Sashe 5
Majnoon Part 1 Complete Hausa Novelp · about 8 min read
sakamakon rashin bacci dabata samuba, Gabanta yazo yayi tsaye yana kallonta, kamar zaiyi magana saikuma yakasa, zaunawa yayi ya kura mata ido yana kallonta, sai yaji ta kara shiga ransa, Gaban rumaisa duka yake tara2 kanta a sunkuye ta kanne idonta, sai karatunta take billahakki, Ganin takai karsher sura yasa tadakatar da karatun, a hankali take bude idonta, tadago kanta sukayi ido hudu, tagumi taga yayi yana mata murmushi, cike da tsoro ta iya furta "ina kwana" sai kuma ta sunkuwar da kanta, tana jiran taji mezaice, murmushi yayi "lafiya lau, sai kuma ya tambayeta meya kawoni dakin nan" Duk da batason hada ido dashi amma a hakan tadaure ta daga kanta ta kallesa, tayi mamakin tambayar da yayi mata, sai kuma tatuna da cewa kodafa yazo dakin cikin maye yake, ajiyar zuciya tayi sannan tace "cikin maye kazo dakin nan" "Oh god, Allah yasa ban dakekiba" fahad yafada yana kallon rumaisa, Sai a lokacin tayi masa murmushi "bakamun komaiba, hasalima nicee..." saita kasa karasa maganar tana kallonsa , fahad yace ihum karasa maganar mana, Rumaisa tace " a a kabarshi kawai katashi kaje kayi sallah" Fahad ya zare ido da mamaki "sallah kuma, lokaci yayi ne" Cike da mamaki rumaisa tace "au bakamasan lokacin salla ba" Fahad yafada a kasale "nibanma iya sallarba, domin rabona da salla tun ina dan shekara 15. Amma tunda nagirma na daina" yana gama fada yamike yana kokarin fita daga dakin, rumaisa ta bishi da kallo harya fita, sannan tayi ajiyar zuciya tana mamakin rayuwar fahad ace mutum dan musulmi amma bai iya sallah ba, sai taji tanason zama dashi domin takowa masa sallah dakuma addini koda Allah zai saka mata da tukuicin abinda takeso wato majnoon, ( nace kekuwa rumaisa meya ganoki, nacewa saikin kowar dashi addini ko kin manta satoki yayi ) nidai nayi shiru naci gaba da rubutuna Yunwa tasoma addabarta a hankali ta mike tsaye, tanufi kofar fita tana leken falon, batasan gidanba, ai kuwa tana leka kanta sukayi ido hudu da wani bodyguard fuskarsa a murtuke ba imani, dasauri ta koma cikin dakin ta jingina jikinta a ginin dakin tana jan nunfashi... Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's Website:_www.abduljega.blogspot.com [10/20, 10:42 PM] +234 905 395 7618 : _Title:-_ *MAJNOON* _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES* 33 and 34 Via *OHW* _A love story_ Fahad nakarasa dakinsa yasa hannu ya warware daurin da rumaisa taimasa akai, sannan yaje yayi wanka, bayan yafito ya dauko wasu sabanbin kaya yasaka dominshi baya yiwa tufafi sawa biyu, Yadan zauna a bakin gado yana nazarin kalaman rumaisa, sonta yakeji yana kara shiga masa zuciya, bayajin zai iya rabuwa da ita, Ajiyar zuciya yayi Sannan Tashi yanufi dakinta yana shiga dakin yasameta manne a jikin ginin dakin ta sunkuwayar da kai, kallonta kawai yayi yana murmushi sannan yajuya zai fita, murya kasa2 rumaisa ta furta "yunwa nakeji" fahad ya juyo ya kalleta "to basai kije ki girkaba abinciba, aina gaya miki bazan kara siyo miki abinciba, domin ke matata ce" rumaisa ta tsuke fuska "to ai bansan inane kichin dinba" Yadda tayi maganar yabashi dariya, yace "muje nanuna miki " Rumaisa tazo gurinsa Tayi tsaye, riko hannunta yayi yana murmushi da sauri ta firgi hannunta cike da tsoro, fahad yace miye haka, "haramun me namiji yataba jikin macce idan har ba matarsa