← Book details Majnoon Part 1 Complete Hausa Novelp Local reading mode
READING PART 10 OF 29

Sashe 10

Majnoon Part 1 Complete Hausa Novelp · about 8 min read

suka hawo jirgi suka shigo 9ja, Karfe 10:30 na safe jirginsu yasauka a airport dake garin abuja, tun a cikin jirgin mahaifiyar fahad take kuka, abban fahad sai lallashinta yake, da kyardai yasamu ta saurara, Suna saukowa cikin jirgi motoci suka dira a airport din, daman abban fahad yasa a kawo musu moter, nan suka shiga motar suka suka wuce asibiti, Suna karasawa bakin asibitin abban fahad ya dubi asibitin ya tsuke fuska "wht anan aka kawomin yaro" yafada a sanyaye, ransa a bace ya shiga asibitin a wulakance yake kallon mutane, yakarasa dakin da fahad yake, a kwance suka samesa duk ansaka masa bandej a jiki, umman fahad takarasa gurin fahad tana kuka, tarike masa hannu, Abban fahad kuwa ma'aikatan yahau da masifa, fada sosai yayi musu ransa ya bace daga karshe yake cewa "wannan wane irin kauyancine da gigadanci, zaku kawomin yarona wannan karamar asibitin me suka sani, asibitin da kowane talaka zai iya kawo d'ansa, abban fahad yayi huci ya dube ma'aikatan, duk sunkuyar da kansu kasa, sannan yace "duk na koreku daka aikin tsaron yarona, domin naga bazaku iyaba" ma'ai katan suka shiga bashi hkr, amma sam yaki hkr, mahaifiyar fahad itama fada tamusu sosai itama ta goyi bayan maganar mijinta, sannan abba yafita yaje yasami likita yace yanaso ya bashi transfer zai dauke yaronsa daga asibitin zuwa wani babban asibiti, ba musu likitan ya yanka masa, yakarba suka dauki fahad suka bar asibitin dashi, wata babbar asibiti suka kaisa, saboda har a lokacin bai farka ba. Duk glass yayanke masa jiki, Likitoci sukayi masa aiki sosai sannan suka bada yakinin cewa insha Allah daga nan zuwa gobe zai farka, Abban fahad yace "toh shikenan" anan suka wuni asibiti suna jinyarsa, mahaifiyar fahad ta tambayi abban fahad "waishin meya faru da fahad ne" abban fahad yace " nikuwa ta ina zan sani, bayan nidake duka bama kasarnar, mudai jira yafarka sai ya gaya mana da kansa" Haka suka zauna ko wannesu cike da bacin rai da kuma jimamamin rashin lafiyar yaronsu, basason komai yasami fahad... ***** ***** ***** Wani irin katon falone, yasha ado da kamshin turare, wata dattijuwar mata mai kimanin shekaru 45 ce zaune tana kallon tv cikin nishadi da kwanciyar hankali, Zarah tafito daga cikin dakinta tayi shirinta nafita tana kamshin, fuskar nan tasha make-up tayi kyau abinta sai murmushi take, takarasa bakin kujerar da matar take zaune ta zauna kusa a ita tana murmushi, ummana kallo kike" Matar data kira da umma ta dubeta tana murmushi " ey, ina zuwa kuma haka aka chaba wannan adon haka" Zarah ta sunkuyar dakai, tana sosar kanta, kamar marar gaskiya "umma gidan su maryam zance kinsan yau ake bikin antyn ta " Umma tace " haka nefa, toh shikenan amma dai kirki dade a gidan domin kinsan halin mahaifinki baya son fitar nan dakike, idan yadawo bak'ya nan babu ruwana" Zarah tayi murmushi tace " insha Allah bazaima dawo ba yatarar bana nan, da wuri zan dawo, nidai zan tafi saina dawo" Harta mike zata tafi umma tace "zarah naga kwana biyunan kindaina fita aiki lafiya kuwa" Zarah tadan langwabe kai tana kallon umma tace "ummana banga ribar fita aikin nan ba domin kona fita bana samun natsuwar zuci, ummana kawai kitayani da adu'a Allah yasa na iya jure bakin cikin dazan shiga nan gaba" Umma ta dube tadan zare ido da mamaki " wane irin bakin ciki kuma 