← Book details Kece Sirrina Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 20

Sashe 8

Kece Sirrina Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bayan dawowarmu Nigeria ne naga yana nunamin wasu halaye da d'abi'u wanda basu daceba. Nacemishi banason irin haka bazantab'a yarda wani abu yashiga tsaninmu inhar bamuyi aureba. Yanunamin cewa banwayeba inaduk karatun danayi baida amfani. inwani abu yashiga tsakaninmu ma aibawanda zaiji tunda aure zamuyi. Ahaka haryarink'a jan ra'ayina.
ranar wata laraba ranar dabazan tab'a mantawa da i'taba.......... Tarushe dawani uban kuka........ Kowa saida yaji tausayin zury a falaoun nan yadda take kuka kamar ranta zai fita sukarink'a batahak'uri Allah zaisaka miki. Tacigaba....... "Ranarne yajani wani hotel yaje yarabani da mutuncina na 'ya mace......kuka kamar zata shid'e.

Alh Gaddafi gaba d'aya yayi shakaf da gumi. Sumy sai tsitstsillo i'do takeyi.
" bayan wata biyu da faruwar hakan nagane cewa inada juna biyu, bak'aramin tashin hankali nashigaba. nasamu Muh'd da maganar , Muh'd yanunasam baisan zancenba sai nadage masa sosai nacewa ba namijin dayatab'a rik'e koda yatsanane saishi sannan yayarda amma abisa sharad'i nacewa saidai inzubar dacikin.... Inanalillahi wai'nna i'laihirraji'un duka na parlour n suke fad'a....
" Nace niban yardaba don bazan aikata kisan kaiba. Daganan Muh'd yanuna cewa kar insake nai man shi, bani bashi tun.
Tunlokacin haryanxu bankumajin d'uriyarsaba har rana maikam tayau. ......... Saidaga baya nakejin ashe yasaba yaudara, sai yanuna yanasonka sai dab da aure bayan yagama lalata 'yar mutane sannan yace yafasa.....yanxu haka last 4month dasuka wuce yanuna yanason wata yarinya da aure, daga baya yawula k'anta yarinya da i'yayenta don sai ranar d'aurin aure da safe yad'auki yarinya akan cewa zata rakashi unguwa haka yalalata yarinya kuma yace yafasa auren haka yabama Iyayen yarinya kunya bayan sun gama gaiyyatar yan uwa da abokan arziki"......taja wata uwar majin tana share hawaye.

Alh Gaddafi yasake wani nauyayyen numfashi. "To shi i'na iyayensa, basusan yana aikata irin abubuwan nanba ne?."

" wannan i'yayen nasa ba i'yayen kirki bane ba mutanen arzaki bane don duk abinda yakeyi dagoyon bayansu da had'in gindinsu yakeyi."

Alh Gaddafi yatarzoko don duk yayarda da magar Zuwairat. "To wllh zan basu mamaki, zasu gane kuskurensu don kafin subani kunya nizanbasu kunya bazanbar yata ta auri fasiki mazinaci ba."

"wllh daddy K'arya sukeyi bahaka Dr yakeba."...... Sumy tafad'a tana shishshure k'afa.

" Ke dalla can rufe maba baki kinga wani alamar Karya ko rashin gaskiya tattare da baiwar Allah nnane? Don haka duk abinda tafad'a bakarya acikinsa......yayar mahaifin sumy ne ke wannan fad'ar. Mommyn sumy tace "gaskiya kam don wannan dagani salahace bazatayi k'aryaba. "

Zee tadubi sumy tace " inkina ganin wannan maganar k'aryace ki bari a zo d'aura aurennan. don sai mahaifinki ya yattaro yan uwa da abokan arziki azo a watsamasa k'asa a i'don, inkinci sa'a ma baiyi reping dinkiba."

Alh Gaddafi yace "bayin Allah nagode nagode sosai da kuka kawomin wannan agajin. Allah yasaka mukada akhairi , kuma Allah yasaka miki wannan zaluncin daya miki."
duka suka amsa da amen. Sai godiya akemusu. Haka suka tashig za su tafi ....... Zury dakyar tatashi tana cize lebe tana rike baya.
sai sannu akemata. Hakasuka fita sai godiya da sa albarka akebinsu da i'ta.

Gurin mai gadin gidan suka nufa. "
a harkun fito?"..... Megadin ya tambayesu.
"Eh wllh harmun fito zamu tafi. " suka wuce abin su.

Suna fita suka tafa zury taciro kayan data tusa acikin , aikinmu yayi 👍🏻.

titi suka nufa don samun abin hawa, sunazuwa kuwa sukasamu saigida..........................

