Part ɗin Umma suka shiga suka same ta ita da ƙawarta Hajiya Turai tana rarrashinta, ganin dunya saka Umma ta yi saurin goge hawayenta.
Makaho Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 59 min read
Kukan Nadra ne ya kara tsananta ta nufi Umma ta shige jikinta ta rungume. Kuka suke yi du duka biyin.
Duk yadda Umma ta so rike kukanta kasa wa ta yi, haka kawai take jin tausayin Nadra ga Sidra da ba su san halin da take ciki ba, damuwa sun yi ma ta yawa. Kula take yi sosai tana ƙankame Nadra kamar za'a ƙwace ma ta ita.
Ammi ce ta shiga ganin halin da suke ciki ta ce
"Me nake gani haka, ke da za ki ma ta nasiha a wuce da ita gidan mijinta shi ne kike kuka?"
Da ƙyar aka ɓanɓare Nadra a jikin Umna suka fita da ita tana kuka tana kiran sunan Umma. Hankalinta ya tashi musamman da ta ji jikin Umman da zafi alamar ba ta da lafiya.
Tana ji tana gani lokaci daya rayuwarta ta juye sama zuwa ƙasa ƙasa zuwa sama. Ko da wasa ba ta kawo wannan ranar ba, ba ta yi tsammanin nan kusa za'ayi aurenta ba kuka da saurayin ƴar ta wacce take ƙauna yake ƙaunarta. Amma yau ita ce za'a ɗauka akai gidan Fahad a madadin Aunty Sidra. Kuka take yi sosai tana ji tana gani aka saka ta a ɗaya daga cikin motocin da suka zo ɗaukar Amarya.
Gwaggo Laraba da Gwaggo Maimuna suka saka ta a tsakiya.
Sauran dangi suka shiga cikin sauran motocin, sai dai ba ƙawar amarya ko ɗaya, kasancewar ba ƙawarta da ta san da zancen auren, ko A'isha Humaira da ta zo ta dai zo ne a matsayin bikin Sidra ba wai ta san ƙawarta ce aka aurar ba.
Sauran yan matan na dangi da kowa sai da motacin suka kwashe su zuwa gidan Amarya.
_Fahad_
Kwance yake a bedroom ɗin sa yana jin yadda abokansa Sadik da mukhatar suke ta yi ma sa knocking ƙofar, amma bai yanka ma su ba sai ma pillow ya saka ya dora a kansa alamar baya son ƙarar ƙofar.
"Fahad please open the door."
Cewar Mukhtar yana bugun kofar. Sadik cikin ƙuluwa da wulaƙancin da Fahad ke yi ma su tun ɗazu ya ce.
"Wai kai wane irin wulaƙanci kake yi wa mutane ne tun ɗazu, sai faman bin ka make yi ka fito mu tafi a raka ka ɗakin amarya ka share mu ka mayar da mu ƴan iska idan ba za ka je ba ai sai ka sanar da mu."
"Sau nawa na fada kowa ya watse, sauran sun tafi ku ma ku tafi ba in da zan je Allah ya ba mu alkhairi."
Cikin takaici suka fito kowa ya nufi motarsa suka bar gidan.
_Nadra_
Har suka isa katafaren gidan Fahad ba ta daina kuka ba.
Motacin duka suka shiga cikin compound ɗin gidan.
Babban gida ne sosai mai girman gaske ga manyan fitilu da suka haska gidan ya koma tamkar rana ne ba dare ba.
Faɗar kyau da tsaruwan gidan ma ɓata lokaci ne, gini ne na alfarma kuma na zamani.
"Fito da ƙafar dama."
Cewar Gwaggo Laraba tana riko hannun Nadra dake kuka.
A hankali ta yi Bismillah ta fito da ƙafar dama.
Tana rike da hannunta suka nufi main door nan ma ta ce ma ta ta shiga da addu'a.
Ta dan jira kafin ta ga ta saka ƙafar dama ta shiga ciki.
"Ma sha Allah."
Shi ne kalmar da kowanen su yake faɗa wasu a zuciya wasu a fili.
Ɗaya daga cikin manyan kujeru dake downstairs aka zaunar da ita. Yayin da suka dinga shiga suna leƙa ko ina na gidan suna yaba kyawun gidan.
Daga karshe dai suka kai Nadra ɗakin da ya kasance mallakinta ne a downstairs.
Saman katafaren gadonta suka zaunar da ita.
Nan suka dinga yi ma ta nasiha sosai da da kuma kara nuna ma ta mahimmancin haƙuri.
Sannan suka yi ma ta Sallama suka fice, kuka take yi sosai kamar ranta zai fita. Hakan ya saka suka dawo suka dinga rarrashinta. Ganin kukan na ta ba na tsaya wa ba ne ba ne.
Sallama suka yi ma ta suka ce da safe za su dawo. Suka bar gidan suna ta santin kyawun gidan.
_Mama_
Tana zaune ita da Aunty Rahama da ƙanwar Mama mahaifiyar Farida wacce suke kira da Aunty Jummai.
Farida na kwance a jikin Mahaifiyarta tana sharar ƙwalla.
Aunty Rahama ce ta kalli Farida tana cewa.
"Ki yi hakuri Farida wannan kukan ya isa, Allah ya zaɓa ma ki ma fi alkhairi, idan Allah ya nufa ke matar Fahad ce wata rana sai ki ga Allah ya karkato da hankalinsa zuwa gare ki ya aure ki, auren nan nasa ba wai yana nufin ba ya da damar auren ki ba ne, ai namiji mijin mace huɗu ne."
Haka Aunty Rahama ta dinga rarrashinta duk da ta san cewa ba yadda Fahad zai yarda ya auri Farida saboda ba ya son ta kwata-kwata amma ta faɗi haka ne don ta kwantar ma ta da hankali.
Mama ne ta kalli Rahama ta ce .
"Ki je ki duba ko sun tafi don karfe goma da rabi yanzu, don motocin da suka kai Amarya tuni sun dawo."
Rahama ta miƙe kenan sai ga kiran Sadik ta shigo wayarta.
Amsa kiran tayi bayan ta ji sallama ta ce .
"Sadik kin kai abokin maku ne?"
"Ina fa Aunty, rashin mutunci ya ma na muka bar shi."
Nan ya sanar da ita yadda suka yi da shi. Kuma ya kira ne don a je a saka shi ya tafi kada ya bar yarinya ita kadai a gidan.Bayan sun yi sallama ta kashe kiran wayar.
Nan ta sanar da Mama yadda suka yi sai Mama ta dauki waya ta kira Fahad. Amma wayoyinsa a kashe. Don haka ta mike fita Aunty Rahama ta bi ta a baya suka nufi part ɗin Fahad.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/LrTZNGwF35IKXX4sLRvFug
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce ✍️
*🎉Happy new year*🎉
Ina ma na barkan shigowa sabuwar shekarar 2026 lafiya. Allah ya ba mu zaman lafiya mai ɗore wa a ƙasar nan.
https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
page1️⃣1️⃣
Nan ta sanar da Mama yadda suka yi, sai Mama ta ɗauki waya ta kira Fahad. Amma wayoyinsa , don haka ta miƙe ta fita Aunty Rahama ta bi ta a baya suka nufi part ɗin Fahad.
Ba kowa a fakon sai sanyin A.C dake tashi a falon.
Bedroom ɗin sa suka nufa Mama ta fara buga ƙofar da ƙarfi. A tunanin Fahad su Sadik ne ba su tafi ba, don haka a fusace ya fara magana.
"Wallahi idan ba ku rabu da ni ba zan tafka ma ku rashin mutunci idan na fito."
"To Bismillah ma ta mutunci kawai."
Muryar mahaifiyarsa da ya ji ne ya saka shi zaro idanunsa waje.
"Ya Salam. Mama ce?"
Tasowa ya yi cikin rashin kuzari ya zo ya bude kofar ɗakin.
Kallonsa ta yi fuska a tamke ta ce
"Me kake yi har yanzu da ba tafi gidanka ba ka bar baiwar Allah ita kaɗai."
Har ya buɗe baki zai yi magana sai Mama ta ɗaga ma sa hannu alamar dakatar wa.
"Ba na son jin komai, mintuna goma kada ka sake yi a cikin gidan nan ba ka tafi ba."
Tana gama fadar haka ya juya ta fice, yayin da Aunty Rahama ma ta mara ma ta baya suka fice a tare.
Kamar zai yi kuka haka yake ji.
Key ɗin motarsa ya ɗauka, sai system ɗin sa da wayoyinsa ya nufi hanyar fita zai fice.
Har ya murɗa handle ɗin kofar zai fice sai ya juya yana ƙare wa ɗakin kallo sannan ya dawo ya kashe komai na dakin .
Ficewa ya yi zuwa farlon nan na ya kashe duk wani kaya na Elections sannan ya fice.
Kai tsaye wajen motocinsa ya nufa, ya shiga ɗaya daga ciki bayan ya ajiye laptop dinsa a kujerar zaman banza. Sannan ya yi wa motar key bayan maigadi ya wangale ma A ya bar gidan.
_Makaho_
Suna zaune bayan sun gama yin breakfast, ruwan tea ya shanye amma bai cinye bread da ƙwai ba.
Tattara kayan ta yi ta haɗa su a can gefen kayan wake-wake da suka ɓata.
"Ma'eesha me kike yi ne?"
"Ba komai wake-wake zan yi."
Sandarsa ya ɗauka ya karasa in da yake jin motsinta ya ce.
"Ba ri na wanke je ki kawai."
"A'a ba za ka iya ba."
"Ba abinda za ki iya yi wanda ni ba zan iya ba, domin nakasa ba kasawa ce "
Lalube ya fara yi har ya ji in da kayan suke , tana kallonsa yana wanke wa yana ɗauraye wa har ya kammala.
Ta kwashe kayan ta je ta jera su a in da ya dace.
Bayan ya shigo ɗakin ne ya ce ma ta .
"Yanzu me zan yi ma ki?"
"Ba komai na gode."
"Na san ke ƴar hutu ca ba ki saba da ayyuka ba, ma su aiki ne suke yi ma ki aiki, to don me ba za ki bari na taya ki ba ?"
Gajeren murmushi ta yi ta goge ƙwallar da ya cika idanunta ta ce.
"Haka ne, duk da ma su aiki ke yi ma ni aikin komai amma hakan bai saka Mahaifiyata koyar da ni ba. Ta na cewa ba lallai mijin da zan aura ya so a ce mai aiki ce ke yi ma sa gyaran ɗaki ko girki ba. Wani namijin sai matarsa kawai take yi ma sa hidima."
