← Book details Kuncin Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 6 OF 32

Chapter 06

Kuncin Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tsaye yake a parking space dake compound din babban gidan.
gida ne babba wanda kana gani kasan naira ta zaunu gurin mazauna cikinsa,
Yananan tsaye jikin motansa da ya bude driver seat kuma bai shiga ba, wayarsa yake dannawa cikin nutsuwa yana nazarin saqon da aka turo masa.
Mai gadin gidan ya qaraso ganinshi tsaye nan bai shiga motan ba yace "yallabai ko da abunda za ai maka?"  ya dago yana kallon maigaidin yace "a'a yakasai jeka abunka" yakasai yace "toh yallabai afito lafiya" ya juya yana komawa bakin aikinsa.
Shiga driver's seat din yayi batareda ya kulle kofar motan ba ya miqo kafarsa daya waje yacigaba da abunda yakeyi.
Yananan zaune for almost twenty minutes wata mota ta shigo compound din, bai dago kansa ba saida ta qaraso tayi parking dan nesa dashi sannan ya daga Ido yana nazarin motan,
ganin wadda ta fito daga driver seat yasa nan take yayi danasanin tsayuwarsa a wajen bai fita ba, aranshi yana cewa me yasa tun dazun bai tafi ba inyaso sai yadawo inya nutsu ya duba saqon nashi.
Laila ta juyo ta kalleshi, take ta fara murmushi tana gyara gyalenta data saqala a kafada, a daya side din ma qawartace ta fito suka taho tare Laila na gaba tana qarasowa cikin zumudi
Duk wani mood din fitan yaji ya fita daga ranshi, ya fito daga motan ya rufeta yana maida wayansa aljihu.
qarasowan su wajen Laila tace "yaya ashe kadawo?..Ina wuni" gently Ahmad ya amsa da "lafiya" batareda ya amsa tambayanta na farko ba, qawarta mai suna luba ta gaisheshi ya amsa shortly, Laila tace "nakira ba adadi baka dauka ba, i just want to know how you are" ta qarasa tana murmushi bakinta kamar gonar auduga" Ahmad yace "oh really?, may be bana kusa"
Amasanshi ta qular da ita wanda har yanayin fuskanta yaso nunawa tayi saurin waskewa da wani murmushin tace "Kai yaya, I've been calling fa" bai bata amsa ba ya dago hannunsa yana duban wristwatch dinsa yace "I'm late Laila, and nayi mantuwa" ya juya tareda cewa "ki gaida su mommy" ya nufi babban part dinsa shida Adam wanda ke nan compound din gidan, yabarsu Laila nan tsaye a parking lot.
Laila ta cika kamar zata fashe, qawarta ta tabo kafadanta tace "kawata waye wannan din?, kinga yanda yake mana magana kuwa,ko shine Ahmad din naki?"  Laila bata juyo ba balle ta bata amsa ta qurawa side din su Ahmad ido ta jijjaga kai tana kwafa tace "daman naji labarin yadawo nazo na ganewa idona" luba tace "uhm, guy dinnan is full of himself" Laila tace "zanyi maganinshi ne, nikuma!!...yakusa zuwa hannu wlh" luba tace "a yanda kike rawan kafa a gabansa dinne zakiyi maganinsa, girl you must be fooling yourself" Laila ta juyo tana murmushi kadan tace "kedai ki zuba ido ki gani" ta nufi gurin motanta tace "mutafi" luba tace "ha'aa bazamu qarasa ciki mugaisa da mutanen gidan bane?" Laila tace "nagama abunda yakawoni nidai, in zaki zo mutafi to" luba ta kyabe baki ta taho suka shiga motan.
Haka Laila ta tada motanta ba kunya megadi yasake bude musu gate suka bar gidan batareda ta qarasa ta gaishe da iyayen Ahmad ba, wanda mahaifishi ya kasance yayan nata mahaifin

