Sashe 11
Majnoon Part 1 Complete Hausa Novelp · about 8 min read
rumaisa, tun agurin ta sanar da ita cewa, idan tagama salla tayi wanka tazo tasameta, domin motar safe zasubi suwuce abuja, Haka kuwa akayi bayan rumaisa tayi salla sannan tayi wanka ta shiya, tazo tasami hajja luba zaune a harabar gidan itama ta shirya, karin kumallo kawai sukayi, suka wuce tasha, basu dad'e sosai ba a tashar suka sami mota nan suka hau hanyar zuwa abuja, ***** ***** ****** A *Abuja* Fahad yana kwance kan gadon asibiti edonsa suka fara motsawa, sunana kokarin budewa, a hankali har edon suka yashe, kallon dakin yakeyi gefe da gefe, firgir ya mike zaune, yana mamakin wannan dakin inane, juyowar dazaiyi suka hada edo da ummansa, cike da farin ciki take kallonsa, Shikuwa mamaki yacikashi, abubuwan da suka faru jiya yarika tunawa, muryarsa na rawa yace " ina rumaisa" Abba yana tsaye ya kura masa edo cike da rashin fahimta, maganarsa, wace rumaisa kuma? Abba ke tambayar kansa, umma takaraso gurinsa ta rike hannunsa tace "wacece kuma rumaisa" Abba shima yakaraso gurin yana cewa "wacece kuma Rumaisa son" duk mamaki yacika su, Fahad ya dafe kansa dake masa zafi yana kokarin tashi tsaye abba ya zaunar dashi, tuni hawaye suka cinciko masa edo, nan yasoma kuka yana fadan "kubarni natafi gurinta abba, wlh banzan samu salamar zuci ba matukar banga Rumaisa ba, itace farin cikina, dan Allah kubarni natafi" Umma ta dube abba, abba ya dube umma sudukansa mamaki yacikasu, wace irin rumaisa ce wannan data rikita musu yaronsu, Ganin basuce dashi komaiba yasa Fahad yakara fashe da kuka yana cewa " nacuce kaina, na cuce zuciyata, ya dube abba sannan yaci gaba dacewa "abba daga yau nadaina shan giya, wlh duk abinda rumaisa bataso zan daina, zan dawo mutumen kirki sabida ita, dan Allah abba kanemamin aurenta, idan bansamu auren rumaisa ba wlh bazan iya rayuwaba, dan Allah abba kanemamun auren rumaisa..." yakarasa maganar yana kuka sosai duk ya fita hayyacinsa, Umma duk ta rikice, tunda take bata taba ganin kukan fahad ba akan macce sai yau, Abba kuwa tuni edonsa sunyi ja sosai, yana tunanin wannan wacece ita kuma 'yar gida waye, tabbas zai nemota kuma zai nemawa yaronsa neman aurenta koda kuwa dukiyarsa zata kare kaf akan wannan matsalar, Abban fahad ya sunkuwo yadafa gadon da Fahad yake zaune yana kallon fahad edo cikin edo yace "waye mahaifinta kuma a ina take" Fahad ya yashare hawayesa yana cewa "A nan garin take, bansan sunan mahaifinta ba amma nasan unguwarsu da kuma gidansu" Abba yace "toh shikenan mujira zuwa gobe idan kakara samun sauki, zamuji musami iyayen nata" Umma tana zaune tana kallonsu sai a lokacin tasamu damar cewa "bazamu jiraba har zuwa gobe, domin bazan iya jurar ganin yarona cikin damuwaba, sannan kuma banason yarona yayi asa'rar wannan yarinyar muje gidan nasu a yau kuma a yanzu " Abban fahad yayi ajiyar zuciya sannan yace "toh shikenan muje " Nan suka shiga hada kayansu, bayansun gama hada kayan, sukaje karbar takardar sallama a tare suduka ukku, Bayan sun karba suka fita motar suka shiga suka, abban fahad ne yaja motar har sun fara tafiya abba yace "mezai hana mutsaya mukarya kafin mukarasa, domin kunsan ni bana iya zama yunwa yanzun nan ulcer ta zata iya tashi" Umma tace "hakanefa, muje mukarya kafin muwuce" toh kawai abba yace suka wuce wata katuwar restaurant, Shidai Fahad ko uffan baice