Part ɗin Inna ya nufa ya same ta saman sallaya ta koma barci. Fita yayi ya nufi part ɗin sa.
Makaho Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 115 min read
Har ya fara taka step ɗin sai ya ji a jikinsa ana kallonsa. Juyawa ya yi suka yi idanun biyu da Sidra. Tana tsaye sanye da kayan barci kanta ba hula ta zuba masa idanun ta kamar za ta cinye shi. Ga idanun sun kumbura alamar ta ci kuka.
Ɗauke kansa ya yi ya fara taka matattakar har yana tsallaken stepe.
Yana shiga bedroom ɗin ya same ta kwance ta fara barci.
Sai dai da alama ta yi sallah, don ya ga sallaya da hijabinta in da ta yi sallah ba ta ɗauke ba.
Trolling bag ɗin sa ya dauka ya fara saka kayan da ya san zai buƙata a can.
Ya haɗa komai har da system ɗin sa.
Wanka ya shiga bathroom ya yi ya fito ya shirya cikin ƙananan kaya sai zuba ƙamshi yake yi.
Time ya duba ya ga lokacin tashin jirgi sauran awa ɗaya da rabi.
Idanunsa ya sauke akan ta lokacin da take gyara kwanciya tana yamutse fuska kamar za ta yi kuka.
A hankali ya karasa bakin gadon ya zauna a gefen ta.
Bargon da ta rufe jikinta da shi ya yaye shi. Tana barci ne amma kamar ba ta jin dadin jikinta.
Tura baki gaba take yi tana ɓata rai. Wani abu ya ji ya fisge shi wanda hakan ya saka ya kai bakinsa saman nata ya fara tsotsa.
A firgice ta bude idanun ta tana sauke shi akansa. Tuna azabtar da ta sha ya saka ta saka ma sa kuka.
Kokarin tashi take kokarin yi ya ma ta rumfa da ƙirjinsa. Nan ya shiga sarrafa har ya raba ta da rigar jikinta, da pant ɗin dake jikinta Cikin kukan tausayin kanta take cewa. Sosai yake wasa da ita yana tsotsa duk inda ya ga dama ya shafa in da yake so.
"Yaya Fahad wallahi wajen yana mun zafi, bai ma san me take cewa ba ya fara gigice ma ta.
Ganin yana ƙoƙarin cire kayan jikinsa ne ya saka ta rintse idanunta tare da sadaƙar wa tata ta ƙare.
Lokacin da ta ji yana karanto addu'ar saduwa da iyali ta saka kuka. Lokacin da ya shige ta ne ta rasa hawaye da bakin kuka, don bakin kukan ma ba ta same shi ba. Sai da ya yi awa ɗaya kafin ya saurara ma ta.
Ganin saura mintuna ashirin da biyar jirginsa ya tashi ya saka ya fada banɗaki da saur. Sauri-sauri ya yi wanka ya fito yana tsane kansa.
Closet ɗin sa ya shiga ya shirya cikin wasu kayan. Time ya duba yana sauri ya ɗaura agogonsa ya fesa turare.
Ganin saura mintuna sha goma sha biyu ya kalle ta cike da tausayi, ta galabaita shi kansa y san bai kamata a ce bayan ya kasance ta daren jiya yau da safe ya sake ba kara ma ta wani zafi kan zafi ba. Idanunta sun canza sun yi ja.
"Am sorry."
Ya fada a ƙasan maƙoshinsa wanda shi kaɗai ya ji kayansa. Trolling bag ɗin sa ya dauka da wayoyinsa yana barin ɗakin da sauri.
Suna zaune a main falon gidan suka juya suna kallonsa. Inna, Mama, Farida, Rumaisa.
Idanun Farida a kansa tana kallon tabon dake gefen wuyansa.
Da sauri ta mike tana cewa
"Me ya same ka?"
Shafa wajen ya yi ya tuna cizo da yakushin da Nadra ta yi masa a daren jiya. Shaidar farcen ta ne a gefen wuyansa.
"Kar ki damu ba wani ciwo ba ne."
Kallon Mama ya yi ya ce .
"Saura mintuna goma zan iya rasa jirgi."
"Ai da na ji ka shiru n dauka ka fasa ne."
"A'a zan tafi, Inna ki duba yarinyar nan don Allah ba ta da lafiya."
Wani kallon ta ma sa kafin ta ce .
"Me kuma ka yi ma ta?"
"Ba komai."
Daga nan ya fice suka tashi suna mara ma sa baya. Direba na wajan mota yana jiran fitowarsa.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce ✍️
*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION*
Page4️⃣3️⃣
"Me kuma ka yi ma ta?"
"Ba komai."
Daga nan suka tashi suna mara ma sa baya. Direba na wajen mota yana jiran fitowarsa.
Yana hangen su ya karasa ya karbi trolling bag ɗin Fahad ya saka a bayan motar.
Cikin hanzari ya yi ma su sallama ya shiga motar. Umarnin taka Motar da sauri Fahad ya ba shi, don haka a guje yake taka Motar suka kama hanyar airport.
Su Mama ba su koma part ɗin su ba suka nufi part ɗin Fahad kasancewar ya ce Nadra ba ta da lafiya.
Farida ba ta so zuwa ba amma ganin Inna ta ce su je su gaishe ta ya saka suka bi bayanta gabaɗaya.
Ba kowa a falon don daman ba su yi tsammanin ganin ta a nan ba, bedroom ɗin suka shiga nan suka ganta dunƙule cikin bargo sai hawaye take yi.
Kallo ɗaya Inna da Mama suka yi ma ta suka fahimci Fahad ne ya yi sake yi ma ta waya aika-aika.
Cikin ruɗewa Rumaisa ta karasa bakin gadon tana cewa.
"Aunty me ya same ki dama ba ki da lafiya ne mayar Yaya?"
Ta yi maganar tana kokarin jan bargon da take rufe ciki.
Da sauri Nadra ta rike bargon tana girgiza ma ta kai alamar a'a.
Hakan ya sa suka fahimci babu kaya a jikinta.
Mama ta ce wa Rumaisa
"Duba cikin kanta ki ɗauko ma ta riga mara nauyi ta saka."
Bayan ta ɗauko rigar ne Mama ta kalli Farida da Rumaisa ta ce.
"Ku ba su wuri Inna za ta taimaka ma ta anjima sai mu shigo Mu duba su."
Cike da takaici Inna ta ce .
"Wallahi da zan ga Fahad yanzu nan ba abinda zai haka ban samu madaki na dake shi ba, wani irin rashin imani ne wannan? Ƙaramar yarinya ka addabe ta tin jiya har yau ma ba ka bar ta ta huta ba saboda rashin imani?"
Cike da takaici Farida ta bar ɗakin tana nadamar shigowar ta ɗakin. Rumaisa ma ta mara ma ta baya suka bar part ɗin suka koma downstairs.
Sidra ce zaune a ɗaya daga cikin kujerun falon . Su ma suka zauna ba wanda ya yi yi magana.
Mama ce ta zo ta wuce su ta shiga part ɗin ta.
Cikin takaici Farida ta ce .
"Wallahi Yaya Fahad ya ba ni mamaki, ban taɓa tunanin ajinsa da jin kansa zai sauke su a kan wannan kucakar yarinyar ba. Wacce sam ba ajinsa ba ce ba ta dace da shi ba, ki duba irin matan da suke son sa yake wulakanta su suke kai kansu amma ya kare a wannan ƙaramar yarinyar da ko..."
Kafin ta kai ƙarshen maganar ta ne ta ji Sidra ta saka dariya tana cewa.
"Iska na wahalar da mai kayan kara, ai ki sani Fahad ba kya gabansa bai ma san kina yi ba, ko can dama ba kya gabansa ballantana yanzu da yake da ma ta. Don haka ina mai baki shawarar ki nemi mijin da yake son ki ki aure shi, tun da har tsawon shekaru da kuka yi da shi a gidan nan ba ki iya janye hankalinsa daga wata mace ba har ya kai wannan matakin to ta ki ta ƙare."
Wani kallo Farida ta yi wa Nadra kafin ta ce.
",Ke kuma a su waye, matarsa ko yar matarsa? Ko kuma budurwarsa ko surukarsa ko tsohuwar budurwarsa? Na kasa gane a wani mataki zan ajiye ki. Sai dai na san abu ɗaya shi ne har yanzu kina mutuwar son Fahad duk da yana auren ƙanwarki? A gurɓataccen tunanin ki zai auri ƙanwarki ya aure ki ne, ko kuma kina shirya planning yadda za ki fitar da ita ne ke ki shiga?"
Wani murmushi Sidra ta yi wanda ita kadai ta san ma'anar sa, kafin ta kalli Farida ta ce.
"Lokaci ne zai sanar da ke manufa ta."
"Hmmm ai lokaci sakarai ne ya kan tafi da mahimman abubuwa."
Dariya Sidra ta yi kafin ta ce .
Kuma yakan tafi da sakarkarin burkan wasu, ke kanki kin san cewa babu macen da Fahad yake so sama da ni a wannan duniyar. Domin ni da kansa ya ce yana so na ba ni ce nake bisa yake wulakanta ni ba, kina mace ai abun kunya ne a wajen ki a ce kin kasa janyo hankalin ɗa namiji gare ki har sai wata daga waje ne za ta ɗauki hankalin..."
Kasa ƙarasawa ta yi sakamakon ganin Mama na zuwa.
Sidra ta gaishe ta cikin girmamawa ta amsa cikin dakin fuska da walwala. Har za ta wuce sai ta ce.
"Ya na ga kamar fuskar ki a kumbure har da idanun?"
Murmushi Sidra ta ƙirƙira kafin ta ce
"Sanyi ne idan ina mura hakan na faruwa da ni."
"Ayyah sorry, za ki je asibiti ne ko magani za'a kawo ma ki sai ki sha?"
"Mama Gara na je na ga likita."
"Okay idan kin shirya direba sai ya kai ki."
Jinjina kai ta yi alamar gamsuwa sannan Mama ta bar wajen.
_,Nadra_
Sosai take yin hawaye na takaicin abun da Fahad ya ya yi ma ta. Sai da Inna ta sake gasa ma ta jikinta sosai sannan ta bar ta ta ce ta yi wankan tsarki.
Tana wanka tana zagin Fahad a cikin zuciyarta har ta gama .
Towel babba ta ɗauro a ƙugunta tana tafiya a hankali yayin da ɗaya ke kanta.
Zama ta yi gaban dressing mirror 🪞 ta shafa man shafawarsa.
Daidai lokacin innat ta shigo cikin ɗakin da faranti a hannunta d Ka jera breakfast.
Nadra ta yi nisa cikin tunani ba ta ma san ta shigo ba. Ta shiga duniyar tunanin abun da za ta cewa Sidra. Don tun da har ialahirin jama'ar gidan nan suka zo don duba ta to tabbas Sidra ma ta san abinda ke faruwa.
Da wani ido za ta kalle ta ne bayan ta roƙe ta akan kada ta yarda da Fahad ta bar ma ta shi kuma ta amince ma ta. Kuma ba lallai Sidra ta gane cewa ba yadda ta iya ba ne. Ta roƙe shi Allah Annabi akan ya bar ta bai saurare ta ba
"Tunanin me kike yi ne?"
Murmushi ta ƙaƙaro kafin ta ce.
"Ba komai Inna."
Ganin gashin nata a jiƙe ya sa Inna ta duba kayan akwatin da Fahad ya siyo wa Nadra. Nan ta yi kiciɓis da hand drayer ta mika wa Nadra.
"Karɓi ki busar da wannan dogon gashin kanki, yaushe zai bushe har ki shirya?"
Murmushi ta yi ta karba tana yi wa Inna godiya.
Bayan ya jona a jikin socket ta busar da gashin kanta ta ɗaure su ne ta mike ta ta nufi set na akwatin kayan ta fito da wata Abaya da underwear ta saka .
Dama yunwa take ji don haka ta cika cikinta sosai.
Sannan Inna ta bar part ɗin
_Ma'eesha_
Tana kallon yadda A'isha ke haɗa gawayi cikin murhun gawayi, har ta ce wa Ma'eesha idan akwai Leda ta ba ta.
Ma'eesha ta memo ledoji ta kawo ma ta ta ga yadda ta ƙyasta ashana a jikin ledar ta hura wuta.
Bayan kamar mintuna biyar ne dai ga wutar ta fara garwashi.
Ma'eesha ta ɗauko tukunya ta wanke ta ɗora a wutar.
"Yauwa A'isha ko kin san yadda ake ɗaurin gawayin siyarwa?"
"Gawayin siyarwa kuma Aunty?"
"Eh, ina da buhu ɗaya ina son na ƙulla na dinga siyarwa."
"Eh na sani."
"Yauwa mu je ki nuna mun."
A tare suka shiga kitchen dake tsakar gidan A'isha ta juye gawayin a ƙasa. Kallon Ma'eesha ta yi kafin ta ce .
"Kin siyo leadar ƙulla gawayin ne?"
,Shiru ta yi don ba ta yi tunanin wannan ba, ga shi ko Naira biyar ba ta da shi. Kasancewar A'isha yarinya mai wayau ce ta karanci yanayin Ma'eesha ta ce.
"Ɗari biyu ake ɗaura gawayin yanzu, kuma dama ni ma kullum ina siya ta ɗari huɗu idan zan yi sana'a ta, don haka bari na siyo ma ko ledar da ɗari huɗun nan idan an gama ƙulli sai na ɗauki gawayin ɗari huɗu."
Ɓoyayyen ajiyar zuciya Ma'eesha ta sauke kafin ta ce .
"To A'isha na gode."
Daga nan ta fita don siyo gawayin.
Bayan ta dawo ne ta ce wa Ma'eesha ta ta kawo ƙaramin roba ko kwano da za su dinga awo da shi .
Ta kawo kwano uku ta ce wanne zai yi, sai A'isha ta zabi daya daga ciki ta ce zai yi daidai.
Haka kuwa aka yi tana aunawa tama zubawa Ma'eesha na ɗaure bakin ledar.j
Kuma ta kan tashi tana duba girkin da ta ɗora a wuta.
Har suka gama suka ƙirga, kuma Alhamdulillah an samu riba sosai. Don lokacin da Ma'eesha ta siye buhun gawayin dubu bakwai ne kuma yanzu an ɗaura na dubu goma sha ɗaya a ciki.
Duk kayan jikinsu ya yi baki musamman A'isha da ta yi zaman zubawa.
Kallon Ma'eesha ta yi tace.
"Aunty ki dinga neman tsohon zani idan za ki daura saboda ɓata jiki."
"To A'isha na gode, ki tsaya ki yi wanka ma na."
"A'a yanzu xan je gidan na yi ."
Don haka sanya zuba ma ta jallop ɗin taliyar da ta dada a kula ta ba ta ta kai gida.
Sannan ta ce ta dauki gawayin kudin ta na dari hudu ta kuma kara na ɗari huɗu, sai dai sam A'isha ta ce ba za ta amsa ba duk yadda ma'eeha tayi hakuri ta bar ta.
Bayan fitar Aisha Ma'eesha ta shiga banɗaki don yin wanka.
Bayan ta fito ta shirya cikin atamfa Holland riga da zani.
Ta zauna t hada tagumi cikin yanayin sanin madafa. Ga shi ASP ya ce sai sun yi bincike zai kira ta.
Ga yunwa tana ji amma ta kasa cin komai.
_Makaho_
Tun da ya idar da sallar asuba ya zauna yana karatun Alqur'ani, da safe ya yi azkar din safiya.
Yana zaman jiran shigowar daya daga cikin mutanen da suka kawo shi nan.
Jin shiru ya saka shi ya mike tsaye bayan ya lalubi sandarsa. Da lalube har ya gano in da ƙofar ɗakin yake, ya ha ƙofar amma sai ya ji ta a datse, wato an rufe da key kenan. Don haka ya hau dukan ƙofar don a zo a bude ma sa ƙofar.
Amma sai ya ji shiru ba alamar za'a zo a bude ma sa kofar, cikin fusata yake dukan ƙofar wanda hakan ya sa ɗaya daga cikin mutanen zuwa ya buɗe ƙofar.
Tun kafin ya yi magana dai MAKAHO ya ce .
"Ku mayar da ni inda kuka ɗauko Ni."
Gajeren murmushi Mutumin ya yi kafin ya ce .
"Kar ka manta mun sanar da kai a hannun waɗan da suka yi garkuwa da kai. Kuma da dukkan alama kashe ka suke da niyyar yi, ba don Allah ya sa mun je akan lokaci da yanzu babu kai a duniyar nan."
"Ba ni hanya na fita !"
Ya fada a kausashe.
"Okay ina zuwa."
Ya faɗa yana lalubar wayarsa a aljihu, bayan ya fito da wayar ne ya ya nemi wata lamba ya danna kira.
Bugu biyu aka ɗauka daga can ɓangaren aka ce.
"Assalamu alaikum "
"Wa'alaika Salam."
"Ina fatan ba wata matsala kuma, yana cikin ƙoshin lafiya ko?"
"Eh yallaɓai, ya tayar da hankali akan sai ya koma gida ne."
"Okay ba damuwa a mayar da shi gida cikin aminci."
"Okay sir."
Daga nan ya katse kiran wayar ya kalli makaho ya ce.
"Za ka iya zama ka yi breakfast kafin mu tafi?"
"Ba zan iya ba."
Ya faɗa ransa a ɓace. Murmushi Mutumin ya yi kafin ya kira wata lamba ya ce su fito da mota za su mayar da shi gida.
Kallon Khalifa ya yi ya ce.
"Za ka iya tafiya ko na rike ka?"
"Ka tafi ina bin ka a baya."
Daga haka ya yi gaba yayin da Khalifa Makaho ke bin sa a baya ta hanyar jin sautin tafiyar takalminsa.
A harabar gidan suka tarar da wata mota mai tinted glass tana jiran su, mutane biyu ne a cikin motar, direba dai kuma wani da yake da wajen me zaman banza.
Wanda ya fito da Khalifa ya bude murfin bayan motar ya ce wa Makaho ya shiga, bayan ya laluba ya shiga ne shi ma ya zauna a gefen sa.
Direba ya tayar da motar yayin da security ya wangale ma su gate ɗin gidan.
Suna tafiya wanda ke zaune gefen direba ya ɗan juya ya kalli makaho ya ce
"Ya kamata ka zama mai taka tsantsan wajen sanin inda za ka dinga zuwa da kuma lokutan inda kake fita. Sannan wace ce wannan yarinyar da kake zaune gida ɗaya da ita me ye alaƙar ku f ita?"
Tsuke fuska Khalifa ya yi kafin ya ce.
",Ina ruwan ku da ita? Ki tsaya matsayin ku Mallamai."
Daga nan ba wanda ya sake magana har suka ƙarasa suka ajiye shi ƙofar gida suka kama hanya suka koma.
Tsaye ya yi rike da snadar jagoransa na tsawon mintuna biyu, kafin ya ɗaga ƙafarsa cikin sanyin jiki ya doshi ƙofar gidan. Ya kai hannu zai tura ƙofar falefalen kenan ya ji sheshsheƙar kukanta na tashi.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan✍️
*JAJIRTATTU WRITERS ASSOCIATION*
Page4️⃣4️⃣
Tsaye ya yi rike da sandar jagoransa na tsawon mintuna biyu, kafin y ɗaga ƙafarsa cikin sanyin jiki ya doshi ƙofar gidan. Ya kai hannu zai tura ƙofar falefalen kenan ya ji sheshsheƙar kukanta na tashi.
Take ya ji jikinsa ya kara sanyi duniyar ta yi ma sa zafi, babu abun da ke cikin zuciyarsa sai tausayin Ma'eesha.
Ya san tana cikin matsin rayuwa, ta taso cikin hutu da jin dadi, sam ba ta san wani abu wai shi matsin rayuwa ba sai a dalilinsa gani yake yi ai duk saboda shi yake fuskantar wannan ƙalubalen. Yarinyar da ta tashi cikin ƙererren gida cikin hutu da jin daɗi, gidanta ɗakinta A.C motarta A.C ga ma su yi ma ta aikin duk hidimar da take so ta ci lafiyyaen abinci ta sha ruwan roba da duk wani nau'in abun sha da yake so. Amma yanzu rayuwa ta juye da ita wai ita ke rayuwa cikin wannan akulkin gidan. Cikin zafi da sauro.
Ƙwalla ce ya ji ta ciko ma sa idanunsa ya yi Saurin ɗauke ta da sauri sannan ya tura ƙofar gidan da sallama a bakinsa.
