← Book details Kuncin Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 16 OF 32

Chapter 16

Kuncin Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Tsaye na'ima taga Ahmad bayan motansa suna saka kayan nasu shida Abban twins at the same time suna magana, qarasawa sukayi gurinsu Anty Amnah tace "son mun tado ka da sassafe ko, ai da ka turo driver ya kaisu bakomai" rufe booth din Ahmad yayi yana murmushi ya matso ya karbi ledan hannunta yace "Bakomai Anty..ina kwana" ta amsa masa su na'ima suka miqa nasu kayan back seat suma Nafisa ce ta fara gaishesa ya amsa sannan ya kalli Na'ima, gaishe sa tayi cikin sanyin murya sai kuma tari yadan zo mata tafarayi kadan kadan, dan qura mata Ido Ahmad yayi sai kuma ya kauda kansa ya yayi sallama dasu anty tareda bude mota, sallama suma sukayi dasu anty Amnah, tayi hugging dinsu tace "sai na ganku on weekends kuma" Abban twins yana murmushi yace "bayan sun koyi qin zuwa akai akai yanzu" nafisa tayi dariya tace "uncle hanyan ne akwai gajiya wani lokaci, amma upper week zamuzo" ya gyada kai yana murmushi yace "Allah ya nuna mana" Na'ima tace "anty in twins suka tashi ki gaishesu" gyada kai anty Amnah tayi tana murmushi tace "toh daughter, safe journey"
Haka sukayi sallama, na'ima tayi saurin bude back seat ta shige, nafisa na dan dariya ta zagaya ta shiga front seat Ahmad ya tada motan suka wuce aka bar su anty Amnah tsaye suna daga musu hannu..
Shiru sukayi while Ahmad yana driving, Nafisa tayi breaking silence din tace "yaya baka taba zuwa gidan da muke zama a Oxford ba ko?" Ahmad ya gyada kai idonshi na kallon titi yace "nadade banshigo England ba nafisa.... bedsides, ai daga baya ma naji labarin tahowanki nan karatun" Nafisa ta gyada tace "hakane...kuma har yanzu kana living a gidanka dinnan dana sani?" Ya amsa da "Eh inanan nafisa, zakije ne?" Tana murmushi tace "Eh yaya zamu kai maka ziyara nida na'ima in Sha Allah..ai zaka dade kafin ka koma ba" yadan kai yatsa yana sosa girarsa kadan yace "I don't know, ina tunanin zuwa New York ne next week" Nafeesa na kallonsa ta gyada kai, ya cigaba "but ba damuwa, ku kirani time dinda kuka shirya zuwan i may be around" idon na'ima kaman ya zazzago dan hararan nafisa, ita ta rasa meyasa nafisan ke son suje gidan Ahmad din all of a sudden, hada Ido tayi dashi yana kallonta ta mirror din gaban motan, tayi saurin kauda kai ta koma daf da window tana kallon titi, tana jinsu suka cigaba da hira sama sama har bacci ya dauketa....
Shigarsu cikin town din Ahmad yayi parking gaban wani babban store yace "I'm coming" sannan ya fita ya shige ciki, bai wani dau lokaci ba ya fito da wata qaramar leda a hannu ya shiga motan suka tafi, basu kai ga isa arean su nafisan ba ya sake tsayawa a gaban wani restaurant nan ma yashiga bai dade ba yafito hannunsa riqe da takeouts, miqa package din yayi gurin nafisa ta karba ta ajiye kan cinyanta, ya zagaya ya shiga motan..

Bayan sun isa haka Ahmad ya tayasu diban kayansu suka shiga elevator dazai kaisu floor dinsu..
Shigansu apartment din Ahmad ya dan bi middle space din nasu da kallo sannan ya wuce gurin mini dining area din nasu ya ajiye su takeouts din da car key dinsa, Na'ima ta fara daukan kayan dake nan falon tana kaiwa dakinta batareda ta kalli inda yake ba, ruwa nafisa ta dauko daga kitchen takawo masa ya karba, yace "Ina duster?" Ta koma ta dauko saita fara goge masa kujeran dining din, bayan ta gama yace "thank you" sannan ya zauna ya ciro wayansa yafara dannawa, fara bude takeout din nafisa tayi yace mata "kunada kayan shayi nafisa" ta gyada kai tace "Eh akwai yaya, in hada maka ne" ya miqe yace "No, zo kibani" shigewa kitchen sukayi Ahmad zai dora shayin