Kasancewar ta buga labule ta shimfiɗa leda ta ajiye katifar ta gyara. Ba wani aikin da ya rage. Hakan ne ma ya sa ta tuna ina z ta damu room freshener spray ko turaren wuta ta turaran wuta da za ya sa a ɗakin ya yi ƙamshi , dole ta nemo ba z ta iya zama daki ba ƙamshi.
"Ba abun da zan yi ma ki kafin na fita, kada na fita kuma ki buƙata wani abu."
"Kada ka damu girki ne kawai kuma Anjima kaɗai zai ɗaura, kuma ba aikin ka ba ne."
"To ba kaya ma su datti da zan yi ma ki wanki?"
"Babu."
Ta fada tana kallon kyakkyawar fuskarsa.
"To zan je na zagaya ko Allah zai sa na samu."
"Ka huta kawai da yawon gyaran takalmin nan ga rana, kuma ba kudin kirki ba?"
"Kin fi so ba zauna ke ce ɗauki ɗawainiya ta ne, ke ce mijin ni ne matar, ba zan iya ba"
"Amma yanzu wanan uwar rana fa, gyaran ma kamar nawa ake gyara takalma?"
"Idan tsinkewa ce Naira hamsin nake ɗinke wa, amma idan sauran gyararrakin ne ya danganta yanayin aikin."
"Please ka bar shi ka hutarwa kanka, a ƙalla muna da abincin da zai kai mu watanni uku muna ci, to me ye na wahalar da kai cikin wannan ranar ka yi ta yawo, kudin da ba na kirki ba, da babban sama'a ce ma da sauƙi. Amma wanann sana'ar ba..."
"Kin raina sana'ar ko? Kina ganin kamar asara ce ko? Duk wanda kika ga ya yi nasara a rayuwa, to akwai tarin asarori da faɗi-tashi da karyewar jari da ya fuskanta waɗanda ba ka gani ba. Sai dai asara ba ta hana shi ci gaba da neman nasara ba, faɗuwa ba ta hana shi sake yunƙurawa ba, karyewar jari bai karya masa zuciya ba. Wahalar da kike sha a yau, ita ce farashin nasarar da kake so ta tabbata gobe. Domin duk nasarar da ba a wahala wajen tabbatar da ita ba, ba ta ƙarko."
Ya ɗauki kayan aikinsa ya fice ba bishi da kallo.
Huɗubar mahaifiyarta take tunawa, in da take cewa .
"Ya ke ƴata Ki zaɓi namiji mai kyakkyawan zuciya, komai matsayinsa, komai kuɗinsa ko rashin kuɗinsa.
A cikin gaskiyar rayuwar aure, za ki gane cewa kasancewa cikin babban gida ko tarin kuɗi mai yawa ba su da muhimmanci kamar yadda ake tunani.
Za ki fi son wanda za ki iya tattauna komai da shi, wanda kuma zai zama uba nagari ga ’yayanku, wanda ba ya yaudara, wanda za ki iya amincewa da shi.
Iyali masu farin ciki ba su da farashi. Kada ki ji tsoron auren namiji da ke cikin hanyar gyara kansa. Amma ki guji na miji marar sana'a kuma bai damu ya tashi ya nema ba."
Wayarta ta ji yana ringin ta duba ta ga ƙawarta ce Nasreen Ibrahim. Tana ɗaga wa ta ji muryarta cikin tashin hankali tana cewa.
"Ƙawata kina ina?"
Ɗan jim ta ji kafin ta ce.
"Lafiya?"
"Na zo gidanku ne nake jin wani zancen da ya ruɗa ni akan kin yi aure."
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce.
"Kina ina yanzu?"
"Ga ni a ƙoafar gidanku ."
Ta cikin wayar ta ji muryar Laila na cewa.
"Nam ba gidansu ba ne ki je can in da take yanzu ita da musakin faƙirin mijinta can ne gidanta yanzu."
"Laila kika dake ma ni wanta magana anan wallahi dai na ci uwar ki a wajen nan."
"Ba dai uwa ta ba Wallahi, cire wayar Nasreen ta yi za ta yi cikin Laila sai ta gudu ciki tana cewa .
"Shegiya ce ni da zan tsaya ki dake ni? Mai ƙirar samudawa ai sai ku kashe ni. Wacce kike zuwa wajen ta yanzu ba ta nan dai a koma in da take mun kora ta ni da uwata.
"Ku jira na ku sakamakon."
Cewar Jamil yana watsa ma ta wani mugun kallo. Tura ba ki ta yi tana cewa
"Yaya Jamil kawar Aunty Ma'eesha ce za ta dake ni."
Bai ko saurare ta ba ya nufi motarsa. Jin Muryar Nasreen na cewa.
"Ma'eesha ban gane wannan kwatancen naki ba, idan na kawo titin zan kira ki sai ki fito ki shiga da ni cikin layin, don ban zo da Driver ba ni nake yin driving ɗin."
Jin haka ya saka Jamil tsaya wa yana kallon tana yana cewa.
"Ba ni ita Please ta yi Mani kwatancen sai mu tafi tare."
"
Jin haka ya saka Ma'eesha cewa
"Wallahi kuka zo da shi gidana ba zan yafe ma ki ba."
Jin haka ta ce.
"Ba zan zo da shi ba kar ki damu."
Daga haka ta kashe kiran ta kalli Jamil ta ce
"Ka yi haƙuri ba ta yarda na je da kai ba, amma next week zan kira ka sai ka zo mu tafi tare ka ga ni yanzu ba ta yarda na je da kowa ba."
"Ba damuwa ki gaishe ta zuwa next week ina jirab kiran naki."
Daga haka ya shige motarsa ita ma ta shiga tata motar suka bar gidan a tare.
Horn ya danna ya tsaya kasancewar shi ne a gaba, ita ma ta tsaya .
"Ban lambar wayar taki ko?"
Ya fada bayan ya sauke glass din mota tasa.
Ta karanta ma sa lambar sannan ta ja motarta ta bar wajen zuciyata cike da tarin tambayoyi.
Kwatancen da ta faɗa ma ta nan ta je ta tsaya a gefen titin, ba ta ga Ma'eesha ba, can ta hango ta tana ƙarasowa wajen motarta. Sai dai kallo ɗaya ta yi wa ma'eesha ta ga ta rame ma ma ta a cikin kwanaki biyun da ba su haɗu ba.
Tana zuwa ta buɗe front sit ta zauna tana yi ma ta sallama.
Amsa wa ta yi tana ma ta kallon mamaki,sai dai ta haɗiye tambayoyin ta ta yi wa motar key ta ni hanyar da ta ga Ma'eesha ta fito.
Tana nuna ma ta hanyar tana bi har suka ƙarasa ƙofar gidan.
A tare suka fito ta ga Ma'eesha ta buɗe ƙofar ta shiga, ita dai Nasreen mamakin ta ƙara hausawa yake yi .
"Bismillah shigo ciki."
Ta yi magana lokacin da ta shiga ɗakin.
Da sallama Nasreen ta shiga cikin ɗakin, ta tsaya tsaye tana ƙare wa ɗakin kallo.
Ba ta zauna ba duk da Ma'eesha ta ce ta zauna saman katifar.
"Zaman me kike yi a nan, wannan kangon wanda bai kai na a ce kina kiwon karnuka a ciki ba?"
Ta yi maganar tana karewa ɗakin kallo, sannan ta fito taskar gidan tana kare ma sa kallo, hatta banɗaki da kitchen ɗin fale-fale dake tsakar gidan sai da ta leƙa.
Sannan ta dawo ta kalli Ma'eesha dake zaune a bakin katifa ta ce.
"Lafiya kike zaune a wannan kangon kuma me kike yi?"
"Zaman aure nake yi ."
Da mamaki take kallona ta ce.
"Zaman aure kuma?"
"Eh."
Ta ba ta amsa ba tare da ta kalle ta ba.
"Wani irin zaman aure kuma da waye mijin naki?"
"Zaman aure da kowace macen aure take yi a gidan mijinta."
Dafe kai ta yi tana cewa
"Am confused about how..."
Kukan da ta saka ne ya saka Nasreen kasa ƙarasawa maganar da ta yi niyyar faɗa, domin kuwa tausayin ƙawar tata ce ta saka ita ma ta rungume ta suna yin kukan tare ba tare da ta san komai ba.
Tsawon mintuna suka ɗauka suna kuka ba mai rarrashin wani, kafin Nasreen ta zame jikinta daga na Ma'eesha, tana goge ma ta hawaye ta ce.
"Me yake faruwa ne, na san ni da ke ba mu ɓoye wa juna komai, don Allah ki sanar da ni kar ki saka kaina ya buga."
Nan Ma'eesha ta ba ta labarin komai, tun daga farko kar karshe. Ba abinda Ke tashi sai sautin kukan Nasreen tana tausayin ƙawarta.
"Amma Allah ya tsine wa Mamy albarka. Allah ya sa ta shiga wuta, wallahi wannan matar ba za ta ga annabin rahama ba. Gabadaya ta juye wa Daddy tunani sai abinda ta ce. Allah ya jikan Mummy."
"Amin ya Allah."
Ma'eesha ta faɗa tana goge hawayenta.
"Yanzu shi wanann makahon ne zai iya riƙe ki?"
Ma'eesha ba ta ce komai ba, don ba ta san amsar da za ya ba ta ba.
"Yanzu ke sai kika yarda?"
"To ya zan yi Nasreen?"
"Ai ba yadda za'ayi a haɗa ki da wannan nakasashen talakar musaki. Haba ke ba za ku nema wa kanki ƴanci ba?"
Murmushin takaici ta yi ta ce.
"To ya zan yi tun da mahaifina ya aurar da ni ga wanda ya ga dama, ba na da wani zaɓin da ya wuce rungumar kundin ƙaddarata."
"Haka ne, amma wannan ai bai dace da ke ba, ta ya ya za'a aurar da ke ga wanda na san ko kuɗin kayan kwalliyarki ba zai iya siye ba ballantana abincin da za ki ci, abun takaici wai sadakinki dubu uku kacal ko kaza yanzu ai ba za'a ce dubu uku ba ballantana mutum, ba kayan lefe ba komai, wanann ke ce kika sigar da wayarki kika kama haya kika siyo abincin da za ki ci kin san wannan auren ba alkhairi a cikinsa. Don haka ki tattara kayan ki yana zuwa ku ci mutuncinsa ki saka ya yi ma ki saki uku, ki zo mu tafi gidanmu ki zauna a can na san iyayena za su karbe ki, kin ga ba ki da kowa a garin nan ba ki san dangin mahaifiyar ki ba, sannan yanzu tun da hakan ya faru ba ki isa ki tafi wajan dangin Daddy ba, don sai abinda ya fada a family suke ɗauka."
