Sashe 26
Majnoon Part 1 Complete Hausa Novelp · about 7 min read
ina tare da matata, wacca tadawomin da rayuwata daidai kamar a baya, natashi daga Majnoon nakoma Mubarak" Dariya maganar tabata, tare da mamakin ta ina yasan dacewa shi Majnoon ne, Takara kafe edonta akan nashi tana murmushi tace "wacece?" Shima yayi murmushi yace " RUMAISAN MUBARAK" Gabanta yasake yafaduwa tana cike da mamakin yaushe aka daura mata aure da Mubarak, bayan tasan dacewa ana daf da fara daurin musu aura komai ya yatarwatse, Dakatar mata da tunaninta yayi daceewa "karkiyi mamaki, domin nasan dacewa yanzu haka shikikeyi akan ya akayi aka dauramun aure dashi, nima a bazata abun yazomin, bayan nakoma gida abinda yafaru shine mummunan labari yasamnin akan cewa kanine ya kashemun iyali matata da yarona KISAN GILLA, wannan shine dalili dayasa mai martaba yasa aka daura aurena dake batare da saninaba, acewarsa ta wannan hanyarce kadai zamu saka miki akan taimakon dakikayi akaina, lokacin da mai martaba yasanar dani cewa andaura min aure dake, banjidadiba, amma kafin nazo nan sainaji kamar kece silar dawowa da farin cikina, kuma danazo sainaji kwata-kwata bana kunyarki, jinakeyi a jikina kamar munyi shekara goma atare, lallai wannan ba komai bane illa alakar zukata biyu, ma'ana zuciyata da taki, rumaisa yanzu nadawo gareki.." Hawaye suka sauko kan kumatunta wanda itama batasan dalilin zuwan suba, shin na tausayin labarin Mubarak ne kona farin ciki ne, hawayenta tashare sannan tace "Allah yajikansu da rahama" Murmishi Mubarak yayi sannan yace "ameen,yana murmushi yace "yanzu saurake ki haifomin wani yaron" Kunya rumaisa taji ta rufe fuskarta tana murmushi, tasowa yayi daga inda yazo kusa da ita, ya kura mata edo wani irin sonta nakara shiga zuciyarsa, yarasa dalili dayasa sonta yashiga zuciyarsa lokaci daya, kafin yazo abuja babu sonta ko kadan a cikin zuciyarsa amma yanzu sonta gabaki daya ya mamaye zuciyarsa, nan take ta meye masa gurbin margayiya matarsa, Cike da fargaba yariko hannunta, saida taji jikinta yadau wata irin sock, da karfi tasauke nunfashi tare da lumshe edo, A hankali yake murza hannu, yana murmushi cikin wata sanyanyiyar murya yace "I LOVE YOU RUMAISA" yakarasa maganar yana kallonta, Wani irin farin ciki takeji har cikin zuciyarta, da karfi ta kanne edonta, saboda wata irin kunyarsa dataji, da sauri ta mike ta janye hannunta daga nashi, tana murmushi ta kauda edonta daga kallonsa cikin b'arin murya tasoma furta "mee..t.." takasa karasa maganar saboda wata irin kunya takeji, da gudu tafita tabar dakin, Prince Mubarak yayi dariya yana kara jin sonta a cikin zuciyarsa, Tana fita ta zarce dakin umma, da gudu tashigo dakin, umma tana zaune akan sallaya taga sallar laa'sar, tafado jikinta cike da farinciki, umma tace "lalala rumaisa karyani zakiyi, wannan irin fadowar haka" Rumaisa tadago kai ta harari umma cikin wasa sannan tace "wato umma shine kukayimun AUREN BAZATA koh, yaushene akayi auren daba a sanar daniba" Umma tayi murmushi tace "karkiga laifina, laifin abban kine shiyace kar'a sanar dake, jiya bayan sallar isha aka daura muku aure a masallaci" Farin ciki kam a gurin rumaisa adaina magana, domin bazai iya misaltuwaba, yau dinnan jinta takeyi kamar ba itaba, Umma tadago daga jikinta tace "kitashi kije kishirya masa ruwan wanka, idan yafito kikaisa dinner yaci abinci koh" Rumaisa ta zare edo "umma nikuma, nifa kunyarsa nake, shibazai iya hadawa kansa ruwan bane" Umma tabe baki "au sai yanzu kika fara kunyasa bayan yazama mijinki, adacen ai bakya kunyarsa, nidan Allah tashi kije banason maganar banza" Rumaisa ta mike tana dariya tafice tabar dakin, Dakin baki takoma, tana shiga tasame zaune kan kujera ya tayar da kansa sama yana tunani, sallamar taace ta katse masa tunani, ya juyo yana kallonta, murmushi ya mata, kanta a sunkuye takaraso gurin, cike dajin kunya tace "zakayi wankane nashirya maka ruwan wanka" Murmushi yayi sannan yace "eh zanyi mana, amma tare dake zamuyi koh?" Dasauri tace "nikuma" tare da nuna kanta, Kai ya kida mata " eh mana kedin, keba matata bace" Cikin rawar murya Tace "to..to..to.." yana murmushi ya katseta dacewa "kwantar da hankali, kije kawai nizanyi wanka dakaina, kije ki huta saina fito" Kai kawai ta girgiza masa sannan tafice tabar dakin, Yana kallonta harta fita sannan yayi murmushi, ya mike yafada toilet, wanka yayi sosai sannan yafito, yasake saka wasu sabanbin