sallamar da Ma'eesha ke yi.
"Har kin dawo?"
"Eh, ina kai ma ta na dawo saboda na bar mijina shi kaɗai. Kuna burina ko wane lokaci na kasance a kusa da kai, har ga Allah ni kan ji dadi idan na ganni a kusa da kai, a duk lokacin da ka fita daga cikin gidan nan sai na ji gidan ba daɗi, gidan ya yi ma ni duhu har sai ka dawo sanan zan ga haske da annuri a cikin gidan nan, kai ne duniyata idan na rasa ka ƙiyama ta ta tsaya."
Ta yi maganar cikin rauni da damuwa.
Ba abun da take tunawa kamar rayuwar da ta yi a baya tare da iyayen ta da suka rene ta cikin so da ƙauna. Ta kuma tuna yadda Mamy ta shigo rayuwar su ta ruguza ma su farin ciki.
Hawaye ne kawai suke rige-rigen saukowa daga idanunta .
Shiru Makahon ya yi yana karantar yanayin ta da damuwa da take ciki.
Kafin ya mike tsaye da nufin fita sai ya tsaya ya kalle ta cikin wani irin murya ya ce.
"Hakurin da kike ba a banza ba ne, ko wanne hawaye da kike zubarwa yana da daraja a wajen Ubangiji. Kowane numfashin da kike shakar juriya da jurewa, yana karuwa da lada. Wata rana za ki dawo ki kalli baya ki ga irin wahalhalun da kika sha, sai ki yi murmushi cikin hawaye kina cewa.
"Lallai Allah bai taba barina ba."
"Bar wa lokaci, domin lokaci magani ne. Kullum ki kasance da kyakkyawan zato ga Allah. Akwai tarin farin ciki da aka adana miki, sai dai yana buƙatar juriya da hakuri.
Kada ki daina addu’a. Kada ki daina fatan alheri. Kada ki daina sadaukarwa. Hakkin ki ne ki ji daɗi, kuma UbangijinKi yana ganinki, zai baki alheri fiye da duk abinda kike zato. Ki ci gaba da hakuri, domin a ƙarshen dare haske yana zuwa. Hakurin ki zai zama hasken gobe in shaa Allahu."
Kalaman sa sun yi ma ta daɗi sosai ba kadan ba, wanda har ba ta san lokacin da ta rungume shi ba tana ajiyer zuciya.
Wanann ne karo na farko a rayuwarsa da mace ta rungume shi bai taba ta da jikinsa ba. Domin Ita kanta Ma'eesha da ba don halin damuwar ba da za ta tuna da zaran ta rungume shi ko ta haɗa jiki da shi take zai raba ta da jikinsa. Amma wanan karon ya kasa raba ta da jikinsa, sai ma rarrashinta yake yi ta hanyar bubbuga bayanta alamar rarrashi .
Ita kanta ta san cewa wanan me karo na farko da ya bar ta har ta rabi jikinsa.
Tsawon mintuna goma suna a haka kafin ya zame ta daga jikinsa ya ha hannunta har kan katifa ya ce ta kwanta.
Ba musu ta kwanta kamar yadda ya buƙata sannan ya ce ta huta zai fita ya dawo.
Jinjina kai kawai ta yi ba tare da ta yi magana ba har ya fita tana kallonsa.
Fitar sa ba jimawa sai ga Nasreen ta yi sallama ta shigo gidan .
Tashi daga kwancen da take ta yi kafin ta ce da Nasreen ta shigo.
Shiga Nasreen ta yi tana cewa .
"Ina Makahon mijin naki yake?"
"
Banza ta yi da ita kamar ba za ta ce komai ba kafin ta ce.
"Ba sunan sa Makaho ba sunan sa Khalifa ki san me za ki faɗa game da mijina a gabana."
"Allah ko me miji, na ga ai makaho ne meye aibun da na faɗa ."
Tashi ki fita kafin na yi ma ki abun da ran kowa zai ɓaci."
"Haba ƙawata ki yi haquri don Allah na daina."
Ma'eesha ba ta ce ma ta komai ba ta share ta.
"Na zo ne dama ina neman shawarar ki, kin san ba na da abokiyar shawara sai ke."
"Ina jin ki."
"
Ta faɗa tana kallon ta ba yabo ba fallasa.
"Wannan saurayina da nake ba ki labari ya matsa akan zai fito mu yi aure, ni kuma ban gama cika burina ba ballantana na yi aure yanzu ke ma kin sani, kuma ina tsoron na rasa shi yanzu ya zan yi? Don har yanzu ban kai matakin da nake burin kai wa ba kafin na yi aure .
Murmushi Ma'eesha ta yi kafin ta ce
"Ko da kina da burin zama hamshaƙiyar ƴar kasuwa ko babbar ma'aikaciya, idan kin samu mijin aure kina da ƙananan sheka ki yi aurenki. Aure shi ne babban security ga mace, musamman wadda take da burika na gina kai. Idan kika yi aure, rayuwarki ta ɗauki saiti, za ki iya kaiwa duk matakin da kike so cikin nufin Allah. Mun ga dubban manyan mata, waɗanda duka sai bayan aure suka samu ɗaukaka. Don haka aure baya daƙile ɗaukaka, ko kashe mafarkai. Amma idan kika bar batun aure, kika mayar da hankali wajen gina kanki, to fa auren zai miki wahala. Ba wai ina nufin wahalar samun miji ba, duk da ita ma akwai ta sosai gare su. Babbar matsalar ita ce idan mace ta samu ɗaukaka kafin aure, aure yana mata wahala. Domin ta saba da rayuwar jin daɗi da sakewa, wataƙila ma ta kai matsayin da take umarni da hani, zai wahala ta sunkuyar da kai ta yi wa miji ɗa'a. Sa'an nan fa shi aure dole sai da ɗa'a, idan aka rasa ta, ko bai rushe ba, ba zai daɗi ba ita kanta ba za ta ji daɗinsa ba. Amma idan ta saba da biyayyar aure tun da ƙuruciya, zai wahala ɗaukaka ta canja ta. Sai dai wani dalilin daban.
Idan na saurari ƙorafin manyan mata waɗanda ba su aure ba, ko ba su yi aure da wuri ba kan zamantakewar aure, ina gane suna da matsala, amma su kansu ba su fahimci mecece matsala tasu ba.
Nisawa ta yi kafin ta cigaba da cewa.
"Na taɓa misalta rayuwar aure da shiga aikin soja: Aikin soja, da ƙuruciya ake shiga, kamar tsakanin 18-25, a wannan shekarun mutum zai iya jure wahalar da ke cikinsa, idan ya saba to shi kenan, zai iya tsufa a ciki. Amma wanda ya girma, ya kai kamar 35-40, ba zai iya ba.. Ba wai rashin kuzari ba, tunaninsa ne ya girma, ba zai iya jurewa ba. To kamar haka aure yake. Allah ya datar da mu."
"Amin ya Allah."
Nasreen ta amsa cikin sanyin jiki tana auna maganar ƙawarta a mizanin hankali. Tabbas maganar Ma'eesha abun dubawa ne, sai dai tana bukatar yin nazari akai. Don haka ta yi ma ta sallama ba tare da ta sake cewa komai ba ta bar gidan . Driving take yi hankalin ta na kan tunanin kalaman Ma'eesha.
_Makaho_
Kamar yadda ya tsara yau ne yake shirin kama ɗaya daga cikin yaran Daula. Don haka bayan ya yi wani bincike akan su ya san shige da ficen yaran da da komai ne ya sa bayan ta fito daga gida ya tsaya yana jiran fitowar abun harin sa.
Dare ya rufe gari ya yi duhu sai hasken fitilu da suke haska titi da rauni.
Makaho na tsaye bayan wata mota idanunsa na kan mutumin da ke tafiya cikin sauri, wato mutumin Daula daya daga cikin yaran sa.
Mutumin ya bi wata karamar hanya, Makaho ya bi shi a hankali ƙafarsa ba sa amo don na wanda ke jin sautin ƙafararsa.
Kwatsam sai mutunin nan ya tsaya cak.
"Na san kana bi na a baya. *Jalaluddeen Kabir arziki *senior intelligence officer*"
Zuciyar makaho ta buga da ƙarfi. Kafin ya ankara ya ji ƙarar mota ta bayansa an kewaye shi.
Wani ya fito daga inuwa .
"Ka yi kuskure Mallam mai gyaran takalmi....

Page7️⃣2️⃣
Zuciyar Makaho ta buga da ƙarfi, kafin ya ankara ya ji ƙarar mota a bayansa an kewaye shi.
Wani ya fito daga daga inuwa.
"Ka yi kuskure Mallam mai gyaran takalmi.
A nan Jalaluddeen ya gane shirin sa yana shirin tonuwa.
"A baya mun saka yaran mu sun je sun ɗaukoka a yayin da kake komawa gida bayan ka tashi wajan gyaran takamin ka n basaja. Sai dai cikin rashin sa'a jami'an ku na DSS suka bi yaran mu suka ceci rayuwarka. Amma duk da haka kake sake saka kanka a hatsari ko? To bari ka ji Alhaji Alhaji Daula ba zai kamu ma ka ba, hana da ɗaurin gidi har a wajen na sama da kai a ƙasar nan. Ya km
Take sai duhu ya mamaye wajen na wasu sakanni wanda a daidai wannan lokacin Jalaluddeen ya shammmace su, tsalle ɗaya ya yi ya haura katanga tare da faɗawa ta baya.
Haske ne ya dawo wanda a lokacin suka ga babu Jalaluddeen a tsakiyar su.
Cike da mamaki suke ta waige-waige suna neman sa amma babu ko mai kama da shi.
"Ina ya shiga ne?"
Suka rabu suna neman sa, gabaɗaya suka zagaye yankin amma ba su gan shi ba.
Shi kuma yana barin wajen hanyar gida ya koma, yana tunanin ya hakan ta faru. Alama ya nuna cewa a kwai mai yi ma sa zagon ƙasa a cikin jami'an su na DSS. Domin su kaɗai ya sanar da su inda zai je, to ya aka yi yaran Daula suka san da zuwan sa, dole akwai munafiki a cikin su. Amma ya gode Allah da ya tsira da rayuwar sa. Amma tabbas zai gano waye ya shirya ma sa wannan abun.
_Fahad_
Wayar Nadra ya kira don ya ji muryarta, don tunanin ta kawai yake yi, don haka ya bar abun da yake yi ya nufi hanyar gida .
Horn ya yi a ƙofar gidan nasa, yayin da maigadi ya fito ya wangale ma sa gate ɗin gidan .
Bayan ya yi parking motar ne ya fito daga cikin motar yayin da maigadi ya ƙaraso wajen
uban gidan nasa ya gaishe shi.
Ya amsa ma sa yana nufar cikin gidan.
Tura kofar ya yi ya yi ya shiga ciki bakinsa dauke da sallama .
Ba ta falon ƙasa sai ya haura sama. A tunanisa zai ga ta jera abinci a dinning table a daidai wannan lokaci. Amma sai ya ga ba ta jera komai b, kuma ba alamar ta yi girki ma.
Bedroom din ta ya nufa kai tsaye, can ya hango ta ƙasan gado ta kudundune kanta a saman gadon.
Da sauri ya karasa sanan gadon ya haura akai, sannan ya janyo ta jikinsa sai ajiyar zuciya take saukewa tana barci.
"Subhanallah!"
Ya faɗa yana taɓa jikinta.
,"Nadfah lafiya me ke damun ki?"
Kuka ta saka ma sa wanda ya kara tayar ma sa da hankali. Rungume ta yi yana rarrashinta .
E ya same ki?"
",Kai ne ka kira Abba ka faɗa ma sa Aunty Sidra na ganin nan?"
Shiru yanayi yana kallon ta wato akan Sidra ta tafi shi ne take kuka.
"Ba ni na faɗa ma ta ba, dai dai maybe Aunty Rahama ce, din ta kira nu da safe tana ta faɗa akan tashin dacewar hakan . Kuma na fahimci gaskiya take faɗa gara ta tafi za mu fi sakewa a cikin gidanmu.
"Ta tafi tana jin haushi na sosai ta tafi ina son na je na fahimtar da ita."
Da sauri ya kalle ta kafin ya ce .
"Yaushe za ki je?"
"Yau nake so na na je saboda ba na son ta kwana da ni a zuciyarta."
Wani kallo irin na baki san net kike yi ba ya yi ma ta, kafin ya ce .
"Zan ya tunani akai?⁷
Sake shigewa jikinsa ta yi tana roƙonsa, wanda wanda hakan ya haifar ma sa da kasala sosai a jikinsa.
Da ƙyar ya yi magana ya ce..
"Too...too....too shi...shi...kanan zan kai ki."
Ɗago da kanta dake sanan ƙirjinsa tana kallonsa jin yadda yake magana kamar wani ɗan koyon magana. Idanunsa ta ga sun kaɗa sun canza launi.
"Ba ka da lafiya ne?"
"Kai kawai ya jinjina ma ta alamar eh."
Saurin tashi za ta yi daga jikinsa amma sai ya rike ta yana sake matse ta da jikinsa.
"Akwai maganin da za ka sha?"
Kai ya jinjina ma ta alamar eh.
"Ina maganin yake na ɗauko ma ka?"
Ya nuna ta alamar iya de maganin sa.
"Ni kuma?"
Ta faɗa yana nuna kanta da hannunta .
"Ta ya zan zama magani? Yaya Fahad wasa kake yi ka tashi mu tafi magrib na gabatowa sai mu yi sallah a can."
"In dai ban samu maganin ciwo na ba ko ɗakin nan ba zan iya fita ba ballanta na kai ki wajan wata kuma."
"To ya kake so ayi?"
"Ke ce maganin ciwo na, jikinki maganin yake ?"
"
Kallonsa ta yi ta gane jarabar sa ne ya motsa saboda ta rungume shi shi kenan ya shiga wanan halin.
"To ka ga ai magrib ya gabato kuma kai idan ka fara ba ka gamawa da wuri za mu...."
Haɗa bakinsa da nata ya yi yana aika ma ta saƙon sa kai wuyar karantawa. Ba ta da wani zaɓin da ya wuce ta bashi hadin kai."
Don haka ko da ya cire manta kayan jikinta ba ta yi yunkurin ma sa gardama ba, ta bar shi ya yi bidirinsa yana sarrafa jikinta yadda ransa yake so.
Kusan mintuna ashirin ya yi yana wasa da jikinta, don ya fara rikice ma ta, kafin ya dauki hanyar shigarta yana karanto addu'ar saduwa da iyali.
Duk sanda ya shige ta sai ya ji ta kamar sabuwa take sake zama ma sa.
Har aka kira sallar magrib bai ma sani ba don yana can ya lula wata duniyar da ya lula, ita ce ma take sanar da shi lokacin sallah ya wuce fa ana sallar magrib amma ina bai ma san tana faɗa ba ya fice daga hayyacinsa.
Sai da aka kira sallar isha'i sannan ya samu natsuwa ya mirgina gefe yana mayar da numfashi. Ba ta tsaya ɓata lokaci ba ta janyo rigarta ta saka ta shiga bathroom. Cikin sauri ta tsarkake jikinta sannan ta fito ɗaure da babban towel a jikinta tana takaicin yadda sallar magrib ya wuce ba ta yi shi akan lokaci ba.
Ko da ta fito ba ta gan shi a dakin ba, don haka ta shirya cikin rigar abaya ta saka hijabi ta fara gabatar da sallah.
Shi ma a nasa bangaren ɗakinsa ya wuce ya tsarkake jikinsa ya yi wanka, sannan ya ɗauro alwala ya fito.
Kasancewar ko masallaci an isar da sallar isha'i ya sa ya yi sallarsa a ɗakinsa bai fita ba.
Bayan ya idar ne ya ya ɗauki key din motarsa da niyyar zuwa ya yi ma su take away, a bakin ƙofar ya hadu da ita tana kokarin shigowa ɗakinsa.
Sanye da hijabi da wayarta a hannunta. Sunkuyar da kanta ƙasa ta yi ba tare da ta ce ma sa komai .
Hannunsa daya ya sa ya ɗago da haɓar fuskarta suka hada idanu.
Kashe ma ta ido ɗaya ya yi ta dauke idanun ta da sauri cikin jin kunya.
"Wai wane kunya kuma ya rage a tsakanin mu ne iya zumata?"
"Ni dai mu tafi."
"Mu tafi ina?"
Kwaɓe fuska ta yi kamar za ta yi kuka ganin yana son ya raina ma ta hankali.
"Kai fa ka ce za ka kai ni idan..."
Sai ya kasa karasa maganar tana kallon kasa.
"Na ce zan kai ki idan aka yi me?"
"Na manta ɗan tuna mun abun da ya faru, yaushe na ce za. Kai ki kuma idan aka yi me? Ba abun da na tuna mu je mu yi take away mu dawo gida mu huta.
Kuka ta saka ma sa za ta koma ɗakinta, ya yi saurin riko hannunta yana cewa.
"Am sorry na tuna abun da ya faru mu je na kai ki."
Ya yi maganar yana dariya, ita ma dariyar ta yi duk da hawayen da ke idanunta.
"Ki daina ɓata ranki domin ba na son ɓacin ranki ballanta zubar hawayenki sarauniya ta."
"Ba na son ki yi wahala bari na ɗauke ki."
Kafin ta yi magana ya dauke ta ya fara tafiya da ita, a hankali yake taka matattakalar benen har ya sauka zuwa falon ƙasa.
Suna fita a jarabar gidan ta fara kokarin zamewa tana so ya ajiye ta sakamakon wasu ma'aikatan gidan da suke kallon su . Bai na ta damar ba har sai da ya kai parking space ya ce wa direbansa ya zo ya bude ma su bayan motar .
Ɓoye fuskarta ta yi a ƙirjinsa saboda kunya. Har direban ya ƙaraso wajen da sauri ya bude bayan motar.
Ya saka ta ciki shi ma ya shiga ya zauna gefenta. Direban ya shiga yi yi wa motar key suka bar gidan.
_Makaho_
Bayan ya bar su mutanen Daula ya bar layin daidai yana kokarin fita daga wata bayan ya ji Harbin bindiga a damtsen hannunsa.
"Ash!"
Ya faɗa bayan Harbin ya shige shi. Sake yin harbi aka yi a karo na biyu, cikin zafin nama ya yi yi ƙasa ya tsallake Harbin.
A guje ya bar wajen yana gudu ana bin sa da harbi har ya samu ya tserewa mai Harbin nasa.
Yana gudu yana rike da hannunsa dake fitar da jini.
Har ya isa gida inda ya tura ƙofar a hankali ya shiga ciki. Ɗaki ya shiga in da ya tarar da Ma'eesha na barci kamar yadda ta saba.
Wani ƙaramin akwati ya ciro daga cikin jakar kayansa. Fita ya yi ya yana rike da hannuna ya ajiye akwatin a banɗaki. Sanann ya dawo ya ɗauki bokiti dake cike da ruwa ya kai banɗaki. Wani dogon wando ya ɗauka a cikin kayansa da niyyar idan ya yi wanka su zai saka.
Karamin akwatin nan ya buɗe ya ciro wani abu kamar scissors ya sa a wajen Harbin, ya ciro bullet din bindigar, sai da ya yi ƴar ƙara na azaba wajan cire bullet din bindigar.
Ya yi wanke wajen ya sa magani jinin ya tsaya ya rufe wajan sanan ya yi wanka.
Yana fitowa ya ga Ma'eesha a tsaye a tsakar gidan tana kallonsa da mamaki.
Pretending ya yi a matsayin sa na makaho wanda baya gani. Da lalube ya ajiye bokitim ya saka rigar sa ciki ya wuce ta a matsayin bai san da mutum a wajen ba.
"Mijina lafiya kuwa?"
Ta yi maganar tana kallon gefe ɗaya, saboda kallo ɗaya ta yi ma sa ta kawar da kanta gefe saboda ba shi da riga sai dogon wando sannan ga murɗaɗɗen surar jikinsa irin na jaruman maza bayyane a jikinsa wanda ke firgita ta.
"Ma'eesha kece kika fito a cikin daren nan?"
"Eh na farka ban gan ka ba ne ya sa na fito na duba ka."
"Ki je ki kwanta wanka na fito yi."
"Okay, Amma wankan a daren nan?"
"Eh zafi nake ji ne na kasa barci. Ke ma zafin kike ji ne?"
"A'a mafarki na yi akan ka wanda na ji tsoro na farka."
"Ina lafiya ba abun da ya same ni je ki kwanta ki huta ina shigowa yanzu."
Ya yi maganar yana dibar ruwa ya zuba a kayan da ya cire, zai wanke.
"Ki shiga ciki ma na."
Ba musu ta bi umarnin sa ta shiga ciki.
Sai da ya wanke kayansa ya shanya sanan ya shiga cikin dakin .
Tana zaune a kan katifar tana kallon ya shigo ta sunkuyar da kai kasa. Sai dai ta lura yanayin da yake ciki ya sauya.
Riga ya saka ya fita ya ɗauro alwala ya zo ya fara sallar nafila kafin a yi sallar asuba.
Sai da aka kira sallar asuba sanan ya tashi ya nufi masallaci.
Ana idar da sallah ya fito daga masallaci ya dauki wsyarsa a aljihu ya kira lambar Taj.
Bugu biyu ya ɗaga tare da gaida shi. Umarnin ya zo ya ɗauke shi ya ba shi. Daga nan ya fara tafiya da sandarsata jagora . A bayan layin suka haɗu ya dauke shi zuwa wani gidan.
Bayan ya yi horn maigadi ya wangale ma su gate Taj ya ja motar zuwa ciki .
Yana parking ya fito da sauri ya bude wa ubangidansa bayan motar ya fito ba tare da sanar jagoransa ba.
Kai tsaye wani karamin ɗaki ya shiga in da aka manna allo da wasu rubuce-rubuce a kai .
Kallon Taj ya yi kafin ya ce .
"Akwai munafuki a cikin mutane mu, jiya an na sanar da cewa zan bibiyu mutanen Daula don na san shirin su, bayan na bibiye su sai suka shirya ma farmaka ta. Abun tambaya waye ya sanar da su shirina.? Sanan bayan na kuɓuta daga hannunsu a hanya an kai ma ni hari har an samu nasarar harbina kuma ba mutanen Daula ba ne cikin jam'an mu ne waye da wanan aikin?"

Page7️⃣3️⃣
Akwai munafukai a cikin mutanen mu, jiya na sanar da cewa zan bibiyu mutanen Daula don na san shirin su, bayan na bibiye su suka shirya farmaka ta. Abun tambaya waye ya sanar da su shirina? Sannan bayan na kuɓuta daga hannunsu a an kai ma ni hari, sanann an samu nasarar harbina kuma ba mutanen Daula ba ne na waye da wannan aikin?"
Yaja hoton kan mutum ya zagaye shi sannan ya saka alamar tambaya a wajen kan.
"Dole na gano ko waye domin farautar rayuwa ta ake yi, kuma ba wanan ne karo na farko da aka farmake ni ba. Sai dai na baya na yi tunanin mutanen Daula ne. Domin na dawo kenan daga wajan gyaran takalmi da yammaci, kan hanyata ta komawa gida ne suka farmake ni suka saka ni a mota. Sai dai cikin ikon Allah lokacin jami'ana da zan ba wa wasu bayanai suna kusa sun hange ni suna tunanin yadda za su tinkare ni saboda ba su iso akan lokaci ba har na gaji da zaman jiran su na kama hanyar gida. Sai Allah ya sa akan idanun jami'an mu abun ya faru suka bi wadan can mutanen har suka kuɓutar da ni bisa umarnin oga. Sannan na gano Harbin da aka yi ma ni ba daga Daula ba ne bullet din bindigar ya fito ne daga weapon serial number DSS stock ."
Jalaluddeen (Makaho) ya juya ga gefe a wani allon yana nazari yayin da Taj ya tsaya yana kallon sa na ƴan saknni kafin ya juya ya kalli allon dake manne a bangon ɗakin, alamar bayanai da hotuna ne ke yawo akai. Kamar ana sake gina abun da ya faru ne a baya.
Shiru ya mamaye ɗakin.
Makaho ya matse sandarsa a hannunsa , zuciyarsa na bugawa a hankali amma cikin karfi. Ya ji wani abu a cikin kansa yana faɗa ma sa cewa. Abun nan bai tsaya ga kwanton ɓauna kawai ba."
"Ka ce an sanar da su?"
Taj ya maimaita tambayar Jalaluddeen a hankali kamar yana auna kalmomin.
Jalaluddeen ya haura tsayuwar sa.
"Eh duk abun da na tura ma su sun san shi kafin lokaci."
Taj ya yi shiru na dan lokaci sanan ya ja numfashi mai nauyi.
"Wannan ba al'ada ba ce."
Jalaluddeen ya matso kusa da teburin da ke tsakiyar ɗakin. Yana jin kowane motsin iska.
"Na riga na fara zargin akwai mutum a cikin tsarin mu."
Jalaluddeen ya faɗa cikin murya mai sanyi.
"Amma yanzu na fahimci ba zargi ba ne gaskiya ne."
Taj bai amsa nan take ba.
Sai ya ɗan juyo da kansa amma idanunsa bai kalli Jalaluddeen kai tsaye ba ya ce .
"Waye kake zargi?"
Tambayar ta yi nauyi fiye da yadda aka furta ta.
"Duk wanda ya san motsi na "
Wannan amsa ta Jalaluddeen ta sa dakin ya kara yin shuru. A waje iska ke kaɗawa tana bugun window dake ɗakin kamar tana kokarin fadar wani sirri. Daidaita lokacin wayar Taj ta yi ƙara, sai ya duba.
Sakon ya fito ne daga wani lamba da ba'ayi seve ba.
*Ya fara tambaya sosai, ku hanzarta kafin ta gano komai*
Taj ya kalli sakon sannan ya rufe wayar da sauri.
Jalaluddeen ya ɗan ɗago kansa.
"Me ya faru?"
Ya tambayi Taj. Shiru ne ya biyo baya kafin Taj ya ce.
"Babu komai."
Amma muryarsa ba ta yi daidai da kalmomin sa ba.
Jalaluddeen ya ɗan matso gaba zuciyarsa ta fara nauyi.
"Ka san wani abu?"
Jalaluddeen ya tambaya a hankali.
"
Taj ya ɗago kai da sauri.
"Me kake nufi?"
Gajeren murmushi Jalaluddeen ya yi, irin murmushin da ba na daɗi ba.
"Na koyi abu daya a wanan aikin."
Sai kuma ya yi shiru bai sake magana ba. Shiru ne ya biyo baya kafin Jalaluddeen ya ce .
"Za ka iya tafiya gobe za ku dake binciken."
Taj ya juya ya fara tafiya har ya kai bakin kofa ya ji Muryar Jalaluddeen na cewa.
",Duk wanda ya fi sani na a nan shi zan fara zargi."
Taj ya dakata da tafiyar da yake yi, kuma bai juyo ba.
"Ka fara makara."
Daga haka ya fita kofar ga rufe .
Taj ya tsaya shi kadai a dakin yana tunanin yadda abubuwa suka sauya ma sa.
A hankali ya ce.
"Ba Taj ba ne... To waye?"
Jalaluddeen yana tsaye a tsakiyar ɗakin sandarsa a hannunsa, tana rawa kadan . Kalmomin Taj ke yi masa yawo a cikin kansa kamar yadda iska mara nutsuwa.
"Ka fara makara."
Wanann kalmar tafi yi ma sa nauyi.
Ya ja wani dogon numfashi ya mayar da hankali sa kan sautin da ke kewaye da shi. Agogo na tick tick a bango iska na shigowa ta window, da nisan motoci a waje.
Sai ya ji wani ƙaramin sauti, sai ya ji wani abu kamar an motsa takarda a hankali. Jalaluddeen (Makaho) ya tsaya cak baya ganin komai amma kununuwan sa sun fi komai aiki. A hankali ya juya kansa zuwa teburin da Taj ya bar shi.
Babu kowa a wurin .
Amma jin sa yana ce ma sa, akwai wani abu da bai kamata ya kasance a wurin ba. Ya taka a hankali yana bin tebur ɗin da hannu.
Sai ya taɓa wa wani abu, Fili ne wani karamin na'ura mai sanyi a saman tebur.
Jalaluddeen ya tsaya .
"Wace irin waya ce wanan ,?" Ya yi tambayar duk da babu mai ba shi amsa. Ya sa hannu ya ɗauka .
"
Na'urar ba ta da kara amma ta ɗan yi zafi kaɗan alamar ta daɗe tana aiki.
Nan take ya fahimci an saka ma sa na'urar saurare a in da yake bincike .
Zuciyarsa ta buga da ƙarfi .
"Wato hakan na nufin duk abun da nake yi ana saurarena."
Ya jefar da na'urar ƙasa ya taka ta da ƙarfi wanda sai da na'urar ta fashe.
Daga wajen ya ji karar tashin Mota ta bar wajen a guje. Jalaluddeen ya juya da sauri amma ba su nan.
"Sun riga sun ji ni."
A lokaci guda wsyarsa ta yi ƙara, wanan karon ba Taj ba ne, wace lamba ce da bai san me ita ba. Ya ɗaga kiran wayar ba tare da ya yi magana ba.
Jin shiru ya sa shi nufar hanyar fita don ya fice .
_Fahad_
Kofar gidan su Nadra horn ya yi maigadi ya wangale ma su gate suka shiga ciki.
Parking space ya yi parking motar sannan ya fito, Fitowar sa ya yi daidai da bude labulen window da Sidra ta yi daga nan ta hangi Fahad yana buɗewa Nadra karfin motar ta fito. Sai da numfashinbta ya yi kamar zai zau dauke.
Ganin wani kallo mai cike da shauƙin so da Fahad ke aika mata, ita ma sai murmushi take yi ma sa.
Cikin takaici ta dunkule hannu ta daki bangon ɗakin wanda ya sa ta saki ƙara saboda zafin da ta ji.
"Wallahi ba zan bari ku yi farin ciki ba sai na farraƙa ku. Ba yadda za'ayi ku yi farin ciki ku bar ni cikin bakin ciki wallahi ko sama da ƙasa za ta hade ba sai na raba ku da juna kuma alkawari na ne wannan."
Tana faɗar haka ya saki labule ta koma ta hau gado ta kwanta.
Knocking Nadra ta yi a kofar falon shiga babban falon gidan. .
"Ammi dake kokarin zuwa bude kofar, tana budewa ta ga Nadra da Fahad a tsaye.
Cike da farin ciki ta ce .
"Ku ne a daren nan haka lafiya?"
"Lafiya lau mun zo gaishe ku ne."
"Bisimillah ki shiga ciki ma na.
Suka shiga ciki suka gai da Ammi sanan Nadra ta nufi ɗakin Umma tana ƙwala na ta kira .
Abba ne ya fito daga part ɗin sa yana ganin Fahad ya sa ya saki murmushi yana cewa .
"Fahad kai ne a daren nan, ina fatan dai ba wata matsala ko?"
"Babu komai Abba muna zaune lafiya."
Nan ya gaida Abba cikin girmamawa sannan ya shida Umma da ta fito yanzu tare da Nasara.
Ta marasa wajen Abba ta ce .
"Abba."
"Na'am ƴar Abba ya faɗa yana rike hannunta suka Zauna a tare. Sai ta yi saurin zama kasa.
"Ina Aunty Sidra ce ban ga ta fito ba ko ba ta ji zuwa ga ba ne."
Ta yi maganar tana nufar dakin su.
"Ki duba tana dakin baƙi."
Cewar Umma tana kalli. Nadra.
"Me take yi dakin baƙi kuma ko tana da bako ne?"
Ba wanda ya amsa ma ta ita kuma ta nufi ɗakin.
Da sallama ta shiga sai ta hango ta kwance kan gado ta ya tana lulluɓe cikin bargo.
Ƙarasawa ta yi kamar ta tayar da ita amma ta fasa cikin rashin jin dadi ta ce.
"Allah sarki Aunty na so mu yi magana ta fahimta da ke ki fahimce ni ko za ki daina jin haushi na. Kuma ba ba ki da lafiya bai dace na tayar da ke ba. Ko ba haka ba na san idan kina barci ba ki son a tayar da ke. Zan tafi Allah ya huci zuciyarki ya kuma ba ki lafiya."
Daga haka ta fice daga cikin ɗakin. Sidra na jin fitar ta ta tashi zaune tare da bin kofar da ta fita da harara.
Ko da ta fita ta koma falo ta samu Ammi ta kawo wa Fahad tuwon aljanna da miyar ɗanyar kuɓewa sai ƙamshin man shanu miyar ke yi.
"Ga girkin uwar gida ka ci na san kana son shi, Allah ya sa Amarya ba ta cika ma ka ciki ba."
"Yauwa Ammi Allah ya bar ma na ke, kamar ko kin san ban yi girki na take away za mu siya dama.,"
Wani kallo Umma ta yi ma ta mai sannan ta ce.
"Take away Nadra kika ce fa? Yaushe kika zama haka? Abinci da za ku ci ke da mijinki ya gagare ki ? Wanan ba tarbiyyar d na koyar da ke ba ne?"
'Oh Allah ta ya zan fahimtar da su ne? Xan ce ma su na kasa girki ne saboda damuwar Aunty Sidra ko xan ce na kasa girki ne dan saboda jarabar Yaya Fahad ?'
Tana tsaka fa tunanin ne ta ji Muryar Fahad na cewa .
"Ba haka ba ne, ni ne na ce ta huta yau kawai na yi ma na take away, akin na ma ta hawa ita kadai a gidan nan."
"Wanan ba dalili ba ne Fahadz kada ka yi kokarin kare ta. Aikin da Nadra ta saba da shi a gidan nan ai bai kai aikin gidan ka yawa ba, kawai dai lalacin da ba ta da shi a baya ne take so yanzu ta koya "
Cewar Ammi tana kallon Nasara.
Umma za ta yi magana Abba ya ce.
"Ku bar ta haka nan in sha Allah ba za ta sake ba."
Kallon Nadra ya yi yana cewa .
"Ƴar gidan Abba kada ki sake bari mijinki ya tafi siyen abinci gidan abinci bayan kina da ran ki da lafiyar ki ba tare da wani baban uzuri ba."
"To Abba in sha Allah."
Tashi Abba ya yi yana cewa
"Zan ɗan fita kika kafin na dawo kun tafi, Allah ya ma ku albarka sai da safe."
Daga haka ya fice suna ma sa sallama. Umma ta tashi ta ba su wuri su ci abinci.
"Ammi ma ta ce ina zuwa ."
Barin wajen ta yi Fahad yana kallon yadda Nadra ta kwaɓe fuska kamar za ta yi kuka .
"Kukan me za ki yi, daga magana kin daki baki kina fadar zance waye ya san ba ki yi girki ba? Ke kika faɗa da bakin ki."
Ya yi maganar yana ƴar dariya. Sanann wanke hannu ya fara cin tuwon.
"Ki yi hakuri mu ci kin ji Nadfah. Ko take away kike so na siya ma ki a hanya?"
Kai ta girgiza alamar a'a.
"Okay to kaza fa za ki ci?"
"Ba zan ci ba."
Ta saka hannu suka fara cin tuwon a tare.
_Jalaluddeen_
Bayan ya fito daga ɓoyayyen gidansa yana tsaye a ƙofar gidan ya ɗan tsaya yana sauraren bugun zuciyarsa. Murmushi kadan ya yi yana kara matse sandarsa dake hannusa. kai tsaye hanyar gida ya koma. Don ya san zuwa yanzu Ma'eesha za ta iya ɗaga hankalin ta. Ya san da ya zo da wayarsa ta yake waya da ita da tuni ta kira shi. Yana tafiya maganar Taj kawai ke aunawa a ƙwakwalwarsa da kuma na'urar saurare da ya gani a ɗakin.
"Ka fara makara"

