← Book details Majnoon Part 1 Complete Hausa Novelp Local reading mode
READING PART 4 OF 29

Sashe 4

Majnoon Part 1 Complete Hausa Novelp · about 8 min read

love story_ Rumaisa kuwa Kuka tayi harna fitar arziki itakam tata kaddarar a haka tazo mata, Data daiga kuka bazai kara sheta da komaiba hakan yasa tadan tsagaita kuka, tatashi tashiga neman bandaki a dakin, cen ta hangi kofa takarasa gurin kofar ta bude, taga ban dakine shiga tayi ta watso ruwa sannan tayi alwala tafito, kayan baccine kawai a jikinta tarasa yadda zatayi tayi sallah, duban dakin take gefe da gefe edonta duk sun kumbura, Babu abinda tasamu wadda zai suturtata a dakin, fara bincike daken tayi a kasan gado taleka tana dube2, wani farin kyalle tagani dasauri ta dauko tana kokarinn warware kyalle, Ware ido tayi tana mamaki a hankali bakinta ya iya furta "HIJAB" mamaki take meya kawo hijab din macce anan, gbanta yayanke ya fadi kardai ace fahad da gaske yake yana wiwa mata fyade, Hawaye tasoma tana tunanin makomarta, a tsorace ta karkade hijab din tasaka sannan ta karkade kasan cafet din dakin tafara sallah, bata jimaba tagama sallar sannan tarafa kwararo adu'a akan Alllah ya kubutar da ita yasa fahad yakasa aikata komai akanta, adu'a tayi sosai kafin tagama saida tayi kuka, Bayan tagama sallar tayi zamanta akan sallayar tana kallon dakin, yunwa takeji kamar yan hanjinta zs su fito, Tashi tayi tashiga nemi abinda zataci, kaf dakin bata samuba hakan yasa ta koma kan gado ta kwanta tana kuka, **** **** **** Tunda Abban rumaisa yafita gidan daddy yanufa yasanar dashi komai dake faruwa, lamarin yayi matukar girgiza daddy, saidai yanajin yadda zai fadawa faisal wannan lamari, Daddy ne zaune a falo shida momy sunyi jugum2 suna jimamin abinda yafaru da rumaisa, sake sake suke kala kala, Faisal yafito daga cikin dakinsa cikin shirinsa na fita office, farin yadine a jikin filtexs irin mai shara2 dinnan yayi matukar yimasa kyau, Cikin ladabi da biyayya ya durkusa yagaida momy da daddy, Ganin yanayinsu kamar da dadamuwa a tattare dasu yasa yakasa hakura saida ya tambaya, duk da shima kuwa tun yafarka yau da safe yakejin gabansaa na faduwa, "Daddy meya farune naga kamar kuna cikin damuwa" faisal yana kallon daddy yana jiran yabashi amsa , nunfashi daddy yaja yanajin nauhin yadda zai gaya masa maganar, daddy ya kalli momy, momyma haka daddy take kallon sai kuma sukayi shiru, Faisal kasa fahimtar komai yayi duk ya soma tsorata domin yanaji a jikinsa akwai abinda yafaru, Ya juya yakalli momy yace "momyna tambaya nake amma kuyi shiru meyake faruwane" momy taja nunfashi kamar zatayi magana saikuma tafasa, daddy ya dubeta yace "fada masa mana" Momy tayi jim kafin tace "Faisal, rumaisa ta bata, yanzu haka nemanta ake" wani irin tashin hankali yaji ya ziyarci duk ila hirin jikinsa, tuni hawaye suka soma fita a edonsa, kasa yadda da maganar yayi, ya dube daddy yace "daddy idan bazaka amince da aurena da rumaisaba basai kasa ammin karyaba domin karya bata kama cekuba, momy kufa iyayena meyasa bakoson farin cikina" Daddy ya sunkuwar dakai, wani irin bacin rai yakeji, koda yadagonkansa eedo sa sunyi ja sosai, ya daga hannu ya wankawa Faisal mari, yanaa huci zuciyarsa har wani zafi take cike da masifa yake fadan "so haukane, ko kuka so zai iya sakaka kafada iyayenka magana, idan mun maka karya meye ribarmu...to.to" daddy yakasa yin maganar domin wani irin bacin rai yakeji, Faisal yana dafe da kumatu, yana mamakin wai yau