bace" rumaisa ta fada saikuma taja da baya, Mumrshi fahad yayi yakara kai hannusa "oya lez go" yana kokarin koma rikota, ta janye daga gurin, tasoma hawaye kuka na kokaron kubce mata, ganin zatayi kuka yasa fahad yadaga mata hannu "ya isa haka muje" fita yayi tabi bayansa tana share hawayenta, Nan yaje yanununa mata ko ina a gidan duk inda ta daga ido bodyguard take gani, a zuci tace wannan gidan ba wurin fita saidai taimakon Allah ko ina da mai tsaronsa, haka dai ya gama nuna mata ko ina sannan, yace shizai fita, sai ya yadawo, Kai kawai takada masa, Yana fita takoma kichin tafara dafa abinci... **** ***** ** Tun wayewar ake tursasawa umma akan tafadi inda takai rumaisa amma umma tace ita wallahi batasan inda rumaisa tajeba" tasha duka iya duka, duk jikinta ya kumbura, Abban rumaisa yana zaune a cikin police station din, domin anan yakwana tare dashi ake ganawa umma wahala, dominshi a yanzu yama daina jin sonta a zuciyarsa, baya mason ganinta, shidai kawai Rumaisa yakeson gani ko a raye ko a mace, Edonsa sunyi ja sosai domin bai samu bacci ba jiya, daya daga cikin police din ne yaoi gurinsa yana fadan "alhj wlh matar taki fada, nifa ina ganin kamar ba Hannunta a cikin batan wannan yarinyar" Abba yadago janjayen Idonsa ya kalli police din yace " taya akayi kasan babu hannunta aciki, kaine mijinta, ko kuma kaike tare da ita, ninasan matata kuma nina baku izinin kamata, dan haka idan zaku iya bincikenta ku binciketa idan kuwa bazakuniyaba tokubarta anan har sai zuwa lokacin da akacemun anga 'yata sannan kusaketa" police din zaiyi magana Abba yadaga masa hannu yana huci "karka kara mun magana, bana bukatar jin kowa a yanzu" Police din ya girgiza masa kai kawai ya fice yabar gurin, abba yajima a gurin yana tunani kala2 sannan yatashi yaje yaja motarsa yabar station din.. **** **** **** Nikaina bazan iya misilta muku iya kukan da faisal yayiba, a yunin jiya domin yunin jiya yakasance masa kamar ranar mutuwarsa, yakasa cin komai a haka yuni har dare, a daren ma bai samu isanshen bacciba, domin daya kwanta zai fara tunanin rumaisa, dolensa ya mike.. Wayewar gari Daga wanka yafito yana goge kansa da tawol, jikinsa duk ba kwari, yakarasa bakin mirror yana kallon kwayar idonsa sunyi ja sosai, Fusakar rumaisa ta soma yimasa gizo a bayansa tana masa Mumrshi ta jikin mirrorn yake ganinta, da sauri ya juya baya saikuma yaga bakomai, hawaye suka sauko masa, a hankali yasa hannu yashare sannan yakarasa gurin shirinsa, kananun kaya yasaka sunyi masa kyau sosai, sannan yasaka ta kalmi cover, ya janyo jakarsa saida ya kallmasa shirinsa na fita aiki sannan yafito waje.... Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's Website:_www.abduljega.blogspot.com [10/20, 10:43 PM] +234 905 395 7618 : _Title:-_ *MAJNOON* _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES* 35 and 36 Via *OHW* _A love story_ Kwata2 fuskarsa ba annuri, a falo yasami momy a zaune tayi jim tana tunani, a lokacin daddy yafita suna cen gurin fafutukar neman rumaisa, faisal ya durkusa ya yagaidata, ba yabo ba fallasa momy ta amsa tana murmushi "har ka shirya fitar ne " Yace "eh, banason nayi late ne" Momy tace " toh amma ai baka karya ba, mutum na fita baici abinciba" Mikewa faisal yayi yana wunkurin barin wurin yana cewa "bana jin yunwa" yana kallon momy, momy tace "to shikenan Allah yakai lfy" Faisal ya amsa da ameen, sanna yasa