Chapter 03
Kuncin Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Schoolwork dinda Na'ima batayi ba washegari kenan suka shiririce wajen kallo,da suka gama na'ima ta tafi kitchen zata dafa musu tuwo miyan ganye
Nafisa na tayata suna hiran samarin ita nafisan, da wa'inda ta baro a gida Nigeria da kuma wa'inda take kulawa sama sama anan oxford
Na'ima na dariyan draman nafisa da umar, saurayinta da tun a BUK suke tare, yanzu haka yana aiki a central bank
Nafisa tace "kinsan Allah, this time around idan nayi blocking dinshi bazan bude ba mun rabu kenan" Na'ima ta dan bude ido tace"toh fah,abun har yakai haka" Nafisa tace "I'm serious this time"
Na'ima tace "toh yanzu dai bari mujira idan kikayi blocking dinshi dagasken sai mu cigaba da wannan maganar" Nafisa ta ajiye alayyahun hannunta data tara ta dauki roban gabanta dayake kan kitchen island din zata buga mata tana dariya
Baya Na'ima tayi tana dariya itama tace "gaskiya ne ai,maganar blocking dinnan har nagaji da jinta kuma anjima zanjiku kuna waya kina kashe murya" Nafisa tace "zan baki mamaki kuwa, zaki gani" Na'ima ta dawo wajen girkin nata tace "aikuwa zansha mamaki randa hakan ya faru" Saboda har ta gaji da bawa nafisan hakuri karta rabu da guy din
A haka suka gama girkin suna hira cikin walwala, bayan sunci sunyi sallahn la'asar kowacce ta tafi nata dakin yin wanka suka shirya suka fita yawon yamma, Walking through the street of the town zasuje Cafe , Nafisa ta tsaida su gefe tayi wa na'ima hoto tana murmushi, ta dauka musu tare sannan ta bawa na'ima wayan ta dauka mata ita kadai, sai da rana ta fadi suka koma gida hannunsu riqe da ledan snacks din da nafisa ta sa suka siya a wani supermarket kamar ba jiya suka yo siyayya ba.
Bayan sun koma gida sukayi sallah suka zube nan falon, Na'ima ta dauko laptop dinta ta cigaba da essay dinta while nafisa kuma tanata danna wayanta,ta zabi hotunan da sukayi tare da wanda tayi wa na'ima ita kadai ta turawa Mami sannan ta zabi wanda take ita kadai banda na'ima tayi posting a Instagram handle dinta sannan ta tashi ta dauko nata laptop din don duba school work dinta itama
Washegaria Monday zasu je school, Na'ima da wuri ta tashi zata hada musu breakfast dan tafi ganewa tayi musu if not nafisa toast da tea kawai zata musu
Tana kitchen din tana kada kwai bayan ta gama chips nafisan ta shigo hannunta riqe da ipad sai lumshe Ido take alamun bacci bai isheta ba ta miqawa Na'ima ipad din, karba tayi taga fuskan mama akan wayan tana mata murmushi tace "Habibti ina kika baro wayanki inata kira"
Na'ima ta amsa "yana daki ne, ina kwana Mami" tace "lafiya lau na'ima,kun tashi lafiya" kafin ta amsa Abubakar dan autan Mamin ya sako kanshi ta bayanta yana gaisheta, Na'ima ta amsa tana murmushi tace "Abu yau bakaje school bane" yace "jiya muka gama Waec anty" Nafisa ta matso tace "Kai dalla ka bawa Mami wayan su gaisa" Gwalo Abubakar ya mata , Na'ima tayi dariya sanin draman da suke kwasa a tsakaninsu tace "rabu da ita,saura Neco yanzu ko" yace "Eh" tace "Allah ya baku sa'a" ya amsa da Amin yana matsawa fuskan Mami ya shigo tace "daughter ba wani matsala ko?" Na'ima tace " A'a babu komai"
"Ma Sha Allah,ku rinqa karatu fa kunji" ta amsa da "toh Mami in Sha Allah" Mami tace "Allah ya taimaka yayi albarka" bayan ta amsa sukayi sallama ta miqawa nafisa itama sukayi sallaman.
Na'ima ta gama hada musu breakfast sunaci anan kitchen din dayake akwai kujerun zama jikin kitchen island din nafisa tace "yau zamuje wajen taron movie premiere a London" Na'ima tace "Really?..wane movie ne" nafisa tace "British movie ne,Lauren ta siya mana tickets ashe tun last week" hankalin na'ima na kan plate din abincinta tace "then me zakujeyi awajen toh" nafisa tace "ita zataje for her content nima dai sort of that,kizo muje it'll be fun"
Na'ima ta juya ta kalleta tana ware ido tace "waaa?..school zan tafi yanzu ma ina gama cin abincin nan" Nafisa tace "muma fa sai mun gama morning lecture tukunna, it'll be fun I'm telling you" Na'ima ta girgiza kanta tace "Bazan je ba"
Tuesday..
Tsaye take a balcony na apartment din nasu dake 4th floor cikin 10-story building. Bayan tadawo daga school kadaici ya dameta a gidan ta fito nan don tasha iska, tana tsaye daga inda take tana hango wucewan mutane da dama a street din nasu, Most at times batason zaman shiru sosai in Nafisa batanan, takan nemi wani abu da zeyi keeping dinta busy to abstain herself from thinking.