Ta yi maganar tana tattara kayan Ma'eesha da ta gani a waje, tana saka wa a cikin trolly ɗin ta.
"Ba in da zan je."
Da mamaki take kallonta.
"Da gaske ba in da za ki je?"
"Eh haka na ce."
"Saboda me?"
"Saboda zaman ibada nake yi."
Nisa wa ta yi kafin ta ce.
" Duk talaucin mijina zan yi haƙuri na zauna da shi cikin kwanciyar hankali da soyayya. Mijin wata bai fi nawa ba duk sunansu mazajen aure, zan yi alfahari da nawa ko a ina ne, domin nawa shi ne nawa, mijin wata ba nawa ba ne. Zan zauna da nawa cikin nutsuwa da kulawa. Ba zan dinga hangen na wasu ko kallon irin abubuwan da yake musu, domin kowacce tana da nata jarabtar. Zan fito in nuna alfahari da nawa, kamar yadda wasu ke yi da nasu. Kila ma na fi su samun kulawa da soyayya. Talauci ba laifi ba ne. Amma boye shi, da zama cikin kima da mutunci, shi ne alkhairi, Idan mijina yana bakin ƙoƙarinsa wajen kula da ni, to zan riƙe shi da kyau. Idan na bar shi, ban san wanda zan haɗu da shi ba, ba kowanne namiji ne zai iya daraja ni ba zan yi haƙuri na zauna da abina. Da dama daga cikin matan da ake ganin suna rayuwa cikin jin daɗi, lokacin da suka auri mazajensu ba su da komai. Sai bayan aure Allah ya buɗa musu.
Ba zan fitar da rai daga rabona, arziƙi na Allah ne, kuma kowa rabonsa ba zai kauce masa ba. Ko ba a sami duniya ba, insha ALLAH za a sami mafi alkhairi a lahira.
Zan kula da mijina, danginsa sun zama dangina, zan kama darajata mu rufawa juna asiri. Mu kula da juna cikin mutunci da biyayya.Rayuwa cikin tausayawa da kulawa da juna cikin soyayya da farinciki yafi na rayu cikin arzikin da babu kulawa bare nuna ƙauna."
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
Follow the TASKAR MAMAN IHSAN channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029VaiufWb3LdQYnzC2vH0z

page1️⃣2️⃣
"Duk talaucin mijina zan yi haƙuri na zauna da shi cikin kwanciyar hankali da soyayya. Mijin wata bai fi nawa ba duk sunansu mazajen aure zan yi alfahari da nawa ko a ina ne, domin nawa shi ne nawa, mijin wata ba nawa ba ne. Zan zauna da nawa cikin nutsuwa da kulawa. Ba zan dinga hangen na wasu ko kallon irin abubuwan da yake musu, domin kowacce tana da nata jarabtar. Zan fito na nuna alfahari da nawa, kamar yadda wasu ke yi da nasu. Kila ma na fi su samun kulawa da soyayya. Talauci ba laifi ba ne. Amma ɓoye shi da zama cikin kima da mutunci shi ne alkhairi. Idan mijina yana bakin ƙoƙarinsa wajen kula da ni to zan riƙe shi da kyau, Idan na bar shi, ban san wanda zan haɗu da shi ba. Ba kowanne namiji ne zai iya daraja ni zan yi haƙuri zauna da abina. Da dama daga cikin matan da ake ganin suna rayuwa cikin jin daɗi, lokacin da suka auri mazajensu ba su da komai. Sai bayan aure Allah ya buɗa musu.
Ba zan fitar da rai daga rabona arziƙi na ALLAH ne, kuma kowa rabonsa ba zai kauce masa ba. Ko ba'a sami duniya ba, in sha ALLAH za a sami mafi alkhairi a lahira.
Zan kula da mijina da danginsa sun zama dangina. Zankama darajata mu rufawa juna asiri,zani kula da iyalanki cikin mutunci da biyayya. Rayuwa cikin tausayawa da kulawa da juna cikin soyayya da farin ciki yafi na rayu cikin arzikin da babu kulawa bare nuna ƙauna."
Gabadaya kalaman ta ɗin sunana kashe wa Nasreen jiki, don haka ta ce.
"Kina son sa kena?"
"Ba sonsa nake yi ba, ina tausayinsa ne."
"Kin tabbata iya tausayi ne kawai?"
"Na tabbata don ba na jin komai a zuciyata game da shi, abu ɗaya na sani shi ne tausayinsa da nake ji a zuciyata."
"Ke ce abar tausayi ba shi ba."
Kafin ta fuskanci Ma'eesha da kyau ta ce.
"Tausayi rabin soyayya ce, amma muje zuwa."
Ta yi maganar tana ciro wayarta ƙirar iphone a cikin handbag ɗin ta. Sannan ta ce.
"Ya maganar cousin brother na, da kika yi wa alƙawarin aure, kin dai san irin son da Abdul yake ma ki, ya ki kowace mace yanzu haka gobe zai dawo daga ƙasar Canada da mararin zuwa ganin ki, kin san kin yi ma sa alkawarin yana dawowa za ki gabatar da shi a wajen Daddy. Kin san ba kasar nan zai ajiye ki ba can ƙasar..."
Dakatar da ita ta yi ta hanyar ɗaga ma ta hannu.
"Ya isa haka nan Nasreen, ya za ki zo kina ma ni wani zancen tsohon saurayina bayan kin san cewa yanzu ni matar aure ce, ko mace ɗaya na auren maza biyu ne?"
"Ba ta auren maza biyu kuma ina son na ceto rayuwar ki daga halakar da kike ciki ne, ki auri attajiri ɗan attajirai wanda ya mutu a ƙaunar ki wanda zai jiyar dake farin ciki da jin daɗi ba wai in da za ki zauna kika wahala ba. Look at you yadda kika koma a kwana ɗaya duk kin bi kin fita hayyacinki, nan da wata ɗaya ba za ki ganu ba. Na tabbata har yanzu ke budurwa ce ba abinda ya shiga tsakanin ki da wanann makahon don haka ki rabu da..."
"Nasreen tashi ki tafi sai anjima."
Kallon mamaki take yi ma ta kafin ta ce .
"Ma'eesha ni kike kora daga in da kike, duk shaƙuwa da amincin dake tsakaninmu?"
"Nasreen matukar kika cigaba da fadar mugayen kalamanki tabbas zan yi ma ki abun da ba ki yi zato ba. Na rungumi kundin ƙaddarata ban yi jayayya da hukuncin Allah ba na dogara gare shi kuma na san ya isar ma ni, kada ki sake yi Mani magana makamancin wannan, idan kuma ba haka ba za mu samu Matsala."
"Ki yi hakuri Allah ya huci zuciyarki, me ya yi zafi, duk wanda ya ce zai haɗiye gatari ɓota zan riƙe ma sa."
Daga nan suka shiga wata firar daban. Ganin rana ta yi ma'eesha ta ce.
"Me zan girka ma ki ?"
"Duk abin da ya samu."
Tukunya ta wanke ta ɗira girki bayan ta fitar da gas din ta ajiye shi a baranda.
Jallop ɗin taliya da dafa ma su wanda ya ji kayan lambu da bisashen kifi.
A plate daya ta zuba ma su ta saka fork guda biyu.
Ganin Ma'eesha ta dauko pure water ta zuba a plate ya saka Nasreen kai hannu ta taɓa.
"Ya na ji ba sanyi?"
"To a wane fridge zan saka ya yi sanyi? Ke ni fa duk yadda rayuwa ta zo ma ni haka zan rungume ta."
"Bari na fita na nemo don wallahi ba zan iya ba."
Tana fadar haka ta miƙe tana ficewa daga ɗakin.
Ma'eesha ta rufe abincin tana jiran dawowarta.
Zuwa can ta dawo bakinta ɗauke da sallama.
"Assalamu alaikum."
"Wa'alaiki Salam warahmatullah."
Shigowa ta yi rike da bakin leda ta siyo bottle water guda biyar da maltina guda biyar ma su sanyi.
Daga nan suka fara cin abincin.
Bayan sun kammala ne sai ma'eesha ta kwashe kayan da aka ɓata ta je ta wanke su tas. Ita kuma Nasreen dama can a gidansu mahaifiyar ta ba ta saka ta aikin komai , sai dai ma su aiki su yi ma ta komai, don haka ba abun da ta iya. Ma'eesha kuwa wani lokacin Mahaifiyarta za ta ce ma su aikin su bari Ma'eesha ta yi saboda mace ce ita gidan wani za ta je wata rana.
Bayan ta gama wanke-wanken ne ta saka ruwan ɗumi a wuta ta ke ta yi wanka, da ta fito ne ta ɗauara alwala don yin sallar azahar.
Bayan ta idar Nasreen ma ta fito da niyyar yin alwala, yamutse fuska ta ji lokacin da ta ga banɗakin, duk da ba datti amma ita gani take yi ta fi karfin ta shiga wannan banɗaki.
Alwala ta yi sannan ga shiga ɗakin, don ko da ta shiga har ma'eesha ta idar da sallah.
Nan ta ba ta wuri ita ma ta yi sallar
Mayyukan shafawarta ma ma su kanshi da tsada ta shafa. Sannan ta shafa turare sannan ta shirya cikin riga da siket na atamafa, ta yi daurin Ɗankwalinta mai kyau, ba ta yi kwalliya ba powder kawai ta shafa da man leɓe.
"Hmmm yanzu ko kin yi kwalliya aikin banza ne fa, don da wani idanun zai gani ballantana ya yaba ya san cewa kin yi kyau."
Tsuke fuska ta yi ganin haka ya saka Nasreen cewa .
"Tuba nake yi. Ba zan sake ba."
Daga nan ne wayar ma'eesha ya yi kara, bayan ta duba mai kiran ne sai ta katse kafin ta yi danne-danne a wayar kafin ta ajiye wayar gefe.
Daga nan suka ci gaba da fira, sai wayar Nasreen ta yi ruri. Gani. Mai kiran ya saka ta yi Murmushi tana cewa .
"Barka da warhaka yallaɓai."
Daga cikin wayar ta ji muryarsa yana cewa.