dasuba, shidai burinsa kawai yaga abar sonsa wato rumaisa, Nan aka ordo musu abinci kala2 suka fara ci... (ganin zasu batamin lokaci gurin kallon cin abincinsy yasa, nabar gurin, nace idan sun gama cin abinci nasu na 'yan gayu, ma hadu a gidan su rumaisa, nan na fece nakarasa tashar mota) ***** ****** ****** *TASHAR MOTA* _A Abuja_ A tasha mai motar ya jibgesu, bayan sun fito suka tare mai napep suka shiga, yakaisu har unguwar, suka biyasa sannan suka shiga cikin gidan, Abban rumaisa yana zaune a falo, lamarin duniya duk ya ishesa, duk ya kara ramewa, Sallama yajiyo a waje ana kokarin shigowa falon, ya kura kofar falon edo yana jiran yaga wazai shigo, Ummansa yagani saida gabansa yafadi, ya mike tsaye cike da mamaki, a zuci yace "kardai ace tasamu labarin cewa rumaisa tabata" Ganin yanayin fuskarta a murtuke, yaji tsoro sosai domin yana matukar tsoron ummansa, Abinda yakara firgitashi saida yaja da baya jiyake kamar mafarki yake, ganin rumaisa da yayi a bayan hajiyarsa, Hannusa yadaga yana nuna rumaisa cike da mamaki bakinsa ke furta "RUMAISA!!" Hajja luba tayi saurin karbe maganar, cike da masifa take fadan "eh rumaisa ce wadda kukayi yunkurin kashewa, to ta Allah bata kuba, ina muguwar matar nan taka take, toga rumaisa tadawo gidan ubanta saiki mutu, kina inane " hajja luba tashiga kiran sunan umma, Abban rumaisa wadda tuni murmushi ya mamaye fuskarsa, cike da farin ciki da jindadi yaga 'yarsa, Hajja luba taji shiru, bataji motsin ummaba , ta dube abba tace "ina matarka take" Abba ya sauke hannunsa ya dube hajja luba yace "barka da zuwa Hajiya, ya hanya " yafada cike dajin kunya, Hajja luba ta dalla masa harara "ni ba wannan na tambayeka ina matarka domin ni danta nazo garin nan" Abba yace "hajiya kiraso kuzauna mana sai muyi magana, ya dube rumaisa yana murmushi yace "rumaisa ta zoki zauna kinji" Rumaisa ta tsuke fuska, hajja luba taja hannunta suka karasa bakin kujara suka zauna Bayan sun zauna abba yayi dariya yace "bari nakawo muku ruwa" da sauri ya mike yaje yadauko ruwa a firij yakawo musu, rumaisa sai kallon abbanta take taga duk ya rame, saida yabata tausayi, kallon gidan take duk taga ya canza mata komai na gidan a hisgitse, Abban rumaisa shima ita yake kallo duk ta koma masa bakuwa, Hajja luba ta katse musu tunina da cewa " wai ba magana nake maka ba nace ina matarka, ko kafita yawon iskancin nata ne" Yanayin fuskar abba ya chanza zuwa bacin rai sannan yace "tana police station" saida rumaisa ta furzar da ruwan dake bakinta saboda razana akan maganar da abbanta yafada, Cike da mamaki hajja luba tace "meta keyi a police station" Abba yace "tun lokacin da rumaisa ta bata nasa aka kamata domin ni nayi zaton cewa akwai hannunta acikin wannan matsalar" Rumaisa tuni hawaye suka sauko kan kumatunta cike take da tausayin umma duk da ba itace ta haifetaba amma tanajin sonta har cikin zuciyarta, rumaisa ta marairaice fuska ta dube abba tace "Dan Allah abba kaje kazo da ita, wlh babu hannunta a ciki" sai a lokacin tayi magana, Abba yadube yaga yata hawaye tausayi ta bashi, yace "toh shikenan" da sauri ya mike, yanufi hanyar fita, Hajja luba tace "ina kuma zakaje" Abba yajuyo yace " zanje station din ne nazo da ita tunda rumaisa ta bukaci ganinta" Bai jira hajja luba tasake maganaba yafita yabar gidan, *Bayan minti 30* Falo ya cika umma da Abba Hajja luba da kuma rumaisa, duk suna