Wasu couple ta hango suna tafiya suna dariya, Na'ima ta bisu da kallo har suka wuce, ta dago hannunta tana kallon wani tabo dake tafin hannunta
qurawa tabon ido tayi tanajin zuciyarta na karyewa abubuwa da dama suna dawo mata cikin kanta , digar hawayenta akan tafin hannunta ne yasa tayi saurin goge idonta tabar balconyn takoma cikin falo , dauko mopper tayi ta fara tattare gidan tana gogewa.
Ranar har bandakin nafisa saida ta wanke , ta sake rearranging din wardrobe dinta dana nafisan ta dafa musu rice and stew, kuma duka ayyukan nan din tayi ne don kawai tasamu something to keep her mind off, something that will abstain her from thinking too much.
Ranar juma'a suna zaune a falo da safe suna hira jefi jefi sun saka skin face mask, na'ima tana karatu a ipad dinta aka kira nafisa, tashi zaune nafisan tayi daga kwanciyar datayi kan kujeran a fili tace "yah faruk" Na'ima tabar abunda take ta juyo, amsa kiran nafisa tayi suka gaisa sai kuma ta miqe da sauri ta leqa balcony, ihun da tayi ne yasa Na'ima ajiye ipad din da sauri ta bita balconyn itama tana duban street din
Yah faruk ta hango jikin mota a gefen street din maqale da waya a kunne yana dago musu hannu, ware idanu tayi ta rufe bakinta da hannu saboda mamaki, buga kafa nafisa tafara yi tana ihun murna batareda damuwan mutane na dago kai suna kallonsu ba, Yana dariya ya matsar da wayan daga kunnenshi Jin tana ihu, da gudu nafisan ta koma falo tayi hanyan fita kayan bacci neh jikinta me dogon hannu da dogon wando ta fice da sauri.
Na'ima ta dawo falon ta tsaya tana murmushi don har ga Allah itama tayi murnan zuwansa don yah faruk mutuminsu ne kuma yayansu....An investment banker sannan first born a gidansu nafisa,shine wanda nafisa take bi, daga ita sai Al'ameen da yake makaranta a Toronto Canada sannan last born dinsu Abubakar. 'ya'ya hudu yan gata wajen Mami da Abba sai Na'ima da suka hada ta zama cikon ta biyar acikinsu.
Tananan tsaye a falon taji beep din password suna kokarin shigowa, da sauri ta juya ta koma daki don dauko hijab itama kayan baccin ne jikinta dan tunda sukayi sallah asuba suka koma bacci nan falon, tashinsu ne bayan sunyi brush sunyi breakfast nafisa ta tsiro musu da saka face mask kafin suyi wanka
Bayan ta sako hijab din tacire face mask din ta dawo falon, suna zaune nafisa sai zuba take kamar gyada, na'ima ta qaraso ta zauna kanta a qasa ta fara gaisheshi tana murmushi
Amsawa yayi shima yana murmushin sai kallonta yake ganin duk ta chanja from the broken girl he once knew, cikin tsokana yace "Habibtin Mami" miqewa tayi tana sunne kai cikin kunya ta wuce kitchen don kawo masa abun sha
Nafisa tace "ya faruk I thought direct flight to Abuja ko Lagos zaka bi daga can Paris din fah" ya juyo yana kallonta yace "what's that on your face?" Sai lokacin nafisa ta tuna da abunda ke fuskanta ta fara dariya tana cirewa.
Na'ima tadawo falon riqe da plate with snacks,drinks and bottle water ta jawo tabe zuwa gabansa ta dora akai ta koma ta zauna suka qara gaisawa yana tambayansu karatunsu
Hira sukasha sosai nan falon cikin raha, a dan zaman da tayi can gidansu nafisan ta fahimci yah faruk mutum ne mai kirki da son 'yanuwan sa, ga kyauta da fara'a, shekara shida ya basu itada nafisan ayanzu da suke cikin shekarunsu na ashirin da hudu
Ganin hiran taqi qarewa especially yanda nafisa take ta zuba yace "toh yanzu dai ku shirya zan koma London tare daku, anty Amnah tace intaho mata daku" nafisa tace "dama fa gobe muke shirin zuwa" yace "Nah..ku shirya mutafi yanzu dan nima goben nakeson wucewa gida" nafisa ta turo baki "haba yaya, kabari sai Sunday mana" yace "a'a ai nazo naga lafiyarku" ya juya yana kallon Na'ima yace "ko habibtin Mami" tayi yar dariya tana kauda idonta tace "kayi kokari yaya mungode sosai" yace "yauwa...ku tashi ku shirya karku dau lokaci please" suka miqe kowacce tayi nata dakin suka barshi nan falon ya miqe yafara kashe kayan wuta na gidan.
Wattpad: Bintu Musa @bintuuu02
✨KUNCIN ZUCI✨
Na Bintu Musa
Read my book "KUNCIN ZUCI" on ArewaPen, Platform available: "all" :: https://www.arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c
WhatsApp group 👇
https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z