"Barka dai ya kike ?"
"Lafiya lau Alhamdulillah. Tun jiya nake kiran lambar ƙawarki tana ringin ba ta ɗaga wa, sai na sake kira na ji a kashe, yanzu ma na kira ba ta ɗaga ba da na sake kira ina zato ma ta ji blocking ɗina ne. Kuma saboda ita zan shigo ƙasar gobe, da ba don haka ba sai nan da watanni uku zan dawo ƙasar."
"Yaya Abdul ka yi haƙuri da Ma'eesaha kawai."
"Ban gane ba, ko dai ta samu wani ne ta yar da Ni?"
"Hmmm."
"Ban gane hmmm ba talk to me."
Ya ji maganar cikin wata irin murya mai cike da karaya.
"Ma'eesha ta yi aure jiya, don haka ka zauna ƙasar Canada ka gama abun da ya kai ka."
"Ke b na wasa da ke kada ki fara yi a yanzu."
"Ba karya nake yi ma ka ba, wallahi wallahi da gaske nake yi ta yi aure."
Wani sauti ta ji daga cikin wayar kafin ta ji shiru. Cikin sanyin jiki ta ajiye wayar tana mai tausaya wa cousin brother nata. Dan ba ta mance wa sanadin ta ya haɗu da ma'eesha. Wata rana da ya kammala karatun master digiri ɗin sa ya dawo ƙadar ya biyo gaida mahaifiyar Nasreen nan ta ga Ma'eesha ta zo wajan Nasreen ya nuna yana son ta, ita ma ta amince ma sa suka fara soyayya da Abdul.
"Wai yana kiran wayarki baya shiga."
"Eh na yi blocking ɗin sa ne. Don bai dace na dinga waya da shi ba."
"Allah ya kyauta."
Da Amin ma'eesha ta amsa ba tare da ta kalle ta ba, kanta a sunkuye da alama tunani take yi.
Da misalin karfe huɗu saura kwata ya shigo da sallama a gidan.
Gabadaya suka amsa ma sa, Muryar mutane biyu da ya ji ya tabbatar ma sa cewa ma'eesha ta yi baƙuwa.
Yana rike da sandarsa ta jagora Da hannu daya ɗaya hannun kuma yana rike da basket da ma su gyaran takalmin ke yawo da shi. Ya ɗaura wani bakin leda a saman kayan aikin."
"Sannu da dawowa."
"Yauwa Ma'eesha sannu da gida. Baƙuwa kika yi ne?"
"Eh ƙawata ce sunan ta Nasreen."
Nasreen ta zuba ma sa idanu tana ƙare ma sa kallo. Tabbas makanta ce kawai cikas ɗin sa sai kuma talauci domin da ace na makaho ba ne kuma ba talaka ba ne za ta iya cewa ƙawarta ta yi mijin nuna wa Sa'a. Domin kuwa ya hadu iya haɗuwa ta ko ina baya da cikas, don ba za'a hada shi da Abdul ba, domin ya yi ma sa zarra nesa ba kusa ba ya fi shi duk wasu qualities da macen da ta san kanta za ta bukata daga wajen ɗa namiji.
Taɓa ta da Ma'eesha ta yi ne ya saka ta dawo duniyar tunanin da ta lula. Jin muryarsa mai amo ta yi yana cewa.
"Sannu da zuwa ina wuni."
"Lafiya lau ya ƙokar"
"Alhamdulillah."
Ta amsa tana ɗauke kai daga kallonsa.
Ma'eesaha ta karbi kayan hannunsa ta shiga cikin ɗakin, da lalube shi ma ya shiga ya zauna jan tabarmar da ya ji ya taka.
"Sannu da dawowa ya rana?"
"Sannu da imani Ma'eesaha, ya hakuri da rayuwa?"
"Alhamdulillah."
"Ba ri na kawo ma ka abinci ko?"
"A'a sallah zan yi . Sai na dawo masallaci."
Ya yi maganar yana ciro ledar da ya dawo da shi.
"Ga tsarabar yalo na kawo ma ki ko za ki iya ci?"
"To na gode Allah ya kara budi."
Cike da jin dadi ya amsa duk da ya san ba cimar su ba ne, ba Apple da ta saba ci ba ne.
Tashi ya yi tana cewa.
"Na ba ka buta ne?"
"Eh na gode."
Suka fito ta miƙa ma sa buta cike da ruwa.
Ya sa ya nufi banɗaki ya shiga.
Bayan ta fito ne ta damu wuri a gefe ya yi alwala ya fice zuwa masallaci.
Ledar yalon ta buɗe ta zuba a mazubi ta wanke, sannan ta dawo da zauna kusa da Nasreen tana cewa.
"Ƙawata ko kin iya ci?"
Taɓe baki ta yi kafin ta ce.
"Ai ko ke ba ki iya ci ba ballantana ni."
Daga haka ta cigaba da danne-danne a wayarta. Ma'eesha ba ta sake bi ta kanta ba ta ɗauki guda ɗaya ta kai baki. Ɗaci da ta ji ne ya saka ta ɗan yamutse fuska sannan ta haɗiye.
Nasreen na kallona ta gefen idanu ba ta ce komai ba, zuwa can ta mike tana cewa.
"Zan tafi gida sai wani lokacin."
"To na gode ki gaida su Mom don Allah."
"Za ta ji."
"Ba za ki tsaya ki yi sallar la'asar ba."
"Idan na je gida zan yi."
Tana tsaye bakin ƙofar tana kallon Nasreen har sai da ya ga tashin motarta sannan ta saki kofar ta koma ciki.
Buta ta ɗauka ta shiga banɗaki ta yi tsarki sannan ta fito ta daura alwala.
Tana alwala tana jin muryarsa mai amo yana rera karatun sallah a masallacin, da alama shi ne liman ɗin.
Bayan ta idar da alwalar ta shiga dakin ta gabatar da sallar la'asar.
Addu'o'i ta yi ta yi azkar na yamma daga nan ta kwanta a saman sallayar.
Bayan kamar mintuna talatin ya shigo gidan da sallama.
Da lalube ya kai bakin kofar ya yi sallama ta amsa tana tashi zaune.
In da ya saba zama ya laluba wato kan tabarma ya zauna tare da Bismillah.
"Ƙawarki ta tafi ne?"
"Eh ya tafi."
"Allah sarki, Allah ya kai ta gida lafiya."
Maltina da ruwa ta ajiye gabansa ta ce.
,Ga Maltina nan da ruwa na ajiye ma ka, bari na kawo abinci."
"To na gode amma ki bar abincin nan, sai zuwa dare."
"Me ka ci da rana."
"Ba komai dama ni ban saba cin abinci sau uku ba, sau biyu nake ci wata rana ma idan ban samu sau biyu ba idan na ci na rana zuwa dare ruwa kawai zan sha na kwanta."
"Wanan ya wuce yanzu akwai sai ka ci idan babu ne sai ka san cewa babu ka yi hakuri. "
"Ba na jin yunwa bari na sha wannan kawai kada ku damu."
Daga nan ba ta sake magana ba ta koma ta kwanta a saman sallayar.
"Bari n je na yi wanka."
"Okay bari na zuba ma ka ruwa na kai ma ka."
"Don Allah ki huta na gode, zan iya ɗiba da kaina, ai na gama sanin kan gidan, bayan kin ke kasuwa ai har fita na yi na dauko jakar kayana. Na san komai na gidan nan, ba na bukatar ki yi ma ni wani aiki sai dai ni na ji ma ki."
"Ai lada nake nema kuma aljannata nake nema."
"In dai Aljanna ce in sha Allah za ki shige ta Ma'eesha, Allah ya yia ki albarka ."
Da Amin ta amsa ta koma ta kwanta. Bayan ya ɗebi ruwa ya kai banɗaki ya dawo wajen kayansa zai ɗauka, kasancewar ya san shi ba ya gani ita kuma tana ganinsa ba zai iya cire kaya a gabanta ko ya canza ba, don haka ya dauki kayan da zai saka da sabulu ya fita ya je banɗaki da su.
Bayan ya yi wanaka a banɗaki ya goge jikinsa ya sauka kaya ya fito bayan ya zuba wanda ya cire a cikin bokitin wankan .
Ruwa ya ɗeba ya sa ido ya wanke kayan ya shanya.
Sannan ya koma dakin, ta daga kai ta kalle shi ta ga ya sauya kaya.
"Ina kayan da kika cire na wanke ma ki?"
"Ka bar shi na gode."
Duk da dama tana tunanin wanki na ba ta wuya, don ba ta saba ba sai dai a wanke ma ta, ma su wanki ke wanke ma ta. Ko underwears ɗinta a warahing machine take wanke wa .
Idan na cire, yau dai ta wanke underwears ɗinta banɗaki da ta cire bayan ta ji wanka.
Lalube ya fara yi ganin ya matsa ta ce ba basket da ta zuba nan bayansa, ta dauka ta fita bayan ta bashi sabulu, ya je ya wanke ma ta su y shanya ma ta kayan.
_Sidra_farkawar ta kenan daga barci ta farka da kuka, sakamakon mafarkin da ta ji wai an kai Nadra gidan Fahad da ya gina da sunanta, irin tsarin da take so, kuma ga kayan ɗaki da kayan kitchen ɗin da aka je aka zuba da sunan ta sun zama mallakin Nadra. Da kanta ta nuna wa Umma irin funitures da take so aka yi order daga ƙasar waje, sannan Abba ya ba ta kudi je Dubai ta siyo irin kayan kitchen da take so, yanzu shi ke nan an mallaka wa Nadra kayan kitchen ɗin ta da kayan ɗakinta da kuma mijinta.?
"No ba zai yiwu ba wallahi, na san wannan duk aikin Ammi ce ita ce za ta ziga Abba akan ya ƙwace komai nawa ya ba Nadra. Dama ba ta ƙauna ta kullun cikin zagina take yi wai ni ba na da kunya da tarbiyya kullum Nadra ce ya yarinyar kwarai a wajen kowa wannan karon zan nuna kowa rashin tarbiyyar da suke kira. Mani za su gan shi muraran kuma ziryan, wallahi ba zan yi biyu babu ba, ba zan rasa burina da nake da shi ba sannan kuma na rasa mijin da nake so ba, ba zan yi biyu babu ba wallahi sai dai ayi mutuwar kasko."
"Ba ni wayarki.."
Ta yi maganar tana kallon Sady baby, ta mika ma ma ta wayar ta shiga TikTok account ɗin abokin Fahad Sadik. Na ci karo da videos ɗin bikin Fahda da Nadra.