Ba ta san ya shigo ba tana can ɗaki tana kuka.
Har ya isa bakin ƙofar ɗaki. Ya yaye labulen ɗakin ya yi shiga da sallama a bakinsa.
Kamar daga sama ta ji sallamarsa, a firgice ta ɗago kai tana kallonsa. Gani take yi kamar gizo ne yake yi ma ta don haka sai ta mayar da kai ta haɗa da guiwarta ta cigaba da rera kuka.
"Ma'eesha."
Ya kira sunan ta cikin nitsatstsiyar muryarsa. Wanda jin haka ya saka ta tashi da sauri ta faɗa jikinsa ta rungume shi.
Ƙam ta haɗe jikinta da nashi ta ƙanƙame tamkar wani ne zai ƙwace ma ta shi.
Kwantar da kanta ta yi a ƙirhinsa tana cigaba da rera kuka. Bayanta yake bugawa alamar rarrashi.
Ajiyar zuciya ta sauke cike da samun mutuwar da ta daɗe ba ta ji ta ba. Wannan ne karon farko da jikinta ya hadu da na shi. Ji take yi kamar su dauwama haka har ƙarshen rayuwarsu.
Tsawon mintuna goma suna a haka kafin ya janye jikinta daga nasa kafin ya ce.
"Ki yi haƙuri ki daina wannan kukan haka nan, ya isa don Allah na dawo cikin ƙoshin lafiya ba abun da suka yi ma ni."
Da gaske ba a bun da suka yi ma ka, ka tabbatar? To me ya sa suka dauke ka idan ba komai za su yi ma ka ba , meye amfanin hakan? Kana lafiya ba abinda ke yi ma ka ciw?"
"Ina lafiya ba komai ba abinda ke yi ma ni ciwo kada ki damu."
Ta dinga duban jikinsa ko za ta ga wani tabo amma babu, ta tabbatar ba abinda ya same shi ta saki murmushi tana cewa.
"Alhamdulillah, na gode Allah ba abin da ya same ka."
"Yunwa nake ji Ma'eesha ban ci abincin da suka ba ni ba."
"To zauna bari na kawo maka abinci."
Ta zaunar da shi bisa tabarma jikinta har rawa yake yi wajen zuwa zuba masa abinci.
Ta zuba ma sa jallop ɗin taliyar da ta dafa, da kuma ruwan Lipton.
W gabansa ta ajiye bayan ta tabbatar da ruwan Lipton ɗin ya yi daidai yadda zai iya sha sai ta kafa ma sa kofin a baki tana mai yin Bismillah.
Ba musu ya bude baki yana sha. Kafin ta fara ba shi taliyar a baki.
Yana ci har sai da ya ƙoshi.
Ta sa baki ta fasa ledar pure water ta bashi ya sha.
"Alhamdulillah."
Ya furta yayin da ita kuma ta ce .
"Ma sha Allah."
",Ke kin ci abincin kuwa?"
"Yanzu dai zan ci tun da na gan ka cikin ƙoshin lafiya."
Tausayin ta ya sake shigarsa cikin sanyin murya ya ce.
"Allah ya yi ma ki albarka."
Da Amin ta amsa tana fara cin abincin.
*America/Washington DC*
_Fahad_
Ambassador Fahad ya isa America da babban buri, ya wakilci Nigeria cikin gaskiya da mutunci. Tun farkon aikinsa yana nuna ƙwarewa da hikima wajen tattauna wa da shugabanni. Yana ƙoƙarin ƙarfafa dangantaka tsakanin kasashen guda biyu.
Ko da ta isa ƙasar shi kansa ya kasa samun mutuwar zuciya kan abun da ya yi wa Nadra. Ya kamata a ce ya kula da ita amma bai damu damar hakan ba.
Ga kunyar iyayen nasa da yake ji, shi ya sa ya kasa kunna wayarsa ballantana ya kira Mama. Don ya san tabbas sai ta yi ma sa fadar abunda ya aikata.
Hakan ya saka har dare ba bai samu damar kiran kowa ba har ya kwanta ya yi barci.
Da Asuba ya tashi a gidansa dake America, ya zauna shiru yana shan coffee yana kallon saƙonnin da suka shigo daga Nigeria . A yau akwai muhimman taro da zai halarta.
Da safe ya shiga ofishin jakadanci cikin nutsuwa. Ma'aikatansa suka gaishe shi cikin girmamawa. Ya fara duba takardu da rahotanni. Yana tambayar su game da matsalolin da ƴan Nigeria ke fuskanta a Amurka.
Da rana ya je wani babban taro tare da jami'an gwamnati. A wajan taron ya yi magana cikin hikima da nutsuwa, yana kare muradun ƙasarsa.
Duk wanda ya saurare shi zai fahimci matashin mutum ne ma mai ilimi da wayewa.
Sai yamma ya koma gidansa a gajiye.
Bayan sallar Isha'i yana zaune a falonsa da laptop ɗinsa da ya zuba wa idanu.
Gajeren murmushi ya yi lokacin da ya kalle ta ta fito daga toilet tana ɗaure da towel. Ganin yadda ta tura baki ne ya ba shi dariya, kallon lips ɗin ta ya yi yana tuna irin tsotsan da ya yi ma sa.
Yana kallon ta har ta shiga closet ɗin sa ta shirya, Inna na zaman jiranta ta fito ta ba ta breakfast ta fara sha.
Daga nan ya rufe laptop ɗinsa ya lalubo wayarsa.
Lambar Mama ya dannawa kira har ta katse ba ta ɗaga ba, a kira na biyu ne ta ɗaga tare da yin sallama.
"Assalamu alaikum."
"Wa'alaiki Salam. Barka da warhaka Mama."
"Yauwa Barka dai ya aiki?"
"Alhamdulillah."
"Sai yanzu ka ga damar kira kuma an kira ka baya shiga?"
"Afuwa Mama ina tsoron ki yi ma ni faɗa ne."
"Faɗa kam dole ne na yi ma ka shi, saboda ka yi a abun da za'a yi ma ka faɗa. Kai da bakinka ka faɗa ma ni cewa kai ba ka son yarinyar nan da aka aura ma ka ita, za ka sake ta ne ta je ta auri wanda take so. To akan wani dalili ne zai sa har ka yi gigin saduwar aure da ita idan ba ka son ta, ko ka canza shawara ne?"
Duk da ita mahaifiya ce da nauyi ta yi ma sa wanann Maganar amma hakan ya dace don yanzu ba ta fahimci in da ya sa gaba ba."
"Mama ni fa har yanzu ba na jin son yarinyar nan a zuciya ta. Kuma abun da ya faru tsakani na da ita ba yana nufin na fara son ta ba ne, kar ki manta ma su bin karuwau ai ba don suna son su ba ne, kawai suna biyan buƙatar su ne dan kau da sha'awar su da zaran sun biya buƙatar su shi kenan, wannan ba soyayya ba ne. To haka abinda ya faru tsakanina da Nadra wannan ai ba shi ne soyayya ba. Kawai dai na biya buƙatar kaina ne saboda ita ce kadai Allah ya halatta ma ni na kusance ta ba tare da na saɓa ma sa ba. Mama da ba don gudun aikata zunubi ba idan kika ga wayayyun ƴan matan da suke bi na ina guje ma su ai ko kallo wannan yarinyar ba ta ishe ni ba. Har yanzu na kara rabuwa da ita ne saboda mutuncin iyayenta amma ba wai don ina son ta ba. Yanzu abu guda na sani yanzu yake ɗan damuna daga jiya zuwa yau. Tun lokacin da mu'amalar aure ya shiga tsakani na da ita na ji na daina jin haushinta, yanzu tausayinta nake yi, ga shi tun da na zo ƙasar tunanin yarinyar ya ƙi barin zuciya ta har sai da na kalle ta na ji nutsuwa anya yarinyar nan ba mayya ba ce ta lashe ma ni kurwa a daren gabaɗaya tunanin ta nake yawan yi na kasa gane me ya sa."
Murmushi Mama ta yi mai cike da ma'anoni kafin ta ce.
"Wato saboda ba ka da kunya ni mahaifiyarka kake yi wa waɗan nan zantuka ko?"
Dariya ya yi ya ce .
"Mama yanzu fa ba zamanin baya muke ba, idan ban sani jiki na faɗa ma ki abun da ke raina ba da qa zan yi? "
"Hmm"
"Yauwa Daddy ya ce na kai yarinyar nan ta zaɓi motar da take so, tafiya ta kama ni ba tare da na shirya ba, don haka zan kira Aunty Rahama a waya su tafi tare da ita sai ta zabi wacce take so."
"Okay ba damuwa, amma sai zuwa gobe ko jibi idan jikinta ya kara warware wa."
Fira suka ɗan taɓa sannan suka yi sallama ya kashe kiran.
_Sidra_
Shirya wa ta yi cikin riga da siket na leshi, ɗinkin ya kama ta yayin da duk surar jikinta suka kasace a bayyane. Shirin mayafi ta rataya a gefen kafaɗarta. Tana rike da handbag ɗin ta da wayarta a hannunta.
Sai zuba ƙamshi take yi tana taku ɗai-ɗai da dogon takalmin ta ma su tsini, sai zuba ƙamshi take yi.
A haka ta fito zuwa falon, Mama ce tare da Inna suke zaune a falon.
Jin takun takalmi ya sa suka juya suna kallon gefen, a hankali take taku sautin takalmin na bada sautin ƙwas ƙwas ƙwas. Kayan jikinta Inna ta kalla ta taɓe baki tare da cewa.
"Gwada da Allah ya sa jikana bai auri wannan yarinyar ba. Wani hanin ga Allah baiwa ne, sai Allah ya bashi kamilalliyar yarinya mai kunya."
Mama dai ba ta ce komai ba har Sidra ta ƙaraso wajen.
"Barkan ku da hutawa."
Ta fada tana zama kan kujera. Mama ce ta amsa da .
"Yauwa kin fito ko?"
"Eh Mama."
"Okay bari na sanar wa direba ya kai k"
"No Mama na fi son na yi driving da kaina."
"Okay, bari na ba ki mukullin motata."
Mama ta tashi ta nufi ɗakinta don ɗaukowa Sidra Sidra mukullin motarta.
Daidai lokacin Aunty Rahama ta yi sallama ta shigo, tana rike da hannun Baby Zahrah.
"Wa'alaiki Salam warahmatullah. Ku ne a gidan yau ma saboda ba ku gaskiya da yawan fita ko?"
"Eh na zo gaida ƙanwata ce Rumaisa ta kira ni ta sanar da ni wai Nadra tana nan gidan kuma ba ta da lafiya. Na ce mun yi waya da Mama amma ba ta faɗa ma ni ba."
"Kai Rumaisa akwai gulma, Allah ya shirye ta."
Mama ta faɗa tana mikawa Sidra key din motarta.
Ta karba tana cewa.
"Aunty Rahama Ina wuni?"
"Lafiya lau Sidra kin zo duba ƙanwarki ce?"
"Uhmm"
Ta furta tana nufar kofar waje . Da kallo suka bi ta Inna ta ce.
"Wa ya faɗa ma ki duba kanwar ta zo?
"Nan Inna ta ba Aunty Rahama labarin korar da Mahaifin Sidra ya yi ma ta da yadda ta zo Babanku ya ce idan ya dawo zai kai ta ya ba wa Mahaifinsu haƙuri."
"Allah ya kyauta."
Aunty Rahama ta faɗa ta durkusa tana gaida Mama, sannan ta gaida Inna. Baby Zahrah ta zauna kan ƙafar kakarta.
"Ina Nadra take ne?"
Mama ta ba ta amsa da cewa.
"Tana can ɗakin Yayanku?"
"Can aka kai ta?"
Inna ta yi saurin cewa.
"Can dai jarababben ƙanin naki ya kai ta. Yarinyar da yake ta ikirarin baya so to tana can ya karɓi budircinta ya bar ta cikin wahala."
Murmushi kawai Sidra ta yi ba tare da ta ce komai ba.
_Nadra_
Tana zaune a bakin gado ta yi tagumi tana tunani, me ya sa har yanzu Aunty Sidra ba ta nemi in da take ba, me ya sa har yanzu ko wayarta ba ta kira ba.
Wayarta ta ɗauka ta lalubo lambar Aunty Sidra ta danna ma ta kira.
Daidai lokacin da Sidra ta shiga motar Mama tana shirin yi wa motar key kenan sai kira ya shigo wayarta.
Ganin Nadra ce sai da ta yi tsuki kafin ta ɗaga ta ce.
"Ya aka yi ne?"
"Assalamu alaikum."
Nadra ta yi mata sallama cikin sanyayyiyar muryarta.
"Aunty kina cikin gidan nan kuwa?"
"Idan ba na ciki akwai inda kika aike ni ne?"
"Allah ya ba ki haƙuri. Dama na ga shiru ne ban gan ki ba tun shekaranjiya."
"Me ya hana ki saukowa ƙasa?"
"Ba na da lafiya ne?"
"Me ya same ki?"
Shiru ta yi ta kasa cewa komai. Dariyar bakin ciki Sidra ta yi kafin ta ce.
"Wato na zo na gaishe ki ko hamshaƙiya mandiya farkar me gari."
Ƙwallar da ya cika ma ta idanun ne ya samu nasarar zubowa.
"Ya aka yi kika yi shiru munafuka maƙaryaciya maciya amana, kin yi zancen karya, kin yi alƙawari kin saɓa na yarda da ke kin ci amanar yardar da na yi ma ki. To ki sani wallahi wallahi wallahi ki sani ja da baya ga rago ba tsoro ba ne sake shirin faɗa ne. Don wanann abun ya shiga tsakanin ki da Fahad kar ki ɗauka na haƙura ina nan akan baka na dole ki tattara tsumman rayuwarki ki bani wajen da kike da zaman wuccin gadi."
*Maman Ihsan ce.*✍️
09065327995
*MAKAHO NE*
*NA*
Maman Ihsan ce✍️
*SADAUKARWA*
Wannan shafin sadaukarwa ne gare ki masoyiyar arziki AMMEY LAYLERH alkhairin Allah ya kai gare ki a duk in da kike. Allah ya bar zumunci masoyiya 🥰
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️
Page4️⃣5️⃣
Ya aka yi kika yi shiru, munafuka maƙaryaciya maciya amana, kin yi zancen karya kin yi alƙawari kin saɓa, na yarda da ke kin ci amanar yardar da na yi ma ki. To ki sani ja da baya ga rago ba tsoro ba ne sake shirin faɗa ne. Don wanann abun ya shiga tsakanin ki da Fahad kar ki ɗauka na haƙura ina nan akan baka na dole ki tattara tsumman rayuwarki ki ba ni wajen da kike zaman wuccin gadi."
Cikin kuka Nadra ta ce.
Aunty Sidra don Allah ki saurare ni ba yadda kike tunani ba ne, wallahi na fi kowa bakin cikin wannan abun da ya faru , ba da..."
Salla rufe ma ni baki, da a baya ne idan kika fada Mani magana zan yarda, saboda na san ba kya yin ƙarya. Amma yanzu kin canza."
"Wallahi ba karya nake yi ma ki ba, ba da son raina hakan ta faru ba, ko da kika ce na je ɗakin Mama na kwanta can na nufa. Ina zuwa ne na tarar da shi a cikin ɗakin Mama. Shi ya ce wa Mama ta ba ni fruit na kai ma sa. Na ce wa Mama ɗakinta zan kwana ta hana ni wai sai gobe idan mijina ya tafi. Ta ba ni fruit na kai ma sa. Kai ma sa da na yi ne ya ba shi damar isar da manufarsa a kaina. Ba yadda zan yi na yi iya ƙoƙarina don ganin na ƙwaci kaina amma ya fi ƙarfina bai bani damar hakan ba."
Ta karasa maganar tana gunjin kuka. Cike da takaici Sidra ta ce.
"Ko ma dai mene ne Fahad nawa ne dole ki bar ma ni shi. Majiya da ba ta ranmin kanta sai wani ya gina sannan ta shige."
Tana faɗar haka ta katse kiran wayar tare da yi wa motar key ta bar gidan.
Cikin sanyin jikin Nadra ta ajiye wayar tana cigaba da rera kuka.
_Daddy_
Zaune yake a ɗakinsa ya saka hoton Mummy da Ma'eesha yana kallo. Ƙwalla ne suka cika ma sa idanunsa. Ya saka hannu ya goge .
Shi sam ya kasa gane dalilin da ya saka baya iya taɓuka komai a cikin gidansa. Baya da kataɓus sai abun da Mamy ta ce yake zartarwa. Ga shi rashin Matarsa uwargidansa da ba ta duniyar da kuma rashin tilon ƴarsa da ya mallaka a duniya ya aurar da ita ga musaki faƙiri yana ji yana gani amma ya kasa komai. A hankali ya bude baki ya furta sunan Ma'eesha.
"Ma'eesha. Ki yafe ma ni, ina ji a jikina ba daidai nake ba, kuma na san ban kyauta wa rayuwarki ba, na cutar da ke, na yi ƙoƙarin hana zuciya aikata hakan na kasa."
Sai ya fashe da kuka. Motsin shigowa ɗakin da ya ji ne ya sa shi yin shiru ya kasa magana.
Kansa a sunkuye ta shigo ɗakin, idanunta akansa ta na nazarin sa.
"Alhaji."
Ya kasa ɗago kai ya kalle ta.
Ta kira sunan a kausashe wanda hakan ya saka shi ya ɗago kai ya kalle ta da sauri.
"Yau ma keɓewa ka yi kana kuka ko?"
"A'a Hajiya ba kuka nake yi ba."
Taɓe baki ta yi kafin ta ce.
"Idan ma kukan kake yi wannan matsalar ka ce, ka je ka yi ta yi kai ne a damuwa. Yarinya tana gidan mijinta cikin kwanciyar hankali me ye za ka damu kanka?"
Idan ita da damu da kai ai da ta zo ko sau daya ne ta duba ka. Amma ita ma sai ta zaɓi zama da wannan Makahon mijinta akan ka, da ba don haka ba ai da ta zo nan gidan idan tana son ganinka. Amma duk ka yi bi ka damu da ita bayan ba ta damu da ka kai ba."
Ta karasa drawer da yake ajiye kuɗi ta ɗebi iya son ranta ba tare da ta ce ma sa komai ba ta fice. Da ido ya bi ta har ta fita daga cikin ɗakin.
Tana fita ta nufi ɗakin ƴar ta Laila, wacce yanzu ita ke cikin ɗakin Ma'eesha. Wanda ya zama mallakin ta a yanzu.
Tana kwance akan tangamemen gadon ta ɗora ƙafa daya kan ɗaya tana chatting.
Inno wacce a baya ita ce mai yi wa Ma'eesha aiki, kamar gyaran ɗaki wankin toilet wankin kayanta da abin da ba'a rasa ba.
Inno ta fito daga banɗaki bayan ta gama wankewa daidai lokacin da Mamy ta shigo cikin ɗakin.
"Hajiya na sake wankewa."
Yamutse fuska Laila ta yi tare da cewa.
"Wannan karon ma idan na shiga na ga bai ma ni ba Tanko zai ɓaci. Fita ki bar mun ɗaki."
Mamy ta raka ta da harara tana cewa.
"Munafuka ta yi ta sunkuyar da kai ƙasa."
Inno dai ba ta ce komai ba, tana takaicin yadda Laila sa'ar ƴar cikinta take wulakanta ta. Sau uku tana wanke banɗaki amma sai ta ce bai fita ba ta sake wankewa Ga shi haka za ta bar banɗakin da ƙazanta ko pad ta cire idan tana period nan take ajiye ma ta sai dai ita idan ta je wanke wa ta ɗauke. Ko period take yi nan za ta bar alama sannan ta kira Inno wai ta je ta gyara. Idan ko ta cire kaya nan za ta zubar da su ƙasa sai inno ta kwashe. Wanda lokacin da Ma'eesha take ɗakin ba za ka taba gane cewa tana period ba idan ya cire kaya sai dai ta ajiye a inda suka dace.
Mamy ta kalli Laila ta ce .
"Ga kudin na san dubu ɗari uku sun ishe ki ko?"
Kamar za ta yi kuka ta ce.
"Ni har yanzu na kasa samun gatan da Ma'eesha ta samu a cikin gidan nan. Ita lokacin da take nan ai miliyoyin kuɗaɗe ne a account ɗin ta sai dai tayi ta zara tana bukatar ta, ki duba ranar da aka aura ma ta makahon nan irin miliyoyin kuɗin da aka cire a account ɗin ta. Amma ni kullum idan ina bukatar sai dai na yi magana ki ɗebo dubu ɗari biyu ko uku ki ba ni."
