← Book details Majnoon Part 1 Complete Hausa Novelp Local reading mode
READING PART 25 OF 29

Sashe 25

Majnoon Part 1 Complete Hausa Novelp · about 8 min read

Cike dajindadi daddy yashiga mota yaje gidan abba yasanar dashi komai da mai martaba yace asanar masa, shima yayi na'am da wannan abin, kuma ya amince da a daura auren rumaisa da Mubarak bayan sallar isha, Goron da suka saya kawai sukaje suka dauka, sukayi alwala suka nufi masallaci, Sukayi salla isha bayan angama, tun ba'a fara fitaba, abba yakarasa gurin liman, yasanar dashi cewa yanason ayi daurin auren 'yarsa a yanzu, lamarin ya girguza liman dakuma mutane dake cikin masallacin, sunyi mamakin yin daurin aure cikin dare, Haka dai aka rabawa mutane goro bayan angama daura auren yarima Mubarak da Rumaisa, ( saidai kawai muyi musu fatan Allah yabasu zaman lafiya) Sannan kowa ya watse, abba yakoma gida cike da farin ciki, yagawa umma da haj luba, komai dake faruwa suma sunyi farinciki soaai, abba yanemi alfarma a gurinsu cewa karsu fadawa rumaisa komai dake faruwa, subarta kawai ayi mata AUREN BAZATA,, Rumaisa na dakinsa sai faman kuka take, jitakeyi kamarma yau dinnance ranar mutuwarta, saboda ita yanzu jitayi kamar batada sauran wani amfani a duniya yanzu tunda aka rabata da Majnoon dinta.. ( amarya rumaisa ansha kuka ) Wazai iya zuwa yafadawa rumaisa cewa, tafa zama amarya yakamata yadaina kuka https://free.facebook.com/Abdul-Mr-Smiles-Novels-220980808286357/?v=feed&_rdr [10/20, 10:54 PM] +234 905 395 7618 : _Title:-_ *MAJNOON* _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES* 117 and 118 Via *OHW* _A love story_ _Bayan kwana biyu_ *KOGI* Umman Mubarak tasamu lfy sosai, domin yanzu dakowama zata iyi yin fira, ta warke sumul tadawo kan karagarta ta sarauniyar kogi, Mubarak mahaka shima yasamu sauki, amma haryanzu zuciyarsa tana cike da zogi da radadin rashin matarsa da kuma yaronsa, Yan kwana biyun nan duk ya kauracewa mutane, bayason zama cikin mutane yafison zama shikadai, Yauma kamar kullum yana zaune ciki dakinsa yayi jugum yana tunani ya game hannayensa akan kirkijinsa yana kallon saman dakin, shima bashida labarin aurensa da rumaisa, Mai martaba da ummansa suka turo kofar dakin suka shigo, suna murmushi, Mubarak yabisu da kallo har suka karaso kusa dashi suka zauna, Mai martaba yadafashi yana kallonsa yace "Mubarak komai daya faru dakai mukaddarine daga Allah, mutum bai isa ya gujewa kaddarar saba, yakamata ace kayi imani da kaddara, anason kowanne musulmi yayi imani da kaddara ta alkhairi ce kota shairi, karfa kakasacin jarabawar da Allah yake maka" Hawaye suka soma sauka kan kumatun Mubarak, zaiyi magana kuka yakubuce masa yasoke kansa cikin kirjin mai martaba yana kuka yace "kashe sufa akayi, kuma KISAN GILLA, kisan rashin imani, mesukayi masa, meyarona yamasa, yaro karami dan shekara daya, haba wannan rashin imanin yayi yawa ..." yakarasa maganar yana kuka, Mai martaba yarika shafar Bayansa a hankali, sannan yasauke nunfashi yace "kayi hakuri komai mai wucewa ne, kadaina kuka" Umma tayi ajiyar zuciya sannan tace "kadaina kukan nan mana Mubarak, mamaci adu'a yakeso ba kukaba" Sai lokacin aka samu yadan sassauta kukansa yafitar dakansa daga cikin kirjin mai martaba yashare hawayesa sannan yace " insha Allah umma daga yau nadaina kukan nan zanci gaba da rayuwa kamar yadda kowa yakeyi" Murmushi mai martaba yayi "haba kokaifa, ai hakan yafi" Suduka sukayi murmushi, sannan mai martaba yayi gyaran murya kafin yace " amm daman munzone musanar dakai, cewa yakamata kaje Abuja kazo da