Da in da yake ba ta cake daga bakinsa zuwa na ta, rintse idanunta ta yi tare da kokarin cilli da wayar sai Sady baby ta yi saurin karbe wayarta. Don ta san idan ran Sidra ya ɓaci idanunta rufe wa yake yi.
Ta fama hannunta dake zubar da jini tana cewa.
"Wallahi ba zan haƙura da Fahad ba, domin nawa ne shi ni kaɗai, ruwa da iska ba abinda zai ma ni shamaki da abun so na ciki kuwa har da ita Nadra, zan iya aikata ma ta komai don na mallake sa."
Kallon ta da tsoro Sady baby take yi kafin ta ce.
"Ko da hakan na nufin bakin cikin ƙanwarki ce?"
"Ko da hakan na nufin mutuwarta ne."
Ganin yadda take zubar da jini ya saka Sady baby kokarin taimaka ma ta, amma ta fisge hannunta tana cewa .
"Sai na aikata abinda ke raina in dai akan Fahad ne?"
"Na sani Sidra za ki iya, ko me kika ce za ki aikata na san za ki iya. Amma ba ki ga yadda kike zubar da jini ba ne?"
*Maman Ihsan ce.*✍️

page1️⃣3️⃣

"Ban damu da jinin ba, kuma bam ji zafin hakan ba, amma kuma abinda aka yi ma ni na raba ni da Fahad shi ne ya fi yi ma ni zafi."
Nan ta dinga rarrashinta sosai da ba ta baki har ta hakura ta yi shiru da surutun nata.
"Ba ni wayata."
"Me za ki yi da ita, bai kamata ki kunna waya yanzu ba."
"Ina bukatar jin Muryar Fahad."
"Kada ki kira shi da wayarki, domin kuwa ba mu san abun da za mu ce ya faru da ke ba har kika bar gida. Ki kira shi da wata lambar don gudun tonuwar asiri ki."
Ta yi magana tana mika ma ta wata karamar waya a hannun ta.
Karba ta yi ta saka lambar wayar Fahad kasancewar tana da lambar wayarsa a cikin kanta .
_Fahad_
Driving yake yi zuciyarsa babu daɗi, sam bai taɓa kawo ranar nan da za ta zo ba wai zai tare a sabon gidansa ba tare da Sidra ba. Yana driving ɗin kamar wanda zai ɓalle sitiyarin motar. Saboda yadda ya rike shi da ƙarfi, har yanzu ya kasa gane dalilin da ya saka Sidra ta aikata haka bayan ya san tana tsananin son sa.
Wayarsa dake gefe ya kalla da idanunsa da suka canza launi zuwa ja ya yi, ganin baƙuwar lamba ce ya saka bai ɗauka ba. Sidra dake jiran ya dauka ko ta ji muryarsa ta cire wayar daga kunnenta don ta san ba lallai ne dama ya dauka ba. Sai da ta yi masa 3 missed call bai ɗaga ba, sai a na huɗun ne ya ɗaga wayar na ajiye ya yi picking call ɗin ba tare da ya yi magana ba, yana jiran me kiran ya yi magana. Jin shiru ya katse wayar don ita ma Sidra ta ƙi ta yi magana.
Dama shi haka yake in dai bai san me kira ba to ba zai yi magana ba sai dai ya katse kiran wayar.
Hawaye ne suka wanke ma ta fuska ta juya ta kalli ƙanwarta ta ce.
"Kila yana can tare da ƙanwata ko? Me yiwuwa ma yana nanne da ita? Kuma zai iya yin sex da ita ko?"
Sai a lokacin Sady baby ta yi magana ta ce.
"To me zai hana shi yin sex da ita tunda matarsa mallakinsa ce kuma an kai ma sa ita har gida, ai ba kowane lafiyayyen namiji zai iya kau da kai a daren farkonsa ya kyale matarsa ba."
Kuka ta saka tana dora hannu aka .
"Wayyo na shiga uku na lalace, kai ba zai yiwu ba na san ba zai taba son ta ba, ba na fata wata alaƙa ta autatayya ta shiga tsakaninsa da Nadra domin ba abinda zai yi da ita ni yake so ba ita ba."
A gaban tangamemen gate ɗin gidansa ya yi parking ya tsaya yana danna horn. Security ya leƙo ganin maigidan ne ya saka ya koma da sauri ya wangale ma sa gate ɗin gidan ya shiga da matarsa.
Parking lot ya nufa ya yi parking, sai da ya kwashe mintuna ashirin ba a cikin motar bai fito ba.
Ganin shiru ya saka security biyu da ke harabar gidan ɗaya ya karasa wajen motar yana knocking glass ɗin.
A hankali Fahad ya dago da kansa da ya kwantar a sitiyarin motar sannan ya zuge glass ɗin motar.
"What happened?"
"Am sorry sir, are you okay?"
"Am okay."
Ya faɗa yana kokarin fitowa daga cikin motar yayin da security ya bar wajen. Don sun ga ya ɗauki lokaci bai fito ba ne ya saka suka fara tunanin ko wata matsala ce ko bai da lafiya ne.
"Wayoyinsa a hannunsa ya nufi main door ya tura ya yi sallama ciki-ciki wanda ko kawai wani a falon ba jin sallamar zai yi ba.
Ƙamshin turaren wuta da room freshener spray suka yi ma sa sallama.
Ba tare da ya kalli ko ina ba ya nufi upstairs ɗin.
A hankali ya tura ƙofar falonsa ya shiga, wayoyinsa ya ajiye saman Centre table sannan ya zauna a daya daga cikin lafiyayyun kujerar da suka yi Falon ƙawanya.
Jinginar da bayansa ya yi da jikin kujerar. Wayarsa ce ta soma ruri ya duba ya ga Mama ce ke kiransa. Sai da ya sauke ajiyar sanan ya daga kiran wayar.
"Mama."
Ya fada cikin shagwaɓa murmushi ta yi Murmushi irin tasu ta manya ta ce.
"Ka isa gidan lafiya?"
"Uhm."
Ya faɗa kamar ba ya so yin magana.
"Shagwabar ce ta motsa ko?"
Bai ce komai ba idanunsa a lumshe yana rike da wayar.
"Ina Nadra take."
"Ban sani ba amma ina tunanin tana ɗakinta."
"Kai kana ina?"
"Ina ɗakina."
"Me za ka yi yanzu."
"Zan yi wanka ne na kwanta."
"Fahad."
"Na'am Mama."
"Yanzu ko dabba ce aka kai ma ka gida aka ajiye ta ai ka duba lafiyar ta ko?"
"Tana lafiya Mama."
"Ka je ka haɗa ni da ita a waya. Nan da mintuna biyar zan kira ka."
Tana fadar haka ta katse kiran wayar.
Fuska babu walwala ya mike ya nufi ƙofar fita, dama kofar falonsa da kofar falonta suna kallon juna ne.
Hannunsa ya daura saman handle ɗin kofar ya buɗe ya shiga da sallama ciki-ciki.
Ba kowa a falon sai kanshi da sanyin A.C dake tashi .
Bedroom ɗin ta ya nufa ya shiga da sallama.
Tana kwance a saman gado ta kudundune mijinta wuri ɗaya sai ajiyar zuciya take sauke wa. Da alama ta ci kuka har ta gaji.
Ƙamshin turarensa ne ta ji ya saka ta ɗago kanta ta zuba ma sa kumburarrun idanunta da suka yi ma ta nauyi saboda tsabar kuka.
Shi ma idanunsa ya a zuba ma ta ba tare da ya yi magana ba. A hankali ta mayar da idanunta ga kanta dake bala'in sara ma ta da ciwo.
Wayarsa ce ta yi ruri yana ganin Mama ce ya karasa bakin gadon ya miƙa ma ta wayar bayan ya yi picking call ɗin ya saka a handsfree.
"Assalamu alaikum."
Cikin disashshiyar muryarta da ta disashe da kuka ta amsa da.
"Wa'alaiki Salam warahmatullah. Ina wuni ."
Duk da ba ta san waye ke magana ba amma zuciyarta ta ba ta cewa
"
Mahaifiyarsa ce .
"Wa'alaiki Salam warahmatullah Nadra ya kike?"
"Alhamdulillah."
"Daga jin muryarki kin sha kuka sosai, ki yi hakuri kin ji komai muƙaddari ne daga Allah, Fahad shi ne mijin ki ki yi hakuri ki zauna da shi a matsayin mijin ki, idan ya yi ma ki wani abun da ba daidai ba ki kira ni ki faɗa ma ni, ni ce mahaifiyar sa zan dauki mataki akansa kin ji Daughter."
Cikin Muryar kuka ta ce.
"To Mama."
"Yauwa Allah ya yi ma ki albarka kin ji."
"Amin Mama."
Ta fada tana goge hawayen da ke ma ta sintiri a idanunta.
"Zan ce ya tura ma ni lambarki sai ya tura ma za mu yi magana da safe."
"To Mama."
"Kin ci abinci kuwa?"
"Ba na jin yunwa."
Tun karfe nawa kika ci a abinci?"
"Tun da rana."
"To yanzu ki samu ki ci abinci zai kawo ma ki. Sai da safe ko?"
Daga nan ta mikawa wa Fahad wayar ya karɓa yana karawa kunnensa.
Kafin ya yi magana ya ji ta ce.
"Ka siya ma ta kaza ne?"
"Wace kaza kuma Mama?"
"Ka fita ka je ka nemo kaza ka kawo ma ta ba ta ci abinci ba."
Tana fadar haka ta kashe wayarta.
Jiki ba karfi ya fice daga dakin ya koma nasa ɗakin ba tare da ya sake kallon in da take ba.
Key ɗin iya ɗauka ya fida daga cikin gidan ransa babu dad'i.
In da ake gashin kaji ya tsaya. Ba tare da ya fito daga cikin motar ba ya yi horn wanda ya janyo hankalin daya daga cikin ma su aiki a wajen.
Ya ƙaraso wajen daidai lokacin da wayar Fahad ta sake ringing.
Ya yi picking still bai yi magana ba don ya san lambar ɗazu ce.
"Ka kawo mun kaza guda daya da fresh milk guda biyu."
Maganar sa ya sauka a cikin kunnen Sidra dake rike da wayar tana jiran ya yi picking.
Katse wayar ta yi tana fashewa da kuka.
