← Book details Kuncin Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 14 OF 32

Chapter 14

Kuncin Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Dan gajeran hutun su na'ima yaqare suka fara shirye shiryen komawa makaranta, duk wani abu da zasu buqata 'yan qananu qananu na amfanin yau da kullum Mami ta hada musu, bawani shopping sukayi ba don acan din babu abunda suka rasa.
Dawowar da na'ima taji bataso sai akasin hakan ya faru, batayi tsammanin zuwanta gidan zai saka mata nutsuwa mai tarin yawa ba wanda har zataji batason komawa England , sai dai tasani komawanta school din yazama dole shiyasa ta ke ture iren iren tunanin daga ranta.

Zaune suke a main falon gidan da yamma, na'ima dake cikin boubou mara nauyi tana zaune gefen Mami nan zaune kan carpet tana tayata ware wasu kaya a leda da mamin ta aiki driver ya siyo safiyar ranan, Mami ta ciro wani expensive air freshener ta miqawa na'ima tace "Habibti sa muku wannan cikin kayanku zai muku amfani" karba na'ima tayi tace "toh" ta ajiyeshi gefenta a kan carpet, nafisa ta dan dago daga kwancen datake kan kujera tace "Mami duk munadasu fa" Mami ta kalleta tace "wai da nace ku qara akan nakun" Nafisa ta miqe zaune tace "Mami kayan zasu mana yawa fa" Mami ta juya gun na'ima tace "Habibti barshi toh" Na'ima tace "A'a Mami munaso, mungode" Mami tace "to kekadai zaki rinqa amfani dashi kar naji kin bata, tunda ita ba'a mata gwaninta" Nafisa ta fara dariya tace "kiyi hakuri Mami" Mami tace "ke kika sani, yauwa nasa lantana ta siyo muku kuka da busasshen kubewa sannan ta hado da daddawa mai dadi dan nacan basa sarrafashi me kyau" bude baki nafisa tayi saura kadan na'ima ta kwashe da dariya ta dan kauda kanta tayi tana murmushi, Nafisa tace "Mami daddawa fa..wallahi warinsa duk cikin jirgin nan sai kowa yaji" Mami tadan tsaya kallon nafisa, dan turo baki nafisa tayi alamun shagwaba ta koma ta kwanta akan kujera tana gyara skin face mask dinda ta saka, Mami ta juya ta kalli Na'ima tace "bakwayin tuwo ne Na'ima?" Na'ima tayi saurin jijjaga kai alaman a'a, tayi murmushi tana dan kallon gefen nafisan tace "munayi Mami"
Faruk ne yashigo cikin qananun kaya bai dade da dawowa daga gurin aiki ba, ya zauna nan falon shima, bayan sun gaisa nafisa tace "yaya kaji wai daddawa Mami zata bamu mu sa cikin kaya mutafi dashi" faruk ya danyi dariya yace "daddawa kuma?" Na'ima tayi murmushi, Mami tace " ni tambayata anan shine, basa dafa tuwo ne ko me?" Faruk yace "Mami inkinga fridge din yaran nan danaje last time, inaga sai kin kai hannu a kowannensu, fast food kawai suke dirkawa cikinsu" Mami tadan bude baki tajuya ta kalli Na'ima tace "harda ke Habibti? naga kuma tuwon yana cikin favorite dinki" Na'ima tayi saurin gyada kanta tace "Allah mami muna dafawa time to time, amma miyan ganye" Mami ta kada kai tace "yamuku kyau, nasan kuma baby ce shugaba, da Abban ku yasiya muku mota kurinka uzurirrika dasu bakwa zuwa shopping na kayan abincin ne ko me?" Nafisa tace "wallahi muna zuwa shopping din Mami" Mami ta harareta tace "na kayan kwalliya da fata ba, my friend shut up" faruk dake zaune ya kada kai shima yana murmushi, Mami ta sake kallon Na'ima tace "na'ima kurinka yin abinci me kyau kunaci banason zama da yunwa, ko baby bataje siyo kayan ba ke kirinqa zuwa kina siyowa inyaso in kin dafa ma karki bata" Nafisa tafara dariya tace "Na'ima sarkin karatun kike bawa saqon nan Mami" Mami tace "nidai na fada muku, meye kuma na rayuwa da fast food da lafiyanku da komai ku ba kutare ba, banaso haka kunajina ?" suka amsa da "toh" Mami tace da faruk "kuma fa tsaf nake hadawa Al'ameen daddawan in qulle masa yatafi da ita Toronto baya wani zancen wari" faruk yace "Al'ameen kikace Mami ba mai bakin rezan nan ba" Nafisa da Na'ima suka fara dariya...