Bayan Ahmad ya shiga part din nasu yawuce Adam dake zaune nan falo yana kallo ya nufi stairs zaije dakinsa dake sama zai chanja kayan jiikinsa don dagaske kuma fitan ya fice masa arai, bayan yayi changing into qananan kaya ya dawo nan falon ya wuce qaramin dining area ya hado tea dinda Mamma, mahaifiyarsa ta aiko musu dazu.
Ya zauna a kujera Adam ya juyo ya kallesa yace "badai har kaje kadawo ba" Ahmad yace "nafasa fitan" Adam ya gyada kai yana maida hankali kan kallonsa, sukayi shiru while Ahmad ya ciro wayansa yana dannawa as yana sipping tea dinsa.
Bayan wasu mintuna Ahmad ya ajiye cup din shayin yana kallon Adam yace "the investors has reached out, they want a meeting" Adam ya juyo yace "wait....about the app?" Ahmad yace "yes" Adam yace " but for real though, you really want to sell it?" Ahmad ya gyada kansa, Adam ya cigaba "Dude, you have almost 6.5 million users, this is huge you know" Ahmad yace "I know, but they are offering big money on this. Beside, this year nakeson launching sabon ai" Adam yace "it's settled then, a Ina sukayi setting meeting din?" Ya amsa da "London but bamuyi arranging date ba tukun" Adam yace "Okay, dama ka dade baka leqa branch nacan ba, this is your chance" Ahmad yayi murmushin gefen baki yace "mundade dai" Adam yace "Dude I'm not the head,you are" ya daga kafada yace "it's part of your job too" murmushi kawai Adam yayi yace  "anyway, I'm happy for you...for real" Ahmad yace "thanks man" ya miqa hannu ya dauko ipad dinsa dake kan table yana qara duba email dinda investors din suka tura masa.

Wuraren qarfe sha biyun rana jirginsu Na'ima ya sauqa Abuja,suka fito duk a gajiye
Bayan sun gama duk wasu formalities suka wuce bangaren arrivals, nafisa sai juye juye take tana neman wanda yazo daukansu, tayi tsuka tace "yaron nan bai iso ba kenan" Na'ima tace "waye yaron, Umar?" Nafisa ta juyo tace "wani Umar kuma, haka kurum yaga kamar nima ina zumudin ganinsa ne" Na'ima batasan lokacin da dariya tazo mata ba tace "nafee babu mai iya miki sai Allah" nafee ta juya tana neman qaninta da Mami tace zaizo daukansu tace "sis mazan ne kamar zuma suke saida wuta" na'ima jijjaga kai kawai tayi batace komai ba.
Can gefe suka hango Al'ameen riqe da name sign da sunayensu rubuce ajiki, shima hangosun da yayi ya ajiye sign din ya nufosu yana fara'a su na'ima suka nufeshi suma, qarasowa yayi tareda yin side hug wa nafisa sannan ya juyo yana kallon Na'ima yace "anty na'ima ya zaman gajiya" tace "Alhamdulillah"
Ya riqe wasu daga akwatin nasu suka qarasa wajen motansa nafisa tace "shine ko ka fada mana ka dawo sai gurin Mami mukejin labari" yana murmushi yace "surprise naso muku fa Mami ta batamin shiri" Suma murmushin sukayi suka shiga motan,bayan ya gama sa kayansu a booth din  ya shiga motan yaja suka bar airport din suka dau hanyan gida.

Shigan motan nasu cikin gidan daya kasance babba wanda kana gani kasan masushi dasu ake murza nera a qasar
suka hango Mami tsaye a entrance din building din ta fito Jin qaran mota, dasauri nafisa ta fice bayan sunyi parking tayi wajenta da gudu gudunta, Mami ta ware hannu tana dariya tace "oyoyo yarana" nafisa ta rungumeta tana murna
cikin nutsuwa na'ima ta qaraso tana murmushi itama, Mami ta sake nafisa ta rungumota tana cewa "welcome habibti" kaso tamanin cikin damuwan da na'ima ta taho dashi taji ya washe jin embrace din Mami,cikin raha suka qarasa cikin main falon gidan suka bar Al'ameen yana debo musu kayan nasu megadi yana tayasa.

Wattpad: Bintu Musa @bintuuu02

✨KUNCIN ZUCI✨
Na Bintu Musa

Read my book "KUNCIN ZUCI" on ArewaPen, Platform available: "all" :: https://www.arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c

WhatsApp group 👇
https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z
Chapter 6 · 0% Book details