Page7️⃣4️⃣
Bayan ya fito daga ɓoyayyen gidansa yana tsaye a kofar gidan ya ɗan tsaya yana sauraren bugun zuciyarsa. Murmushi kaɗan ya yi yana kara matse sandarsa dake hannusa. Kai tsaye hanyar gida ya koma dan ya san zuwa yanzu Ma'eesha za ta iya ɗaga hankalin ta l. Ya san da ya zo da wayarsa ta yake waya da ita tuni ta kira shi. Yana tafiya maganar Taj kawai yake aunawa a ƙwakwalwarsa da kuma na'urar saurare da ya gani a ɗakin.
"Ka fara makara.!"
Mai keke nape ya tare ya sanar da shi unguwar da zai kai shi.
Har bakin layin su ya kai shi sanan ya ce ya dakata a nan zai sauka.
Yana sauka kenan sai ya tambaye shi kuɗin sa, ɗari biyar ya ce ma sa kuɗin sa. Take ya zare dubu daya a cikin aljihun wandonsa ya mika ma sa. Yana mika ma sa ya kama hanya, mai nape ya ciro ɗari biyar da niyyar ba shi canji amma sai ya ga ya fara tafiya.
"Mallam ga canjin ka!"
Alama ya yi masa da hannu alamar baya son canjin.
"Ikon Allah ga mutum Makaho har da sandar jagoransa amma ya bar canji haka kamar wani mai kudi?"
Ya ja kekensa ya bar wajan yana sake mamakin wanan makahon.
Cikin nutsuwa yake tafiya har ya karasa kofar gidan. Ya sa hannu ya tura kofar fale-fale bakinsa dauke da sallama.
Da sauri Ma'eesha ta fito daga ɗaki yana sakin ɓoyayyen ajiyar zuciya.
"Wa'alaika salam warahmatullah."
Ta amsa tana murmushi.
"Sannu da dawowa Mijina."
Ta kama hannunsa ta taimaka ma sa ya zauna a saman tabarma .
Sai sannu take jera ma sa kamar mai ciwo.
Tashi ta yi ta kawo masa breakfast,kunun gyada ce ta yi sai ƙosai da ta soya. Kasancewar yanzu ta daina yin abinci kala-kala ko akwai saboda canjin rayuwa da ta samu kanta a ciki.
Sai da ya sha kunun gyaɗar da ƙosai ya ƙoshi kuma ya ji dadin kunun sosai ba kadan ba.
Bayan ta kwashe kayan tta dawo ta zauna gefen sa .
"Mijina."
"Na'am matata."
"Ina fatan dai lafiya da na ga an isar da sallar ina ka dawo ba har gari ya waye lokacin da ka saba dawowa ya yi ba ka dawo ba, haƙiƙa hankali na ya tashi a lokacin musamman da na kira wayar ka na ji ga a kashe. Hankali na ta sake tashi kada a yi amfani da makantar ka a cutar da kai, ka san mutane idan suka ga mutum Makaho ne ba wuya za'a cuce shi ."
"Kar ki damu ba abin da zai same ni in sha Allah. Na gode da nuna ƙauna da kulawa. Allah ya bar mu tare."
"Amin ya rabbil izzati."
_Fahad_
Bayan sun kammala cin abinci ne Nadra ta kwashe kayan ta je kitchen ta wanke su.
Sannan ta shiga ta yi wa su Umma da Ammi sallama . Har ta kai bakin ƙofar fita daga dakin Ammi dai ta kira ta.
Dawowa ta yi ta ce .
"Ga ni Ammi."
Wani leda ta miƙa ma ta tana cewa.
"Karbi wanan kayan mata ne na gyaran zamantakewar aure. Ina so ki sha su. Wasu haka nan za ki sha ki yar da robar, wasu da madara za ki sha su . Duka dai an rubuta su za ki gani sai ki dinga amfani da su.
"Kai Ammi dan Allah ki bar su ko wadanda Gwaggo Laraba ta ba ni ban gama sha ba, sanan kin kara ma ni wasu."
"Eh nata daban nawa daban don haka karbi ki je ki yi ta sha ki zama ƴar gatan mijinta."
Ba musu ta karba ta rike zuwa falo Ammi na bin ta a bayan ta suka tarar da Umma na yi ma sa sallama.
Har wajen motat Ammi ta raka su in da Fahad ya ba ta kudi ma su yawa. Cike da murna ta koma cikin gidan bayan ta ga wucewar motarsu daga cikin gidan.
_Sidra_
Bayan fitar Nadra sai ta tashi daga likimon da ta yi kamar mai barci .
Wayarta ta ɗauka tana kuka ta sanar wa Sady babu abun da ya faru. Sady baby ta yi farin ciki kuma ta yi bakin ciki. Farinciki shi ne jin Nam da wata ɗaya za'a aurar da Sidra kuma ga ƙauyensu, bakinciki kuma shi ne jin yadda zaman Fahad da Nadra ya yi daidai suke zaman aure cikin soyayya da juna.
"Daina kuka ƙawata, don Allah ya isa haka ki kwantar da hankalinki akwai wani Mallami da zan kai ki wajen sa aikinsa yana ci sosai, idan muka je kika sanar da shi matsalar ki to ki ɗauka bukatar ki ta biya kawai. Aikinsa kamar yankan wuƙa ne."
"Ni fa Wallahi ban yarda da bokayen nan ba maƙaryata ne, karya suke yi mafi yawan maganar su."
"Ke ba boka ba ne shi fa Mallam ne, ki kwantar da hankalinki bukatar ki ta mallakar Fahad za ta biya ki sa wannan a ranki."
"Kai gaskiya hankali na bai kwanta da zuwa wajen boka ba Wallahi."
"Wallahi ba boka ba ne gobe ki zo mu je za ki tabbatar da abun da nake faɗa ma ki ."
",Shi kenan zan zo duk da ban san yadda zan fito daga gidan ba. Abba ya tsaurara ma ni, idan ba damuwa ke ki je a madadina ma na."
"In ji waye ya faɗa ma ki cewa zan iya zuwa a madadin ki, ai ke za ki je da kanki ya ganki, idan ya so daga baya zan dinga zuwa ina karɓo ma ki magani ko ba ki je ba. Yanzu ki yi dabara ki bar gidan nan gobe in sha Allah."
Shiru ta yi tare da nazari kafin ta ce.
"Zan duba yiwuwar hakan."
Sallama suka yi ta katse kiran wayar tana tunanin hanyar da za ta bar gidan nan.
*Bayan kwana biyu*
_Nasreen_
Tana zaune ita da saurayin ta a wani tsadadden gidan cin abinci. Suna tattaunawa kan maganar auren su.
Kamar an ce ta daga kai ta kalli kofar shigowa. Jalaluddeen ta gani tare da wani mutum wanda zai iya haifar ta. Dukkansu sanye suke cikin shigan Suit baƙaƙe.
Sun zo sun zauna a wasu kujeru biyu da ke gefe ɗaya.
Shi mutumin yana sanye da bakin glass a idanunsa yayin da Jalaluddeen bai saka glass ba.
Kallon saurayin nata ta yi a dan firgice ta ce.
"Sai anjima za mu yi waya ina sauri zan je wani wajen."
Kafin ya yi magana har ta bar wajen ta fita da sauri. Mamaki ya kama shi amm ba wanda zai tambaya, don haka ya biya kudin abincin ya fice. Dama daga ita har shi kowa da motarsa ya zo suka hadu a wajan .
Gudu Nasreen ke yi kamar za ta tashi sama, burin ta kwai ta isa gidan Ma'eesha.
Tafiyar da za ta dauke ta Mintuna ashirin da biyar ta isa a mintuna goma sha biyar.
Ko sallama ba ta yi ba ta shiga ƙwalawa Ma'eesha kira .
"Ƙawata!"
Da sauri Ma'eesha ta fito waje tana tambayar Nasreen lafiya. Ba ta tsaya bayani ba illa iyaka ta janyo hannun Ma'eesha tana cewa.
"Zo mu je da sauri ba lokaci."
Ganin yadda take jan hannun ta ne ya saka ta fisge hannunta tana cewa.
"Anya kanki daya kuwa ?"
"Idan muka je za ki gani."
"Ba inda zan je ba tare da izinin mijina ba."
"To wajan shi mijin ne za mu je."
"Wai me ke damunki ne haka?"
"Yau zan nuna ma ki asalin waye mijinki, za ki yarda cewa mutumin da na kawo ma ki photo na ce shi ne mijin ki amma kika ƙaryata ni to yau za ki tabbatar wanan shi ne mijin ki. Ba Lokaci mu je."
_Mamy_
Zuwa yanzu ta rame ta fige ta fita a hayyacin ta sosai ba kadan ba. Don ko barcin kirki ba ta iya yi. Da zaran ta kwanta daddare to za ta kasa barci ne sai mafarkai barkatai da take yi a duk lokacin da barci ya yi nasarar ɗaukarta.
Gefe guda kuma ga matsalar dake tsakanin ta da Laila. Din kullum sake rasa abubuwa suke yi a gidan. Ga shi ta rasa ta ina matsalar take . Ba ta zargin ƴaƴanta amma sai dai masu aikin gidan su take zargi.
Ranar da ta dinga bala'i akan sai an fitar da kayan da aka ɗaukar ma ta . Haka ta dinga binciken ɗakin masu aiki amma ba ta samu komai ba.
Abubuwa sun yi ma ta zafi ga shi bokan da yake ma ta aiki ya nemi maƙudan kudade a wajen ta saboda aikin da ya yi yana neman warware wa. Ya umarci da ta bayar da kuɗaɗen don ya sabunta aikinsa.
Da kyar ta iya shawo kan Sidra ta yarda da cewa za ta bi ta su tafi gobe.
_Alhaji Daula_
Zaune yake a tangamemen falonsa da waya kare a kunnensa yana magana. A tsaye bayansa kuma wasu murɗaɗɗun maza ne guda biyu.
Sai da ya kammala wayarsa sanann ya juyo ya kalle su.
"Yanzu yaushe contenar za su iso ne?"
Ɗaya daga cikin su ya ce.
"Yau da misalin ƙarfe biyu na dare za su iso ta jirgin ruwa."
Jinjina kai ya yi kafin ta gyara zamansa ya ce.
"To da zaran sun iso a raba makaman ga waɗan da suke jira kamar yadda aka saba. Sannan ku kasance cikin shiri saboda wanan Intelligence officer ya sa idanun su akan harkokin mu. Ku bi komai a sananu saboda yana da basira fiye da tunanin ku, na ji labarin waye Jalaluddeen sai kun yi taka tsantsan.
"Na so mu ga bayansa kamar yadda muka yi wa sauran jami'an da suka nemi shiga gonar mu, amma shi mun gagara sanin sa sai daga baya."
Cewar daya daga cikin yaran Daula.
"Ka san shi yana da matuƙar lissafi ya ɓoye kansa wanda ba mu san shirin sa ba sai dai ya yi nisa a binciken da yake yi. Ya matukar iya basaja Yallaɓai yana da abubuwan da ya sani akan mu."
Jinjina kai ɗaula ya yi sannan ya ce.
"Ranar da kuka ritsa shi ai kasa kashe shi kuka yi, wai a ce duk yawan ku mutum ɗaya ya gagare ku har ya tsere ba mu sani ba, taron mara sa amfani kawai."
Ya yi maganar cikin takaici.
"Ka yi hakuri yallaɓal za mu shirya ma sa gadar zare zai faɗa."
"Haka kullum kuke cewa, ku ne ma su shirya gadar zare karshe shi ba zai faɗa ba ku ne za ku fada ciki.."
Ya yi maganar yana amsa wayar da aka kira shi.
_Ma'eesha_
Kallon Nasreen take yi da maɗaukakin mamaki .
"Ban gane mijina ba ina kika gan shi, ko dai can wajen gyaran takamin da yake zama ya yi?"
Dariyar rainin hankali ta yi kafin ta ce.
"Ko ma sai ina ne za ki ga ashirin waye mijinki ki san da waye kike zaune ."
"Na san da wanda nake zaune Khalifa ne mijina dan asalin garin Maiduguri ko ina da wani mijin ne bayan shi."
Sanin cewa duk yadda ta yi kokarin fahimtar da Ma'eesha ba za ta fahimta ba ne ta saka bin ta a hankali ta yadda za ba za ta bijire ma ta ba.
"To amma ba jimawa na kira wayarsa ba ta shiga ."
"Eh idan mun je can za ki gan shi kuma za ki ga abun mamaki ."
Hijabi ta saka suka fita in da ta rufe gidan da makulli sannan ya shiga motarta da niyyar za ta kai ta wajen mijinta.

Page7️⃣5️⃣
Hijab ta saka suka fita in da t rufe gidan da makulli sannan ta shiga motarta da niyyar za ta kai ta wajen mijinta.
_Makaho_
Yana zaune a tsadadden gidan cin abincin shi da ogan sa Assistant Director Sulaiman don bai yarda ya je ɓoyayyen gidan nasa sa ogansa ba, don a halin yanzu kowa abun zargi ne a wajansa.
"Ka ce Harbin da aka yi ma ka ba daga mutanen Daula ya fito ba?"
Jinjina kai ya yi yana kallon Ogan nasa kafin ya ce .
"Ƙwarai kuwa ba daga mutanen Daula ba ne, ɗaya daga cikin mutanen mu ne suka harbe ni bullet din bindigar ya fito ne daga weapon serial number na DSS stock."
Mamaki ne bayyane a fuskar ogan nasa kafin ya ce
"To yanzu waye kake zargi?"
"A halin yanzu kowa abun zargi ne a wajena musamman wannan da suka san shiri na. Shin kai Assistant Director zan zarga da nake tura rahoto office din ka, ko kuma zan zargi Deputy director ne wanda idan ka karanta rahoto kake tura wa office din Deputy director idan ya dace? Don na fahimci duk bayanan da nake aika wa da shi suna isa gaa su safarar makamai . Shin kai zan zarga ko wani a ofishin ka yana karanta rahoto kafin rahotanni su kai gare ka?" Ko kuma wani ne zan zarga cikin wadanda cikin manyan da suke mataki na sama?"
Zuciyarsa ta buga wanda hakan ya sa ya juya bayansa. Zaro idanun waje ya yi hango Nasreen sa Ma'eesha.
"Sir zan bar wajen nan yaxu kawai matsala."
Kamar walƙiya haka ya bar wajen nan take. Sulaiman bai ce komai ba ya cigaba da cin abincinsa. Don dama shi Makaho ruwa kawai ya buƙata ya ce ba zai ci abinci ba.
"Assalamu alaikum"
Nasreen ta yi ma sa sallama yayin da Ma'eesha ke bayan ta.
"Baba dama wani nake nema wanda na gani a nan tare da kai?"
"Wai maganar me kike yi ne yarinya? Ba kowa da nake tare da shi ni kaɗai ne a nan wajan."
"Baba da shekarun ka za ka yi irin wanann magana, na gan ku tare."
"Yarinya don Allah ki bar nan ba na son hayaniya.""
Ma'eesha ta ja hannunta suka fita waje.
"Ba kin ce mijinki yana wajen gyaran takalmi ba?"
"Eh yana can ma na."
"Mu je wajen za ki ga baya wajen hakan zai sa ki yarda da ni.,"
Suka shiga motar Nasreen ta ja suka bar wajen aguje.
"Wai gudun meye haka dan Allah idan ba za ki iya tafiya a hankali ba ki ajiye ni ko ki ba ni na yi driving a hankali."
Ta yi maganar tana tuna lokutan da kullum idan za ta fita da mota sai Mummy ta yi mata maganar ta yi driving a hankali kada ta yi tuƙin ganganci. Kullum abun da Mummy ke yi ma ta magana akai kenan.
Ƙwalla ne ya cika idanunta a hankali ta ce.
"Allah ya jikan ki Mummy Allah ya kai haske kabarinki ."
"Amin ya Allah."
Nasreen ta amsa idanunta na kan driving da take yi.
"Ina sauri mu karasa wajan da mijinki yake gyaran takalmi ne, ina mai tabbatar ma ki da cewa ko mun je yanzu baya wajen, shi ne dai wanda na gani a wannan gidan cin abincin da muka fito. "
Shiru ya biyo kafin ta ce .
"Na lura fa kina son mijin nan naki da yawa, me ya sa kike son sa a matsayin sa na makaho shi ba komai yake da shi ba faƙiri ne fa, ba kuma wai dukiya ba ballantana na ce saboda kuɗin sa ne. Ko kyawun surarsa ne ya rude ki?"
"Ina son sa ne sabida Allah ba don wani abu ba, kuma yana da zuciya mai kyau, duk da na shiga damuwa lokacin da aka aura ma ni shi ba tare da sani na ba, sai dai Idan zuciya ta shiga damuwa, ta rikice, ta rasa natsuwa, babu wani abu da zai kawo mata sassauci kamar tunawa da Allah, ambaton Allah, da kuma roƙon Allah. Da kike maganar kyawu ya kamata ki sani. Kyau yana da matakai, mafi ƙasƙanci shi ne kyawun kamanni, matsakaici shi ne kyawun magana, mafi tsayi shi ne kyawun ruhi, mafi daraja shi ne kyawun hali, Amma mafi tsarkakarsu duka shi ne kyawun zuciya. Nutsuwar zuciya tana cikin abu biyu,
Tawakkali, ka miƙa lamuranka ga masaninin dake riƙe da gaibi,
yarda, ka yarda da tabbacin cewa abin da Allah ya zaɓa maka shi ne mafi alheri ne Mutumin da yake dogaro ga ALLAH, ba ya jin haushi idan bai samu abu ba, Idan kuwa ya samu koda kaɗan ne yana godiya, ba ya jin tsanani idan ya fuskanci ƙalubale, zuciyarsa tana da salama."
Jinjina kai Nasreen ta yi kafin ta ɗan kalli Ma'eesha ta ce.
"Tun da kike da shi ya taba furta ma kalmar soyayya? Ya taɓa cewa yana son ki?
Dariya ta yi kafin ta ce .
"Soyayya da aure suna bukatar hakuri, fahimta, da kyautatawa. Idan miji ya kula da mace tagari, shi ma zai zama hasken rayuwarta. Rayuwa ba ta da sauƙi, amma da kyakkyawan zamantakewa za'a iya cimma farin ciki da zaman lafiya. Gaskiyar soyayya tana bayyana ne a cikin aikace-aikace, ba kawai a cikin magana ba. Idan miji ya zama ginshikin farin cikin matarsa, domin ita haske ce a gare sa, kuma shi haske ne a gare ta."
'To ni dai shawara da zan ba ki tun yanzu ki koyi hakuri da rashin sa, domin shi za ki iya rasa shi a kowane lokaci."
"Kada ki sake yi ma ni maganar nan ba na so."
"In sha Allah, amma akwai ranar da za ki gasgatani."
Bayan sun shigo unguwar ne Ma"eesha ta nuna wa Nasreen in da yake zaman gyaran takami. Suna ƙarasawa ta yi parking gefe.
Da maɗaukacin mamaki take kallon Makaho yana zaune ba cikin kayan da ta gan shi ba, wato suit din jikinsa da ta gan shi da shi a can. Yanzu hanyan da ya bar gida ne da su wani yafi mai arha wanda ake cewa ka yi shirun ka Maraya. Da hula taɓa ka ji hadisi da ya saka. Sai takamin soso dake ƙafarsa. Saɓanin can da ta gan shi da tsadadden takaomi.
"Yanzu dai ga shi wajen sana'arsa yana aiki. Wai me mijina ya yi ma ki da kike so sai kin raba ni da shi? Me ya yi ma ki ne a rayuwa? Don Allah ya isa haka kada ki sake kawo Mani magana akan mijina ko kina zargi da ya isa haka!"
Nasreen ba ta ce komai ba ta yi wa motar key suka bar wajan.
Murmushi Jalaluddeen ya yi tare da magana a zuciyarsa..
'Yarinya ba fi karfin makircin ki na wuce sanin tunanin ki.'
Tun da suka kama hanya ba wanda ya sake magana a cikinsu. Nasreen ta fara tsorata da shu'umancin Jalaluddeen. Duk shirin ta na shirin tona ma sa asiri sai ya wargaza shi.
Ta ya ya ma a cikin kankanin lokaci kuma bayan ta tabbatar ya ga su ne a wajen shi ne ya bar wajen. Sannan sun biyo bayansa a kankanin lokaci ne har ya isa ya zo nan ya canza kaya ya fara aikin gyaran takami. Gudu fa ta kure a mota amma duk da haka sai da ta tsallake wannan ma?
Cikin takaici ta buga sitiyarin motar da ƙarfi wanda hakan ya sa Ma'eesha cewa.
"Sauke ni a nan zan karasa da kafata."
Ba ta saurare ta ba ta cigaba da tuƙin da take yi.
"Ki damu da abun da yake gabanki ya fi ma ki da ki tsaya zaman saka wa bawan Allah ido da neman ganin aibun sa. Ta ya daga ganin wani a wani gari ki ce mijina ne, sannan yanzu kin ga wani a tsadadden gidan cin abinci ki ce shi ne, mutumin da yake aiki tuƙuru dan ganin ya samu abun da ya kawo ma na ko ba yawa ne zai samu kudin zuwa gidan abincin nan? Sannan nawa ma yake samu a rana ɗaya, ku rabin abincin wajen nan baya da shi ko da zai kai sati yana aiki yana tara kuɗin. Ke burin ki ki raba ni da shi ko?"
Murmushin takaici Nasreen ta yi sanan ta ce .
"Wata rana yana zuwa wanda idan gaskiya ta yi halinta, ranar da za ki shiga tashin hankali da mamaki ranar da za ki zubar da hawaye kina nadamar rashin yarda da zance na yana zuwa. Ki rubuta ki ajiye wallahi sai kin yi nadamar ƙaryata ni da kika yi ."
"Nadama, nadama fa kika ce."
"Ai yanzu ma ga nadamar nan na yi na biye ma ki na fita daga gidan aure na ba tare da izinin mijina ba. Kin sa na shiga tsinuwar mala'ikan Ubangiji ina zaman lafiya ta. Kada ki sake kawo ma ni wani zancen akan mijina ya isa haka nan."
Daidai lokacin Nasreen ta yi parking a kofar gidan, Ma'eesha ta bude murfin motar ta fita ba tare da ta yi magana ba.
Tsawon mintuna biyar Nasreen na cikin motar tana tunani, kafin ta ja motar ta bar kofar gidan.
_Sidra_
Washegari dama suka yi da Sady baby akan ta zo ta raka ta wajen Mallamin da yake ma ma ta aiki.
Don haka ko da ta yi breakfast ta cewa Umma za ta shiga ɗakinta ta kwanta sai rana za ta fito. Don Umma ce kadai ke sakar ma ta fuska a gidan.
Don haka ko da ta yi shirin fita ta ƙofar kitchen ta fice, ba ta bi ta gate ba sai ta bi kofar baya wanda an dade ba'a bude kofar baya wanda an daɓe ba'a bude kofar ba. Ta fita daga gidan ba wanda ya ga fitan ta.
A bakin titi ta hadu da mai keke nape ta tare shi ya tsaya.
Har za ta shiga sai ta ga wata mata da yara biyu a ciki.
Da kin kalli matar kin san tana cikin matsin rayuwa bisa la'akari da kuɗaɗun kayan jikinta da na yaran.
Kallon matar ta yi tana yamutse fuska alamar wacce ta ga abun ƙyama .
"Tafi Mallam ba da kowasu irin mutane nake haɗa numfashi."
"Ki yi hakuri Hajiya ba kusa sauke ta ai sai ja kai ki duk in da kike so."
Ba ta saurare shi ba ta matsa gefe tana tsuki. Ganin haka ya ja nape ɗin sa ya bar wajen.
Ma su nape sun kai biyar tana tare wa da ta kalli kayan jikinsu ta ga alamar ba ma su tsafta da kwalliya ba ne za ta ce su tafi. Sai Surutai take yi ita kadai.
"Idan ba dole ce ta sa na yi satar fitar nan ba ai da na dauki key din mota na fita da waɗan nan kucakan mutane da nake gani."
Tana nan har kiran Sady baby ya shigo wayarta, ɗagawa ta yi tana cewa .
"Na fito daga gidan ina titi."
"Ba abun hawa ne?"
"Ba ki gan su ba wasu ƙazamai da su ko wanka ba su yi ballantana ki ji ƙamshin turarerensu."
"Ina ruwan ki da kuma wankan su? Ke dai ba burin ki akai ki in da kike so ba? Dan Allah ki shiga ina jiran ki kafin gidanku su san kin fito."
Suna gama magana sai wani ta tsayar. Ba laifi ya yi duk da ba yadda take iya ta samu ba. Haka ta shiga ciki tana yamutse fuska ta sanar da shi in da za ta je.
Ko da ya sauke ta a kofar gidan Sady baby ta tambaye shi kudinsa ya ce ma ta dubu ɗaya ta fito da dubu daya a cikin jaka ta cilla ma sa kuɗin, sai kuɗin ya fadi kasa.
Mai nape din ya juya ya kalli gabas da yamma kudu da areawa ya ga ba kowa a kusa da yake kallon su.
Ya fito daga keke nape ɗin ya zaro wuƙa da ya soke a ƙugunsa. Ya saita wuƙan daidai saitin maƙogoronta fuskarsa a murtuƙe. Idanu Sidra ta zaro wajen cikin tashin hankali da tsoro.

