← Book details Kuncin Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 4 OF 32

Chapter 04

Kuncin Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Basu wani dau lokaci ba suka Isa London,suka dau hanyar gidan anty Amnah dake arean Kensington.
Anty Amnah likitace kuma tana auren babban likita mazaunin London da yaransu twins maza kimanin shekaru bakwai. Sunyi murnan ganinsu sosai, twins sai tsallen murna suke.
Bayan sun huta anty Amnah tayi serving dinsu abinci sunaci ana hira

Daren ranan suna bisa gado cikin dakinsu wanda suke sauka idan sunzo gidan, Na'ima na zaune ta miqe kafanta hannunta riqe da ipad dinta twins suna kwance jikinta suna game tare, Kiran Abba ne yashigo wayan ta dauka da sallama tana gaisheshi, amsawa Abba yayi ta dayan bangaren tareda tambayanta ya karatu,tace  "Alhamdulillah Abba" yace "hope babu wani matsala" tace "Eh" yace "Ma Sha Allah, ku dage da karatu Na'ima,banason wasa" tace "in Sha Allah,nagode Abba" yace "Ina nafisan" ta amsa da "gatanan" tana miqawa nafisa wayan, bayan sun gama gaisawa da Abban taji nafisan na tambayan ina Mami, 
Suna cikin maganan dinki da Mamin ta miqo mata wayan bayan ta saka a handsfree, bayan sun gaisa Mami tace "Na'ima ga kayanku nan ansiyo wanda zaku saka a bikin, inason aika muku wajen me dinkin nafisan bansan wani kalan dinki kike so ba kuma" cikin sanyin murya Na'ima tace "kowanne kalla yayi" Mami tace "A'a badai kowanne kowanne kala ba,saka wayan a handsfree" Nafisa dake gefe tace "a handsfree yake fa Mami"
Mami tace "yauwa kinaji nafisa, ta fada miki kalan wanda takeso din sai ki turawa meerahn, nidai zan aika kayan gobe sai ku gama tsakaninku" Nafisa tace "toh Mami zanyi magana da ita a WhatsApp" da haka sukayi sallama nafisa tace "Meerah never disappoint, zansa ta turomin latest one's sai mu zaba"
Na'ima bata amsa mata ba  ta karbi wayan nata ta miqawa jabeer dake kusa da ita ya cigaba da game dinda sukeyi.
Suna nan zaune anty Amnah ta shigo dakin tace "sun hanaku bacci ko" na'ima tace "a'a game ai mukeyi" nafisa tace "anty ya faruk bai dawo ba?" tace "A'a" don tunda yakawo su nafisa aka taba hira dashi ya sake ficewa akan akwai gurin da zaije.
Anty Amnah tace "Boys, it's time for bed" jabeer yafara kukan shagwaba akan shifa a wajensu na'ima sai kwana tace "my friend get down from that bed" Na'ima tace "anty kibarsu mu kwana anan din" anty Amnah tace "a'a zasu takuraku, oya muje" Haka ta tusa kansu suka bar dakin tana musu saida safe.

Washegari suna breakfast gaba dayansu, nafisa ta saka faruk a gaba da roqon sai yayi rescheduling flight dinsa anty Amnah ma na tayata , mijinta da yake gurin yace "what if he has something to do back home" Anty Amnah tace " babu ma...beside, it's weekend. work can wait till Monday, right son?" faruk ya danyi dariya yace "zan duba available flight for Monday then" nafisa tace "zaka samu in Sha Allah" mijin anty dasuke kira uncle yasir yace yayi murmushi yace "su nafisa qorafi ya fara karbuwa" dariya tace tace "zai samu uncle"
Itadai na'ima tayi shiru tanacin abincin dake gabanta sannan tana sauraronsu, faruk ya amsawa nafisa da "I'm not sure yet" ya dauki wayanshi dake kan table din zai duba
Nafisa ta juya ta kalli Na'ima tareda kai mata qaramin bugu a kafada tace "kinaji inata faman roqo ko ki tayani" Na'ima tayi murmurshi batace komai ba tacigaba da shafawa jafar nutella a jikin bread, faruk ya dago kansa yace "habibtin Mami ko in tafi" dariya tayi kadan tace "a'a yah faruk" Anty Amnah tace "itama batason ka tafin ai, kawai nafisa tafita baki ne"
Faruk ya gama rescheduling flight din ya ajiye wayan yace "there... it's done, saiku shirya anjima mu tafi park" nafisa ta ajiye tea din hannunta tayi masa thumb up tace "you're the best" twins ma sai sannan suka fara ihun murna jin ance park

Haka suka tattara aka tafi park anty Amnah ta hada musu lunches dinsu suka saka a booth dan ita da Abban twins sunce baza suje ba zasu huta a gida.
Wunin ranan a park sukayi, acan sukayi sallolinsu suka ci abinci, faruk yasasu sun hau different wheels yana musu video sannan sunyi games kala kala shima har nafisa taci kyautan teddies ma twins, sunci banza sunci wofi dai sannan suka koma gida da yamma duk a gajiye.