"Wai fa kaza ya zo siye da fresh milk, ita zai kai wa su ci kenan? Kazar da kowane ango ke siya wa matarsa a daren farkonsu shi ne ya siya ma ta. Kazar ba shi da idan ta ci sai ta biya kenan fa."
Lokaci daya ta rikice da kuka wanda hakan ya saka Sady baby rarrashinta.
"Ba zai yiwu ba dole na bar garin nan gobe na koma Kaduna, duk abinda zai faru ya faru amma sai Fahad Majidaɗi ya dawo mallakina."
_Makaho_
Bayan ya idar da sallar isha'i daga masallaci gida ya nufa. Don karfe tara ne yanzu, sai sa ya tsaya ya yi karatun Alkur'ani mai girma. Da sallama ya tura kofar fale-falen gidan ya shiga
Daidai lokacin tana fitowa daga wanka daga ita sai towel da ta ɗaura rabin cinyarsa a waje suke.
Sai ƙamshin shower gel din ta take yi. Amsa ma sa sallama ya ji ta yi tana ma sa Barka da shigowa.
Ya amsa yana lalube har ya ji ya kawo bakin kofar sannan ya shiga da sallama.
Lokacin akwai wutar nepa,
Tsane ruwan jikinta ta ke yi ganin shi makaho ne ba gani yake yi ba ya sa ta warware towel ɗin ta shafa man shafawar ta ta shafa.
Zama ya yi kan tabarmar da ya kan zauna , har ta gama shafar ta ta saka turaren ta ma su kamshi sannan ta saka kayan barci ta .
"Ka yi hakuri ina shirya wa ne."
"Ba komai Ma'eesha."
"Na ga abincin nan ya rage ne ya sa ban yi sabon girki ba kada ya zama ɓarna."
"Kada ki damu Ma'eesha ba wani yunwa nake ji b."
"Kar ka ce haka tun breakfast ba ka ci komai ba, ta ya mutum zai yi ta zama da yinwa ana rayuwa da yunwa?"
Murmushi ya yi tare da cewa.
"Ba iya abinci muke buƙata don mu rayu ba, muna buƙatar mu riƙa ji a ranmu cewa akwai wanda yake sonmu, yake fahimtarmu, yake taya mu alhini a lokacin damuwa, yake fahimtar maganar da ke ranmu a lokacin da muka yi shiru, yake fahimtar damuwarmu a lokacin da muka rufe ta da murmushi. Mutum zai iya jure talauci, ya yi haƙuri da yunwa, amma ya kasa jure rashin masoyi mai kulawa. Kalma ɗaya mai daɗi da masoyinka zai gaya maka za ta iya haska tsakiyar zuciyarka da sanya maka farin ciki da natsuwa a lokacin da kake fuskantar ƙalubalen rayuwa."
Ƙwalla ta goge yayin da take ƙokarin ajiye ma sa abincin a gabansa. Sannan ta kawo ruwa da Maltina ta ajiye ma sa.
Ya fara cin abincin kenan suka ji sallama daga tsakar.
Amsa wa ta yi sannan ta janyo hijabi ta saka daidai lokacin da ake ƙara bude murya an rangaɗa wata uwar sallamar.
_Nadra_
Yana fita daga dakin ta saka sabon kuka Har ya dawo ba ta daina ba . Cikin kuka take cewa.
"Sidra ina kika tafi kika bar ni a muhallin da bai dace da ni ba. Ke kika dace kina nan don Allah ki dawo zan tafi na bar ma ki komai naki ne, wannan gidan gidan tamkar gidan aro ne a gare ni, ki dawo na bar ma ki gidanki mijin ki komai na ki ce ni ba mazauniya ba ce."
Ƙamshin turarensa da ta ji ya haifar ma ta da faɗuwar gaba.
Dara-daran idanunta da suka kumbura ta kalle shi da su
Wani kallo yake yi ma ta wanda ya sa ta faduwar gaba.
*Ku yi hakuri da wannan*🙏🏻

page1️⃣4️⃣
Wani kallo yake yi ma ta wanda ya sa ta faɗuwar gaba.
Da sauri ta ɗauke idanunta daga kallonsa ta mayar kan yatsun hannunta tana wasa da su.
A hankali ya ƙaraso gaban gadon hannunsa rike da faranti da ya ɗora rabin kaza akai, sai dayan hannun nasa wanda ya rike robar fresh milk da glass cup.
"Ki zauna da kyau."
Tsintar kanta ta yi da bin Umarninsa. Bayan ta tashi daga kwancen da take ta yi kanta a ƙasa har lokacin ba ta daina hawaye ba.
Sai lulluɓe jikinta da mayafinta take yi.
"Ga shi nan ki cinye shi, ko na kawo ma ki tea ne?"
Ma ta girgiza ma sa alamar alamar a'a.
_Sidra_
Bayan ya ci kuka ta ƙoshi ne sai ta kalli Sady baby tana cewa.
"Yanzu dama namiji baya da kunya?"
"Tofah, me aka yi ne?"
"Wallahi In fada ma ki siyen kaza ya tafi kazar amarci wanda a sani na idan ta ci kazar nan fa kin san me zai biyo baya."
"To sai aka ce ma ko sai zai yi abu da ita ne zai siya ma ta kaza?"
"Yau ne fa daren farkonsu hakan yana nufin yana da lokacin ta kenan, ban taɓa tunanin hakan daga wurin Fahad Majidaɗi ba. A baya fa shi da kansa idan kika fahimce shi za ki ga kamar ya tashi Nadra ce. Musamman da yake ganinta kullum cikin dogon hijab da yadda take sunkuyar da kai sai yake ce ma me ya sa ƙanwata take yin abu kamar munafuka ce shi baya son haka. Sai na ce ma sa wai kunya ce nan. A lokacin ya ce baya son mace mai kunya haka ba zai iya auren duk mace mai wannan yanayin ba, amma da ke namiji munafiki ne har da zuwa siyen kazar amarci."
Hawaye ma su zafi ta goge tana cewa
"Ba zan zauna a garin nan ba, dole na tafi na koma Kaduna gobe, na tari yaƙin dake gabana."
"Ba za ki hakura da Fahad ɗin nan ba kuwa Sid?"
"Ba zan zan iya ba Sady baby ba zan iya ba ƙarya da ciwo. Ba abinda ya ragu cikin son da nake ma sa.
Gajeren murmushi Sady baby ta yi kafin ta ce.
"Sai dai addu'ar da za ki yi kada wani abu na autatayya ya shiga tsakaninsa da Nadra. Domin idan wani abu ya shiga har ya yi sex da ita a wannan daren komai zai lalace ma ki, domin hakan na nufin sun zama abu ɗaya ne shi da ita. Musamman idan ya kasance ita virgin ce, to saboda samun ta da cikakken budurcin ta ko ya ya ne sai ya ga darajarga da ƙimar ta a idanunsa. Kuma ba zai taba mance wannan halaccin nata ba, ke ɗaiɗaikun maza ne fa suke sakaci da irin wannan mace domin shi ne saka ta yi daraja a idanunsa. Amma idan ya ga cewa ya aure ki ya fahimci ke ba virgin ba ce wallahi duk son da yake yi ma ki sai ya ragu mutuncin ki zai zube a idanunsa Sosa da sosai."
Ta yi maganar tana kallon Sidra wacce ta yi mutuwar tsaye kamar ba ta jin ta .
"Shi kenan komai zai lalace na tabbata Nadra virgin ce, saboda ita mai tsoron Allah ce, mai horo da bin Umarninsa da hani ga saɓonsa, ba za ta taba bari a raba ta da mutuncin ta ƴa mace ba. Infac ma ba in da take zuwa daga guda sai makaranta, ko kawaye bata da aji sai wata yarinya daya A'isha Humaira. Ke ko za mu fita da ita sai da dalili ba iri na ba ce mai yawan tsiya ko satar hanya ina ji na fita, kuma idan na yi satar hanya na fita duk da tana ba ni shawara na daina amma duk da haka tama rufa ma ni asiri wajan iyayen mu ta ce ina ɗaki ina barci."
Goge hawaye ta yi ta ce.
"Bari na sake kiransa ."
"Kada ki kira shi ki ji abun da zai tayar ma ki da hankali."
Ba ta saurare ta ba ta kira lambar Fahad Majidaɗi.
_Fahad_
Shigowarsa ɗakin kenan ya miƙa wa Nadra ruwan shayin da ya haɗo ma ta duk da ta ce ba ta so.
Miƙa ma ta shayin ya yi daidai lokacin da wayarsa ta so ma ruri, sai ya duba still numbern da aka kira shi da ita ne.
Ya ɗaga daidai lokacin da da Nadra ya kai kofin da ke hannunta bakinta ta kurɓi tea, jin zafi ya sa ta saki wata ƴar ƙara wanda ya sa Fahad ɗan rikicewa ya ce.
"Am sorry na yi ma ki shi da zafi ko?"
Nan ma aka yi katarj da Sidra ta ji su kuma sai zuciya ta ake kitsa ma ta wani abun daban. Don haka sai ta katse kiran wayar zuciyar ta na tafarfasa sosai da sosai. Kuka da nadamar barin gida ya zo ma ta lokaci guda, ta kalli Sady baby ta ce.
"Ba na faɗa ma ki tun da ya je siyen kazar kazar nan na san me hakan ke nufi . Yanzu fa ihunta na ji ta yi tana ƙara shi ma daga jin muryarsa a rikice yake har yana ce ma ta sorry ya yi ma ta shi da zafi ko?"
Ta ɗora hannu akai tana kuka mai tsuma zuciya. Allah wadaran halin maza wallahi, Nadra karamar yarinya ce fa dududu shekarunta 18 amma shi ne har ba zai iya kawar da kai akanta ba. Ai ba sa'ar aurensa ba ce. Don ko da aka haife ni sai da Ummanmu ta sake haifar yara guda biyu suna mutawa kafin aka haife ta ita ce ta rayu ai ko kusa da ni ba ta kai ba. Don na ba ta shekaru bakwai a duniya. Don idan ba ki manta ba yanzu ina 22 years ne ita kuma yanzu take 18 ai ba kusa ni da ita. Kuma wallahi ba ta isa ta raba ni da Fahad ba shi ma munafiki ya ba ni mamaki."
Nan da dinga sambatu ita kadai a ba wanda ya tanka ma ta. Kafin ta kalli Sady baby ta ce.
"Za ki iya saka diraba ya mayar da ni Kaduna gobe da safe?"
"Eh amma ki bari zai kai ni wani waje da safe zuwa karfe goma za mu dawo na san kin shirya zuwa lokacin ko?"