Page7️⃣6️⃣
Ta fito daga keke nape ɗin, ya zaro wuƙa da ya soke a ƙugunsa.
Fuskarsa a murtuƙe. Idanu Sidra ta zaro waje cikin tashin hankali da tsoro.
"Sana'a ta nake yi ba Maula ba, na kawo ki in da kike so ki bani kuɗina cikin girmamawa."
Cikin tsoro da fargaba ta ce.
"Ka yi hakuri kada ka cutar da ni bari na ɗauko kuɗin na ba ka."
"Ƴar wulaƙanci kawai na fi ki ɗanyen kai wallahi. Yanzu na ga dama sai na fassara ki a wajan nan na yi tafiyata."
Yana sakin wuyanta ta duƙa ta ɗauki kudin ta mika masa, kaba ya yi ya shiga nape ɗin sa yayin da ita kuma ta faɗa gidan Sady baby q guje.
Daidai lokacin Sady baby na zaune a falo tana waya, ganin yadda Sidra ta faɗo falon a guje ya sa ta katse kiran wayar da sauri ta nufi Sidra tana cewa.
"Lafiya?"
Kafin ya ba ta amsa ta leka harabar gidan ganin ba kowa ya sa ta karasa bakin gate ɗin, ta rufe da sakata sannan ta koma falo wajen Sidra.
"Meke faruwa kika firgice haka?"
Ba ta ba ta amsa ba sai dai ta nufi toilet dake cikin falon Sady baby. Don ta tsorata sosai cikinta sai da ya murɗa.
Bayan ta fito ne Sady baby ta ce .
"Wai meye haka ina ta tambayar ki ba ki ce komai ba kin saka ni cikin tashin hankali?"
"Wallahi mai nape din ta ya ɗauko ni Ɗan daba ne shi da wuƙa yake yawo ban sani ba. Daga na jefa ma sa kudi shi kenan ya zaro wuka zai kashe ni, sai da na bashi hakuri ya sa na ɗauki kuɗin na mika ma sa ya ƙyale ni."
Taɓa baki Sady baby ta yi kafin ta ce .
"Allah ya kyauta."
"Amin ya Allah ."
"Za mu tafi yanzu ne ko sai kin huta?"
"A'a wani hutu byNa na sanar da ke cewa satar fitar na yi kun sani."
"Okay."
Ta faɗa tana nufar bedroom ɗin ta, ba jimawa sannan ta fito sanye da ƙaramin gyale da key din motarta a hannun ta.
A tare suka fita Sady ta rufe ƙofar falon da key sannan suka nufi harabar gidan.
Sai da ta fara wangale gate ɗin gidan sannan ta shiga motar Sidra ma ta shiga ta ruwa miyar key ta fita daga gidan.
Bayan ta fitar da motar waje ne ta fito ta rufe gate ɗin da key sannan ta ta koma cikin motar ta ja suka bar unguwar.
"Wai ina maigadin gidanki ne?"
"Na sallame shi saboda yana sa mun idanu a cikin Lamira?"
Daga haka suka j yi nisa a tafiya ba wanda ya yi magana .
_Makaho_
Da sallama a bakinsa ya shigo cikin gidan. Hannusa daya riƙe da sandarsa ta jagora, dayan hannun muka yana rike da kayan gidan takalmi.
"Ma'eesha dake cikin daki ta ji dawowarsa ta fito amsa, da sauri ta karasa in da yake ta karbi kayan gyaran takami dake hannusa tana yi ma sa sannu da zuwa.
Ya amsa ma ta yana bin bayanta zuwa cikin ɗaki.
Da sallama ta shiga ta amsa sannan ta rike sabadrasa tana nuna ma sa tabarmar da zai zauna.
"Ba sau kin wahalar da kanki wajen nuna ma ni wajen zama ba. Na riga na san komai da yake cikij dakin nan
Zama ya yi t kawo ma sa ruwa. Pure watar bayan ta fasa leda ta zuba kofi
Karba ya yi ya karba tare da yin bisimillah ya sha.
Farantin da ta jera masa kulollin da ta zuba ma sa abinci ta kawo ma sa ta ajiye a gabansa.
"Ga abinci ."
"Na gode Allah ya yi ma ki albarka."
"Amin ya Allah."
Tana kallon da tana tuna zancen ƙawarta Yasmeen. Duk da ta san cewa Nasreen ba makaryaciya ba ce. Komai ta faɗa akan gaskiyar ta ne, to sai dai kuma wanan karon ba za ta ce Nasreen karya take yi ba illah iyaka ta ce ta dai yi ma dai yi ma sa kuskuren fahimta ne. Don ko a photon da ta gani ta san wancan na jikin photon wayayye ne ɗan boko, shi kuma wanan mijin nata ɗan gargajiya ne ko turanci bai iya ba. Sannan shi wancan da Nasreen ta nuna ma sa video yadda yake tafiya cike da izza da isa yayin da mijinta kuma tafiyarsa ma irin ba wadanda suka taso ƙauye yake yi, takunsa ba ɗaya ba ne da wancan. Duk da cewar dai Dukansu suna da ƙira irin ta jaruman maza.
Ta cikin bakin glass dake idanun sa yake kallon ta, sannan ya cire glass ɗin ya juyar da kwayar idanunsa tamkar waɗan da basa gani da idanunz wato makafin da za ku ga idanunsu a bude amma bai da amfani.
"Ma'eesha kina kusa kuwa?"
Sai a lokacin ta dawo daga tunanin da ta faɗa tana cewa.
"Ina kusa da kai, me kake bukata ne?"
"Na ji kin yi shiru ne kamar ba kya wajen, lafiya kuwa ?"
"Eh lafiya lau Alhamdulillah."
"Kamar akwai abun da ke damun ki Ko?"
"Eh to gaskiya ɗazu ƙawata Nasreen ta zo ta ce na raka ta wani waje. Na kira wayarka don neman izinin ka amma ba shiga , shi ne na raka ta ba tare da izinin ka ba. Ka yi hakuri ba yi farko da karshe kenan in sha Allah ba zan sake fita ba izinin ka ba ka ka yafe ma ni."
"Ba komai kada ki damu."
"Dama ka ce idan cikin unguwa zan siye abu ko kuma dai a ce gidan Mallam Liman zan iya zuwa ka lamunce ma ni ko?"
Jinjina kai ya yi alamar eh haka ne.
Abinci ta zuba ma sa ya fara ci, farar shinkafa ce da miyar stew da naman Sa wanda ta siyo a bakin layin su.
"Allah ya sakawa bayin Allahn nan da alkhairi."
Ta yi maganar tana tuna yadda suke abincin su ya kare ranar gari ta sha. Amma sai ga shi Allah ya aiko waɗan da suka kawo ma su tallafin dubu ɗari biyar ga shi yanzu suna cin abi mai kyau.
"Wasu mutane kike magana akai?"
"Waɗan da suka kawo ma sa kayan abinci nake nufi.."
"Ayyah, ga shi yanzu shi muke ci. Allah ya saka da alkhairi."
"Amin ya Allah."
Daga haka ya cigaba da cin abincin yana da tuna Nasreen yana murmushi wanda shi kadai ya san Ma'anarsa.
_Nadra_
Bayan sun bar gidan Abba suna kan hanyar su ta komawa gida ta kalli Fahad dake driving.
"Yaya Fahad."
"Wai ba na faɗa ma ki cewa ki daina kira na da Yaya ba ne? Ta ina na zama Yaya a wajen ki ? Ba na son kalar dangi."
Murmushi ta yi kafin ta ce.
"To ya kake so na kira ka?"
"Ke ba ki san sunan da ya dace ki kira ni da shi ba ne?"
"Gaskiya ban sani ba."
"To ki bincika ki nemi suna mai dadi da za ki sakawa mijinki ."
"To."
Shiru ne ya biyo baya kafin ta sake kallon sa ta ce.
"Ka san wani abu?"
"A'a sai kin faɗa ina jin ki."
"Ban samu yin magana da Aunty Sidra ba ko da na je tana barci, kuma ba na son na tayar da ita ka san ba ta da isasshen lafiya."
Shiru ya yi bai tanka ma ta ba, ta juya da niyyar sake yi ma sa maganar Sidran sai ta ga ya murtuƙe fuska tare da yi ma ta wani kallon da ya sa gabanta faduwa , don haka ya ja bakinta ta yi shiru don ba fuskar da za ta sake yi ma sa wani magana.
Har suka karasa gidan ba wanda ya yi wa wani magana. Ganin yadda ya sauya fuska ita ma ta yi fushi ta yi banza da shi ita ma.
Yana gama parking ta fito daga motar ta wuce bakin ƙofar shiga falon. Dai sai dole ta sakavta tsaya sakamakon ƙofar a rufe kuma key ba hannusa.
Shi ma yana lura da yanayin ta amma sai ya share ta, ya ɗan me take yi wa fushi saboda bai ba ta damar magana akan Sidra ba. Bayan tun ba yau ba yake faɗa ma ta idan suna tare ta daina kawo ma sa hirar Sidra baya so, sunan ta na baya son ji amma Nadra ya lura ba ta jin magana sai ta yi masa zancen Sidra dole.
Bude ƙofar ya yi ta shiga da sauri, da ido ya bi ta kafin ya shiga sanan ya rufe kofar.
Kashe komai na falon ƙasa ya yi sannan ya haura upstairs.
Ɗakinsa ya nufa ya shiga, dama ita ma Nadra ɗakinta ta nufa ta shiga ta bude drawer ta ajiye magungunan mata da Ammi ta ba ta.
Sawa ƙofar key ta yi tana tura baki ita a dole ya ɓata ma ta rai take fushi da shi.
Cizon yatsa ta yi sai ta ji wani zaƙi kamar zuma a yatsar. Sai ta tuna da maganin matan Nam maybe akwai wanda yake zuba. Don haka ta fito da su ta ga wani robar zuma ne yake ɗan zuba wanda daga wurin murfi ne.
Sai ta mayar da sauran shi kuma zumar ta zauna tana sha saboda dama akwai ta da son zaƙi.
Sai da ta sha rabi sannan ta ajiye sauran.
Wanka ta yi ta shirya cikin riga da wando na barci ta haura saman gadon kenan sai ta ji ƙarar an tura ƙofar an shigo .
Da mamaki take kallon sa bayan ta rufe ƙofar da key sanan ya ajiye key a saman Side drawer. Wato tana da wani key din dakin kenan a wajan sa.
Kwanciyar ta yi ta juya ma sa baya . Murmushi kawai ya yi ya kashe hasken ɗakin ya haura saman gadon tare da janyo ta jikinsa.
_Ma'eesha_
Bayan ta gama duk ayyukan da ta na dare ta shiga wanka lokacin karfe tara na dare ne, ga hadari ya haɗu a garin sai iska ake yi.
Ga banɗakin babu rufin sama wato ko rana ruwa da rana ake yi zai sauka kan mutum. Don katanga ce kawai aka yi. Tana tsaka da wanka sai ruwa sama ya faɗo da ƙarfi.
Ga ruwan saman da sanyi sosai haka yake zubowa kanta. Ga shi ba ta gama wankan ba . Kuma ita ba ta son ruwan sama ya dake ta.
Haka ta watsa ruwan ta fito waje da sauri, sauran ruwan fita watsa a ƙafarta bayan ta fito .
Kafin ta kai ga shiga ɗakin ma haka ruwan ke fuskanta har ta shiga da sauri tana rawar sanyi.
Yana tsaye a tsakiyar ɗakin wanda dawowarsa kenan shi ma ya cire riga daga shi sai dogon wando, ya kalle ta yadda ta fado ɗakin tana rawar sanyi. Tausayinta yake ji har cikin ransa yana addu'ar Allah ya kawo ranar da komai zai yi daidai sai ya ɗaga darajar ta a cikin mata ya mayar da ita tamkar zara a cikin taurari. Sai ya jiyar da cewa tafi kowace mace sava a duniya. Amma da sauran lokaci akwai babban kalubale a gabansa.
Shin ma ta ya zai fuskanci iyayensa da zancen cewa ya yi aure ba tare da sanin su ba? Ya zai fuskanci zai fuskanci uwar da ta rene shi cike da so da ƙauna da kulawa wanda babu algusu da wanan maganar? Sanan ta yi ma sa kyautar ƴarta to ta ya ya zai iya sanar da ita cewa ya auri wata mace bayan ga ƴarta can na zaman jiransa.
Jin sautin kat kar kat ne ya sa ya kalli Ma'eesha fa haƙurinta ke karkarwar sanyi jikinta ba rawa. Ga towel da ta yi wa ka da shi ya jikin shi ma .
Kasancewar ta san ita kadai ce a ɗakin shi mijinta makaho ne baya gani ko da ma yana gani ba ta san ya dawo gidan ba ya sa ba tare da tunanin komai ba ta zame towel din jikinta ya faɗi ƙasa
Gabaɗaya jikinta dai kaɗuwar sanyi yake yi, fito da idanunsa waje ya yi ganin ta tsaye jikinta na rawa babu komai a jikinta.
"Ya Salam!"
Ta faɗa kamar mai koyon magan a can ƙasar maƙoshinsa.Wutar nepa ce ta ɗauke a daidai wannan lokacin. Lalube ta fara yi inda za ta ga wayarta ta kunna torchlight. Ji ta yi ta faɗa jikin mutum wanda da alama shi ma ba riga a jikinsa, buɗe baki ta yi da niyyar yin ihu yaji saukar tattausan lips a fatar bakinta.
Gabanta ne ya faɗi jin bakinta a cikin bakin wani mutum da ba ta san ko waye ba, a tunanin ta wani ne ya shigo ɗakin, don tun da take da mijinta bai taba rike ko da hannunta ballantana ya haɗa bakinsa da nata.

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.k✏️
*GARGAƊI*
Wannan littafin mallakar marubuciyarsa ce, ban yarda a sarrafa ma ni shi ta kowace hanya ba tare de izinina ba. Kuma ban yarda a karanta shi s YouTube ba tare da izinin ba, don haka a kiyaye!
*SANARWA*
Wannan ƙirƙireren labari ne, ban yi shi don cin zarafi ga kowa ba, idan suna ko hali ya zo ɗaya to arashi ne, mai kashe auren wawa
Page7️⃣7️⃣
Gabanta ne ya faɗi jin bakinta a cikin bakin wani mutum da ba ta san ko waye ba, a tunanin ta wani ne ya shigo ɗakin, don tun da take da mijinta bai taɓa rike ko da hannunta ba ballantana ya haɗa bakinsa da nata.
Jin yadda zuciyarta ke bugawa ya sa ya zare bakinsa daga cikin nata ya yi ma ta raɗa a kunne."
"Mijinki ne."
Sannan ta ɗan samu natsuwa a zuciyarta. Sake ƙanƙame ta ya yi a jikinsa ya xora bakinsa cikin nata tare da tsotsan harshenta a hankali.
Jin yadda ƙafarta ke rawa ne ya sa ya ɗauke ta cak tare da ɗora ta kan katifar ya kwantar.
Tsawon mintuna biyar suna a haka, duk da a tsorace take amma ba ta yi yunkurin hana shi abun da yake yi ma ta ba.
Hannunsa ya da ya shiga shafar fatar jikinta. Wanda hakan ya da ya rikice jikinsa ya ɗauki rawa shafar ta yake ta ko ina daga samanta har ƙasa. Musamman ƙirjinta da suka ɗimauta shi, don a cike dukiyar fulaninta suke.
Ya kai bakinsa ya fara tsotson ɗaya kamar jariri yayin da yake wasa da ɗaya yana murza shi son ransa.
Ƙarar wayarsa ta aiki ne ya cika ɗakin wanda nan take ya dawo da shi cikin hayyacinsa.
Cikin mutuwar jiki ya cire bakinsa da hannunsa daga Mamanta.
Wani Gwauron numfashi ya sauke cikin kasala ya sauke cikin kasala ya sauka daga kan tatifar ya nufi kayan da ya cire, wayar na cikin aljihun rigarsa.
Ɗaga wayar ya yi tana dab ta tsinkewa. Bai yi magana ba ya tsaya yana sauraren abun da na cikin wayar ke faɗa.
"Okay gani nan zuwa."
Ɗaya daga cikin yaransa ne ya sa shi ya kula da motsin mutanen Alhaji Daula.
Ya godewa Allah da ya sa yaron ya kira shi a daidaita wannan lokacin, don har ga Allah ya yi farin ciki da kiran wayar nan ya dawo da shi hayyacinsa. Don gani yake lokacin da za su yi rayuwa irin na cikakkun ma'aurata bai yi ba. Har sai ta san waye shi, ta fahimci cewa Khalifa Makaho ƙarya ne, Jalaluddeen Kabir arzika shi ne gaskiyar mijinta. Shi ya sa lokuta fa yawa yake gujewa abun da zai sa ya haɗa jiki da ita saboda bai san iya inda abun zai tsaya ba a matsayin sa na lafiyayyen namiji. Duk da ya san ba ta jin dadin hakan amma bai nuna hakan ya dame shi ba. Sai dai ya saka a ransa har sai ta ksrɓe shi a yadda yake ta san komai game da shi ta amince da shi a yadda yake, sannan ya gabatar da ita ga iyayensa sun yarda sun amince da ita an yi shagalin bikinsu tare da sanyawar albarkar iyaye. To daga nan ne zai iya kusantar ta a matsayin matarsa su yi cikakken rayuwar aure kamar kowasu ma'aurata. Duk da ya san sai ya fuskanci kalubale daga wajan Ma'eesha da iyayensa amma ya shiryawa hakan lokaci yake jira. Kuma dole zai gargaɗi Ma'eesha ta kiyaye cire kaya a gabansa domin hakan zai iya sa wa ya watsar da ƙudirin sa na cewa sai ta san waye shi zai yi mu'analar aure da ita. Ga shi yanzu ma da ba don kiran wayar da ake yi ma sa ba ai da komai ya lalace ba yadda ya tsara ba.
Ma'eesha kam dama a tsorace take da shi tuni ta nemi kaya ta saka.
"Na ji ƙarar wata waya kuma ka amsa ka ce kana zuwa."
"Eh wayar ce ina tafiya sai na ji ba taka abu, na laluba na ji waya ce, aka kira na ce na tsinta ce. To shi ne yanzu me wayar ya kira yake sanar da ni in da yake na kawo ma sa wayar."
"A'a dan Allah kada ka fita daga cikin gidan nan, yanzu fa dare ne. Why not shi me wayar ka sanar da shi in da kake ya zo ya same ka ya karɓi wayarsa.
Ta kunna torchlight ɗakin ya yi haske.
"Na riga na ce zan kai ma sa "
Fita waje ya yi bayan mintuna ya dawo da alama wanka ya yi.
Sai ta kashe hasken wayar da sanin zai canza kaya. Shi ma ya san haka don haka bai damu ba ya shigo don ya sauya kaya.
"Yanzu fita za ka yi?"
"In sha Allah."
Ya yi maganar yana lalubo wata rigar sanyi mai leda a jiki kuma tana da hula. Sai da ya fakaici idanunta ta soke bindiga a wandonsa.
"Don Allah kada ka fita a daren nan.,"
"Kada ki damu zan kula da kaina, ki yi ma ni addu'a."
"Ko na raka ka ne?'
"Ba buƙata, ki kwanta ki huta ai yanzu kin daina jin sanyi ko, saboda jikina hita ne na ɗumama ma ki jiki ko?"
Kunya ta ji kawai ta dukiyar da kai tana murmushi.
"Sai na dawo ki kulle ƙofar zan buga ku bude idan na dawo."
"Allah ya tsare ya dawo mun da kai lafiya."
Da Amin ya amsa yana ɗaukar sandarsa ya fice daga ɗakin.
_Sidra_
Bayan Sady baby ta yi parking motar a bakin titi ne suka fito suka karasa da ƙafa, sakamakon lungun mota bai iya shiga ciki.
Suna zuwa ƙofar gidan ta ji gabanta ya faɗi kamar ta juya, wanda har sai da ta tsaya cak, amma Sady baby ta janyo hannun ta tare da yi ma ta alamar su shiga ciki.
Gidan shi kadai ne a layin kuma gidan ya fita daga sahun jama'a don ya juya wa sauran gidajen baya, wato sai jama'ar da ke kusa da shi ba su ganin wanda ke shiga ko wanda ke fita.
Cikin sanyin jiki ta bi Sady suka shiga cikin gidan.
Ƙamin gida ne mai ɗauke da ɗakuna biyu, sai banɗaki da kitchen a gefe.
Da sallama suka shiga cikin gidan, shiru ba wanda ya amsa sai Sady baby ta ƙarasa kofar wani daki tana sallama.
Ya amsa sallamar ta shiga ciki, bayan kamar mintuna uku ta fito ta cewa Sidra ta shigo ciki.
Shiga ta yi da sallama a bakinta ya amsa yana zaune a saman tabarma da wani faranti a gabansa. Ƙasa ne a cikin farantin, sai wata ƙwarays dake da ƴaƴan wuri a ciki. Daga gefe kuma magunguna ne da yawa da aka ɗaura aka ajiye.
Sidra ta shigo tana yamutse fuska alamar tana jin wari. Kallon ta yake yi yana haɗiyar yawu kamar wani tsohon maye.
Gefen Sady baby ta zauna ta buɗe baki ta ce .
"Sannu Mallam."
"Yauwa."
Sady baby ta gyara zama ta ce .
"Mallam wannan ƙawata ce tana so..."
"Ki yi shiru ba sai kin faɗa ba, na san komai dake tafe da ita."
Tsayawa suka yi suna sauraron abun da zai faɗa.
"Wato sunanki Sidra kina da saurayi da kike mutuwar so Fahad sunan sa. Ƴar uwarki ce Nadra ta yi asiri ta janyo da hankalinsa wajenta, ke kuma ta yi maki kurciya kika bar gari , ta canzawa iyayen ku tunani suka sura ma ta saurayin ki, yanzu haka ma ko ganinki baya son yi ko?"
Da maɗaukakin mamaki Sidra ke kallon Mallama jin yadda ya fadi sunan ta da na Nadra da Fahad, sanan abun da ya ba ta mamaki wai Nadra ta yi ma ta kurciya ta bar garin saboda ta auri Fahad.
"Mallam dama Nadra son Fahad take yi kuma ita ta aikata ashirin da ta raba mu da shi? No wonder lokaci ɗaya daga wata ta ma ni wulaƙanci saboda ta samu daukaka na ji ba zan iya hakura ba zuciyata ta dinga azalzalata akan sai na ɗaukaka fiye da ita na rama wulakanta ni da ta yi, ashe ba yin kaina ba ne?"
"Ƙwarai kuwa aikin asiri ne."
"Aiko ba zan taba bari da samu salama a gidan Fahad ba sai na ɗauki fansa."
"Kar ki damu ki ɗauka bukatar ki ta biya za'ayi ma ki ko ma mene ne kike so ayi ma ta. Ko kashe ta kike so a yi ko haukata ta kike so ayi duk zan yi, ke ko jemage zan iya mayar da ita."
"A'a Mallam ba na son a yi ma ta komai kuma kada a canza ma ta halitta ko haukatarwa ballanta kashe wa. Kawai so nake yi ka raba su ya sake ta ta bar gidan kawai nake bukata. Sanan na maye gurbinta a wajensa da iyayen sa da nawa kowa ya kasa magana ka rufe bakin kowa."
Jinjina kai ya yi sanan ya ɗora da cewa.
"Akin akwai wahala idan kika bada haɗin kai komai zai zo da sauƙi."
"Malam kudi ba matsala ta ba ne ka fadi miliyan nawa zan bayar."
Shiru ya yi na wasu sakanni.
"Ba wani kudi zan karɓa a gare ki ba, kawai za ki zo ki bani kanki ne kawai bukata za ta biya."
Kallon rashin Fahimta ta yi ma sa kafin ta ce .
"Ban gane na baka kaina ba!"
"Wato budurcinki shi ne ladan aikin ki."
A zauren ta mike tsaye tana yi ma sa wani kallo, kafin ta mayar da duban ta ga Sady baby, ta ga ba ta damu ba ko mamakin jin kalamansa.
_Makaho_
Yana isa bakin wani daji dake gefen gari, sai ya tsaya cak ya duba agogonsa
"Lokacin ya yi."
Ya cigaba da tafiya.
Bayan wasu mintuna tsohon sansanin ya bayyana a gabansa. Babu hayaniya, babu dariya, babu motsin da aka saba ji.
Ya ɗan ɗaga gira ɗaya yana cewa.
"Shiru ya yi yawa."
Ya taka zuwa gaba. Kwatsam ya ji an ce.
"Tsaya nan!"
Muryar ta fito daga bayansa. Kafin ya juya gabaɗaya wasu mutane uku, suka fito daga gefen wani gini. Wasu biyu kuma suka bayyana daga duhu.
Ya lumshe ido kaɗan
"Wato haka ne."
Wani dogon mutum ya fito daga cikinsu
"Ka wahalar da mu sosai officer."
Makaho ya yi shiru, mutumin ya yi dariya .
"Ka yi tsammanin ba za mu gane ka ba, Makaho mai gyaran takalmi ?"
"Na ɗauka wasan ya yi kyau."
"Ya yi kyau amma baya isa."
Mutanen suka matsa kusa da shi, ya kalli mutanen ɗaya bayan ɗaya.
"Shugabanku yana ina?"
Dogon mutumin ya yi murmushi. Sanan ya ce .
"Har yanzu kana tamabaya?'
"Eh har yanzu."
"Nan take wani daga hagu ya yi kokarin cafke shi, sai ya kauce gefe mutumin ya faɗi ƙasa da karfi.
"Ku kama shi"
Gabaɗaya suka yo kan makaho, ya ja baya cikin sauri ya kauce wa na farko ya ture na biyun ya fadi ƙasa. Wani ya yi ma sa dirar mikiya daga baya amma sai ya juya akan lokaci. Hayaniya ta cika wurin, dogon mutumin ya zaro bindiga .
"Ya isa!"
Kowa ya yi shiruz ya daga bindigar zuwa kan Makaho.
"Ka gama."
Makaho ya kalle shi ba tare de tsoro ba.
"Mutumin da ya tona ma ni asiri yana nan."
Fuskar dogon mutumin ya sauya na ɗan lokaci ƙafan . Makaho ya yi murmushi. Dogon mutumin ya matse haƙora.
"Kama shi!"
Sai dai kafin wani ya motsa ƙarar tayoyi sun fara tashi daga wajen sansanin. Kowa ya fara waige-waige, sai hasken fitilun motoci ya zagaye wajen.
Dogon mutumin ya zaro ido yana kallon makaho ya ce .
"Me ka yi ?"
Jalaluddeen ya gyara tsayuwarsa yana cewa.
"Na zo ni kaɗai, amma ban ce ni kaɗai na shirya ba."
Dogon mutumin ya kalli hasken da ke kara kusantowa, sanann ya kalli Makaho.
"Ka yaudara mu."
Makaho ya ɗan karkatar da kai .
"Ba ni kaɗai na iya yaudara ba"
"Ku tarwatse!"
Dogon mutumin ya faɗa da karfi. Nan take mutanen suka fara gudu ta ko ina . Wasu suka nufi bayan gine-ginen sansaninsu, wasu kuma suka ruga zuwa cikin dajin dake bayan sansaninsu.
Makaho ya lura da wani mutum dake sanye da baƙar hula, yana sulalewa zuwa wata karamar ƙofa dake bayan wani ɗaki.
Zuciyarsa ta buga ya ce .
"Shi ne."
Tun kafin ya fara gudu mutumin ya ɓace ta ƙofar. Makaho ya kutsa tsakanin mutanen da suka rage a gabansa.
Ka tsaya!"
Mutumin bai waigo ba, ya shiga cikin wani dogon korido mai duhu, makaho ya bi bayansa. Ba abun da ake ji sai sautin amon takalminsu. Da ya fito daga ɗaya gefen koridon sai ya hangi mutumin a tsaye bakin wata ƙofa.
A karon farko mutumin ya waiwayo, fuskarsa ta bayyana karkashin hasken wata.
Makaho ya tsaya cak.
"Kai..."
Mutumin ya yi murmushi
"Na yi mamakin tsawon lokacin da ka ɗauka kafin ka gane."
"Kai ne shugaban?"
"Ka yi tunanin zan zauna ina aika mutane ne kawai?"
Makaho ya matso gaba tare de cewa.
"An daɗe ana nemanka."
"Kuma an dade ina kallonka."
Shugaban ya bude kofar dake bayansa yana cewa .
"Ka san mene ne kuskurenka mafi girma?"
Makaho bai ce komai ba.
"Ka yi zaton kai kadai ne ka iya farauta?"
Ya shiga cikin ɗakin, Makaho ya bi shi, yana shiga dai ya tsaya cak. Babu komai a ɗakin sai teburi ɗaya a tsakiya. Akan teburin kuwa akwai hotuna .
Hotunan makaho ne lokacin da yake gyaran takalmi, har ma da lokacin da yake shiga Masallaci, jikinsa ya ɗan yi sanyi .
Shugaban ya tsaya a ɗaya gefen ɗakin yana cewa.
"Na san kai tun ranar da ka shigo garin nan."
Idanun makaho suka ƙanƙance.
"To me ya sa ba ka kashe ni ba?"
Murmushin Alhaji Daula ya yi tare da cewa .
"Saboda ina so in ga iyakar abin da za ka iya gano wa.
Shiru ya mamaye ɗakin na wasu daƙiƙu, sai kuma Daula ya yi magana a hankali .
"Yanzu kuma ina so in ga yadda za ka fita daga wurin nan."
Kafin makaho ya yi magana sai ƙarar kulle kofa ya ji daga bayansa
"Klik."
Ya juya da sauri ƙofar ta rufe, da ya sake waiwayo wa gaba shugaban ya ɓace.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065357995