'yarnan, meke damun kine a gurin aikin" Zarah tayi murmushi a lokacin duk kwalla sun cika mata edo, tana sauri tabar gurin kar umma ta gane kuka take shirinyi tana fadan " saina dawo zan fada miki umma " dasauri ta fice daga falon tafita harabar gidan, Umma ta tabe baki "toh" sai kuma tayi shiru tana kallon kofar da zarah tafita, sannan tace " Allah yakauta, ina jiran dawowarki" ita kadai take maganar sai kuma tajuya taci gaba da kallonta, Zarah na fita hawaye suka sauko mata, dasauri tashige motar ta,ta daura kanta kansitari, tana hawaye, zuciyarta har wani zafi take mata, rashin faisal a gareta ba karamin tashin hankali bane, a duk lokacin da suka hada edo dashi wani irin sonsa yake kara shiga zuciyarta, saboda ta sami salamar zuci yasa tadaina zuwa gurin aikin domin tagaji da irin wulakanci da faisal kemata, amma duk da haka haryanzu zuciyarta cike take da kaunarsa, Sitarin motar ta daka tana hawaye sannan tadaki kirjinta daidai gurin zuciyarta tana fadan "laifin kine zuciyata, kece kika sakani komai, kece kika ingizani inda ake wulakantani, inda aka daukeni marar zuciya mai nacin soyayya... kuka takeyi cike da tausayi, cikin kukan take fadan "meyasa kika kamu dason maso wani, tabbas kuwa kin sakani a koshin walaha,..." kuka ya kubuce mata, takasa karasa maganar ta saukar dakai kan sitiri, ta jima a hakan kafin ta dago kanta, tatsayar da kukanta sannan tashare hawayenta, ta sai-sai ta kanta, ta kunna motar tayiwa mai gadi hoh ya wangele mata kofa sannan tafice tabar gidan... *Wacece zarah...* Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's Website:_www.abduljega.blogspot.com [10/20, 10:45 PM] +234 905 395 7618 : _Title:-_ *MAJNOON* _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES* 61 and 62 Via *OHW* _A love story_ *Wacece zarah* Zarah heesham shine asalin sunananta, black beauty ce ga diri ga k'ira sonkowa kin wadda yarasa, Zarah ta kammala karatunta na degree yanzu haka tana aikine a wani company, a company ne suka hadu da faisal, tun farkon haduwarsu da ita tafara nuna masa so amma shi saiya rika basarwa, Hakan yasa tanace harsaida takai data furta masa, tun da ta furta masa cewa tana sonsa kuwa a take a gurin ya yi watsi da maganar tare da dayima wulakanci, ko da gargadin cewa karta kara bijiro masa da irin wannan maganar, Amma duk da haka zarah bata daina binsa ba tanayi masa magiya akan yakarbi soyayyarta amma faisal yaki, kullum wulakancinsa kara karuwa yakee. Zarah tayi masa kuka har ba iyaka amma kwata2 yakiji tausayinta, shi ace warsa baya kaunarta, shi bata yimasa baki daya, duk wulakanci na duniya faisal yayiwa zarah akan yaga yacire mata sonsa a cikin zuciyarta amma ina yakasa...hakadai zarah taketa hakuri dashi, tana kara lallashin zuciyarta akan ta dage wata rana zatayi nasara akansa, ( wace rana ce wannan ) oho Iyayen zarah ma'aikatan kwainatine, mahaifinta da mahaifiyar duk aiki suke, mamarta doc ce, mahaifinta kuwa librarian ne a wata university, Su biyune a gurin iyayensu daga ita sai kanwanta Nafisat wacca suke kira da feena... _Wannan kenan_ ***** ***** ****** Haj lubace zaune a daki tasaka rumaisa gaba tana tambayarta akan tagaya mata yadda wannan abin yafaru kuma ta sanar da itada meye silar faruwarsa, rumaisa kuwa bayan kuka babu abinda take, hajja luba tace "to nidai nagaji da wannan kukan naki, tunda bazaki fadamunba, ni zan koma waje idan kingama kukanki saiki kirani kisanar dani" tana gama fada ta mike tsaye, Rumaisa tayi