← Book details Kuncin Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 7 OF 32

Chapter 07

Kuncin Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Sunga gata gurin Mami don tun kafin suyi wanka su huta ta fara sallamansu da home made juices datayi musu na musamman. Al'ameen ya shigo musu da kayan mami tasashi yakaimu dakunansu,
Bayan sun huta kadan anan falon suka nufi stairs gurin dakunansu dake jere gefen na Mamin, na'ima ce dakinta daf da falon mami
Tasamu dakin sai tashin qamshin turare yake, ko ina neat ta miqa hannu kan gadon ta dauko teddy bear dinda Abubakar ya taba kawo mata farkon zamanta gidan, ta rugume teddyn tana bin dakin da kallo kamar yau ta barshi,qarasawa tayi ta bude babban wardrobe dinta, nan ta ga kayanta jera cikin tsanaki sai qamshi suke ga sabbin kaya a gefe masu yawa an jera matasu wasu a hanger,
tana nan tsaye gaban wardrobe din a sannu farin ciki yake samun waje cikin zuciyarta aranta tace "I missed this" lallai tayi missing pampering dinda mami take mata, and she made the right choice coming back
Mami ce ta shigo hannunta riqe da sabbin towels wankakku tana cewa "Kinga dazu fa nace lantana ta jera muku su a bandakunan ku, ashe ta manta" na'ima ta qarasa da fara'a zata karbesu daga hannun Mamin, bata miqa mata duka ba ta dauki uku ta bata tace "sauran na nafisa ne" na'ima tace "bari nakai mata mami" tace "a'a kiyi wankan tukunna sai ku sauqa qasa ga abinci can, Na'ima ta amsa da "toh" Mami tayi murmushi tace "welcome home daughter" itama murmushin tayi kawai batace komai ba Mami ta juya ta fita daga dakin tajiyo shiganta dakin nafisa.
Bayan tayi wankan ta shirya cikin simple black abaya mara nauyi tayi daurin dankwali da mayafin ta fice, tasamu nafisa a falon har ta fito itama suna magana da Al'ameen da Abubakar wanda yadawo daga school babu jimawa.
Abubakar ya taso da fara'a yace "Anty nah oyoyo" na'ima na murmushi ta shafa kansa tace "kaima oyoyo".
Cikin walwala suka zauna nan falon aka fara hiran yaushe gamo.
Mami ta fito daga kitchen dinda ke babban falon  hannunta riqe da food flask tayi gurin dinning area tana jerashi jikin sauran 'yan'uwansa kan table  tace "abar surutun haka,kuzo kuci abinci tukunna" suka miqe dukansu suka qarasa dining din , bayan sunyi settling nafisa tace "Mami, Abba fa??" Mami tace "yana gurin aiki ai kinsani,bakuyi waya bane" nafisa ta janyo coolern dataga favorite dish dinta ta fara zubawa a plate tace "yacemin he'll be home when we arrive" Mami tace "bai baro gurin aikin ba tukunna" ta juya tana maida hankalinta kan Na'ima data fara cin abincin da ta zuba, tace "Habibti ki dudduba coolers din ko akwai favorite dinki" Nafisa tace "tuwon da ta zuba shine favorite dinta Mami" Abubakar juya yana kallon Na'ima yace "tuwo kuma anty" Na'ima ta gyada kai sannan tace "Ina yah faruk fa" Al'ameen yace "wannan ya fice aiki tun safe ai" Mami ta qara da "sai dare ma zai dawo halan, yace they have a lot of works" na'ima ta gyada kai tacigaba da cin abincinta.

