← Book details Kuncin Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 5 OF 32

Chapter 05

Kuncin Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Washegari da safe suka kai yayan nasu airport da motan anty amnah, hatta na'ima saida taji kaman tayi kuka balle nafisa datara fara hawaye
Faruk yace "come on girls, nan da 3 weeks or so zaku dawo fa kuma"
Nafisa ta qarasa kusadashi tariqo hannunsa tana hawaye, yana murmushi ya zare hannunsa,ya dagawa na'ima hannu alamun Bye itama ta daga nata hannun cikin sanyin jiki, ya juya na nufi cikin waiting lounge.
Na'ima tadan daga murya tace "Allah ya kaiku lafiya yaya"
haka suka koma gurin motan su cikin sanyin jiki suka bar airport din. Bayan sun koma gidan anty Amnah suka shirya kayansu tareda mata sallama suka tafi train station dan komawa oxford saboda motan da faruk din yaje daukansu na anty Amnah ne.

After that memorable weekend in London, rayuwa ta cigaba yayinda suka maida hankali kan karatunsu wanda saura few months su gama.
The weeks that follows sunyi
qoqari wajen hada wasu daga cikin thesis dinsu before the spring break, don dama auren Salman yazo within their break, hakan yasa lokacinsu yazamo swamp with schoolwork, dukda basa zuwa school din akai akai don sun shigo phase na research a fagen karatun nasu, wani lokacin raba dare suke zaune nan falo kowacce tana nata aikin bisa laptop

Duk da ayyukansu na makarantan da suka sako gabansu hakan bai hanasu zaman hira da cinye cinyen banza da hofi ba, Dan nafisa ta koyawa na'ima cinye cinyen itama basa zama shiru haka nan, aikace aikacen gidan nasu kuwa daman tun farko basu raba a junansu ba, duk wacce ta samu time yi take wanda dama na'ima ce rinjayen aikin da dafa musu abinci most at times, Kuma hakan bai taba damunta ba infact she love doing all the work tabar nafisan ta huta because she'll ba glad to do more than that to nafisa.
Ance kaso mai sonka, to hakan take wajen Na'ima, tanason kyautatawa nafisan
most at times takan shiga dakin nafisan ta gyara ko Ina ta wanke toilet sannan ta debo kayanta na wardrobe ta goge mata su tas ta jera. Wani irin bond ne mai tsafta a tsakaninsu wanda in ba wai sani kayi ba bazaka taba cewa qawance ne mafarin haduwarsu ba. Gashi dai ko daga yanayinsu mutum zaiga banbancin dabi'a sosai yayinda na'ima ta zamo mara hayaniya,don in kaga tana dogon surutu to da nafisa ne, ga hakuri da shanye komai a ciki while nafisa mutum ce mai surutu da rashin hakuri a wasu lokutan,
But friendship blend them together and became sisters from different mothers.