Daga ƙafarta ta yi cikin sigar rarrashi ta ce
"Ki kwantar da hankalinki da sannu zan saka ke ma ya bude ma an ki account ya zuba ma ki kuɗaɗe. Yanzu na kasa gane kansa ne kullum ckikin ƙunci yake. Kuma kin san Ma'eesha tun tana karama suke tara ma ta kudin lokaci guda ba ne suka saka ma ta."
"To ina su gwala-gwalan nata da kika ce za ki kawo ma ni."
Cikin damuwa Mamy ta ce.
"Har yanzu na kasa gane in da ya ajiye gold din nan."
Cikin takaici Laila ta tashi ta figi kudin ta zuba a handbag ɗin ta ta fice daga dakin bayan ta ɗauki wayarta.
_Makaho_
Yana zaune a tabarma a barandar kofar ɗakinsu. Ma'eesha na zaune a gefen sa ta zuba ma sa idanu tana kallonsa. Ji ya yi a jikinsa ana kallonsa don haka ya ce.
"Wannan kallon fa ba mene ne?"
Murmushi ta yi mai sauti kafin ta ce.
"Idan ban kalli mijina ba waye zan je na kalla?"
Dariya ya yi kafin ya ce .
"Ba wanda za ki kalla sai ni kuwa, saboda ni ne na ki. Ni ma Allah ya nuna ma ni ranar da idona za su bude na kalli Matata farin ciki na."
"Amin ya Allah."
Ta faɗa tana murmushi, zuciyarta cike da farin ciki. Haka kawai take jin kanta cikin nishadi da farin ciki da walwala.
Ɗan yamutse fuska ta yi tana cije lips ɗin ta.
Tuna date ta yi ai yanzu ne lokacin period nata.
"Inna lullahj wa'inna ilaihi raji'un."
Shi ne kalmar da ta fada a cikin zuciyarta. Domin ita kadai ta san irin wahalar da take sha idan tana period. Don tana jin jiki sosai. Ga shi ko Naira biyar ba su da shi a cikin gidan nan, ballantana ta yi tunanin siyen magani da alluran da ake yi ma ta.
Sallama suka ji yaro ya yi daga ƙofar gidan. Sai suka amsa a tare yarin ya shigo.
"A bani gawayi na ɗari huɗu."
Cewar yaron yana miƙa ma ta ɗari huɗu ƴan ɗari biyu guda biyu. Daga gidan Mallam Liman yake kasancewar A'isha ta yi wa Ma'eesha tallar gawayin wajen mutanen gidansu.
Tana rike da mararta ta dafa su da hannu biyu. Ga yaron tsaye yana miƙa kuɗi. Ta kalle shi da idanunta da suka fara canza kala, kafin ta yi karfin halim cewa.
"Aje kudin nan ka je ka ɗauka a wancan kitchen ɗin."
Yaron ya ajiye ya nufi kitchen don ɗauko gawayin. Jin yadda ta yi magana ya sa Makaho cewa.
"Ma'eesha lafiya kike kuwa?"
Gudun ta tayar ma sa da hankali ya saka ta yin murmushi mai sauti ta ce .
"Ba komai kada ka damu."
Ta yi kokarin ganin murya ta ba ta yi raunin da zai gane ba .
Yaron yana sai anjimanku, Makaho ne ya iya amsa ma sa. Makaho ya ce.
"Kika ce idan anjima na ba ki labarin abun da ya faru bayan an sace ni ko? Yanzu zan ba ki labarin komai har zuwa dawowa ta."
Tana jije lips cike da ƙarfin hali da dauriya ta ce.
"Mu bari zuwa wani lokacin, yanzu bari na shiga na ɗan kwanta.
"Kamar ba ki da lafiya."
"Lafiya ga ƙalau."
"Na san sai ba kya barcin yamma, don ke ma kin san bai da alfanu."
Ba ta iya sake yin magana ba a daddafe ta shiga ɗakin ta zube kan katifa ta fara murƙususu tana hawaye.
_Sidra_
Tana fita direct unguwar su ƙawarta Khadijah ta zame. A ƙofar gidan ta dinga danna horn. Maigadi ya leko bayan ya ga ko waye ne sa sai ya buɗe ma ta gate ɗin gidan.
Bayan ta yi parking ne ta fito da sauri kasancewar ta san daidai wannan lokacin Mahaifiyar Khadijah ba ta gida ta je wajen aiki.
Haka ta faɗa cikin falon a guje tana kuka. Khadijah na kwance kan kujera tana chatting kallo daya ta yi ma ta ta ɗauke kai, ci gaba da abun da take yi ta yi ba tare da ta kula Sidra ba.
Ganin haka Sidra ta fisge wayar daga hannun Khadijah ta yi jifa da wayar saman ɗaya daga cikin kujerun da suke falon.
Murmushin takaici Khadijah ta yi kafin ta ce.
"Na san wannan ranar tana zuwa. Ranar da za ki zo kina yi ma ni kuka ba, irin haka na guje ma ki amma kika ƙi saurara ta kuma biye wa shawarar Sady baby. Ga shi yanzu ta kai ki ta baro. Gani kike yi kamar ita ce mai ƙaunarki, ko kiran ki na yi ba ki ɗaga wa, ranar da za ki gudu ba yadda ban yi da ke ba ko saboda mutuncin zuri'ar gidan ku da tozarta su da za ki yi. Amma kika ƙi saurara ta. Kin ɗauka za su jira ki ne sai kin dawo kafin a sake maganar daurin auren ko?"
Murmushin takaici ta yi kafin ta ce.
"Sai kuma kika yi saɓanin fahimta ya kasance aka aura ma sa ƙanwarki a madadin ki. Kuma na ji dadin hakan dama ita ce ta dace da shi."
"Lallai Khadijah yau na san cewa ba ki so na ba ki ƙaunata, abun har ya kai haka? Ni kike taya wa farin ciki.?"
"Da kin saurare ni hakan za ta faru ne?"
"Duk wannan ya isa, so nake yi ki ba ni shawarar da zai sa Fahad ya zama mijina."
"Wani kallon ba ki da hankali Khadijah ta yi ma ta kafin ta ce .
"Kin taɓa ganin in da aka haɗa ya da ƙanwa zaman kishi su auri namiji daya su zauna matsayin kishiyoyi? Mu fa musulmai ne ba maguzawa ba."
"Amma idan ya saki ƙanwa ko ta mutu zai iya auren yayarta ko?"
"Eh zai iya. Amma an fi yi idan ƴar uwa ce ta mutu zai iya auren ƴar uwarta, amma idan ya sake ta ne tana raye akwai kunya ki auri mijin ƙanwarki."
Wani kallo Sidra ta yi ma ta kafin ta ce.
"Kunya, gaba na ba shi ba baya ba. Kuma duk hanyar da zan sai na bi shi wajen ganin na mallaki Fahad kamar yadda na sa wa raina cewa nawa ne shi kaɗai har gaban abada."
"Hmmm Allah ya shirye ki."
Ba ta sake magana ba ɗauki wayarta ta kira lambar wayar ƙawarta Sady baby.
Bugu ɗaya ta daga tare da cewa.
"Ƙawata."
Sidra ba ta amsa ba ta ce.
"Kina ina ne?"
"Ina nan Kaduna."
"Okay gani nan zuwa."
"Allah ya sa lafiya don ni tsoron ki nake ji "
"Ki kwantar da hankalinki mafita za ki ba ni."
Tana gama fadar haka ta dauki handbag ɗin ta. Ko kallon Khadijah ba ta sake yi ba ta fice daga falon . Da kallo Khadijah ta bi ta tana yi ma ta addu'ar shiriya.

Page4️⃣6️⃣

Tana gama fadar haka ta ɗauki handbag ɗin ta. Ko kallon Khadijah ba ta sake yi ba ta fice daga falon. Da kallo Khadijah ta bi ta tana yi ma ta addu'ar shiriya.
"Allah ya shirye ki Sidra. Da na ga kin shigo kina kuka na dauka nadama kika yi ashe ba haka ba. Dama mahaukaci ba zai taɓa warkewa ba sai dai ya ji sauƙi."
_Ma'eesha_
Tun da ta shiga ɗaki ta kwanta sakamakon canjin yanayin da ta ji ne ya sa Makaho shhga damuwa. Ya san ba haka take ba, duk da baya ganin ta amma ya san akwai abun da ke damunta, ko don yanayin maganar ta ma.
Hankalinsa ne ya ji ya tashi domin baya son damuwarta, kullum yana son ganin ta cikin walwala, kamar yadda itaa take kokarin ganin ta faranta ma sa rai. Kullun zuciyarta cikin bakin ciki da damuwa take amma ta kan ari murmushi ta yafa a saman fuskarta don ganin ta ɓiye bakin cikin da take ciki. Domin akwai ciwo a zuciyarta. Musamman kan mahaifinta. Wani tausayin ta da ƙaunarta ya ji ya ƙara ginuwa a zuciyarsa.
Ba kyawun fuska kawai namiji yake nema a soyayya ba. Akwai wasu abubuwa masu girma da suke gina zuciyarsa da kwanciyar hankalinsa. Idan mace ta fahimci waɗannan, zata iya rike soyayya cikin hikima.
Girmamawa
Girmamawa shi ne ginshikin zuciyar namiji. Namiji yana jin darajarsa ne ta yadda mace take mu’amala da shi, a gaban mutane da a ɓoye. Idan mace tana girmama shi, tana sauraron ra’ayinsa, tana kuma kula da mutuncinsa, hakan yana kara masa kwarin gwiwa da jin cewa yana da matsayi a rayuwarta.
Rashin girmamawa kuwa na iya kashe soyayya ko da akwai kauna.
Biyayya (cikin hikima da mutunta juna)
Biyayya ba bautar mutum ba ce, a’a fahimta ce da haɗin kai.
Namiji yana son mace da zata iya bin shawararsa, ta nuna yarda da jagorancinsa a wasu al’amura, musamman idan yana kokarin alheri a gare ta,
Idan mace tana ta gardama a kowane lokaci, hakan na iya kawo zuciyarsa tayi nesa da ita, amma idan tana nuna biyayya cikin hankali da mutunci, hakan yana gina zaman lafiya. Fahimta da goyon baya
rayuwar namiji tana cike da nauyi da ƙalubale. Yana bukatar mace da za ta fahimce shi, ta tsaya masa a lokacin wahala, ba wacce zata kara masa matsin lamba ba.Lokacin da ya gaji ko ya shiga damuwa, yana bukatar wanda zai kwantar masa da hankali, ya ji cewa ba shi kadai bane.
Goyon baya daga mace yana kara masa ƙarfi da kwarin gwiwa a rayuwa. Idan namiji ya samu girmamawa, biyayya cikin hikima, da kuma fahimta daga wacce yake so, zuciyarsa zata zauna lafiya, soyayyarsa kuma zata kara zurfi.
Soyayya tana dorewa ne idan bangarorin biyu suna bawa juna abin da zuciya ke bukata.
Sandarsa ya laluba ya tashi a hankali ya fara tafiya har ya ji ya taɓo kofar ɗakin. Da sallama a bakinsa ya yaye labulen ɗakin ya shiga.
Tana kwance akan katifarta ta dafe mararta tana karanta duk addu'ar da ta zo bakinta. Sosai idanunta ke tsiyayar da hawaye tana ambaton sunan Allah. Dama kowace mace akwai yanayin da period nata yake zuwa duk wata. Ita Ma'eesha takan yi fama da ciwon ƙasan cikinta kuma ciwon na ma ta tsanani.
Lokacin al’ada, mace na iya jin abubuwa daban-daban a jikinta da kuma zuciyarta saboda canjin hormones.
Da farko, yawanci ana jin ciwon ƙasan ciki (cramps), wanda wani lokaci yana iya zuwa har baya ko ƙafafu. Wasu matan ciwon nasu yana da sauƙi, wasu kuma yana iya zama mai tsanani.
Haka kuma ana yawan jin gajiya da kasala. Jiki yana iya yin nauyi, kuma mutum ya fi son hutawa ko kwanciya.
A bangaren yanayi kuwa, ana samun sauyin hali (mood swings). Wani lokaci mace na iya jin haushi, ko damuwa, ko kuma ta ji kuka ba tare da wani dalili mai ƙarfi ba.
Wasu kuma suna fama da ciwon kai ko ciwon jiki gaba ɗaya. Haka kuma ciki na iya kumbura (bloating), wanda ke sa a ji kamar ciki ya cika ko ya yi nauyi.
Akwai kuma sha’awar wasu abinci (cravings), musamman kayan zaki ko abinci na musamman, kuma wani lokaci yunwa na ƙaruwa.
Amma ya kamata a sani cewa ba duk mata suke jin abu iri ɗaya ba yana bambanta daga mutum zuwa mutum.
"Ma'eesha lafiya kike kuwa?"
Cije lips ɗin ta ta yi ta goge sun hawaye tana kokarin daidaita nutsuwarta da muryarta.
"Na'am ka shigo?"
Ta amsa cikin sanyin murya.
Lalubar katifar ya yi ya karasa kai ya lalubo hannunta.
"Me ke damun ki?"
" Ba komai barci zan yi."
"Amma kin san barci a irin wannan lokacin na yammaci ba kyau ko?"
Kuka ne ya ƙwace ma ta sai ta faɗa jikinsa tana sakin wani sabon kuka. Kwantar da kanta ta yi a faffaɗar ƙirjinsa tana ci gaba da kuka.
Shi kuma hankalinsa ya tashi zuciyarsa ta yi ma sa nauyi. Take idanunsa suka sauya zuwa ja.
_Nadra_
Tun bayan da ta gama waya da Sidra ta take riskar kuka. Kuka take yi sosai ta rasa me ke yi ma ta daɗi.
Daidai lokacin Aunty Rahama ta yi sallama ta shigo cikin ɗakin.
"Subhanallah, me ya samu ƙanwata ce take kuka haka?"
Sai a lokacin Nadra ta lura da ita ta yi saurin goge hawayenta.
Ƙarasawa ta yi ta zauna gefenta, sannan ta dafa kafaɗarta ta ce.
"Nadra."
Sunkuyar da kai ƙasa ta yi tare da cewa
"Ina wuni Aunty."
"Lafiya lau ya kike ya jikin?"
"Alhamdulillah."
Ta amsa cikin sanyin murya.
"Me ke damun ki ne kike ta kuka?"
"Ba komai."
"A'a akwai komai kam."
Shiru Nadra ta yi ba tare da ya sake yin magana ba.
Aunty Rahama ta kalle ta cike da ƙaunarta ta riko hannunta cikin nata cikin hikima ta ce .
"Ina son ki dauke ni kamar ƙawar ki."
Kallon ta Nadra ta yi cike da mamaki ta ce.
"Ke fa babba ce."
Dariya ta yi kafin ta ba ta amsa da cewa
"Ai ba sai sa'arki za ki yi ƙawance da ita ba, ko wacce ta haife ki za ki iya ƙawance da ita ballantana wacce ta girme ki. Kasancewar ina matsayin yar mijinki ba yana nufin ki dinga jin kunya ta kina ɗauka ta sirikar ki ba. Ki ɗauke ni kamar ƴar uwarki ta jini. Na san cewa kina cikin damuwa idanunki ma ya nuna hakan. Idan bakin ki ya ɓoye damuwar da kike ciki to idanunki da da fuskarki ba za su yi karya ba. Na san dole akwai damuwa ki faɗa ma ni zan ba ki shawara. Kuma na yi ma ki alƙawari ba wanda zai ji abun da muka tattauna. Ko mahaifiyar da ta haife ni ba za ta ji komai ba, zan rike ma ki sirrinki domin ina ƙaunarki fisabilillah.
Shiru Nadra ta yi domin kuwa tana buƙatar wanda za ta fada wa damuwar ta ko ta yi shawara da ita. A duniya dama mutane biyu ne abokan shawarar ta . Ummanta ce sai kakarta Ammi. To ga Umma kwance ba lafiya, ta ya za ta iya faɗa ma ta abun da zai tayar ma ta da hankali, sai kuma kakarta Ammi ,to ita kuma idan ta sanar da ita ta san za ta sanar wa Abba ne sai sun saka Sidra ta bar gidan nan. Amma ta ji hankalinta ya kwanta da Aunty Rahama. Shin ta faɗa ma ta damuwarta ko ta yi shiru?
_Sidra_
Gudu take yi a saman titi kamar wacce za ta tashi sama. Tana driving tana jin ƙuna a ranta. A cikin ƙanƙanin lokaci ta isa gidan Sady baby.
A waje ta yi parking motar ta sannan ta tura ƙaramar kofar ta shiga.
Madaidaicin gida ne sai motoci guda biyu a harabar gidan.
Knocking ɗin kofar falon ta shiga yi. Ta kai mintuna biyu har ranta ya ɓaci sai ga Sady baby ta buɗe ƙofar wani saurayi ya fito, kallo daya Sidra ta yi ma sa ta ɗauke kai. Murmushi Sady baby ta yi ma ta tana cewa.
"Babban yarinya kin iso ?"
Ba ta tanka ma ta ba ta shiga cikin falon. Taɓe baki Sady baby ta yi tabi bayan Sidra.
Suna zama kan kujera Sidra ta watsa ma ta harara tana cewa .
"Kin ga abun da kika janyo ma ni ko? Ga shi a dalilin bin ki na ina neman rasa Masoyi na wanda nake mafarkin mallakarsa a matsayin mijin aure na. To abinda ba zan yarda da shi ba kenan. Dole na same shi ta kowace hanya."
"Yanzu ya kike so a yi?"
"Na mallaki Fahad Majidaɗi."
Shiru Sady Baby ta yi kafin ta ce.
"Ƙanwarki da yake aure fa?"
"Ya rabu da ita ya aure ni?"
"Kina ganin iyayen ki da iyayen sa za su yarda da hakan kuwa?"
"Ban damu da amincewar su ko akasin haka ba, abu ɗaya nake buƙata shi ne amincewar Fahad. Ko da ya amince idan iyayen sa suka hana shi fa zai hanu. Saboda yana da biyayya. Ko ƙanwarki ai ba don yana son ta ya aure ta ba, ya yi biyayya ne kawai. Hanya daya za mu bi shi ne Fahad ya amince da auren ki ya saki ƙanwarki, sannan iyayen ki da iyayen sa ba za su iya hana wa ba za su yi shiru kamar ba sa ganin komai. Amma hakan zai faru ne ta sanadiyar aikin da wani Mallami zai yi ma na."
Wani kallo Sidra ta yi Sady baby kafin ta ce
"Ni na je wajen wani neman taimako?"
Girgiza kai ta yi kafin ta ce.
"Is not possible."
"To idan ba haka ba ban hango himmatuwar cikar burinki ba. "
Wani dariya ta yi kafin ta ce .
"Ba wani Boka ko Mallam da zan je wajen sa, domin duk maƙaryata ne, a baya sun yi ma ni aiki ba abinda na gani, kuma na saka wa raina ba zan sake bin kowane Boka ba."
"Rally?"
Kau da kai Sidra ta yi kafin ta ce .
"Kawo wata hanya amma ban da wannan."
"Okya ina da wata hanyar da za ki iya cika burinki na raba Fahad da Nadra amma ba lallai iyayen sa su yarda ya aure ki ba, kuma su iyayen naki ba za su ba ki auren sa ba."
"Na yarda in dai zai rabu da ita, saboda idan ina kallon ƙanwata a matsayin matarsa zuciyarta za ta yi bindiga ne."
"Okay raba su ba abu ne mai wahala ba, saboda ba wai suna son juna ba ne , dukkansu sun yi biyayya ne."
"To ya za'ayi ?"
"Na san yanzu baya kasar idan ya dawo sai ki zo mu fara shirya planning yadda shirin zai tafi cikin tsari."
_Umma_
Zaune take a falonta tayi tagumi lokaci zuwa lokaci take goge hawayen da ya cika ma ta idanu.
Kallon Abba wanda ya murtuke fuska take yi.
"Abban Sidra."
Ko kallon ta bai yi ba ballantana ya amsa. Sai da ta sake fada a karo na biyu sannan ya fara magana a kausashe
"Sau nawa na faɗa ma ki ba ni da ƴa mai wanann sunan, ita ba ƴa ta ba ce a yanzu, daga ranar da ta zubar ma ni da ƙima na cire ta daga cikin zuri'ata. Na sha faɗa ma ki kada ki sake yi ma maganar yariyar nan kin kasa dainawa ko?"