matarka, domun azo nan asha Biki" Gaban Mubarak yafadi cike da mamaki yake cewa "mata kuma abba yaushe akayi auren banace afasaba, nifa bana sonta" Umma tayi saurin cewa "to mudai ko baka sonta mun riga mun daura muku aure saidai kayi hkr, domin mu bazamu zamo butuluba, a yadda naji labari, yarinyar nan tayi maka taimako sosai a rayuwarka" Mubarak yafara gunguni, mai martaba yace "katashi kaje kayi wanka, kafin kafito zansa ashirya maka motoci, kaje kazo da matarka" Amma abba, nifa bana sont..." mai martaba yadaga masa hannu yadakatar dashi dacewa "indai kanason farin cikinmu, to katashi katafi, ta wannan hanyarne kadai zamu sakawa yarinyar nan aka abinda tamana akanka" yana gama maganar yamike yanufi hanyar fita, umma ta mara masa baya, atare suka fita, sukabar Mubarak zaune akan gado zuciyarsa cike da sake2, Har suka fita Mubarak kallon kofar yake, bayan sun fita yaja tsaki, sannan yatashi akasale "wannan wane irin AUREN BAZATA ne, aure babu ko soyayya" yafada yana kokarin shiga toilet yayi wanka, Bayan yafito yazo bakin mirrio yashafa mai, sannan yaje yadauko wasu hadandin kayan sarauta yasaka, bakaramin kyau yayiba, yafito yarimansa sak, yazo bakin mirror yana kallon kansan, sai kuma yayi murmushi, Wani irin farin ciki yakeje a yanzu bayan fitowarsa daga toilet wanda shikansa baisan da zuwansa ba, Tun a lokacin daya samu labarin matarsa da yaronsa sun mutu, baikara tsintar kansa cikin farin cikiba kamarna yanzu ba, Saida yafeshe jikinsa kaf da turare sannan yafita, koda yakarasa harabar gidan, Mai martaba yasa anjera masa motoci a kalla zasukai guda biyar, Yana zuwa yashiga mota ta tsakiya nan suka fita daga hatabar gidan suka hau hanya, mai martaba yayi musu fatan Allah yakai lafiya yadawo dasu lfy, Suna barin gidan, mai martaba yakira abban Rumaisa yasanar dashi cewa gasu Mubarak nan kanhanya, Abba rumaisa yayi farin ciki sosai, bayan sun katse wayar Sannan yaje yasanar da umma da haj luba, nan fa suka shiga gyaran gidan, rumaisa tana dakinta, cikin bakin ciki batasan irin wainar da ake toyawaba, Sai bayan sungama shirya gidan tsaf sannan umma taje dakin rumaisa, a kudundune tasameta gefen gado, kamar shege a gurin rabon gado, Umma tazauna kusa da ita, tafara yimata 'yan nasihohi akan tadauki kaddara akan abinda yafaru da ita, Nasihohin sun ratsa jikinta sosai, daga kashe dai umma tace "yanzu dai kitashi kije kiyi wanka domin zamuyi baki a gidan nan, kuma dan Allah karki nuna masu alamar kina cikin damuwa, kisaka fuskarki a murmushi kinji" Murmushi karfin hali Rumaisa tayi " tohm umma insha Allah zanyi kokarin yin hakan" Umma ta mike tana murmushi "tohm shikenan idan kin gama wanka kikirani nazo zabama miki irin kalar tufafin da zaki saka" Rumaisa tace " tohm" tana gama fada, umma tajuya tana kokarin barin dakin, Rumaisa ta kwalla mata kira , ta juyo , Rumaisa tace "umma halam bakin waye zasuzo" takarasa maganar tana Murmushi, itama dai fada mata din nan da akayi baki na nan zuwa, harta soma jin farin ciki, wanda batasan meye dalilin yinsaba, Umma tayi murmushi tace "bakin abban kine " tana gama fada ta fice tabar dakina, Rumaisa tatabe baki "bakin abba, daga ina kuma? " itaka kadai take magana, Murmushi kawai tayi sannan tafada toilet, Wanka tayi sosai domin tana wankan tanajin nishadi, kamar bata cikin wata damuwa, karasa wannan tafito, Bayan tafito harta zauna tana shirin fara mekup tatuna da umma tace takirata idan tafito, Tashi tayi ta janyo hijab tasaka, tana kokarin bude kofar, a daidai lokacin umma taturo kofar tashigo, tayi turus tana