Ana gobe zasu tafi Na'ima na tsaye gaban madubi a dakin nafisan tana tattare mata mayukan da zata koma dasu, wasu oil ta dauka ta juya gurin nafisa dake zaune kan gado hannunta da waya tace "zaki koma da wannan?" Nafisa ta dago kai ta kalle ta tace "a'a inada wannan acan" ta maida kanta kan wayan tacigaba da dannawa.
Deban wasu mayukan na'ima tayi a hannunta ta nufi gurin akwatin nafisan datake mata arranging kayan tace "har zamu koma baki hadu da umar ba nafee, meya faru ne?" Nafisa ta ajiye wayan hannunta tana kallon Na'ima tace "we broke up since" Na'ima dake arranging kayan cikin akwati ta dago ta kalleta tace "you're taking a break dai, badai break up ba" nafisa ta gyada kafada tace "Dagaske im done with that guy kuma, i need my sanity, it's high time infara prioritizing peace of mind dina na'ima" Na'ima dai sai kallonta take sanin it's a big decision for her, aranta tana ayyano yanda nafisan keda kyau, gata, kudi amma sai Allah bai sa mata sa'a akan soyayya ba, namijin da bai kai ba yake juya zuciyar kawartata son ransa.. miqewa tayi ta zauna kusada nafisan cikin kwantar da murya tace "but are you okay with this decision?" Nafisa ta gyada kai tace "tunda mukayi fadan nan nayi blocking dinsa, he makes no efforts akan gyara relationship din, zanyi ta bata lokaci na ne akan someone that will not make effort to have me neh Naima?" Na'ima tadan riqe hannunta tace "it's okay...Ina bayan duk abunda kikeso ko kikayi deciding..in umar ba alkhairy bane a cikin rayuwanki a sannu Allah zai kawo wanda yafishi, the one that will make the most effort to love you earnestly" Nafisa tayi murmushi tana riqe da hannun Na'ima tace "thank you sis, you know I'm grateful to have you in my life right?" Na'ima tayi murmushi tace "me to nafee" ta miqe tana kama kunkumi tafara bin dakin da kallo tace "saura me kuma zan hada miki, banason sai mun koma ki fara mitan bakiga wasu abubuwanki ba" Nafisa tayi 'yar dariya ta koma ta kwanta tace "toh mummy na'ima,kin sakamin inner wears din" na'ima ta gyada kai ta sake komawa bakin madubi tana duban ko akwai abunda zata qara dauka...

Washegari ya kasance flight din sha dayan safe garesu, dawuri suka tashi kasancewan na'ima anan dakin nafisan ta kwana yasa bayan sun idarda sallah suka wuce dakin Mami tare
Zaune suka sameta kan sallaya dan yawanci in Abba yatafi masallaci ita dakinta take dawowa tayi nata sallan..bayan sun gaisa Mami tace "kun gama shirya kayan naku dai ko, dan banason mantuwa" Na'ima tace "Eh Mami in Sha Allah" nan suka zauna tare da mamin sukayi azhkar dinsu da karatun qur'ani, Mami na musu nasiha akan makarantan dazasu koma.....Karfe goma saura suka shiga falon Abba, sun sameshi zaune kan zujera hannunsa riqe da cup din tea yana hira ya samarin gidan, na'ima ce ta fara zama a qasa nan kan carpet sannan nafisa ta bi bayanta suka gaishe da Abban, yana murmushi ya amsa gaisuwan sannan yace "yaran Abba kun shirya ko" suka amsa a sanyaye, Abba ya sake cewa "Toh, Allah ya kaiku lafiya, Allah ya bada sa'an karatu" suka amsa da Amin, Abba ya cigaba.."banason wasa, kumaida hankali akan ibadunku da karatu, I'm very proud of how hard kuke maida hankali ga karatun amma ku qara himma, sannan a batun ibada kuma nasan indai akan tarbiyan da muka baku ne banida haufi akan kuna maida hankali, Amma tunda ba'a gabanmu kuke ba inason kuji tsoron Allah ku maida hankali akan sallolinku, Allah ya muku albarka.. we'll surely missed you" kasa amsawa nafisa tayi ta miqe ta qarasa gurin Abban tafara kuka tana riqe hannunsa, ajiye tea cup din yayi ya bude mata hannunsa ta fada jikinsa tana kuka, Abba yana dan buga bayanta yace "saura kadan ai daughter, besides zamuzo celebrating gamawanku ai" , idon na'ima itama ya kawo hawaye tananan zaune, Mami dake zaune kan kujera a gefe ta bude nata hannun tace "Zo Habibti" tashi na'ima tayi ta qarasa gurin Mami itama ta shige jikinta tana hawaye, barin jikin Abba nafisa tayi ta koma jikin Mami itama tana sake wani kuka, Al'ameen da Abubakar suka koma gurin Mamin suka tsaya jikinsu duk yayi sanyi, Faruk yace "kukan nan ya isa ku tashi mutafi kafin lokaci ya qure" suka dago daga jikin Mamin tana goge musu hawayen tace "saura kadan fa yarana, ku maida hankali kunji, sannan ko menene yafaru ku kiramu, it's just a call away"

