← Book details Kuncin Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 9 OF 32

Chapter 09

Kuncin Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A Week Later...
Na'ima ce zaune cikin dakinta akan gado, hankalinta yana kan abunda take typing cikin laptop dinta, yau satinsu daya da dawowa gida and a lot has happened, sunje shopping, nafisa ta jasu outing cikin gari and all other fun things, jiya ma part dinsu ya farukn dake gefen main building din gidan suka wuni suna game din ps wanda har da Al'ameen da Abubakar din sukayi.
Nafisa ce ta shigo dakin hannun ta riqe da leda ta miqa mata, karba na'ima tayi tana duban cikin ledan taga sweets da chocolates masu yawa, nafisa tace "karki fado sunana idan mami ta kamaki kinasha wlh" na'ima tayi dariya sanin Mami ta hanasu yawan shan kayan zaqin, farkon dawowansu ta barsu sunasha amma ganin suna iya shanye chocolate kusan ashirin a zama daya tace bataso, karsu sake siyo kayan zaqi masu yawa a gidan.
Nafisa tace "ki shirya muje gurin fitting dinnan meerah nata kirana a waya" na'ima tayi mata questioning look tace "fitting kuma?" Nafisa ta amsa "na gown din da zamu saka wajen event din bikin salma mana" Na'ima tace "nifa bazanje event ba nafee" zama nafisan tayi kusada ita tace "meyasa? Mami ta hanaki ne" ta jijjaga kai tace "a'a kawai bazanje bane" shiru nafisa tayi batace komai ba har na'ima ta maida hankalin ta kan laptop din dake kan cinyanta ta cigaba da typing, can nafisan ta miqe ta fita na'ima ta bita da kallo jikinta na sanyi.
Fitan nafisa ta shiga falon mami ta sameta nan zaune da faruk suna magana, turaren wutane gaban mamin tana mixing dinsu cikin kwalba, nafisa taqarasa kan kujeran gefen faruk ta zauna
Mami tace "baby baku fara shirin fitan bane rana tanayi fa, kincemin zaku fita dazu" faruk yace "Ina zasuje?" Nafisa tace "dama fitting zamuje gurin meerah na gown din event din bikin, Mami kinji Na'ima nacewan bazataje gurin dinnern ba" Mami ta dago kanta daga abunda takeyi tace "ai daman ban aika kayan events da ita ba" kafin nafisa tayi magana faruk ya katse ta da "Ai tafiki hankali datace bazataje ba" nafisa tace "haba yah faruk it's just event fa" yace "yes but nafee kinsan kalan mijin da salma zata aura ai, you know who he is, yawanci guys masu ji da tashe acikin Abuja da wajenta zasu halarci event din, you can't be exposing na'ima to that sort of places" Mami dai na sauraron fadan da faruk yakewa nafisan batace komai ba, nafisa tace "but yah faruk i thought it's high time she starts living her life, doing the things she likes the way she wants to" Mami tace "Many things but not this nafisa, and you know things are not over yet" Nafisa na kallon Mami tayi shiru batace komai ba, Mami ta cigaba "quite sure zataje gidan bikin ta gaisa da wasu 'yan'uwan because it'll be rude of her not to,tunda komai dadewa zasu iya haduwa da ita a cikin gidan nan, but not going to parties...and that's final" nafisa tace "Yes Mami" ta miqe ta fice daga dakin suka bita da kallo.

Haka suka shirya Na'ima zata raka nafisan gurin dinkin, cikin abaya na Na'ima black while na nafisan maroon color, bayan sunyi sallama da Mami ta basu saqon toiletries da zasu biya super market su siya mata, suka fice a motan nafisan.

Bayan sun isa babban fashion store din wanda yakasance gurin dinki, designing da kuma saida dinkakkun kaya suka tadda meerahn tsaye a reception tana magana da receptionist din nata, ganinsu na'iman yasa ta tako garesu tana murmushi tace "look who we have in town" ta qaraso tayi hugging din nafisa suna fara'a sannan ta juya tayi hugging din Na'ima tasake cewa "I've been waiting for you guys like for'everr" na'ima na murmushi dan tasan meerah, ita tayi mata duk dinkunanta farkon zuwanta gidansu nafisa, Nafisa tace "sorry sis" meerah na fara'a ta amsa da "now you have to pay me double" sukayi dariya gaba daya ta jasu suka tafi fitting room din,bayan tayi serving dinsu ruwa na'ima na zaune kan resting sofa wasu staff mata guda biyu suka shigo tare da meerah suka hau gwada nafisa dake tsaye kan gajeran stool, nafisa tace "husna tazo kuwa?" Meerah tace "tazo almost a week now"

Bayan angama sukayi salla a shagon dinki sannan suka wuce gurin aiken da mami ta musu, basu suka dawo ba sai yamma.