kallonta tana sosa kanta " amm daman yanzu nake batun zuwa kiranki saikuma gashi kinzu" Umma tayi murnushi tace "gani nayi baki fitoba shine nace bari ninazo, kin fitone?" Rumaisa tace "eh nafito" "Tohm jmuje" Bakin mirrio suka fara zuwa umma ta taimaka mata tayi kwalliya mai kyau, Sannan umma taje tadauko mata wasu sabanbin kaya daga cikin kayan aurenta da kabir, rumaisa ta karba tasaka bakaramin kyau tayiba, sai faman murmushi take, Sai da umma ta tabbatar data shirya rumaisa tsaf sannan tabar dakin, tabarta a tsaye tana tubanin wai suwaye zasuzo haka, dahar za'ace sai umma ta shiryata, saikace wata small girl... https://free.facebook.com/Abdul-Mr-Smiles-Novels-220980808286357/?v=feed&_rdr [10/20, 10:54 PM] +234 905 395 7618 : _Title:-_ *MAJNOON* _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES* 119 and 120 Via *OHW* _A love story_ Da yamma ana batun suka sauka garin abuja, Basu dire ko inaba sai kofar gidan su rumaisa, mai gadi ya wangale musu kofa, suka fara jiro motocinsu a cikin gidan, Abba yafito cike da fa'a yatar besu, yakarasa dasu dakin baki, Rumaisa tana zaune a cikin dakinta sai kukan motaci takeji suna direwa a harabar gidansu, taso tatashi ta leka ta Window domin tagani amma sai kuma kawai tafasa, Tana zaune umma tashigo fuskarta dauke da fara'a, ganin umma tashigo yasa ta mike tana fadan "umma sunzo koh" Umma tayi saurin cewa "eh sunzo, kaje dakin baki, sunacen saiku gaisa" Tohm " kawai tacewa umma kanta soke akasa tafita tabar umma tsaye acikin dakin, tanufi dakin baki, Cike da faduwa gaba tatura kofar dakin baki, wani irin kamshi ya doki hancinta, dasauri ta sauke nunfashi, sannan ta taka kafarta a cikin dakin, tare dayin sallama, Yana zaune kan kujera yayi wani irin zama kasaita, yajuyo sallamarta, a hankali ya dube inda take tare da karba sallamar, a lokacin hartashigo dakin kanta a kasa tayi tsaye guri daya, takasa zuwa ko ina, Yabita da kallo zuciyarsa sai duka takeyi da karfi, a hankali take jiyo sautin Muryar sa yana fadan "shigo mana" tunda tajiyo sautin muryar takejin gabanta na faduwa, Taso ta dago kanta domin ta gazgata sautin da kunnuwanta kejiyo mata, amma kuma saita tsinci kanta da kasa yin hakan, Bata dago kantaba a haka take tafiya kanta a kasa harta karasa bakin kujera tazauna, Yanayin yadda tazauna yabashi dariya, yayi d'an murmushi kadan yana kallonta yace "amm fuskar taki tsadane da ita dahar bakyason d'agota mutane sugani" Gaban rumaisa yakara faduwa itadai jitakeyi kamar tasan mai muryar, kuma akace mata baki sunzo, ita da taji saukar ambaliyan motoci a harabar gidansu, ai yakamata taga mutane a dakin akalla sukai su goma amma saita rika jin muryar mutum daya, kodai sauran bazasuyi magana bane saita dago kanta, duk a zuci take wannan zancen, A hankali take dago kanta sukayi edo hudu da majnoon dinta, saida taja da baya saboda razana, ayya kuwa edanuwanta gaskiya suke nuna mata cewa Majnoon ne a kusa da ita, Suka kafe juna da edo suna kallon juna cike da jindadi da nishadi, Sun jima a haka kafin bakinta yasoma rawa tanason ta furta wani abu, Mubarak yadaga mata hannu "basai kinyi maganaba ninidai mubarak, ba mafarki kikeba, domin nasan zuciyarki zata saka miki hakan" Murmushi rumaisa tayi jitakeyi kamar ta burma ihu, dariyar haure daya tayi tana kallonsa tace "mekazoyi gidanmu" Nunfashi Mubarak yasauke yana kallonta yace "ummm nazone natafi da matata" Rumaisa tadan zare edo cike da mamaki tace "wacece kuma matar taka, kuka ina take" Sai da yayi murmushi Sannan yace "a yanzu haka
Chapter 25 · 0% Book details