"Har karfe goma?"
"To ya za'a yi fitan nawa ya zama dole ne, kuma idan ya tafi kai ki da motar ba yadda zan yi."
Jinjina kai ta uku tana cewa.
"Shi ke nan zan jira karfe gomar."
"Yauwa ƙawar arziki, kaya ce da na yi order matar ta kira zan je na karɓa shi ya sa, amma muna dawowa zai kai ki har gida."
Godiya ta yi ma ta sannan ta Sady baby ta fice ta bar ma ta dakin bayan ta karbi wayarta.
_Ma'eesha_
Tana saka hijabi akan kayan barcin na ta ta fitq waje don duba mai sallama. Don Muryar mace ce ta ji ba ta namiji ba.
Ba kowa ba ce fa ce Larai Dillaliya wacce makaho ya fara kai Ma'eesha gidan ta kasa zama ciki ta ce za ta kama haya.
Ita dai Ma'eesaha ba ta gane ya ba , amma Larai sai washe baki take yi tana jin daɗi.
"Sannu da zuwa."
"Yauwa sannu amaryar Khalifa ya kuke ya Khalifa?"
Jin haka ya saka Ma'eesha ta yi tunanin cewa. Ko Larai dangin Khalifa ne. Don haka da fara'a ta ce.
"Bismillah shigo ciki ma na."
Ta yi gaba Larai na bin bayanta suka shiga ɗakin.
Da sallama suka shiga Larai Dillaliya ta kalli gaban Khalifa makaho ta Maltina da bottle water.
"Ma sha Allah."
Sannan ta kare wa ɗakin kallo ta ga komai sabo ne ba tsoho ba, sai ta fara tunanin dama akwai canji a hannun yarinyar kenan. Sai dai ba ta ji dadin haka ba, don ta fahimci yrinyar ta fiye kayan bukata. Ta dauka ba su da komai ne sai ta ce ma ta tana siyen kayan saka wa da takalmomi da handbag ta siye a wulaƙance don ta fahimci komai na yarinyar mai tsada ne kuma kamar tana cikin matsala ko nawa aka ba ta za ta karba.
Muryar Khalifa ta ji yana cewa.
"Ina wuni?"
Sai a lokacin ta daina kalle-kallen da take yi ta ce.
"Lafiya lau Khalifa ya amarya?"
"Alhamdulillah."
Daga nan ba wanda ya sake magana. Ma'eesha ce ya mike ta kawo ma ta ruwa ta ajiye ma ta. Ta dauki plate za ta zuba ma ta abinci kenan sai ta ji Muryar Makaho na ce wa.
"Baiwar Allah lafiya a daren nan ko?"
Don sarai da ya ji muryar ta ya gane ta.
"Am dama na ce bari n zo ne don na ga kamar za ku bukaci kuɗi sai na siyen abun da amarya ke da su, kamar ko akwati haka da kayan saka wa da takalmomi da handbags da sarƙa da ƴan kunne da sarƙa duk...,"
Tsawar da Ma'eesha ta daka ma ta ne ya ba ta mamaki ta mike da sauri .
"Tashi ki fita!"
"Ban gane ba daga taimako?*
"Kin ga jin zo wajen ki neman taimako ne?"
"Ba ku zo b amma na san sai kun zo wata rana, sai kun zo wata rana kuna nema ma da kanku. Don wannan makahon mijin naki Makaho ba ya iya ɗaukar ɗawainiyar ki zai yi ba. Don Allah na tuba ai ba na tunanin cewa a yini ɗaya yana haɗa Naira ɗari biyar. Tun da kuma ha ba kowa zai ba wa maka..."
"Mallama tashi ki fita kafin na ba ki mamaki a gidan nan, dama abun da ya kawo ki kena"
Jiki ne rawa Larai ta mike ta bar gidan.
Ranta ya ɓaci kasa magana, illa iya kai ta kawar da komai ta yi shirin.
Bayan ta yi shirin kwanciya barci duk da tana jin zafi haka dai ta rufe ƙofar ɗakin.
Ba zai yiwu ma ta a ce wa makaho ya zo su kwanta tare ba, Hakazalika ba ta jin ta yi ma sa adalci idan ta bar shi ya kwanta ƙasa kan tabarma. Don haka sai ta rasa yadda za ta yi don ita ma ba za ta iya kwanciyar a ƙasa ba. Amma sai ta yanke shawarar bari shi makahon ya bi zaɓin abun da ke ransa. Idan ya hau katifar ya kwanta kusa da ita ba za ta hana shi ba, don haka ta kalle shi yana zaune kamar wanda yake tunanin wani abu ta ce .
"Ni zan yi barci sai da safe."
"Jinjina kai ya yi yana cewa.
"Allah ya tashe mu lafiya."
Da Amin ta amsa ma sa sannan ta yi addu'ar kwanciya barci ta kwanta abun ta.
Kashe hasken wayarta ta yi don dama shi ta kunna. Duhu ya gauraye ɗakin .
Sai dai ta kasa barci kwata-kwata sakamakon zafin da ta ji ya addabe ta .
Don ta saba kwanciya cikin sanyin A.C nan kuma zafi da sauro ne suke addabar ta suna kuka.
Sosai ta rikice tana ta mutsu mutsu.
Jin motsinta ya yi yawa baya. Kamar awa ɗaya da kwanciyar ta ya saka ya kira sunanta.
"Ma'eesha lafiya, ko zafin ne ke damunki"
Kamar za ta yi kuka ta ce.
"Na kasa barci wallahi."
"Kamar jira yake yi ya taso da lalube ya ƙaraso wajan katifar yana cewa.
"Ki yi hakuri na yi ma ki fifita kin ji?"
Yana nan zaune gefen katifar ya ce ta bashi abun fifita.
Tashi ta yi ta je ta nemo ma sa ta kawo ma sa bayan ta kunna fitilar wayar.
Tama ba shi ta kashe ta kwanta.
Daga nan ya dinga yi ma ta fifita ba daɗe wa barci ya yi awon gaba da ita.
Shi kuma yana nan zaune har ya soma gyangyaɗi, sakamakon rashin barci jiya da bai yi ba ya kwana juya yana ma ta fifita ga yau bai yi ba har dare ya raba yana ma ta fifita. Idan ya daina take cikin barci za ta ji zafi na shig busowo za ta fara motsawa shi kuma da ya ji motsi zai cigaba.
Farkawa ta yi ta ga shi zaune yana yi ma ta aikin fifita.
Ta tuna haka jiya ya kwana zaune yana ma ya fifita. Sai ta ce.
"Am ka bari ya isa haka nan na gode."
"Ba za ki iya ba."
"Sanyi nake ji ka bar shi kawai."
Sanyi a yanzu ko ba ku da lafiya ne?"
"Lafiya lau nake amma na gaji da fifitar ne ya na sa na ji sanyi."
Daga haka ya daina ita kuma ta kudundune cikin sani har kabta da ƙafarta na ciki. Ta rasa yadda za ta yi tausayinsa ya sa ce ma sa haka amma ba wai don tana jin sanyin ba. Tana addu'ar a ranta Allah zai kawo ma ta mafita.
*Wace ce Ma'eesha?*
Ma'eesha Ibrahim Khalil, shi ne cikakken sunanta. Ibrahim Khalil shi ne cikakken sunan mahaifinta. Mahaifiyarta kuma sunanta Saliha.
Ibrahim ya haɗu da Saliha ne a gidauniyar tallafawa marayu wanda mahaifinsa Shamsuddin ke daukar kusan rabin ɗawainiyar marayun. Duk lokacin da Alhaji Shamsu kan shigo gidan marayun tare da Ɗansa Ibrahim Khalil yake zuwa. Ya kan taya mahaifinsa raba wa marayun kaya da sauran abun bukatunsu.
Wanda anan ne Ibrahim Khalil ya ga Saliha ya ji yana son ta. Lokacin da ya sanar wa mahaifinsa zancen auren Saliha mahaifinsa ya nuna jin fadinsa domin shi mutum ne mai son marayu da tausaya ma su. Sai dai Ibrahim Khalil ya fuskanci ƙalubale daga wajan mahaifiyarsa kan rashin amincewar ta da auren Saliha. Saboda an yi bincike ba'a san daga ina ta fito ba wai ba ta sani ba ma ko ba ƴar Sunnah ba ce. Wata kila cikin shege aka haife ta ta aka jefar da ita.
Sai da Mahaifin Khalil ya tsaya tsayin daka sannan aka yi auren Ibrahim Khalil da Saliha. Ta tare a gidansa dake nan cikin garin Kano.
Zama suke yi cikin soyayya da ƙaunar juna. Yana son ta saboda nagartar ta, don tana da hakura juriya da hangen nesa. Alhaji Shamsuddin yana son sirikar tasa ganin yadda Ɗansa ke son ta, sai sai tsakanin ta da uwar mijinta ce kadaran kadahan. Ba ta nuna ma ta soyayya kuma ba ta nuna mata tsana.
Bayan shekaru ɗaya Allah ya albarka ce su da haihuwar ƴa mace. Ranar ya kasance ranar farin ciki ne a gare su.
Farin ciki a wajen Ibrahim Khalil da Saliha ba'a magana. Haka ma Alhaji Shamsuddin, ya yi farin ciki sosai, ɓangaren Hajiya A'isha ma ta yi farin ciki sosai duk da ba ƙaunar Ma'eesha take yi ba amma tana ƙaunar Ma'eesha.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya Ma'eesha na girma har ta isa shiga makaranta aka sanya ta makarantar kuɗi. Sai sai duk weekend akan kai ta gidan kakannin ta ta yi hutu. Don Hajiya takwarar Ma'eesha ce ta tsara haka duk weekend sai an kai ma ta takwarar ta can gidanta ta yi ma ta kwana biyu. Idan kuma ana cikin hutu can take ma ta weekends.
Haka rayuwa ta cigaban da tafiya har Allah ya raya Ma'eesha ta kammala primary school. Kuma har lokacin iyayen ta ba su saka samin wata haihuwar ba.
Sai dai arzikin Ibrahim Khalil ya kara bunƙasa, don kasuwancinsa saidai yake samun cigaba.
Har wata rana Saliha ta samu Ibrahim Khalil da zancen za ta fara kasuwanci ita ma. Sai ya nuna ma ta ai mahaifinsa ma ya yi maganar ta fara kasuwanci har ya ce ta ke ta fadi sana'ar da take so zai ba ta jarin da za ta fara.