*UrS QuEeN BEE MaRaFa💋*
[9/8, 5:42 AM] Queen BEE Marafa💋: *KECE SIRRINA 2⃣0⃣*

*°°In Dedicated to KHALEESAT HAIYDAR°°*

*♻ €°W°F♻*

NA___
Habeeba Muh'd Marafa _*{HM²}*_

_________________
Biki budiri gidan alh khabeer saishiye shiryen biki ake.

______Neenah ce kwance akan k'aton gadonsu, i'don ta alumshe kamar mai bacci amma babacci take. Mommyn Neenah wanda sukazo tun kwana tud'u dasuka wuce.
I'ta da farida sukashigo. "Yawwa mommy kinganta ba kullum haka i'dan an tambayeta tace bakomai".
haj farisa tazauna a gefen 'yartata tad'aura kanta bisa cinyar ta rik'e hannunta cikin nata. A hankali neenah tabud'e i'don. tasakarma mommy nta murmushi, itama mayarmata tayi. "Sweet neenah".
"Na'am mommy."
Tashafi gefen fuskarta. " my neenah kifad'amin abinda ke damumki karkib'oyemin ko mai, kingani mommynki CE ko?".
"Eh mommy, Ammni ba'abinda ke damuna kawai dai banason hayaniya ne saisa nakezama na ad'aki.'

Neenah tafad'i hakanne kawai amma i'ta kanta batasan meke damuntaba.

Farida dake gefe tace "mommy k'arya takeyi akwai abinda ke damunta, karki yadda saita fad'a miki."

"To ko auren ne bakiso?."

Neenah tazsburo bashiri " lalala mommy wllh i'naso Allah."

" A yo nazata bakyaso yanzu insa a tsada auren, kinga sai ayi na ya Muhammad da farida kawai."
Neenah harda d'an hawayenta " wllh Allah mommy i'naso kuma ni ba'abinda ke damuna barima kiga."
Tasauk'a k'asa tafara tsalle2 da rawa. Farida da mommy sai dariya suke mata. Farida tace "mara kunya agaban mommy n kike kuka akan Khalil. Hhhhh Zakiyi bayana kikashiga hannunsa ai. (Niko araina nace lallai farida harkene zakima wani maganar kunya keda agaban kowama tsula tsiyarku kuke keda salim. Hmmm.)

"A To inbazaki saki jiki kirinka shiga cikin jama'a kawai zansa a katsa aurennan."

" A'a wllh mommy zanrinka shiga. Barima kiga".
tad'aura dogon Riga akan bes d'in dake jikin.
"Mommy kuzo mujeto." takama hannunsu sukafita.

_________M.k gabad'a yafita hayyacin, ba damur aurensa kedamunsa ba neenah ce kedamunsa. tadami zuciyar sa kullum yana rik'e da kirji jiyake kamar zuciyar zata fa don zafin datake masa. Dukya rame yayi wani iri.

(O kamar ba m.k mezanen tattoo ba tattoo duk ya goge ba'ayi waniba😂).

Fauzan ne yatasashi agaba dole saiya fad'amishi abinda ke damunsa. " yanxu Muh'd har akwai wani damuwarka dazaka i'ya boyemin?, wllh banyi tunanin taha daga garekaba. Ko auren ne bakaso? Tunda banga wani alamu nafarinciki dakakeyiba".

"Hmmm fauzan bazaka ganebane. "

"aikuwa kam bazan ganeba tunda bazaka fahimtar daniba, amma intai tsami zamuji ai."

"Tau nidai yanzu frnds d'inmu sai damuna suke wai evens wanne da wanne za'ayi?."

" Ba abinda za'ayi."

"Kamarya ba'abinda za'ayi mifa banason rashin mutunci. "

" Wani irin rashin mutunci?, nifa bawani even daza'a don ko sisina bazan bayarba".

"Banza matsiyaci. dama saboda bakason bada kud'inka saisa kace baza'ayiba?".

"Kai banason buroubanci fa dan iska kawai, aiba shegen dayake nemamin."

" Oho makade mude zamu had'a pertyn mu, kuma wllh naga kafar mutum agurin bazai fito da i'taba don ballata zanyi."

"Aikin banza kawai ubanme dama zaikaini Allah yakiyaye."

Haka sukagama fad'ansu nabanza da wofi wanda anjima kad'an zakagansu suna shek'a dariya.

______________________________
Around 9:34pm, Alh khabeer ne da i'yalensa gakuma d'an uwansa da matarsa duk sun hallara a parlour n sai hira suke cikeda nishad'i . wayar alh khabeer ne tafara ringing picking yayi batareda yaduba wayeba yakara a kunnenshi.

"Assalamu alaikum".

Daga d'ayan bangaren naji ance "babuk'atar wannan. Inafata kagane dawanda kake magana?".

Abba da mamaki yagama mamayeshi yace " a'a."

"To alh Gaddafi ne!."

"Alh Gaddafi" abba yarink'a nanatawa a zuciyarsa. Hankalin kowa yadawo kan Abba ganin yadda lokaci daya yanayinsa yasanza.

