← Book details Majnoon Part 1 Complete Hausa Novelp Local reading mode
READING PART 15 OF 29

Sashe 15

Majnoon Part 1 Complete Hausa Novelp · about 8 min read

yanzu nake kudurin da nakammala shirin nan nazo nasameki, tund'a nashigo naji gidan yayi tsit, kamar bakowa" Momy tayi murmushi tace "eh ina daki, ai naji shigowar motarka, tashi kawai banba, yanzun nanma abban kane yafito dani, yace nazo nafadama yana nemanka" Gaban faisal yafadi, cike da mamaki ya dube momy yace "nemana kuma momy, Allah yasa dai lafiya" Momy tace "koma dai meye zakaji, karkayi jinkiri yana dakinsa yana jiranka" tana gama fada tajuya tabar dakin, Faisal yabi kofar da kallo harta fice, yana yin dayaga momy a ciki bai gamsu dashiba, yanaji a jikinsa kamar akwai matsala, furzar da isaka yayi a bakinsa, yaci gaba da shirinsa, tunani kala2 yarika zo masa, Yakasa samun sukuni, ya kosa yaji me daddy zaice masa, Kasa kammala shirin yayi, ya tashi ya nufi dakin daddy, Yana karasawa ya tura kofar dakin yashiga, zaune ya sami daddy saman wata 'yar karamar kujera dake d'akin, Momy kuwa tana zaune bakin gado, ko wannen su yayi shiru, fuska ba annunuri, Yana shigowa dakin yaji gabansa yafadi, ya sunkuyar dakai kamar marar gaskiya, yakarasa kusa ga daddy ya durkusa sannan yace "daddy gani" cikin ladabi da biyayya Daddy yayi ajiyar zuciya yana duban faisal "faisal kana son farin cikina kuwa" Cike da mamaki Faisal yayi saurin dago kansa ya dube daddy yace "sosai makuwa daddy, fatana akoda yaushe naganka cikin farin ciki da kwanciyar hankali, sai kuma yayi shiru yana kallon daddy Daddy yakara cewa "kana tausayin 'ya macce kuwa" Faisal duk ya rikice da tambayoyin da daddy kemasa, kuma yarasa dalili yin tambayoyin, girgiza kansa yayi "eh daddy inajin tausayinsu sosaima" Daddy yasauke nunfashi yana batun zaiyi magana, Momy tayi saurin katsesa dacewa "nifa banga amfanin tsayawa yimasa wad'an nan tambayoyin ba, kawai kafito fili kafada masa abinda yasa kakirashi" Daddy yayi shiru, yana jin nauhin yadda zai fadawa faisal cewa yafita harkar rumaisa, Jin yayi shiri yasa momy ta dube faisal ta kira sunansa, Faisal ya juyo gefen momy duk ya tsorata, shima dai yakosa yaji mezasu fada masa, Momy tace "tun bakiyi wayoba kakejin labarin matan da suka illata mazajensu akan auren dole, kayi tunani da nazari bisa akidarmu ta addinin musulunci, kazamo mai tausayi a zuciyarka, faisal! Takara kiran sunanshi yakara dago kansa edonsa sunyi ja sosai, sannna taci gaba dacewa "ba so bane mutum ya tilas tawa wanda baya sonsa akan dole saiya sosa, taya zakaji abin idanhar akace yau gashi za'a yiwa kanwarka aure dole, za'a aura mata wadda bataso, bata muradin gani, a lokacin tasauke nunfashi sannna tace "faisal! Takara kiran sunansa a karo na ukku, ykara dago kansa a lokacin harya soma hawaye, domin ya fahimci inda maganar momy ta dosa, momy tace "gabar auren dole bata taba gushewa a cikin zuciyar wasu matan, kalilan ne a cikinsu zasu iya manta dashi, duk wacca kuwa kaga tamanta to katabbatar koda akayi mata aure batada wadda takeso, amma muddi tanada wadda takeso akayi kokarin rabata dashi toh akoda yaushe bazata taba mantawa dashiba, duk wani dadi daza kabata, duk wata kula dazaka bata, duk wani so dazaka nuna mata, hakan bazaisa ta sauke akalartaba naganin ka cuceta, mazaje da dama sun fuskanci rashin zaman lafiya a gidajensu sakamakon auren matayen da basa sonsu, faisal kanasone kakasance daya daga cikin wad'an nan mazajen..." tana karasa maganar da