As lokacin tafiyansu gida yana kusantowa sai Na'ima ta zamo so uneasy ta zamo wata sanyi sanyi har nafisan tafara ganewa amma batayi mata magana ba saboda wasu dalilai
Ana gobe zasu tafi, na'ima na dakinta tayi wanka tana zaune gaban mirror tana shafe shafen ta na al'ada, bayan ta gama tacire hulan wankanta tana kallon kitson da sukaje saloon aka mata ta dauko wani hair oil tafara shafawa acikin lines na kitson tana tunani, bayan ta gama ta maida hulanta tasaka kayan baccinta ta hau gadon,ji tayi ta kasa baccin, ta jawo laptop dinta dake bedside drawer shima zata dan duba ko zai dauke mata hankali, shima tana dannawa ne absent minded, daga karshe kawai ta miqe ta tafi kitchen
bude cupboard tayi ta debo chocolates da cheese balls ta fito ta nufi dakin nafisa
Samunta tayi ta dora box dinta akan gado tana gaban wardrobe tana zaben kayanda zata koma gida dasu, Na'ima ta shigo ta zauna kan gado tana cewa "wai dama baki gama hada kayan naki ba?" Nafisa na tsaye ta kama qugu tana nazarin kayan wardrobe din tace "sai na hada sai kuma inji badasu nakeson tafiya ba" na'ima tace "Allah ya shiryeki nafee, hada kayan ma saikinyi ruwan ido bayan tulin kayanki da kika baro can gida" Nafisa ta juyo tace "Hey...it's not my fault, I want nice and big collections" Na'ima tayi murmushi tace "ruwan ido dai,bawani nice or big collections, kowanne so kike" Nafisa tace "wlh kuwa, duk wanda na dauko sai inga inason bari, kawai zan barsu Inaga" Na'ima tace "kinjiki, sai munje ki damemu da mita akan da kin dauki wasu,matsa in nema miki" ta amsa da toh tana dawowa wajen gadon ta dauki chocolate daya zata bare. Miqewa na'ima tayi ta tafi wajen kayan tana dubawa sukayi shiru na wasu mintuna sannan cikin kwantar da murya Nafisa tace "na'ima in bakyason komawa babu me saki dole..you know that" juyowa na'ima tayi tace "nafee we've talked about this over and over and i said yes, why don't you believe me?" Nafisa tace "the eyes don't lie na'ima I saw it in you, how you became silent these days, shin in tambayeki...why do you choose to deprive yourself happiness ne wai na'ima?" Ta miqe ta qaraso gaban na'iman tace "that pathetic,stupid person!! Should be the one hiding, not you" ta dafa kafadan na'ima tace "those vicious and wicked people should be the one's living unhappy now, not you Na'ima"
Fashewa da kuka Na'ima tayi nafisa na riqe da ita suka zauna nan gadon, nafisa na hawaye.
Tayi kukan tana goge idonta cikin sanyin murya tace "tsoro nake kada ayi forcing dina back to where i left, I don't don't know how to face what I've left nafisa" nafisa tace "Abba da mami bazasu taba barin hakan ya faru ba kinsani"
Na'ima tace "Amma dole watarana hakan ya faru" Nafisa tace " bance bazakije wajensu ba tunda bakida kamarsu, but forcing you back dinne ba wanda zai saki hakan, kuma kisani Allah yana tare dake a komai" Na'ima batace komai ba tana share hawayenta idonta na kallon kasan dakin.
Nafisa tacigaba "we will always be there, abubuwan da suka faru sun riga da sun faru,bance babu sauran gwagwarmaya agabanki ba amma what I want you to do is to Embrace life strongly as it comes,life is too short for you to be stuck up because of that stupid man, Embrace love when you find it,rayuwar nan bata jiran kowa  na'ima, it's high time you actually start living to the fullest" tana gama fadin haka ta miqe ta koma wajen kayanta tafara diban na tafiyan, Na'ima na nan zaune tayi shiru tana maimaita maganganun nafisa, encouraging words din suna shiga cikin kwakwalwanta.
May be it's high time she start seeing all of this in a different direction, duk abubuwan da suka faru a baya zata ajiyesu for now idan lokacin komawanta yazo Allah zai mata jagora.

Nan dakin nafisan ta kwana sukayi ta hiransu kafin suyi bacci
nafisa na bata labarin yanda umar ya dameta da kira wai zaizo daukan su in sun sauqa, na'ima tace "blocking dai ya fasu" nafisa ta ture ta da hannu tace "kin shiga uku da rashin mantuwa" na'ima ta kama dariya

Wayewar washegari suka tattare gidan sukayi storing abunda sukasan zai baci kafin su dawo sannan suka tafi airport dan jirgin safiya zasu bi
Jirginsu ya tashi zuwa Nigeria zuciyar na'ima cike da wani irin yanayin da bazata iya fassarashi ba.

Wattpad: Bintu Musa @bintuuu02

✨KUNCIN ZUCI✨
Na Bintu Musa

Read my book "KUNCIN ZUCI" on ArewaPen, Platform available: "all" :: https://www.arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c

WhatsApp group 👇
https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z
Chapter 5 · 0% Book details