Daren ranan bayan Abba yadawo yaci abinci ya huta sukaje gaishesa cikin babban falonsa, bayan sun shiga da sallama nafisa ta qarasa kusa dashi ta zauna tana fara'a tace "Abba" shima cikin fara'a ya amsa da "yaran Abba, kun dawo lafiya" na'ima ta qaraso zata zauna nan qasa yace "tashi ki zauna a kujera daughter"  tana dan murmushi tace "nan yayi" ya sake insisting ta tashi din sannan ta tashin ta zauna a wani kujera dan nesa dasu,Mami ta shigo falon hannunta riqe da tray na tea flask da cups akai na'ima ta miqe ta karba ta qarasa  ta ajiye nan table din dake gaban Abban ta koma ta zauna, Mamin ta wuce dakin dake nan falon yin uzuri.
Suka gaishe da Abban ya amsa yana tambayansu karatun nasu
Nafisa na tsiyaya masa tea din a cup tace "Abba abokinka dinnan has been very helpful a lot, watanni biyu ma dasuka wuce shi yakaimu London gidan anty Amnah" Mami ta fito daga dakin ta qaraso ta zauna nan gefensa itama, Abban yace "haka yakamata ai, kuma yana bani report ai yace kuna qoqarin karatun balaifi" ya juya yana kallon Na'ima yace "haka ko na'ima"  na'ima tace "Eh Abba" Mami tace "nafisa zaka tambaya don na'ima bani da haufin tana karatu" murmushi na'ima tayi tace "nafisa tana karatu fa sosai Mami" Nafisa tayi saurin amsawa da " sosai sosai ma" Atare Abba da mami suka juya suna kallonta, Abba yayi murmushi yana kai cup din shayin bakinsa while mami da na'ima suna yar dariya sanin halinta.
Sunanan falon suna hira Al'ameen yashigo falon da sallama yayi settling shima a kujera yadan dukarda kanshi tareda cewa "barka da dare Abba" Abba ya amsa then followed by Abubakar shima yaqaraso ya zauna kusada Al'ameen din.
Har kusan karfe tara suka kai suna hira, na'ima ta sake anata hiran da ita jefi jefi take sa baki, nafisa na bawa iyayen nasu labari game da rayuwarsu a England din na'ima na tayata kadan kadan, by then sun sauqo qasa itada nafisa da Abubakar kan babban carpet din dake shimfide a falon hannunsu riqe da kofin shayin da nafisa ta zuba musu daga cikin na Abban.
Faruk ne yayi sallama ya shigo cikin sanyi alamun gajiya a tattare dashi, yan'uwan na amsa masa tareda sannu, nafisa ta ajiye tea din ta miqe tana riqo hannunsa yana fara'a yace "yan gatan mami sun dawo kenan"  yajuya ya kalli Na'ima yace "habibtin mami, kun iso lafiya" tana murmushi ta amsa da "lafiya yaya" suka gaisheshi gaba daya ya amsa tareda zama nan qasan carpet shima yana me gaishe da iyayen nasa, suka amsa Mami na tambayanshi gajiyan aiki  Abba yace "arinqa sararawa jiki da brain din dai babana" faruk yace "Abba aikin ne these days suna buqatan lokaci sosai" Abba yace "Allah ya bada sa'a" ya amsa da Amin Mami ta tambayesa ko yaci abinci ya girgiza kai. Nan falon nafisa ta kawo masa abincin yanaci aka cigaba da hiran dashi cikin raha.  
Cikin walwala da fahimtar juna iyayen ke gudanar da hiran tsakaninsu da yaran nasu, wanda hakan yasa yaran suke bude cikinsu openly suna fadan abunda ke mind dinsu wajen iyayen, idan fannin gyara ne take iyayen suke gyara musu cikin lumana,idan na raha ne suma ayi dariyan dasu.
And for that moment
Na'ima knew..This is home
These people right here
Are like missing piece of her heart
And she won't trade them for anything.

Wattpad: Bintu Musa @bintuuu02

✨KUNCIN ZUCI✨
Na Bintu Musa

Read my book "KUNCIN ZUCI" on ArewaPen, Platform available: "all" :: https://www.arewapen.com/book?id=690bd06dec64f173aa42354c

WhatsApp group 👇
https://chat.whatsapp.com/JcjTYhJtKFh92V5nqhBk3z
Chapter 7 · 0% Book details