tambaya tana duban faisal Hawaye sosai faisal keyi duk ya fahimci maganganun momy, kuma jikinsa duk yayi sanyi, amma shikansa yarasa ta yadda zaiyi ya manta da maganar rumaisa, taya za'a yadaina sonta, Hawayensa yashare yana sharbar majina yad'ago kansa ya dube momy sannan ya juya ya dube daddy sannna yace "rumaisa bata sona koh, wannan shine abinda kuka kasa fadamin ?" Daddy yace "kafahimci maganar momynka faisal, rumaisa bata son....." Faisal yadaga masa hannu yakatse masa magana, yadanyi shiru kamar bazaiyi maganaba, dakin yayi tsit nadan wani lokaci, kafin faisal yace "basai kakara maimaita kalmarba, dumin itace kalma mafi girma dana tsani naji anfurta akan soyayyata da rumaisa, nikaina nasan hakan kuma inajin hakan a jikina, tabbas so ya rufemun edo ta yadda bazan iya hango matsalar da zata faru dani nan gaba ba, ba karya mutane suke fad'aba da har sukace so makahone, nazubar da *HAWAYEN MASOYA* bila adadin a kan rumaisa, to amma a yanzu komai yazo karshe indai nine kadai wadda zai iya gushe farin cikin gidan nan to banyiwa kaina adalciba kuma! Kuma bansaka muku da alkhairin da kuka yimunba, nasan dacewa koda na aure rumaisa to tabbas nabar *BAYA DA KURA* domin akoda yaushe zan iya fuskartar barazana daga gareta" yad'anyi shiru, yana kokarin share hawayen sa, Sannan yaci gaba dacewa "daddy indai nine matsalar ku to kusa aranku Matsalar ta kau, daga yau nabar rumaisa koda kuwa ita kadaice macce a duniya bazan aure taba, koda kuwa idan ban aureba sonta zai iya illatani a shirye nake dayin hakannnn...." yakarasa maganar yana kuka, Momy itama hawaye take, kamar zata masa kuka tausayinsa takeji har cikin ranta, a hankali tafara magana bakinta na rawa "ba abinda zai faru dakai faisal, idan kasa natsuwa a zuciyarsa, komai zai wuce zai zamo kamar komai baitaba faruwaba" Faisal ya mike tsaye da kyar duk jikinsa rawa yake, kuka yake marar sauti, har yakai bakin kofar fita sai kuma ya juyo ya dube daddy yace "inaso kamun uzuri naje naga rumaisa koda sau dayane" Daddy jiki ba kwari yace "na amince kaje, yaushe zakaje " Faisal yace "yanzu" Momy tashere hawayenta tace "yanzu kuma kabari zuwa gobe ..." Daddy yayi saurin cewa "a a kibarshi yatafi yanzun, shikedai yasan meyakeji a zuciyarsa," Faisal ya juya yana kokarin bude kofar dakin yafita, daddy yakara kiransa, yajuyo, daddy yace "idan kadawo zan shirya maka tafiya zuwa Kogi (lokoja) kaje cen ka samu hutu zuwa kwana biyu kadawo" Kai kawai faisal ya girgiza masa sannan ya fice yabar dakin, Dakinsa ya nufa ya karasa kammala shirinsa, sannna yadauki keys na motarsa ya nufi asibiti..... Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's Website:_www.abduljega.blogspot.com [10/20, 10:47 PM] +234 905 395 7618 : _Title:-_ *MAJNOON* _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES* 85 and 86 Via *OHW* _A love story_ Note* ina mai baku hakuri akan rashin jina daba kuyiba kwana biyu,haka yafarune sakamakon muna exam ne amma yanzu mungama, insha Allah yanzu bakuda shamaki da labarin majnoon kullum zaizo muku, nagode da kulawarku, kuma ina baran adu'a agareku Allah yabamu sakamako mai kyau, nagode Fans Muje zuwa... Koda faisal yakarasa asibitin duk yad'an saki jikinsa, a mota yatsaya yakara daidaita kansa sannna ya nufo cikin asibitin, Umma tana zaune a kusa da rumaisa tana mata fira cike da farin ciki, domin a yanzu rumaisa takara samun sauki, Faisal yashigo dakin tare dayin sallama, suka amsa masa a tare, Yakaraso gurin yagaida umma cike da