zazzaune, sunyu jugum2, umma dukta galabaita tayi baki, ta wahala sosai, Abba yana zaune yana kallon hajja luba, Umma tatashi tazo gurin rumaisa kwalla duk sun cika mata edo tace " Dan Allahki rumaisa kiyafemin, Alhakinkine ke fita akaina, nasan dacewa na cuceki, na hanaki jindadi a gidan nan, amma wlh yanzu nayi nadama sosai, dan Allah kiyafemin" Kuka rumaisa takeyi ta d'ago umma ta rungumeta tana fadan " nayafe miki ummata, wlh nayafe mike har cikin zuciyata" Umma tana kuka tace " nagode rumaisa" suka kara kakkame juna, suna kuka, Duk haushi umma take bawa hajja luba, Hajja luba taja tsaki sannan tayi gyaran murya, domin ita har yanzu bata sauka daga dokin zuciyar data hauba, tace " ni ba ruwan da kukanki, kukan munafinci, mtsw, Hajja luba ta juya gurin abban rumaisa tace " kai kuma bara kaji, maganar auren dole dazakayiwa rumaisa na janye wannan maganar, kabawa rumaisa wadda takeso, idan kuwa ba haka wlh nida kaine" Cike da mamaki abban rumaisa yake kallon Hajja luba, wai kodai batasan wadda rumaisa takeso bane, mahaukacine fa, taya zai aurar da diyarsa ga mahaukaci, Cikin sanyin jiki abba yace "hajiya waddafa takeso dinnan mahau..." bai karasa maganarba sukaji an turo kofar falon aka shigo tare dayin sallama, Fahad ne shida da iyayensa... Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's Website:_www.abduljega.blogspot.com [10/20, 10:45 PM] +234 905 395 7618 : _Title:-_ *MAJNOON* _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES* 65 and 66 Via *OHW* _A love story_ Falon gabaki daya kallon kowa su yake kallo, abban rumaisa, da umma, hajja luba da basu san suba su na mamakin suwaye su, Rumaisa kuwa tuni jikinta yadau rawa, muryarta na rawa ta dube fahad cike da masifa tace "mekazo yi a gidanmu, meya kawoka" Abban rumaisa ya cika da mamaki ya dubi rumaisa yace "suwaye wadan nan kuma" Rumaisa ta fashe da kuka tanajin yadda zata gayawa abbanta cewa shine wadda yasaceta, sai tayi shiru kawai tana kallonsu taji dame sukazo, Tun shigowarsu fahad yake kallon Rumaisa sannan suka karaso cikin falon, suka gaisa da juna, Abban fahad yace "ni sunana Alhaji sani babba" abban rumaisa yayi saurin katsesa da cewa "ok nagane, Allah sarki, ban taba ganin ganinkaba amma inajin labarin sosai a garin nan" abban fahad yana murshi yace "eh hakane kasan ni bamai yawan zama kasar nan bane" abban rumaisa yace "eh hakane, lafiya kuwa " yafada yana kallon abban fahad, Abban fahad yanisa sannan yace "nine mahaifin fahad, wato wannan yaron" yajuya yana kokarin nunawa abban rumaisa fahad, sai yaga wayam babu fahad a gurin, Koda suka juya, a lokacin har Fahad yakarasa gurin rumaisa edonsa sunyi ja sosai, ya durkusa a gabanta, Falon gabaki daya saida kowa yayi mamaki, Ya dago kansa ya kalleta a lokacin har hawaye sun fara fita a cikin edonsa, murya a sanyaye yace "kada zuciyarsa tayi zargin cewa nazone domin na cuta miki a a, hakika rumaisa bazan taba mantawa dakeba a tarahin rayuwata saboda irin gudun muwar da kika bani wacca ita narasa tun a baya da rayuwata bata kasance a yadda kika tsinceniba, banada alkhairin dazan iya saka miki dashi sai dai ina rokonki Alfarmar abu guda daya agurinki" fahad yadanyi shiru yana kokarin share hawayensa, folon gabaki daya shi ake sauraro, sannan yace "Dan Allah rumaisa ki yarda ki aureni, ta wannan hanyarce kadai zan iya saka miki akan alkhairin da kikaimun"