Page7️⃣8️⃣
Ya juya da sauri da sauri kofar rufe, da ya sake waiwayowa gaba shugaban ya ɓace.
Makaho ya juya da sauri zuwa ƙofar, ya ja makullinta ƙofar ta ƙi buɗewa. Ya sake gwadawa shiru. Sautin wata murya ta fito daga cikin lasifika ta fito da bai lura da lasfikan ba a cikin dakin.
"Na ce ma ka ina son in ga yadda za ka fita."
Jalaluddeen ya ɗaga kansa.
"Ka fi son magana fiye da bayyana."
Sautin dariyar Daula ta cika ɗakin , kafin ya bude baki tana cewa.
"Har yanzu kana da ƙwarin guiwa kenan."
Muryar ta katse shiru ya mamaye ɗakin, Makaho ya juya yana kallon ɗakin.
Teburi, hotuna, katanga huɗu, babu window. Ya matsa kusa da Teburin, ya ɗaga ɗaya daga cikin hotunan a bayan hoton akwai wani karamin rubutu .
"Ka daina kallon abun da ke gabanka."
Ya ɗaga gira ɗaya, sanann ya ɗauki wani hoton ya juya bayan hoton, rubutun iri ɗaya ne, na uku ma haka, na huɗu ma haka . Duk suna ɗauke da saƙo ɗaya. Ya sauke hoton a hankali .
"Daina kallon abun da ke gabanka."
Idanunsa suka zagaye ɗakin, sai ya ɗaga kansa sama, a can kusa da rufin ɗakin ya hango wata ƙaramar buɗaɗɗiyar mashiga da iska ke ratsawa. Ya yi murmushi kaɗan.
"To kenan."
Ya jawo tebur zuwa ƙarƙashinsa, ya taka kujerar dake gefen teburin sannan ya mike, har yanzu bai kai ba. Ya yi tsalle ya kama gefen mashigar, ƙarfen ya yi ƙara, ya matse haƙora ya ja jikinsa sama. Da ƙyar ya kutsa cikin mashigar, ƙurar dake ciki tasa ya yi tari Ya cigaba da jan jikinsa s hankali, mashigar ta yi duhu sosai. Bayan wasu mintuna ya fara jin iska mai ƙarfi, alamar yana kusa da fita, ya cigaba can gana ya hango ɗan haske, da ya isa ƙarshenta ya cire wani tsohon murfi. Murfin ya faɗi kasa da ƙarfi, ya leƙa. Yana sah'man wani tsohon sito ne a bayan sansanin, ya sauko a hankali da ƙafafunsa suka taɓa ƙasa. Sai ya ji murya a bayansa.
"Na san za ka samu hanyar fita."
Ya juya nan take, ba kowa ba ne face Daula yana tsaye cikin duhu hannayensa a cikin aljihun wandonsa. Kamar dai tun farko yana jiransa a wajen.
"Ka san me ya sa na bari ka fito? Saboda na gama abun da nake yi .
Makaho ya kalle shi ba tare da ya motsa ba.
Ƙarar motoci suka sake ji a kusa da su, murmushin dake kan fuskar Daula ya ɗauke, ya karkatar da kai yana sauraro. Sai ihu suka ji daga cikin sansanin .
"Sun shigo wanann hanyar ku gudu!"
Nan take hayaniya ta kaure mutanen Daula suka fara fita daga gine-ginen sansanin suna guje-guje.
Daula ya zubawa Makaho idanun yana kallon sa da mamaki.
"Kai ne ka shirya wanan tun farko?"
Murmushi Makaho ya yi ya ce .
"Ka ce kana kallona tun farko, amma ka manta cewa ni ma ina kallon ka?"
Tashin hankali ya bayyana a idanun Daula, ya juya zai bar wajen da sauri, amma kafin ya yi wani yunƙuri hasken fitilu sun haske shi.
Muryoyi suka fara bada umarni daga ko ina, mutanen kungiyar suka rikice, wasu suka jefar da makamansu suka gudu, wasu suka ɓuya.
A cikin wannan rikicin ne Daula ya amfani da wanan damar ya ɓace cikin duhu. Makaho ya yi ƙoƙarin bin bayansa ya kuma fasa ya tsaya ya kalli sansanin, ya kalli mutanen da ake cafkewa, ya kalli motocin da suke wajen sanan ya sauke numfashi .
Ya juya ya nufi wajan fitilu, wani jami'in ya ƙaraso wajen sa da sauri.
"Sir! Kana lafiya?"
Makaho ya share ƙurar dake jikinsa.
"Ina lafiya."
"Sir mun yi tunanin mun makara."
"A'a."
Ya faɗa yana sake duban duhun da shugaban kungiyar wato Daula ya ɓace.
"Kun zo akan lokaci ."
Jam'in ya kalli inda yake kallo sanan ya ce .
"Sir shugaban fa?"
Shiru ya ɗan ratsa tsakaninsu kafin makaho ya ce.
"Ya tsere."
Jam'in ya ce."
"Za mu bi shi?"
Murmushi Makaho ya yi murmushin dake nuna cewa ya san wani abu.
"Zai dawo."
"Sir ta ya ka san cewa zai dawo?"
"Zaro wata takarda ya yi daga cikin aljihunsa. Takardar da ya ɗauko daga ɗakin Daula. A takardar akwai adireshi ɗaya da kwanan wata, ya miƙawa jami'in.
"Saboda yanzu mun san in da zai kasance nan gaba."
Ya fara tafiya zuwa wajan motocin.
A bayansa kuwa sansanin da ya kwashe watanni yana bincike a kansa yana rushewa a hankali. Duk da ya san wanan ba karshen yaƙin ba ne farko ne.
*ABUJA*
_Yasmeen_
Kwance take a katafaren gadonta na alfarma tana barcin ta hankali kwance. Tana sanye da rigar barci wacce ta tsaya daidai guiwarta.
Wayarta ce ta yi ƙara wanda hakan ya sa ta ɗan yamutse fuska ta kai hannu ta hanyar karɓen wayar da katse kiran wayar ta hanyar danna power din wayarta.
Sai da aka kira sau uku sannan ta ɗauki wayar da sauran barci a idanunta.
"Hello waye yake damuna ina barci da safiyar nan ."
Ta cikin wayar ta ji Muryar Aliyu yana cewa.
"Ba shakka Hajjaju ki sha barci lafiya lau abun ki, kin dai san jirgi baya jira, kin saka na siya ma ki ticket daura mintinan talatin jirgi ya tashi kina barci."
A zabure ta tashi zaune tana cewa.
"Subhanallah ai lokacin ya kusa ban sani ba, na gode Aliyu."
Daga haka ta katse kiran wayar ta diro daga kan gadon cikin hanzari.
Bathroom ta faɗa don yin wanka, bayan ta saka hular wanka ta sakarwa kanta shower 🚿
Tana wanka tana waƙa cikin nishaɗi.
Che che kule...
Har ta gama wanka ta fito tana waƙa abun ta hankali kwance.
"Nan da nan ta shafa man shafawarta da turare , har ta ɗsuko wasu riga da siket na leshi ta mayar tana cewa .
"Yanzu yana gani na da wanan kayan zai fara masifa wai sun matse ni ba na son shigar mutunci. Wallahi Yaya Jalal ɗan yawa ne, ba don son da nake yi ma ka ba ai da tuni na rabu da kai na kama ɗaya daga cikin masoyans.,"
Doguwar rigar material ta daka ɗin kin bubu ne sai ta ɗauki karamin mayafi da ya shiga da kalar material ɗin.
Ta ɗauki handbag ɗin ta mai ɗan girma ta daka kayan sawari ta kala ɗaya. Ta ɗauki abun da ta san za ta buƙata.
Ta saka takalmi ta fito da sauri kamar wacce aka jefo ta faɗo falon.
Ummee dake waya da ƙawata ta cire wayar daga kunne ta ce .
"Ina zuwa naka kike sauri?'
"Ummi zan je gidan Mom ce Saddiƙa na waje tana jira na, kuma can zan kwana."
"Okay ki gaishe ta."
Daga nan ta cigaba da wayarta da ƙawarta hankali kwance.
Yasmeen na fita harbar gidan direba ya taso da sauri ganin alamar fita za ta yi kuma sauri take yi.
"Hajiya ina kwana."
Ya ɗan durƙusa yana gaishe ta.Banza da shi ta yi ba ta ko kalle shi ba ballantana ta amsa.
Tana buɗe gate ɗin gidan ta ga Aliyu na jiranta.
Bude gaban motar kawai ta yi ta shiga ta zauna gefensa.
"Yanzu ke da ban kira ki ba da sai dai ki yi wani bikin jirgin , kin san kina da tafiya kika kwanta kina barcin asara."
Wani kallo ta yi ma sa kafin ta ce.
"Wani barcin asara?'
",Eh ma na su barcin bayan sallar asuba barcin asara ne."
"Ba zan biye maka ba saboda ina cikin farin ciki zan je na ga masoyina Yaya Jalal nawa na kaina, da ba don wanan tsinannen aikin nasa ba ai da yanzu ina ƙarƙashin igiyar aurensa.
Ya san za ki je wajen sa?'
"Bai sani ba surprise zan yi ma sa."
"Umme ta sani?"
"Ba ta sani ba na yi ma ta ƙaryar zan je gidan su Mom na kwana ne."
"Allah ya kyauta."
Ba ta tanka shi ba har suka karasa Airport. Godiya ta yi ?masa sannan ta fita da sauri ta shiga ciki.
Isar ta da mintuna biyar bakwai jirgin nasu ya tashi.
_Ma'eesha_
Ba ta yi isasshen barci ba kasancewar mijinta ya fita da niyyar kai waya bai dawo ba.
Tsoron ta kada a cutar da shi kamar ganin shi makaho ne ba gani yake yi ba.
Kasa barci ta yi karshe dai ta fita ta ɗauro alwala ta zo ta fara sallar nafilfili tana yi ma sa addu'ar Allah ya kare shi a duk in da yake .
Don ta kira wayarsa da ta siya ma sa ta ji wayar a gida. Wato bai je da wayar ba ya bar ta a gida.
Har aka yi sallar asuba ta tashi ta gabatar da sallar asuba, sanann ta zauna zaman yin azkar din safiya.
_Makaho_
Ko da suka shigo cikin gari ana kiraye-korayen sallar asuba. Har bakin layin unguwar ya ce su kai shi, suna zuwa ya ce kada su shiga ciki su bar shi nan kawai.
Suka bi umarnin sa suka tsaya ya sauka suka yi ma sa sallama cikin girmamawa.
Ba kowa a farkon layin kasancewar asuba ce yanzu duk wanda ya fito daga gidansa masallaci yake shiga.
Ganin ana shirin tayar da sahu ya sa ya samu ruwa a masallaci ya yi alwala ya yi sallah.
Bayan an isar ne ya yi addu'a sanan ya fice, yau bai tsaya jiran sai gari ya waye sanan ya tafi gida ba. Da sauran duhu ya bar masallacin.
Da sallama ya tura ƙofar fale-falen ya shiga cikin gidan.
Tana jin sallamarsa ta fito da hanzari tana cewa.
"Kana lafiya dai ko? Ba abun da ya same ka? Ya aka yi ka daɗe daga kai waya? Su ne suka tsayar da kai?"
Haka ta dinga jera ma sa tambayoyi ya ma rasa me zai ce ma ta .
"Ina son zan yi wanka.'
Ya faɗa kamar wanda baya son yin magana.
"To akwai ruwan zafi bari na zuba ma ka "
Da hanzari ta juya jikinta har rawa yake yi tana kokarin sa ma sa ruwan zafi.
Da kallon tausayi yake bin ta ta cikin bakin glass dake idanunsa.
Girgiza kai ya yi yana maganar zuci.
'Wahalar ki ta kusa ƙarewa in sha Allah, za ki yi farin ciki a rayuwarki.'
Sai da ta kai ma sa ruwan sannan ta dawo ta ɗauki sabukun wankansa ta kai ma sa.
Ɗakin ya shiga ya ɗauki jallabiya a cikin kayansa ya nufi banɗaki don yin wankan.
Ita kuma ta fara kokarin neman abun da za ta haɗa ma su na breakfast.
Sai da ya gama wanka ya fito tana ganinsa ta karasa gabansa da sauri Sannan ta yi ma sa jagora zuwa cikin ɗaki . Ita kuma ta koma ta cigaba da aikinta.
Zuwa karfe takwas ta gama komai, ko fa ta shiga dakin ta same shi ya kwanta bayan ya sauya kayan jikinsa, yana dafe da kansa ya ɗora hannu kamar wanda kansa ke ciwo.
Fita wajen ta yi ba tare da ta tayar da shi ba ta cigaba da aikin gida, har kayan da ya dawo da su ta wanke, duk da ta ji wata takarda a aljihun wandonsa sai ta cire ba tare da ta warware takardar ba, ta je ta ajiye ma sa a saman wajen kayansa.
Ta cigaba da aikinta. Har ta gama ta yi wanka ta shirya cikin doguwar rigar atamfa, ɗinkin stone work ya karɓe ta ya zauna ma ta ɗagwas a jiki.
Turarenta ta shafa wanda ta siyo lokacin da ya ce ta siyo kayan abinci da kudin tallafin da aka ba su.
Don haka ta siyo turare kasancewar nata ya ƙare wanda ta zo da shi daga gidan Mahaifinta, sai dai wanda ta siya bai kamata bwancan tsada ba. Ta yi la'akari da matsayin ta na yanzu da na baya ba daya ba ne.
Tana gama ɗaura ɗankwali ya bude idanunsa a hankali tare da sauke su a kanta.
Ba ta ma san ya bude idsnu ba ta cigaba da shirinta, ta saka ɗan kunne da sarƙa har da warwaro.
Kansa yana ɗan yi ma sa ciwo don haka sai ya sake lumshe yana cike lips ga jikinsa da yake jin yana na ma sa ciwo.
"Sorry, ba ka da lafiya ne?"
Bude idanunsa ya yi sakamakon jin tambayar da ta yi ma sa.
"Lafiya ta kalau."
Ya yi maganar yana tashi tare da jingine bayansa da bangon ɗakin. Kafin ya mike yana cewa .
"Zan samu ruwa mai zafi ba yi wanka da shi?"
"Eh na saka ma ka na san yanzu ma ya yi zafi."
Ta yi magana tana tashi zuwa waja, shi ma tashi ya yi ya fita zuwa banɗaki.
"Wanka ya yi da ruwan zafin da ta kai ma sa ko da ta fito ta jera abun breakfast a tsakiyar ɗakin.
Da sauri ta tashi tana rike sandarsa tana cewa .
"Ka yi a hankali na ajiye abinci kafa ka ci karo da shi ka zubar."
Murmushi ya yi a ƙasan ransa ya raɓa yana bin gefe.
Fita ta yi daga cikin ɗakin sai da ta daidaici ya gama shirya wa sannan ta shigo da sallama.
Yana tsaye yana saka boturan gaban rigarsa.
"Bisimillah."
Ta janyo hannunsa zuwa gaban abincin sanan ta ce ya zauna.
Zama ya yi ta zuba ma sa kunun gyada da ƙosai wanda ta yi ma su shi a matsayin abincin kalaci.
Bayan sun gama yin breakfast ne ya yi hamdala yana cewa .
"Na gode sosai Allah ya yi ma ki albarka mar'atussaliha."
"Amin Mijina."
Fita ta yi ta kwshe kayan da zummar wankewa. Sai wsyarsa dake cikin aljihun sa ya yi haske.
Kasancewar wayar a silent take, gudun kada Ma'eesha ta kula da wayar ta fara zarginsa.
Messages ne ya yi reply ya mayar ta ajiye.
Bayan awa daya ya fito daga gidan, bayan ta ce ma ta zai je wajen sana'ar sa ne na gyaran takami.
A kan hanya yana tafiya kamar an ce ya ciro wayar, sai ya ciro daidai lokacin da kiran Yasmeen ke shigowa wayarsa.
Ɗaga wa ya yi tare da cewa.
"Hello."
Murmushi mai sauti ta yi .
"Surprise!"
"For what?"
"Na biyo ka garin da kake yanzu na sauka daga airport ka zo ka ɗauke ni?"
Ta faɗa cikin shauƙi.
"Ke wai kin yi hauka ne?"
"Wallahi Yaya Jalal da gaske nake yi, na zo na gan ka ne ."
"Yasmeen kin san me kike faɗa kuwa?"
"Wallahi na sani kawai na yi missing naka ne shi ne na zo na gan ka kai ma ka ganni."
Dafe goshin sa ya yi cike da takaici.
"To yanzu da kika biyo ni me zan yi ma ki.'
"Ganina za ka yi ma na, ga ni q nan fa ban san kowa ba kuma ban san garin ba ka zo don Allah."
Ta yi magana kamar za ta yi kuka.
"Ki juya ki koka in da kika fito."
Kuka ta saka ma sa wanda hakan ya sa ya ji wani iri a jikinsa, don baya son jin kukan mace.
"To yanzu zan kira wani na ba shi lambar ki zai zo ya ɗauke ki, zai kai ki hotel ɗin da nake kafin na zo."
Ya yi magana ransa a ɓace ya kashe kiran wayar. Lambar yaronsa ya kira ya sanar da shi in da take sanan ya tura ma sa lambar wayarta. Ya kuma sanar ya je reception din hotel ɗin ya karbi key ya ba Yasmeen zai kira su ya sanar da su zuwanta.
Ya kira hotel ɗin ya sanar da su idan yaron sa ya zo da Yasmeen a ba ta key din ɗakinsa ta shiga.
"Lallai yarinyar nan sai na koya ma ta hankali, don ba ta da lissafi sam a rayuwarta, duk abun da ya zo kanta za ta aikata ne ba tare da yin tunani ba."

Page7️⃣9️⃣
Lallai yarinyar nan sai na koya ma ta hankali, don ba ta da lissafi sam a rayuwarta, duk abun da ya zo kanta za ta aikata ne ba tare da yin tunani ba."
Fasa zuwa wajan sana'ar sa da ya saba zama ya yi saboda dama wajen na kusa da gidan Daula ne, yana zama wajen ne yana kula da shige da ficen Daula da mutanen sa.
"Yanzu sun riga sun san waye shi har suna farautar rayuwarsa, cigaba da zama a wajan hatsari ne ga rayuwarsa. Don haka ya kira mai nape ɗin sa, kasancewar cikin jama'a yake, idan ya ce zai kira yaronsa ya zo da mota ya dauke shi za'a fara zarginsa.
Yana nan in da yake ya kira mai nape din ta sanar da shi in da yake. Ba komawa mai nape ɗin yazo da sauri saboda ya san yau ranar sa'a ce a gare shi. Don duk ranar da ya kira shi hotel kawai yake kai sa ya jira shi ko a awanni zai kwashe bai fito ba yana zaman jiransa. Sai dai idan ya tashi biyansa ranar zai ba shi kuɗaɗen da zai kai sati ɗaya kafin ya tara shi.
Yana zuwa makaho ya shiga cikin keken bayan ta fara shigar da sandar jagoransa da kayan gyaran takalminsa.
"Yallaɓai ina wuni."
"Lafiya lau Alhamdulillah."
"Ya aikin ya ƙoƙari?"
"Alhamdulillah."
"Ma sha Allah, ai tun da na ga kiran ka na ce yau ranar sa'a ce a gare ni."
Bai tanka ma sa ba idanunsa na kan tayi yana tunanin wani abun daban.
*KATSINA*
Wani babban gida ne na alfarma, kallo ɗaya za ka yi wa gidan ka san cewa an narka dukiya wajen yin sa. Girman gidan ya kusan kai wani unguwa guda.
Idan ka shiga cikin gidan kamar Estate ne, saboda gine-ginen dake ciki zai tabbatar ma ka da cewa gidan gidan iyali ne. Don duka gidajen da dake wajen duka iri ɗaya ne, komai hatta fenti da tsarin gidajen iri ɗaya ne. Gine-ginen guda huɗu ne komai Iri ɗaya ne, sai dai akwai wani babba wanda ya fi sauran girma, amma tsarin ɗaya ne.
Alhaji Sulaiman Musa shi ne asalin mamallakin wajan, yana da mata biyu Hajiya Amina da Hajiya Maryam. Sai mahaifiyarsa wato Dada da take zaune tare da su, duk da gidan na ta na wajan amma ba ta zama ta tare tare de babban Ɗanta. Don ta tsufa sosai sai rigima.
Yara uku Dada ta haifa namiji ɗaya mata biyu, mijinta ya rasu ya bar ma su tarin dukiya, duk da cewar kafin ya rasu ya raba wa ƴaƴansa kashi mafi tsoka na dukiyarsa. Don hatta jaririyar da aka sace yau shekaru arba'in kenanƊa na farko shi ne Alhaji Sulaiman Sauƙi, sai kuma sai ƙanwarsa Dr Fatima da take aure a Abuja, sai kuma ƴar autar su wacce aka sace ta tun tana jaririya. Yau shekaru talatin da biyar kenan
Alhaji Sulaiman baban ɗansu wanda yake da mata guda biyu Hajiya Safiya da Hajiya Saratu. Yana da yara guda biyar. Uwar gidansa Hajiya Safiya ta haifa ma sa uku duka maza ne. Barrister Haidar shi ne babba sai Captain Kabeer wanda shi soja ne sai Mujahid wanda yake kasuwanci yana kula da harkokin mahaifinsu ita kuma Amaryarsa Hajiya Saratu ta haifa ma sa mata biyu. Lubna, Jamila. Su kuma suna karatu a University .
Sai kuma Dr Fatima tana can a Abuja tana aure tare da iyalanta ita ma. Ta haifi yara guda uku. Jalaluddeen, Sadik da Saddiƙa.
Sautin hayaniya ne ya kaure a ƙofar gate ɗin daga waje, wanda ana jin hayaniya har a cikin gidajen su. Alhaji Sulaiman Sauƙi ya duba CCTV camera ya hango abun da ke faruwa wani tsoho ne, wanda ya yi ma sa kama da wanda ya sani amma ya mance ina ya san mutumin.
Hayaniya ce ta kaure kasancewar security din da ke gadin gate ɗin har mutane uku ne.
Dada ce ta fito tana salati tana kiran Sulaiman ina kake me yake faruwa kar dai ace hari aka kawo ma na mu shiga uku. Wayyo Allah ga shi Soja baya nan a gidan yau ya tafi wani gari waye zai cece mu?"
Tana maganar tana kokarin shiga karkashin kujera. Sauti m dariyar da ta ji Barrister Haidar na yi ne ya sa ta leƙo tana kallon su. Alhaji na gaba tana bin sa a baya yana yi wa Dada dariya.
"Kai ka shiga hankalin ka mahaifiyar tawa ce kake yi wa dariyar shaƙiyanci ?"
"Sorry Dad tuba nake yi ba zan sake ba."
Ganin Ɗan nata da jikanta sun fita ne ya da tsoron ta ya rayu. Hajiya Safiya suka fito tare da Hajiya Saratu su ma suka rufawa mijin nasu baya.
"Me yake faruwa ne?"
Cewar Alhaji yana tambayar ɗaya security din wanda shi yana daga cikin gidan ne.
"Alhaji wani tsoho ne kamar mahaukaci wai dole sai ya shigo cikin gidan nan "
Ɗaya daga cikin security ne yake sanar da, maigidan.
Dubansa ya maida kan wanan abun kafin ya sake cewa .
"Bawan Allah lafiya kuwa?'
Ya yi maganar yana kallon yanda goshin tsohon nan ya kumbura ya ya ja kalmar ba na shi na ba."
"Tashi ka shiga ciki sai mu yi magana ko?"
To na gode Alhaji Allah ya kara arziki.,
Gabaɗaya iyalan gidan suka hadu a babban gidan.
"
Shiru kowa ya yi yana jiran jiran jin abun da zai ce..
"Hajiya ba ki gane ni ba?"
Sai a lokacin Da ta ce
"Maude kai ne?"
Ta yi magana cike da mamaki, ba ta gane shi ba saboda shekaru sun ja.
"Eh ni ne Hajiya."
"Ban ga mijinki ba Alhaji yana raye kuwa?"
"Ya riga mu gidan gaskiya."
"Allah ya jikansa."
Gabaɗaya falon aka amsa da Amin.
"Hajiya ina yaranki Sulaiman da Fatima?"
"Ga Sulaiman nan zaune Nam duka iyalansa ne, Fatima na aure a Abuja."
"Ina ƙanwar Fatima da kika haifa?"
Shiru ne ya biyo baya kafin ya ce .
"Kodayake ba mai wanan amsar sai ni da na yi tambayar duk da na zo a ƙurarren lokaci."
Ɗaya daga cikin. Masu aikin ne ta kawo ma sa abun sha da abinci a babansa.
"Ban gane me kike nufi da ka fi kowa sani ba."
"Tabbas na zo ne na sauke nauyin da ke kaina kuma na roƙi gafarar waɗan da na zalinta ko ba su yafe ma ni ba zan samu sassauci a zuciyata.
"Me ka sani game da sace ma ni ƴa da aka yi shekaru talatin da biyar da suka wuce?"
"Hajiya ki gafarce ni domin ni ne na sace maku jaririya shekarau talatin da biyar bayan, na kai ta gidan marayun a garin kaduna da hannuna na fita da ita daga ɗakinki. Sai dai ba da son raina na yi haka ba dole ce ta saka na aikata haka.?"
"What?!"
Cewar Captain Kabir da yake shigowa falon mahaifinsa sanye da kakinsa na sojoji a jikinsa. Ganin fuskarsa ya tsorata maude.
Dad ya lura da mahaifiyarsa ta sume a wajen ba ta motsi.
"Dada?!"
Ya karasa kujerar da take zaune cikin tashin hankali. Kowa ya yi kanta ban da Captain Kabir dake jifan maude da mugun kallon da ya kusa saka shi fitsari a wando.
_Yasmeen_
Bayan Makaho ya tura yaronsa ya ɗauko ta kai tsaye hotel ɗin da ya kama ya kai ta.
Har reception suka karasa ya yi ma su bayanin cewa Jalaluddeen ne ya ce ya kawo ta
Kasancewar shi ma ya kira su daga can ya sanar da su a ba su key.
Karba yaron nasa ya yi ya kai ta har ƙofar ɗakin ya mika ma ta key ya bar wajan.
Bude ƙofar ta yi ta shiga tana karewa ɗakin kallo.
Murmushi ta yi tana cewa.
"Yauwa Ya Jalal yanzu na ɗan samu rabin nutsuwa kafin ka ƙaraso.
Wayarta ta ɗauka ta kira wayar da sai dai har ta katse bai ɗauka ba har sau uku bai ɗaga ba. Karshe ma ta ji wayar a kashe.
"Na san dai dole za ka zo ka same ni nan."
Ta yi maganar cike da farin ciki na zuwa kusa da shi.
Bakin gadonsa ta zauna tana tunani kafin ta tashi ta shiga bathroom don yin wanka. Wanka ta yi sa sabulunsa mai ƙamshi wanda ta jima tana wanka tana jin ina ma a ce an yi auren su tare suke yin wanka.
Bayan ta gama ta fito daga toilet ɗaure da towel.tana rera waka a bakinta. Gabatanta na ya fadi sakamakon ganinsa tashe bakin ƙofar ɗakin yana aika ma ta da wani mugun kallo.
*Ku yi hakuri da wanan ba na da caji.*🙏🏻