" kasaurari dakyau abinda zan fad'amaka. Kai gaggawar dakatar da mutanen daka gayyata d'aurin auren d'anka don cutar da 'yata. Ashe danka fasiki mazinaci ne saisa akeson lakama yata a cuceta to asirinku yatonu kuma alkhadarinku yakara, duk wani iskancin da d'anka yake aikatawa kake goyenishi baya nasani. Don haka nakesanar dakai karnaga kafar wani mutumin banza kofar gidana dazancen yazo d'aurin aure, inba hakaba zansa a d'aure mutum kuma har abada bazai fitoba . abu nak'arshe banason batun wani bada hakuri ko makamancin haka, don 'ya tawace kuma nafasan auren sanan k'azaman kayanku dakuka kawo suna k'ofar gida kuzo Ku d'auka!!!!."
Kit yakatse wayar.

Abba dayayi mutuwar zaune, ba'abinda zuciyarsa yakeyi sai tafasa . "yau ani akefad'a ma irin wad'annan bak'ak'en maganganun don na nemawa d'ana auren 'yarsa balaifi."
A fili yake maganar .

"ha'a wani irin magana kuma Abba?..... M.k ya tambayeshi. Abba yayshiru zuciyarsa na tafarfasa. Alh mukhtar yace" wai mayake faruwane yaya? duk kasamu duhu don Allah kafad'a mana."

" Ko wanine yamutu?"..... Ummi ta tambayeshi. Yagirgiza kai.

" To dan Allah kasanar damu mana".....mommy tafad'a.

Abba yafara magana ya irgemusu duk yadda sukayida alh Gaddafi.

Daddy yayi matukar harzuka" wayeshi dahar zairink'a gayawa mutann magana don mun nemi aure agunsa wayeshi?." Yatashi a fusace .
"Muhammad d'aukomin key d'inmota inje nanuna masa shibakowa bane shidin banza da wofi.......hakuri akebawa dad amm fad'a yakeyi.... Abba yace "mukhtar kazauna". Daddy yazauna zuciyar sa na watsatstsaka.

Abba yace "abun bab'ukatar fushi. Muhammad abinda nakeso dakai shine kakwantar da hankalin kacire yarinyarnan aranka Allah zaibaka wanda tafita. ( Very very soon ma kuwa). Shikenan banason k'arajin wata magana akan haka."
Daganan Abba yatashi Yay part d'insa.

M.k dawani farinciki yadirarmai a zuciya yarinka hamdala "wannan koma waye yaje yahada wannan abu bak'aramin taimokona yayiba. Gefe guda kuma inyatuno da auren neenah da Khalil bafashi saiyaji kamar ana kuzamishi ruwan zafi...... Maganar daddy ne yadawo dashi.

" kowa yaje yakwanta dare yayi."
Haka kowa yay nasa guri zuciyarsu duk ba dad'i.

_____________________________
Washe gari Friday.
ranar d'aurin auren: neenah da Khalil, farida da Salim m.k kuma ................

*Kawai kumin addu'ar samun miji nagar🙈* _nd to get money💶💵😜_.

_Love you mah fans😍😍😘._

*UrS QuEeN BEE MaRaFa💋.*
[9/8, 5:42 AM] Queen BEE Marafa💋: *KECE SIRRINA2⃣1⃣*

*°°In Dedicated to KHALEESAT HAIYDAR°°*

*♻E.W.F♻*

NA____
Habeeba Muh'd Marafa _*{HM²}*_

_________
Raran m.k kokad'an baiyi bacci ba , ga tsananin ciwon da zuciyarsa kemasa in yatuno da auren Khaleel da rayuwarsh. duk maganin dayasha abanza jiyake kamar ana karamishi.numfashinsa saiwani sama2 yakeyi yanajin wani iri. m.k salati yafara don yaukan yasaddak'ar mutuwa zaiyi. Dakyar yalalubo wayarshi yay dealing Num din fauzan, don yafad'a mishi Sirrin zuciyarsa kafin yabar duniya.

A cikin gida kuwa saishagalin biki akeyi kowa kaganshi kasan yanacikin farin ciki.

_Sa'ada banbili_ akad'auko musamman don yiwa amare da 'yan biki makeup. Inkaga amare biyun nan bazaka ganesuba especially neenah datake wani shek'i da silb'i sunyi balain kyau harsun gaji da hedewa. Farida sai rawar kai ake, jitake kamar takai kanta gidan Salim .kawayen su sunzo sosai inkagansu anci gayu kowacci tanaji da kanta bak'arya 'ya'yan manyane.

Neenah farida sai frnd d'insu, suna zaune a babban falon baki sai hira suke akan zancen aure .
neenah data zuba uban tagumi agefe tanajin duk irin iskancin dasuke.
Chapter 8 · 0% Book details