daddy ne yadaga hannunsa ya maresa hawaye kadai ke fita a cikin edonsa, ya dube daddy da momy, muryar na rawa yasomma magana "yaune karo na farko daka fara dukana daddy, badan komaiba sai dan akan innason rumaisa, yadanyi shiru kamar zaiyi kuka, sai kuma yafasa sannan yaci gaba da cewa "bazan hanaka dukanaba domin kai mahaifinane kuma kanada incin dukana aduk lokacin dakasoz, amma bazaka iye cire soyayyar rumaisa a cikin zuciyata ba, idan kuwa kukayi yunkurin rabani da rumaisa ts karfi da yaji to tabbas kuna kokarin rabani da rayuwata ne, kuka yasomayi sannan yamike har a lokacin dafe yake da kumatunsa, kamar zai tafi saikuma yatsaya ya juya musu baya yana fda "idan har kuka rasa wani farin ciki a cikin gidan nan ni zanyi duk yadda zanyi nadawo muku dashi,, ammani abu daya kalilan kukasa cikamun, da kunsan irin yadda nakeji akan son rumaisa da bazaku hanani auren tabs, da kunsan yadda zuciyata kemun zafi a yanzu dabazakuyi yunkurin fadamun wannan maganarba, amma bakomai bazanga laifin kuba amma dai zance kunyi sonkai" yanaa gama fada yanufi hanyar fita, Momy tani zuciyarta tayi snyi, hawaye take cike da tausayin d'anta daya kasa fahimtar abina suka fada masa, daddy kuwa edinsa sunyi ja sosai yama rasa mezaiyiwa faisal, Faisal kuwa tunda yatashi tsaye yakejin jiri, yana dibarsa yana kai daf da kofor fita yaji bugun zuciyarrsa yasoma karfi, dafe kirrjinsa yayi yana jan nunfashi da karfi, a hankali ya sulale ya fadi kasa... Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's Website:_www.abduljega.blogspot.com [10/20, 10:42 PM] +234 905 395 7618 : _Title:-_ *MAJNOON* _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES* 29 and 30 Via *OHW* _A love story_ Tana tsaye a gurin tana kuka, a hankali ta sulale kasan carfet, Tana rokon Allah daya kara tsareta daga shairin fahad, Cike da mamaki Fahad yabar dakin, baitaba jin tausayin macce ba idan yazo kosantarba sai Rumaisa, Dakinsa ya wuce, ya cire rigarsa, daga shi sai singlet da wandon rigar daya cire, yayi zaune bkin gado, yana maida nunfashi, telephone kawai yakira yasa a odo masa giya, bada jima waba kuwa ma'aikacin gidan yashigo dakin da kwalabe a hannnunsa, ya zubesu a gabansa sannan yafita, fahad yabude kwalba daya yafara korawa yana lumshe edo, kamannin rumaisa kadai kemasa gizo, yarinyar kara shiga ransa take... Giyar yasha yayi mankas har kusan karfe 2 na dare baiyi bacciba, tunain rumaisa yahanashi bacci, tashi naga yayi yana tangadi kamar zai fadi, yana sambatu yafita, yana tafiya kamar zai fadi yanufi dakin rumaisa, yana zuwa ya tura kofar dakin yashiga.. A inda yabarta a tsaye anan ta sulala kasa, tayi bacci, tayi sharkar kasan carfet, yakarasa gurinta yayi tsaye a kanta, yana kallonta yana tangadi kamar zai fado mata, kakin amai yasoma yi hakan yayi sanadiyar tashin rumaisa daga bacci taganshi a kanta, da karfi ta zabura ta miki tana fadan innalillahi wa innalillahi raju un, Amai yafara kwararowa tana tsaye tana kallonsa, wani irin tashin zuciya takeji kamar itama zatayi aman wani irin kyankyami, tayi mamakin ganin fahad yanashan giya, a take cewa lallai kuwa wannan yana cikin bala'I ga nema mata kuma ga shan giya, Saida yagama kwara amansa sanna ya kalleta yana murmushi cikin salon murya irin ta mashaya yake fadan "rumaisa nakasa bacci saboda ke, com to me plx" yana kokarin fado mata da sauri takauce masa tana kokarin gudu, ya riko hannunta gam, kuka tasaka tana dukan hannun amma yaki sakinta, cizo takai