Page8️⃣0️⃣
Bayan ta gama ta fito daga toilet ɗaure da towel tana rera waƙa a bakinta. Gabanta ne ya faɗi sakamakon ganinsa tsaye a bakin ƙofar ɗakin yana aika ma ta da wani mugun kallo .
Sunkuyar da kanta ƙasa ta yi tana tura baki tare da zancen zuci.
'Mutimin nan fa ɗan yaw ne yanzu zai iya wulaƙanta ni, na yi dogon tafiya saboda shi amma yana zuwa ya rasa me zai tarbe ni da shi sai mugun kallo da harara."
"Ki saka kaya ina zuwa nan da mintuna biyar.
Yana fadar haka ya fita daga bedroom ɗin ya koma ya koma falo ya zauna.
Zama ya yi kan kkujera yana nazarin aikin da ke gabansa.
Yana nan zaune sai ya daidaici ta gama, don haka dai ya mike ya same ta tsaye daga gani tana cikin fargaba ne.
"Me kika zo yi?"
"Na zo na ganka saboda na yi missing naka ko barci me dadi bana iya yi shi ne na zo na kanka?"
"Ummee ta san kin zo?"
"Ba wanda ya sani ce m ta na yi zan je gidan Mom can zan kwana, saboda na san ba za ta hana..."
"Okay wannan shi ne dalilin da ya da kiks zo ba tare da kin yi tunani ba ko?'
"Wallahi na yi tunani sosai da sosai Ya...."
Za ki rufe ma Ni baki ko sai na tattaka ki a wajan nan wawuyar banza kawai."
Da sauri ta kalle shi kin kalmar da ya kira ta da shi na wawuyar banza kawai . Ganin yadda ransa ke ɓace ne ya da jikinta yin sanyi sosai. Ita s gurɓataccen tunanin ta zai ji dadin zuwan da ta yi ma sa ne, amma dai ga shi ta ga ransa ne ya ɓaci.
Kuka take kokarin yi amma ya daka ma ta tsawa tare da yi ma ta gargaɗin idan ta yi kuka dai ya ma ta dukan da kuka ma sai ya gagare ta.
Tana ji tana gani ta haɗiye kukanta tare da nadamar zuwa wajensa da ta yi.
Ya ma rasa me zai ce ma ta ko me zai yi ma ta.
"Kin yi magana da wani ne daga gida a waya bayan kin sauka?'
"Na kashe watoyina duka ba wanda zai same ni."
*ABUJA*
_Saddiƙa_
Tsms zaune a falo ita da Mom wacce dawowar ta kenan daga asibiti.
"Mom next week ne wai bikin wata ƙawar mu ban sani ba sai yau, wai auren haɗi ne za'ayi ma ta ."
"Ayyah to Allah ya sa na yi a sa'a."
"Amin ya Allah. Bari na kira Yasmeen na sanar da ita ko tekun ta zai samu yi ma na ɗinkin ankon bikin."
Ta yi maganar tana lalubo lambar wayar Yasmeen.
Tama kira aka sanar da ita wayar a kashe.
"Mom kin ga wayar a kashe yake, bari na kira lambar Wayar Ummee na ce ta haɗa ni da Yasmeen."
Ta lalubo lambar wayar Ummee ta danna ma ta kira, bugu biyi Ummee ta ɗauka .
"Hello Saddiƙa."
"Ina wuni Ummee."
"Lafiya lau ya Mom ɗin taku take?"
"Tana lafiya lau."
"To ma sha Allah."
"Ummee dama ina son magana da Yasmeen ne na kira wayarta ba ta ɗaga ba."
"Ban gane ba, shin ba ke ce kika zo kika ɗauke ta kuka tafi gidan ku ba ta ce za ta kwana can?"
"Ummee duk yau ba mu yi waya da ita ba wallahi?"
Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un. To ina ta je har da ɗaukar kaya?"
Ta yi maganar tana Katse kiran wayar, lambar wayar Yasmeen ta kira switch off.
Hankalinta ya tashi sosai ba kadan ba. Kusan duk lambar wayarta ta kira bai shiga ba. Daidai lokacin Abbi ya shigo gidan.
Ganin yanayin ta ya sa ya tambaye ta lafiya.
"Wallahi Yasmeen ce ta ce za ta je gidan Yaya ta kwana, to ban kawo komai ba saboda duk gida ne. Har take sanar da ni Sadduƙa ta zo yana jiran ta a waje da motar Saddiƙan za su tafi. To sai yanzu Saddiƙan ta kira wayata wai tana so ta yi magana da Yasmeen ta kira wayarta ba ta shiga ba. Na tambaya ta ba ta gama gidansu ta ce duk yau ba su yi waya ba ballantana su hadu."
"To ina ta shiga ne?"
"Wallahi ban sani ba."
Nan ta dinga kiran wayar kewayen Yasmeen da ta san za ta iya zuwa gidajen su amma kowa ya ce ba ta je ba.
Abbi ya ce wa Umme ta zo su tafi, da hanzari ta shiga ta ɗauko mayafi a ɗakinta sannan suka fito. A jarabar gidan suka hadu da Yusuf suka sanar da shi abun da ke faruwa.
A motarsa suka tafi har zuwa gidan Alhaji Kabir arzika, wato mahaifin Jalaluddeen Kenan.
Ko da suka shiga cikin falon sun tarar da Dad da Mom suna tattaunawa akan maganar rashin sanin in da Yasmeen take, ga Saddiƙa ta shiga tashin hankali. Ta rakuɓe a gefen sa, sai kuma Sadik da ta tsaya a bayansu.
Da sallama suka shigo ciki, suka amsa ma su fuskar kowannen su ɗauke da damuwa.
Gaisawa aka shiga yi tare da alhinin halin da aka shiga. Tun safe ga shi har yamma ta yi ba labarin in da ta je.
Ummee ta kalli Yayan nata ta ce.
"Yaya ban san inda za mu samo ta ba?"
"Kin kira ƴan uwanki kin tambaye su?"
"Yaya ba za ta je can ba, don ba wani son shiga mutane take yi ba, ba taɓa zuwa dan ra'ayin kanta ba, duk ranar da ta je to ni ce na saka ta dole. "
Caraf Saddiƙa ta ce.
"Allah ya sa ba wajan Yaya Jalal ta tafi ba."
Kowa sai da ya kalle ta, kafin Sadiƙ ya ce.
"Kin yi hauka ne? Me zai saka ta je wajan sa?"
"A duk lokacin da muke fira da da ita tana yawan cewa ji take yi kamar ta shirya ta je garin da yake ta same shi. Ko kuma ta ce wai kamar ta bude ido ta ga an kai ta gidansa matsayin matarsa."
"Bari na kira shi a waya."
Cewar Sadik yana fito da wayarsa daga cikin aljihunsa.
*Kaduna*
Cikin kuka da sangarta take magana.
"Yaya dama na faɗa ma ka ba so na kake yi ba ni ce nake son ka, amma ka ce kana so na kai ma, ko sau daya ba ka taba nuna mun kana so na ba, kamar dai dole aka yi ma ka ba son ranka ba. Tun yaushe na iso garin nan da safe na iso amma sai yamman nan ka zo wajena."
Kallon ta ya yi na wasu sakanni yadda take kuka sanan ya kalli abincin da aka kawo ma ta daga hotel ɗin wanda ko taba shi ba ta yi ba.
Zai yi magana ya ji wayar da na vibrating ya ciro ya duba. Sadik ne ke kiransa a waya, ya ɗaga wayar ya ce.
"Hello Sadik ya aka yi?"
"Yaya wai Yasmeen ta zo wajenka ne?"
Sai da ya ɗauki sakanni kafin ya ce amsa a taƙaice.
"Eh."
Salatin da Ummee ta yi ne ya sauka a cikin kunnen Jalaluddeen.
Taune lips din sa na ƙasa ya yi yana jin sa wani iri. Dad ne ya yi wa Sadik alamar ya ba shi wayar. Karba ya yi ya kara wayar a kunnensa.
"Jalaluddeen."
"Na'am Dad ina wuni?"
"Lafiya lau ya aiki?"
"Alhamdulillah."
"Ma sha Allah, ka saurare ni da kyau ina fatan kana ji na?"
"Eh ina ji Dad."
"Yanzu a ina kuke ne?"
"Muna hotel a ɗakin da nake zaune."
"To ban yarda Yasmeen ta kwana a hotel ba, yanzu ka ɗauke ta ka kai ta gidan abokina Alhaji Tanko ta kwana a gidan ka kai ta har wajan matarsa, zan yi ma sa waya na sanar da shi zuwan ku kafin da safe ka je ka ɗauke ta ka kai ta airport ta dawo. Ka ba ta wayar zan yi magana da ita ."
Sai da ya saka wayar a handsfree sanan ya miƙa ma ta wayar.
"Hello Dad ina wuni?"
"Yasmeen ina ma ki kallon mai hankali ashe ba haka ba? Ta ya za ki yi tafiya har wani gari baki sanar wa kowa na?"
"Dad idan na faɗa ba barina za'ayi ba shi ya sa kuma na..."
Kunya ya hana ta karasa maganar da take son yi.
"To ki kwantar da hankalinki next week in sha Allah za'a ɗaura ma ku aure, idan ya so duk in da za ki bi shi ba damuwar mu ba ne."
Murmushin jin dadi ta yi yayin da Jalaluddeen ya yi tsinci kansa a wani yanayin da ya kasa gane me yake ji, sai dai jikinsa ya yi matukar sanyi da jin hukuncin da Dad ya yanke.
Miƙa ma sa wayar ta yi tana kallon fuskarsa.
"Kana ji na ko?"
"Eh ina ji Dad."
"Dama kai ne ka kawo uzurin sai ka karasa aikin da kake yi kafin ayi auren ku, kuma wanan aikin naka ban san ranar da za ka kare shi ba, don za ka iya saka kanka wani aiki kamar yadda wani aikin ka gama sannan ka saka kanka na Daula ba mamaki daga nan shi wani za ka shiga. To ko ka gama ko ba ka gama ba in sha Allah ranar juma'a za'a ɗaura auren ka da Yasmeen. Ka tabbatar ka bar garin Kaduna ka halarci bikin ka. Idan ya so bayan bikin ruwanka ne ka kai ta garin da kake ko ka bar ta nan, ya fi ma na kwanciyar hankali da ace tana satar jiki tana zuwa kuna haɗuwa."
"Shi kenan Dad ."
Abin da ya iya cewa kenan sannan sukayi sallama ya kashe wayar.
*KATSINA*
Bayan Dada ta fardaɗo daga sumar da ta yi ne ta kalli wanann mutumin sanann ta kalli kowa ɗaya bayan ɗaya kama daga kan Alhaji, Hajiya Safiya, Hajiya Saratu, Barrister Haidar, Captain Kabeer, sai Mujahid wanda shigowar su kenan shi da Lubna da Jamila .
"Amma me na yi ma ka da ka raba ni da jaririyata wacce ba ta san kanta ba, ka nisanta da mahaifiyarta a lokacin da take buƙatata."
Kuka ta fashe da shi tana tsinewa Maude. Tsohon maigadinsu wanda ya yi ma su gadi shekaru arba'in baya da ya wuce.
"Allah ya ɗebe ma ka albarka la'anannen Allah mai raba ɗa da uwa. Wallahi ba za ka ga annabin rahama ba."
Alhaji Sulaiman ne ya rarrashe ta akan ta ya shiru su saurare shi su ji da abun da ya zo.
Da ƙyar aka iya shawo kanta ta yi shiru tana aika wa Maude da kallon tsana. Wanda shi kuma ya galabaita ruwa yake kallo yana son ya ɗauka robot ruwan ya jiƙa maƙoshinsa amma ya kasa sanda kunya.
Fahimtar hakan ya sa Alhaji Sulaiman cewa ya ɗauki ruwan sanyi ya sha.
Hannunsa har rawa yake yi wajen ɗaukar robar ruwar ya ɓalle marfin ya sha.
Bayan ta ya sha ya numfasa ya ce.
"Haƙika haƙƙin ku ba zai bar ni ba, don Allah Hajiya ku gafarce ni, na so a ce n samu mahaifin jaririyar da na ɗaike shi ma na roƙe shi gafara. Wato na kasance mutum mai son kansa da yawa da kuma son zuciya. Ba komai ne ya saka na aikata hakan ba sai son ganin na cire matata a cikin damuwa
Wato a lokacin da wanan abun ya faru ina yi ma ku gadi tun kafin ki haifi haifi Sulaiman, lokacin da kika haife shi sai na ji kamar a ce ni ma na zama uba. Kasancewar matata ba ta taɓa haihuwa ba. Har kika haifi Fatima lokacin na je Kaduna wajen matata nake sanar da ita kin sake haihuwa. Take ji kamar ita ce ta haihu. Har kuka take yi kan rashin haihuwa hakan muke neman magani amma ba mu dace ba. A duk lokacin da nake kallon yaranki Sulaiman da Fatima suna wasa a gidan nan ji nake kamar na sace su na gudu. Ana cikin wanan halin sai na koma Kaduna dama idan zan yi tafiya nikan turo ma ku wani Ɗan uwa na ne ya zo ya yi ma ku gadi zuwa ranar da zan dawo. Wata rana da dawo bayan na kwashe watanni biyu ina can, ranar da na dawo sai ban ga Ɗan uwana dake gadi a bakin gate ba. Kasancewar na ji an tayar da sallah a masallacin da ke kusa da ku na san ya tafi sallah ne. Don haka na shiga gidan kai tsaye, sai na zagaya ta baya sai nake jin sautin kukan jaririya. Wanda na leƙa ta window a na ga jaririyar kwance kan gado.
Take zuciya ta raya na ɗauke ta na kai wa matata da na baro tana jego amma ba jariri ba ta haife shi da rai ba. Sai kawai na zagaya saboda na san irin lokacin ba kowa gida Alhaji na kasuwa yara suna Makarantar boko. Na shiga na tura ƙofar a hankali, jin saukar ruwa a banɗaki na fahimci wanka kike yi. Na ɗauke ta da sauri na saka cikin wata babbar jaka na cire Safar ƙafarta na saka ma ta a baki gudun kuka ya fito.
Har na fita maigadi bai dawo masallaci ba.
A hanya na haɗu da wata mata na ce ma ta ta taimaka ta biyo ni ta rike jaririyar nan muna sauka a gare ki sai ta juya ta dawo mu je Kaduna zan ba ta ko nawa take so. Na ɗebi kuɗin da ke aljihuna ma su yawa na ba ta. Ta kalli jaririyar ta kalli kudin sai ta amince ta kebe ta muka tafi a matsayin ita ce mai jaririyar .
Sai dai muna sauka a Kaduna ta nemi motar da zai koka Katsina ta shiga ciki.
Na nufi gidana da jaririyar sai dai nuna zuwa na tatar da labarin mutuwar matata. Na shiga tashin hankali sosai. Na rasa yadda zan yi da jaririyar sai na kira abokina dake unguwar mu kuma yana aiki a gidan marayu, sai na mika masa jaririyar na ce ya kai ta gidan marayu ta tashi a can . Don ban isa na koma da ita wajan iyayenta ba . Wanan shi ne Abun da ya faru shekaru arba'in da suka wuce. Yarinyar da ya kamata ta tashi cikin gata da kulawar iyaye amma ta tsinci kanta a gidan marayu. Yarinyar da iyayenta suke taimakawa suke ciyar da bayin Allah ta tashi a inda sai an kawo taimako sanan ta samu.

Page8️⃣1️⃣
"Yarinyar da ya kamata a ce ta tashi cikin gata da kulawar iyaye amma ta tsinci kanta a gidan marayu. Yarinyar da iyayen suke taimakawa suke ciyar da bayin Allah ta tashi a in da sai an kawo taimako sannan ta samu."
Kuka ne yake yi yana tari wanda ko a hanya ka gan shi sai ka tausaya ma sa.
"Daga na kuma sai me ya faru?"
Captain Kabeer ya yi tambayar bayan ya ga tarin ya tsagaita ma sa.
"Eh to nikan tambayi halin da yarinyar take ciki, yana sanar da ni tana cikin kishin lafiya .
Har zuwa lokacin da yarinyar ta cika shekaru goma sha Bakwai, aka yi ma ta aure, hankali na ya tashi da na ji labarin, amma kasancewar na ji an ce shi wanda ya aure ta mahaifinsa ne yake ɗaukar nauyin kaso saba'in na gidauniyar marayun. Kuma sanannen mutum ne ya yi suna Mutumin kirki ne daga nan hankalina ya kwanta. Sau tari nikan ji kamar na dawo m ku da ƴarku tun da wacce na kai wa jaririyar Allah ya karɓi rayuwarta. Amma gani nake za ku hukunta ni don ban san matakin da za ku ɗauka a kaina ba. Ga shi dama ba wanda ya san ni na sace jaririyar, ko da muka haɗu da Ɗan uwana da na bari yana ma ku gadi na bugu cikinsa ta hanyar tambayar ya kuke ya yaran ku zuwan yanzu yaranki nawa? Sai yake sanar da ni iya Sulaiman da Fatima ne kun sake haihuwa aka sace jaririyar har yau ba'a san waye ya sace ta ba. Haka na cigaba da rayuwa ta duk da ba na cikin natsuwa yadda ya kamata har na yi wani auren matata ta haifa ma ni yara biyar. Duk da auren sake jefa ni cikin tashin hankali ya yi sakamakon bana da kwanciyar hankali ga matata masifafdiya mulkin sake sakani damuwa take yi. Ga bakin cikin yaran da na haifa da sam ba sa jin magana. A haka dai wata rana na ji labarin yarinyar da na kai gidan marayu har ta haihu ta haifi ƴa mace sunan jaririyar Ma'eesha, wato ita jikar taku ce Ma'eesha. Daga nan ban sake jin halin da suke ciki ba sakamakon mai sanar da ni Allah ya yi ma sa rasuwa. "
Shiru falon ya ɗauka idan ban da ajiyar zuciyar da Dada ke yi, dama ita tana ji a jikinta ƴarta tana raye sai dai ba ta san in da za ta samo ta ba. Shi ya sa ko fa mahaifin yaran nata kafin ya rasu ya tashi rabawa yaransa dukiyarsa ta ce ya raba har da Babyn da aka sace wata rana Allah zai bayyana ma su ita, har yake cewa yau shekaru talatin da biyar ba wanda ya sani tana raye ko tana mace. Amma duk da haka ya raba aka ajiye ma ta kason ta yau shekaru biyar kenan.
"Yanzu idan har muka je wajen shi mahaifin da ya aura wa Ɗan sa ƴar uwar mu za mu same shi yana raye?"
Cewar Alhaji Sulaiman sauƙi.
Tabbas yana raye sai dai baya ƙasar. Amma na tabbatar matarsa na nan garin Kaduna har gidansa na sani saboda ba ɓoyayyen mutum ba ne."
Sai a lokacin Barrister Haidar ya yi magana ya ce .
"Ina ganin ba can ya kamata mu fara dosa ba. Shi wanda ya kai yarinyar gidan marayu za mu je da shi, na san gidan marayun dole sai ya bayar da sunan sa da ranar da ya kai yarinyar da komai da photonsa an tabbatar shi ne kafin su ne za su hada mu da asalin wanda ya dauki yarinyar."
Jinjina kai ya yi
"Tabbas an yi haka sai da suka yi ma ni tambayoyi na samar da su tsintar ta na yi, sai da aka karbi sunana da passport ɗina aka yi cike-cike sanan suka karɓe ta, suna da ƙa'ida da tsari."
"To me muke jira maza ku dauko motoci mu kama hanya!"
Cewar Dada jikinta har rawa yake yi .
"Kin ga ki kwantar da hankalinki Dada, yanzu yamma ta yi ki bari gobe da asuba mu za mu tafi ni da Kabeer da Haidar."
Ɗaura hannu aka ta yi ta fashe da kuka .
"Anya Sulaiman kana farin ciki da bayyanar ƴar uwarka kuwa? Ta ya zamu bari sai gobe sannan ka ce wai ba da ni za'a je ba to da waye za'a je idan na da uwarta ba?"
"Ba haka nake nufi ba Dada, kin ga dare zai ma na a hanya kuma yanzu ba samun jirgi da zai tafi Kaduna ba zai yiwu ba. Don haka tun da ba wai an ganta ba ne, bincike za'ayi sai mun fara zuwa gidan marayun an bincika an tabbatar aka hada mu da mutumin ya hada mu da iyalansa muka tabbatar da gaskiyar magana sai a ɗauko ki ki zo ku mu kawo ma ki su."
"Yanzu kana nufin kai da Soja da Lauya ne za ku tafi?"
"Eh in sha Allah, daga baya sai ki ganta idan an tabbatar."
Da ƙyar aka shawo kanta ta yarda akan za ta zauna , gobe sai su kama hanyar zuwa Kaduna tare da Maude da zai ma su jagora.
BQ aka kai Maude ya zauna aka kai ma sa abinci da ruwa .
_Nadra_
Fitowar ta kenan daga wanka tana ɗaure sa babban towel da kuma wani ƙarami a hannunta tana tsane ruwan da ke kanta.
Handrayer ta jona a socket ta nusar da ruwan dake ya jiƙa ma ta kai.
Man shafawarta ta shafa da turaren jiki mai sanyin ƙamshi. Dama ita ba ma'abociya yin makeup ba ne.
Tana kokarin shiga closet ɗin kayanta sai ta ji ƙarar buɗe kofa, Fahad ne ya shigo bakinsa dauke da sallama.
Ta amsa tana kallonsa, sanye yake da wando three quarter da ƙaramar riga sai ƙamshin turarensa mai daɗin ƙamshi yake yi.
Ɗaya daga cikin akwatin kayan lefe ya ɗauko daga cikin closet ɗin.
Ƙananun kaya ne a ciki, irin ma su nuna jikin nan da kuma marasa nauyi. Don wasu kayan ma gani take da su da babu duk daya ne .
Tana kallon da ya fito da wata figaggiyar riga da siket.
Rigar kamar bra take daga sama kasan rigar ma duk saukan rigar ba za ta rufe cibiya ba. Siket din kayan iya rabin cinya zai tsaya ma ta.
Mika ma ta rigar ya yi tana cewa .
"Daga yau idan ina gida irin wanan kayayyakin nake bukatar ki dinga saka ma ni ina gani. Dan gaskiya na gaji da ganin kullum cikin manyan kaya da Abaya. Ke da saka su sai dai idan fita za ki yi ko kuma ba na gidan . Idan kin ji sallamar baƙi ki saka hijabi kawai .
Kallon kayan take yi ba ta karɓa ba, take sai jikinta ya yi sanyi sakamakon tuna Sidra da ta yi wacce da ba don ƙaddara ta ƙaddaro cewa ita ba matar Fahad ba ne da yanzu ita ce a matsayinta. Tuna yadda Sidra da Fahad suka je kasuwa suka yo siyayyan kayan ta yi, tana tuna yadda Sidra take ba Sady baby labarin irin kananan kayan da ta siyo wanda banbancin su da babu kadan ne. Da ƴan iskan kayan barcin da suka zaɓo ita da Fahad ma su bayyana jiki. Ko rigar da yake ba ta ba ta sake kallo ba don ta san shi da Sidra suka zaɓo shi don ta burge shi. Har ta buɗe baki da niyyar yi wa Fahad zancen Sidra sai ta tuna ya ce baya son tana maganar Sidra don haka sai ta fasa. Amma jikinta ya yi sanyi sosai tuna cewa wannan kayan fa da sunan Sidra aka siye shi ko ma ita ta zaɓe shi amma yanzu ita ce za ta yi amfani da shi.
"Tunanin me kike yi?"
"Ba komai."
Murmushi ya yi yana cewa.
"Ina fatan kin gane me nake nufi ko? Na fi son kananan kaya matata za ta dinga saka min dan haka ki saba."
Shiru ya yi tana rike da kayan ba ta saka ba
"Bari na saka ma ki tin da baki iya sakawa ba ."
Jin haka ya sa ta yi saurin cewa.
"Zan saka da kaina."
,"okay ina jiran ki a falo."
Ya fada yana ficewa daga ɗakin . Dole ta bi umarnin sa ta saka kayan, amma sai ta ji ba za ta iya fita da shi ya ganta a haka ba. Sai ta ɗauki dogon hijqbi ta saka tana tafiya a hankali kanta ƙasa kamar munafuka.
Jin ƙarar kofar ya sa ya juyo yana washe baki, take fara'ar fuskarsa ta ɗauke yana kallon ta cikin hijabi take ya tsuke fuska.
_Sidra_
Da maɗaukacin mamaki take kallon matashin malamin. Duk da cewar ba zai haura shekaru talatin da biyu zuwa da uku ba, amma ta yi mamakin jin kalamansa. Sanan kuma Sady baby ba ta damu ba.
"Mallam ka san me kake faɗa kuwa ?"
"Ke Mallama idan har zan yi ma ki aiki to fa ba zan karbi kudin ki ba, jikinki kawai nake so ki bani haɗin kai ku ga aiki da cikawa ."
"Wai ƙawata ba ki ji me yake cewa ne? Wai sai ya yi lalata da ni fa?"
'Eh yi meye ai idan bukata za ta biya ba wani abu ba ne , ku tuna Fahda kike so ba kowa ba kuma za ki mallakar shi sai yadda kika yi da shi a rafin hannunki don haka ki Amince kawai kamar biya ma sa bukata shi ma ya ya ma ki aiki ki ga biyan buƙatar. Idan kuma ba ki aminci ba ba to ba wani Mallam da na sani sai dai ki koma gida ki je a kai kuma ƙauye a aura ma ki ɗan kauye ku je can ku ƙarata ki lalace.
Tana faɗar haka ta fita waje ta janyo ma su ƙofa ta koma cikin mota tana jiran su gama abun da za su yi .
_Jalaluddeen_
Tun bayan jin hukuncin mahaifinsa jikinsa ya yi sanyi da hukuncin, domin shirin sa ta gama wargaje wa shirin sa ya lalace.
Kallon Yasmeen ya yi wacce farin ciki ya cika ta da jin zancen Dad din.
"Za ki tashi mu tafi kuwa?"
Da sauri ta tattara kayanta ta shirya tana murmushi.
"Hankalinki ya kwanta ko?"
"Abun da kike so kin samu hankalin ki ya kwanta ko?"
Murmushi kawai ta yi ta nufa hanyar fita daga ɗakin ta fice. Sai da ya dauki sakanni sannan ya samu zarafin fita daga cikin ɗakin ya fice kai tsaye.
Tana jiransa a gefe ya ganta daga nan suka fice a tare. Bayan ya ba d key din ɗakin ya yi gaba tana bin sa a baya har suka fice daga hotel ɗin .
Kai tsaye gidan Alhaji Tanko Abokin Dad ya kai ta.
Yana zaune a bayan motar shi da Yasmeen sai yaronsa dake driving motar . Shi ya nuna wa yaron hanyar gidan kasancewar ya taba zuwa sau ɗaya, wani zuwa da Dad ya yi ɗaurin auren ƴar Alhaji Tanko, ya kira Jalaluddeen ya sanar da shi yana garin, shi ne Jalaluddeen ya zo bisa kwantancen da Dad ya ma sa .
Bayan ya yi horn a ƙofar gidan ne maigadi ya leƙo ya ƙaraso wajen motat ba tare da ya bude gate ɗin ba ta karamar ƙofa ya fito.
"Assalamu alaikum."
"Wa'alaiki salam."
"Don Allah waye kai Yallaɓai an ce na tambaya ne?"
"Jalaluddeen ne"
Ya faɗa daga bayan Motar da yake .
Da sauri Maigadi ya wangale ma su gate suka shiga ciki.
Jalaluddeen ya fito bayan direban ya yi parking, ita ma ta fito riƙe da jakarta.
Direban na bayan motar yana jiransu yayin da suka nufi main door din gidan .
Ya kai hannu zai danna ƙararrawar kofar kenan sai ga ɗaya daga cikin ƴan matan gidan ta buge ƙogar za ta fito.
Idanunta ya sauka akan Jalaluddeen, ta zuba ma sa idanu tana kallon sa ita ba ta matsa ta ba shi hanya ba. Sai da Yasmeen ta dawo ta tsaya gaban Jalaluddeen sanan wanan budurwar ta ɗauke ido yana barin wajen cike da kunya.
Da sallama suka shiga Alhajin yana falo tare da matarsa . Bayan sun gaisa ya sanar da shi saƙon Dad, Alhajin ya ce Dad ya sanar da shi ba damuwa zai iya tafi gobe sai ya zo ya kai ta airport.
Sallama ya yi ma su ya fita yayin da matar gidan ta ƙwalawa ɗaya daga cikin yarinya kiraz ta fito Nam ta sanar da ita je da Yasmeen ɗakinta su kwana zuwa gobe.
Tashi Yasmeen ta yi ta bi bayan yarinyar wacce ta ɗauki kakar kayan .
Jalaluddeen na cikin mota sai kiram Ma'eesha ya shigo wayar. Bayan ya ɗaga ne ta nemi izinin fita gidan Mallam Liman ana biki sam ta mance sai kusan yamma ta tuna shi ne ta kira shi da yamman . Ya ba ta izinin fita sanan ta yi godiya ta katse kiran wayar.
Kai tsaye hanyar gida ya ce wa yaronsa ya kai shi. A bakin layin ya sauka ya dauki sandarsa a bayan motar ya yi wa yaron sallama sannan ta fara tafi zuwa cikin layinz don can baya ta sauka sau da ta tabbatar ba mai ganinsa ta fito da sauri.
Tafiya yake yi cike da damuwa, ya so kafin a tayar da zancen aurensa da Yasmeen ya sanar da su auren Ma'eesha da ya yi, ga shi zuwan Yasmeen ta lalata ma sa shiri.
A haka ya karasa cikin damuwa har cikin gidan, ba ta nan kasancewar ya san in da take ajiye key kan window ne sai ya ɗauka ya buɗe kofar.
Ya shiga ciki tana safa da marwa a cikin ɗakin
Vibrating na wayarsa ya ji daga cikin aljihu, ya ɗauka Dad ne, amma sai ya ga abokin sa Khalil ne .
Ya amsa sallamar bayan ya daga wayar.
Daga cikin wayar abokin ke cewa.
"Ya na ji muryarka wani iri?"
"Dole ka ji muryata wani iri ma na, wai ranar jama'a ne aurena da Yasmeen."
"To me ye na damuwa bayan ka san da wanan zancen ba tun yau ba, ka sanar wa abokanmu kawai Malam .
"Ba wanda zan sanar, dama ka san ba wai na fiye yawan mu'amala da aboka ba ne."
Daidai lokacin da Ma'eesha ke shigowa gidan, sakamakon tuna zai iya dawowa ga yamma ta yi lokacin dawowarsa ne, don haka ba ta zauna s gidan bikin ba ta ma su Allah sanya alkhairi ta dawo don ta tarbi mijinta.
Cak ta tsaya bakin ƙofar sakamakon jin muryarsa yana cewa.
"Rabo na da wasu abokan fa tun da muka gama karatu a America ban sake haduwa da su ba, sai dai wani lokaci da na je London na haɗu da su Faisal a can . Sai kuma Ahmad da ya matsa sai na je bikinsa to a lokacin na tafi ƙasar Canada. Daga nan ban sake bi ta kansu ba, sai yanzu kawai dai na kira su na sanar da su cewa ranar Juma'a ne ɗaurin aure na da Yasmeen? Ba wani gayyatar da zan yi kai ma ɗan ka kira ni ne kuma ban ce ka ma ni gayya ba, ba abun da za'ayi daga an ɗaura auren shi kenan kowa ya watsa ba ruwana da wani events ko wani bidi'a."
Kalamansa sun matukar gigita ƙwaƙwalwar Ma'eeha wanda ta ji wani jiri na ɗibarta ga numfashinta dake barazanar ɗaukewa.
Kalaman da ta ji tana yi ne suke ma ta amsa kuwa a cikin kunnenta kamar za su fasa ma ta dodon kunnen.
"Dad ya ce na bar garin nan dole na koma Abuja na halarci bikin aurena da..."
Kafin ya karasa maganarsa ya ji faɗuwar abu kada tim. Da hanzari ya daki wayar kasa ya fito da sauri, Ma'eeha ya gani kwance kada ba ta numfashi."