"Ba'a canza wa tuwo suna duk in da za'a je a dawo kai ne uban Sidra ba wanda ya isa ya sauya hakan. Ai hannunka baya ruɓewa ka yanke ka yar da shi."
"Idan hannuna zai ruɓe tuni zan yanke shi na yar tun kafin ya fara cin sassan jikina."
Cikin damuwa Umma ta ce.
"Yanzu yadda ka kore ta ba ka tunanin halin da za ta je ta saka kanta a ciki? Kora ba shi ne mafita ga yaran da suka aikata kuskure a rayuwarsu ba, saboda za su iya shiga wani halin da ya fi wanda suka shiga aka kore su, don Allah ka bari a kira ta ta dawo."
"Kin san wani abu?"
Abba ya tambaya yana kallonta
"Sai ka faɗa."
"Daga yau kada ki sake tayar ma ni da wanan zanen."
Yana gama fadar haka ya fice ya bar ta.
Umma na kuka ta nufi part ɗin Ammi tana sa ran samun sassauci idan ta yi wa Abba magana a matsayin ta na mahaifiyarsa.

Page4️⃣7️⃣

Ammi da ke zaune tana waya da Gwaggo Laraba ta ji kukan Umma ta kashe wayar.
Cikin tashin hankali ta ke cewa Umma.
"Ke lafiya?"
Cikin Muryar kuka Umma ta ce.
"Don Allah ki saka baki Mahaifin Sidra ya yafe ma ta ko za ta dawo gida."
Tsuki Ammi ta ja tana cewa.
"Ba zan taɓa saka baki Abdullahi ya dawo da wannan gantalalliyar yarinyar ba."
"Haba Ammi ke fa mahaifiyarsa ce ke, kuma ke kadai na san cewa za ki iya yi ma sa Magana ya saurare ki. Da zaran kin saka baki shi ke nan."
"To ba zan saka baki akan wannan yarinyar ba, idan ya ga dama ya yafe ma ta wannan ra'ayinsa ne ta dawo ban damu ba, idan bai yafe ma ta na kuma ta yi ta zama a duk in da take. Akan me za ki damu da yarinyar da ba ta gujin ɓacin ranki. Yarinyar da ba ki isa ki saka ta ko ki hana ta ba, yarinyar da ba za ta faranta ma ki ba sai dai ta baƙanta ranki.Ni ba ruwana da sabgar ta tun can dama, ballantana yanzu. Ki shawo kan mijinki idan ya yafe ma ta shi ke nan."
Cikin sanyin jiki Umma ta bar ɗakin Ammi ta rasa tudun dafawa.
_Maeesha_
Murƙususu take ta yi a jikin Makaho cikin azabtar ciwon da take ji. Makaho kuwa jin yadda take yi ya san tana cikin mawuyacin hali ne.
Alluran da da ya kamata a ce ta yi shi tun last month ne ba ta yi ba, wanda hakan y saka ta cikin wannan halin. Kasancewar dama alluran *Depo-provera* ne da yake yi kowanne wata uku amfanin alluran dama ana yin sa wajen rage ciwon mara lokacin haila muka yana daidaita haila idan tana da matsala, ciwon haila na raguwa sosai. Kuma alluran tana da tsada sosai fiye da painkillers.
Ta san cewa ba za ta iya jure ciwon marar da take yi ba, don rashin kwanciyar hankali da nutsuwa ya sa ta mance da cewa duk wata uku alluran ke aiki, ga shi tun last month ya dace ta je likita ya yi ma ta amma ta kasa. Ta san cewa ba ta da kudin da za ta yi alluran kuma ba za ta iya jurewa ba.
Cije lips ɗin ta take yi wanda sai da ta ji gishiri-gishiri alamar ta fasa lips ɗin ta da hakori ne.
Wayarta ta laluba a nan kan katifar bayan ta zame jikinta daga na Makaho.
Lambar wayar ƙawarta Nasreen ce ta nemo ta danna ma ta kira. Bugu biyu ta ɗaga tare da cewa.
"Hello ƙawata ya aka yi ne?"
Yadda ta ji saukar numfashin Ma'eesha ya sa ta ce .
"Are you okay."
Ba ta ba ta amsa ba sai sheshsheƙar kukan da take yi.
Hakan ya saka Nasreen ta katse kiran wayar, dama tana driving ne za ta koma gida. Don haka ta juya akalar motar zuwa hanyar unguwar da Ma'eesha suke .
A cikin mintuna goma ta iso kofar gidan, daidai lokacin da makaho ke rarrashin ta yana cewa maganin me zai siyo ma ta.
Sallamar Nasreen ne suka ji wanda Makaho ne ya iya amsa wa.
Cikin ɗakin ta shigo ganin halin da ƙawarta take ciki ya sa ta ji tausayin ta. Don a baya lokacin da ta ce wa Ma'eesha ta rabu da makaho ba sa'ar aurenta ba ne sun dan samu rashin fahimta, musamman da Nasreen ta ba Abdul adireshin gidan Ma'eesha ya zo ran Ma'eesha ya sake ɓaci da Nasreen. Sai yau da ta kira ta a waya.
Ganin kayan jikinta ya fara ɓaci ya sa ta gane halin da ƙawarta ke ciki.
"Oh my God."
"Nasreen ta faɗa tana dafe goshi."
"Mu je ki gyara jiki mu tafi asibiti."
Ta taimaka ma ta ta tashi suka fita har banɗaki ta kai ta, sanan ta fito ta duba bokiti ta dauka sai a lokacin ta lura da ruwan zafi dake kan murhun gawayi. Don haka ta ɗebi ruwan zafin ta sirka ya ɗan yi ɗumi sannan ta kai ma ta a banɗaki. Bayan ta ajiye ma ta ta fito yana ƙarewa gidan kallo tana mamakin yadda Ma'eesha ke rayuwa a cikin wannan akulkin gidan. Wanda ko maigadin gidan uban Ma'eesha ya fi karfin wannan gidan. Taɓe baki ta yi tana cewa.
"Idan ta gaji ko ta ga uwar bari da kanta za ta saka ya sake ta, na san dole za ta zo ta same ni da wanan zancen. Muje zuwa. Yanzu da ta dawo gidan mu kamar yadda na ba ta shawara da yanzu tana cikin rufun asiri, da gangan na ki taimaka ma ta da kudi na bar ta sai wahala ta koro ta.
Tsuki ta ja a ƙasan ranta, zuciyarta cike da takaici.
Motsin Ma'eesha dake fitowa tana dafe bango ne ya sa ta fito.
Taimaka ma ta t yi suka shiga ɗaki. Akwatin kayanta ta buɗe ta duba pad wato audugar mata, da pant ta ba ta ta saka da ƙyar.
Doguwar rigar material ta ba ya ta saka sai hijabin da ta saka.
"Wani asibiti za ki kai ta?"
"Ko ma wane asibiti ne ni na san wanda zan kai ta kuma ni zan kashe kuɗin ko nawa ne duk da ba a wuya na hakkokin ta suka rataya ba, idan ban da kankanba ina kai ina Ma'eesha alhalin ba za ka iya daukar ɗawaini..."
"Ya isa haka Nasreen, ban kira ki dan ki ci zarafin mijina ba, yana da hakkin sanin in da za mu je, ke ƙafata ƙafarsa ko..."
"Really? Kina cikin ciwon ma bakinki ba zai iya jure aci Mutuncinsa ba, tun da na zo kin kasa magana, amma akan mijinki kin yi karfin halin magana duk da maganar daƙyar take fita ma ki."
Cikin jigatuwa Ma'eesha ta ce .
"In dai akan kare mutuncin mijina ne zan yi."
Cikin sanyin murya ya ce .
"A'a Ma'eesha ki ji da kanki, ku tafi Allah ya dawo da ku lafiya ya yaye ma ki lalurar da ke damunki."
"Idan tare da kai ba na fasa zuwa."
Sanin halin Ma'eesha ya sa Nasreen ta ce.
"Ku fita mu je."
Sandarsa ya laluba suka fita a tare. Duk da bai so bin su ba, amma bai so zuwa ba don dai Ma'eesha ta ce dole sai da shi za su tafi.
Bayan motar ta bude ma su da taimakon ta Ma'eesha ta shiga ciki har lokacin tana dafe da kasan mararta tana hawaye. Makaho ya zauna gefenta yana ma ta sannu .
Nasreen ta yi wa motar key suka bar unguwar.
Wani tsadadden asibiti suka nufa. Asibitin da Ma'eesha ke zuwa ganin likita. Daidai lokacin kuma Doctor Irfan likitan da yake duba Ma'eesha ya fito daga office ɗin sa.
Ganin Ma'eesha ya sa ya tsaya yana kallonta da mamaki ya ce.
"Hajiya Ma'eesha lafiya?"
Kallo ɗaya ya yi ma ta ya gane matsalar, don haka ya ce .
"Me ya hana ki zuwa akan akan lokaci?"
Wai Nurse mata biyu ya kara ya da suka shigar ma sa da Ma'eesha ciki
Kallon Makaho ya yi kafin ya ce .
"Yaushe aka fara bari mabarata suna shigo ma na asibi..."
Kasa karasa maganar ya yi sakamakon jin Muryar makaho.
"Ni ba mabaraci ba ne, ban taɓa nema a wajen kowa ba, don ina makaho ba shi zai ba ku damar wulakanta ni ba, ba don lalura ba ine zai kawo ni asibitin nan?"
"Doctor tare muke da shi kada ka damu."
Bai sake magana ba ya bar wajan don zuwa duba Ma'eesha.
Wani ma'ikacin asibitin ne ya zo wuce wa, ganin Makaho ya sa ya taimaka ma sa ya zauna, kasancewar akwai kujerun zama a wajen.
_Nadra_
Haka nan take jin za ta iya yarda da Aunty Rahma. Don ta rasa da waye za ta yi maganar ta ji sanyi. Kallon Sunyi Rahama dake sakar ma ya murmushi ta yi kafin ta ce.
"Aunty wai da gaske na ci amanar Aunty Sidra?"
"A'a ba ki ci amanar ta ba, waye ya ce kin ci amanar ta?"
"Na ga yata ce uwa daya uba ɗaya, kuma ita ce take soyayya da Yaya Fahad suke son juna, wata ƙaddara ta saka ta bar garin a ranar aurenta da Yaya Fahad. Ita a tunanin ta idan ta idan ta tafi za'a dakatar da ɗaurin aure sai bayan ta dawo sanann za'a ɗaura. Amma iyayenmu suka kasa hakuri suka ce ba za su fasa daurin auren ba sai sai za su ɗaura da ni a madadinta. Wallahi Aunty Rahama ban san cewa aure na aka daura da Yaya Fahad ba, na ɗauka cewa da ita aka ɗaura ma su, sai dare ake sanar da ni wai ta gudu an maye ma sa gurbinta da ni. Ba ni da yadda zan yi ba dan yi jayayya da hukuncin iyayena ba, dole na yi masu biyayya. Na zauna da shi da niyyar idan ta dawo ya sake ni ya zauna da ita, saboda tare suka tsara rayuwarsu. Amma bayan ta dawo sai na lura da ita take son sa amma shi kamar ya fitar da ita daga rayuwarsa. To tun da har yanzu tana son sa ai bai dace a ce na cigaba da zama da shi ba ko?"
Dariya sosai Aunty Rahama ta yi kafin ta ce.
"Ke ba ki son sa ne?"
Tura baki gaba ta yi tana cewa.
"Ni ina da wanda nake so?"
"Auzubillahi. Kina da aure kina maganar akwai wanda kike so? To ki daina ba kyau."
"Shi ma Yaya Fahad ɗin fa baya so na, da kansa ya ce zai sake ni wai na je na auri shashashan wanda yake so na, Ya sayyadi yake kira da shashasha."
Yadda ta yi maganar ne ya sake ba Aunty Rahama dariya sosai.
"To na ji, amma ya fada ne ba zai sake ki ba."
"Wallahi da kansa ya ce zai sake ni kuma ba da wasa yake yi ba, baya so na sai ya dinga ce ma ni wai ban waye ba bagidajiya ce ni, sanann Aunty Sidra tana ca ma ni wai Yaya Fahad baya son bak'ar mace sai fara kamar ta.
"Ƙarya ne wannan , shi a familynsa ba bakake ne , ko mahaifinsa baki ne da sai ya tsane shi ko ya?"
Shiru Nadra ta yi kafin ta ce.
"Ki taimake ni ya sake ni sai ya auri Aunty Sidra."
"Ba zai yiwu ba, Fahad na da ɗabi'a daya, idan ya so abu bai same shi a lokacin ba to abun ya kan fita ransa duk son da yake yi ma sa kuwa. Ko aka ja masa rai kafin a ba shi abu to yakan yi zuciya da shi ne. Don haka idan ba wani karfin ikon Allah ba to ya hakura da Sidra kenan. Kuma na tabbatar zai so ki kuma ke ma za ki so shi. Ba don yana ƙanina ba ne amma na tabbata ba macen da Fahad zai ce yana so ta ce ba ta son sa karya ne, don ya hadu ta kowane fanni, ke ba ki jin son sa?"
"Tab ni kan ba na son sa kuma ba zan taba son mutum mugu mara imani irinsa ba."
"Fahad ba mugu ba ne, abun da ya ma ki kowace mace cikakkiyar budurwa takan tsinci kanta a yadda kika tsinci kanki, sai dai ya danganta da yadda kowane namiji yake zuwar wa matarsa. Na san bai kyauta ba tun da ya tafi ya bar ki a cikin wanan halin, amma ki yi ma sa uzuri ba haka kawai y tafi ba, tafiyar dole ce ta kama shi."
Nisawa ta yi kafin ta ce .
"Ya jikin naki?"
"Da sauki."
"Ma sha Allah, an ce na kai ki za ki zabi motar da kike so, Baba ne ya ba su ki gift."
"Aunty ba sai na je ba na ba ki zabi kowacce ne kika samu indai ta yi ma ki to ta yi ma ni."
"Kin ba ni zaɓi?"
"Eh."
"To shikenan sai kin ga sako, sannan zan kawo ma ki wasu sabulai na wanka da maiyukan shafawa da wasu magungunan gyaran jiki da za ki dinga amfani da su."
"Gyaran jiki kuma su ne har da na sha?"
",Eh haka suke, anjima zan dawo in sha Allah. Ko akwai abun da kike so ne?"
"Ba komai na gode."
Sallama ta yi ma ta sannan ta fice daga ɗakin.
A ranar da yamma sai ga Aunty Rahama ta kawo galleliyar motar da ta zaɓawa Nadra,sai ɗaukar idanu take yi. Sannan ta shako manyan ledoji guda biyu na kayan gyaran jiki na ciki da waje.
Daidai lokacin Sidra ta yi horn maigadi ya wangale ma ta gate, ta shigo da motar Mama da ta fita da ita, idsnunta ta sauke akan galleliyar motar dake sheƙi da daukar idanu.
*Maman Ihsan ce*✍️
09065327995
Follow the MAKAHO NE channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb7CzOoIXnljBnIJjp2z

Page4️⃣8️⃣
Daidai lokacin Sidra ta yi horn maigadi ya wangale ma ta gate, ta shigo da motar Mama da ta fita da ita , idanunta ta sauke akan galleliyar motar da ke sheƙi da ɗaukar idanu.
Cike da mamaki ta furta .
"Mercedes Benz G Class ?"
Ba ta gama cika da mamaki ba sai da ta ji muryar Aunty Rahama na cewa.
"Sidra ga motar ƙanwarki ta iso."
Cike da basarwa da kokarin danne bakin cikinta take murmushin yaƙe.
"Ta yi kyau sosai na taya ta murna."
Tana faɗar haka ta karasa wajan motar. Mota ne da mata ke so, tana da karfi sosai da nuna Class (matsayi)
Ƙare wa motar kallo ta yi duk da ba z ta iya cewa ga kudin motar ba, amma ta san cewa an kashe miliyoyin kuɗi.
Aunty Rahama ta fito da ledojin kayan gyara da ta siyo wa Nadra.
Sidra ta bi ta da kallo har ta shiga ciki sannan ta mara ma ta baya, sai dai idanunta na kan Sunyi Rahama sakamakon ganin ta zagaya ta ƙofar da zai shigar da ita part ɗin Fahad ba tare da ta ji cikin main falon gidan ba.
Cije lips ɗin ta na kasa ta yi kafin ta tura kofar falon ta shiga ciki.
Da fara'a Aunty Rahama ta shiga cikin part ɗin Fahad. Kayan da ta siyo ne ya ya ma ta bayanin yadda ake amfani da su .
Key din motar ta karkaɗa wa Nadra.
"Motarki ta iso
Farin ciki Nadra ta nuna kafin ta yi wa Aunty Rahama godiya.
Sai da ta tabbatar ta saka Nadra ta fara shan magungunan nan na gyaran jiki sannan ta bar ta.
Downstairs ta nufa da niyyar sanar wa su Mama motar Nadra ta iso.
Mama da inna ne kawai a main falon suna fira. Sallamar Sunyi Rahama ne ya ba su mamaki don ba su san ta dawo gidan ba. Bugu da kari kuma ga shi ta fito daga part ɗin Fahad.
"Ke dama har yanzu kina cikin gidan nan?"
Cewarsu Inna bayan ta ɓalli goro ta tauna.
"A'a yanzu na dawo, na kawo wa Nadra motarta ne?"
"Ma sha Allah."
Inna da Mama suka hada baki wajan fadar haka.
Tashi suka yi Inna na mita ciwon ƙafa da take yi ya sa ta gaba.
Suna isa harabar gidan sai ga Rumaisa da Farida sun shigo gidan.
Su biyu ne a bayan motar yayin da direba ke driving nasu.
Suna fitowa suka ga su Mama wajen motar Nadra suna addu'ar Allah ya kare ya sa ya more.
Farida kam ko wajan ba ta karasa ba ta yi shigewar ta ciki yayin da Rumaisa ta karasa wajen motar cikin farin ciki.
"Wow wanann motar na mata ma su aji ne. Na taya ta murna wallahi dama ni ma a siya ma ni irinta."
_Ma'eesha_
Tana zaune bayan an kammala ma ta allura ne Nasreen ta shigo.
Kallonta ta yi da alama ta samu saukin ciwon marar da ke damunta.
"Ƙawata ya jikin naki?"
"Da sauƙi"
Murmushi ta yi tana cewa.
"Na ga alama ai."
Doctor ne ya kalle ta ya ce.
"Za ku iya tafiya yanzu. Amma ki dinga kula sosai, sai nan da wata uku sai ki sake dawowa."
"To Doctor na gode sosai."
Nasreen ne ta kalli Doctor ta ce.
"Shi ke nan ko?"
"Eh ai ba wani abun da ya rage kin riga kin biya kuɗin."
Godiya suka yi ma sa, suka fice.
A in da Makaho ya zauna a suka same shi, Ma'eesha ce ta karasa in da yake zaune ta yi ma sa sallama. Ya amsa yana miƙewa tsaye rike da snadarsa.
"Ma'eesha ya jikin naki."
Murmushi mai sauti ta yi tare da cewa.
"Alhamdulillah na ji sauƙi sosai sai abun da ba za'a rasa ba."
Farin ciki ne ya ziyarce shi ya furta kalmar Alhamdulillah.
A tare suka fito Nasreen na gaba su suna baya sun jera a tare suna tafiya.
Bayan sun shiga motar ne Nasreen ta yi wa motar key suka bar asibitin.
Har ƙofar gida ta sauke su, suka fita ta yi ma su sallama, Khalifa ya nufi cikin gidan, Ma'eesha ta tsaya tana yi wa Nasreen godiya sannan ta shiga gidan, Sa da ta shiga Nasreen ta ja motarta ta bar kofar gidan.
*BAYAN SATI ƊAYA*
Baba ya dawo daga tafiyar da ya yi da kwana biyu kenan ya ce wa Sidra ta shirya don ya kai ta ta ba wa Abba hakuri.
Ita kam ba ta so hakan ba don tana zaune gidan ne saboda Fahad. Tana so da zaran ya dawo za ta ɗana tarkon da take ganin shi ne tsakanin da zai kai ta ga masoyinta Fahad Majidaɗi. Ba yadda ta iya haka ta shirya cikin shiga ta kamala da mutuntaka.
Don ranar hijabi ta sanya a saman doguwar rigar amtamfar da ke jikinta.