Haka su na'ima sukayi sallama da iyayen nasu cikin sanyin jiki, faruk ya tisa qeyarsu mota, maigadin gidan ya qaraso ya taya su Al'ameen saka kayansu a booth, tare suka tafi dasu Abubakar airport din, suka bar Mamin da Abba nan tsaye bakin entrance din gidan suna daga musu hannu

Zaune suke a waiting lounge suna jiran lokacin tashin jirginsu yayi, Nafisa tace "Abu please siyo mana abun tabawa, banason zaman shiru" miqewa Abubakar yayi ta sake cewa "ice coffee please" ya tambayeta flavor din da takeso ta fada masa ya juya gurin na'ima itama ta fada masa kalan wanda takeso, miqewa Al'ameen yayi suka tafi tare.

Sunanan zaune Na'ima ta hango shigowar su Ahmad gurin shida Adam kafadarsa rataye da jaka while Adam jaye da qaramin akwati, sai Laila dake biye dasu itama, kauda kai na'ima tayi daga kallonsu,
Faruk ne ya fara miqewa ya isa wajensun yana miqa musu hannu sukayi musabaha sannan su na'iman suka miqe suma, nafeesa tace "ita kuma wannan me kama da mayun ko meye na biyosu airport oho" Na'ima na jinta bata ce komai suka qarasa wajenda su Ahmad din suke tsaye, gaishesu sukayi Ahmad ya amsa yana kallon Na'ima wadda itama yau tayi nata jarumtar ta kallesa, baifi na few seconds ba Na'ima ta dauke idonta jin yanayinta na canjawa ta juya tana kallon Laila dake kallonta itama, samun kanta tayi da qin saka mata gaisuwa ta kuma dauke kai... Adam yace "yan makaranta, za'a koma kenan" nafisa tace "wallahi kuwa yaya, kuma London din zakuje ne?" Adam ya nuna Ahmad daya maida hankalinsa kan waya yace "ga Mai tafiyan nan ai" Nafisa ta kalli Ahmad tace "Ashe flight dinmu daya yaya" Ahmad ya dago kansa daga danna wayan, cikin nutsuwa yace "It seems so..kuma flight din 11 dinne?" Nafisa ta gyada kai tace "Eh" sannan ta juya ta na kallon Laila, in a mocking way tace "hajiya Laila..kema London din kika nufa ne?" A daqile Laila tace "A'a" tana dan qara matsawa kusa da Ahmad, Na'ima na kallonsu... kallonta Ahmad yayi suka hada ido sai taga yadan matsa daga kusa da Laila still bai daina kallon idonta ba, Na'ima ta kauda kanta jin zuciyarta namata wani iri ta koma kallon mutanen dake wucewa.

Su Abubakar ne suka qaraso wajen hannunsu riqe da ice coffee, Adam yace "wannan kuma fa, nasu waye?" kafin nafisa ta amsa Laila ta rigata miqa hannu ta karbi duka cup biyun dake hannun Abubakar tace "Abunda naketa craving this days..thanks" Nafisa ta dan harari Lailan ta karbi na hannun Al'ameen, Abubakar ne yace "Anty Laila ki riqe nawan amma vanilla flavor din na Anty Na'ima ne" Laila tace "Oh sorry" ta miqawa na'iman, Na'ima ta miqa hannu kafin ta karba Laila ta sake matashi a jikin ta, nan ice coffee din ya kware gaba daya a jikin brown abayan na'ima, baya Na'ima tayi tace "Bismillah" ta riqe daidai gurin da ya zuban gashi har gyalenta ya taba, faruk ya taka zai je gurinta sai ganin Ahmad yayi ya rigashi isa, kowa daskarewa yayi nan tsaye, Ahmad ya kamo dan bakin gyalen daidai inda shima ya tabun, cikin kwantar da murya yace "Are you okay?" gyada kai kawai na'ima tayi, Ahmad ya juyo ransa adan bace yace da Laila "Are you blind?" Laila ta wani juya kai tace "to ai bansani ba" Nafisa ta harareta sannan ta isa gurin na'ima ta ciro hanky daga jakanta dake sakale a kafadanta ta fara gogewa na'ima jikin riganta..Sai sannan su Abubakar suka nufi gurin na'ima suna mata sannu, faruk dai na tsaye shida Adam.
Adam sai kallon abokin nasa yake da dan mamaki, Nafisa na goge wa na'iman jiki tace "muje restroom a dan wanke" ta kalli Ahmad tace "yaya bari muje restroom kawai" Gyada kai Ahmad yayi ya sake bakin gyalen na'ima suka wuce, Laila kaman ta fashe haka taji a wannan moment din, bata taba zaton Ahmad din zai nufi gurin na'ima ba, atake abubuwa dayawa suka darsu mata acikin rai.....

Bintu Musa ce ✍️📚

✨KUNCIN ZUCI✨
Na Bintu Musa

ArewaPen
https://www.arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c
Chapter 14 · 0% Book details