Page8️⃣2️⃣

Kafin ya karasa maganarsa ya ji faɗuwar abu kasa "Tim." Da hanzari ya saki wayar ƙasa ya fito da sauri. Ma'eesha ya gani kwance kasa ba ta numfashi.
Taune lips ɗin sa ya yi har sai da ya fashe jini ya fito, ya san ta ji komai kuma yadda ta ji ta wanan hanyar zai yi wuya ta fahimce shi.
Ƙarasawa ya yi wajan da take ya dauke ta ya shiga ɗakin da ita. Ruwa ya yayyafa ma ta amma ba ta farfaɗo ba. Sau uku yana zuba ma ta ruwa ba ta farfaɗo ba. Don haka hankalinsa ya fara tashi ya ɗsuki wayarsa ya danna ma wata lamba kira.
Bayan an ɗaga kiran wayar ne ya yi magana cikin bayar da umarni ya ce.
"Ka zo karamin gidan da nake kwana yanzu-yanzu."
Daga haka ya katse kiran wayar yana Safa da marwa a cikin dakin.
Tsayuwar motar da ya ji a kofar gidan ne ya sa ya ɗauko hijab ya saka ma ta sanan ya dauke ta ya nufi hanyar fita daga gidan .
Yaronsa na ganinsa ya bude bayan motar da sauri, yayin da Jalaluddeen kwantar da ita s bayan motar.
Sanan ya koma ciki ya ɗauki wayarsa ya rufe gidan suka bar unguwar.
A saman cinyarsa ya dora kanta yana kallon fuskarta. Wani tsadadden asibiti aka nufa da ita a nan cikin garin .
Yana parking din motar Jalaluddeen ya fito da sauri ya dauke ta ya nufi ciki da ita .
Emergency aka kai ta likitoci biyu suka tsaya a kanta.
Sai Safa da marwa Jalaluddeen yake yi gabaɗaya ya rasa nutsuwarsa.
Kiran sallar magrib da ake yi ne ya sa shi fita zuwa masallacin dake jikin asibitin.
_Sidra_
Tana ganin Sady baby ta fita ta tsaya tana nazari .
"Kin ga Mallama ba dole sai kin amince taimaka ma ki zan yi ki auri wanda kike so, ku yi rayuwa na har abada ki mallake shi sai yadda kika yi da shi, komai zai yi sai da izininki. Idan muka ba ki son shi ki haƙura kawai ma na ."
"Ba zan iya hakura da Fahad ba."
Jin ta yi shiru alamar amincewa ya yi murmushi yana shafa siririn gemunsa.
Tura ƙofar ɗakin ya yi ya sa sakata ya rufe window.
Tana ji tana gani ya umarce ta da ta cire kayanta, ba ta yi musu ba ta cire kayan kamar yadda ya buƙata.
Idanunta ta rintse tana hawaye, a yadda ta tsara rayuwar ta da Fahad a daren farkon auren su amma yanzu duk ya rushe ga wani banza nan zai raba ta da mutuncinta na ƴa mace.
Ƙara ta saki lokacin da ya shige ta da ƙarfi sakamakon azabtar da ta ji.
Sanin asirinsa zai iya tonuwa ne ya sa ya saka hannu ya toshe ma ta baki, ta yadda muryaryarta ba zai fita ba.
Hawaye kawai take ya babu sautin kukan baya fita ya toshe bakin.
Sai da ya biya buƙatsrsa sanan ya bar ta nan kwance.
Kayan jikinsa ya saka sannan ya kunna hasken ya ganta jini ya ɓata ma ta jiki. tishu fefa ya yago ya mika ma ta.
"Karɓi ki saka cikin pant ɗin ki kada jinin ya ɓata ma ki kaya."
Kakan takaici da nadama ta saki a lokacin da bai da amfani.
Karɓa ta yi ta saka ta mayar da kayan jikinta, ba ta iya tafiya sosai haka ta ke ɗingisa ƙafa ta fita idanunta a kumbure.
Sady baby na ganin tafiyar ta san aikin gama ya gama . Murmushi ta yi wanda ita kadai ta san ma'anarsa. Tabbas ta ji farin cikin rasa budircin Sidra, domin kuwa dama burinta ta ga rayuwar Sidra ta lalace. Ba ƙaunar Sidra take yi ba, hasalima tsanarta ta yi. Ba ta son ganin rayuwarta ta inganta. Bayan ita ma tana son Fahad din amma ko da ba ta son sa ba za ta bari ta ga rayuwarta ta yi kyau ba. Shi ya sa ta ba ta shawara ta gudu ranar aurenta gara ta samu ɗaukaka ta yi suna lokacin kowa zai ƙaunace ta fiye da yadda take, kuma hakan zai sa ta rama wulaƙanci da aka yi ma ta. Tabbas Sidra ta yarda Sady baby mai ƙaunarta ce yake ɗaukar shawararta. Duk da halin da ya shiga bai ishe ta ba sai da ta saka ta rasa budurcinta.
Tafiya Sidra ke yi tana hawaye. Da sauri Sady baby ta fito daga motar ta taimaka ma ta ta shiga. Sanan ta bar ta cikin motar ta koma wajen Mallamin nata.
Bayan kamar mintuna goma ta dawo ta ce.
"Ya ce daren yau zai fara aiki akan Fahad din, jibi zan zo na karbi maganin da zan kawo ma ki ki yi amfani da shi."
Ba ta ce ma ta komai ba illa hawayen da take yi .
"Mu je na ajiye ki gida ne ko gidana za mu je?"
"Gidanmu za ki kai ni."
"Okay to, idan kin je ki gasa jikinki sosai da ruwan ɗumi ki zauna ciki, sanan ki bi kofar baya kada wani ya ga shiganki, ki tabbatar sai kin gasa jiki kafin ki fita wajan iyayenki, idan so samu ne ki kwanta kawai sai da safe."
Ba ta ce ma ta komai ba ta cigaba da goge hawayenta, dansani take yi da ba amfani .
_Jalaluddeen_
Har ya dawo masallaci sallar isha'i amma ba Ma'eesha ba ta farfaɗo ba, ganin yadda ya tayar da hankali ne ya sa suka kwantar ma da da hankali.
Ko ruwa bai saka a cikinsa ba ballantana abinci .
Da misalin karfe goma sha ɗaya na dare ne yana zaune s kan kujera ya zuba ma ta idanu.
A hankali ta fara motsa ƙafarta sanan hannunta. Zuwa can ta sauke idanunta akansa.
Tana kallon sa sai ta rintse idanunta da ƙarfi, hawaye na zuba a idanunta ba abun da take tunawa illah maganar Nasreen da take ta kokarin fahimtar da ita akan sanin waye asalin mijinta, amma sai take ganin laifin Nasreen tana kalubalantar ta ashe tana da gaskiya ita ce ta ƙi ta fahimce ta.
Ganin ta farfaɗo ya saka shi sakin murmushi.
"Ma'eesha sannu ko?"
Wani takaici ne ya sake cika ta har ya fashe da kuka.
"Ka yi nisa da inda nake ba na ƙaunar ganin ka, ka san yadda na tsani maƙaryaci da mayaudari kuwa? Ashe kai na kama da laifin da na fi tsana a rayuwata? Da a mafarki na yi wanan mafarkin idan na tashi sai na yi sadaka. Dama na faɗa ma ka duk ranar da na gane ka yi ma ni ƙarya za mu samu matsala, ƙarshen rabuwa ta da kai kuma ya zo. Dama Nasreen gaskiya take faɗa mun cewa kai ba Makaho ba ne basaja kake yi kama raina wa mutane hankali. Abun takaici ma har da ni da ban cancanci ka ɓoye ma komai ba. Na yarda da kai fiye da kowa.
Kau da kanta gefe ta yi don ba ta so magana da shi. Ko ganinsa ba ta son yi.
Ƙoƙarin tashi zaune take yi duk da kanta na Sara ma ta da ciwo amma ta daure, tana ƙoƙarin taimaka ma ta sai ta ɗaga ma sa hannu alamar dakatar wa.
"Kada ka taɓa Ni!"
Ta jingina da kyau sannan ta juya ta kalle shi cikin ido, cike da ƙunar rai ta ce.
"Zan yi ma ka wasu tambayoyi ka ba ni amsa, wannan karon kafa ka kuskura ka ce za ka yi ma ni ƙarya."
"Meye sunanka daga wani gari kake?"
"Sunana Jalaluddeen Kabir Arzika, daga Abuja, kuma ni...?"
Ɗaga ma sa hannu ta yi alamar ya isa .
"Da gaske kai Nasreen ta gani a Abuja tare da wata mace har ta kawo ma ni photon amma na ƙaryata ta bayan ka ce Maiduguri za ka tafi wajen wajen dangin ka amma ka je Abuja?"
"Eh nine."
"Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un. Nasreen na yi nadamar rashin yarda da ke tun farko ku yi hakuri don Allah."
Kauka ne ya ci ƙwrfinta, da zaran ya zo zai taɓa ta sai ta dakatar da shi da hannu.
Ɗan tsagaita kukan ta yi kafin ta ce .
"Maganar da na ji kana ya a waya da gaske ne ranar juma'a kai ne wanda za'a ɗaurawa aure ta wata mace? "
Shiru ya yi kansa a ƙasa don amsar ta yi ma sa nauyi ya faɗa.
"Faɗa mun kai ne?"
"Eh ni ne amma wallahi ba da..."
"Ya isa!"
Ta daka ma sa tsawar da sai da ya yi mamaki.
"Ba na bukar sake jin komai daga gare ka, iya abun da nake so na sani kenan kuma na sani, saura abu guda nake umartar ka da ka yi ma ni."
"Mene ne shi?"
"Ka sake ni saboda dama auren namu bai da amfani ba shi da banbanci da babu, sunan aure ne kawai amma ba rayuwar aure muke yi ba, yanzu na fahimci dama ba ja so na kana da wacce ja shirya rayuwar aure da ita, shi ya sa a zamantakewarmu ba ka taɓa nuna mun alamar soyayya ko wani abu da zan yadda kana so na ba. Don Allah ka sake ni."
"Ba zan iya sakinki ba Ma'eesha, da za ki bani dama ki saurare ni mu fahimci juna za ki gane ..."
"Ba za ka sake ni ba ko? To shi kenan za mu gani. Babu wani dama da xan ba ka na sauraren ka. Da a baya ne ko zan iya sauraren ka saboda na yarda ba za ka yi ma ni ƙarya ba, amma yanzu da gane gaskiya ne wallahi, wallahi, wallahi , ba wata magana da za ta fito daga bakinka na yarda da kai . Ban taɓa danasanin saninka a rayuwata ba sai yau. Na yi danasanin saninka a rayuwata , na yi nadamar zama da kai. Ban taɓa ganin ka da muni ba sai yau, ban taba jin muryar da na tsani ji kamar Muryar ka ba a yau na tsane ka wallahi,. Maƙaryaci, mayaudari...'
Kula ne ya ci karfinta sosai har yake ihu tana dukan katifa tana kuka mai cin rai
Doctor ne ya shigo yaga halin ta take ciki da yadda take cewa Jalaluddeen ya fita . Lura fay hakan ya sa ya ce ma Jalaluddeen ya fita.
Yadda yake ta Surutai duk ta rikice ya da Doctor ya kira nurse ta yi ma ta allurar barci.
Sai da ta yi barci sannan suka fita daga ɗakin. Lokacin karfe sha biyun dare. Doctor Kamal ya tafi gida ita nurse ta tsaya a asibitin.
*KATSINA*
Washegari
Bsyan sun sun yi wanka sun yi breakfast suka shirya don zuwa Kaduna. Maude ma an kai ma sa breakfast ɗinsa da sabbin kayan da idan ya yi wanka zai saka, Alhaji Sulaiman ne ya aika ma sa da kayan nasa.
Ya yi wanka ya shirya kamar ba shi ba. Ya fito yana jiran fitowar su. Captain Kabeer da Barrister Haidar ne suka fara fitowa. Maude duk da tsufarsa ya durƙsmusa yana gaishe su. Barrister Haidar ne ya amsa Amma Captain Kabeer ma ko kallo bai ishe shi ba ballantana ya amsa .
"Amma ba dai da motata za'a tafi da wanan abun ba ko?"
Cewar Kabeer yana yi wa Maude wani wulakantaccen kallo.
"To Amma da motar ka Alhaji ya ce za mu tafi."
"Wanan mutumin ba zai shigar ma ni mota ba wallahi sai dai motarka?"
"Anya Kabeer ka san darajar Ɗan adam kuwa?"
"Wani irin tambaya ne kake ma ni Yaya Haidar, shi ya san darajar mutane ne, da za'a ba ni dama sai na kashe shi. Amma bari mu gama abun da muke so dai ya gwammace mutuwarsa da rayuwarsa."
Cikin Maude ya ɗuri ruwa wani tson wanan sojan ya shige shi lokaci guda.
"Shi kenan a tafi da Motata, bari na je na ɗauko makullinta."
Ya yi maganar yana tafiya zuwa ɗauko key din motarsa. Dadai sauran mutanen gidan na fitowa. Alhaji Sulaiman da Mahaifiyarsa yana sake kwantar ma ta da hankali. A gefe Hajiya Safiya da Hajiya Saratu ne , sai Lubna da Jamila. A baya kuma Mujahid ne wanda zai wakilci Alhaji Sulaiman yau a wani zama da za su yi da abokan Harkokinsu.
"Ina kuma za ka tafi?"
"Zan ɗauko key din motata ne."
"Ba da miyar Kabeer za mu tafi ba "
"Motata za ta fi bari na ɗauko ."
"Kafin Ya yi wani magana har ya wuce da sauri."
"Ko kuma baƙin halinsa ya sa ya ce ba za'a tafi ma sa da mota ba ,in dai Kabeer ne shi ya fi komai sauki a wajensa bai da mutunci."
Cewar Dada tana tafiya da ƙyar saboda ciwon ƙafa.
Suna isa sai ga Haidar ya iso da key din motar, ya bude wa Mahaifinsu bayan motar ya shiga, sanan ya ce Maude ya shiga gefe. Yayin da shi ya shiga mazaunin direba. Kabeer ya zaune gefensa wajen me zaman banza.
Allah kiyaye hanaya aka yi ma su tare da addu'a Allah ya bayyanar da su. Da amin suka amsa.
Horn ya danna maigadi ya wangale ma sa gate ɗin gidan ya fita, har sai da aka rufe gate mutanen gidan suka koma ciki suna addu'ar Allah ya sa a gane inda suke cikin gaggawa.

Page8️⃣3️⃣
Horn ya danna maigadi ya wangale ma sa gate ɗin gidan ya fita, har sai da aka rufe gate gate mutanen gidan suka koma ciki suna addu'ar Allah ya sa a gane in da suke cikin gaggawa.
_Jalaludden_
Yadda ya ga rana haka ya ga dare. Domin gabdaya bai rintsa ba, ya shiga ɗakin da aka kwantar da Ma'eesha sama da sau goma yana duba ta amma tana barci. Har yanzu allurar barcin ke aiki a jikinta. Har ya kai ya zauna cikin dakin yana gadinta har aka kira sallar asuba ya tashi ya nufi masallaci.
_Fahad_
Sake haɗe fuska ya yi ganin yadda Nadra take ƙarasowa wajen sa sanye da dogon hijabinta. Wato ya ba ta kayan da za ta saka ta zo in da yake shi ne ta ɗora wani hijabi a saman kayan.
Tama ƙarasowa kanta a sunkuye kamar mara gaskiya.
Miƙewa tsaye ya yi yana kallon ta ba ta yarda ta kalle shi ba.
Hannunsa ɗaya ya sa ya zare dogon hijabin da ta saka, da sauri ta shige jikinsa ta ƙanƙame shi sosai. Saboda ita har ga Allah tana kunyar ya ganta cikin figaggiyar riga da ya ba ta. Murmushi ya yi sannan ya ɗauke ta ya zauna kan kujerar sanan ya ɗaura ta a saman cinyarsa.
Kunya take ji har lokacin, sai ta ɓoye fuskarta a ƙirjinsa.
"Nadfah."
Ya kira ta cikin sigar raɗa a cikin kunnenta.
"Wanan kunyar ta ki fa tana cutar da ni wallahi. Kunyar me ya rage a tsakaninmu? Allah na tuba wani dare ne jemage bai gani ba? Ba abun da za ki ɓoye ma ni wanda ban gan shi a jikinki ba ko ban san shi ba, na san ki ciki da waje har..."
Hannunta ta sa ta toshe ma sa baki yana dariya.
Cire hannun ya yi yana cewa.
"To ka dena faɗa, ke ma ina son ki kasance a yadda nake buƙata ina son ki da dukkan zuciyata, i love You with all my heart."
"Love you more..."
"Na kusa komawa America next week zan koma in sha Allah, sannan ina so mu tafi tare da ke my sugar."
Shiru ta yi tana tunani ba kowa ya faɗo ma ta a rai ba sai Aunty Sidra. Ita ce kullum maganar ta tana cewa idan ta tafi America ita dai Nigeria sai dai ziyarara don can za ta zauna da Fahad.
Take yanayin ta ya sauya saboda tuna Sidra, sai take ji a ƙasan ranta kamar ita ce ta janyo komai da yake faruwa a yanzu. Hawaye ne ya cika idanunta. Tabbas ta san cewa tana son Fahad kuma ba ta san lokacin da soyayyan Fahad ya shige ta lokacin guda ba. Amma tana tausaya wa Halin da ƴar uwarta ta shiga a lokacin da ta rasa shi, wanda har yanzu ta san tana son sa amma ba yadda za ta yi. Ba zato ta ji ya kai harshensa a saman kumatunta yana lashe hawayen da ya wanke ma ta fuska.
Sai da ya lashe hawayen sanan ya ce.
"Kin san na tsani zubar hawayenki ko? Ba na son ɓacin ran ki ballantana har ki zubar da hawaye. Me ya sa kike son sa wannan majidaɗin ne ya ji ba daɗi? Idan tafiyar America ne ba ki so to ni zan tafi ni kaɗai ba zan tilasta ma ki abun da ba ki so ba."
Ganin wani hawaye ne ya kai baki ya yana lashewa sai suka ji takun tafiya ƙwas ƙwas ƙwas, ana zuwa inda suke. Cire bakinsa ya yi daga fuskarta ya kalli wace isashshiya ce ta shigo ma su har falo na knocking ba neman izinin. Ita ma kallon ta ta yi sai da gabanta ya faɗi ta yi saurin ɗaukar hijabinta ta saka musamman ganin kallon tsanar da take jifanta da shi.
_Sidra_
Bayan Sady baby ta sauke ta ta kofar baya na gidansu ne ta fito daga cikin motar tana tafiya a hankali.
Leƙowa ta yi ta tana cewa
"Zuwa jibi za ki ga sakamako aikin da zai yi ma ki, kuma zan je na karɓo ma ki wasu saƙon da ya ce zai ba ki."
Ba ta ce komai ba, ta bude ƙofar bayan ta shiga cikin sanɗa. Sannan ta saka sakatar ta rufe.
Sady baby ta ja motarta ta bar wajen, sai dai ba ta lura da wata motar da take bin su a baya tun lokacin da suka bar unguwar da suka je wajen Mallaminta. Sai da ta bar wajen sanan motar da ya biyo su tun daga can ya sauke baƙin glass ɗin motarta ya kalli gidan da kyau, sanan ya zagaya ta gaban gidan ya kalli gidan sannan ya ja motarsa ya bar wajan.
_Ma'eesha_
A hankali ta buɗe idsnunta da suka yi ma ta nauyi ta sauke shi a kan fuskarsa. Cike da takaici ta rintse idanunta.
"Kin farka ya jikin naki?"
Idanunta a rufe kamar me barci amma ba barci yake yi ba.
Kanta ke Sara ma ta kamar zai tsage gida biyu. Ga jikinta sam ba ƙarfi ko kaɗan a jikin nata.
Wayarsa ce ta soma ruri ya fito da wayar daga cikin aljihunsa ya duba mai kiran wayar. Idanunta suka sauka an tsaddadiyar wayar tasa ta miliyoyin kuɗi.
Lumshe idanunta kawai ta yi kamar tana barci .
Ɗan matsawa gefe ya yi yana amsa wayar. Duk da a hankali yake magana amma tana jin abinda yake faɗa..
"Hello."
Can cikin wayar ya ji muryarta tana cewa.
"Gud morning my Sweet Yaya J."
Cikin yanayin rashin son magana ya ce.
"Kin shirya ne?"
"Eh kai nake jira."
"Ba zan samu zuwa ba zM turo a zo a ɗauke ki a kai ki airport."
Kamar za ta yi kuka ta ce .
"Please mu tafi tare ma na, ja ga dama ba mu yi tsare-tsaren bikin ba."
"Kin ga ba na son magana, ki shirya a zo q ɗauke ki kada ki rasa jirgi."
Daga haka ya kashe kiran wayar. Ya kira yaronsa da ya kai su gidan jiya, ya sanar da shi ya je ya ɗauko Yasmeen ya kai ta airport.
Daga nan ya kashe wayar ya sa a aljihu, yana tuna diramar da Ma'eesha ta yi yana kuma tuanin yadda zai iya shawo kanta ta saurare shi .
Tunani kawai take yi na neman mafita don shi ne a gabanta yanzu ba komai ba.
Damuwa bata da amfani akan duk abinda ba ta da ikon koma wa baya ta canza shi, ko kuma ta hana faruwarsa, sai dai ta cinye ma ta lokaci, ta hana ta amfanar damarta ta yau wajen aikata abunda zai amfa ne ta a duniya da lahira. Za ta yi haƙuri, ta fuskanci al'amuranta ga Allah , zai kawo miki sauyi da mafita a mafi dacewar lokaci.
Doctor ne ya shigo cikin ɗakin idanunsa akan Ma'eesha da ta lumshe idanu. Sanan ya kalli Jalaluddeen.
"Assalamu alaikum."
Jalaluddeen ya kalli Doctor dake shigowa sanan ya amsa sallamar.
"Wa'alaika salam."
Hannu ya ba shi suka yi musabaha sannan sannan ya ce.
"Da alama ko barci ba ka yi ba ko?"
Bai amsa ba idanunsa na kan Ma'eesha.
"Ka ci abinci kuwa, na ga kamar kai ne mai jinyar jikin daga jiya zuwa yau har ka rame."
Gajeren murmushi kawai ya yi nan ma bai amsa ba.
"Ya jikin nata?"
"Da sauki."
"Ta farka kuwa?"
"Da safen nan ne ta ɗan farka ta kuma rufe ido amma na tabbatar ba barci take yi ba."
Doctor ya karasa wajan gadon ya ce.
"Assalamu alaiki."
"Wa'alaika salam."
Ta amsa isanunta a rufe tana yamutse fuska tare da ɗan dafe kanta.
"Doctor kaina kamar zai fashe nake ji."
"Sorry, za ki samu lafiya in sha Allah. Bari wanda ya kawo ki ya taimaka ma ki ki tashi zaune sai ki wanke baki, za'a kawo ma ki breakfast ki ji sai ayi ma ki allura za ki samu sauki."
Duk da halin da take ciki amma sai da ta ce
"Ba na son ganinsa Doctor don Allah ya fita, sanan ka tura Mani nurse mace ta taimaka ma Ni zan yi wanka na yi sallah."
"Na ga shi ya kawo ki, me ya sa ba ki son ganinsa? Meye alaƙar ku da shi?"
"Ban san shi ba, taimaka ma ki kawai ya yi da ya ga na fadi, ya kawo Ni asibiti na gode ya fita don Allah ya kama gabansa."
"Ka ji abun da ta ce Yallaɓai."
Doctor ya yi maganar yana kallon Jalaluddeen.
Bai ce komai ba ta fita daga ɗakin, wanda hakan ya sa shi ma Doctor ya fita don tura ma ta nurse kamar yadda ta bukata.
Ba jimawa wata Nurse ta shigo ta taimaka ma ta ta shiga toilet ta yi wanka ta dauro alwala. Kayan hijira ta sake sakawa sanan ta bude kofar. Nurse din ta taimaka ma ta ta yi tafiya zuwa inda ta shimfida ma ta sallaya ta mika ma ta hijab ta yi Sallah.
Fita ta yi sai ga ta ta dawo ta breakfast da aka jero a faranti . Tea da bread ne sai soyayyen ƙwai.
Da kyar ta iya shan ruwan tea kadai sanan Nurse din ta yi ma ta allurar da Doctor ya sa ta yi ma ta bayan ta kwanta.
Ba nunawa barci ya yi awon gaba da ita, da ba don maganin ya sa ta barci ba da damuwar da take ciki ba za ta iya bari ta yi barci ba.
Bayan ta yi bacci Jalaluddeen ya shigo dakin ya tarar tana barci .
Wayarsa ce ta yi ruri Mom ce ke kiransa .
Ya daga tare da sallama .
"Assalamu alaikum."
"Wa'alaika salam warahmatullah. Na ji muryarka da damuwa."
Murmushi mai sauti ya kirkiro sanan ya ce .
"Ba komai Mom, barci na tashi ne"
Ya yi maganar yana jin dadin yadda Mahaifiyar tasa ke lura da yanayinsa ko ba sa tare.
"To albashirin ka!"
"Goro"
ya faɗa kamar an ma sa dole ya ɗauka zancen auren sa da Yasmeen za ta ma sa.
"An gano ƙanwata da aka sace tun tana jaririya."
"Ban gane ba "
Sai ta tuna shi bai san zancen ba, saboda ba hannunta ya girma ba, kuma sau biyu ya taba zuwa Katsina ya gaida dangin mahaifiyar tasa. Sadik da Saddiƙa da suka tashi a wajen Mahaifiyarsu ne suka san labarin bacewar ƙanwar mahaifiyar tasu.
"Mom ban gane ba."
"Wato yara uku Dada ta haifa na farkon shi ne Yaya Sulaiman da ka sani mahaifin su Kabeer, sai ni nake bin sa, to akwai mace da Dada ta haifa bayan ni sai dai tun tana jaririya aka sace ta. An yi neman ta da cibiya har an gaji. Duk da mahaifin mu har ya rasu bai cire ran cewa tana raye ba wata rana za ta dawo. Ko da ya rabar ma na da dukiyarsa har da nata kason wanda dukiyar nan nan Yaya Sulaiman na kula da su. To yanzu zanen ya fito wai tsohon maigadin gidanmu a lokacin ya sace ta yanzu dai suna hanya zai kai su inda ya kai ta. Shi ne nake cewa tun da kana gari sai gobe za ka bar garin ka taya su neman inda za'a samo ta."
Kallon Ma'eesha dake barci ya yi .
"Mom ki yi hakuri ina da wani abu mai mahimmanci ne a gaba na, wanda ba zan iya barin sa ba. Amma tun da shi wanda ya sace ta ya san in da ya kai ta komai zai zo ma su da sauki ba za su sha wahala ba."
"Okay ba damuwa, na sanar da su kana garin, ko da sun kira sai ka sanar da su uzurinka. "
"To na gode Mom."
"Ba komai, ka tabbatar ka gama abun da kake yi zuwa gobe, wanda ba ka samu damar ƙarasawa ba sai ka bari bayan auren naka sai ka yi. Ka tabbatar ka dawo gobe."
"To Mom."
Ya amsa yana kallon Ma'eesha.
Bayan sun gama waya da kamar mintuna talatin sai ga kiran wayar Haidar ya shigo wayar Jalaluddeen. Amsa kiran ya yi ta hanyar sallama, bayan ya amsa ya ce .
"Kana ina ne Bros ga mu a Kaduna."
"Okay daidai ina kuke ne?"
"Yanzu muke shigowa, na ji an ce hotel kake ko za ka iya sanar da mu?"
Duk da baya cikin hotel ɗin amma sai ya sanar da su, ya san ba nisa da asibitin.
Fita daga asibitin ya yi bai tsaya kiran waya a zo a ɗauke shi da mota ba ya tari mai nape.
Yana isa hotel ɗin ya yi wanka sauri-sauri ya shirya cikin ƙananan kaya.
Kira ne ya shigo wayarsa ya duba ya ga Haidar ne.
"Barrister kun iso ne?"
"Eh mun iso, Ni da Kabeer ne kawai muka zo, shi mahaifin mu ya tafi wajen abokinsa Sanatar garin nan shi da mutumin da ya san inda take yake.
Ya amsa da ba damuwa , lambar ɗakin ya sanar da su sannan ya katse kiran wayar.
Knocking aka yi ya ba su izinin shiga ciki. Suka gaisa sanan suka zauna kan sofa.
"Me zan sa a kawo maku?"
"Ba komai kada ka damu."
Cewar Kabeer yana danne-danne a waya.
Haidar ne ya gyara zama ya kalli Jalaluddeen ya fara magana .
"Ka san zanen da ya kawo mu garin nan ko?"
"Eh Mom ta kira ni ta sanar da ni, sai dai ba zan samu damar bin ku ba sakamakon wani uzurin da nake sa shi."
"Ban yi mamakn jin haka daga bakinka ba, domin ba ka ɗauke mu ƴan uwan ka ba."
Kabeer ya yi magana yana kallon wayarsa kamar ba shi ne wanda ya yi maganar ba.
Jalaluddeen bai kalle shi ba ya lumshe idanunsa tare da kwantar da kansa jikin kujerar da yake kai.
Haidar ya kalli Kabeer ya ce.
"Duk bai kai can ba."
"Dama ni ban taɓa saka shi a cikin mu ba, duk da ba mu dade da sanin cewa muna da dangantaka da shi ba. Amma na tabbatar da dangin uwar da ta rike shi ne da ya bar abun da yake yi ya tafi. Amma wanan da muke nema fa da mahaifiyarsa da shi uwa daya Uba ɗaya, ana neman ta yana faɗin baya da lokaci? To shi kenan idan kuma har muka same ta na ga ka taka ƙafarka ka je Katsina sai na yi ma ka rashin mutunci!"
Sai a lokacin Jalaluddeen ya ce .
"Waye kai? Me kake da shi? Me kake taƙama da shi? To shi kenan ka rubuta ka ajiye ni Jalaluddeen sai na taka ƙafata cikin gidanku cike da isa da alfahari idan ka isa ka dakatar da ni."
"Haka ka faɗa?"
Banza ya yi fa shi ya miƙawa Haifar hannu tare da yi ma sa addu'ar Allah ya bayyana ta. Daga haka ya fice ya bar su a cikin ɗakin.
Cikin takaici Kabeer ya ce .
"Kana ganin wulaƙancin da ya yi ma na ko? Ba lafinsa ba ne kai da ka saka muka zo kai ka ja ma na wulaƙanci. Idan ba don ina duba dangantaka ba har ya isa ya faɗa mun magana na kyale shi?"
"Kabeer ba ka da hakuri, ba ja san uzurin da ke gabansa ba, tun da ya fadi haka sai a tafi a haka ma na, meye na ɓacin rai a ciki, daga kai har shi kowa na ji fa izza da isa shi ya sa ba ku jituwa da shi."
Bai ce komai ba ya tashi ta fita. Haidar ma ya bi bayansa suka fita a tare . Suna fita sai ga ɗaya daga cikin ma'aikatam hotel ɗin ya zo ya rufe ɗakin kamar yadda Jalaluddeen ya ba shi umarni."