Washegari wayewar sunday yakamata su na'ima su koma oxford don school, amma tunda suka tashi nafisa take mitan itafa ta gaji, bayan sun idar da sallah ta cigaba da mitan, na'ima najinta batace komai ba ta miqe tana linke sallaya.
Ganin na'ima bata kulata ba tace "sis ko mubari sai gobe?" Na'ima tana murmushi tace "Allah ya kaimu toh" dan tasan qarshenta hakan ce zata faru daman, nafisa tace "Kinga dama bawani lectures muke ba dama, it's not a big deal"  na'ima ta koma kan gadon ta kwanta tace "hakane anty Nafisa"
A gurin breakfast nafisa ta fadawa su anty Amnah bazasu koma school ba acewarta basuda wani active school activity ranan Monday din" faruk ya juya yana kallon Na'ima yace "dagasken take?" ta gyada kai tace "Eh" baice komai ba anty Amnah tasake tambayanta "na'ima are you sure" ta sake amsawa da "Eh dagaske ne anty"  nafisa tana murmushi tace "bafa karya mukeba" faruk yace "ai nasanki ne nafisa" anty Amnah tace "toh shikenan sai ku huta sosai, nima zanje hospital akwai patient dina dazan duba she's under my care" faruk yace "Ina uncle fa" tace "yana bacci tukunna, ya kwana a hospital jiya"

Yammacin ranan sai ga faruk da ticket na football match da za'ayi da dare cikin Chelsea stadium, one of the most known stadiums in London, tsalle nafisa ta rinqa yi kamar ba ita tayita mitan gajiya ba, itadai na'ima nata fara'a batasan komai gameda ball ba amma tanason zuwa taron itama don she's curious to see the match in person.

Dawuri faruk ya kaisu stadium din dan 8:00 pm za'a fara match din, bayan yayi parking a gurin da yayi booking suka fito zasu taka zuwa cikin stadium din babu anty amnah, tace batason shiga hayaniya kanta yana ciwo kuma ta gaji, shigansu cikin stadium din yayi gaba suna binsa a baya yana neman seat numbernsu. Nafisa ta juyo ta kalli Na'ima tace "Nice huh?"  Na'ima tana murmushi tace "it's beautiful..so beautiful" after sun samu gurin zamansu basu jima ba aka fara match din faruk ya miqe yace "I'm coming" yafara kutsawa cikin mutane zai fita daga stadium din, bai jimaba yadawo hannayensa riqe da popcorn da drinks ya rumgumosu a qirjinsa, zama yayi yana miqa musu yacewa nafisa "what did i missed?" ta amsa da "not much"
At first na'ima bata gane yanda wasan yake tafiya ba sai nafisa ke kwatanta mata kasancewar ita ta taso cikin maza a gidansu suna yawan kallon football match.
Cheering din mutane da ihun nafisa dake gefenta ne yafara sa mata interest sosai akan wasan, aqarshe dai da ita aka miqe ana ihu a stadium din. Ba qaramin nishadi match dinnan ya sanya na'ima ba, bakinta har kunne dan fara'a, faruk ya sunkuyo kusa da ita yana daga murya yace "do you like it?" Tana jijjaga kai cikin yar dariya tace "sosai"
Ranan taga football celebrities dinda ko a mafarki bata taba tsammanin ganinsu face to face ba, it's one of the nights that na'ima bazata manta ba.
Bayan an tashi daga match din suna komawa gida ta tambayi faruk "Kuma yanzu shikenan an kori dayan team din" yana dariya ya amsa da "Eh" ganin she's new to it, nafisa ta juyo daga front seat tace "BoBo zan siya mana tickets muje next match tunda kinaso" Na'ima tace "ai da dadi ne,bansan haka ball din yake da dadi ba"  nafisa ta juya tana kallon faruk sukayi dariya sannan ta juyo tace "welcome to the team girl"

Wattpad: Bintu Musa @bintuuu02

✨KUNCIN ZUCI✨
Na Bintu Musa

Read my book "KUNCIN ZUCI" on ArewaPen, Platform available: "all" :: https://www.arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c

WhatsApp group 👇
https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z
Chapter 4 · 0% Book details