Ta yi farin ciki sosai washegarin ranar dama ya kama weekend ne za su je su kai Ma'eesha gidan kakannin nata, don haka suka tafi tare da ita.
A nan ne surukin nata ya tambaye ta wace sana'a take son fara wa, nan ta sanar ma sa cewa ko kowace sana'a ce za ta iya.
Nan ya fara ba ta zunzurutun kuɗaɗen da za ta fara sana'a da su, ya ce ta fara da siyar da atamfofi da leshi da su shadda da material.
Nan ta fara sana'a nan da nan Allah ya sa ma ta albarka ta bunƙasa. Ta fada haɗo wa har da takalmomi da haka da su sarƙa da ƴan kunne.
Don a yanzu haka manyan shaguna ne guda biyu yake da su a kasuwa wanda ake kula ma ta da su. Kuma ta samu mutane ma su amana dake kula da su.
Ma'esha na ta shekaru goma sha uku ta sauke Alkur'ani mai girma aka yi ma su walima. Tarbiyya daidai gwargwado ta samu daga wajan mahaifiyarta. Ma ta mai karamci da Dattaku ku , ta san ya kamata ga ta da hakuri juriya da hangen nesa.
Duk da kasancewar tana da masu ma ta aiki a gida hakan bai sa ta bar Ma'eesha sakaka ba tarbiyya ba, don ta koyar da ita duk wasu aikace-aikace aikace na gidan da girki da komai, wai a cewar ta ƴa mace ce gidan wani za ta je ba kowane namiji ke son mai aiki na ma sa komai ba musamman kula da ɗakinsa da kuma yi ma sa girki. Don haka take saka ya tama shiga cikin ma su aikin suna girki tare da Inno wata Dattijuwa dake yi wa Mummy aiki, matar akwai hankali kuma jininsu ya hadu da Ma'eesha.
Har ma'esha ta kai shekaru goma sha takwas iyayen ta ba su sake samun haihuwa ba. Kuma a lokacin ne ta kammala karatun secondry school. Kuma a wannan lokacin Daddynta ya siya ma ta mota.
Aka koya ma ta driving ɗin motar har ta iya wanda lokacin ne Daddy ya so tura ta ƙasar waje ta yi karatu a can amma Mummy ta hana. Ta ce gara yarinyar ta ta zauna a gabanta tana kallon ta hankalin ta zai fi kwanciya akan ta je can wata ƙasa da ba ta san tarbiyya da ɗabi'ar da za ta koya ba, ita dai a bar Ma'eesha a gabanta tana kallon halin da take ciki don ƴa mace tana da rauni. Don ta ba wa Ma'eesha tarbiyya mai kyau ba ta yarda da yawon gidan ƙawayenta. Ƙawarta daya ce a duniyar nan sai dai abokan karatun ta.
Wata rana Mummy ta fito daga gida tana bayan mota direba zai fita da ita zuwa kasuwa ta duba kayan da babu. Don yanzu har Dubai take fita siyen kaya. Sai ta ga wata mata rakuɓe kusa da gidansu ita da yar biyu saurayi daya sai budurwa guda ɗaya.
Ba ta ce komai ba suka wuce, bayan ta dawo za ta shiga gida tana bayan motar, still su ta fara gani, sai wannan matar ta rugo da sauri ta nufi motar, ganin haka ya sa Mummy ta ce wa direban ya tsaya.
Bayan ta sauke gilashin motar ne ta ce.
"Baiwar Allah lafiya daga ina haka, yaranki ne can?"
Ta daga kai kawai ta kasa magana, da ƙyar ta iya cewa .
"Ki taimaka ma na da abinci yunwa, tun jiya ba mu ci komai ba ni da yara na."
Tana gama fadar haka ta zube a wajen a sumammiya, yayin da saurayi da buduwarwar suka ƙaraso kanta suka kiran sun Mamy, buduwarwar har tana kuka. Da sauri Mummy ya fito cikin motar tana salati.

page1️⃣5️⃣
Tama gama faɗar haka ta zube a wajen a sumammiya, yayin da saurayi da budurwar suka ƙaraso kanta suka kiran sunan Mamy, budurwar har tana kuka. Da sauri Mummy ta fito tana salati.
"Baiwar Allah lafiya?"
Direban ne shi ma ya fito daga cikin motar yana cewa.
"Suma ta yi ya kamata mu yayyafa ma ta ruwa watakila ta farfaɗo."
Da sauri Mummy ta ce .
"Kawo ma na ruwan ko?"
Da sauri ya bude murfin motar ya dauko robor ruwa ya zo ya yayyafa ma ta, ajiyar zuciya nauyi ta sauke sannan ta fashe da kuka tana cewa.
"Yauwa wayyo na shiga uku na lalace ku taimaka ma ma da abinci."
Jin haka ya saka Mummy ta ce .
"Ba damuwa mu je ciki za ku ci abinci."
Laila ta kama mahaifiyar ta ta da taimakon ta ta tashi tana rike da hannunta. Mummy ta ce wa direban ya ja motar zuwa ciki ita za ta karasa shigowa da ƙafa .
Ya shiga cikin motar ya ya tayar suka bi bayansa da ƙafarsu, budurwar na rike da Mahaifiyarsu.
Bayan Mummy ta murɗa handle ɗin kofar ta shiga da sallama ta ce su shigo. Suka shiga ciki kowa ya zauna akan Centre carpet.
"Haba ku tashi ku zauna akan kujera ma na."
Mummy ta fada tana Murmushi. Suka hada baki wajen cewa.
"A'a nan ma ya yi."
Ɗaya daga cikin masu aikin gidan ta kira ta ba ta umarnin kawo abinci wa ɓakin.
Mau aikin ta gaida su ta wuce don cika umarnin matar gida.
Ba jimawa aka cika ma su gabansu da kayan ciye-ciye, ta yi servin ɗin su abincin da za su ci.
Sannan ta zuba ma su farfesun a cikin bowl huda uku kamar yadda ta zuba ma su abinci. Kasancewar ta hana mai aikin ta zuba ma su abinci da lemu.
Ta koma ɗakinta ta basu wuri don su sake su ci abincin.
Tana barin wajen jiki na rawa kowa ya dauki plate ɗaya na abincin suka hau ci cikn haɗama.
Nan da nan suka cinye suka ɗauki farfesun shi ma suka cinye suka shanye romon da lemu suka sha ruwa.
Laila ta buɗe ƙular ta ha sauran abinci ta kara masu duka suka cinye suka lashe plate.
Bayan sun shanye lemu sun sha ruwa ne suna zaune sai ga Mummy ta fito da fara'a tana ma su sannu da zama.
Nan suka hau yi ma ta godiya.
Horn ɗin mota suka ji a bakin gate, nan fa nan maigadin gidan ya bude gata.
Motar ta cinno kai ta shiga cikin nutsu ake driving motar.
Bayan an yi parking motar ne sai mamallakiyar motar ta ziro fararen ƙafarta ta fito daga cikin motar. Hannunta daya riƙe da makullin motar ɗayar hannun kuma rike da handbag ɗin ta.
A hankali take tafiya kamar mai jin tausayin ƙasa.
"Hajiya Ma'esha kin dawo?"
"Eh na dawo ina wuni?"
"Lafiya lau ya karatun?"
"Alhamdulillah."
Daga nan ta shiga cikin ga gidan ta tura kofar falon da sallama.
"Assalamu alaikum"
Gabanta ne ya faɗi sakamakon ganin wannan matar da yaranta ke kiranta da Mamy.
Amma sai ta dake ta karaso ciki ta gaida Mummy.
"Ina wuni Mummy?"
"Lafiya lau kin dawo?"
"Eh Mummy na gaji."
Murmushi ta yi sannan ta ce .
"Ba ki ga baki ba ne?"
Ma'eesha ta kalli Mamy wacce ta ji sam matar ba ta kwanta ma ta ba.
"Ina wuni?"
Washe baki ta yi tana amsa wa Ma'eesha gaisuwar. Sai ta kalli dayan saurayin za ta gaishe shi ya yi saurin cewa.
"Ina wuni ranki ya daɗe."
Murmushi ta ɗan yi sannan ta amsa ma sa cikin fara'a, sai budurwar ita ma ta gaishe ta, ta amsa ma ta cike da fara'a.
Matar ta kalli Mummy ta ce .
"Hajiya taimaka ma na za ki kamar yadda Allah ya rufa ma ki asiri mu ma ki rufa ma na."
"Me kike so na taimaka ma ki da shi in dai bai fi ƙarfina ba zan yi ma ki in sha Allah."
"Ba mu da wajen zama, gidan hayan da muke ciki maigidan ya Kore mu saboda ba mu da kuɗin da za mu biya shi na haya, ga mijina ya rasu yara biyun nan nake da su to ba abun yi tun da ba su damu damar yin karatu ba. Don Allah Hajiya ki taimaka ma na ko za ki samar ma na wajen da za ki raɓa mu za mu dinga yi ma ki aiki dukkan mu, ko ba ki biya ki komai ba in da za ki ba mu abincin da za mu dinga ci muna so Hajiya."
Ta karasa maganar tana fashewa da kuka. Cikin tausaya wa Mummy ta ce kar ki damu ba aikin da muke bukatar ayi mana , ma'aikata sun ishe mu, amma ba na da ikon ba ki wajen zama a gidan nan ba tare da izinin maigidan ba. Amma za ku zauna a B.Q na gidan nan kafin ya dawo sai a san abun yi."
Gabadaya suka haɗa baki wajen yi ma ta godiya suna farin ciki da wannan ni'imar da Allah ya yi ma su.
Mummy ta kalli Ma'eesha ta ce.
Tashi ki kai su BQ ɗakin da ba kowa sai su zauna a ciki.
"To Mummy."
Cewar Ma'esha ta fada tana mikewa tsaye, duk da dai hankalinta bai kwanta da lamarin mutanen ba. Ba yadda za ta yi ne ta hana mahaifiyar ta taimaka ma su amma jiki ta ya ba ta akwai wani abu mara daɗi da zai faru da su a dalilin mutanen nan.
Tana gaba suna bin ta a baya har suka ƙarasa BQ ɗin gidan.
Ta bude kofar ta shiga suka bi ta a baya. Madaidaicin falo ne da ɗakuna biyu a ciki da toilet da kitchen dake nan cikin dakin. Akwatin set ɗin kujeru a falon ɗakina biyu suka kowane akwai katifa a ciki.
Fitowa ta yi ta bar su suka ta jin daɗi suna yaba wajen.