Page8️⃣4️⃣
*Ku dinga haƙuri da typing error ba na samun lokacin yin editing.*
Bai ce komai ba ya tashi ya fita. Haidar ma ya bi bayansa suka fita s tare. Suna fita sai ga ɗaya daga cikin Ma'aikatan hotel ɗin ya zo ya rufe ɗakin kamar yadda Jalaluddeen ya ba shi umarni.
_Sidra_
A hankali take tafiya cikin sanɗa har ta shiga ta ƙofar baya na kitchen ta wuce zuwa ɗakinta ta cikin corridor da zai sada ta da ɗakinta.
Ajiyar zuciya ta sauke ganin har ta shiga ba wanda ya ga shigowar ta
Bathroom ta shiga ta haɗa ruwan zafi tana hawaye ta shiga ciki. Kuka take yi sosai ta yi nadamar abun da ta aikata.
Sai da ta daure ta gasa jikinta sosai sannan ta yi wanka ta ɗauro alwala sannan ta fito.
Doguwar riga ta saka tana jin ƙuna a ranta, ta tabbatar da a gidan aurenta ne mijinta na Sunnah ne da yanzu yana nan yana tausaya ma ta da lallaɓa ta kuma lada za ta samu. Amma wanan ga tarin zunubin da ta kwasarwa kanta, duk a dalilin soyayyar Fahad ta kai ta ga wanan halin.
Sallah ta gabatar bayan ta idar ta mike dama ita ba mai yawan yin addu'o'i da azkar ba ne, ballanta karatun Alkur'ani. In da suka sha banban da Nadra Kenan. Domin Nadra akwai yawan addu'a da azkar da karatun Alkur'ani. Amma Sidra tana idar da sallah za ta tashi.
Tana cire hijabinta sai ta hau saman gadon ta kwanta tana tunani.
Umma ce ta turo kofar ɗakin ta shigo. Ba ta yarda sun hada ido da Umma ba don kar ta gane ta yi kuka.
"Sidra."
Cewar Umma tana zama bakin gadon.
"Na'am Umma."
"Ɗazu na zo na sanar da ke za mu fita da Ammi sai na yi knocking ba ki bude ba."
"Eh Umma na yi barci ne, sannun ku da dawowa."
"Yauwa sannu. Na tambayi ma su aikin gidan sun ce ba ku fito kin ci abinci ba lafiya?"
"Umma na ƙoshi, na ci snacks dake cikin fridge."
"Amma ba za ki ci abinci ba."
"A'a Umma na ƙoshi ."
"Akwai abun da ke damun ki."
"Ba komai Umma ina lafiya."
"Sidra."
"Na'am Umma."
Ya kamata ki shiga hankalin ki ki nutsu, hakika ina cikin damuwar hukuncin da mahaifinki ya yanke na cewa nan da wata ɗaya zai aurar da ke ga duk wanda ya ci karo da shi a ƙauyen su. Shawara ta ki fito da miji kafin lokaci ya kure ma ki. "
"Umma duk samarin da suke cewa suna so na na wulaƙanta su, na kore su na yi masu gargaɗin na fi karfin su Umma. Har sai da ta kai ta kawo ana shakkar tara ta da maganar so. Ba wanda yake so na yanzu duk na watsa su saboda Fahad. Umma ba zan ɓoye ma ki ba har yanzu ina son Fahad kuma zan iya aikata komai don na same shi. Don wallahi Umma sai Nadra ta bar mun gidana da mijina."
"Subhanallah!"
Hawaye ta goge tana huci.
"Wai ke ba za ki taba canzawa ba! Ke a matsayin ki na musulma ba za ki yarda da ƙaddara ba.?"
"Ƙaddara! Ai Umma da tuntuni ƙaddarar ta zo ta hana ni haɗuwa da Fahad, sai da muka haɗu sannan ta ce za ta raba mu, ƙaddarar ma haƙuri za ta yi ta bar ni da shi wallahi."
Da mamaki Umma ke kallonta.
"Anya kanki daya kuwa?"
"Umma komai ta faru komai ya lalace an mai matakin da zan iya tunzura Allah wallahi. Ba zan sadaukar da mutunci..."
Kasa ƙarasawa ta yi don kada Umma ta gane ta aikata wani abun. Umma mamaki take yi ta ɗauka Sidra ta yi sanyi ne, ashe halinta yana nan ba abun da ya sauya.
"Kina ji na ko?"
"Eh ina ji."
"Wanda ya bar wani abu da zuciyarsa ke so saboda Allah, Alkah zai musanya masa da abin da ya fi alheri a duniya da lahira. Idan zuciyarki tana son wani abu, amma Allah ba ya so, sai ki danne son zuciyar, ki hana kanki, ka fifita umarnin Allah da na Annabin sa a kan son ranki, to Allah zai saka maki da abin da ya fi shi alheri. Zai cika zuciyarki da imani, ya ba ki farin ciki da kwanciyar hankali da albarka a tare da lafiya a jikinki. A lahira, kuma Allah zai ba ki lada mafi girma da daukaka, wato Aljanna. Wannan alƙawari ne tabbatacce, babu kokwanto a cikinsa. Duk wanda ya gwada hakan da zuciya mai tsarkakakkiyar niyya, zai ga tasirinsa a rayuwarsa. Ki tsarkake niyyarki saboda ALLAH kawai, za ki ga abin mamaki daga falalarsa. Amma wanda ya ji tsoron tsayuwa a gaban Ubangijinsa, kuma ya hana zuciyarsa bin son rai, to lalle Aljanna ita ce makomarsa.
ALLAH Ya sa mu cikin waɗanda suke fifita yardarSa a kan son zuciyarsu, ya azurta mu da daidaito a duniya da rabauta a lahira."
_Sady baby_
Sam ba ta lura da cewa akwai motar da take bin ta tun da ta bar wajen Mallam da Sidra ba. Har ta kawo Sidra gida yana bin ta har ya zagaya gaban gidan sannan ya bi Sady baby a baya.
Tana shiga layin unguwar su kafin ya karasa gida ya sha gabanta da mota. Ba shiri ta taka burkin motar.
Ya fito a fusace daga cikin motarsa sai huci yake yi.
Sady baby tana fitowa daga motarta da niyyar yin tsiwa, amma ganin wanda ke gabanta da yanayin fuskarsa ta sa gabaɗaya gaɓɓan jikinta yin sanyi.
Tas tas ta ji saukar maruka biyu a fuskarta wanda har ya da ta wuntsila ta faɗi ƙasa. Wani gishiri-gishiri ta ji a bakinta wanda hakan alama ce ta cewa bakinta ya fashe har ya fitar da jini.
Kallon sa take yi sai numfashi yake yi kamar matashin ɓauna.
"Ashe rashin imani ki har ya kai haka, anya ke mace ce kuwa ? Ina karin maganar da kuke yi cewa ciwon ƴa mace na ƴa mace ne?"
"JB ni ka mara??"
"An mare ki, wallahi ji nake ma kamar na kashe ki kowa ya huta da annoba."
"Au ni ce ma annobar? Sakayyar da za ka yi ma ni kenan?"
"Akan me za ki yi ma ni haka? Akan me za ki kawo ma ni mace verging bayan ba haka muka yi da ke ba. Cewa kika yi yarinyar nan ita ma ƴar hannu ce tana mu'amala da maza, wanan dalilin ya sa na amince na yi ma ki wannan aikin ashe ba haka ba ne, yarinyar nan cikakkiyar budurwa ce ba ta wani ɗa namiji da ya taɓa sanin ta sai ni. Akan me za ki lalata rayuwarta me ta yi ma ki haka da zafi?"
Kafin ya yi wani magana wayarsa dake cikin aljihun wandonda ya yi ruri. Ya duba mai kiran wayar, ganin Yayansa ya yi tsuki sanan ya ɗaga.
"Meye kuma?"
"To mara mutunci ka zo yanzu ina son ganin ka."
Muryar mahaifiyarsa ya ji saɓanin na Yayansa da ya yi zato."
Kashe wayar kawai ya yi ba tare da ya amsa ma ta ba.
Kallon Sady baby wacce bakinta har ya kumbura ya yi sannan ya fara magana cikin kakkausar murya.
"Ki jira haɗurmu da ke."
Daga haka ya shiga motarsa ya yi ma ta key, sai da ya buɗe Sady baby da ƙura sanan ya bar wajen . Kuka take son yi amma bakinta ya kumbura ya kasa motsa shi sai hawaye kawai take yi .
Tashi ta yi daga faɗuwar da ta yi, ganin har an fara kallonta jama'a ma su wucewa.
Da ƙyar ta iya jan motar tana hawaye tana jin zafin abun da JB ya yi ma ta. Sai dai ba ta yi mamaki ba, dan idan ta tuna waye shi idan ransa ya ɓaci.
JB. Cikakken sunansa shi ne Jabeer cikakken sunan sa. Wani sangartaccen ɗan ma su kuɗi ne a garin Kaduna. Mahaifinsa hamshaƙin ɗan kasuwa ne da yake kasuwanci har a kasashen waje. Sunan mahaifinsa Alhaji Kamil sai mahaifiyarsa Hajiya Karima. Su biyu iyayensu suka haifa yana da Yaya namiji mai suna Munnir. Tun tasowar Jabeer mahaifinsa ya sangarta shi sosai, saboda son da yake yi ma sa. Ko mahaifiyarsa tana kokarin ganin ta ba shi tarbiyya mai kyau amma son da mahaifinsa ke ma sa yake ganin kamar tana takura na yaronsa. Har yake ganin ba ta son Jabeer kamar ba ita ta haife shi ba. Don ba wanda ya isa ya yi ma sa faɗa ballantana duka, sai abun da ya ga dama yake yi. Hatta Yayansa Munnir bai isa ya ma da faɗa ko wani abun ba take zai kai kara wajen Mahaifinsu wanda shi kuma zai yi wa Munnir faɗa ya goyi bayan Jabeer. Karshe mahaifin nasu ya dauke shi ya kai kasar waje ya yi karatu a can sai ya gana saboda takurar da ake yi ma sa. Don baya son a kira shi da Jabeer dai dai JB.Wanan tafiyar ta kara lalata tarbiyyarsa bai ma tsaya ya yi karatu ba sai shashanci da harkar neman mata. Dole ta sa mahaifiyarsa ta je ta dawo da shi don dole.
Driving yake yi yana jin kukan Sidra na dukan dodon kunnensa. Bai taba nadamar abun da ya aikata ba sai wanan karon. Ko don bai taba mu'amala da cikakkiyar budurwa ba ne sai kanta ya san budurci. Don duk ƴan matan da ya yi mu'amala da su to sune suke kawo kansu har wajensa. Amma kanta ya yi wa mace dole ba tare da sanin budurwar ba ce . Abokin Sady baby ne shi JB tun da ta ji labarin yadda yake sakarwa mata kudi bai san zafinsu ba ya sa ta shiga rayuwarsa. Suka zama abokai, kuma yana sakar ma ta kuɗi sosaiz har motar da take hawa da gidan da take zaune shi ya ba ta su.
Dalilin abun da ya haɗa su da Sidra kuwa roƙonsa ta yi ya taimaka ya yi ma ta abun da take so, don ce ma sa ta yi Sidra za ta raba sunna ita kuma tana son ta dakatar da ita, ya yi basaja a matsayin Mallam su raina ma ta hankali kada ta je wajan wanda zai raba auren da gaske. Ta tsara abun da zai faɗa wa Sidra. Da ƙyar ya yarda akan cewa zai yi , ta samo gida da komai ta tsara ta kawo shi gidan sannan ta kira Sidra akan ta zo su tafi.
_Ma'eesha_
Tana kwance saman gadonta bayan barcin ya sake ta sai kuma ciwon kai ya ma ta sauki shi ma.
Ta bude idanunta da suka yi ma ta nauyi. Saman ɗakin ta fara kallo sannan ta kalli kofar ɗakin. Ganin ƙofar ɗakin a rufe ya sa ta lumshe idanunta . Daidai lokacin da Nurse ta shigo cikin ɗakin.
"Assalamu alaikum kin tashi?"
"Wace'alaiki salam
warahmatullah."
"Wace'alaiki salam warahmatullah."
"Ƙanwsta kin tashi."
"Na tashi sannu da ƙoƙari da ni."
"Wani kokari? Ai wanda ya kawo ki yanzu ya ba mu dubi ɗari ya ce duk abun da kike bukata a siya ma ki ga kuɗin nan a hannuna, ko na ba ki ki rike a hannunki?"
Shiru ta yi tana kallon kuɗin bandir ɗin dubu ɗaya ne ta fito da shi daga cikin handbag din ta. Sannan ta ɗauko wani dubu ɗarin ta ce .
"Wannan kuma nawa ne ya ba ni kyauta. Gaskiya yana da kirki ya kike da shi ne."
Ta yi maganar tana janyo kujera ta zauna tana farin cikin kuɗin .
"Me da me kike bukata a siya ma ki?"
"Ba na bukatar komai. Amma ki ciro dubu talatin ki ba Ni zan yi wani abun da shi."
"Okay ."
Ta yi maganar tana ciwo kuɗin, ga kirga dubu talatin fa sannan ta mika ma ta ."
"Na gode ."
Ƙadan pillow ta saka kudin sannan ta kwanta daidai lokacin da ya shigo da sallama. Ciki-ciki ta amsa yayin da Muryar Nurse din ga ya cika dakin ta amsa tana washe baki.
"Barka da shigowa Yallaɓai."
"Barka."
Buɗe idanunta ta yi tana kallon yadda yake ta kowa cikin ɗakin cikin takunsa na ƙasaita. Tana tuna yadda yake dogara sanda yana tafiya kamar nakasashshe. Yanzu ga shi yadda yake tafiya irin na lafiyayyun maza. Ba abun da ke ma ta zafi kamar idan ta tuna wai ranar juma'a ɗaurin aurensa.
Juyar da kanta ta yi ganin hawaye na shirin zubo ma ta.
Bari na ba ku wuri Yallaɓai ."
Da sauri Ma'eesha ta rike ma ta hannu tana girgiza kai Ammar a'a .
Ganin haka ya sa ya ce .
Ta zauna ba damuwa, duk da ba haka ya so ba. Ya so ya yi magana da ita sosai .
"Ba wata matsala ko?"
"Ba komai sir, yanzu za'a kawo na ta abinci ta ci sai na ba ta magungunan ta."
"To ba damuwa bari na je masallaci daga nan akai wanda zan je na gani, amma nan fa awa daya in sha Allah zan dawo . Ki kula da ita sosai ."
"In sha Allah, a dawo lafiya."
Daga haka ya nufi kofar fita, bayan ya bude kofar sai da ya juyo ya kalle ta sannan ya fice .
Yana fita ta nufi bathroom ta ɗauro alwala ta fito. Sallar azahar ta gabatar.
Ganin Nurse din na cewa za ta kawo ma ta abinci ya sa ta ce ma ya ta bari zuwa anjima. Don ita ta san me ta shirya .
"Aunty akwai nisa nan da kasuwa?"
"Ba sosai ba nisan."
"To don Allah ina son ki siyo ma ni wani hijabi ne."
"Ba damuwa wani kala."
"Fari nake so."
"To bari na je na dawo, dama na tashi aiki wanda ya kawo ku ne ya ce na zauna na kula da ke ya biya ni."
Daga haka ta fita . Wanda hakan ya ba Ma'eesha damar tashi daga saman sallayar da ta idar da sallah.
Takalmi ta saka ta karasa wajan gadon ta cire kuɗin da ta amsa dubu talatin ta fice daga cikin dakin da sauri. Tana addu'a Allah ya sa kada ta hadu da Dr ko Jalaluddeen.
Haka take tafiya kanta a ƙasa kada wani ya ganta ya gane ta. Cikin ikon Allah har ta fito daga asibitin ba wanda ya gane ta.
Tana fita cikin asibitin ta rasa ina za ta je. Don ba ta da wajan zuwa, ba za ta iya komawa gidan aurenta ba. A fahimtar ta Jalaluddeen baya son ta, dole aka yi ma sa aka aura ma sa ita ba tare da yana so ba. Kuma bai ki tayin Dady da Mamy ba. Shi ya sa ya ajiye ta tsawon watanni da suka yi babu abu dayya da ya yi ma ta wanda za ta ce yana son ta. Bai nuna ma ta alamar so ba ko kaɗan, shi ya sa rayuwar aurensu ya daga banban da rayuwar auratayya da ta saba gani. Ashe yana nan yana neman macen da zai aura ita kuma ya mayar da ita banza. Kodayake ba laifinsa ba ne, an na shi ita a arhar banza bai sha wahala ba ya same ta, babu lefe babu kuɗin gaisuwa ko baiko dai kuɗin sadakin da aka ce ya bayar da dubu uku, wanda ko kaza ce za'a aura ma sa ta fi karfin dubu uku a yanzu ballantana mutum. Kuka ne ya ƙwace ma ta ta saka bayan hannunta ta goge.
'Tabbas ba in da zan tafi a halin yanzu, ban isa na je gidan Mahaifina ba. Haka kuma ba zan iya komawa gidan mijina ba. Don na tsane shi fiye da kowa da komai a halin yanzu. Ba na da kowa ban san inda dangin mahaifina suke ba na tafi wajensu na huta da wajan rayuwar. Na tsani zaman garin nan dole na tafi ko ma ina ne, barin garin nan ya zama ma ni dole ko zan sami sassauci.'
Ta yi nisa cikin tafiyar da take yi ashe har ta kai titi ba ta sani ba. Kai tsaye ta hau saman titi ba tare da sanin ina take jefa ƙafa ba.
Ihun jama'a ta kuma ƙarar taka birki da ta ji ne ya sa ta dawo cikin hayyacinta. Sai dai kafin ta yi wani yunƙuri har motar ta ɗan ture ta ta fadi ƙasa.
Rintse isanunta ta yi gabanta na tsananta faɗuwa.
" Ke wata irin mahaukaciya ce za ki hau titi kai tsaye? Yanzu da wani abu ya faru fa?"
Cewar Captain Kabeer yana kallonta a fusace. Barrister Haidar ne ya fito daga cikin motar cike da kulawa yake kallonta .
"Sannu baiwar Allah ba ki ji ciwo ba ko?"
Ɗago da dara-daran idanunta da suka canza launi zuwa ja ta kalle shi. Sai da zuciyarsa ta harba da ƙarfi sakamakon kallon fuskarta. Cikin sanyin murya ta ce.
"Ku yi haƙuri don Allah, ba na cikin nutsuwata ne. Amma Allah ya kare ba abun da ya same ni."
Da ƙyar ta iya jijina ma ta kai, tashi tayi ta kalli tsaddadiyar motar da ta kusan kaɗe ta.
Cike da takaici Kabeer fara magana .
"Dan Allah ka zo mu tafi Yaya, ana jiran mu fa, nan da gudan marayun ma akwai tazara."
Bai tanka ma sa ba ya shiga motar ya tayar suka bar wajen. Don har an fara cunkoson ababen hawa.
Ma'eesha kam mai nape ta tare ta ce ya kai ta tashar mota.
"Wace tasha za mu je Hajiya?"
"Kowace tasha da ake hawa mota zuwa garuruwa."
"To bisimillah shigo mu tafi."
Shiga cikin nape ɗin ta yi ya dauki hanyar kai ta tashar mota kamar yadda ta buƙata.
Barrister Haidar bayan sun bar wajan suka nufi hanyar gidan marayun da aka sanar da su cewa su je mahaifinsu na hanyar shi da Sanata
Zuwan su ya yi daidai da zuwan su sanata da mahaifinsu. Kusan a tare motocin nasu suka shiga cikin gidan marayun .
In da aka tarbe su cikin girmamawa kasancewar an ga sanata a tare da su.
Har office din shugaban aka je tare de Maude.
Nan aka yi ma sa tambayoyi ya bayar da amsa da ranar da aka kai yarinyar da kayan dake jikinta da komai sai da ya bayar .
Babu ɓata lokaci aka fara bincike don wanda ke kan kujerar a yanzu ba shi ba ne a lokacin da aka kawo ta. Don wancan shi wancan ma ya rasu wani ne yanzu da ke kai.
Da ƙyar aka gano file din da bayanai kamar yadda Maude ya faɗa. Sai dai komai da tsari suke yi hatta ranar da aka dauke ta da wanda ya dauke ta yana cikin file ɗin.
"Waye shi wanda ya dauke ta?"
Yana daya daga cikin masu tallafawa marayun gidan nan dansa ya aura wa ita."
Cewar shi shugaban.
"Amma yanzu baya ƙasar nan yana jinya a kasar Egypt tsawon lokaci. Shi da matarsa , Amma shi Ɗan sa yana garin nan na san gidansa."
"Ba damuwa mu tafi gidan Ɗan nasa."
Motoci uku ne suka haɗu na sanata biyu da kuma na Haidar da suka zo da shi daga Katsina. Kai tsaye suka kama hanyar zuwa gidan Alhaji Ibrahim Khalil.
_Nadra_
Kallon Farida da take yi ma ta wani kallon tsana ta yi na wasu sakanni sanan ta dauke kai. Tana ganin rashin dacewar abun da ta yi na shigo ma su gida kai tsaye ba izinin har cikin falo.
"Farida!'
"Na'am Yaya Fahad."
Ta faɗa a shagwabe.
"Wani irin dabbanci ne za ki shigo ma ni gida kai tsaye ba neman izini."
Kuka ta saka ma sa ba tare da ta ce komai ba.
"Nadra dai barin wajen ta yi ta ba su waje, don ta ga kallon da take yi ma ta. Dama ta san ba ƙaunarta take yi ba, kuma ta ji labarin ita ma son Fahad take yi shi ya sa take zaune a gidan tsawon shekaru sa saboda shi.
Tana ganin Nadra na barin wajen ta fara magana .
"Yaya Fahad yanzu shi ne za ka dinga yi ma ni faɗa a gaban matarka ko?"
"Wani dalili zai saka ki shigo ma na gida kai tsaye Babu izini."
"Yanzu dan zan shiga gidan ka sai na nemi izinin. Ai da yanzu Ni ce a gidan da ba don wanan..."
"Ya isa!"
Ya dakatar da ita don ya san halinta yanzu za ta iya cin mutunci ga Nadra.
"Kuma ina nan akan baka na sai ka aure ni."
"Kawai ba, ki ɗebo kayanki ki zo ki zabi daki daya mu zauna matsayin mata da miji kin ji ko?"
Jin maganar banza da ya faɗa ma ta ne ya sa ta kau da kai tana magana kasa-kasa.
"Da sannu za ka shiga hannuna Wallahi."
"Me kika ce?"
"A'a ba da kai nake yi ba."
Wayarta ce ta yi ringing.
"Hallo Mumsy ga shi."
Tun da ya ji ta ce Mumsy ya san ƙanwar mahaifiyarsa ce wato mahaifiyar Farida. Tun da aka yi aurensa da Nadra bai yi magana da ita a waya ba. Don ko ya kira ta ba ta ɗagawa tana fushi da shi saboda bai auri ƴar uwarsa ba ya fita waje ya auri bare.
Farida ta mika masa wayar, ya karba ya kara a kunnensa.
"Assalamu alaikum."
"Wa'alaika salam."
"Ina wuni Mama."
"Lafiya ya kake ?"
"Alhamdulillah."
"Dama ƙanwarka ce Farida za ta je karatu America tun da auren bai yiwu ba ta koma makaranta. To sai na ga tun da kana da gida a America sai ta zauna a gidanka hankalina zai fi kwanciya. Ba na son. Ta zauna in da ba wanda zai tsawatar ma ta ko da ta yi ba daidai ba. Amma na san za ka kula da ita ta yi karatu yadda ya kamata ."
Shiru ya yi yana nazari kafin ya ce .
"To ba damuwa Mama."
"Yaushe za ka koma ?"
"Sai next week."
"To tafiyar za ta yi ma ku daidai kenan. Sai ku tafi tare ."
"Allah ya kai mu."
Sallama suka ya mika ma Farida wayar ya haura sama. Farida na ganin ya haura ta yi kasa da murya ta ce .
"Mama ya ya haura sama."
"To yanzu sauran aikin ya rage na ki, ba sai na koya ma ki ba, idan ya so wanan karon ma ki tsaya shashanci kada ki yi amfani da damarki akansa."