saurin riko hannunta, tana shanshekar kuka tace "zan fada, dan Allah kizauna wlh zanfada " Haj luba tayi ajiyar zuciya sannna ta zaune tace "fadamun ina jinki, meye silal faruwar komai" ta fada ta kallon rumaisa edo cikin edo, Muryar rumaisa na rawa tafara fadawa hajja luba, komai daya faru, harda dukan da abbanta yamata akan saita aure faisal, tun bata karasa gayawa hajja luba, Hajja luba ta dakatar da ita, zuciyarta tadau zafi zanta yabace sosai cike da masifa take fadan "shi Usman (abban rumaisa) shine zai miki auren dole, harda duka, wato kenan badan Allah yasa kinzo nanba , dasaidai kawai naji auranki daga sama, to wlh bai isaba, yadda yake nuna ikonsa akanki nima haka inada iko akansan domin nice na haifesa, hajja luba tayi shiru tana huci, sannan ta kara kallon rumaisa tace "kikace kinada wadda kikeso koh" Rumaisa tace "eh inada" Haj luba tace "ya sunansa kuma d'an gidan waye" gab rumaisa ya tsinke yafadi, domin acikin labarin data bawa hajja luba bata sanar da ita cewa mahaukaci take soba, rumaisa tayi shiru tana kallon hajja luba, batasan sunan majnoon ba ballema hartasan sunan iyayensa, a wane gari yake oho, itama bata saniba, tsoro takeji karta fadawa hajja luba cewa wadda yakeso mahaukacine ne, domin tasan dacewa, zata dauki maganar tata ashirmen banza, Tayi shiru hajja luba ta tsureta da edo, bakinta na rawa ta soma furta " bansan..." Hajja luba ta dakatar da ita domin duk zuciyarta tadau zafi, wani irin haushin abban rumaisa takeji, tace " bana mason kifadamun sunansa ko sunan iyayensa, wlh babu makawa shizaki aura kuma nayi miki alkawarin indai ba mutuwa nayiba saikin auresa" sai kuma ta koma fada " maganar banza maganar wofi yanzu ai zamani ya chanza andaina yiwa mata auren dole, 'yar jikan tawa kwaya daya tak, za'a nemi amata auren dole salon idan aka kaita gidan mijin bakin ciki yanemi kasheta, toh bai isaba wollah" Rumaisa tayi shiru sauraronta kawai take, tasoma ganin nasara acikin lamarinta da majnoon, amma saidai tana fargabar ya Hajja luba zata dauki abin idan har taji labarin cewa mahaukaci takeso" Dafa kafadunta Hajja luba tayi hakan yayi sanadiyar fitowarta daga duniyar tunanin data shiga Hajja luba ta dubeta tace "kitashi kije kiyi wanka, kizo kici abinci, insha Allah gobe zamu koma abuja, kuma ina mai tabbatar miki dacewa zaki aure wadda kikso" Rumaisa ta rungumeta tana kuka " nagode inna" kukan farin take, Sannan A hankalin tafito daga jikin Hajja luba tana share hawayenta sannan ta mike tafita tabar dakin tanufi ban daki, Wanka tayi tafito koda tafito Hajja luba ta ajiye mata abinci, zaunawa tayi taci ta koshi, sai alokacin tasamu natsuwa, Daki takoma takwanta saman gado, tunina barkatai suka rika zomata, yanzu ya fahad yake oho itama bata saniba, sai dai har yanzu akwai sauran tausayinsa a zuciyarta, wannan me yake nufi *so'ne ko tausayi*, Majnoon dintafa yanzu wane hali yake ciki, tabbas tayi kiwarsa sosai, kalaman Hajja luba suka rika dawo mata a kwakwalwa nacewa dole saita aure wadda takeso, murmushi tayi cike dajindadi, a zuci tace "Allah yasa hakan nee" nan dai taci gaba da tunani kala kala, har bacci yazo mata... Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's Website:_www.abduljega.blogspot.com [10/20, 10:45 PM] +234 905 395 7618 : _Title:-_ *MAJNOON* _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES* 63 and 64 Via *OHW* _A love story_ *Washe gari* Tunda sassafe hajja luba tazo tatashi
Chapter 10 · 0% Book details