Sallama ta yi wa mutanen gidan in da Nadra ta rako ta har wajen motar Baba.
Sai da suka bar gidan ta koma ciki tana addu'ar Allah ya sassauta zuciyar Abba ya yafe ma ta.
Sai dai addu'ar ta ba ta karɓu ba, domin Abba shafa ma idanunsa toka ya yi ya ce sam ba zai karbi Sidra ba ya riga da ya yafe ta a matsayin ƴarsa.
Duk yadda Baba ya kaɗa ya ya raya Abba ya ƙi. Domin shi kaifi ɗaya ne, idan ya faɗi magana ya fada kenan ba zai taɓa sauya wa ba.
Sidra har ga Allah ta ji dadin hakan a zuciyarta sai dai ba ta bari hakan ya faru ba, don dai kukan karya take yi.
Don Abba bai faɗa wa su Umma zancen zuwan na Baba ba, saboda ya san Umma za ta tayar da hankalinta. Don haka a ɓangaren baƙi ma ya sauke Alhaji Umar Majidaɗi.
Duk wani motsi na Sidra Abba na lura, domin ya san wace ce Sidra shi ne mahaifinta. Ya fahimci duk wannan kukan wasan kwaikwayo ne, ba ta yi nadama ba murmushin da ya fi kuka ciwo ya yi lokacin da ya ga tana murmushi.
Ita kuma ba komai ya saka ta yin murmushi ba, sanin cewa za ta koma Familyn Majidaɗi, dole ne ta samu kusanci da Fahad da familynsa.
Haka Baba ya dawo da ita gidansa, ya yi wa iyalansa bayanin yadda suka yi da Abba. Ya ce Sidra za ta ci gaba da zama a gidan ba wani lokaci har zuwa Allah ya sazuciyar Abba ya yi sanyi.
Ya kuma nuna ma su yanzu an zama daya kasancewar ko ba abota yanzu akwai surukantaka aure ya haɗa an zama dangi. Ga Nadra nan tana matsayin sirikar gidan kuma Sidra yarta ce.
Haka rayuwa ta cigaba da gudana a cikin gidan, Sidra ta saki jiki da Nadra ta ja ta a jiki sosai, ta nuna ba komai yayin da ta gama duk wani shirin da za ta aiwatar dawowar Fahad kawai take jira don ta aiwatar da shirinta. Don yadda take jin haushin Nadra da kishinta yanzu ta daina ji.
Don ta lura kamar Nadra ba ta gaban Fahad bisa la'akari da ko kiran wayarta baya yi. Ko messages baya tura ma ta, hakan ya sa ta ji sanyi a ranta tana ganin ai ba ta gabansa.
Saboda kullun sai sun yi waya da ƴan gidan, wata rana ma video call suke yi, zai gaisa da Mama, Baba, Inna, Rumaisa, da Farida. Ko tana Wajen ba zai taɓa cewa a ba ta waya ba, kuma ba zai taɓa tambayar ta ba.
Hakan na damun Mama amma ba ta taɓa yi ma sa Magana ba ta zuba ma sa idanu, ta san ta in da za ta kama shi.
Ita kanta Nadra hakan na ma ta ciwo a zuciya, duba da yadda ya yi ma ya ya saka kafa ya bar ƙasar bayan ya san tana cikin mawuyacin hali, bai taɓa tambayar ta ya jikinta ba ballanta ya yi ma ta sannu. Amma tana addu'ar Allah ya dawo da shi lafiya za ta ba shi mamaki.
Haka take ta rayuwa a gidan ba tare da ta nuna tana da damuwa ba. Ga kayan gyaran jikin da Sunyi Rahama ta kawo ma ta Inna tana sa ma ta idanu don ganin tana amfani da su. Sabulai ma haka da su take amfani har da man shafawa.
Hakan ya sa ta yi kyau fatar jikinta sai ƙyalli take yi ta yi kyau kamar ba ita ba, baƙar fatarta dama mai kyau ne sai ta kara kyau.
Sai dai abin da ba ta sani ba duk abin da take yi akan idanunsa take yi, don yana kallonta daga can in da yake. Idan ya dawo yana zaune baya komai zai yi ta aikin kallonta, duk abinda take yi. Yana mamakin yadda ta yi kyau ta canza kamar ba ita ba. Haka zai shagala yana kallonta, musamman da yawan tunanin yarinyar ke addabar sa. Haka nan kawai begen ganinta yake yi da son jin muryarta, Mama jin kansa ya hana ya kira wayarta ko ya ce ba ta waya su yi magana. Amma tunanin tariyar ya hana ta sukuni.
*BAYAN WATA UKU*
Ana gobe Fahad zai dawo ƙasar ne ya kira waya ya sa Mama ta sa ma'aikata su je su gyara ma su gidansu.
Mama ta gama sauraren sa tana kare da waya a kunnen ta kafin ta ce .
"Yaushe kake so a gyara ma ka gidan?"
"Yau nake so, sanan Rumaisa ta bi su ta gyara ma na bedroom."
Shiru kawai Mama ta yi tana tunanin yadda za ta ɓullo ma sa akan halin ko in kula da ya nuna wa Nadra.
_Ma'eeaha_
Tana zaune gaban murhun gawayi ta haɗa tagumi, tunanin ta a abun da za su saka wa cikinsu take yi.
Tun jiya ba su da abincin da za su ci, kuma ba su da kuɗin siye.
Don hatta gawayin da za ta kunna babu ya ƙare.
Tashi ta yi ta shiga ɗaki ta dauko farar leda sosai wacce suka siye garin kwaki rabin mudu. Shi suka sha jiya daddare suka kwanta. Yau da safe suka sha koko wanda ko sugar babu.
Garin ta ɗiba a kofi ta ɗauki ɗaurin gyaɗar hamsin da ya rage, ta raba gyadan gida biyu ta ɗauki rabi sannan ta ƙulle sauran.
Bayan ta jiƙa garin ta zuba gyaɗa tana sha tana ɓata fuska kamar mai shan magani.
Sallamarsa ta ji yo daga ƙofar gida bayan ta kammala shan garin.
Ta amsa ma sa tana yi masa sannu da zuwa.
Ya shigo gidan hannunsa ɗaya rike da sandarsa dayan hannun kuma rike da basket kayan gyaran takalminsa.
"Sannu da zuwa."
"Yauwa ya gidan?"
"Alhamdulillah."
"Ma sha Allah."
Karɓar kayan gyaran takalminsa ta yi ta ajiye gefe. Sannan ta ɗebo ma sa ruwa ta ba shi ya sha.
"Ya kasuwan?"
Ta tambaye shi tana kallon kyakkyawar fuskarsa.
"Alhamdulillah zan ce, amma yau kam ma kamar jiya, ko mutum ɗaya bai kawo gyaran takalmi ba haka ba gaji da zama na dawo."
Murmushi ta yi tana cewa.
"Ba komai, kada ka damu duk abin da ba ka samu ba to ba rabonka ba ne, Allah ya kara ma na wadatar zuciya."
"Amin Ma'atussaliha Allah ya yi ma ki albarka."
"Amin mijina."
Sauran garin rogo da ta rage ne nake sha bari na jika ma ka naka."
Jinjina kai kawai ya yi ba tare da ya sake magana ba, amma kallo ɗaya za ka ma sa ka gane cikin damuwa yake.
Garin ta jika ma sa ta kawo ma sa bayan ta zuba ma sa sauran gyaɗa.
Bayan sun gama sha ta ce .
"Dama ina son na sanar da kai an kwantar da mahaifiyar Rumaisa asibiti, idan ka amince zan je na duba ta."
"To bari na yi wanka sai mu tafi tare."
Ya fadi haka yana miƙewa tsaye. Ta zuba ma sa ruwan wanka ta kai ma sa banɗaki..
Kofuna da suka yi amfani da shi ta wanke ta koma ta zauna.
Tana nan zaune kan tabarma har ya fito wanka ya shiga ɗakin, sai da ta tabbatar ya shirya ta shiga da sallama.
Kayan jikinta take kokarin ragewa lokacin da ya fice daga ɗakin.
Yana zaune a barandar kofar ɗakinsu rike da sandar jagoransa, ta fito ta yi wanka cikin sauri ta shirya cikin doguwar rigar Abaya mai ruwan toka, ta yi rolling kanta da mayafin.
Fitowa ta yi hannunta rike da wayarta.
"Na shirya yallaɓai."
"To ranki ya daɗe."
"Ka san ba mu da kuɗin abun hawa ko?"
"Ba damuwa zan iya tafiya a ƙafa ke nake tunani."
"Mu je ai ba mu da nisa da asibiti. Amma fa ka ajiye sandar nan zan rike hannunka har mu tafi."
"To ba Kya jin kunyar idanun mutane?"
"To ba mijina ba ne?"
"Eh haka ne, amma ai su iyayen ƙawarki fa?"
Ɗan jim ta yi kafin ta ce.
"To rike sanadarka mu tafi."
Ta yi maganar tana dariya.
A tare suke tafiya gwanin sha'awa, har suka kai asibitin kasancewar ba su da nisa da Asibitin da unguwar su.
Kasancewar Nasreen ta yi sanar da ita in da aka kwantar da mahaifiyarta ya sa ta nufi wajen kai tsaye.
Mahaifiyar idanunta biyu Nasreen na ba ta magani tana sha. Sai wasu mata guda biyu. Da ƙawayen Ma'eesha su uku. Sai kuma mahaifin Nasreen.
Bayan sun gaishe su tare da yi ma su ya jiki suka amsa cikin dakin fuska.
Kasancewar duk sun san Ma'eesha kuma sun ji labarin auren nata da makaho. Don haka suka zuba ma ta idanu suna yi ma ta kallon tausayi.
Khalifa ya ma su sallama ya fice yana jiran Ma'eesha har sai ta fito su tafi.
Ganin kallon da ake ma ta ya sa ba shiri ta yi masu sallama za ta tafi.
Mahaifin Nasreen ya ba ta 10k ta ki karba sai da ya nuna ɓacin ransa ta amsa tana godiya.
Ta yi farin ciki da kuɗin kasancewar ba su da kudi ba su da abinci. Ko da ta sanar wa makaho ya ce Allah ya saka da alkhairi.
Bayan fitowar su daga cikin wata ɓakar mota ta fara bin bayan su.
A hankali motar ke tafiya tana bin su, sai dai matukin motar ya yi parking motar ya fito yana bin bayansu, kasancewar hanyar da suka bi mota ba za ta iya bi ba, don hanyar tafi sauri ya sa ba su bi titi ba. Sai dai hanyar ba mutane sosai.
Idan sun ɗan yi tafiya kadan makaho sai ya tsaya. Kafin ya cigaba da tafiya. Ita dai Ma'eesha ba ta ce komai ba.
Daidai lokacin da wani mai keke nape ya biyo ta gabansa.
Makaho ya sa hannu ya tare shi, sai ya tsaya yana cewa.
"Ina za ku je?"
"Ma'eesha ki shiga ya kai ki gida."
Da mamaki ta kalle shi kafin ta ce.
"Kai kuma fa."
"Kada ki damu zan kula da kaina."
"Ba zan bar ka kai kaɗai ba."
Tsawo ya daka ma ta yana cewa.
"Na ce ki shiga!"
Yadda ya daka ma ta tsawa sai da ta firgita ba ta san lokacin da ta shige ba.
Tana shiga ya yi wa mai nape alama da hannu ya tafi, take ya ja keken suka bar wajan.
Suna tafiya ya cire baƙin glass ɗin dake idanunsa ya juya bayansa cike da karsashi yana jifan mutumin da ke bin su da wani mugun kallo wanda da sai da hantar cikinsa ta kaɗa.
Baya ya fara ja kafin ya juya zai gudu, tsalle ɗaya Makaho ya yi ya dira a gabansa. Shaƙo wuyansa ya yi cike da ƙaraji yake cewa .
"Kai har kana da zarrar da zan ka dinga bibiya ta?"
Idanunsa sun firfito waje saboda shaƙar da ya yi ma sa.
Daidai lokacin wayar mutumin dake gaban aljihun rigar suit ɗin sa ta fara ruri.
Sake shi ya yi sannan ya zaro wayar dake gaban aljihun suit ɗin mutum yana kallo.
MADAM shi ne sunan da ta bayyana akan screen din wayar.
Amsa kiran wayar ya yi sannan ya yi ma sa da alama ya yi magana.
Kafin ya yi maganar suka ji muryar me kiran na cewa.
"Ka ga fitowan su daga asibitin ko har yanzu suna ciki, sannan na ce ka yi mani bincike akan yarinyar da ka tura ma ni photon su kwanaki ta rike ma sa hannu suna tafiya, meye a tsakanin su, kuma shi da yarinyar ne yau ma suke tare ko wata ce daban?"
"Duk ita ce Madam."
Ya yi maganar yana kallon idsnun makaho.
"To ka tabbatar daga yau zuwa gobe ka samu duk wasu bayanai kafin ka bar garin nan."
Cike da ɓacin rai da takaici makaho ya cije leɓansa na kasa wanda sai da ya Fahe jini ya fito."

Page4️⃣9️⃣
Cike da takaici da ɓacin rai da takaici makaho ya cije leɓansa na ƙasa wanda sai da ya fashe jini ya fito.
Sannan ya saka hannu ya katse kiran wayar mutumin.
"Duk wani shirin ku ina sane da shi, kuma duk bibiya ta da kake yi na sani, daga kai har sauran mutanen da suke bibiya ta na san komai, ni ba shashsha ba ne. Wato har ka tura ma ta da photon mu ko?"
Shiru ta yi yana kallonsa da idanun sa da suka kaɗa suka yi ja.
"Wato kai ne me zarrar da kake bibiya ta ko? Har ja ɗauki photon mu ka tura da shi ko? Akan aikina ma sai an saka ma ni idanu ?"
Cike da tsoro mutumin yake kallonsa, ganin da ya yi ya ma sa kama da mayunwacin zaki.
"Idan har kana son rayuwarka da ladiyarka to ka fita daga cikin wannan sabga, domin kuwa shine zamanka lafiya, idan ba so kake yi na binne ka da ranka ba. Idan kuma kaƙi ji ka cigaba da bibiya ta ko yarinyar da ka ganni da ita , sannan ka nemi sanin alƙar da ke tsakanina da yarinyar ka sanar ma na ta to fa ka sani shi ne kuskure mafi muni da za ka tafka a rayuwarka."
"Ka gafarce ni yallaɓai ni ma umarni nake karɓa ba yin kaina ba ne."
Cikin ƙaraji makaho ya ce .
"Shi ya sa na ce ma ka ka daina."
"Ba zan iya ba yallaɓai domin ina dai akan Madam ne raina fansa ne a gare ta."
Wani gajeren murmushi makaho ya yi kafin ya ce .
"Shi ke nan za mu gani."
Ya yi maganar yana saka ƙafarsa ɗaya ya kwashe ƙafafuwan mutumin wanda hakan ya saka ya zube a saman guiwoyinsa da ƙarfi, wanda sai da ya saki wata ƙarar azaba, don ji yake ba yi kamar guiwoyinsa sun daina aiki."
Makoho yana huci ya bar wajen, yana mai mayar da baƙin glass din sa ya ɗauki sanadar jagoransa ya fara tafiya yadda makafi ke yi.
Tun mutumin na ganinsa har ya ɓacewa ganinsa, har lokacin ya kasa miƙewa ya tashi.
_Ma'eesha_
Sam hankalin ta ya kasa kwanciya, ganin yadda makaho ya shi ne ya daka ma ta tsawa cikin wata iriyar Muryar da ba ta san yana da ita ba. Da ba ita ya yi wa ba ko ba a gabanta aka yi ba da sai ta ce ba Khalifa mijinta ba ne ya yi ma ta wannan tsawar. Don za ta iya cewa ko mijinta ko yatsa aka saka ma sa a ba su ki ba zai an iya cikawa ba, amma yau ta ga a abun da ya ba ta mamaki sosai ba kadan ba.
"Hajiya ina za mu je ne?"
Ta yi zurfi cikin tunani sai da ya sake magana sannan hankalinta ya dawo jikinta, ta sanar da shi in da zai kai ta, don dama ba su da nisa da Asibitin da suka je.
Bayan ya sauke ta ƙofar gida ne cikin kudin da mahaifin Nasreen ya ba ta ciki ta ba shi dubu ɗaya, ya ba ta canji ɗari biyar kasancewar ita kadai ya ɗauka.
Ƙofar gida ga nufa ta bude kofar langalangan su ta bude .
Ta shiga gidan bakinta dauke da sallama.
Zama ta yi saman barandar ɗakin ta haɗa tagumi. Tana jiran shigowarsa.
Jin shiru ne ya sa ta kira wayarsa don ta ji lafiyarsa amma sai ya kasance wayar na gida. Don ta ji sautin wayar a cikin ɗaki.
Hankalinta ya kasa kwanciya tuna kwanakin baya an sami waɗanda suka yi garkuwa da shi, cikin ikon Allah ya kuɓuta.
Har ta ji an kira sallar Magrib sannan ta tashi ta yi alwala ta fara gabatar da sallah.
_Makaho_
Da Kafa ya ƙaraso unguwar yana tafiya yana saƙa abubuwa da yawa aransa.
Yana shigiwa unguwar ana kiran sallar Magrib, don haka ya tsaya ya gabatar da sallar Magrib a cikin jam'i a masallaci ya yi sallah.
Bayan an idar jama'a sun fara watsewa me Mallam Liman ya karasa gaban Makaho.
"Assalamu alaikum Mallam Khalifa."
"Wa'alaikium Salam Mallam Liman kai ne?"
Liman ya mika masa hannu akan su yi masabaha.
Bayan sun gaisa ne Mallam Liman ya bar Khalifa zaune, har lokacin ɗaxu yake ji. A ransa. Don haka ya fara karatun alƙur'ani mai girma.
Kuma ya ji sa'ida a cikin ransa, don kaso hamsin na baƙin cikin da yake fama da shi ya ragu.
Bayan an yi sallar Isha'i ne ya tashi ya nufi hanyar gida.
Da sallama ya shiga cikin gidan.
Ma'eesha dake zaune kan sallaya ta fito da sauri tana kare ma sa kallo. Kasancewar akwai wutar nepa.
Hannayen sa duka biyu ta rike tana cewa.
"Kana lafiya ko? Me ya faru ne ka ce na dawo kai na ga ka tsaya?
Bayan cewa a tare suke tafiya kafin y aikata wannan abu .
"Kada ki damu kawai na tausaya ma ki ne ya saka na yanke shawarar je ki Hau keke nape ni zan je da ƙafa.
"Amma me ya sa za ka wahalar da kanka bayan akwai kudi a hannuna?"
"Kada ki damu na dawo cikin ƙiahin lafiya. Don a masallacin unguwar nan ne na yi sallar Magrib sa Isha'i.
"Alhamdulillah."
Ta faɗa tana ja ma sa hannu suka shiga cikin ɗakin.
Bayan sun zauna a tabarma ne ta kalle shi tana yi ma sa sannu.
"Ka san ba mu da abinci a gida nan , lokacin da na dawo gidan ba na da nutsuwa da na girka ma na wani abun. Amma yanzu bari na siya indomiee na girka ma na zai fi sauki."
"Sannu da ƙoƙari Allah ya ma ki albarka."
Sai a lokacin ta lura bakin Khalifa ya fashe.
Cikin tashin hankali ta kai hannu ta kan fuskarsa tana cewa .
"Subhanallah me ya same ka ne?"
"Kada ki damu ina cikin ƙoshin lafiya.
Kamar za ta yi kuka ta ce.
Bakinka da ya kumbura."
"Eh ba damuwa ba zafi ai, hakori na ne ya ya datse leɓen."
"Haba mijina kamar ƙaramin yaro ne mai z ka datse baki haka?"
Bai ce komai ba, ita ce ta tashi tana cewa ina zuwa yanzu xan dawo."
"Ina za ki je a daren nan."
"Zan siyo indomie ne nan shagon waje."
Jinjina kai kawai ya yi ba tare da cewa komai ba..
_Nadra_
Tana zaune a part ɗin Fahad kamar yadda ya bar ta har tsawon wanan lokacin ita ke rayuwa a ɓangaren. Kasancewar ta har yanzu ta kada sake wa da mutanen gidan sosai. Tana yi ma su kallon surukai take yi ma su.
Sallamar Mama ce da Aunty Rahama suka shigo falon. Bayan ta amsa ma su sallama.