Page8️⃣5️⃣
*End of book 1. Last free pages*
*To yanzu sauran aikin ya rage naki, ba sai na koya maki ba, idan ya so wannan karon ma ki tsaya shashanci kada ki yi amfani da damarki."
"Mama ba zan yi sake ba, dama ai saboda muna gida ɗaya ne ga mahaifiyarsa ga mahaifinsa, Sanan kuma ka ƙanwarsa Rumaisa hakan ya sa na nake ɗaga kafa ba na iya yin wani abun. Sannan kuma shi Fahad ɗin yakan share ni kamar bai gane me nake nufi ba. Sai da na fito na nuna ma sa irin son sa nake yi ma sa ne yake cewa wai Sidra zai aura. Mama sai da na yi kamar na bar gidan na dai daure na zauna, har aka fasa auren bayan gudun Sidra na saka rai zai aure ni shi ne matsiyatan iyayennta suka sura ma sa ƙanwar. Wallahi wanan karon Mama ba zan saurara ba ko kaɗan. Dama ba idan kowa akan mu idan mun tafi American daga ni sai shi wallahi idan har ban ja ra'ayinsa zuwa gare ni ba na daina amsa sunam mace."
Sautin saukowa ta ji daga sama ya sa ta yi wa mahaifiyarta ta kashe kiran wayar .
Nadra ce ta karaso wajen ta kalle ta da murmushi a fuskarta .
"Aunty Farida ina wuni?"
Banza ta yi da ita tana danne-danne a waya tana taunar cingam a bakinta.
A takaice tunanin Nadra ta ɗauka ba ta ji ba ne, don haka ta sake gaishe ta a karo na biyu.
"Mtswww"
Tsukin sa ta yi ne ya tabbatar ma ta da cewa ta ji ta Msawar. E b za ga yi ba. Don haka sai ta juya ta koma sama.
Da harara ta bi ta kafin ta ce.
"Wallahi sai na yi maganinki sai zama da Fahad ya gagare ki."
Ta faɗa da karfi don ta ji ta. Kuma ta yi nasara, domin maganar ya shiga kunnen Nadra. Murmushi kawai ta yi. Dama ta zo ne ta kawo ma ta abin sha da abinci. Amma tun da ta ga take-takenta ta san ba shan komai za ta yi idan ga ba ta ba.
Don haka ta shige ɗaki ta yi kwanciyarta. Don dama daiurewa kawai take yi ciwon kai ke damunta.
_Jalaluddeen_
Yana shigowa ɗakin ya ga Nurse din da ta bari ta kula da Ma'eesha hankalinta a tase.
Kallo ɗaya ya yi ma ta ya gane tashin hankali da take ciki.
"Me ya faru?"
"Yallaɓai wallahi ashe dabara ta yi ma ni tana son fita ne."
"Ban gane be meke faruwa ?"
"Cewa ta yi na ba ta dubu talatin cikin kuɗin da ka bayar. Sanan ya ce na je kasuwa na siyo ma ta hijabi. Ko da na dawo daga kasuwar ban ganta ba. Ba ta cikin toilet na zagaye gabaɗaya asibitin nan ba ta ciki. Na sanar wa Doctor shi ne da ya yi bincike ya gano da ƙafarta ta fita bayan fitar da na yi."
Bai iya cewa komai ba ya juya ya fita daga cikin ɗakin.
Wajen Doctor ya je don neman karin Bayan. Doctor ya nuna ma sa yanda ta fita ta hanyar CCTV camera da ya duba. Isso Jalaluddeen ya zaba wa computer yana kallon yadda take tafiya kanta a sunkuye alamar rashin gaskiya.
Godiya ya yi ma sa sanan ya fito ya nufo inda ake parking motoci in da yanar yaronsa na jiransa.
Gefen wajen me zaman banza ya zauna sannan direban ya ja motar suka bar wajen.
Gidan da yake zaune tare da Ma'eesha ne ya umarci direba ya kai shi.
Ko da direba ya yi parking kofar gidan Jalaluddeen ya fito ya shiga cikin gidan.
Ba kowa gidan kamar yadda ya bar shi.
Sai wayar Ma'eesha dake ajiye a tsakiyar ɗakin. Komai yana zaune a mazauninsa kasancewar ta mace mai tsafta.
Wayarta ya durƙusa ya ɗauka, sanan ya karewa ɗakin kallo na wasu daƙiƙu sannan ya fito cikin sanyin jiki.
Ya san ba za ta dawo gidan ba kasancewar tana fushi da shi. Har ta yi furucin saki da ta tsani ganinsa a rayuwar ta fiye da kowa. Hakan ya za na ma sa alamun cewa ba za ta zo inda yake ba. Sai dai to ina za ta tafi?"
Abun da ya tsaya ma sa a rai kenan. Mutum ɗaya ce ta faɗo ma sa a rai wato Nasreen.
Don haka ya fita da sauri ya bude murfin motar wajan zaman direba. Alamar ya fito ya yi ma sa da hannu. Ba musu ya fito. Jalaluddeen ya zauna mazaunin direba ya yi wa motar key suka bar wajen.
Waɗanda da suka ga shigar da fitar sa mutane biyu suka bi motar da kallon mamaki.
Kai tsaye ya ɗauki hanyar gidan su Nasreen yana sarrafa motar cikin ƙwarewa. Yaronsa dake zaune a gefesa yana son ya yi maganar cewa uban gidansa ya rage gudu amma ganin fuskarsa kawai ya ba shi tsoro, ya kasa yi ma sa magana. Domin yanayin da ya ga fuskarsa yanayi ne da tun da yake bai taɓa ganinsa ciki ba.
A kofar gidan ya yi parking ya fito daga cikin motar. Ƙaramr door din gidan ya yi knocking. Maigadin gidan ya leƙo ya kalli Jalaluddeen ya kalli motar da ya zo da shi ne ya gane ba ƙaramin mutum ba ne.
Hannu Jalaluddeen ya ba shi suka yi masabaha. Sanan ya nemi da wajen Nasreen ya zo.
"To Yallaɓai bari a sanar da ita zuwanka."
Ya koma ciki ba jimawa ya dawo ya sanar da shi cewa tana nan zuwa.
Ba jimawa ta fito ta zuba wa bayansa idanu. Kasancewar ya juya baya yana tsaye jikin motar, ya ɗan kwantar da kansa a saman motar.
Duk da cewar ba ta san ko waye na amma ƙirar jikinsa kaɗai zai tabbatar ma ka da cewa tsayayyen namiji ne.
"Assalamu alaikum."
Ta yi ma sa sallama. Ya amsa yana juyowa suna fuskantar juna.
Da mamaki take kallonsa yadda ya zo kai tsaya ba tare da ɓadda kama da yake yi yana raina wa ƙawarta hankali ba.
"Lafiya me ka zo yi nan ƙofar gidan?"
"Ƙawarki nazo nema, na san ba in da za ta zo da ya wuce nan."
"Tofah! daɗi na da gobe saurin zuwa, an zo wajen kenan, ta ga hanya yau ta gane shayi ruwa ne. Tabbas hakan ya ma ni dadi da ta gane ko kai waye, Alhamdulillah ko ba komai yanzu za ta tabbatar da cewa ba karya nake yi ma ta ba gaskiya nake faɗa ma ta. Kai wanda take kallo kamar waliyi kai ne ka yi ma ta karya."
Girgiza kai ta yi tana murmushi.
"Sai dai na tausaya ma ku daga kai har ita ababen tausayi ne, yanzu na san tana can cikin damuwa da bakin ciki, yadda ta tsani ƙarya da yaudara da cin amana. Ga Jsji ta kama ka da aikin aikata ma ta su. Tabbas na san shawo kanta ba abu ba ne mai sauƙi. Amma ko ba komai na yi farin cikin gaskiya ta yi halinta kuma..."
"Ya isa, idan kin san inda za ta iya zuwa bayan wajenki to ki faɗa ma ni."
"Ban sani ba, ka je can ka neme ta, yadda ka saka ta cikin halin da take ciki sai ka nemo ta ka shawo kanta."
"Idan har kin san tana cikin gidan nan ki fito ma Ni da ita, idan kuma ba haka ba, kika bari na tabbatar tana ciki wallahi sai kin yi nadamar ƙaryar da kika yi ma ni."
"Oh Allah, me zai saka na yi ma ka karya? Kodayake duk abun da mutum yake yi sai ya ɗauka kowa ma shi..."
Tsawa ya daka ma ta wanda sai da hantar cikinta ta kada.
"A halin yanzu raina a ɓace yake kada ki tunzura ni. Ina matata na tambaye ki."
"Wallahi ban san in da ta tafi ba."
Ganin yadda ta tsorata da yanayin ta ya tabbatar ma sa da gaskiya ta faɗa. Don haka ya shiga motarsa ya yi ma ta key a guje ya bar ƙofar gidan.
Tafiya kawai yake yi ba tare da ya san in da zai ganta ba.
_Alhaji Sulaiman_
Horn motocin da sauke ciki suka yi a ƙofar gidan Daddy. Maigadi ne ya leƙo. Ganin manyan tsadaddun motocin da suka zo ƙofar gidan ne ya sa da sauri ya bude gate. Motocin suka fara shigowa cikin gidan .
Daidai lokacin da Laila ta fito za ta je unguwa. Ganin irin motocin ya sa ta fadin .
"Wow."
Haidar da kabeer suka fara fitowa, ta zuba ma su idanunta ko ƙyaftawa ba ta yi.
Alhaji Sulaiman da abokinsa Sanata suka fito tare, sai Maude da jikinsa ya yi sanyi, sai kuma daya ma'aikacin gidan marayun wanda ya biyo su.
Barrister Haidar ne ya tura Maigadi a je a sanar da maigidan yana da baƙi.
Daddy dake zaune da Mummy a falo sai kuma Jamil dake zaune a carpet.
Maigadi ya shigo ya sanar da Daddy zuwan baƙin. Kafin Daddy ya yi magana har Mamy ta leka ta window. Ganin manyan motoci ne ya saka ta jijina kai tana yi wa maigadi magana.
"Ka yi sauri ka shigo da su manyan mutane ne ba'a barin su a barin su haka."
Zama ta yi tana jiran shigowar su.
Da sallama suka shigo cikin falon, Daddy da Jamil suka miƙe suna yi ma sa sannu da zuwa . Suka shigo kasancewar set biyu ba kujera ne a falon don haka duk suka zauna akan kujera. Laila ma fasa fita ta yi ta shigo ciki din ganin abub da zai turewa buzu naɗi.
Bayan an gaggaisa Mamy ga sa mai aiki ta kawo ma su ruwa da abun sha, sai ma'aikacin gidan marayun ya fara maganar abun dake tafe da su. Sannan ya gabatar da dangin Mummy ga su nan sun zo suna bukatar ganin ta ita da ƴaƴan da ta haifa. Gabaɗaya falon shiru ya yi kamar ruwa ya ci su. Daddy jikinsa ya gama yin sanyi.
"Wato tabbas ni ce na auri ƴar uwarku kamar yadda kuka damu tabbaci hakan daga gidan marayun. Kuma mahaifina ya ɗauke ta ne bisa ƙa'ida. Muna zaune da ita har Allah ya albarkace mu da samun haihuwa, muka haifa ƴa mace mai suna Ma'eesha. Wanda a yanzu Ma'eesha tana da shekaru goma sha takwas zuwa sha tara. Kuma sai dai ina mai matukar ba ku hakuri ƴar uwarku ta rasu watanni huɗu da suka wuce."
"Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un."
Kalmar da suke furtawa kenan lokacin da suka ji labarin mutuwar. Jikinsu ya yi sanyi musamman Alhaji Sulaiman da ƴaƴansa.
"To ina ƴar da ta haifa?"
Nan ne kowa ya yi shiru don ba mai bakin ba da amsa a cikinsu. Sai da Alhaji Sulaiman ya sake tambaya a karo na biyu sannan cikin sanyin jiki Daddy ya ce
"Ban san in da yake ba?"
"What? Wanan ma ai zancen banza ne!"
Kabir ya faɗa yana miƙewa tsaye. Ita kuma Laila da take tsaye ta bude baki cike da tsiwa ta ce.
"Kamar ya zancen banza, nan ba wanda ya san inda take ku je can ke neme..."
Kafin ta kai karshen zancen da take son faɗa ta ji saukar lafiyyaen mari wanda ya sa ta wuntsilawa ta faɗi, wani duhu take gani sannan da wani sautin shuu da take ji a kunnenta jin ta da ganinta ya ɗauke na wuccin gadi.
Ƙaramar mara kunya, na sake jin kin yi magana a wajan nan."
Gabaɗaya falon suka juya suka kalli Captain Kabeer wanda ya yi ma ta marin.
"Mamy ina kike ba na ganin komai sai duhu."
"Na shiga uku daga magana kake neman makantar mun da yarinya ka kashe ma ta kunne?"
A hankali ganinta ya fara dawowa ta sauke isanunta akan Kabeer wanda ko shakka babu ta san cewa shi ne ya mare ta.
Kuka take yi tana son ta yi wata maganar amma ta kasa.
"Alhaji ka yi ma ni cikkaken bayanin komai domin mu san in da za mu ɓullowa bakin zare.
Nan Daddy ya ba su labarin duk abin da ya faru bayan rasuwar mahaifiyar ma'eesha zuwa hukuncin da Mamy ta yanke na aurar da Ma'eesha ga makaho . Da yadda komai ya faru har zuwa ranar da makaho ya dauke ta suka bar gidan ba su sake saka su a idanu.
"Wani unguwa suke zaune?"
Cewar Alhaji Sulaiman da idanunsa suka kaɗa suka yi ja.
"Ba wanda ya san unguwar da suke, ko shi kansa ba wanda ya san in da yake."
"Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un."
"Amma ka ɗauki ƴa ka ba shi, ba ka san shi ba ba ka san unguwar da yake ba? Dole na shigar da kara akan ku."
"Wallahi ba llaifina ba ne, matata ta kawo shawara ni kuma duk da na ƙyamaci abun. A zuciyata amma na kasa hana ta. Duk hukuncin da ta yanke ba na iya cewa komai, duk da a zuciyata ina jin ba daidai ba ne amma ba ma iya cewa komai"
"Wanan matsalarku ce idan muka shigar da kara akanku za ku nemo in da take."
Mamy hankalinta ya tashi ta rikice .
Shiru Falon ya ɗauka kowa ya kasa magana, yayin da ake yi wa Mummy kallon zargi.
"Ko z mu iya ganin photon su?"
"Eh za mu samu."
Cewar jam'i ya nufi dakin da suke ajiye kayan ajiya. Don lokacin da Laila za ta koma ɗakin Ma'eesha fa zama duke kwashe kayan fa basu bukatar su. Suka kai can.
Bayan Wai mijina dawo da photon dake manne a bangon ɗakin Ma'eesha.sai wani guda daya na Ma'eesha tana sanye da hijabi ranar da ta yi waliamar saukar Alqur'ani mai girms.
Gabaɗaya suka zuba wa photon idanun.
Barrister Haidar ya mike tsaye yana cewa.
"Wallahi ita ce. Ita ce na gani ba kowa ba, ita ce wallahi na kusa kaɗewa da mota , har Kabeer na ma ta fadar ba ta da hankali ne. Ta ba mu hakuri ta tafi."
"Da gaske kake faɗa? To ina kuka ganta kuma ina ta nufa a lokacin.?"
"Wallahi ba mu sani ba, amma da dukkan alama tana cikin tashin hankali, yanayin ta ma ys nuns hakan, don idsnunta ma a kumbure suke."
"Ko zu mu tafi, amma ku sani da ka amsa za ku amsa kira daga kai har matarka, duk in da kuka kai yarinyar nan sai kin fito da ita. Idan kuma ba haka ba sai kunyi nadamar mafi muni a rayuwarku."
Daga haka suka fice daga gidan rai a ɓace..
_Ma'eesha_
Bayan mai nape ya sauke ta s tashar mota ne ta nufi cikin tashar. Wani ya ganta ya ce .
"Tafiya za ki"
"Eh."
"Okay wani gari za ki je?"
"Bauchi."
"Okay to yanzu ga motar da ke kan layi ba ta cika ba za ki ɗan jira kaɗan."
"Ba damuwa."
"Bisimillah ga wuri ki zauna."
Ya yi magana tana nuna ma ta wani benci dake gefe.
Ƙarasawa ta yi ta zauna saman bencin. Kifa kanta a saman cinyarta ta yi tana kuka kasa-kasa.
Abubuwa biyu ne suka taru suka cunkushe ma ta zuciya. Na ɗaya ƙwryar da ya yi ma ta na tsawon watanni ba tare da ya sanar da ita gaskiyar lamari ba. Na biyu kuma kishin auren da zai yi. Domin gani take yi ba sonta yake yi. A zaman da suka yi tare da juna. Domin a tunaninta ita ce take son sa amma ba shi ba. Bai ɗauke ta matar aure ba sai yanzu ne yake so ya auri wacce yske so. Sam ta kasa gane cewa yana gani tsawon watanni da suka yi a tare ba ta taɓa tunanin ba makaho ba ne. Sai yanzu wasu abubuwan suke zuwa ma ta akai.
Ranar da ta cire kaya a gabansa jikinsa ya dinga rawa kamar mazari. Wanda ko da ta tambaye shi cewa ya yi baya da lafiya ne. Sha surar jikina ne ya kiɗima shi. Da kuma idan za ta cire kaya sai ya yi saurin fita ya bar ma ta ɗakin. Har wata rana ya ce ma ta ta daina cire kaya a gabansa duk da ba ya gani. Sannan ranar da aka yi ruwan sama tana wanka har ta shiga rawar sanyi ta tuɓe kayan jikinta. Ba ta ɗan yana ɗakin ba tana lalube ta ci karo da shi har ya rungume ta ya yi kissing nata. Ga abubuwa da yawa da ya kamata a ce ya zarge shi amma ba ta yi hakan ba. Kuka take yi kasa-kasa.
_Haidar_
Yana rungume da photon Ma'eesha da na mahaifiyarta.
"Ka san Allah ko Kabeer yarinyar nan ita na gani na kusan kaɗewa da mota."
Captain Kabeer dake driving ya ce.
"To me ya sa ka bari ta wuce?"
"To wata hujja ne da ni da zan tare ta akan cewa ita muke nema? Duk da lokacin da na kalle ta sai da zuciya ta ta buga. Na ji wani abu a raina game da ita. Duk da cewar tana kama da Dada amma hakan ba yana nufin na ce lallai ita ba ce.
Ya yi magana yana kallon ta sosai. Fara ce doguwa ba ta da ƙiba. Duban manyan idanunta ya yi har zuwa dogon hancinta da karamin bakinta.
"Wallahi kamannin Dada ta ɗauka sai, wata kila ma tafi Fadar kyawu."
_JB_
Horn yake dannawa ba kakkautawa wanda duk wanda yake gidan kama daga ƴan gidan zuwa ma'aikatan gidan kowa ya san cewa shi ne ya dawo . Hatta maƙotarsu idan suka ji wanan horn na rashin mutunci sun san shi ne.
A guje maigadi ya wangale gate ɗin gidan dan kada ya ɓata lokaci JB ya tafka ma sa rashin mutunci kamar yadda ta saba.
A guje ya shigo cikin gidan, bayan ya yi parking dai da ya kwashe mintuna goma a cikin motar bai fito ba.
Ko da ya fito daga motar duk wanda ya kalle shi in dai ya san shi to ya san cewa yanayinsa ya canza da akwai abun da ke damunsa. Domin shigowarsa cikin gida ma kawai idan ka gani ka san cewa shi ne kaɗai ya fita Zakka a cikin gidansu.
Tura kofar Falon ya yi ya shiga kai tsaye ba tare da ya kalli cikin falon ba ballanta ya ɗan su waye a ciki. Kai tsaye ɗakinsa ya nufa ya tura ƙofar ya shiga ciki.
Mahaifiyarsa wacce suke kira da Mimi tana zaune a falon tana tattauna wata magana ita da Yayansa Munnir.
Da kallo suka bi shi domin sun ga yanayinsa ya sauya jikinsa a sanyaye yake.
"Kamar wani abu na damun Autana."
Nima haka na gani Mimi. Allah dai ya sa ba wata maganar ya ɗauko ta dame shi ba."
Cewar Munnir din cikin damuwa.
"Amin ya Allah, wallahi duk lokacin da Jabeer ya bar gidan nan ba na da kwanciyar hankali har sai na ga dawowarsa. Ga shi baya jin maganar kowa mahaifinsa ya riga ya ɓata shi duk yadda na so gyara shi abun ya ci turaz sai na gyara can sai ka ga ya ɓalle ta nan."
"Addu'a za ki cigaba da yi ma sa Allah ya shirya shi."
"Addu'a kam ina nan ina ta yi ma ku."
"Dare ya yi ya kamata ka je wajan matarka"
"Okay bari na je na ji meke damunsa kafin na tafi."
Ya tashi ya nufi ɗakin Jabeer, yana kwance ya yi ruf da ciki ba abun da ke ma sa yawo a kansa sai abun da ya aikata wa Sidra. Kukan ta ne ya ke ma da amsa kuwa a kunnenta, abu biyu ya tsaya ma sa rai . Na ɗaya bai taɓa mu'amala da cikakkiyar budurwa ba sai kanta. Na biyu kuma yadda ba da son ranta ba bisa tilas ta amince da hakan. Wanda shi dai dai mace ta kawo kanta da kanta wajansa, kuma ya san duk ƴan hannu ne sun saba, ita kuma fa? Me ya sa Sady baby ta yi masa ƙaryar ciwa ita ma ƴar hannu ce kada ya damu. Bai taɓa nadamar yin zina ba sai yau.
kusan a tare Yaya Munnir da mai aikin girkinsu suka nufi ɗakin Jabeer. Ita mai aikin gidan ta jera abincinsa a faranti za ta je ta kai ma sa. Tana shiga da sallama bai amsa ba hakan bai dame ta ba ta saba. Tana kokarin ajiye abincin sanan table dake gaban sofa ya daka ma ta tsawa.
"Uban waye ya ba ki iznin shigo min ɗaki?"
"Ka yi hakuri abincinka na kawo ma ka."
."idan ba ki ɗauke shi kin fita ba sai na tafka ma ki rashin mutunci banza jaka kawai"
Ta fita da sauri ta san shi idan ta tsaya jayayya zai iya kai ma ta duka.
"Assalamu alaikum warahmatullah"
Munnir ya yi sallama ya shiga. Bai amsa ba idanunsa a lumshe.
"Meke damunka duk ka canza?"
"Mallam dalla ka fitar mun daga ɗaki, bayan ka gama munafurcinka wajen Mimi ka haɗa ni da ita sanan ka zo kana tambaya ta, to ban sani ba!"
Nurmushi Munnir ya yi yana kallon ƙanin nasa yana cewa.
"Kai kullum maganarka ina baya ka a wajen Mimi, to ka sani ba abinda nake faɗa mara kyau a gare ka, ka canza halinka idan ba ka ga Mimi ta so ka fiye da kowa ba.".
Tashi tsaye ya yi yana yi na da wani kallon banza kafin ya ce
"Mallam fitar mun daga ɗakin munafu..."
"Tas" ya ji saukar mari a kumatunsa. Rintse idanunsa ya yi ya san ba kowa zai mare shi ba face Mimi ce.
"Wai me ya sa ba ka da mutunci ne?"
"Da kin ƙyale shi Mimi yana da damuwa na lura da hakan."
"Idan yana da damuwa sai ya sauke kan mutane? Tun yaushe mahaifinsa ya dawo kasar nan, yana dawowa shi ya fara tambaya. Ina ka je ne tun safe !?"
Bai tanka ma ta ba kuma baya da niyyar yin maganar.
Ta bude baki zata fara masifa Mahaifinsa ya shigo yana cewa .
"My son Ina ka je ne tun safe wayarka ba ta shiga?"
Ganin halin da suke ciki ne ya ce .
"Me kuma aka yi ma sa waye ya ɓata ma sa rai? Amma kun san ba na son ɓacin ransa a gidan nan ko? Me ya sa za ki yi ma sa faɗa hakan yaro ai ɗan hakuri ne."
Cike da takaici Mimi ta bar ɗakin. Munnir ya mara ma ta baya suka fice.
_Jalaluddeen_
Yawo kawai yake yi da mota s garin Kaduna ba tare da ya san in da zai nufa ba.
Gefen hanya ya yi parking ga yinwa dake ɗawainiya da shi, wanda rabon da ya ci abinci tun jiya da rana.
Kifa kansa ya yi a sitiyarin motar yana tunanin ina ya kamata ya tafi neman ta . Yau kadai gare shi, gobe dole ya koma Abuja bisa umarnin iyayensa.
Magana ya fara yi shi kadai kamar wani zararre.
"Ina kika tafi Ma'eesha, kewa kwanciyar hankalina, idan kina kusa da ni zuciyata tana samun salama. Ina godiya da Allah ya haɗa rayuwata da taki. Kullum ina kara son ki fiye da jiya. Murmushinki yana sa ranar tawa ta yi haske. Ba kyawunki kadai nake so ba ina son zuciyarki da kyawun halayenki. Ko da mun samu saɓani baya rage irin son da nake yi ma ki. Kece Aminiyata matar da nake son na raba rayuwata da ita har karshe. Ina alfahari da ke, kuma zan cigaba da kula da ke gwargwadon iyawa ta. Na gode da haƙurin ki da kuma ƙaunar da kika nuna ma ni. Ina so na zama wanda zai goge ma ki hawayenki tun kafin su zubo.Ina kike Ma'eesha?"
_Fahad_
Dawowarsa gida kenan ya zauna akan kujerar dake Falon sama. Wani karamin box ne a hannunsa ya ajiye gefensa. Fitowar Nadra kenan daga kitchen za ta shiga ɗakinta ta ji ya kira ta .
"Nadfah."
"Na'am yaushe ka ka dawo.?"
Ta yi magana tana karasowa inda yake .
" Zo ki zauna kusa da ni."
"Lafiya wanan kallo haka kamar za ka cinye ni?"
Ya janyo ta ya zaunar da ita saman cinyarsa.
"Ina kallon ni'imar da Allah ya ma Ni ne, wani lokaci har mamaki nake yi, me na yi da na cancanci samun mace kamar ki?"
Ta yi murmushi.
"Yau dai kana nema wani abu a wurina."
Dariya ya yi tare da cewa
"Ba komai nake nema ba, ina so ne kawai kisan cewa ina son ki ko da ban faɗa kullum ba zuciyata kullum tana fadin haka."
"Ni ma ina son ka."
"Ki yi ma ni alkawarin idan wani abu ya dame ki ba zaki yi shiru ba, ni ne abokin rayuwarki."
"Na yi ma ka alkawari."
Ya sumbaci goshinta. Sanan ya dauko wani karamin box din nan da ya dawo da shi ya ba ta .
Karba ta yi ta bude.
Ɗan kunne da sarƙa ne na gold, har da warwaro da zobe.
Zaro idsnunta ta yi sanan ta rungume shi tana cewa.
" Allah ya ba ni ikon faranta ma ka rai kullun."
"Amin ya Allah, Murmushin ki nake so na gani kowane rana."
Murmushi ta yi.
"Tare de Farida za mu je America."
Take murmushin dake kan fuskarta ta gushe.
"Ya dai ko akwai matsala ne?"
Murmushin karfin hali ta kirkiro tana cewa
"Ba komai Allah ya kai mu."
"Amin ya Allah. Don Mama ta ce ba ta yarda na bar ki a ƙasar nan ba tare da ke ba umarni ne ta ba ni."
_Mamy_
Gabaɗaya sai sintiri take yi a falon ta, sakamakon rashin ganin Ma'eesha. Don Jamil ya faɗa ma ta cewa ya je gidan bai samu Ma'eesha ba an ce ba gidan suka kwana ba daga ita har mijin nata. Dama ta ki faɗa ne don ba ta son Ma'eesha ta hadu da dangin mahaifiyar ta. Musamman da ta lura manyan mutane ne karshen wahalar Ma'eesha zai kare. Shi ne ta tura Jamil ya je ya duba ko Ma'eesha na gidan ya je ya dawo ba ta nan.
Cikin tashin hankali ya Jamil ya shigo falon yana cewa.
"Dangin Mahaifiyar Ma'eesha fa sun shigar da kara akan ke da Daddy, yanzu haka ana bukatarku a offishin ƴan sanda."
"Inna lillahi wa'inna ilaihi raji'un na shiga uku na lalace, yanzu ina zan nemo makahon nan a kama shi ya fito ma su da ƴarsu."
*To Alhamdulillah, nan na kawo karshen littafin MAKAHO NE book 1, kuma shi ne free pages, book 2 kuma paid book ne. Normal group ₦500 ne posting sai ɗaya a rana. VIP group kuma 1k ne, posting sai biyu a rana, da ya zama complete shi ma kudinsa 1k ne. Sai s tura kudin ta wannan account number 2242538358 sai s tura shaidar biya ta wanan account number. 09065327995*