Itadai Na'ima tunda tagama shigo da kayansu daki bata sake fita ba, ta cire dankwalinta da ribbon din da ta daure timilin gashinta sannan ta nemi waje nan bakin gado ta zauna tana jin wani iri sanin presence din wanda ke cikin apartment din nasu...
tananan zaune tana jiyo hiransa da nafisan jefi jefi can kuma saiga nafisa ta shigo ta juya ta rufe kofan sannan ta qaraso gurin na'ima cikin qasa da murya tace "meye hakan kuma na'ima mutum yakawo mu tun daga London amma kin wani shigo daki kin barsa a falo" Na'ima tana kallonta tace "ba gashi kuna hiran ba nafee, mezance masa in na fitan" Nafisa tace "A'a Na'ima, yayanmu ne fa, saikace wani baqo, at least show your care mana, shida ba wani dadewa zeyi ba yanzu zakiji yace zai tafi ma" Na'ima ta gyada kai tace "to ganinan fitowan" Nafisa ta miqe tace "yauwa ko kefa" ta fice..shiru Na'ima tayi sai can kuma ta dauki ribbon din nata tasake daure gashinta ta dau veil din tamayar jikinta kafin ta fice falon, zaune ta gansa shi kadai a falon yana danna wayansa, ya dago kai suka hada ido tayi saurin sauqe nata idon, rasa abunda zatace masa tayi sai kawai ta nufi kitchen a tunanin ta nafisa na can, Ahmad yadan bi bayanta da kallo yadanyi qaramin murmushi baice komai ba
Bata samu nafisan a kitchen ba sai taga takeout din nasu anan kan kitchen island, qarasowa tayi ta fara budewa da daddaya takai hannu ta dauki chip daya tafara ci, Ahmad  yashigo kitchen din ta dan kallesa ta dauke kai, shima wucewa yayi gurin gas ya duba tea din, sauqewa yayi ya dauki cup  ya dauraye a pampo sannan ya juye shayin ya juya gurin na'ima dake nan tsaye, miqo mata shayin yayi yace "Here..drink this" dan kallon shayin na'ima tayi ta kuma kallonsa taga idonsa akanta, miqa hannu tayi ta amshi shayin takai baki, ya juya ya fita sai gashi yadawo da ledan abunda ya siya a store dazu, dan tari Na'ima tafara kadan, ahankali yace "sorry" ta gyada kanta kawai, bude ledan yayi ya ciro wasu magunguna na mura da tari ya balli daya ya dan kalleta yace "dauko ruwa" ta ajiye tea din ta dauko bottle water a fridge sannan ya miqo mata maganin yace "Here..sha wannan" itadai na'ima batace komai ba ta miqa hannunta, bude tafin hannunta tayi da nufin ya saka mata maganin sai taga shiru bai bata ba, dan dagowa tayi ta kalleshi sai taga kallon tafin hannun yake baya ko kifta ido, kafin ta dauke hannun taga ya sa dayan hannunsa yana riqo tafin hannun yace "what's this?" Jin kamar an jona mata electric wire yasa Na'ima saurin kwace hannunta ranta adan bace tace "don't touch me" ajiye maganin yayi yana kallonta cikin sanyin murya yace "meya wannan a hannunki? tabon menene?" tayi shiru batace komai ba yasake kwantar da murya yace "Na'eemah" dagowa tayi ranta yana dan baci akan tamabayar da yayi mata wanda a ganinta ba abunda ya shafesa bane, tace "karka sake tabani" shidai yana kallonta ya gyada kai alaman "toh" sai kuma yasake cewa "what's that on your hand Na'eemah?" Na'ima ta hade rai tace "ciwo naji..but wait, why are you even here? all of this" tayi maganan tana nuna su takeouts da shayin sannan ta dago ta kallesa tace "all this caring..nasan zakace don mu qannenka ne shiyasa but all of these are making me uncomfortable, you're making me uncomfortable har nafisan ma" Tsayawa kallonta kawai Ahmad yayi ta kasa jure kallonsa ta kauda kanta ta cigaba da cewa "we are fine on ourselves for more than half a year now please stop making us uncomfortable"
Ahmad bai daina kallontan ba, can kuma ya gyada kai baice komai ba ya juya ya fara takawa ya fice daga kitchen din yabarta nan tsaye tana jin wani iri kuma..
Tananan tsaye taji fitansa daga apartment din, a wannan moment dinne kuma taji duk wani qunci ya daure mata zuciya, dana sani ya fara shiganta sai kuma ta dago tafin hannunta tana kallon katon tabon dake cikinsa, kawai hawaye ya fara fita daga idonta tana sharewa...
Takasa motsawa daga inda take tsaye a kitchen din, tanata kallon shayin da magungunan tunani iri iri suna mata yawo a cikin zuciya, Nafisa ce ta shigo kitchen din tace "sis naji kamar an fita, yayan ne ya tafi?" Na'ima ta dago ta kalleta tace "bansani ba nima nafisa" Nafisa takai hannu tafara duba magungunan tace "Allah sarki maganin mura ashe ya siyo miki, toh ina ya tafi kuma babu sallama" nan ma Na'ima bata amsa ba, nafisa ta juya ta fice daga kitchen din sai gata tadawo da waya a hannunta tayi dialing line din Ahmad tasaka a handsfree..daga wayan yayi tacan bangaren tareda sallama, nafisa tace "yaya nafito banganka ba nace ko wucewa kayi babu sallama" cikin nutsuwa yace "Eh nafisa, sorry something came up ne" Nafisa tace "bakomai yaya mungode Allah ya saka da alkhairy, sai munzo din muma" yace "Okay bakomai" tareda kashe wayan.
Nafisa ta kalli Na'ima tana nazarinta batace komai ba, cikin sanyin murya Na'ima tace "shine kikace in fito kuma na fiton ke kika shige daki nafisa" Nafee tadanyi dariya tana kai chips bakinta tace "Abu fa naje nema a dakin kuma bansamu ba" jijjiga kai kawai Na'ima tayi ta juya ta fice da kitchen din nafisa na bin bayanta da kallo, murmushi tayi sai kuma ta juya ta kalli kofin shayin data samu a gaba na'iman lokacin shigowanta...