Ba ta yi mamakin ganin Aunty Rahama ba kasancewar ta ji ana firan daowarasa kuma sai shirye-shirye ake yi a cikin gidan.
Gaishe da Mama ta yi ta amsa sannan ta gaida Aunty Rahama.
Ita ma ta amsa tana ƙara jinjina kayan gyaran jikin da take kawo ma ta.
Mama ta kalli Aunty Rahama tana cewa.
"Ki tabbatar da ta tattara komai na ta an mayar da su ɗakina, sannan ita ma ta biyo ki kamar yadda na ce."
"To Mama, ki ɗan turo ma na daya daga cikin ma su aikin nan ko da Laraba ce ta zo ta taya mu kwashe kayan."
"Kin san baya son ma su aiki na shigar ma sa ɗaki ko?"
"Eh ta tsaya ƙofar falo."
"Okay."
Mama ta amsa tana fita. Aunty Rahama ta kalli Nadra ta ce.
"Yar gatan Mama, Mama ta ce ku tattara komai na ki za ki koma ɗakinta da zama. Ki yi Sauri za mu fita."
Cikin fadin ciki Nadra ta fara tattara duk abin da ta san nata ne."
Aunty Rahama ta fara fita da akwatunan kayan tana kai wa bakin kofar falo,sai Laraba ta dinga ɗauka.
Sai da suka gama fitar da komai sannan Laraba na kashewa tana sauka da su sannan suka fito.
Kai tsaye ɗakin Mama suka nufa suka tarar ta jera akwatunan a in da ya dace
Da sallama suka shigo Mama ta amsa sannan ta ce.
"Ya kamata yanzu ku tafi ko?"
"Eh Mama yanzu za mu tafi."
Ta juya tana kallon Nadra kafin ta ce .
"Ƙanwata shirya za mu je gyaran gashi kuma ayi ma ki lalle."
"To Aunty Rahama na shirya hijabi kawai zan saka."
"Okay saka mu tafi."
Dogon hijabinta ta saka, kasancewar yanzu ta daina saka dogon hijabin da ta saba sakawa a gida. Hakan ya faru ne saboda taimakon Aunty Rahama don sai da ta yi da gaske sannan Nadra ta daina yawo da hijabi a gida. Don gara ta dinga bayyana adonta ga mijinta ba kullum zama da hijabi kamar mai takaba ba.
Bayan ta shirya suka fita tare, a motar Aunty Rahama suka je.
Gidan sai ƙamshi girke-girke ake yi na tarbar Fahad.
Bayan kamar awanni biyu da fitar su ne suka dawo gidan. Bayan an tsara wa Nadra Lalle me kyau zaben dukawar baƙi da ja aka yi ma ta. Dai gyaran gashi kasancewar ba ta cika son kitso ba ita.
Sosai ta yi kyau ga gashin ya zubo sai sheƙi da wani kanshi take yi.
Wanka ta yi addu'a lokacin da ake kokarin zuwa ɗauko shi a airport.
Da taimakon Aunty Rahama ta shirya tsaf, cikin wani tsadadden leshi ɗinkin riga da siket ya ɗan kama ta, ya zauna ɗagwas a jikinta.
Ta so saka Abaya Amma Aunty Rahama ta hana ta ce ta bar shi wanan ya fi ɗaukar hankal, kuma ba kowane namiji a gidan.
Dole ta bar shi. A don ranta ya so ba .
Wani turare ta fesa ma ta a jiki wanda shi na musamman ne.
Horn suka ji daga bakin gate wanda hakan na nuna sun iso, Rumaisa da Farida suka je tarbon sa,.
A tare suka fito daga bayan motar sun saka shi a tsakiyar suna ta farin ciki.
Mama da Sidra ne a falon suna farin ciki da shigowarsa. Sidra ma ta ci kwalliya cikin dogon rigar atamfa ɗinkin fitted goun ɗinki ya matse ma ta jiki.
Yana shigiwa suka mike tsaye ya karasa ya Side hug ya yi wa Mama sannan ya karasa wajen Inna dake zuwa ita ma ya yi ma ta yana dariya.
Sidra ta gaishe shi ya amsa a yabo ba fallasa. Sannan ya nufi part ɗin sa da tunanin ko Nadra na can.
Su Rumaisa suka bi shi da kayan part ɗin sa suka ajiye a falo.
A tunanin sa Nadra na bedroom amma ya ga ba ita ba komai nata.
Bincike ya yi a CCTV camara ya ga komai.
To ina suka kai ta ko dai tana sabon gidansa ne da aka gyara jiya.
Da wannan tunanin ya yi wanka ya fito, shirya wa ya yi cikin ƙananan kaya sai zuba ƙwmshi yake yi .
_Ma'eesha_
Kafin ta je ta siye indomie sai da ta fara zuwa Chemist ta siye wa makaho Khalifa magani na rage zugin ciwo sannan ta tsaya ƙofar wani gida da ta ga an ɗaura gawayi a leda suna ajiye a kofar gidan.
Ta siye gawayin wajen yaran da ke kofar gidan sannan ta nufi shago ta siyo ma su indomie da ƙwai biyu ta nufi gida.
Ta same shi a tsaye a tsakar gidan rike da sandarsa, ya amsa sallamar da ta yi.
"Lafiya na gan ka tsaye haka?"
"Bayan ki zan bi na ji ko lafiya daga nan zuwa Wajan me kanti siyen indomie na ji shiru, shi ne na ce bari na bi bayan ki ko lafiya kika daɗe?"
"Na ke Chemist na siye ma ka magani ne, na tsaya na siye gawayi kafin na zo wajen mai Indomie."
"Allah sarki to na gode ƴar aljannah."
Murmushi ta yi ta ajiye kayan a kofar ɗaki, maganin kuma ta mika ma sa shi .
"Me zan taya ki da shi ne?"
"Ba komai ka zauna ka huta idan na gama sai kawai ka ci."
Kujera ta ajiye ma sa a tsakar gidan tana cewa.
"Bari na ajye maka kujera ka huta muna fira har na gama."
Ta taimaka ma sa ya zauna kan kujerar, ita kuma tana huta wuta har ya tashi ta wanke tukunya ta ɗira ta zuba ruwa, da kayan Hadi, ƙwani ɗin ma ta saka shi bayan ta wanke su don su ma dafaffe za su ci ƙwan.
Har ta gama suna fira sai dai ta lura tun da ya dawo baya da walwala da alamar damuwa a tare da shi. Sai dai ta danganta hakan da ciwon da ke bakinsa ne.
Har ta gama ta ɗora ma su ruwan wanka da za su yi idan sun kammala cin abinci.
Pure water ta ɗauko cikin leda ta ajuye ma su, sannan ta shimfida tabarma ta ajiye abincin jan tabarma ta taimaka ma sa ya dawo kan tabarma ta ajiye ma sa abincin a gabansa.
Suka fara ci don dama ta riga ta ɓare ɓawon ƙwan, baya jin cin abinci amma haka ya daure ya ci sakamakon idan bai ci ba za ta shiga danuwa, shi kuma baya son damuwarta.
Bayan sun gama ta ba shi magani ya sha da ruwa.
"Bari na zuba ma ka ruwan wanka ko?"
Tashi ya yi ya shiga ɗakin ya duba kayansa ya ciro jallabiya wacce idan ya yi wanka ita zai saka a banɗakin.
Koda ya fito ta hada ma sa ruwan ta kai ma sa, shiga ya yi ita kuma ta fara wanke-,wanke.
Bayan ya fito ita ma ta shiga ta yi wankan nata.
Yana ganin ta fito ya fito cikin ɗakin don ya ba ta damar shirya wa ta saka kaya.
Da kallon mamaki take bin sa har ya fice. Ta rasa gane dalilin da zai saka a duk lokacin da za ta cire kaya ko za ta saka kaya sai ya fita ya bar ma ta ɗakin. Bayan shi ba gani yake yi ba to meueye amfanin fitarsa tun da bai da idanun ganin jikinta.

Page5️⃣0️⃣
Da kallon mamaki take bin sa har ya fice. Ta rasa gane dalilin da zai saka a duk lokacin da za ta cire kaya ko za ta saka kaya sai ya fita ya bar ma ta ɗakin. Bayan shi ba gani yake yi ba to meye amfanin fitarsa tun da bai da idanun ganinta.
Rigar barci ta saka riga riga ce iya guiwarta ba ta da hannu sai na singileti ta saka sai turaren da ta fesa.
Fitowa ta yi ta gan shi tsaye ya jingine sandarsa a bangon ɗakin ya tura hannayensa duka biyu cikin jallabiyar da ke
Jikinsa yana kallon sararin samaniya. Da dukkan alamu ya yi zurfi cikin tunanin da yake yi. Kallonsa ta yi na wasu daƙiƙu kafin ta ƙarasa wajensa tana murmushi.
"Lafiya ka zo nan ka tsaya kuwa?"
"Lafiya lau, me kika gani?"
"Na ga daga fitowa ta wanka ka yi saurin fitowa daga ɗakin."
"Na ba ki waje ki shirya ne."
"To ni ban damu da ka fito ko kana nan ba, domin ko na cire kaya a gabanka ai ba gani na kake yi ba to me ye amfanin fitowarka?"
Murmushi kawai ya yi wanda shi kaɗai ya san ma'anar sa.
"Mu koma ciki to."
Ta yi maganar tana jan hannunsa zuwa cikin ɗakin ɗayan hannun ta ɗauki sandarsa.
Tunani yake yi a zuciyarsa yadda Ma'eeha ta kamu da son sa. Duk da ba ta san shi waye ba daga ina ya fito, duk da nakasar sa da halin talauci da yake nuna ma ta ba ta taɓa nuna ma sa wani abu da zai tabbatar ba ta son sa ba, kullun halin da take nuna ma sa a aikace shi ne nuna soyayyar ta a gare shi.
Zama suka yi a tabarmar da yake kwanciya akai. Tana fuskantarsa duk da shi kansa kasa yake kallo don daga ita sai rigar barci wacce ko gama rufe guiwarta ba ta yi ba. Kuma kanta ba ɗankwali babu ta tufke gashin kanta.
Wayarta ce ta soma ruri ta ɗan mika hannu ta dauki wayar.
ASP Nasir ne ke kiran wayarta.
Sam ita ta ma mance da shi, kuma ta san kiran nasa yana da nasaba ne da zancen ɓatar mijinta da ta kai rahoto, tun da ya ce za su yi bincike zai su neme ta.
Har wayar ta katse tana tana tana tunani, har sai da Makaho ya ce ma ta.
"Ba kiran wayarki ake yi ba?"
"Eh kira ne ya katse."
Daga haka bai sake yin wata magana ba, sai wani kiran ya sake biyowa baya.
Ɗaga wa tayi tare da yin sallama.
"Assalamu alaikum warahmatullah."
"Wa'alaiki salam."
"Ina wuni ASP ."
"Lafiya lau, ya kika ji da fargaba?"
"Alhamdulillah."
"Kin ji ni shiru ko, to sai dai na ce ki kara hakuri muna nan muna bakin iya ƙo..."
Murmushi da ta yi ne ya saka ya yi shiru, don ya san in dai Ma'eesha da ta zo station na su cikin tashin hankali tana kuma na ɓatar mijinta ce bai kamata yanzu ace tana wannan murmushi ba sai dai idan ya dawo su ba su sani ba."
"Ya dawo gida ne?"
"Eh ya dawo gida yanzu haka yana kusa da ni."
Shiru ta yi na ɗan lokaci kafin ya ce.
"Na taya ki murna."
"Na gode sosai."
"Idan ba damuwa zan iya tambayarki ?"
Ta san zancen da zai ma ta, saboda ta ga mamaki da tarin tambayoyi akan fuskarsa ranar da ta je kai rahoton ɓatar mijinta. Don haka ta ce na sa.
" Yanzu barci nake ji."
"Okay good night and sweet dreams."
Daga haka ta kashe kiran wayar. Ta kalli Makahon mijinta ta ce.
"Police ɗin da na kai ma sa rahoton ɓatar ka ne yake kira na."
Kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce .
"Amma da dukkan alamu ba ranar da kika kai rahoton ba ne kika fara saninsa. Dama can kun san juna kuma akwai alaƙa a tsakanin ku."
Kallon mamaki take yi ma sa yadda ya iya fahimta cikin sauƙi.
Shiru ne ya biyo baya kafin ya katse shirun da cewa.
"Lokacin da na ɓata har wajen police kika je kai rahoto."
Murmushin ta yi kafin ta ce.
"A lokacin da ka bata na shiga tashin hankali sosai ba kaɗan ba, na shiga makamancin tashin da na shiga lokacin da na rasa mahaifiya ta. Domin a wanan duniyar ba ni da kowa sai kai ka na mayar fitila ta kuma madubin dubawa ta, idan na rasa ka ban san inda zan tafi ba. Don ba zan iya rayuwa ni kaɗai ba, mahaifiyata Allah ya dauke ta, mahaifina ya juya ma ni baya. Ya nuna baya bukatata danginsa na sun juya ma ni baya. A baya duk da kakata Hajiya Turai da ta haifi Babana ba ta son mahaifiya ta, amma ni tana so na sosai, amma lokacin da mahaifina ya juya ma ni baya ita ma sai ta juya ma ni baya. Ban san inda dangin mahaifiyata suke ba, ban san in da zan samo su ba."
Ta yi maganar tana goge hawayen da ya gangaro ma ta.
"Ita mahaifiyarki ƴar ina ce?"
Tamabayar da ya yi ma ta kenan yana jin ba dadi a zuciyarsa.
"To an ce dai ƴa gidan marayu ta tashi, a ziyarar da kakana je kaiwa gidan marayu yana raba ma su kaya da abinci ne wata rana suka je da mahaifina gidan marayun in da ya ga mahaifiyata ya ce yana son ta. Wanda dalilin haka ya sa kakata Hajiya Turai ta tsani mahaifiya ta saboda rashin sanin asalinta."
Kamar an fama ma ta in da ke ma ta ƙaƙayi sai kuka take yi har da sheshsheƙa.
Shi ya ma rasa me zai ce ma ta da in da zai rarrashe ta. Don shi sam bai iya rarrashin da daɗaɗan kalamai ba.
Ɗan bubbuga bayanta ya yi alamar rarrashi, a hankali take dauke ajiyar zuciya.
Bayan wasu mintuna ta ce
"Har yau ban san tarihin rayuwarka ba, daga ina ka fito su waye iyayen ka suna raye ko ba su raye ban sani ba. Kuma ya kamata na san komai game da mijin da nake aure. Idan ƴaƴan da aka damu da su ne ko aka san danginsa ai ba za'a taɓa aurar da su ga Mutumin da da ba'a san asalin ko waye shi ba an yi bincike ina danginsa suke ba. Amma ka ga ni ba su damu da ko ɗan yankan kai ne ba sun ba da ni sun huta."
Ta yi maganar cikin ƙunar rai.
Tunawa ta yi da yadda Mamy ta shigo rayuwarsu, da yadda Mummy ta karɓe ta ba tare da sanin mugun nufin da ta zo da shi ba
Yau da gobe ba ta canja kowa, sai dai yau da gobe na bayyana ma ka haƙiƙanin mutane.
A hankali take tuna rayuwar ta ta baya tana zubar da ruwan hawaye.
Shi ma Makaho a nasa bangaren tunanin da yake yi daban ne
Soyayya na bukatar wani matsayi na karfi da kulawa tana bukar ɗauakar ɗawainiya ba wai kawai rabon damuwa ba.
Shi kam zai iya cewa ta wannan ɓangaren ya gaza yin duk waɗan abubuwa. Amma ita har yanzu ba ta taɓa ganin gazawarsa ba.
"Ka ɗan bani taƙaitaccen tarihin rayuwarka ma na."
Sai da ya ji gabansa ya faɗi, amma sai ya dake bai nuna hakan ba.
"Na tamabaye ka kwanakin baya akan sanin asalinka amma ba ka sanar da ni ba, kuma ya kamata na san da wa nake zaune, kamar yadda ka san tarihin rayuwata ban ɓoye ma ka ba, wanda ko yau ka tamabaye ni wani abu a shirye nake da na sanar da kai."
"Babu wani abun birgewa a cikin sanin tarihin rayuwata, ba na son tunawa ne shi ya sa ban sanar da ke ba, ki bari idan lokaci ya yi zan sanar da ke."
"Haba wani lokaci kuma zai yi, aure fa muka yi ya kamata na san wani naka ko wani abu naka."
Shiru ya yi kafin ya sauke ajiyar zuciya ya fara magana.
"Sunana Khalifa kamar yadda kika sani, Ni na fito ne daga Jahar Maiduguri a wani ƙauye muke rayuwa da iyayena da dangina duka a kauyen muke. Ina nufin kowa nawa yana cikin ƙauyen. Ni dama ko da aka haife ni da laluran makanta aka haife ni, ma taso ina raywai ni kaɗai ne ba tare da abokai ba, kasancewar ba na gani sai dai idan yara na wasa na kan je nisa da su na zauna ina sauraren su. Don ni ne na fari sai ƙanina guda ɗaya da nake da shi. Mukan yi wasa da shi a gida musamman idan mahaifiyarmu ta hana mu fita takan ce mu yi wasa mu biyu a gida, hakan ya sa ƙanina ya daina fita wasa shi ma. Sai dai shi an saka shi makarantar boko wanda Ni kuma iya makarantar islamiyya aka saka ni. Ina da shekaru ashirin wani iftila'i ya faɗawa ƙauyen mu na rikicin ta'adda ci in da aka kashe mafi yawan ƴan ƙauyen mu. Daga baya kuma gobara ta tashi a kauyen in da aka yi asarar rayuka da yawa har da iyeyena da ƙanina da sauran dangina na uwa da na uba. A ƙwauyen ɗaiɗaiku ne ba su da yawa.
Daga nan kowa ya dinga watse wa ana barin ƙauyen, wanda ni ma na bi sahun wasu har na tsinci kaina a garin nan.
Kuka sosai Ma'eeha ke yi tana tausaya ma su, sai dai ita tana da abu ɗaya, idan mutum ƙarya ya faɗa taka ji a ranta cewa ƙarya ne, shi ya sa lokacin da Mummy ta kawo Mamy gidan nan ba ta goyi bayan ta ba, kamar ta san abun da ke faruwa a kasar zuciyarta.
Haka wannan labarin na makaho duk da ta tausaya ma sai dai a kasar ranta, take ji kamar kada ta amince don haka ta ce.
"Wannan maganar da ka yi Mani na tarihin rayuwar ka idan na gane cewa ƙarya ne to ka sani za mu samu matsala da kai. Na tsani karya da cin amana, idan mutum ya yi ma mi daya daga cikin su ma nakan ji na tsani mutum.
"Kina tunanin ƙarya na yi ma ki?"
"Ban ce ka yi ma ni karya ba, na dai faɗa ma ka ne don ka sani."
_Fahad_
Zaune yake a dinning table shi da mutanen gidan, an loda ma sa kalolin abinci. Inna, Baba, Mama, Rumaisa, Farida, sai kuma Sidra.
Sai kalle-kalle yake yi ya rasa ta ina Nadra za ta ɓullo.
Mama na lura da yanayinsa kuma ta harbo jirginsa. Tsakuran abincin kawai yake yi ya kai wa baki amma ba wai don ya shirya cin abincin ba ne.
Sidra kan idanunta kur akansa ta zuba ma sa idanu kamar za ta cinye shi.
Sautin takalmi ne suke ji alamar ana zuwa waje da suke. Da sauri Fahad ya juya yana kallon wajen. Aunty Rahama ce da Nadra suka gani suna nufar dinning table idanun Fahad kur akanta ko ƙyafta idanun baya yi.
Da sallama suka ƙaraso wajen, gabadaya suka amsa ma su sallamar.
Zama suka yi kan kujeru biyu da suke jere wanda ba kowa akai.
Nadra ta gaida su suka amsa ma ta, yayin da ɗaya daga cikin ma su aikin ta fara sevin din su.
Ko da wasa ba ta ɗaga kai ta kalli in da Fahad yake ba. Shi kuma idanunsa na kanta, tambaya kasa yake yi.
Ya aka yi ta yi wani haske ta washe, ga fatarta sai ƙyalli take yi, ta kara cika ta zama babbar mace. Ɗaga kansa ya yi ya kalli Mama, yaga shi take kallo.
Kansa ya mayar kasa yana cigaba da cin abinci nasa.
Nadra ma ba wani cin abincin kirki ta yi ba ta tashi ta nufi ɗakin Mama.