masa, da sauri yasaki hannun yana wash, Tasamu tabar gurin, yakara daga kasan ya hengeta acen gefe tana kuka tayi wani kakkame jiki, Yanufi gurinta yana tangadi, yana fadan rumaisa com plx, com an hug me, I need u , rumaisa, Kokarin kai ga jikinta yake da karfi tasa hannu taturesa, rakafff kakeji yafadi kasa kansa ya daki gefen gado, jini kadan yafito, shiko ajikinsa bai damuba, kokarin tashi yake sai kuma yakasa, Rumaisa tayi tsaye tana kallonsa, lallai giya bala'ice, ace mutum yajiciwo amma shi baimasan anyiba, Kasa tashi yayi a gurin ya sulale ya kwanta a hankali bakinsa ke furta rumaisa, I need u rumaisa, " har bacci yadaukesa, Rumaisa tayi tsaye akansa tana kallon jinin dake fita akansa, tausayi yabata sosai, a hankali ta durkusa gurinsa cike da tsoro jikinta na rawa, ta kira sunansa cikin siririyar murya, taga ko motswa baiba, hannunta na rawa takai a jikinsa tadan dakesa kadan taga bai motsaba, gabanta yafadi, kardai ace ta kashe dan mutane, Sai kuma ta lura da kirjinsa na harbawa, hakan ya tabbatar mata da cewa yana raye, Mikewa tsaye tayi tarasa yadda zatayi, gajini yana fita a kansa, Jitayi tanason tataimaka masa , a hankali tashiga neman tissue, tsumma a dakin, tazagaye kaf dakin bataga komaiba, Rigarta ta bacci datazo da ita daga gida ita tatuna, dasauri tadaukota ta yaga sannan tadawo gurinsa har a lokacin jikinta rawa yake, ta daga kansa kadan tasa tsumman ta dauremasa kansa, sannan ta mayar dashi a kwance... Kamar daga sama taji ya cafki hannunta.. Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's Website:_www.abduljega.blogspot.com [10/20, 10:42 PM] +234 905 395 7618 : _Title:-_ *MAJNOON* _The mad man_ _Author_:- *MR, SMILES* 31 and 32 Via *OHW* _A love story_ Cike da firgita taja hannun da karfi ta mike tsaye jikinta sai rawa yake, Hannun fahad kuwa ya sulalel kasa yafadi, har a lokacin bakin sa yana furta I need you rumaisa, Tajima a tsaye tana kallonsa, kafin taje tadauko sauran tsumman rigar data daure masa kansa, ta share aman dayayi, takara kallonsa ta girgiza duk tausayinsa takeji, sannan tajanye daga gurin, takoma gefe daya acikin dakin ta takure, jikinta sai kyarma yake, a hankali hawaye kefita a cikin idonta, tana tsoron kartayi bacci fahad ya farka ya farmata, soboda haka ta hana idonta bacci sai shanshekar kuka take, gangad'I tafarayi sai kuma ta farka da sauri, a haka dai bacci yagarara zomata tana zaune tafara jin kiran sallah, nan tamike tashiga toilet tayi alwala sannan tafito, Ba sallaya a dakin, ta karkade kasan carfet tafara sallah, Bayan tagama, tayi adu a sosai sannan tafara karanto alqur'ani mai girma a daidai inda ta hadda ce, reroshi takeji cikin murya mai dadi gaske, Sautin yakeji yana shiga masa kunne yarasa ko meye, jinsa yakeyi kamar ana rairai masa waka, amma dai ba waka bace, a hankali yasoma bude idonsa, a lokacin har gari yasoma wayewa, Kadan ya iya furta wash, a lokacin yadafe kansa, domin ciwon dayaji yanai masa, a hankali yake kokarin tashi yasa hannu yadafe kansa gefen da yakejin zafin, mamaki yake meya jimasa ciwo, kuma waya daura masa tsumma a kai, juya yayi gefen daya kejin sautin na fita, idonsa suka sauka kan rumaisa, baki ya saki yana kallonta ita kuwa cike da mamaki ita kuwa wannan metakeyi haka yafada a zuci, Kamar mai kowon tafiya yafara taka kafarsa yana kokarin karasa gurin Rumaisa, . Jin motsin mutum a bayanta baisa ta tsayar da karatun da takeba, idonta sunyi ja sosai
Chapter 4 · 0% Book details