Bayan Na'ima ta koma daki tayi changing into qananan kaya mara nauyi, fitowa tayi ta hau share gidan nafisa ma ta fito suka hau tsaftace gidan tare suna hira, sai da sukaga ko Ina yayi tsaf yana kyalli sannan suka tafi yin wanka kuma, Bayan na'ima tayi wanka ta saka wani kayan ta dauki kayan nafisa dake dakinta ta fita kai mata.
Yammacin ranan suna zaune anan falo itada nafisa, cheese ball ne a hannun Na'ima tanaci amma absent-mindedly, ta qurawa carpet ido bama ta Jin gulman da nafisa dake gefenta take mata akan lamuransu na IG, tunani Na'ima ta fada sosai .... tayi abu kuma ya dameta, duk wani iri takeji wunin ranar akan maganganun da tafadawa Ahmad
Wani fannin na zuciyar na encouraging dinta akan abunda tayi yayi daidai amma wani fannin kuma akasin hakan takeji, bini bini zata dago hannun nata ta kalli tabon, Amma inta tuna cewa dalilin namiji wannan tabon ya zanu a tafin hannunta sai taji cewa gwara da ta kyari Ahmad din, ta dade da yiwa kanta alqawarin itada maza kuma haikata haikata sai kallo daga nesa, shiyasa har yau duk mazan da suke binta anan oxford bata taba sauraran ko daya ba kuma batajin zata sauraran, Amma meye Ahmad yake yiwa zuciyarta aduk lokacin da suka hadu ne? Ta sake tambayan kanta a karo na ba adadi kuma babu amsa..
Jin shirun nata yayi yawa yasa Nafisa dago kai ta kalleta tace "NA'IMAA" juyowa na'ima tayi adan birkice tadan ware ido tace "Uh" nafisa tace "tun dazu inata miki magana, me yake damunki ne" Na'ima ta jijjaga kai tace "babu komai fa" nafisa ta sake cewa "gashinan kinata tunani tun dazu, me ya faru dazu tsakaninki da yaya Ahmad?" Na'ima tace "ni babu komai" nazarinta nafisan ta tsayayi sai kuma ta juyo gaba daya tana facing dinta tana murmushi tace "akwai abunda ya hadaku ne da muka koma gida sis...Ina jin kamshin wani abu tsakaninku" Na'ima ta cusa cheese ball din hannunta a bakin nafisan tana dan dariya tace "wai kamshi..mezanyi dake ne nafee? Yaushe ma na hadu dashi" Ta qarasa tana jijjaga kai, nafisa ta fara tauna cheese din tana dariya itama tace "in tayi tsami zanji ne, da bakinki zakimin bayani yarinya" na'ima ta jijjaga kai tana murmushi sai ga kiran Mami yashigo wayanta....

Washegari ya kasance Monday akwai zuwa school Amma Na'ima bata tashi ba sai wajen qarfe 10 kasancewar batada lecture ranan kawai submitting wani essay dinta zata je yi, brush tayi harda wanka kafin ta fita zuwa kitchen dan tayi breakfast, nafisa tasamu a kitchen din ta dafa musu noodles tana zaune jikin kitchen island din suna video call da faruk, leqawa na'ima tayi tana murmushi tace "yaya Ina kwana" faruk yana murmushin shima yace "habibtin Mami nakiraki ashe kina bacci" ta gyada kai cikin sanyin muryarta tace "yau baka fita aiki ba ne yaya" yana kallonta yace "Eh banje ba....a train kuka dawo ne jiyan? naji muryanki wani iri kamar sanyi ya kamaki" kafin ta amsa Nafisa tace "yaya Ahmad ne fa yakawo mu" faruk yadanyi stiff sai kuma yace "Ma Sha Allah, cemasa kukayi yazo ya kaiku kenan?" cikin sanyin murya Na'ima tace "Nafisa ce ta fada masa yaya" faruk yadan kalli nafisa data dan harari Na'ima,yana dan hade giran sa yace "ce miki akayi baida aikin yi ne" Nafisa tace "nifa shi ya tambayeni yaushe zamu koma, kuma laifi ne dan ya kawomun yaya" faruk ya dan sake fuskansa yace "yayi kyau hakan, ya taimakeku ma" da haka suka gama wayan, bayan sunyi breakfast din suka fice zuwa school din.
sai da suka biya park dinda suka bada ajiyan motan su dazasu koma gida, suka daukota sannan suka wuce makaranta..

Bintu Musa ce✍🏻📚
ArewaPen @Bintu Musa

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z

✨KUNCIN ZUCI✨
Na Bintu Musa

ArewaPen
https://www.arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c
Chapter 16 · 0% Book details