kai yafita yabar gidan yanufi gurin aiki, Katuwar office ce mai matukar kamshi turaren airfrshn yake a ciki ga takardu birjin akan table, Faisal yana zaune akan wata lallausar kujera, tana juyi dashi, yayi kuru yana kallon kofar office din, edo sa sunyi ja sosai, tunani rumaisa yake, a ranar daya fara gininta, ba zato ba tsammani hawaye suka soma gaggarowa a fuskarsa, yarasa meyasa son rumaisa yakama zuciyarsa har ta yadda bazai iya mantawa da itaba, son rumaisa yazame masa wani irin tabo a cikin zuciyasa wadda bazai iya warke waba, amma duk da haka yana zargin kansa, ayya soyayya baso take ta horar dashiba, ayya ba alhakin soyayyane yake fita akansaba, Hawaye suka kara saukowa kan kuma tunsa, a zuci yake fadan DAMA HAKA SO YAKE lallai kuwa akwai babbar matsala da wadda yakamu da son maso wani, hausawa nacewa son maso wani, koshin wahala, a hankali naji sautin kukansa yafara fita, da karfi ya daki table dinda ke gabansa, yana kuka yake fadan " why! Why! Why lov, meyasa kamun haka, meyasa ka ingizani gurin da baa sona, plx lov I accpt my fault, nasan nayi kuskure plx...! Yakarasa maganar yana kuka, ya saukar da kansa akan table din yana kuka, Yajima yana kukan kafin yaji an fara knocking kofar office dinsa, da sauri yake kokarin share hawayensa tare da kokarin gyara kansa, Saida ya tabbatar daya saita kansa sannan yace "yes com in" murya a raunane, Tunda aka bude kofar kamshin turaren almiski yadaki hancinsa, yaji wata irin ni'ima tasaukar masa a jiki, ya lumshe edo, sannan yadago kai ya kalli kofar a lokacin da take kokarin shigowa, caraf suka hada edo tana murmushi, takaraso cikin office din ta zauna a kan kujerar dake duban tashi, kyankyawar maccice ajin farko ga kyau ga murmushi mai kyau, (to wacece wannan) nakasa bawa kaina amsa.. Shikuwa ya kura mata edo, gizon fuskar rumaisa yake gani akan fuskarta, Tayi shuri tana kallonsa, cike dajindadi taga yau ya kura mata edo yana kallonta, ashe dama akwai ranar da faisal zai kalleta haka, a zuci take fadan Allah yasa dai yafara sona, cike da farin ciki tayi gyarar murya, yadan zabura a sannu sannan yadawo hayyacinsa, cike da jindadi tace "kwalliyar ta maka ne" Sai a lokacin faisal yagane cewa ba rumaisa bace a gabansaba, janjayen edonsa yadago ya kalleta sai kuma ya sunkuyar dakai ya tsuke fuska, uffa bai furta mata ba, Murmushi tayi tana kallonsa tace " nasan haryanzu cikin tsanata kake, amma dan Allah kayi hakuri, yaufa kwanana ukku kenan bangan kaba, kullum sainaso gurin aiki nayita nemanka, lafiya dai kuwa meke faruawa?" Shiru yayi mata yamaa kasa dago edonsa ya kalleta, Yanayin fuskarsa take nazari ga alama kuka yayi cikin salon kisisina ta furta " meke damunka ne dear?, ko anmaka laifine?" A hankali bakin faisal yasoma rawa yasoma fadan "ZARAH plx liv my office, bana bukatar kowa a yanzu inaso na huta" murmushi naga wadda yakira da zarah tayi kafin tace "aini dama a kullum baka bukatar zuwana gurin ka, nikuwa gashi nadake sai zowa nake, kuma ni bana ganin laifin kaina domin nasan wannan ba komai bane face sonda zuciyata take maka... tadan marairaice fuska kamar zatayi kuka "dan Allah faisal ka aminta da...." Da sauri yadaga mata hannu yana huci, kalamanta haushi suke bashi, ya nuna mata kofar fita yace "ki fita nace" Zarah tayi murmushi takara gyara zama, tana kokarin yin magana, Faisal ya mike tsaye yadaka mata tsawa, I said liv my