kaya, sannan yafita, A falo sukasha fira sosai shida su umma da haj luba, har aka kira sallar magriba, sannan ya mike yaje yayi alwala yatafi masallaci, bai dawoba saida aka gama isha, Koda yashigo gidan, anjera masa abinci kala2 akan diner table, rumaisa ce tamasa jagora har suka karasa bakin diner, suka zaune , bayan sunzauna tayi serve dinsa, Yana cin abincin suna fira duk da ba wata mata sosai take masaba, tarasa dalilin dayasa yanzu yake mata kwarjini, Hakadai yaci abinci yayi nak, Sannan sukayi saida safe, yatashi ya wuce sashen baki, ita kuwa ta wuce dakin umma.. Tana shiga tazauna gefen gadon da umma take kwance, ta sauke nunfashi tana kallon umma, Umma tace "a ina kikabar mijinnaki" Rumaisa tayi murmushi tace "umm yatafi dakinsa wai bacci yakeji" Umma ta harareta cikin wasa "to shine bazaki tayashi bacci ba, kefa nalura dake Allah yanzu kinaso kizamo wata huhulahu, idan kikayi wasa da mijiki wata zata kwace mikishi kina zaune kinyi sakaci, shifa namiji kulawa yakeso da tarairaiya tamkar kwai, kikula da mijinki fiye da yadda zaki kula da kanki, kibashi farin ciki fiye da yadda zaki bawa kanki, ki rike abinki hannu bibbiyu, karkiyi wasa dashi" Jikin rumaisa yayi sanyi, tare dajin wani irin kishi, akan umma tace wata zata iya kwace mata shi, murya a sanyaye tace "yanzu umma yazanyi" Murmushi umma tayi sannan ta dafata tace "kije kitayashi bacci, karkisa komai a ranki, kinji Rumaisa" Girgiza kai tayi jiki a sanyaye "toh umma" sannan ta mike tafita, Kafin taje dakin saida ta wuce dakinta ta sanya katon hijab, sannan takarasa dakinsa, Yana kwance akan gado yana wasa da wayarsa, taturo kofar dakin tashigo, suna hada edo yasaka mata murmushi, dukar da kanta tayi harta karaso kusa da gadon tazauna a bakin gadon, Uffan baice da itaba, yaci gaba da dannar wayarsa, shima miskilin karshene, Ta jima a zaune batayimai maganaba shima baimataba, Dadai taga bayada imanin yimata magana, sannan ta sauke nunfashi cike da kunya tace "zowa nayi natayaka bacci" Murmushi yayi sannan yace "uhim ga gurinan ki kwanta nibanajin bacci yanzu" Bata kara furta uffanba, ta juya tagefe daya ta kwanta, batare data cire hijab dintaba, a hakan ta kudunne cen karshen gado ta juya masa baya, Yanayin kwanciyarta yabashi dariya, yayi murmushi tare da girgiza kai, Yajima yana game din kafin ya ajiye wayarsa sannan yatashi yacire rigarsa, yakoma dagashi sai singlet da dogon wando rigar daya cire, Sannan yadawo kan gadon yakwanta, tanajin kwanciwarsa ta kanne edonta, duk jikinta yayi sanyi, Bayan ya kwanta yakurawa bayanta edo, sannan ya ja jikinsa yakarasa kusa da ita, hannunsa yasa ya sarkafota ta baya, Yajuyo da fuskarta daidai gurinsa, yasa hannu yana shafa fuskar, Nan take jikinta yadau kyarma, ya lura da irin yadda jikinta yake rawa, hakan ya tabbatar masa dacewa batayi bacci ba, murmushi yasaka sannan yasauke muryarsa yace "kunyata kikeji ne, dabazaki bude edonba" Ta girgiza masa kai, Yayi murmushi yace "toh shikenan, kisha kwanciyarki lafiya saida safe" yana gama fada ya manna mata kiss a goshi, sannan ya juya ya janyo blanket ya rufe jikinsa, Tajima a yadda yabarta, bata motsaba domin takasa yin komai duk jikinta yayi sanyi, Saida ta dainajin motsinsa sannan ta bude edonta, koda tajuya taganshi har yayi bacci, A sannu tatashi ta kura masa edo tana kallonsa, sai kara shige masa rai yake, taja jikinta takarasa kusa dashi, jikinta narawa ta kwanta akan kirjinsa, saida tayi wani sauke nunfashi, Ashe shima ba bacci yakeba, a hankali yake sauke hannayensa akan bayanta, yakara manneta kam a jikinsa, A hakadai har sukayi bacci, ko wannensu zuciyarsa cike da kaunar juna.... https://free.facebook.com/Abdul-Mr-Smiles-Novels-220980808286357/?v=feed&_rdr [10/20, 10:54 PM] +234 905 395 7618 : _Title:-_ *MAJNOON* _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES* 121 and 122 Via *OHW* _A love story_ _Washe gari_ Tu da sassafe aka shiga hada musu kayansu, komai anshirya musu na zuwa kogi, Karyawa kawai sukayi, sannan suka shiga motaci, rumaisa da Mubarak, a mota daya, abban rumaisa da umma a mota daya, haj luba kuwa motarta ita kadai, sai sauran bodyguard din suka shiga sauran motocin Haka dai suka kwashe gidan gabaki daya suka wuce kogi, Daga baya daddy yakira abba yasanar dashi cewa shima zaizo amma sai zuwa gobe a motarsa zaizo, yau dinma yanada aiki daya tsayar dashine, abba yamasa fatan Allah yakawosa lafiya,