Shigowarsu gidan bayan sunyi parking Na'ima ta lura da wata baquwar mota, wata sleek ride dake fake nan parking space din, suka fito Nafisa ma data lura da motan tace "Su yaya Ahamd sunzo kenan" suka wuce cikin gidan hannun nafisa riqe da ledan kayan da suka siyo.
Shigarsu falon Na'ima ta hango Mami zaune da wasu maza biyu zaune kan kujera sunyi backing dinsu, dayan yana having conversation da Mami while dayan yana riqe da waya a hannunsa yana kallonsu mamin, qarasawa sukayi cikin falon nafisa na gaba, Mai maganan yadan dago ya kallesu yace "Nafisa" ta amsa da "Yah Adam sannunku da zuwa" yace "yauwa" Mami tace "baby kundawo" nafisa tace "eh Mami" Suka qarasa nafisa ta ajiye kayan gaban Mami sannan suka zauna kan kujera kan Na'ima na qasa, Nafisa ta sake cewa "Yaya sannunku da zuwa, Ina wuninku" Ahmad ya dago cikin husky voice dinsa yace "lafiya nafisa" shima Adam ya amsa, Cikin sanyin murya Na'ima tace "Ina wuni" tadaiji Adam ya amsa amma mai deep voice din da ake kira da Ahmad dinne bataji ya amsa ba, tadan dago kanta ta kalleshi, Caraf idonta cikin nasa yana nazarinta.
Kauda idonta tayi da sauri ta maida kallonta kan tv dake falon tanajin bugun zuciyarta acikin kunnenta, Tunda take bata taba ganin idanun da suka mata kaifi takasa jure kallonsu kaman na bawan Allahn nan ba. Shima Ahmad dauke idonsa yayi yana cigaba da danna wayarsa, Mami tace "kadai ce bazaka dawo gida ba Ahmad, ka riqe Lagos dinnan har dawowa yana maka wahala" Ahmad ya juya ya kalli Mami a nutse yace "akwai wasu abubuwan danakeson nayi settling ne acan mami" Mami tace "ai zamanka dai anan din yafi,tunda can din bawai iyali ka ajiye ba" ta cigaba tareda juya wa tana kallon Adam "kaima Adam baka fada masa gaskiya ko" Adam yayi dariya yace "nima gajiya nayi da fada masa gaskiya, may be yanzu zeji taku Mami" Mami ta maida hankalinta kan Ahmad tace "Ai mamma tacemin kunyi maganan kuma har yanzu baka dawo ba" Ahmad yadan shafa kanshi yace "in Sha Allah za'ayi yanda kuka ce din Mami"
Itadai na'ima duk ta taqure acikin falon kaman ace cass ta arce, Adam ya juyo yana kallonsu yace "nafeen Mami yaushe kika dawo?" Nafisa da tunda ta gaishesu ta maida hankalinta kan waya ta dago kanta tana murmushi tace "for a week now yaya" yace "Ma Sha Allah, kin kusa gamawa amma" ta gyada kai tace "Eh saura 4 to 5 months haka" yace "Allah ya bada sa'a" yana kallon Na'ima da tun dazu idonta ke kan Tv bata juyo ba yace "Mami baquwa kukayi ne" Mami ta amsa da "Eh 'yar dan'uwana ce dake can Nijar,tare suke karatun da nafisan ma" Adam yace "Allah sarki" Mami tace "zo ku miqamin kayan sama in na shigo zan waresu" na'ima ceh farkon miqewa kamar wanda falon ke mintsini, Ahmad yadan dago ya sake kallonta ta qarasa ta karbi kayan, nafisa tace "to yaya sai anjimanku" suka amsa da toh, tabi bayan na'ima da har ta isa stairs, suna shiga falon mamin nafisa tace "ke yanzu naga texts din mutumin bari kiga" Na'ima dataji duk kafafunta a sanyaye ta nemi kujera ta zauna anan falon tana tuna idanun wannan bawan Allah data baro a falo, nafisa ta qaraso kusa da ita tana nuna mata wayan tace "Kiji wai yanzu ma yana hanya zaizo" cikin sanyi na'ima tace "kibarshi yazo sis, you have to settle fadan nan naku once and for all" nafisa tace "Allah ko?" Na'ima ta gyada kai, shiru nafisan tayi kamar me nazarin wani abu sannan ta miqe ta tafi dakinta,diban kayan na'ima tayi ta dorasu kan table din dake nan falon sannan ta fice tana ture duk wani tunani daga ranta.

Bintu Musa ce ✍🏻

✨KUNCIN ZUCI✨
Na Bintu Musa

Read My Book "KUNCIN ZUCI" on ArewaPen::https://arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c

WhatsApp group 👇
https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z
Chapter 9 · 0% Book details