ladabi da biyayya, Umma ta amsa masa cike da fara'a, Rumaisa kuwa tunda suka hada edo dashi sau daya taji gabanta yafadi, ta kauda kanta daga kallonsa, Faisal yayi mata ya jiki, ta amsa masa da cewa naji sauki, Ganin yayi tsaye yaki magana sai mazurai yake da edo yana sosar keyarsa, yasa umma ta fahimci akwai magana a bakinsa daya keson yayi da rumaisa, Hakan yasa tamike tabar bakin tafita waje, Faisal yakaraso kusa da rumaisa yana kallonta suka kara hada edo, da saurin rumaisa ta kauce edonta akan nasa, Ya sauke ajiyar zuciya yace "rumaisa karkiyi tsammanin nazone akan maganar soyayyarmu! Aa, wannan karon nazone akan neman gafararki akan tilastaki danayi akan dole saikin soni, kiyafemun" Rumaisa tayi rau rau da edo duk kwalla tacika mata edo muryarta na rawa tace "nibakamun komaiba, sannan kuma ni bana ganin laifinka domin *DAMA HAKA SO YAKE* bai cika kai kansa inda ake sonsa ba, yafison yaje inda zai sha wahala, tayadda daga baya koda yasamu mai sonsa yarikeshi da daraja, ina mai baka hakuri abisa Rashin karbar soyayyarka dabanyiba, kayi hakuri zuciyatace takasayin hakan " Faisal yasauke nunfashi ya share wasu guntuyen hawaye dake makkale a gefen edonsa "shikenan, Allah yazabawa kowa abinda yafi zama mafi alkhairi agaresa" Ameen " rumaisa ta amsa masa, Sai kuma sukayi shiru, tunani barkatai suka rika zoma faisal, duk yaji bayajin dadi, Zuciyarsa duka takeyi tara2, yanzu shikenan an rabashi da abarsonsa, abar alfaharinsa, kai ina bazai yuyuba ace zai iya rabuwa da rumaisa, to idanma ya rabu da ita wazaiso, shifa ita kadai yafara so, duk a zuci yake wad'an nan maganganun, Da karfi sukaji anturo kofar dakin, hakan yayi sanadiyar fitowarsa a cikin duniyar tunanin daya shiga, Umma ce tashigo dakin cike da fara'a batama tsaya tunanin mesukeyiba, ta takarasa kusa da rumaisa tana murmushi tace "abbanki yace majnoon yafarka, kizo muje idan zaki iya tashi" Da karfi rumaisa ta mike zaune tana dariya, duk farin ciki ya cikata "umma zan iya tashi, harda guduma zan iya, muje " tafada cike da zumudi tana kokarin tashi Umma tayi murmushi sannan tataimaka mata takarasa tashi tsaye, Faisal dake tsaye a gefe duk mamaki yacikashi waye shi wannan majnoon din dahar fadar sunansa zai saika rumaisa dariya da farin ciki haka, kodai shine wanda takeso? Basu kula Faisal ba har suka fita daga cikin dakin suka nufi dakin jinyar majnoon, Faisal ya tsaya turus yana mamaki, zaiso yaga wanda rumaisa takeso, yaga dame yafishi, Kasa hakura yayi dole yabi bayansu, A tare suka shiga dakin umma da rumaisa, sai kuma ga faisal a bayansu, Hajja luba, likita , da kuma abban rumaisa duk suna cikin dakin, Majnoon ya dube mutanen dake zagaye a dakin yana mamakin suyawe su, Edo kawai ya kura musu yabisu da kallo Likita yakarasa kusa dashi yace "ya jikin naka, me kakeji a yanzu" Majnoon ya dube likita yana mamaki, muryarsa na rawa yace "miya samenine " Likita ya sauke ajiyar zuciya, a lokaci yatuna matsalar ciwon mantau da kedamun majnoon, sannna yace "kasamu hatsarine akan titi" Cike da mamaki majnoon ya ke maimaita maganar "nasamu hatsari" ya dube likitan yace "a ina nayi hatsari, kuma a yaushe, suwaye wa dannan" ya nuna su abban rumaisa, Likita ya dube su abban rumaisa yayi murmushi sannan ya juya gurin majnoon yace "wadan nan yan uwan kane" Majnoon yakara maimaita maganar " 'yan uwana kuma?, ni harda yan uwa nake dasu" Likita yace "sosai makuwa " Majnoon duk komai yadaure masa kai a hankali ya dube
Chapter 15 · 0% Book details