Yana ganin ta shiga cikin ɗakin, ya mike tsaye yana cewa.
"Alhamdulillah."
Farida da Rumaisa suka ɓata fuska Farida na cewa .
"Ya ba ka ci abincina ba, Ni na dafa ma ka abincin don na burge ka fa?"
"Ayyah sorry anjima ki ɗumama ma ni zan ci."
Murmushi ta yi tana cewa.
"Zan saka ma ka a microwave oven na kawo ma ka shi."
"Yaya nawa fa ba ka ci ba."
"Ke ma har da ke?"
"Jinjina ma sa kai ta yi."
"Me kika dafa ma ni?"
"Faten doya."
Yadda ya yamutse fuska ne ya saka mutanen dake wajen yin dariya.
Takaici ta ji wanda ganin haka ya sa ya ce.
Zai ci ita ma. Wanda hakan ya sa ta saki ranta ta daina jin haushi.
Hankalinsa na kan Nadra da ta nufi part ɗin Mama.
Don haka part ɗin ya nufa kai tsaye.
Tana zaune kan kujera tana tana chatting da wata mata da Aunty Rahama ta haɗa su a waya, ita ce Aunty Rahama ke siyen kayan gyaran jiki a wajen ta tana ba wa Nadra. Kuma Aunty Rahama ta sanar wa matar halin da Nadra ke ciki. Kuma matar tana ba ta shawarwari. Wanda ta taimakon su ne ma Nadra ta daina sigar manyan hijabai da take yi a baya.
Yanzu ma tana sanar wa matar ne dawowan Fahad. Duk da tana son ta rabu da shi ne sa koda yayarta na son da har yanzu, sai dai matar da Aunty Rahama suna ɗora ta akan hanyar da za ta mamaye zuciyarsa ne.
Ƙamshin turarensa da ta ji ne ya haifar ma ta da faɗuwar gaba, wanda hakan ya sa ta ɗaga kai ta kalle shi. Yana tsaye ya zuba ma ta Mayun idanunsa.

Page 5️⃣1️⃣
Ƙamshin turarensa da ta ji ne ya haifar ma ta da faɗuwar gaba, wanda hakan ya sa ta ɗaga kai ta kalle shi . Yana tsaye ya zuba ma ta mayun idanunsa.
A hankali takowa ya fara yi zuwa gabanta cikin takunsa na ƙasaita.
Miƙewa tsaye ta yi sai dai ta kasa kallon cikin idanunsa. Har sai da ya matso dab da ita.
"Ba ki ga na dawo ba ne?"
"Na gani."
Ta faɗa tana kallon gefe fuskarta ba walwala."
"Okay kin ganni amma ba ki iya gaishe ni ba? Saboda kin raina ni ko saboda me? Saboda kin ga gadon barcina ko?"
Kafin ta yi magana Mama ta turo ƙofar ta shigo.
"Lafiya?"
Komawa bayan Mama ta yi tana kuka, shi kuma ya saki baki yana kallonta da mamakinta.
"Me ka yi ma ta?"
"Ba abun da na yi ma ta. Na zo ne na sanar da ita ta tattara kayanta za mu koma gidanmu."
Wani kallo Mama ta yi ma sa kafin ta ce .
"Ta tattara me?"
Sanin ba magana mai daɗi zai fito daga bakin Mama ba ya sa ya juya ya fice daga ɗakin. Don baya son Mama ta yi ma sa fada gaban wanan yarinyar.
Tana fita Mama ta kalli Nadra wacce daga kukan shagwaba zuwa na gaskiya, sakamakon jin Fahad ya ce za su koma gidansa wanda ita kam ba za ta so hakan ba.
"Mama zan zauna tare da ke ba zan bi shi ba."
"To kada ki damu kina tare da Mamanki ."
Nan ta cigaba da rarrashinta har sai da ta saki jiki.
"Shiga ɗaki ki kwanta ki huta."
"Ba musu ta nufi bedroom ɗin Mama dan ta kwanta. Sai da Mama ta ga shigarta sannan ta nufi ƙofar fita.
A corridor da zai sada ka da part ɗin Mama ta same shi tsaye ya rungume hannu a ƙirji ya zuba wa ƙofar idanu.
"Lafiya kuwa?"
"Mama wai me kike nufi da ni akan wanan yarinyar ne, na ga ta takan raina ni ne sannan kina goyon bayanta."
"Au haba? Zaginka ta yi ko me?"
"Na shirya ta zo mu koma gida."
"Ba in da za ta je."
"Saboda me Mama?"
"Tun da ka bar ƙasar nan ka tafi daidai da sau ɗaya ka taba kiran ta a waya ka ji lafiyar ta? Ko ka taɓa tamabayar wani cewa ya take, ba ka san da ita ba sai yanzu da ka dawo ne take da amfani a wajen ka? To bari ka ji ka tattara naka ka koma kai kaɗai dama can ka ce ba son ta kake yi ba."
Tana faɗar haka ta nufi main falon gidan. Kallon ƙofar ɗakin Mama ta yi kafin ya karasa ya tura ƙofar, ba ta falon sai ya nufi bedroom kai tsaye.
Kwance take a saman gadon Mama ta juyawa ƙofar baya.
A hankali take tafiya cikin ɗakin, har sai da ya karasa dab da ita sannan ta ji ƙamshinsa.
Tsoro ne ya kamata tana kokarin ja da baya ya yi saurin janyo hannunta ya riƙe.
Tsuke fuska ta yi tana kau da kai, da mamaki yake kallonta ganin yadda ta murtuke fuska.
"Yaushe kika raina ni har haka ne?"
"Tun ranar da ka nuna ma ni ko kai waye."
"Ni?"
Yayi tamabayar yana nuna kansa.
"Yaya Fahad me kake tsammanin gani daga gare ni? Na yi farin ciki da murnar dawowarka? Idan ba ka sani ba ka sani ba na farin ciki da dawowarka ba na ƙaunar ganin fuskarka a kusa da ni."
"Da gaske?"
Kai ta jinjina ma sa alamar eh. Gajeren murmushi ya yi kafin ya ce.
"Why?"
Kamar tana jira ta fashe ma sa da kuka tana cewa.
"Ka mance da abun da ka yi ma ni a daren da za ka tafi? Ka mance azabtar da ka gana ma ni, babu imani da tausayi ka saka ƙafa ka bar ƙasar nan ba tare da ka iya bude baki ko sannu ka ce ma ni ba ballanta ka taimaka ma ta ni? Kai kawai kanka ka sani ko na mutu buƙatar ka ta biya ko? Ka bar ƙasar ba ka da damu da halin da nake ciki ba ballantana ka kira ka tamabaye lafiyata akan halin da ka saka ni, amma kake tsammanin zan yi farin ciki da dawowarka?"
Ta karasa maganar tana kukan da yake fitowa daga ƙasar ranta, wanda ke nuna ƙuncin da zuciyarta ke ciki.
Shiru ya yi yana kallonta, wato abun da ya yi ma ta ya tafi ta rike shi a ranta duk tsawon watannin da ya yi a can, dama tana jin haushi da baya kiran wayarta kenan ko ya tambaye ya take. Shi kansa ya san bai kyauta ba, amma kuma ya zai yi .
Janyo ta ya yi a jikinsa ya rungume yana bubbuga bayanta alamar rarrashi.
"Ko ban ta fi ba idan ina ƙasar ba abinda zan iya yi ma ki, domin ko ina nan Innar dai da na kira ma ki ita ce zan sake kira ma ki ita. To banbanci da ina nan ko ba na nan, sannan da ban kira ki ba kin damu da ni ne, ko kin taɓa cewa bari ki kira ni ko tura ma ni saƙo?"
Tsabar takaici ture shi ta yi daga jikinsa tana ja baya, wato har yanzu girman kan nasa da jin kansa yana nan ba abun da ya sauya. Wato ba zai ba ta hakuri ya yarda ya yi ma ta laifi ba ko, sannan tsabar ya raina ma ta wayo ita ce za ta kira shi .
Ganin ta tura shi ta cigaba da kuka ya share ta ya yi fice daga ɗakin. Don shi baya jin zai iya ba ta haƙuri..
Goge hawayen ta yi ta na mamaki girman kai da jin kai irin na Fahad Majidaɗi.
Har ya fita ya dawo ya kalle ta ya ce.
Ki shirya mu koma gidanmu anjima."
Ina za fice Daga cikin dakin.
_Makaho_
Har karfr goma sha biyu ba dare suna fira da Ma'eesha, ita kanta ta san cewa ba su taɓa dadewa suna fira irin na yau ba. Ganin karfe goma sha biyu ya yi ne ya sa Ma'eeha ta rufe ƙofat ɗakin.
Nan kuwa zafi ya fara yi ma su sallama. Wanda ya sa ya Ma'eesha jan gajeren tsuki , Makaho ya ce
"Me ya faru ne kike tsimi?"
"Zafin nan ne yadda ya addabe mu."
"Kada ki damu za ki yi barci me daɗi."
Kan katifarta ta nufa ta hau sai da ta yi addu'ar kwanciya barci sannan ta kwanta .
Kwanciyarta ke nan ta ɗauki mefeci a gefen filon sannan ta kashe hasken da ta kunna, dama torchlight ɗin wayarta ce ta kunna.
Tana ɗan fifita idan barci ya kama idanun nata sai ta saki mafecin ya faɗi, daga nan kuma zafi zai sa ta farka ta kasa barci.
Ji ta yi ana lalubarta cikin barci, cikin tsoro ta ce.
"Yaya Khalifa?"
"Na'am ba ni mafecin na yi ma ki fifita."
Sai a lokacin ta saki aniyar zuciya tana cewa.
"A'a ka bar shi kai ma na san barci kake ji."
"Kada ki damu ba na jin barci, idan ma ina ji to zan kwanta."
Ba musu ta mika masa mafecin, ya fara yi ma ta fifita wanda ya sa nan da nan barci me daɗi ya ɗauke ta.
A daren ranar bai rintsa ba kwana ya yi yana yi ma ya fifita kamar yadda ya saba yi ma ta. Ita har mamakin yadda baya barci take yi. Ai dare mahutar bawa ne, ko ta hana ta ce ya yi barci baya yi.
Da Asuba ne ta farka daga barci tana mamakin sa.
"Ma'eesha kin tashi ne?"
"Eh na tashi sannu da ƙoƙari."
Wanka ya je ya yi sannan ya ɗauro alwala ya wuce masallaci.
Ita ma wankan ta yi ta ɗauro alwala ta gabatar da sallar asuba.
Sai da safe karfe shida da rabi ya dawo gidan.
Ƙamshin girkinta ne ya yi ma sa sannu da zuwa.
Ruwan Lipton ne wanda ya ji kayan ƙamshi take dafa ma su, don ta siyo kayan tea da biredi wanda ta siyo a shago da safiyar nan.
"Assalamu alaikum warahmatullah."
"Wa'alaika salam warahmatullah. Sannu da zuwa."
"Yauwa sannu da ƙoƙari Ma'eesha ."
Tabarma ta shimfida ma sa tana cewa.
"Ga tabarma nan daga cikin baranda na shimfida ma ka "
Ta ja hannunsa zuwa wajen tabarmar ya zauna, sannan ta durkusa cikin girmamawa ta gaishe shi, ya amsa ma ta cikin farin ciki da sanya albarka.
Ruwan shayin ta zubaa sa da madara pick powder na sachet da milo sachet ɗaya ta zuba sugar kadan ta ba su shi.
Dole ce ta saka yake cin abinci a gidan, ba wai don komai ba sai don gani yake yi da kunya ya zauna mace ke ciyar da shi.
Ita ma ta zuba na ta ta zauna gefen sa tana sha
Bayan sun gama ta ce
"Alhamdulillah . Ka ga jiya ba mu da abincin da za mu ci ba mu da kuɗin siye, amma yau Allah ya rufa ma na asiri ko?"
"Haka ne, Allah ya kara rufa ma na asiri duniya da lahira."
Ya faɗa yana kokarin tashi.
"Yau zan fita da safe."
"Lafiya dai ko?"
"Lafiya lau, kin san wata rana akan samu kasuwa da safe ne kawai."
"To Allah ya bada sa'a ya sa a samu abun da ake so."
"Amin ya Allah. Na yi wanka kafin na tafi sallar asuba bari na tafi yanzu."
Ta mike ta ɗauko ma sa basket kayan gyaran takalminsa, har kofar gida ta raka shi sai ta ba shi kayan tana yi masa addu'ar Allah ya tsare ya bada sa'a.
*ABUJA*
Wata hamshaƙiyar mara ce mai kimanin shekaru hamsin. Tana sanye da wani tsadadden leshi a jikinta. Kunnenta da wuyanta ɗan kunne ne da sarƙa na gold. Lokaci zuwa lokaci takan kalli mutumin da ke gefenta wanda yake sanye cikin suit.
Cikin ɓacin rai ta miƙa ma sa hannu alamar ya ba ta, mika ma sa wayar da ke hannunsa.
Ta karɓa ta fara duba wa hotunan Makaho ne tare da Ma'eesha. Wanda aka ɗauke su lokuta mabanbanta na farkon wanda aka ɗauke su ne da suka fito tana rike da hannunsa ranar da za ta siya ma sa waya. Da kuma wanda aka ɗauke su ranar da za su je asibiti gaida mahaifiyar Nasreen har ya sa Ma'eesha ta shiga keke ya ma sa duka.
Ranta a ɓace take kallon mutumin wanda ake kira da Jimoh ta yi kafin ta ce.
"Yanzu dan ya gano kana bin bayansa shi ne ya yi ma ka wannan shaƙar?"
"Ai Madam da ba don kiran wayar da kika yi ma ni ba da Allah kadai ta san abun da zai ma ni, kin ga yadda ya dimfaro ni kamar mayunwacin zaki?"
"Me suka je yi asibitin? Sannan kuma har yanzu ka kasa gano wace ce wanan yarinyar da kuma abun da ke tsakaninsu da ita?"
"Ban gano ba sai dai akwai wani a unguwar da suke an ce shi ya ba su hayan gidan da suke zaune a ciki shi da yarinyar."
"Okay, a unguwar da suke zaune shi ma a anan yake da zama?"
"Eh a nan yake da zama , sai dai ina jin tsoro."
Wani kallo ta yi ma sa saboda ta san me zai ce.
"Tsoron me kake ji?"
"Kada ya sake kama ni a karo na biyu, Madam yaron nan naki fa ba shi da sauki."
"Wancan karon ma ai sakarcin ka ne ya saka ka bari ya gan ka, kai ba ka san yadda za ka iya takunka ba?"
"Yarinyar dai maƙura ce a wajen kyau, sai ka ce aljana ce ita?"
Da sauri ta kalle shi ta kuma kalli hoton dake wayar ta zuba wa fuskar Ma'eesha idanu tana kallon kyakkyawar fuskarta wacce kyawun yarinyar sai da ya firgita ta. Ta kalli hannunsu dake sakale cikin na juna, shi yana sanye da baƙin glass ita kuma tana sanye da doguwar rigar Abaya.
Tsuki ta ja kafin ta ce.
"Kuma ba ka tunanin cewa ita yarinyar abokinyar aikinsa ce?"
"Madam ba na tunanin abokinyar aikinsa ce domin a tarihi Jalaluddeen baya aiki da kowa, shi kadai yake aikinsa duk hatsari aikin kuwa."
"To ka ce a wani gida yake zaune da yarinyar ko?"
"Ƙwarai kuwa."
"To me ya sa wanann karon bai kama hotel ba?"
"Madam a farko a hotel yake zaune daga baya ne ya daina kwana a hotel yake kwana a gidan shi da yarinyar."
Kallon mamaki take yi ma sa kafin ta ce .
"Kana nufin a gida ɗaya yake kwana da yarinyar?"
Ƙwarai kuwa Madam sai kin ga gidan, gida ne na ƙasƙantu miskinai, kai wannan ma ba zan kira shi da gida ba sai sai akulki ko kango. Don wallahi ko gidan da kike kiwon karnuka ya fi wanan gidan sau dubu."
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Yaushe Jalaluddeen ya zama haka? Rabon da ya kira ni a waya ma na mance kuma ko na kira shi baya shiga. Amma na san inda zan bi na san komai."
Ta yi maganar tana haurawa upstairs, ba dadewa ta fito riga da handbag da mayafinta, da hannu ta yi wa Jimoh alamar su tafi.

5️⃣2️⃣
Ta yi mahada tana haurawa upstairs ba daɗewa ta fito riƙe da handbag ɗin da mayafinta, hannu ta yi wa Jimoh alamar su tafi.
Suna fita ta rufe ƙofar direbanta na ganinta ya taso da sauri, ta ɗaga ma sa hannu cike da izza, dole ya koma. Jimoh na bin ta a baya ta nufi wata tsadaddiya mota ta nufa yana bin ta a baya, key din motar ta mika ma sa ya karba ya bude ma ta bayan motar ta shhga ta zauna. Zagayawa ya yi mazaunin direba ya shiga ya yi wa motar key, horn ya yi maigadi ya wangale ma sa gate suka bar gidan.
_Fahad_
Yana fita daga part ɗin Mama part ɗin Baba ya nufa, saboda ya san shi kadai ne idan ya yi ma sa Maganar komawarsu gidansu zai ce su tafi ba tare da Mama ta yi gardama ba. Don ya lura yanzu Mama so take ta hana ma sa matarsa.
Da sallama ya shiga falon Baba, cikin sa'a kuwa ba kowa sai shi kaɗai yana duba wasu documents.
Baba ya amsa ma sa sallamar yana cewa.
"Ambassador kai ne ?"
"Eh Baba."
Ya zauna saman Centre carpet ya yi shiru. Ganin shirun da ya yi ne ya sa Baba fahimtar akwai magana a tare da shi.
Tattara hankalinsa wuri ɗaya ya yi ya ce.
"Kamar akwai magana a bakinka ko?"
Ɗan sunkuyar da kai ya yi kafin ya ce.
"Dama ina son mu koma gidanmu ne?"
"To In ban da abun ka wanan ai ba wani abu ba ne, ka ɗauki matarka kawai ku tafi ma na."
"Am dama dai Mama ce na ga kamar ba za ta amince ba."
"Kan wani dalili za ta hana ka ɗaukar matarka?"
Wayarsa ya dauka ya lalubo lambar wayar Mama ya danna ma ta kira.
Bugu biyu ta ɗaga tana yi ma sa sallama.
"Assalamu alaikum."
"Wa'alaiki Salam, ki zo part ɗina ina son ganinki."
"To Alhaji."
Ta kashe kiran wayar tana kallon Aunty Rahama da Inna da suke firar kallon da Fahad ke bin Nadra da shi suna dariya.
"Bari na je Alhaji na jira na."
Tana faɗar haka ta mike don zuwa amsa kiran wayar Baba.
Koda shiga falon Baba ta tarar da shi da Fahad ne a falon. Tun da ta shigo kansa yake a ƙasa ba ta kawo cewa shi ne ya zo da Baba da wata maganar ba.
Zama ta yi kan kujerar da Baba yake zaune, kujera mai zaman mutum uku ne.
"Barka da hutawa Alhaji."
"Yauwa Barka dai ya gidan?"

"Yaushe Fahad da matarsa za su koma gidansu ne, tun da ya dawo ai zamanta ya kare a nan sai ta koma ɗakin mijinta ko?"
Kallon Fahad Mama ta yi ta gane cewa shi ya kawo wa mahaifinsa zancen.
"Au har ka kasa jurewa ka kawo ƙarata ne tun yanzu? Ashe ba za ka iya jure wa ba, da wuri haka?"
"To wane dalilin zai sa ki hana ma sa matarsa ma?"
"Alhaji idan na ba ka labarin abun da yaron nan ya yi wa yarinyar nan za ka goyi bayana. Ni na yanke shawarar ma gara ya sake ta kawai tun da ba son ta yake yi ba."
"Subhanallah me ya kawo wanan zancen kuma? Ba na son na sake jin makamancin wannan zancen, Fahad ko da wasa idan ka saki Nadra za ka hadu da mummunan ɓacin raina."
"Alhaji ka tsaya ka saurare ni ina da dalilin da ya sa na ce ya sake ta. Aure ibada ne amma idan da cuta barinsa halal ne."
"Wacce hujja kike da ita da za ki ce ya saki matarsa."
Murmushin takaici ta yi kafin ta ce.
"Hujjoji ma nake da su ba hujja ba. Hujjata ta ɗaya yaron nan da bakinsa ya ce baya son yariyar nan zai sake ta, na biyu na sanar da kai abinda ya yi ma ta a ranar da ta kwana a ɗakinsa, sannan ya saka ƙafa ya bar ta cikin halin jinya bai taɓa kiran wayarta ya tambaye ta jikinta ba. Kuma bai taɓa kiran wani ya tamabaye ya jikinta ba, tsawon watannin da ya yi a can mulkin nuna waya bai taɓa tamabayar ta ba. Sai yanzu da ya dawo ya ce ta bi shi saboda zalunci to ba za'ayi wannan da ni ba, ba zai iya yi ma ta adalci ko tausaya ma ta ba."
Shiru falon ya ɗauka na tsawon mintuna biyu kafin Baba ya ce.
"Fahad ba ka kyauta ba gaskiya, ba'a haka, ai ko dabba ce ka siyo ai ka dinga duba lafiyar ta, idan ba ka nan dole ka nemo mai kula da ita ballantana bil'adama. Ta ya za ka wofantar da yarinyar da aka ba ka amana? Ban tsammaci haka daga gare ka ba."
Sai a lokacin ya daga kansa yana cewa.
"Baba don Allah ku yi hakuri, ba yadda ake tunani ba ne, duk da ban kira ya kuma ban tamabaye kowa ita ba amma ina kula da ita duk wani motsi nata akan idanuna take yin sa, ina kallonta, kuma na tabbatar tana cikin ƙoshin lafiya. Gabadaya hankalina yana kanta tun da na bar ƙasar nan."
Shiru suka yi suna sauraron sa kafin Baba ya ce.
"Ka faɗa ma ni gaskiya meye ra'ayin ka akan wannan yarinyar ? Ba na son a takura wa kowa a cikin ku, shin za ka iya zama da ita a matsayin matar aurenka kuma ka kyautata ma ta da yi ma ta adalci ba cuta ba cutarwa? Shin kana son ta ?"
"Baba ban sani ba ko son ta nake yi yanzu, na dai san a baya da aka aura ma ni ita ni kan ji haushi da takaici ko ganinta ba na son yi, a duk lokacin da na ganta sai na ji raina ya ɓacj na dinga jin haushin Sidra. Saboda ita ce ta ja faruwar komai. Amma daga baya ɗan zaman da na yi da Nadra na fahimci ta fi Nadra nagartar da kowane namiji yake buƙata daga wajen ƴa mace. Domin ta fi Sidra hankali da nutsuwa, tarbiyya, haƙuri juriya da hangen nesa, kuma tana aiki da ilimin ta na Addini. Waɗan nan ɗabi'un nata da na fahimta ya sa na daina jin haushin da nake ji na aura ma ni ita, kuma na san duk namijin da ya samu mace mai ɗabi'un nan da na lissafa tabbas ya zaɓawa ƴaƴansa uwa tagari. Na san cewa a baya da nake soyayya da Sidra i na duba hasken fata da ƙyale-kyale ne amma yanzu na fahimci ba shi nake bukata ba, nagartacciyar mace wacce za ta yi yarda waɗan da suka isa da ita su yi ma ta tsawa ta bi umarnin iyayenta ko mijinta nake buƙata. Ba ma mance huɗubar Mahaifinsu lokacin da Sidra ta gudu bayan mahaifinsu ya ba ni Nadra a madadinta sai yake sanar da ni cewa. Ya san ya yi ma ni sakayya da wacce zan ci jin dadin zama da ita, idan da Nadra nake so ba zai taɓa ba ni Sidra a madadinta ba, amma tun da Sidra ce to ya ba ni Nadra ba zan taɓa nadamar aurenta ba, domin ya san cewa zan fi jin dadin zama da ita akan Sidra. Kuma na zauna na yi tunani na ga cewa idan har Sidra na girmama iyayenta ba za ta taɓa guduwa a ranar aurenta ba, hakan na nuna rashin ɗa'a da biyayya ce ga iyaye. Amma ita Nadra duk da tana da wanda yake so kuma sun tabbatar za ta yi biyayya ga umarnin su sun isa da ita ya sa suka aurar da ita ba tare da amincewar ta ba. Wanda ko da aka sanar da ita ba ta bijire ma su ba ta yi ma su biyayya ta zauna da wanda suka zaɓa ma ta. To ire-iren waɗannan tunanin na yi na ji na daina jin haushin aurenta kuma ɗabi'un yarinyar suka burge ni. A yanzu ban sani ba ko ina son ta amma kuma na san cewa zan iya zaman aure da ita ta zama uwar ƴaƴana in sha Allah na ɗauki ƙaddarar da Allah ya rubuto ma ni cewa ita ce matata ba Sidra ba."
Hannu Mama ta ɗaga tana godewa Allah da ya amshi addu'ar ta cikin gaggawa, kullum addu'ar ta Allah ya karkato da hankalin Fahad kan matarsa.
Murmushi Baba ya yi ya ce .
"To Hajiya za'a iya ba shi matarsa?"
"In sha Allah, yanzu ma kuwa don sai yanzu hankalina ya kwanta."
_Makaho_
Bayan sun yi sallama da Ma'eesha yana ta tafiya akan hanya har ya iso bakin titi. Kai tsaye ya nufi wajen da yake zama yana yin aikinsa na gyaran takalmi.
Zaman sa na jimawa sai ga wasu motoci sun fito daga layin da ke tsallaken da su makaho ke sana'a. Motoci ne guda biyu ɗayar irin na ɗaukar kaya ne amma bayanta a rufe yake. Ɗayan kuma motar ce baƙa ce mai tinted glass ba'a ganin wanda ke ciki .
Tun da motocin nan suka fito ya zuba ma su idanu ta cikin glass wanda ba wanda zai ce ga abun da yake kallo.
Direban motor kaya ce ta tsaya daidai in suke ya yi parking, wanda hakan ya sa bakar motar dake bin motar a baya ita ma ta tsaya.
Direban babban motar ya fito yana cewar.
"Mallam gyaran mun takalmin nan yanzu sauri nake yi."
Ya yi maganar yana miƙa wa makaho takalmin. Ganin makaho yana ɗan lalube ne ya sa ya ce .
"Kai ba ka gani ne?"
Mai yalon dake kusa da makaho ya ce.
"Eh baya gani makaho ne amma ya iya aiki sosai."
Zai yi magana kenan sai wanda ke cikin bakin motar ya fito yana cewa.
"Wani irin sakarcin ne wanan za ka tsayar da mu akan titi bayan ka san ba mu da lokaci ko?"
"To ya kake so na yi so kake idan mun sauka na fara tafiya ba takalmi ga shi daji za mu je idan ƙaya na taka fa me za ka ce?"
"Ba abun da zan yi amma ka sani idan har ka bari kolayen nan suka fito kai ne a cikin hatsari da ka ɓata ma na lokaci, nawa ne takalmi da ba za ka siye sabo ba?"
"Kolayen ai duk an siye su sai mun tafi za su zo ta Wajan sannan kuma idan zan siye takalmi ai ba nan zan samu ba sai na je wani wajen da za mu ɓata lokaci."
Wayar direban motor kaya ce ta yi ringing, ya dauka yana cewa.
"Afuwa oga kaya za su isa cikin aminci ba matsala, dama wani Kolo ne yake son ba mu matsala amma yanzu shi ma an siye shi ya shigo daga ciki."
Daga nan ya katse kiran wayar yana cewa.
"Wai har yanzu Makahon nan bai gama gyaran takalmi ba ne?"
Daidai lokacin ne Makaho ya Miko ma sa takalminsa ya karba yana dubawa.
"Ikon Allah Makaho mai basira, lallai idan mun dawo zan neme ja muna da takalmin da muka tara sun tsinke."
Ɗari biyar ya ba makaho ya karba yana cewa .
"Nawa ne nan?"
"Ɗari biyar ce."
"Ba na da canji?"
"Bai ma san yana yi ba tuni ya shiga motar ya yi ma ta key."
Mai siyar da Yalo ne yake cewa .
"Rabon ka ce."
Kallon mai Yalo ya yi kafin ya ce.
"Ina zuwa zan je na dawo."
"To Allah ya tsare."
Barin kayan aikinsa ya yi a wajen ya tafi da sandarsa.
Can nesa da wajen ya tsaya sai ga wani mai nape ya zo ya tsaya a gabansa.
Shiga yayi suka bar wajan.
Kai tsaye wani hotel suka nufa in da Makaho ya fito ya bar mai nape din zaune ciki yana jiransa, don ko sandarsa bai ɗauka ba a cikin keke nape ɗin ya bar shi.
Cikin hotel ɗin ya shiga ba tare da ya yi wa kowa magana ba, sama ya haura sama.
Ɗaya daga cikin ɗakunan ya sa key ya buɗe ya shiga ciki.
Kayan jikinsa ya fara ragewa sannan ya shiga bathroom don yin wanka.
Almost 30 minutes ya ɗauka yana sakarwa kansa shower 🚿, kafin ya gama wanka ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa da wani karami yana goge ruwan kansa.
Man shafawa mai sanyin ƙamshi ya shafa har ya ɗauki turare zai shafa sai ya yi wani tunani ya fasa shafawa ya ajiye.
Ƙananan kaya ya saka wando three quarter fari ya saka da farar riga. Gudun A.C ya ƙure sannan ya hau saman lafiyayyen gadon ya kwanta, ba jimawa barci me daɗi ya yi awon gaba da shi kasancewar daren jiya bai yi barci ba kwana ya yi yana yi wa Ma'eesha fifita.

Page5️⃣3️⃣
Ƙananan kaya ya saka wando three quarter fari ya saka da farar riga . Gudun A.C ya ƙure sannan ya hau saman lafiyayyen gadon ya kwanta. Ba jimawa barci me daɗi ya yi awon gaba da shi, kasancewar daren jiya bai yi bari ba kwana ya yi yana yi wa Ma'eesha fifita.
Sai da lokacin sallar azahar ya yi sannan ya farka, ya yi awa huɗu yana barci.
Bathroom ya sake faɗawa ya yi brush da toothpaste ya yi wanka ya fito ya shirya cikin jallabiya fara.
Fita ya yi don zuwa masallacin da ke cikin hotel ɗin.
Har zuwa lokacin mai nape ɗin da ya kawo shi yana nan yana zaman jiran fitowarsa. Sai dai a lokacin mai nape ɗin ya gama cin abinci a cikin takeaway yana shan ruwa.
Sai da aka idar da sallar sanann ya koma cikin hotel ɗin.
System ɗin sa ya ɗauka yana shigar da wasu bayanai.
Manyan wayoyinsa da ke ajiye a saman table ya ɗauki daya ya kunna.
Wata lamba ya lalubo ya kara a kunne, bugu daya aka ɗaga.
"Hello sai yau ka ga damar a same ka a waya kenan."
Murmushi mai sauti ya ba yi wanda ya ba fito har ta cikin wayar. Kafin ya ce.
"Ina hotel a ɗakin da ka sani."
Daga haka ya katse kiran wayar kafin ya ɗauki ɗayar tsadaddiyar wayarsa ƙirar Samsung Galaxy Z fold 5 farashin wayar ya kai miliyan biyu da dubu ɗari shida. Irin wayar da ake lanƙwasawa ce ta koma ƙarama idaaka buɗe ta kara girma.
shiga what's up ya yi yana duba tarin saƙonnin da suka shigo ma sa, na wasu ya buɗe, na wasu bai bude ba. Har zai aje wayar sai ya shiga bude saƙon da ya ga messages nata ya fi na kowa yawa. YASMEEN shi ne sunan da ya furta kuma sunan ne a jikin wayar da ya yi Seve da shi.
"Messages ne barkatai wasu photon ta ne kawai tana hawaye, wani kuma emoji ne na kuka, wasu kuma voice message ne tana nuna damuwa na rashin ji daga gare shi ba kira ba saƙo. Messages na karshe da ta tura ba ta yi magana ba sai rera ma sa kuka kawai take yi.
Bai ma ta reply ba ya kashe wayar ya ajiye kawai.
System ɗin sa ya sake ɗauka ya shigar da wasu bayanai.
Daidai lokacin aka fara knocking ƙofar. Tashi ya yi ya je ya bude kofar . Tashi yayi ta bude kofar nan ya ga Abokinsa da ya kira ya sanar ma sa yana hotel ɗin.
"Khalid."
Ya fada a saman leɓensa.
Murmushi Khalid ya yi yana cewa yau dai ga ni ga *Senior intelligence officer*.
"Dama ba ka gani na ne?"
"Yanzu kam wa ke ganinka ai sai sai wanda kake tare da su."
Wayarsa ce ƙarama wacce Ma'eesha ta siya ma sa ta soma ruri a cikin aljihun kayan da ya cire na wanda ya zo da su.
Kallon kayan Khalid yake yi daidai lokacin da ya ga Khalifa ya ɗauki wayar, sannan ya duba ya san mutum ɗaya ce za ta kira shi a wayar.
"Nurul ƙalb"
Sunan da ya fito kenan don da wannan suna Ma'eesha ta yi Seve number ta da shi a wayar.
"Assalamu alaikum."
Daga can ɓangaren ta sa da wa'alaika Salam.
"Mijina ya kake?"
"Lafiya nake matata."
"Ma sha Allah, ga abincinka na ajye ma ka don Allah ka dawo ka ci kada ka zauna da yunwa ka ce sai yamma."
Murmushi mai sauti ya yi kafin ya ce.
"Kada ki damu ni ba na jin yunwa."
Nan dai da ƙyar ya shawo kanta ta hakura akan idan ya dawo da yamma sai ya ci.
_Nadra_
Tana zaune a falo a falon Mama sai ga Sidra ta shigo ta same ta.
"Ƙanwata kina zaune ne ke kaɗai?"
"Eh, sannu da shigowa Aunty Sidra."
"Yauwa sannu."
Zama ta yi a gefenta tana ma ta murmushin yaƙe.
"Sai ga Fahad ya dawo ko?"
"Eh Aunty."
"Kin yi magana da shi ne?"
"Eh cewa yayi wai na tattara kayana mu koma gidansa."
Sai da gaban Sidra ya fadi amma sai ta dake ba ta nuna tashin hankalin take ciki ba
"To ke me kika ce ma sa?"
"Cewa na yi ba zan koma ba, don Mama ma ta goyi bayana ta ce ba zan koma ba."
"Da kyau, yanzu ya alƙawarin da kika ɗaukar ma ni?"
"Aunty Sidra ai ban ɗaukar ma ki alkawarin komai ba."
Wani kallo ta yi ma ta kafin ta ce.
"Lokacin da na ce ma ki ina son Masoyina har yanzu ke da kanki kika ce ba son sa kike yi ba biyayya kika yi wa iyayen mu, na ce ki taimaka ma ni ya sake ki ya aure ni ni ma zan taimaka ma ki don ki auri Ya Sayyadin da kike so?"
Jinjina kai Nadra ta yi kafin ya ce.
"Eh tabbas mun yi haka, amma da kike ce ma ni wai sai na yi ma sa rashin mutunci da fitsara na dinga wulakanta shi sanann na dinga waya da tsohon saurayina dole zai sake ni a lokacin na ce ma ki ba zan iya aikata abu ɗaya da kike so na aikata ba. Ba don ko komai ba ke kanki shaida ce ko kare ne ba zan iya wulakanta shi ba, ballantana Ɗan Adam, ko kin manta cewa da duk wulakancin da kike yi wa ma'aikatan gidanmu da zaginsu da kike yi har ki ɗaga hannu ki mari mutanen da a haife sun haife ki me nake yi a lokacin. Kuka fa nake yi. Da a ce zan iya aikata hakan da a kan Waɗanda kike aikata wa zan yi. Ya kamata ki yi amfani da ilimin da Allah ya ba ki wajen tuna cewa Yaya Fahad mijina ne yi ma sa biyayya wajibi ne saɓa ma sa tamkar na saɓawa umarnin Allah ne. Tabbas na yi iya taimakon da zan yi ma ki wajen ganin ya sake ni ya aure ki, tun kafin wani abu ya shiga tsakanin mu na roƙe shi da Allah cewa tun da ba so na yake yi ba ke ni ma ba son sa nake yi ba ya taimaka ya sake ni ya aure ki tun da kin dawo kuma kina son sa shi ma yana son ki ya aure ki. A lokacin yake sanar da ni cewa zai sake ni amma ko ya sake ni ba zai taɓa auren ki ba, tun da har kika iya guduwa a ranar aurenki da shi. Tun a lokacin ya cire ki daga rayuwarsa, idan har ya nemi abu bai samu a lokacin da ya so ba ya fitar da abun kenan daga cikin rayuwarsa. Shi idan ya juya wa abu baya taɓa waiwayarsa har gaban abada."
"Ƙarye ne , ƙarya ne wallahi.Fahad nawa ne ni kaɗai, kuma sai na raba ki da shi na aure shi."
",Zan yi farin ciki da haka, fatan nasara."
Nadra ta faɗa tana murmushi. Daidai lokacin Mama ta shigo da sallama. Ganin yadda suka yi cirko-cirko ya sa ta kalli Sidra da ta tsuke fuska ta ce.
"Lafiya kuwa?"
"Lafiya lau Mama."
Ta faɗa tana aro murmushi ta yafa a kan fuskarta.
Ba dai gamsuwa Mama ta yi ba, amma sai ta bar zancen tana cewa.
"Shiga bedroom ki tattara kayanki ki zo ki bi mijinki ko kuma gidanku."
Daga Sidra har Nadra sai da ƙirjinsu ya buga a tare.
Ganin yadda ta kwaɓe fuska ne ya sa.
Mama tsuke fuska don kar ta kawo ma ta wasa.
"Mama don Allah ki bar ni a nan."
"Okay to je ki roƙi Babanku shi ya zartar da hukunci ba ni ba."
Hawaye ya fara yi ma ta sintiri akan fuska tana cewa.
"Shikenan na shiga uku ni Nadra."
Janyo ta Mama ta yi ta zaunar da ita a gefenta, sannan ta riko hannunta cikin nata, cikin sigar rarrashi ta ce.
"Meye abun tashin hankali kuma ƴata, ina ce da can ai kike zaune da shi kafin kuka dawo nan?"
"To ai lokacin..."
Sai ta yi shiru ta kasa cewa komai.
Murmushi kawai Mama ta yi don ta san dalilin Nadra yanzu.
"Kar ki damu ba komai in sha Allah, komai ya wuce da yardar Allah. Idan ya yi ma ki wani abu da ba daidai ba, ko abin da kika san ba ki so to ki yi sauri ki ɗauki wayata ki danna ma ni kira, za ki ga hukuncin da zan ɗauka."
Mama ta lura da Sidra ta ga rashin jin daɗin da ta shiga yanzu -yanzu. Kuma ta fahimci har yanzu tana son Fahad ba ta fitar da shi daga cikin rayuwarta ba, duk kuwa da Kasancewar yanzu yana auren ƙanwarta ce.
"Mu je ta taya ki tattara kayan yamma ta yi."
Ta yi maganar tana jan hannun Nadra.
"Yi zamanki Mama bari ba taya ta tattara kayan."
Aunty Rahama ta yi maganar tana shigo wa hannunta riƙe cikin na Baby Zahrah.
"Dama ba ki tafi gida ba?"
"Eh na je kaeɓowa Nadra saƙo ne dama ."
Ta yi maganar tana jan hannun suka nufi bedroom ɗin Mama.
Sidra kam ficewa ta yi daga cikin ɗakin ba tare da ta yi wa kowa magana ba. Murmushi kawai Mama ta yi ta girgiza kai.
Aunty Rahama na taya ta shirya kaya tana sake ba ta shawarwari. Hatta kayan gyaran jiki ta fito da su a cikin handbag ɗin ta ta saka ma ta cikin wata ƙaramar jaka. Sannan ta ciro wani ƙaramin roba da ke da wani hadin ta bude murfin goran ta ce.
"Karɓi ki sha."
Girgiza kai kawai ta yi alamar a'a. Amma ganin ba wasa a fuskar Aunty Rahama ya sa ta karɓa ta shanye.
Sauran kayan duk ta yi ma ta bayanin yadda za ta yi amfani da su.
Bayan sun ja akwatunan zuwa falo ne ma su aikin gidan suka kwashe su suka fita da su bisa umarnin Mama.
Direban Fahad ya jera akwatunan a bayan mota.
Fahad ya nufi part ɗin sa dan ɗaukar wasu abubuwan bukatar. Tsarabr da ya kawo ma su daga America ya sanar wa Rumaisa ta fito da su tare da bayanan na kowa.